Makaranta duniya chapter2
Makaranta duniya
Chapter2
Gwauron numfashi alhaj yaja hakanne ya jawo hankalolinsu cike DA tausayawa malam saddiq yace kayi haquri alhaj
Rai bace mudassir yace to wai zaman me muke KO wulaqancinne bai ishemuba alhaj ya katseshi ta hanyar kallonsa gamida cewa ai Allah ya rufa mana asiri mudassir don haka mum wuce wulaqanci kaman zaiyi kuka yace to mu tashi mu tafi mana malam saddiq ya tashi tsaye alhaj tashi mu tafi kar dare yai mana anan daqar ya cicciba ya tashi tashinsa keda wuya murja ta leqo ahh baba kunata zamako Ku shigo daga ciki mana alhaj din yace a.a ai munyima haramar tafiya fuska a yamutse tace daman ba kwana zakuyiba yace a,a komawar tamu Ina gani shi zaifi kumama munyi haramar tafiyan mun barku DA alkhairi jikinta yai mugin sanyin DA harta kasa furta wata kalma
Tana kalonsu sukaja takalmansu sukai waje kana ganinta zaka fuskanci akwai don damuwa a tare DA ita daga yanayin yaddah take nade tabirman tanayi tana kada Kai tunda suka fita babu Wanda yacema kowa komai illah mudassir daketa surutansa babu Wanda ya bashi amsa kuma babu Wanda ya hanashi har suka samu Mai taxi ya kaisu Tasha shagon wani abinci suka shiga kowa yaci ya koshi suna fitowa sukaji Ana kwada Kiran sallar LA,asar don haka suka fada masallacin dake tashar domin sauke farali suna kammalawa ba tare DA bata lokaciba suka hau motar Kaduna cikin ikon Allah kuma ta cika nanda nan
Misalin qarfe shadaya da rabi suka Iso Kaduna cikinma anguwarsu nan suka tsaya sallama a qofar gidan malam Sadiq don daman gidansa zaka Fara isa kafin ka isa gidan alhaj abdurrashid din kowanne daga cikinsu bama dan uwansa haquri yake don gani suke kaman KO wanne daga cikinsu ya cancanci DA,a kwantar masa DA hankali sannan sukai gaba sukabar malam Sadiq yana kwankwasa qofar gidansa ya kwankwasa yakai sau uku sannan matarsa asiya taxo baking gate din tana tambayar waye yace bude nine mun dawo cikin qanqanin lokaci ta gane muryar Mai gidan Nata don haka duk wani far DA shakku ya fita daga zuciyarta nan tasa hannu ta zare sakatan ahh Baban yara kune DA dare haka ? Yaqe yai mata Wanda akace yafi kuka ciwo
Ya shiga gidan gamida kullewa tace ba kwana daman zakuyiba inace kwana kace zakuyi yace kedai Bari kawai Ki godema Allah kawai Daya dawo damu lfy tai murmushi gamida cewa aiko shine abin godiyan namu akoda yaushe a tare suka fada daki ya dubeta ya yara tace duk sunyi barci suna dakinsu sannan ya numfasa tace to me zakaci yace idan kinada ruwan zafi hadamin shayi kawai ya isheni Amman saina Fara watsa ruwa tace to shikenan ta nufi kichin shi kuma ya nufi bangaren DA bayi yake a cikin dakin ba,a jimaba ta kallama hada masa shayin shima ya fito sanye Da jallahbiya ya zauna yanasha suna hira Amman bai fada mata abinda ya faru a bauci ba
A gidan alhaj abdurrashid kuwa suna shiga aka game babu kwanciyar hankali a tare dasu a falon hajiya suwaiba suka zube gabaki dayansu mudassir yace Kai yau munga wulaqanci yaya imam kaima Allah ka duba girman iyayennan namu guda biyu ka kyale jamila ka cireta a rayuwarka” cikin rashin fahimta hajiya suwaiba tace wulaqanci shi sulaiman dinne ya wulaqantaku KO murja nanfa mudassir ya kwashe duk abinda ya faru ya fada musu hajiya suwaiba ta share kwallan data zubo mata tace tabdi Allah abin tsoro mutum abin tsoro yanxu a gidan suleman kuka fuskanci wannan wulaqancin babu komai kansa yai mawa dagashi har murjan zasu gani a kwaryan cinsu
Kai kuma imam wannan ya zame maka darasi don kafiyarkace ta jawo wannan cin fuskanda akai mana in banda haka me akai akai sulaiman balle abinda yake hangen yana dashi kayi haquri imam ka cire jamila a ranka baka DA makusa Ina Mai tabbatar maka idan ka wallafama Allah komai zakaga canji mafi alkhairi Amman fa idan kabi abinda nace
Alhaj yace shi kenan komai ya wuce sulaiman dai namu ne don haka yaje rayuwace Kuma makarantar duniya azuzuwa gareta masu yawa duk ajin daka Shiga akwai irin karatun DA zata koya maka KO Mai sanyi walau Mai zafi Sannan ta yayeka ta nunama jama,a idan na cizon yatsane ka ciza harka kuntsire dan yatsan naka babu Mai kallonka
Yanxudai saikayi haquri Sannan don Allah mu riqe wannan maganan a cikinmu Sannan mu taya IMAm DA addu,a
Hawaye shar ashar suka zubo daga idanun NASA yai saurin miqewa yabar dakin hajiya suwaiba tace na taba ganin sakaran yaro irin imam ace ka kwallafa rai akan Abu Daya koce masa akai komaine Idan mutum yakeso yake samu mtwss…
Alhaj yace yanxu dai sa masa Ido zamuyi hukunci dai uban jamila ya yanke to meye namu a ciki hajiya suwaiba tace to tuwon zaku tuttura yanxu zai wuce kuwa alhaj yace ni bana marmarin komai banmajin yinwa alwala zanje na dauro nA fara nafiloli hajia suwaiban tace kaidai Bari a kawo maka kar yinwa ta hanaka barci nan suka barta DA takumi duk sukai waje suka barta DA jimamin abinda sulaiman yai musu don ganin abin take kamar a mafarki
Muddassir ne ya shigo dakinsu DA kwanon abinci a hannunsa ganin halin DA yayan NASA ke ciki yasa ya donkwafar DA kwanon gamida jan wani dogon tsaki yace Allah yasadai yaya wannan kukan DA kake na wulaqanci DA muka Shane imam ya dago DA idanuwansa sunyi jajir yace meka Sani Kai meka Sani mudassir yace kamar ya mena Sani?yace yaddah zuciyata ta kamu dason jamila ba
Mudassir ya juyo rai bace baisan sanda bakinsa ya subuce ya furta Amman indai hakane Allah ya tsinema wannan zuciya taka yaya imam bakai baqin cikin wulaqancin DA akaima abbanmu ba wai kaman yaya sulaiman ne zai dubi idon baba wai yace dashi Mai yasa bai kirashiba kafin yaxoba kuma su hanamu abinda zamuci mu tashi tun daga Kaduna zuwa bauci
Amman ka kasa zubda hawaye akan wulaqancin DA akai masa Amman wlh kaban kunya yaya imam jamilan banza jamilan WoFi wacce dubunta ke yawo a gari a gobe idan kaga dama zaka Iya samun wacce ta fit a Amman mahaifinka har abada baka isa ka samu Wanda ya fishi a garekaba KO kuma ka canja……
Ya data masa tsawa Kai mudassir dakata karkai tunanin DA tsaranka kake magana ballentana har Kai tunanin kawomin raini kodan Allah ya jarrabeni har kaga ruwan hawaye a idona!
Sukai shiru na Yan sakwanni suna kallon juna kamin imam yaci gaba DA cewa ba laifina bane sannan bawai bana baqin cikin wula qancin Dana jawo ma baba bane wlh har dashi ya sanyani kuka ace kamar yaya sulaiman ya kasa rufa mana asiri
Amman inason ka gane jammila ta zauna cikin raina yaddah baka tsammani bansan lokacin DA nayi zurfiba Dana Sani dabanyi wasa DA rayuwata ba
Yaddah zuciyata ke qonewa a yanxu komai na Iya faruwa Dani Ina zansa kaina yau wlh Ina takaicin wannan ranan DA bazan Iya sarrrafa kaina ba
Ya fadi ta baya bisa shimfidarsa mudassir najin wucewar numfashinsa DA sauri DA Sauri mudassir ya yafito kofin ruwan Daya shigo dashi yasa hannu ya kamfato ya shiga watsa masa
Yaya ka daure mana haba yaya imam haka yaci gaba DA shafa masa ruwan har a hankali ya samu ya lafa Ido jajir ya dubeshi haba yaya daman haka kake
Murya dishes ya amsa Ido tam da kwallah meya faru naga ka jiqani DA ruwa?yace kamar zaka mutufa yaya wannan bai kamacekaba qara bamu kunya zakai har idan yaya sulaiman yaji wai har suma kake SBD jamila ya kamo hannayensa ya riqe tamau yace karka fadamasu baba insha allahu daga yau na cire jamila a raina baxan sake tunanintaba balle rashinta ya dameni ya zuba masa Ido Allah yasa yaya zanfi kowa murna idan har hakan ta kasance
Yanxu abinda ke gabanmu yaddah zamuyi mu tallafama iyayenmune don Susan sun haifi yayan halas don girman Allah yaya ka kwantar DA hankalinka
Ya fada a raUnane karma damu muda insha allahu zanyi qoqari kaje ka kwanta abinci DA bai iya Ciba kenan haka ya kwana DA yinwa
Kwana biyu kenan gidan alhaj abdurrashid na cikin tashin hankali saidai bawai abinda sulaiman yai musu baneba a,a saina rashin ganin imam DA sukai
A gidan tun safiyar jiyan hakanne ya gigita zuciyarsu
Tambayoyine cike a zukatansu N me imam yake nufi sannan Ina yaje?
Wannan tambayoyinne ta Hana iyayensa sukuni musamman ma mahaifinsa yace shin Ina Iman yaje Mai imam din yake nufi Mai zaisa yaimin haka nida nai Iya qoqarina wajen ganin burinsa ya cika ya tsame hannun NASA cikin tuwon malam saddiq yace kayi haquri alhaj insha allahu Allah zai dawo mana DA imam har Gida alhaj yace dole na damu malam saddiq imam ya shiga raina tun sanda na haifeshi yaron ya zauna a cikin zuciyata to damuwansa damuwTace baxan tabajin dadiba idan har baya tare Dani malam sadiiq yace karka damu munanan muna adu,a insha Allah imam zai baiyyana cikin ikon Allah
Mudassir ne ya fado falon babu KO sallama idonsa a rufe bakinsa kawai ke fadin baba yaya imam ya haukace yaya imam ya haukace baba gaba dayansu ya gigitasu duk suka miqe tsaye inna lillahi wa,inna ilaihirrajiun malam sadiq ya riqeshi Ina yake yanxu?a Ina ka ganshi ? Ya fashe DA kuka cikiin sheshsheqar kuka yace yanxu aka kamoshi a abuja road yana tafe yana sumbatu suka sake daukar salati man take zuciyar alhaj abdurrashid ta buga
Hmm lol
Naku har kullun
The C. E. O. @littafan Hausa zallah