Makaranta duniya chapter21
Makaranta duniya
Chapter21
sulaiman! Ashe kalau’ ka ke shi ne ko dan sako mu san
ka na lafiya’? Duk ka ruda ‘mu, matarka na can cikin damuwa‘.”
Ya yi wata yar dariya yace”Kuma dai Baba dason damun kanku ku ke. Saboda Allah bata zan yi?” Yace “Halin mota ake ji, mutum ya bar gida sati uku‘ daga lntabiyu, ka ji shi shiru babu labari, dole hankali’ ya daga mana”.,Yace To ya sauka, gani kalau na riga na kama aiki ne, shi ne na bari karshen wata in taho in gayo maku”. ’ ‘_ ‘
‘ Alhaji ya sauke ‘numfashi, sanyi ya ratsa zuaiyarsa, yace “Masha-Allah! To Allah ya tsare, sai a kula da .hakkin ‘jama’a, domin amana ce aka damka “maka. Yanzu’ a ina ka ke zaune?” Yace “Ina tare da wani ma,aikacine~ mun saba tun lokacin da na yi sabis’muka hadu “Yana da kyau. Ni bari in koma, tunda na ganka”. ‘ Yace “Kai haba Ai dai ka bari zuwa gobe”. Ya. ‘ dubi agogonsa, “Saura dan lokaci kadan mu tashi, mu je ka jira.- ni sai mu wuce tare ko?” Yace “Ba laifi,
amma tunda la’asar ta yi, bari in yi sallah a masallaci. Zan ma jira ka ka sameni nan”.
Yace “Shi kanan”. Tare suka wuce, ya raka shi masallacin ma’aikatar, ya yi alwala ya shiga. Shi
kuma SUlaiman ya koma ofis. ‘
‘ wash gar-i da wuri Alhaji ya koma, bayan ya kara yiwa Sulaman nasiha akan’rayuwa, musamman abokin daya gansu’tare, hankalinsa bai kwanta da shi
ba. Bai karbi komai wajen Suleman ba, ko wanda abokin nasa ya‘ bada a ba shi’bai karbaba cewa ya yi yana da kudin motarsa. Alhaij ya dawo, ya tabbatar wa kowa Suleman na nan lafiya lau, aiki ya kama nan take. .
Murja ta ji sanyi a ranta, sai daiSuleman zai. zo yau, zai zo gobe, sai da ya shafe wata uku cif! Babu sako. Rannan kwatsam! Ya diro kamar daga sama. Har ya fara canzawa, yana neman yin kiba. Tsarabarsa cikin jaka. .
‘ anan ‘ ~ya samu har su gwaggo da mahaifiyarsa, kowaya yi ta sa al’barka. Ranar lahadi da yamma, yai shirin‘ komawa. Murja ta yi ta rokonsa kar ya kara dade,wa irin na farko
Yai mata alkawérin hakan,’tare da ba ta kudi. masu dan dama, yace ta aje koda za ta bukaci wani abu ko Jamila, ko kUma lalurar rashin lafiya. Ya fito yayi sallama da su Alhaji, ba tare da su ya ba su wani abu ba.
‘ Su ko tunanin hakan bai zo cikin ransu ba, Amma tsarguwa ta sa yace Kuyi hakuri Mamanmu, kudin sun kare, sai dai wani zuwan”.’Ta wangama baki .tace’ ” ‘
‘ ‘ “Haba Sulaman, yaushe aka fara aikin? Kuma banda abinka, wannan zannuwan da ka gwangwajemu
da su, ai sun isa. Allah yasa albarka, yakuma tsareka daga sharrin makiya”. –
Alhaji yace, “Amin Suwaiba. Kin kare magana, kaidai ka kula da kanka. ka kula da amana! Ka ji ,binda nace?” Yace Naji Baba .sai na sake dawowa.’Duk sukace “Allah yatsare”.
Ya mike suka fito tare. Murja na tsaye tsakar gida sabe da Jamila. Ya kama hannunta ya yi mata wasa,‘ya’wuce suna ta masa addu a, ita da Mama A shago ya gasu Imam da Mudansir, Ya tsaya yai masu sallama su ma, sannan suka wuce tare da Alhaji. Sai daya raka shi bakin titi, ya dawo
Wata daya ya kare. Sulaman bai zoba, wani, ya shiga, shi ma ya kare. Murja ta fara shiga damuwa. Me ya sa Sulaiman ya saba mata ,alkawari? Abin na‘ ‘ damunta, tana mamakin hakan.
Me ya sa da bata damu da-zamansa wani wuri , shi kadai ba, sai yanzu? gaskiya ta kasa gane dalilin, daurewa kawai take yi. ‘Yan kudin daya bar mata ma sun kusan karewa, dun sau ‘da yawa,‘idan ta lura babu kudi agidan, ta kan dauko ta bada ayi cefane.’
Me zai faru’? A‘karshen wata na biyu, ta fara
fama da ciwon ciki,- amai ya biyo baya. kowa ya
dubeta, ya san ciki gareta, saboda haka Mama ta‘ dauke mata wahalar Jamila, domin ba ta dade da yaye taba har yanzu tana taba rigima. A dakin ta take yini, tana kwana, da yamma Imam ya murmusa ta a baya,
su tafi Islamiyya su ’uku;
~ Tun ana koro shi da ita har Malaman suka
; hakura. suka bar ta, ‘tana‘ tsinta a karatun. domin
sosai zaka ji ta tana yi a gida
Wannan karon ma watannin uku Suleman ya yi, sannan yazo gida. Ya iske Murja cikin laulayi. farin~ ciki ya kama shi, ita kuwa ta canja masa fuska, sai da yai ta rarrashi, sannan ya samu kanta. Wanan zuwan ma ya kawo wasu Mama sunkin sabulai da mayukan shafawa.
Sannan washe gari ya shiga kasuwa ya siyo
masu galan na manja da ledar Magi. Hadi da‘tiyar‘” gishir’i. Suka yi ta sa masa albarka. kafin Alhaji ya” umarce shi da ya samu wani abu ya kai wa jama’an
Dutsen Abba, ya gaishe su.
‘ A hakikanin gaskiya bai yi niyyar zuwa ba, a tunaninsa Kauran Juli kawai za shi ya dawo, alhali wancan zuwan ma da ya yi bai je ya gaida dangin Babansa ba.
Buhun omo ya siya. can ya fara sauka. ya gaida su a tsaitsaye ya wuce Su kowa murna’kawai suke yi, suna masu alfahari da shi, ganin ya fita.daban da kowa a cikinsu. ‘
Shi kansa ya dade da sanin hakan, shi ya sa yake matukar ji da kansa. Bayan ya tafi. suka yi ta rabun buhun omo, wanda saboda yawansu, kowa gwangwani‘biyu ya samu.
tsarabar Sule daga birni. lol
Wannan tafiyar ma da zai yi, ya aje wa Murja kudi har sun fi na wancan karan yawa, saboda yanayin da take ciki, ya sa kafa ya yi tafiyarsa. Hajiya Suwaiba na ganin yadda Murja ke falle kudi take cin abinda take so, amma ko alama zuciyarta ba ta taba raya mata wani abu ba. illa ma farin-cikin Murja na samun abinda ya kamata, mai juna biyu ta rinka samu. lta ma ba ta da rowa. domin duk abinda ta siyo, ko Mama ta sani ko ba ta sani ba za ta kawo mata ta tara yaran duka SUci
Tafiya ta ci-gaba haka, kusan Sulemanya zabi watanni uku su zama lokacin zuwansa gida, har watan haihuwar‘ matarsa ya tsaya. Aka yi rashin sa’a bai yi daidai da lokacin dawowarsa ba. Ai kuwa bai dawun ba. sai da kwanakin nan ashirin da uku suka cika. Ya zo gida lokacin Murja na da kwana sha shida da haihuwar Maryam. .
gaba daya hidimar‘ Alhaji ne ya yi ta. Bayan ya natsa, ya gama shan gori‘wajen Mai-Jego. Alhaji ya samu‘; a falo bakinsa yana shan _ iska. Ya zauna gefensa, suka kara gaisawa kafin yace, “An sha hidima ko Baba’?”
Ya yi dan murmushi yace “Hidima ai an saba ta Sulaiman Allah dai ya kara mana lafiya da abinda lafiyar za ta ci”. Ya gyara zama yana fadin “Amin. dama cewa na yi hari in tambayeka ko nawa ka
kashe. sai in mayar‘ maka, dun na zoda ‘yan kudi a aljihuna”.
Alhaji ya bata fuska, yai zuru yana kallonsa jim, sannan yace, “Ni za ka mayarwa kudina Suleman?” Yace, “Ba wai ina nufin…” Ya daga masa hannu. “Dakata Sulema! Kome ka ke nufi, ni na fi gaban ka ce za ka mayar’ min da binda na kashe Me ka daukeni?
Amma lafazinka ya ba ni mamaki, yanzu kai a ganinka har ka zama wani abu ko? Ba haka rayuwa take ba, idan akwai sauran haukar yarinta a kanka, to ina mai jawo hankalinka da cewa ba’a ma na gaba haka, kuma ka sani har yanzu kai ba kowa bane, face Suleman. Ka ji ni da kyau?” ‘
Jikinsa ya yi la’asar, ya sauke numfashi yace, “Ka yi hakuri Baba.” Ya kada kai yace, “Ni ba wannan ya‘dame ni ba, zaman da ka ke yi wata uku-uku ya fara damuna. Ya kamata ka sake lale, ko kuma ka dauki matarka ku koma can. Ni shawarar da zan ba ka kenan, sai ka je ka yi tunani akai”.
Ya muskuta yace, “Ai dama akwai kishin- kishin gwamnati za ta raba mana wajen zama nan da wata biyu. Ina da niyyar in tafi da ita, ban dai fadi bane, saboda abin bai tabbata ba tukuna”.
Yace “To Allah ya tabbatar mana da alkhairi. Amma magana ta gaskiya ko an ba ku, ko ba’a ba ku ba, dale ka nemi wuri ka dauki iyalin ka. Ai iyali
yace, “Gaskiya. to na gode Baba, nan yasa hannu aljihu”. Ya zaro dari biyar ya’ aje masa. allah ya yi albarka, ya jikan magabata”. Yace “Amin Suka ci gaba da hirarraki, har yanzu guiwarsa salube take, saboda birkin da Alhaji ya taka masa. Kamar wasa, maganar komawarsu Bauchi ta kama Kwanansu daya a Kankiya. Murja ta je yiwa mahaifiyarta sallama ta‘ kuma sanar .da ita canjin muhallin da suka samu, koda ita ba ta sa albarka ba. .tadai fita hakkinta. “ Basarwar kuwa ta yi ko a jikin Hajiya Aliyaa. yadda ta nuna zahiri. Haka Murja ta gama ban-kwana gari-gari inda dangi suke. Mama ta bukaci a bar mata jamila, dun ita ma tana son ‘yar budurwa, kuma ta ‘ shaku da Jamila sasai.
Babu abinda suka dauka, illa suttura. ranar tafiya sai da Murja ta yi kuka. ita kuwa Jamila daga masu hannu, ta rinka yi bakinta har kunne sai da Mudansir ma yayi Imam kuwa ba shi da matsala. tunda Jamilarsa na nan an bar masa, shi ma bye-bye din ya yi masu har motar da Suleman ya, dauko shata ta tashi. “ ‘ Tun daga nan rayuwa ta sauya kwarai Suleman ya yi tsadar gani. Tun yana wata shida bai
zoba
har ya kai ga yana rufe shekara, bai zoba ko sakoba
ga mahaifiyarsa ma balle wadanda suka sha dawainiyarsa.
Duk lokacin daya samu damar zuwa. Alhaji na yi masa gargadi akan kula da mahaifiyarsa, ita kuma Inna Mairp tana masa fada akan kar ya zama kaza ci share baki.
Sai dai sam hudUbar‘ ba ta shiga zuciyarsa~ Bayan shekaru biyu ya sayi mota, wayyo lta kanta Murja ta fara ganin canji, tun daga wannan lokacin. Suleman na ji da kanSa kuma abu mafi daga mata hankali shi ne yawace-yawace.
Daman can tana zargin yana yi, da mota ta samu sai abin ya tabbata. Ranta ya yi ta baci, babu halin ta gaya masa gaskiya, ko ta fadin wani sabon bacin ran za ta samu, saboda irin maganganun da zai daddankara mata. ‘
Idan ta zauna shiru. Mamaki ya kan kusan kasheta, tace a ranta, “Dama haka samun kudin yake?” ga wasu ba Dumin ji Suke sun fi kowa, a rinka fadi, ana daukar kai ana ganin mutane kanana.
Ana jin warinsu. Sun manta cewa duk wanda yace shi wani ne. Wallahi ba wannin bane. Lokacin da yakekallon mutane karmami, to su a jaki suke kallansa. Wasu kuwa boyewa ma suke yi, ba su son ace su din ne. ‘
irin hakan ke sawa a girmamasu, dun kuwa ya san an gaji sahihin arziki. Ko dama ita dukiya daban, arziki daban. Allah ka ba mu mai amfani.
A lukaci guda aka sa Mudansir da Jamila makarantar’ da imam. ke zuwa ‘Imam‘baya gajiyar goyon Jamila. Mama ta yi ta fada, “Wai sai ka yi ciwon ‘kirjine imam’?
Ka rinka barinta mana tana tafiya da kafarta
‘dariya yakeyi yacé, “Ba ta da sauri ne Mamanmu”. Tace “Ko nan da Islamiyya ne goyata ka keyi.
Ya kada kai. “Mamanmu Jamila ai karama ce, nan gaba ita kanta ba za ta so guyon ba”. Ta tsura masa ido tace, “Ba dai ka so a fadi, laifinta ko? To
Allah ya sa kar ta girma ta juya maka baya, don na‘ lura auren nan da gaske ka keyi”.
‘Dariya kawai yakeyi, domin yana jin dadi. duk lokacin da aka ce Jamila matarsa cE. Suna aji‘ biyu, na firamare. Imam ya zana (Cummun Enterance) ya tafi sakandire.
Sun yi kewar juna kwarai da gaske, shi da ‘yan uwansa. musamman Jamila. Haka dai suka yi _ta
karatunsu, ko wane yana kara wayau, tare da kaunar junansu. – ‘
**********
Shakaru biya a jere damina ba ta kyau‘, manoma sao godiyar Allah kawal. Alh. Abdul—Rashead na daya daga cikinsu. Ba karamin hali gidan ya shiga ba na rashin abuhuwan bukata na yau da kullum. A. wannan tsakanin. ne- Murja ta sake haihuwar ‘Ya mace. Hankalin Alhaji ya tashi. dun yana ganin ya .kamata Mama ta ja Bauahi ta dubu Mai-Jago. ‘ ‘* Yadda za’ayi yai masa yawa. Mama keta
kwantar masa da hankali. Kwatsam! Ana saura kwana
‘uku suna. lnna’Mairo ta zoda ‘yan kayayyakin Baby da atamafa turmi biyu.
Mama ta yi tagumi tace, “Ai Inna’ ban jin zuwa’ Bauchin‘ nan ‘zai samu,~ saboda ba kudi, tun da sakon haihuwar nan yazo. Alhaji ke tsaye neman kudi, amma Allah bai sa an samu ba”. cikin tauSayi, tace.
“Ah! Tunda haka ne kudin matar‘ da naba Asaba, sai in ba ki, ke ku tafi tare da Raliya”. Tace‘ “Ayi haka? ldan ita ma tana son tafiyar fa?” Ta yi dan tsaki. ‘
“Haba Hajiya, zuwanki . ai ya ,fi ‘ nata . muhimmanci. Dama adashi- nane ban ,kwasa ba, tunda su Murjar’ sukazo, na ganta da ciki nace ni zan’kwashi na kusa da na karshe. Kin ji yadda ni ma na samu kudin. Saboda haka kece za ki, uwar ‘ya uwar angon
Tayi ‘yar dariya tace “To Allah ya nuna mana lafiya. Gobe’kenan za mu tafi dun ayi shirya~shiryen
suna da mu”. Tace “Kwarai da gaske Shi ‘yasa nayo .gaba na kawo miki dan abinda ya samu. In Allah ya kai mu gobe Raliyar na tafe sai ta taho miki da kudin”. Tace‘.
“Allah ya kai mu lafiya”. “Amin”‘.Anan ta wuni. Alhaji ya dawo ya same ta, suka sake‘maimaita zancen gabansa. Shi ma ‘fatan alkhair‘i ya yi tare da yiwa Allah godiya daya kawo mafita. ‘
Washe gari tun karfe tara Raliya na Kaduna. Mama ta shirya tsaf! Har da yaran biyu za ta tafi da yake hutu‘ aka‘yi, saboda Jamila ta je ta ga ‘yan- uwanta; . ‘ Babu bata lukaci suka nufi tasha, suka fada motar bauci, suka dauki hanya. Suna zuwa, da yaka adireshin wajen ba boyayye bane, nan‘da nan mai Tasin da suka shiga, ya kawu su. Murna awajen Murja abin baya misaltuwa.
Ko dama bata saran zataga kowa daga Kankiya ba, shi yasa ma ba ta ko tambaya ba Sulaman ya
dawo mota cike da kayan suna adangin abinci.
abubuwan sha da sauransu.
Ga wani firdeden raga yana harbin iska. Shi kansa ya nuna farin-niki daya gansu. Nan da nan suka hadu da makwabta, aka yi’ta soye-soya cin-cin da
naman kaji da na Sa. . Washe gari aka sha shagalin sunan. Hafsat. gida ya cika susai, amma su Mama da Raliya ne’ kadai’ ‘yam ‘ .uwa na jini. Duk wanda ka gani’, daga makwabta,sai
matan abokai. ‘To ai dole zo domin kowa ya san Suleman da sakin hannu ga kuwa ‘abokanansa musamman abokansa. Hhmm .Inuwar giginya kenan,’na nesa ka sha’ ki
‘ Kwanansu Mama uku, sannan suka yi shirin tafiya. Kayan suna da yawa Murja ta tanadar, su tace akai a raba kowa ya samu. Haka ta kulle wa Imam _ nasa daban tace a kai masa. Suna zaune dakin da aka saukesu da daddare
Suleman ya yi sallama ya shigo. Suka amsa ya nemi wuri, ya zauna gefen katifa. “Ana ta shiri ko Mamanmu?” Tace “Har ma mun kare”.
Yace “Madallah. Toga wasu ‘yan kudi‘ku kara na muta”. Ya miko mata’Naira hamsin-hamsin guda hudu. Tace”Kaida ka yi hidima Suleman, ai da kabarshishi, muna da kudin mota”.
Yace “Babu komai ki‘ kar’ba Mamanmu”. Ta amsa tana fadin. “Allah ya yi alharka”. Yace “Amin. Yauwa Mamanmu, nace ko za ki bar mana Jamila ta gama hutunta anan?” .
cike da fara’a tace, “Me zai hana SulEman? ga ta nan, da” ka yi magana tun dazu ma ai da ban hada kayanta cikin jaka ba. Sai dai kayan ba yawa”;
Yace “Karki damu, idanna fita na karo mata wasu”Tu shi kenan, hutun dai saura kwana goma- sha biyu ya kare”; Yace “Ba “matsala Mamanmu”. Ya ji‘ma nan .suna ta hira, Murja ta shigo ita ma ta
zauna aka yida ita sun jima, domin sun kusan sha biyun dare.
Akan dole Jamila ta zauna bayan tafiyarsu ta nemi wuri ta raba, ta yi ta kuka kamar hawayenta zai kare. Tun Murja na rarrashinta har ta gaji, ta kyale ta. lta kantaba ta ga dalilin cewa a bar ta ba, in banda
fitinar Suleman. A haka ya dawo daga kai su tasha ya sameta. ‘
Ya kamo hannunta ya dawo da ita dakinsa, ya yi ta rarrashinta tare da labarta mata abubuwan da zai siyo mata har da keken hawa. Hawayan dai sun daina zuba, amma a ranta cunkushe yake tana tunanin Mama da Imam. ‘
Bai yi kasa a guiwa ba, bayan sallar la’sar ya daukesu a mota ita da Ummi ya shiga da su gari, a can ne ya zabgowa Jamila siyayya har da kekenta. Murna kamar’ za ta haukace. Abinka da yarinta, tuni ta mance kuncin da take ciki. Shi ya yi ta koya mata keken har‘ ta iya, ko dama Ummi na da na ta tuntuni.
Sati biyu suka wuce. Murja ba ta ji Suleman na maganar’ maida Jamila ba. A daki ta same shi, bayan dawowar sa aiki ta fara yi masa maganar “Baban Jamila, ya kamata ka siyo wa Muda kekensa, ka yi kukari ka. maida ta. Ka ga sun kwana hudu ,da kumawa makaranta”.- ..
Ya yi shiru kamar’ mai tunani. Ta nisa tana dan murmushi tace. “Ai‘na gaya maka ba zai yiwu ka maida jamila da keke daya ba, dole ka siya wa Muda…”
‘ Ya katse ta, “Wai ke wa ya gaya miki Jamila za ta koma?” Ta yi galala! Tana kallonsa, “Ban gane ba?” Fuska murtuke yace, “Ta ta zokenan, har na fara nema masu makarantar kudi ita da Ummi”. Ta kada kai tace, “Hakan bai dace ba Baban Jamila…” ‘
Yace “Wai ke ba kya ganin yarinyar nan ba ta san komai bane? Har’ wani karatu akeyi a makarantar gwamnati? Kuma ki dubi jikin Jamila yanzu har’ ta canza, saboda tana samun abinci mai kyau tana ci! Amma koda yaushe tuwo miyar daddawa, yaushe yaro zai yi kumari, fatar‘sa ta yi kyau’?”
Zuru ta yi masa da wani katon tagumi’, ya kai aya. Ta jinjina kai tace, “Hu’hun! Baban Jamila ka kuwa san me ka ke fadi?” Yace “Kar ki gaya min maganar banza don Allah! Nace na amshi ‘ya ta, idan da akwai wanda zai ce wani abu ina jiransa”.
Tace “Ba haka rayuwa take ba Baban Jamila.
Ko za ka amshe ta, ha ta wannan sigar ya kamata ka bulloba. Na tabbata Baba da Mamanmu ba su da matsala, idan ka je ka same su hankali kwance, kace za ka dawo da Jamila nan, na tabbata ba za su hana ba. Amma daga hutu, ka ce baza ta koma ba, gaskiya akwai nau’in raini a ciki”.
Ya watso mata harara yace “Tashi ki fita Murja”. Takaici ya sa ta mike ta yi waje kamar tayi kuka. Ya ja dogon tsaki yace, “Ni da ‘yata? Allah ya yi min arziki, ba 2a ta mora ba, sai in bar ta can tana wahala?”
Kwana biyu Murja na ta nunawa Suleman kuskuren abinda yake so ya aikata. Har shawara ta ba, shi cewa gara ya maida ta gaba dayansu ya canza masu makarantar kudin.
Take nan ya bata amsa, shi ba shi da karfin biya wa ‘ya‘ya uku kudin makaranta. Babu yadda ta iya, haka nan ta sanya masa ido har su Jamila suka . fara zuwa makarantar kudi.
Ai kuwa sai da aka maida ta baya, maimakan., ‘ ‘ aji hudun da take, aji biyu suka dawo da ita. Suleman. ‘ ya wuni yana ciwon baki, akan wannan koma bayan da Jamila ta samu.
Murja dai ba ta tanka ba, hasalima ido ta sa’ masa ta ga irin bayanin da zai yi masu ranar da zai je Kaduna. lta kanta Jamilar ta kan tambaya, yaushe za ta koma Kaduna? Kai tsaya yake ce mata, ai ta dawo ” nan da karatu. , ‘ ’ ,
can gida Kaduna shiru babu labarin dawowar’ ‘. x
Jamila. Alhaji ya yi ta fada yana ganin laifin Mama da . ta baro ta, bayan ta san halin Suleman
Kullun ran Mamabaya mata dadi, Kodan’Alhaji “ na fada, domin ita ma tuni ta amsa laifinta. Suidai ba ta yi zaton Suleman zai yi wasa da karatun na ‘Jamila ba
Tafiya ta yi tafiya har Wata biyu tunanin su ya fara sauyawa, sai dai ba su hakikance ba, dun ba sa zaton Suleman zai iya aikata masu hakan, duk da cewa Gwaggo da Inna nata ciwon bakin Suleman zai iya daukar ‘yarsa, domin ba kunya gare shi ba. Kuma take-takensa suna nuna wuyansa ya isa yanka. Da yamma likis! Motar’ Suleman kE fakin kofar gidan Alh. Abdul-Rasheed, ya fito ya bude but ya kwaso wasu leduji guda uku farare. . .- ‘
Kananan kaya ke jikin sa, fuskarsa manne da wani bakin tabarau. Kai tsaye cikin gidan ~ya yi sallama. Mama na zaune kofar kicin tana tsinkar alayyahu. Cike da fara’a ta amsa, ta zarce da fadin “Mutanen Bauchin ” Ya zube. ledoji gefe, ya dauke gilashin fuskar’ sa “Mamanmu!” Ya tsugunna.
“Ina yini’?” Tace “Lafiya lau. Ya mutan gidan’?” Shima yace “Kalau suke”. Ta dube shi da kyau, “Wai kai kadai ne? Ina mutuniyar’ tawa?” »Ya yi dan murmushi yace, “Tana Bauchi Mamanmu, na yi, na yi, ta za. ta ki. Nace haka za ki wa Mamanmmu? Ai kuwa ke da ita”. . ‘
Ta kama baki ” ‘Yar’ ‘butar’ kasa! Lallai‘ Jamila ta yi halacci, amma har da laifinka da ka ki dawo da ita kan lokaci, har’ karatu yai nisa, wani hutun ma ake nema. To ta kyauta, sai ka nemi wata makarantar can; ka sanya ta”.
Ya shafa kai yace, “Ki na nufin shi kenan a bar ta can?” Tace, “Wallahi ta sha zamanta, ai ko
tace eh ta taya Murja aiki. Duk ranar da ta tako’yan kafafuwanta tazo.nan sai na girbe su”
_ Suka fashe da dariya. “ina Baba da yaran.’ tace”Sun tafi aski, yanzu zaka gansu, dun sun jima da fita. Shiga in kawo maka ruwa ka sha”. Ya mike ya kwashe kayan daya shigo da su, ya wuce daki. can Mama ta kai masa ruwan sanyi. Bai kai ga sha ba
sukajiyo sallamar su Alhaji. Yara’suka zubo da gudu, suna fadin, “Jamila oyoyo” Mama ta fara dariya, “Yara ku shigo, ku ga jamila’har rige eigen shigowa falon suke cirko cirko! Suka tsaya suna zane ido, ka na suka ce, “Sannu da zuwa Yaya’ Yace “An gaishe da samarin Baba.” Imam ya zagayo gana kana ya tsaya, “Ina Jamilar‘ Yaya?” Ya amsa, “Tana Bauchi, ta ki dawowa”. Jikinsa ya‘yi sanyi yakoma lakwas! Ya zauna, ya rasa me zai ce. Sallamar Alhajin suka ji, suka amsa, ya shigo yana fadin, “Wai matas ba zata rugo ta tarbeni bane?” Mama tace, “Wane matas? Ai nai mata kurciya”. Ya zauna, “Ban gane ba? Ba dai ta ki dawowa ba?” Tace “ga. zahiri; Jamila ai ta ban mamaki. amma za ta zo ta same ni”. Suleman ya amshe. “Ni kaina ban yi zaton za ta ki dawowa ba. Ta ban haushi har na raukwasheta..nace da-nasan haka zatayi DA tun farko ban karbeta ba lol
alhaj yace hard a laifinka sulaiman wata biyu ba dole yarinya ta manta damuba shikenan don ni ma na sake ta”. Suka tuntsir‘a da dariya. “Yi hakuri Baba, auran nan fa mai asali ne, : babu maganar saki”. Yace “Ba yanzu ba, sai na huce
., yasu‘Murjar da sauran yaran?
“Ya kuma aiki da hanya?” Yace, “Duk lafiya Baba, Suna gaisheku”. “Muna amsawa”. ‘ya tura wa Mama yace “Mamanmu ga wasu yan abubuwa nan babu yawa”. Tace “Mai yawan kenan. Allah ya yi albarka”, Ya amSa da “Amin”. ‘Ta bude ledojin, guda kayan sabulai ne da » mayukan shafawa da man ‘girki na turkey, kamar ‘ yadda ya saba kawuwa. Dayar’ kwalin biskit da alawa ir‘i-iri, sai silifas dan Madina ya siyowa su Mudansir’ ‘ ‘ Nan da nan murna ta rufe su, suka hau shewa.’ ‘ ‘mama tace”Lallai Yaya ya washe kannensa. .Madalla, to ba ku ce kun gode ba?” Duk suka yi masa “godiya. Mama ta raba masu tsaraba, suka fito tsakar 1 gida suka bar su a falon, suna ta hira har‘ aka kira sallah ‘ Washe gari Kauran Juli ya nufa, kuma yanata‘maida bayanin akan maganar Jamila, nan take Gwaggo tace shi dai ya dauke ‘yarsa kawai, ba wani . zancan’ta ki dawowa. ‘ Yadda Jamila ta shaku da Hajiya Suwaiba babu Yadda za’ayi tace ba za ta dawo ba.
inna mairo ta umarceshi daya maidata tunda ba Alhajinne suka ce ya karbi ‘yar ba.
; . Ransa bace ya dawo. dalilin da yasa bai ba ‘ kenan
dan haka kuma ko‘ furar’ da gwaggo ta“ Ba‘shi, bai sha ba. Yana dawowa gida Kaduna yace‘zai
wuce. Alhaji yace, “Dama yau zaka koma?” Ya amsa. “Eh, Wallahi”. Yace “Amma baka da hausa,
maimakon ka ce’daga can za ka wuce; shi ne ka sake
dawowa?” Ya yi dan yake yace‘ “Babu komai Baba'”To shi kenan. Allah ya tsare. Yauwa. dama ina so in yi maka magana. Ya kamata wani zuwan’ka je Kankiya, ka gaida surukar ka”. Yace “To, kafin lokacin ma Murja ta gama wanka, sai mu taho tare”. Yace “Haka ya yi kyau”.
Suka yi sallama, suna masa addu’a, har’ ya. shiga mota. Imam ya matso a marairaice yace, “Yaya kazo mana da Jamila, idan zaka dawo”. Yace “Za’a zo da ita”. Ya yi murmushin jin dadi, ya sake fadin. “Ka ce ina gaisheta”.
“Za ta ji Imam”. Cikin kunya ya fiddo ledar’ hiskit biyu da cingam (Bazooka), shi ma biyu ya mika masa. “Ka kai mata tsaraba”. Ya amsa yana ‘yar dariya. “Ta gode Imam”. Alhaji kansa dariya yake yi. Suna kallo ya tada mota, ya kama hanya, sannan suka
dawo gida.
*********
Kamar an shuka dusa maganar da Inna ta yi wa
Suleman wata shida kenan cur! Babu ko labarinsa Haka zancan ya sha ruwa, tun ita ma abin yana mata ciwo a zuciya, har ta hakura ta bar shi da halinsa.
Ranar wata juma’a suka wayi gari da wani babban al’amari daya gigita su, ba kadan ba. Daga ciwon kai. Gwaggo ta kwanta barci, amma tashi sai a darussalam.
Wannan mutuwa ta bigi zuciyar kowa a Kauran Juli, balle ‘ya’yan cikin ta. Shi kansa Alhaji ya jima hawaye bai yanke masa ba. Wasika ya rubuta aka kai tashar mota. aka ba wani amintaccen Direba mai zuwa Bauchi ya kaiwa Sulaman ma’aikatar su.
Rana ta biyu suka iso da iyalansa. Duk cikar’ taron nan, babu wanda Jamila ta yi hari sai Mama, ta fada jikinta ta rungumeta, ko ba’a tambaya ba an san .tana kewar Mama.
IMamanmu wai Gwaggo ce ta rasu?” Tace ba wai Jamila, gwaggo ta bar mu”. ldanuwanta kwalkwaI! da hawaye tace “Allah ya jikanta”. Tace”Amin Jamila”. Ta sake dubanta. “Ina su Yaya Imam?”
Ta amsa “Suna waje, ba ki gansu ba?” Ta amsa da kai, “Sunanan waje,.je ki duba su”. Ta mike ta fita, ta yi ta’nemansu. sai data gansu a kofar gida. Suka bi juna da kallo kowanne baki har kunna, kafin ta rugu ta makale wa Imam.
Yace“Jamila yaushe ku ka zo” Ta dubeshi baki ya ki rufuwa. “Yanzu”. Ta kamo hannun Mudanslr. yaya Muda Yave “Jamila kenan. Kin ga Mamanmu?” Tace “Na ganta. ina ta murna tunda Dadi yace za mu Kaduna”.
Imam yace, “Ba ke kika ki dawowa ba. Kin fi son Bauchi ko?” Tace “Dadi ne yace ba zan dawoba ‘ ya samu a makarantar kudi. Har ya siyo
min keke. .
,Mudansir ya karba, “Ke ta mace za ki hau
keke?” lmam ya fara dariya yana cewa. “Kai dan
kauyen ina ne? Mata ma suna hawa keka mana”. Ya ’ware ido, “Ni ma zance Yaya ya siyo min”. Nan hira ta
barke, da ka gansu, ka san suna cikin farin-ciki. sabanin sauran jama’ar dake cike a gidan.
Kwanaki bakwai suna amsar gaisuwa, sannan Sulaman da Murja suka yi niyyar tafiya Kankiya. Kiri- kir‘i Jamila tace ba ta zuwa, ita wajan Mama za ta zauna. Mama ta zungureta tace
. ‘ “Tafi ki ban wur’i uwar gulma. sai yanzu ki ka san da ni? Da na baro ki nace a dawo dake, ba kin dawowa ki ka yi ba?” Ta marairaica tace
“Allah Mamanmu ba ni na ki dawowa ba, Dadi na yace anan zan yi makarantar’ kudi ko Umma? Allah tambayeta ki ji?” gaban Mur’ja ya fadi da ta ga Hajiya Suwaiba ta zura mata ido “Dadin na ku ne yace ba za ki dawo ba mai karyar tsiya!” Ta dubi Murja, “Dun
Allah Umma ba Dadi na yace ba zan dawo ba? Har nayita kuka.
Murja ta rasa me zata’ ce? Yaketa hau‘yi tana kallonta. gaba daya jikin Mama ya mutu, dun ta: harbo jirgin. amma ta wayance. “Ni babu ruwana da
marairaicawar ki.
AI yakamata kije Kankiya, rabonki da can Ina
ganin tun ki na goye”. Ta cunno baki. Mama na mata dariya. Murja kuwa kunya ca ta sa ta barin wajan. Ko a jikin Suleman, lokacin da Murjar take masa korafi a hanya. Hasalima cewa yayi, “To sai me idan ta fadi’?”
Babu komai kuwa, domin Mama ba ta dauki abin da zafi ba, illa tace a ranta, “Lamarin Sulaman sai shi”. Ba ta gayawa Alhaji ba, don kar ransa ya baci. A haka aka ci-gaba da tafiya.
Hajiya Suwaiba ba ta fasa abubuwan da take yi ba na game da zumunci. Jamila kuwa ta koma dindindin! Gaban iyayenta. Idan ka ganta Kaduna. to hutu suka samu, iyayen suka kwasu su ganin gida. wanda shi ma baya wuca sau biyu a shakara.
Kuda yaushe al’amarin Sulaman kara lalacewa yake yi, tun ba sa ganewa har suka gane Suleman baya son taimakun kowa, iyakar kyautar‘sa. ba ta wuce sabulai da man shafawa.
ldan kuwa kudi ne. iyakarsu dubu biyu, idan ya yi zurfi ya bada uku. Tun wayoyin hannu ba su cika gari ba, shi yaka rike babbar waya, haka ita ma Murja ya siya mata, dun kece raini cikin matan abokai
Amma shi da mahaifiyarsa dinki daga sallah sai sallah. ‘ Ba’a maganar dangin Babansa. wadannan yan kauye, jahilai ba su san komai ba. Shi yasa yake‘ tunakaba a cikinsu. Yana fafe da mota da wayar! hannu. ohni duniya Ki koyar damu alkhairi’ Abubuwa sun sa Alh. Abdul-Rashaed tsaka. gari ya yi tsauri, ga shi kullum ’karfinsa kara raguwa ‘ ‘ yake yi, aikin gonar ma da kyar yake yinsa, dun ma su’ Imam na taya shi a ranakun da babu makaranta. Tsakiyar damuna ake a halin yanzu. ,
Al’amura _duk sun tsaya cik! Allah da ikonsa abin ya zo daidai da lokacin biyan kudin jarabawar (S.S.C.E.), hade da ta jam Kenan zai biya wa Imam
Duk da cewar kudaden ba wasu na kirki bane. gaba daya dubu biyu ne. amma ga wanda bai da su, dole su zama masu yawa a gare shi. Hankalin Alhaji a tasha yake damin lokacin rufewa yana ta karatowa. Imam har kuka yakeyi. ‘
Ga shi roko da yawon maula ba al’adar Alhajin bace. Ya sani idan ya tambaya. koda anan makwabtan sa, ne zai samu wanda zai biya, sai dai yana jin nauyi. dun bai saba ba. v
,‘ A nan kam tausayin Imam ya rufe Alhaji, yadda ya ganshi yana ta zubda hawayensa
sakamakon koroshi da aka yi saboda jibi za’a rufa biyan kudin. ldan ya tuna kalamansa, ya kan ji kamar
shi ma ya yi kwallar. “Kowa ya biya Baba‘ ni kadai na rage”.
A karo na farko da Alhaji ya dauki lamhar Wayar Suleman, wacce ya bayar wai ko za’a gaya masa wani sakon. Ya debi ‘yan cinikin da aka yi a kiyus dinsa, ya nufi wajen masu buga waya. Ya ba su lambar, suka nemo masa Suleman.
Sau biyu tana tsinkewa, sai a karo na‘uku ya dauka, “Hello!” Ya fadi cikin takama. Alhaji ya yi masa sallama, ya amsa da kyar, ka na ya tambaya, “Wanene?” Yace “Baban Kaduna ne”. A lokacin ne ya dan saki fara’a, “Ah, Baba ya ku ke?” Yace “Lafiya lau, ya mutan gidan‘ya aiki?” ’
“Wallahi lafiya lau. Ina fatan dai lafiya’?” Yace “To ba kalau ba, amma an gode Allah. Kanninka ne maganar jarabawa ta taso, gaba daya su biyun, ga .shi kudin sun yi wuya, ka san damina idan ta yi tsaka, sai hamdala”.
Yace “Haka ne, to nawa ne kudin?” Yace I “Dubu biyu ne gaba daya”. Ya dan yi Shiru jim, kafin ya sauke numfashi yace, “Kash! Wallahi Baba jiya jiya na kwashe kudin hannuna na kashe. Ka san Ummi za ta cika shekaru biyar, ana ta ‘yan shirya-shir’yen (Birthday) dinta”. Alhaji yace “Haka ne, amma wannan .al’ada ya kamata ku bar ta Suleman, dun ba musulunci bane. Yahudawa aka sani da bikin cika shekara. Manzon mu kuwa ya hanemu da koyi da Yahudawa. Sannan kai
idan ka kwanta, ka yi tunani, kullum fa cinya kwanakinka ka ke yi. lokacin haduwarka da Allah, yana qara matsowa.
To menene abin murna har da kade-kade da shaye-shaye? Ai abin da ya fi kyau. shi ne ka zauna. ka natsu ka’ karantu zunubanka, domin ka gyara.
abubuwan da ka yi kuma na kirki.
Ka kara kaimi, dun ganin ka je gaban Ubangiji. ka‘na mai dariya. Ina fatan za ka watsar da wannan akida, dun ‘ba ka gaje ta ba”.
_’ Ya numfasa yace, “Shi kenan baba, dai yadda ta yiwu, idan na samu zan aiko. A gaida
Mamanmu . Yace “Ai jibi ne ma za’a rufe”. “Jibi. jibi?” “Wallahi”.
“To bari mu gani, in son samu, zan aiku Direban nan mai‘kawo sako”.Suka yi sallama, kowa ya kashe Waya nan take Allhaji ya‘mika dari da hamsin kudin wayar da ya yi.
can bangaren Bauchi kuwa yana kashe waya, ya yi tsaki. Murjé ta dube shi tace “Me ya faru da su Baban?” Yace “Wai su Imam ne zasuyi jarabawa…
Da sauri ta amshe, “Shi ne ka ce ba ka da kudi Baban Jamila? Wannan menene a gabanka saboda Allah? (Birthday) din nan fa ba wajibi bane, kuma na tabbata a lissafin da muke yi yanzu kudaden nan ba za su shige duka ba. Dun Allah ka bayar akai masu, tunda
tunda ka ga Baba ya‘ yi magana da kansa. Wallahi ta kuka masa ne”. –
Yana ta kirgar kudin dake hannunsa shi, bai ma san ta kare maganarta ba, saboda ba sauraranta yake ba. Ta zura masa ido ya gama wawware
kudaden da zai kashe. Ya mayar da saura aljihu, ka na ya duheta. yace”Me ki ke fadi ne?”
Tace “Ai ya wuce, tunda ba ka ji ba, amma ka sani idan ba ka taimaki Baba ba, wa zai taimake shi?” Yace “Ku mata ba ku da hankali, saboda ba ku san zafin neman kudi ba, shi yasa da ance taimako, sai ku diba ku bada. Idan ba ka na nuna ba kullum ka ke da shi ba, ai damunka za’ayi ta yi.
Ta tabe haki tace, “Hmm! Allah shi kyauta, ni da ina da su da na bada”. Ya murtuke fuska, yace “To ya isa. ki na iya tashi tun kafin raina ya bani”.
Tace “Allah ya ba ka hakuri”. Ta mike ta fice daga dakin. Ya kwashe kudinsa ya dauku makullin
mota, hade da (List) din abubuwan da zai siyo a kasuwa
kasuwa ya fice abinsa.
**********
lol
masu karatu duniya makaranta Ku daure mu hadu a book3 kuma na qarshe
inda zakuji yaddah labarin zai juya DA wani lamari Mai ban mamaki
duniyace zata koyar DA wani darasi Wanda kowa zaiso ya jishi don tausayawa
plz Ku ringa comment naku har kullun
The OWNER OF LITTAFAN HAUSA ZALLAH PAGE@FCB
FOR MOTE DETAIL CONTACT ME OR WHATSAP ME @08035453572