Makaranta duniya chapter5

Makaranta duniya

                  Chapter5

Janye wayar tai daga kunnenta tana mamakin irin wannan hali na sulaiman lado mijinta yace bai kamata Ki dinga daga hankalinki akan sule ba wai namijmafa kenan Wanda shine ya kamata ace yana dawainiya dake Amman a,a sai mazan yayanki mata sune suke miki alkhairi Ki duba kiga duk kudin sule Amman Kafin ya aiko miki DA dubu Daya sai a dibi watanni kayan DA kike sawama basu wadacekiba ai sule  sai addu,a kawai washe gari DA sassafe kuwa ta gama shiri misalin qarfe goma DA rabi ta isa Kaduna asibitin DA aka kwantar alhajn
Ba qarakin tashin hankali ta shigaba ganin halin DA yayan Nata yake ciki ba um babu a,a sai Ido kwala kwala kawai DA yakebin jama,an dake  zuwa masa dubiya bayan ta isa asibitynne tacema muda to tunda baxo kaika koma Gida ka huta alah bashshi gobe idan ka dawo daga makaranta ka biyo ka qara ganin jikin Baban naku yace  to Inna sannan ya tafi  tafiyarsa ba wuya hasiya matar malam saddiq ta Iso DA abinci nan suka gaisa gamida gabatar DA kanta ga Inna mairon  malam saddiq shine yadau nauyin komai duk wani Abu DA za,a buqata a asibity a aljihunsa yake Zara ya biya gamida duk wasu magunguna DA za,a saima marar lfyn kullun sau biyu yake zuwa dubashi DA safe kafin ya tafi aiki sannan kuma DA yammah idan sun tashi kafin ya isa Gida yake biyowa don ganin yaddah jikin NASA yake
Wata ranan asabar ba makaranta mudassir DA Inna mairo suna kusa DA marar lfyn shi kuwa barcinsa kawai yake
Sulaiman ya Kira wayar mudassir yana dubawa yaga shine saiya miqama Inna mairo yace mata yaya sulaiman ne ta amsa gamida kangawa a kunne assalamu alaikum ta amsa amin Anya kuwa sule kanada imani kuwa ace alhaj yana kwance a asibiti rai a hannun Allah Amman ka kasa bar  duk wani Abu DA kake kaxo ka dubashi Kai sule wlh kaji tsoron Allah wlh Ina guje maka ranan Dana Sani wato danacema ka turo DA wani Abu domin a rage hidiman asibity don ka nunamin Kai ishashshene shine kaqi KO ?ba komai duniyace wlh Ina jiye maka tsoron ranan DA zakazo kana Dana Sani katseta yai DA ya isa haka Inna haba nifa SBD irin wadannan maganganun nakine yasa ban cika zuwa wajenkiba KO kiranki a wayabafa DA kike wani zancenki daman ai yanxu din DA niyyar jin yaddah jikin NASA yake na Kira sannan kuma na shaida miki Dana turo DA abinda ya samu dubu biyar ne Ki dau dubu biyu shi kuma Baban sai a bashi dubu uku don yasai magani maganar zuwa Kuwai baxan xoba don inada uzurirrika a gabana DA yawa takaicin maganganun NASA yasa ta katse wayar cikin fushi ba tare DA tacema mudassir din komai ba ta miqa masa wayar tana maida numfashi a kwana a tashi ba wuya yau alhaj abdurrashid ya dibi sati biyu a kwance a asibity ran an wata laraba DA yammah bayan mudassir ya dawo daga marakaranta a qarqashin wata bishiya ya hangi Inna mairon tasu tana hutawa ya qarasa wajenta suka gaisa gamida tambayan jikin Baban nashi tace masa DA sauqi sun dan taba hira sosai kamin su tashi su koma wajen Marar lfyn suna Shiga sukaga kan gadon NASA wayam cikin Sauri suka qarasa gamida tambayar wani Mai jinyar wani majin yaci dan Allah malam Mara lfynnan fa wani ne yaxo ya daukeshi? DA murmushinsa yace a,a ai sauqine yaxo don DA Kansa ya tashi saidai baicema kowa komaiba DA alamun ban daki yake nema shine muka Nuna masa yanxu haka yana ciki
Wohoho wato farin cikine ya rufe zukatansu gabaki dayansu mudassir bar ya bude baki zaice wani Abu sai ji sukai an turo qofa DA alamun ya fito daga ban dakin kenan yana rarrafawa a jikin bangoda Sauri suka qarasa wajensa mudassir ya tallafoshi suka dawo dashi kan kadon jinyar NASA gamida yi masa sannu DA jiki Kai kawai ya ke Iya daga musu Amman babu baki
A bangaren imam ma kusan hakan zamuce hajia suwaibace zaune ta rafka takumi a gefen gadon DA aka kwantar imam duniyar gaba Daya yai mata zafi kamar  an tasheshi daga Mafarki firgirgit ya farka ganin a inda yake yasa mamaki ya rufeshi cikin mamaki kuma yaga ummansa a kusa dashi jin motsinsa yasa ta dawo daga duniyar tunanin data shiga imam ka tashi saunu ya jikin naka? Ummah meye ne ya sameni har aka kawoni nan bata Iya amsa masa ba a hankali a hankali abubuwan DA suka faru suka dinga dawo masa kuka ya somayi gamida Neman gafarar mahaifiyar tasa akan in Allah ya yarda bazai qaraba so yake ya cire jamila kota halin qaqa a ransa yasa shi zuwa shan wadannan kwayoyin wai duk dan ya manta DA ita Ana cikin hakane likita ya shigo don a irin lokacinne yake duba marasa lfy ganin imam ya dawo hayyacinsa yasa ya zauna gamida yin masa nasiha sosai akan abinda yai ba daidai bane sannan DA yin masa alqawarin in Allah ya yarda bazai qaraba yace likita don Allah ka taimaka ka sallameni yau domin na nemi gafarar mahaifina  ya yafemin likitan yace ba damu Zan baka sallama yau sannan ya fice ya barsu bayan ya fitanne yake tambayar Ina abbansu yake ce masa tayi yana kwance a asibity ya zama kamar matacce don ba inda ke amfani a jikinsa nan ya qara rudewa bayan ya dan natsa ba tare DA tace masa komai ba yace mama Bari na shiga bayi nai alwala nai sallah kamin likita ya sallamemu tace to shikenan bayin ya fada yana kwallah gamida cewa dole baqin ciki ya kashe baba
Waje hajia suwaiba ta fita ta samu waje ta kebe sannan ta Kira mudassir Kira Daya ya dauka salamu alaiku wslm mama daman yanxu nake zumudin kiranki sai gashi kin kirani tace KO Ina fatan lfy wanI abune ya faru?cike DA doki yace  na gaya miki mama yau baba ya tashi harda shiga bayi DA kansa jikinta ya day rawa tace don Allah muda ?yace  wlh mama ya farka barci muna waje DA Inna mairo shigowan DA zamuyi mukaga bashi akan gadon DA yake muna tambaya akace mana yanxu ya tashi DA kansa harya nufi  bayi DA kansa aiKO ba,a jimaba ya fito DA kansa yana  dafa bango take ta shiga hamdala ga Allah tace kasan wanI Abu muda yace a,a tace shima yayanka yayI sarai don har an bamu sallama yau farin cikin muda ya qaru Allah sarki mama bashi wayar mu gaisa tace shima ya Shiga bayi wai zai Fara sallah ne kafin mu taho yace  to shikenan saikun iso kenan tace eh cike DA farinciki ya kashe wayar
Ba tare DA bata lokaciba likita ya basu sallama gamida magungunan DA za,a siya masa Sannan duk bayan sati biyu ya dinga zuwa cheak up suka nufo Kaduna direct asibityn DA aka kwantar DA abban nasu suka sauka don su Fara ganin yaddah ya qaraji DA jikin NASA imam yayI kuka sosai gamida Neman gafarar abban NASA babu baki saidai Kai kawai Daya kada masa alamun babu damuwa asiya na wajen matar malam saddiq hajiya suwaiba taita mata godiya gameda dawainiyar DA suka dingayi da marar lfy a asibityn
Inna mairo ta kada Kai tunanine kawai ya fado mata hajia suwaiba tace lfy mairo ?
Tace wai a duniya bare yafi  dan uwa wannan Abu yana daure min Kai tadanyi murmushi Wanda bai Kai ciki ba tace mairo kenan kibar wannan maganar don Allah
Tace dole nayi suwaiba Ina amfanin naka ya lalace wai kamar sule ace alhaj baida fly ya kasa zuwa ya dubashi 
A kwana a tashi jikin alhaj sai samuwa yake don yanxu yana magana garau mudai saidai kawai muce Allah e kare gaba wata ranan juma,a DA yammaci sun fito DA alhaj qarqashin wata bishiya dake Cikin asibitin domin yasha iska doguwar tabirma suka shimfida alhaj na zaune hajia suwaiba na gefensa tana bare masa lemon DA malam saddiq ya kawo masa Mairo kuma na gefe Daya sai Kawai gani sukai ta goce DA kuka
Gaba Daya hankalinsu ya dawo gareta lfy Mairo duk suka jefa mata wadannan tambayoyin
Ta share hawayenta gamida fadin baqincikine ya dameni na rasa inda zansa kaina Kai jama,a ka haifi DA Amman baka haifi halinsaba nan take suka game inda ta dosa dukansu sukai shiru kamin Alhj ya sauke nannauyan numfashi yace idan kika dauki damuwa kika daurama kanki kema kina gab DA fadawa ramin Dana fada gwara Ki manta DA komai Ki barma Allah
Tace kayyah ai dole wannan Abu ya dameni kaman sule ya zama kaza ci ka share baki lallai banga dalilin DA zaisa hankalina ya kwantaba bakina DA nashi nace yaxo ya dubaka yacemin bazai samu daman zuwaba Kai karewama KO waya ya Kira yace  ya masu jiki bayayi
Sai wata banzar dubu biyar Daya turo DA ita wlh haushinema ya hanani fada domin aje a Ciro
Duk suka dubeta tare da tausayawa Alhj yace don me zaki raina abinda ya turo ?dubu biyar ba kudi bane?tace uhhm cewafa yai wai a baka dubu uku dubu biyu kuma nawa  Mai zamuci dasu Ku barsu  a bankin duk sanda yaxo ya cire kayansa ya koma dasu muda ya cabe gaskia ne Inna me zamuyo DA kudinsa ummansu tace Kai Kuma wayasa  bakinka
Ah ansa dashi mana Ki barshi ya amayar DA abinda ke cikinsa
Halin sule ba boyayye bane balle  a rufa masa meya tsinana mama Wanda zamuyi alfahari dashi ?saima mugun butulci da yayi mu……..
Alhj ya katseta ya isa Mairo idanma qorafinne nine ya dace nayi tunda banyiba kuwa banga dalilin da zaisa zaki Ari bakina kicimin albasa ba
Kudi kuwa aje a cirosu mu raba Allah yasa musu albarka
Tace yaya indai kudine nidai wlh na yafe kuma zanci gaba DA roqon Allah akan ya ciremin damuwar sule a raina in kasance kamar ban haifeshiba a doron kasa……..
Hajiya suwaiba tace kiyima girman Allah Ki kame bakinki me yai zafi haka   tsam ta miqe tabar wajen Cikin ikon Allah alhaj yai garau aka bashi sallama
Bayan sallar isha,I malam saddiq ya shigo domin ganin jikin  alhaj din shi kadai ya samu a falon yayi tagumi sallaman DA malam saddiq yai ya dawo dashI daga tuniyar tunanin Daya Shiga firgirgit ya dubeshi ya sauke numfashi
Ah malam Sadiq ne yace wlh ahh shigo mana  zauna banyan ya zauna Alhaj ya janyo musu tiren abinci gamida sauke numfashi malam Saddiq yace alhaj DA alamun akwai dakuwa a ranka ya kamata ace ka  saukeshi a irin halinnan DA kake komai zai Iya faruwa wannan abun Daya faru ya kamata ace mu wallafama Allah komai
Alhaj yace wlh  ba matsalar imam ce ta rinjayi damuwataba Ina hangoma Sulaiman abubuwa DA dama akan irin rayuwar Daya tsinci Kansa a ciki ne mahaifiya ba wasa bane  kA baqanta mata raima bata furtaba kana cikin matsala ballentana har ta zubda hawaye a kanka ita tana ganin dole sulaiman ya kyautatamin Tasha nuna bacin ranta akan hakan Amman na  yau yafi muni
Tunda harta zubda hawaye akansa
Malam Sadiq yace hakane lallai akwai tashin hankali a ciki inaganin ai haquri shine zaifi tunda ita DA take mahaifiyarsa haqqinta Daya wajabta akansa yana saukewa ai saitai haquri DA hakan alhaj yace kayyah malam Sadiq kaidai ai sha,ani kawai wai an cuci baqauye
Nida hankalin NASA zai karkata kan mahaifiyar tasa Aida yafiyemin komai farin ciki nayi nayi ta kwantar mata  DA hankalinta Amman Sam ta kasa musamman ma akan wannan rashin lfyn nawa DA yaqi zuwa dubani
Yace uhm tanada gaskiya wata qila kuma akwai wasu dalilan dayasa  takeson ganin lallai sulaiman din ya kwautata maka ne
Alhaj yayi Jim gamida kada Kai
To meye a cikin rayuwa shi DA  ai duk na kowane don ka taimakeshi bai zama hujjah akan dole sai shima ya taimakeka ba
Ya zura masa Ido zai Iya zama mana alhaj ai bama saika fadaba ga Mai hankali wajibine yasan abinda ya dace
Alhaj yac dan abinda nai masa baikai ace kowa ya damu akan akan rashin kyautatawarsa gareni ba
Badan darene yanxuba Dana fada maka dan taqaitaccen abunda ya faru shekarun DA suka gabata
Malam saddiq ya gyara zama zansoji Alhj idan har zaka gayamin domin ni kaina kaina a daure yake gameda lamarin sulaiman alhaj  din yai Jimmm shiru tunaninsa ya zurfafa

             Waiwaye adon tafiya

Www.Facebook.com/abdullahi.Ismail.salanke

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE