Makaranta duniya chapter6

Makaranta duniya

            Chapter6

WaiwAYE…

Abdul-Rasheed Yusuf, haifafien Kauran Juli ne. ta dake birnin Zariya. Babban da ga imam Yusuf Kauran Juli yayi zurfin karatun Muhammadiyya. sannan ya kai matakin mastas a karatun boko.
Kafin ya yi auren fari da Hajiya Suwaiba, a lokacin da yake babban ma’aikaci a ma’aikatar ayyukan gona ta tsohuwar jihar Kaduna. Watau tun zamanin da suke hade da jihar Katsina.
Mairo ita-ce ‘Ya ta biyu a gidan kuma auta. sai dai ita bata sami isasshen karatun bokon ba, aji shida na firamare ta kammala, akayi mata aura.
Amma saukakkiyar Alqur’ani ce. A cikin garin Dutsen Abba ta yi auranta, kuma suna zaune lafiya da mijinta shekara da shekaru. babu haihuwa kamar yadda abin yake a gidan Alhaji Abdul-Rasheed.
Wannan al’amari yaci gaba har Zuwa lukacin da gwamnati ta kirkiro da hukumar bunkasa kogin Niger da ‘ raya karkara ta jihar Kaduna.
‘Alhaji Abdul~Rasheed ya sami nasarar zama darakta na wannan hukuma. liyafa tayi gaba sosai. kowa yana jin dadin alhaji Abdul-Rasheed a matsayinsa na mutum mai son zumunci da kishin al’ummar sa.
Shi ya sa koda yaushe ake rabon kayayyakin da suka shafi aikin noma. Jama’ar Kauran Juli basu da matsala. ta  musamman bangaren taki da ingantattun irin zamani.
Babu shakka mutaneu gundumar Kauran Juli na alfahari da wannan Da nasu. A wannan tsakani ne cikin hukuncin Ubangiji allah yaba Mairo ciki. bayan ta shafe shekaru guma sha bakwai a dakin mijinta. Lokacin haihuwa ya20 ta
haifi danta namiji. son kowa kin wanda ya rasa, kuma Allah ya ci da shi sunan Suleiman.
Ba karamin alkhairi ta samuba daga Yayanta har
da katon ragunan suna. aka yankawa Sulaman raguna biyu. Bayan shekaru uku da haihuwar Suleman. mahaifinsa ya kwanta ciwo  Wasa wasa sai da ya shekara daya da rabi a kwance.
Dawaniyar tana kara hawa kan Alhaji Abdul- Rasheed. kasancewar Isiya bashi da karfi kuma babu mai tallafa masa a danginsa. ma’ana kowa ta kansa yake yi wajen neman abinda zai ci.
Wannan ciwo iya binciken asibiti suka rasa ainihin ganin ko menene musabbacin ciwon shiya kaishi ga rasa rayuwarsa, bayan shekara daya da rabi yana jinya. Rasuwar |siyaku shi ya bude shafin farko na makarantar dan tilon dansa a duniya. ‘
Watau Suleman. inda ya koma karkashin kulawar ‘yan uwan mahaifin nasa. yayin da ita Mairo ke
zaman‘takaba. Bayan ta kare. ta nemi komawa gida.
gaban iyayen ta. ta kuma sami amincewar’yin hakan
daga‘mahaifinsu, saboda har yanzu tana da kuruciyar ta. tana da bukatar sake sabon aure.
Sai dai shi Suleman dangin ubansa basu bata shiba, a cewar su, tunda aure zata sake. dole ya zauna a gidansu. Abin bai yiwa Mairo dadi ba. don ta san tabbas Sulaman zai fuskanni matsaloli na maraici.
Amma babu yadda ta iya. dole ta hakura, ta kyale ta mika neman taimakonta wajen Allah. Bata hada wata uku ba. aka daura auranta da Lado, wanda shi ma tasa matar  rasuwa tayi shekara guda kenan
Allah da ikonsa. a cikin shekaru uku ta haifi ‘ya’yanta mata biyu. RAliya  da Halima wacce  suke kira da Asabe, sabuda sunan Kakarsa Malam Ladonne d
duk da hankalinta na kwance a gidan mijinta, a koda yaushe tunaninta na kan Suleman. Saboda ya tashi a halin yanzu ya kamata. ace yana makaranta ko yaya ne. yana samun ilimin zamani. lna. Suleman bai sami wannan gatan ba, na Muhammadiyyar ma bai samu ba ballantana
na bokon
Aikin su kawai, rani da damina. suna tafe aikin gnna sai yawo a gari. Babu suturar kirki. Kota dinka masa ta aika masa da shi. rashin kulawa ke sawa su lalace nan da nan. Haka takalma, basa sati a kafarsa. za’a nema a rasa. koya batar dashi da kansa. ko kuma cikin  yaran gida wani yasa ya  batar‘.
Da al’amarin ya buwayi lnna Mairo. Sai ta kyale ta kauda ido a kansa. duk da abin yana mata ciwo kuma abinda tayi gudu kenan, don tasan dangin mahaifinsa
basu damu da sha’anin llimiba tareda ba iyalai kulawa, lrin yadda ya dace. lslyaku ne ,kadai yakeda wannan buri. gashi Allah baimasa tsawon raiba.
Haka rayuwar ta kasanca har zuwa ranar wata asabar shekara ta dubu daya da dari tara da saba’in da tara. cikin gidan Alhaji Abdul—Rasheed daka Barnawa Kaduna.
Shigar fararan kaya ya yi, wanda yake riga  hade da malun-malun, ya dura kubansa mai tsada. Ya dubi Hajiya Suwaiba dake zaune gafensa. Yaca “Nina yi harama
” Tace”Yau kam sammako zakayi Alhaj naga ka shirya da wuri ne Yayi dan murmushi
Yace “Na jima banJe gida ba, saboda tafiye- tafiyan da muka sha zuwa kudu. Shi yasa naga ya kamata in shiga gida da sauri don mu sami isashshen lukaci dasu Baba”.
Tace “Hakan ya dacc, to Allah ya tsare. a sauka lafiya”. Ya amsa da “Amin, summa amin. Ina fatan duk
kayayyakin nan an zuba su muta?” Tace “Tuni Magaji ya

shirya su a mota “. Ya mike yana fadin to “Madalla”. Tare suka fita gamida yin masa rakiya jikin motar sa kirar (Peguat 504). kalar samaniya. Suka yi sallama.  ‘Dirabansa Magaji ya bude masa ya shiga,  sannan ya koma mazauninsa, yaja motar suka fice
. isowar Alhnjn keda wuya, tun a hanya jama,a  ke dibar gaisuwa Inda yaga Dattijai kuma yasa diraban ya tsaya ya sauko su gaisa
Direbane yayi fakin kofar gidansu alhaj wanda aka lailaye DA siminti daban da sauran na karkarar . Yarane  sukaxo suna rite rigen diban kaya a mota motar  suna shiga dasu cikin gidan
Mahaihyarsu. gwaggo Atine ta fito da murnarta ta tarbe shi. Suka rankaya daki tana masa lale marhabum.  suka guise. ya tambayi Baban sa
Tace bai dude do fita ba. Ta kawo masa ruwa. itama ta sallami yaran da suka shigo da kaya. duk ta yankar masu lemo
A cikin su akwai Sulaman. shi ne yaro na karshe data mikawa lemu daya. tace “Ka kuwa gaida Bahanka? Ya kada kai. Ta sake fadin “To me kake jira? Wuce kaje ka gaida shi“.
Yayi gaba. tana biye da shi har cikin dakin tana fadmin“Sakarai. gaisuwar ma baka iyaba. sai an gaya maka?” Alhajin ya zubo masu ido, yana murmushi yayin da yake zubewa gabansa “Wanena wannan?”
alhaj dinya tambaya. Tace “Sulaiman  mana dan wajen qanwarka mairo
“”Ina kwana lnji sulaiman. Ya amsa yana
“Ya iyayen ka? Duk suna Iafiya?” Yace “Lafiya lau”. “Ajin ka nawa makaranta?” Ya yi shiru yana ‘yar dariya. gwaggu tace “Makaranta? da dai kunya nawa yake nomewa ka tambaye shi. daya baka amsa”. Ya tambaya “Kina ‘nufin baya karatu?”
Ta amsa “Haka nan yake zauna”. Fuska yamutse. Yace “Me yasa tuntuni ba’a sanar da niba?” Tace “Menene amfanin sanar da kai? Tunda bamu da iko dashi? Su haka ’yayansu suke yawo, mahammadiyama bata ishesuba ballentana boko
Yace to gaskia DA sake don bazai  yiwu abar yaro kyakkyawa kamar wannan ya taso ba ilmiba
Ta gyara zama. Tace “Yafayi kyan gani ne, dan kwana ukun da ya yi anan, yana ‘samun’ wanka akai akai, baka ga uban kir’cin dake jikinsaba, sai da uwarsa tayi kuka data gan shi”. ‘
Ya kada kai cike da tausayi. Yace~”Har da laifin ku gwaggn, nida an sanar dani, ‘dana nuna ma’su nawa ikun. Aiba hujja bane. don suna dangin ubansa, ace su kadai ke da hakki a kansa, Uwarsa ma tana da nata‘ hakkin’. Maraya kuwa yana da hakki akan ‘kowa yabashi kyakkyawar kulaWa. Amma wannan ai nakasu ce

Naku har kullun

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE