Makaranta duniya chapter7

Makaranta duniya

            Chapter7

Ya dubi Suleman, “Kai! Ruga gidan lnnarku kace DA ita. ldan Baban su Asabe yana nan, ta tambaye shi tazo ina kiranta”. Yace “To” Ya miqe ya yi waje da saurinsa‘  Alhaji ya dubi gwaggo yacigaba.
Duk wanda  ya taimaki maraya, yana da babban rabo, damin Manzun Allah (S.A.W) cewa ya yi “Ka fada da kafada zasu shiga aljanna da duk wanda ya taimaki maraya. Ya kula da shi ya dauki nauyin duk wata dawainiyarsa. shima yaji dadi, tamkar sauran yara masu ubanni.”
Na yi zaton dangin ubansa zasu iya, domin sune hakkin dan ke wuyansu. tunda sun kasa, tomu dangin , uwarsa zamu dauka. Allah ya tayamu rikewa”.
gwaggo ta numfasa. Tace “amin sUmma amin. Babu shakka kayi dogon tunani kuma ko Malam yayi maganar nan jiya jiya yanata fada an bar yarnlo babu
karatu”. Yace “ninasan Babansa zai so ya yi karatu don
lsiyaku wayayyene duk da cewa baiyi zurfi a karatunba. Mutum ne shi mai kokari da kishin kai.alhaj yace lnsha-Allahu
dansa ba zai tagayyara ba” yana rufe baki, yaji sallamar ta “Kai! Ba dai har
yaje gidan ba?” Duk suka tamhaya. Ta karasa shigowa dakin. cike da murna tana fadin “A hanya muka hadu. Dama Malam ya shiga yake gaya min ya ga wucewar motarka, shine nace masa zanzo mu gaisa” ta zauna
Alhajin yace “Allah sarki Toya kwana biyuu. ya yarin?” Ta amsa “Lafiya lau. ya su Hajiya’suwaiba?
Shima ya amsa “Kalau take. Tace duk a gaishe “ku. Wannan RAliyaa ce ko Asahe?” Gwaggo’ta amsa “Asabe ce. baka ga dan hancinba. kamar an lakuta kashi a bango?” ‘ ‘
Suna dariya. Alhajin. Yace ‘”Gwaggo kishi kikeyi, hala ita Baha yafiso?” Tace “Shi RAliya ya zaba, tafi hanci ga farl’. ‘ ’ ‘ ‘
Mairo taCe “Fari ai bashi ne kyau ba gwaggo koba kiji ana cewa wasu ba don fariba. sai bola?” tace duk bakine na ‘jama,a  Alhaji ya amsa. ‘ai
“Haka ma batura’yace da kansa”. Tayi ‘yar“ dariya. Tace “Lallai kuna son ‘yarnan taku. Na bar
maganar, tunda kun kakkare ta”. Suna dariya Alhaji ‘ya gyara zama. Yace, “Mairo
‘ashe Suleman baya karatu? Na20 naga yaro duk ya lalace, ya dawo dan kauye fitik! Kamar marar gata’?
, Meyasa baki gaya min ba?” Ta sunkuyar da kai tana dan murmushi, saboda kunyar dan fari. Yaci gaba da fada “Haba! Bakiji yadda raina ya baciba dana ganshi jiki duk kircil Kai sunkuye. Tace “To ai Yaya Alhaji, ‘su gwaggo “ ne ya kamata su gaya ‘maka; Ni kuma ganin basu‘tankaba, shi yasa nima na‘ kaUda kaina
Gwaggu taca “Mu din ma abin na damunmu amma sun fimu karfi kuma a wajensu yake Amman ba. wai an ware shi bane. kaf ‘yayansu haka suke. kamar tumaki. Ni yanzu ma tsoron abinda zai biyo baya shi nake gudu, idan aka ce za’a karbe shi wadannan mutanen masu fassara kala’kala”:
Alhaji yace “Da kaina 23 um ai wannan ha hujja bane don nasu yaran basa karatu shi kuma sai a kyale shi haka, alhalin akwai yadda za’ayi?
Wallahi niban sani bane, da tuni nayi wa tufkar
hanci. Gara su ‘yayansune. shi kuwa wannan marayane, akwai bambanci tsakaninsu. Allah ya shigo da Baba lafiya, yau yau din nan zamu tafi!”
gwaggo ta numfasa‘tace “To! Allah yasa ayi nasara a kansu. Suleman kam yana bukatar taimako”. kuma”Za’a taimake shi da yardar Allah, sai mun cire masa rigar maraici”. Fuskarta cike da murna. Tace “Allah ya baka iko Yaya” Suka amsa da “Amin”.
A masallaci alhaji ya hadu da mahaifin sa. Bayan kammala.sallah, suka rankaya gida. Abinci suka iske
ajiya yana jiransu. Nan tsakar gida, katuwar barandar data yiwa’wajan inuwa suke zaune gaban kwanikan abincin.
Sanin Alhajin masoyin tuwon “dawa ne miyar kuka, shiyasa gwaggulon ta rangada masa, miyar kuwa ta sami ‘isashshen nama da lafiyayyar daddawar kalwa. Sannan ta malala mata man shanu yana yawo saman miyar. lol
Shiyasa dadinta baya misaltuwa. Tuwo kam ya tuku lukui—lukui! Sai wucewa kawai. Mairo ta kawo ruwan dauraye hannu, suka dauraye.
Suka jefa hannu tare suka .fara cin abincin. Sundanyi shiru na ‘yan mintuci; kowa yana tantance zakin miyar kafin Alhaji yace “Akwaifa magana Baba”. Yace “Inajin ka”. Yace “Ashe Suleman baya karatu. shine ban sani ba?”
‘Ya dan mUskuta ya dubeshi. Yace “Baya yi AbdulRasheed,;kuma kai kanka kasan ba zaiyiba. tunda gidansu ba karatu bane a gabansu. Babansa ne
kadai ya samu da karfin tsiya ya gama sakandiran nan. Ni. kuwa nasa idone, saboda bani da karfi a
kansa”. Da sauri ya amsa “Ku daina fadar haka Baba, ya za’ace bamu da iko
Bayan Musulunci yabamu namu ikon? Ka gane
Baba? Babu wata doguwar magana, daga nan idan
, mukaci’ abinci, muna tashi Dutsen Abba zamu
nufa ……don?” “Karbar’ Suleman daga hannun su,
tunda sun kasa rike maraya, daidai da tsarin Babansa”. Ya yi dan shiru kansa sunkuye, kafin yace “Allah yasa mu iya”. Yace “Insha-Allahu zamu iya”. Suka”ci-gaba da cin abinci, suna ‘hirar‘rakin duniya.
Karfe uku suka fito. tafiya. ga kuma jama’a har. Sunzo ganinsa A gurguje ya gana dasu. sannan ya
masu hasafin daya saba kowanne aka bashi NASA a  cikin“
ambulan. Alhaj gaba Baba liman na baya . Sulcman na beye dasu ya baza kunne’murna kaman
ta kashe shi. ya shiga motar. Diraba yaja su, har Dutsen Abba. Suna tsayawa kofar gidan. Yara suka yanyame. motar suna Ihu.
“Ga Sule Ga Sule Bakinsa har kunne, suka fito. yayi cikin gida da sauran yara. Bayan ’yan gaishe- gaishe da ‘yan uwa da mahaifin su lsiyakun. aka kawu masu ruwa suka kukkurba. Kafin Liman yace.
“Magana ke tafe da mu Malam Tanko akan Sule, ne Abdul-Rasheed nan zai maku bayani. Tare da fatan za ku fahimce shi. kubashi hadin kai”.
Ya dubi Alhaji yaci-gaba “Abdul-Rashced  yimasu bayani”. Ya gyara zama. Yace “Baba, maganar ‘ Suleman ce ta kawoni, a hakikanin gaskiya so nake in roki arziki ku bani shi in rike, sabuda nima in rinka jin motsin yara a cikin gidana tunda har yanzu allah bai nufeni da samu ba. Wannan shi ne abinda ke tafe damu tare da fatan za ku karbi rukona”.
Malam tanko yayi shiru tsawun lukaci, kafin ya nisa. Yace ‘“Gaskiya Alhaji kazo min da babban batu, wanda daba kai bane, babu wanda zan saurara akan wannan magana. Domin mu ‘yayanmu bama badasu
riko. Anan suke girma cikin dangi kuma su tashi cikin sana’armu ta noma.
Kai da ganin Sule kasan ba ragun namiji za’ayiba, don kuwa yanzu, duk tsaransa basa kamoshi, idan ya kama latanya. bugu da kari inakallonsa tamkar ubansane, sasai yana debe min kewa. Amma bazan hanaka ba Alhaji, uzurinka mai ban tausayine. Saboda haka ga Sule nan duniya da lahira na mallaka maka shi”.
Suka dubi.juna Alhaji Abdul-Rasheed da Baba Liman, kowannan su yayi ajiyar zuciya.‘liman yace “Alhamdulillahi! Nayi farin ciki da wannan karamci‘ Malam Tanku. Allah yabar’ zumunci'”. Alhaji ya karba.
“Nima godiya nake Baba. Allah yabani‘ikon rike amana”. .Duk suka amsa da Amin”. Haka”yan uwan‘ marigayi lsiyaku kowa‘ya tofa albarkacin bakinsa, dagaji kasan akan dule zasu bada suleman Matan gida nata ‘ mamaki, wasu .na fadin shi kenan Sule zai zama dan birni.
Yayi sallama da kowa ya Shiga mota, ko dama ‘yan tsummokaransa ‘na can Kauran Juli daya jedasu. Sauran ‘yan gidan sukayi Cirko-cirko da gani suna kewar’ dan-uwansu. Naira dubu Alhaji ya aje masu. ,
Yace su kucincina babu-yawa. Take nan~ ya kara siyesu.‘ suka kama hanya, cike da. murna» kamar yadda suka bar zuri’ar Malam Tanko baki har kunne, suna rabon kudi. ‘ ‘
cikin’yan mintoci.allah ya dawo da su gida. Daga yadda‘suka shigo cikin gidan. gwaggo Atine ta tabbatar da‘ anyi nasarar tafiya. .ltama da murnar ‘take masu
marhabin. Bayan sun natsane take tambayarsu Ina fatan dai tafia tayi kyau sukace kwarai kuwa
ta yi kyau. Hankali kwance Abdul’Rachaed yayi Yan dabaru da hikima, take nan Malam Tanko ya amince. tai mirmushi sannan  Ta dubi Suleman tace”Yaro zai zama dan
birni, iye! Saura kar ka maida hankali a karatun, kaga  yadda zamu gauraya dakai”. Ya sadda kai yana murmushi
muddun kaqi maida hankali akan karatun to dawowa dakai
za,ai kaci gaba da noma. Kanason zuwa gonar‘ ‘ ne DA
yawan ciyawa?” lnji gwaggo. Ya makaqe kafada
yana kada kai, Alhaji yace “Tomu bari mu lallaba. sai kuma an
kwana biyu, ina da tafiye- tafiye cikin watannan”.

Duk suka amsa da”Toshi kenan. Ailah ya tsare. ya yi albarka”. yace”Amin”. Gwaggo ta mike tana cewa “Maza ka dauko
jakar kayan naka”. Alhaji yace “Wane kaya? Ai ku barsu nan, ku
bada sadaka kawai. Ina zamu da wadannan tsummokaran? Ta wuce tana ‘yar dariya.
Gaba daya suka fita daga dakin. Alhaji yana mikawa Mairo wasu sababbin kudi ’yan Naira biyar- biyar Wanda shi kansa alhajin baisan adadénsuba mairo nata zuba godia  Gwaggo ce dauke da daurin a buhu”. Alhaj yace “Me muka sumu a  buhu haka Gwaggo?” Tace “Duk sakon Suwaiba ne, tsarabar kauye ce,
Yace Ina fatan babu daddawa a ciki.” Suka bushe da daria “Daddawa ‘yar bakin jini, ba ason daukarta. Amma yanzu ka gama lashe ta cikin miya”.
Yace “ba cewa nayi bata da dadi ba Gwagga. kashe mota takeyi da wari. kaji but yayi sati yana maida bayani”. Dariya suke tayi har” kofar gida.
“Daddawa kam akwaita a ciki. don na san abokiyar tafiya ce cikin girkin da Alhaji kafiso,ko kuwa?” Yace “Kin yi gaskiya gwaggo na to mun gode”. Magaji direba ya tashi da sauri, ya karbi kaya ya jefa but. ‘ Ya rufe, yayin da Alhaji da Suieman suka shige motr  yana kara sallama da iyayensa. ‘
Direba na zama, ya tada mota yaja suka rankaya. Su gwaggo nata masu fatan sauka lafiya. lta ma Mairo bata bata lokaciba, ta kwashi tsarahar da gwaggon ta deban mata ta wuce gida. cikin jin dadi da
murnar’ tafiyar Suleman Kaduna.                  ***********
Suna isowa Kaduna. basu wuce gida ba. sai da Alhaii yasa direba ya kaisu  wani katon shago inda ake siyar DA kayan zamani. kuma na yayi.
Alhaji ya jibgowa Suleman ingattattun sutura cikin farashi mai sauki da kudi kalilan masu alha kudin da kenan. Sannan ga takalmansa sandal kai harda  kambas. sai silifas dan Medina na wanka dana yawon tsakar gida. da
Kaya niki-niki! Suka isa gida, farin-cikin Suleman ya kara habbaka, murna kamar ta kashe shi. suka isa gida. Ya rungume ledojin kayansa.
Magaji ya rungumo huhun tsarabar falon Hajiya Suwaiha, suka shigo Suleman na ta zare ido don bai
taba ganin kayataccen muhalli irin wannanba. Lokacin
da ake zuwa dashi, a gaye yake babu wayau.‘ Hajiya Suwaiba ta fito tarbansu “Lale! Ah harda‘
bako mukayi?”‘Alhaji yace yaro kika samu”. ” Ai na ga kamar Sulen Mairone! Koba shi bane?” _
Ya amsa “Shine, daukoshi nayi yazo nan ya zauna yayi makaranta”. Bakinta har kunne. Tace “Masha-Allah!” Ya katse ta “Wai ashe yaron nan haya karatu, sai zuwa gona da yawon ciyawa?”
Baki sake tace ‘Kai haba? Sulemanfa ya kai shekara takwas!” Koda yake bamamaki. kauye suke
kuma naga daman kamar Babansa ne kadai wayayye. ka?
ga kuwa babu wanda zai kula da abinda ya dace. Yanzu
kana nufin ya dawo nan dindindin? “lnsha-Allahu. ai takanas muka tafi da Babana muka
roki su bani shi in rike, don mu rinqajin motsin yara., Kawai dabara nai don mu karbeshi cikin ruwan sanyi, hankali kwance”l
Tayi’ yar dariya ta ‘dafa kansa “Wallahi ka kyauta Alhaji. ‘ka taimaki maraya. Allah ne kadai zai biya ka. Don Allah dubi yaro kyakkyawa. ‘ ‘ ‘
Ya taso babu ilimi, ai an  cutur dashi. Ubangiji ya bamu “ikon rikewa”. Kalamanta suka karawa Alhaji farin-ciki. ya amsa ,da “Amin. ga kayan da muka shiga shago nadan siya masa”. Tace ‘To, Suleman muje kayi wanka,’ sai kaci abinci ko?
Ya_ amsa da kai. Ta karbi jaka daya, ya bitada ragowar biyun. bayi ta shiga dashi tasa soso da sabulu. ta wanke shi tas! Ta bashi’mai ya shafa.
Ta bude sabbin ‘kayansa ta zabo- masa wani t shirt da Wanda yasa.
‘ alhajin na‘kishingide da jallabiya jikinsa yana kallo talabijin .sulaimanne ya shigo falon idanunsa kirr kan talabijin din Ya dubi  shi, yaga yaddah ya saki baki kawai yana kallan talabijin din. Alhajin na fadin to: ‘ zauna”.mama sule sam bai jishiba, har Hajiya Suwaiba’ ta
kawo masu abinci da ’yan kayan lambu yankakku ta aje
Ta cira kai ta dubi Suleman. ta kwashe da dariya‘ yadda ya gantsare gaban T.V. ya yai mata zuru, da ido da baki
duk wanda ya ganshi sai yayi dariya. Alhaji yace. “Suleman ki kewa dariya ko?” Tace “Shi kuwa’
‘ dubi yadda ya tsaya. kamar kashi ya koralo qata. babu wurin yi”. Alhaji ya hau dariya, “Tunda kuka fito naketa cewa ya zauna, ko jinama baya yi”,
‘Ta janyo hannunsa tace “Kai bangaura! Zauna mana”. Sannan faya dawo cikin hankalinsa, ya dubeta yana yan mazurai. Tace‘ “Duk kallon ne haka? To zauna ga abinci”..Yana zama, ya sake maida hankalinsa kan talabijin din Alhaji yace “Ka kwantar da hankalinka, kaci abinci, Idan
kallone, sai ka gaji da shi”. , Tace “Kallo za’ayi ko karatu?” Yace “Ahto.’kema kin san dole ayi kallo kafin a saba”.‘Tayi ‘yar dariya tana dubansa “Tokai fa abincin’?” Ya kada kai “A koshe na ke yanzu, ayimin hakuri zuwa bayan issha’i”. Tace “Anyi maka. Naga’tsarabar Gwaggn, kullum dai’bata ~ gajiya. Na gode”.
Yace “niya kamata’kiyiwa godiya dana nayoo miki dakon daddawa”. Tace “Waya ficin muriyar daddawar?” Ya fara dariya “Kun hada baki da Gwaggo kenan don
‘ltama haka tafadi? Lallai Gwaggo ta San gaskia Sukaci gaba da dariya. Washe gari DA safe hajia suwaiba tace dole a nema wa Suleman burush don wanke baki, don haka Hajiya Suwaiba ta bashi kudi. Toxo  in nuna maka inda za ka siyo”.
Suka fito harabar gidan mai girman gaske ne. kuma yana kunshe da yawan gidajen da suka kai takwas. Ta dube shi. Tace “Ka na fita ta kofar nan, zakaga mai dan shago jikin Katanga, ‘kace ya ‘baka burush din wanke baki”
_ Yace “To. Tana tsaye yajé. ya dawo da burush din a hannunsa, suka koma cikin gidan tare. Yana biya da ita har bayi, ta shafa masa man gage baki. Tace “Ungo
maza ka dirje bakin”.
Ya karba ya jefa .bakinsa, ya tallabe haba. Yace “Wash! Akwai zafi abun”. Ta kara ware ido. Tace “bude, bakin in gani .
Ya bude gaba daya’ bakin ya gauraye da jini. Tace “Inna-lillahi! Baka taba wanka baki bane Suleman?” Yace “Da ruwa kawai muké kuskurewa”. “Ruwa kawai?” “Eh! ldan munzo alwala, da asuba”. Ta kada kai. Tace “Dale baki ya rube. Wata sabuwa kenan, ai babu maganar burush. Ina zuwa”. ‘ .
Ta yi waje tana fada. “Wannan rashin kulawa da_’ yawa take! Gaba daya bakin yaro ya rube!” Kicibis suka
. yida ‘Alhajin ya fito daga dakin sa. “Ke dawa kike fada?” Tace “Kaga bakin Suleman? Gaba daya ya rube‘, yana sa burash, jini kawai ke zuba, duk dasashinsa ya kwaile”.
lol. 

naku har kullun

www.Facebook.com/abdullahi.Ismail.salanke

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE