Makaranta duniya chapter9

MakarantA duniya

          Chapter9

Har garin Allah ya waye, baya wa su Mansur magana, abin bai wani dami Mansur da Naseer ba, amma shi Khalid da yake tsaransa ne sai yake tambayarsa abinda ke damunshi shi.
‘ Suleman ne kadai kwance cikin dakin Khalid, ya shigo ya same shi ya zauna ‘gefe. Yace ,”Wai meke damunka ne Suleman?” Ya watso masa-harara. Yace “Ban sani ba”. Yace “Naga dai haka kawai bazaka daina yiwa mutane magana ba”. Ya tashi zaune 

Yace “kai Malam! Banson. surutu,fa ba dai gulma bane? ldan har abinyi ce aje ayi tayi”. Khalid ya bishi da kallo, kafin. Yace “Aiba’gulma bane, gaskiya ne. kuma Baba ne yace a gaya masa duk abinda wani ya yiba daidai ba”. Ya Watso masa harara.
– “‘Nadai gaya makaba na son surutu, tunda abin haka .daga yau ba ruwana da kowa kuma ka sani, har Murjar ma babu ruwana da ita”.
: Yana dariya. yace “Murja?” daidai lokacin
Mansur ya turo  kai cikin dakin ya cafe “Me~ Murja tayi, ake maganar ta?” Khalid yace “Wai fushinmune ya shafeta. Suleman ke cewa har ita babu ruwansa’da ita”. Mansur ya kyalkyale da dariya; ya”zauna daga Bakin gadon ya dUbEshi”Kai, yaron nan  kai dama har ka kama da gaske ne?
don’ Baba’yana wasa, yana newa yana maka ‘rikon Murja? Lallai Sulaman‘ kai yarone. To waima me
ya kawo maganar Murja cikin maganar mu? Na lura baka son gaskiya Suleman. idan Baba bai yi maka fadaba, towa ka keso yayi maka? Ka yi tunani mana”. ‘
Ya ja dugon tsaki, ya tashi ya bar masu dakin, suna tayi masa dariya. Khalid Yace “Kenan shi nan ya kama da gaske yana son Murja ne?” Ya tabe baki. Yace, “Uho masa”. Sukaci gaba da dariyarsu.
Ranar litinin da sassafe. Hajiya SUwaiba‘direba ya fara ajiyewa a asihiti (Nursing home), sannan ya dawo ya kwashe Alhaji dasu Suleman. Tana zaune tana jiran Likita harta gaji, ta kaiga kwanciya bisa dogon bencin. Jimawa kadan.
Likitoci sukazo aka shiga da saban katin yau tare da sauran masu jinya. Allah da ikonsa nata ne farko, koda yaka ta doka sammako. Saboda haka ita ta fara shiga wajen Likita, wacce ta kasance mace ce
Ta yi mata bayanin komai har da irin magungunan data sha. Take nan tai mata gwaje-gwaje  ta tura a dakin yin gwajin. ‘
‘  jini kala biyu da fitsari, duk ta bayar ta zauna jiran sakamakon cikin ‘yan mintocin da baSu wuce ashirin ba, aka kirata ta amshi sakamakon guda uku, ta
koma ofishin Likitan. Tana zaune gafe harta sallami wacce ke gabanta.
Sannan ta dubi Hajiya Suwaiba. Tace “Kawo in gani”. Ta tashi ta mika mata kafin ta zauna jugum Tana jira. Tana gama dubawa. ta kalleta dauke da fara’a.
Tace “Madam baki gane juna biyu gareki bane?” “Na’am?” Ta amsa, don bata fahimci bayanintaba”. Nace “ciki gareki wata biyu..
Take nan ta dauke wuta, ido waje baki sake take ; kallon Likitan. Itama ta zura mata nata idon. Tace “Kamar baki yarda ba? ‘Ai yakamta ma ki gane hakan. sai ka ce wannan karonne na farka?”
Tayi wawan ajiyar zuciya. Ta daga hannu sama tana fadin “Allah, Allah na gode maka”. Mamaki ya kama. Likita ganin hawaye na zuba mata, saboda haka ‘ ta katse ta “Meya sa haka Madam?”
Ta kada kai cike da murna. Tace “Dole ne Likita. Wallahi dole inyi kukan farin ciki, ban taba samin cikiba, shekaru ashirin da takwas kenan da auranmu Dukta, yaba zanyi kuka ba?” ‘
Likitan da kanta ta tashi ta dafa kafadunta biyu. Tace “Gaskiya ina taya ki murna ke da Mai gidanki. Amma ki kwantar’ da hankalinki, ki saurari bayanin da zan yi miki, duka?” Ta gage hawaye. yayin da Likita ke dawowa kujerarta ta zauna.
“Kamar yadda na gaya miki, kinada ciki,.sannan akwai maleriya a tattare da ke kuma illa ce babba ga mace mai ciki,‘ ta sami zazzabin ciwon ‘sauro. Saboda
haka dole zaki fara kilinik, tun yanzu, donmu tabbatar” da cewa maleriyar nan ta rabudake.
so yannu zan‘ rubuta miki‘ magaunguna, zan? kuma baki takardar kikai~can sashin masu ciki. zasu’ kara miki dukkan hayanan da suke dangane DA . ciki
Ta amsa “To Dukta  sannan”. Likita ta rubututa mata abubuwan DA zata buqata
Hajiya Suwaiba na tsuma kamar tayi tsuntsuwa ta kaiwa Alh‘aji albishir. Ta miko, mata takardu daya taa magunguna. daya Wanda zata kai sashin masu ciki, ne
Tana ta godiyar tafice. Kai tsaye hanyar-yan masu cikin ta wuca, ta kai takardar. Sister tayi mata dukkan bayanai ‘akan shirye-shiryen fara awo da zuwa ganin ‘ Likita, duk bayan sati biyu.
_Ta dawo gida ‘dauke’ da farin-ciki :‘da baya misaltuwa, lokacin kuwa karfe goma ne daidai na safiya. ‘ Tana aje mayafi. Alwala ta ‘shige bayi tayi, ta hau” ; sallaya ta bada nafila raka’a biyu, ta yiwa Allah’godiya tare da kara nuna farin-cikin ta ga kyautar daya bata,_ ” sannan ta rokeshi karin lafiya kuma ya‘ albarkaci abinda yabata. ‘
Bayan ta kammala, tayi shiru kan sallaya tana  tunanin irin hakurin da kowa Yake. Lallai hakuri maganine. Duk wanda yace hakuri bai yi masa rana ba. ‘ tabbas baiyi hakuri bane
Gaba daya ma taji ta warke babu‘abinda ke damunta. Jimawa kadan ta fito ta dauko ruwa, ta zauna shan magungunan data siyo a famasin asibitin.
Sannan ta kwanta ta yi ta tunanin M Maraicinta da irin zumuncin gidansu, kowa ta kansa‘yakeyi. lta kadai mahaifiyarta ta haifa ta mutu. ko ganin kalarta batayiba. Shekara daya tsakani. Shima mahaifinta ya kwanta dama. Ta dai tashi babu tsangwama wajen ‘yan uwan mahaifinta. Amma basu da kulawa akan zumunci.
Ga su suma din duk sun kare, sai ‘yaya  da jikoki. Wannan kansa na gabas, wancan nasa na arewa. Ta numfasa, zuciyarta ta sake dauko tunanin Alhaji. Wane goron albishir ya kamata ta karba a wajensa? Ta yi dan murmsuhi, tana kada kai, bata san lokacin da barci ya saceta ba. ” , ‘ Karfe daya ta farka tayi sallah, ta nufi kicin, abincin data rage DA safe ta dauko shi ta cinye ta sake shan magunguna, Daga nan ta dawo kicin ta fara hidimar abinci. a , Haka take bata cika dora girki da wur’iba. sanin cewa daga Mai~gidan har ‘ya’yan gidan basa dawowa, sai biyar ta kawo jiki.
Sai dai ko inbaqi tayi Lafiyayyen abincin da Alhajin yafiso shi ta mulka masa, watau tuwon dawa miyar‘ kuka. Komai yaji, . A gefe kuma farar
shinkafa ta dafawa samarin kasancewar.
don dama tanada miyar dage-dagen naman rago. Bayan ta kammala, ta sallaci la’asar ta sake gyara jikinta. ta kwanta a falo tana kallo sama- sama kamar yadda ta Saba. ‘ ‘
Yaran suka fara shigowa,‘ta amsa ’sallamarsu, “Ya jiki MamanmU?” Ta tashi zaune tana amsawa “Jiki yayi sauki  Shi kuwa Suleman rai, bane ya dube‘ ta. Yace “Wallahi’ Mamanmu. ki ‘gaya masu. ba ruwansu danifa, to”. ‘ ‘
Ya kama hanya zai .shige daki yana kwafa, tasa
baki ta kirashi “Tozo mana, me akayi’?” Ya dawo ya
tsaya kamar’ zai fashe, “Nace meya faru?” Ya’tsaya yana hura hanci, ya kasa magana saboda tsabar fushi. Tana maSa dariya.‘ Tace “Kai Sule- Zuciya ‘kamar; kutnru? Me “aka yi nace?” , Mansir yayi ‘yar dariya. Yace,”’Mamanmu bafa wata magana. bane, wai’don ance Suleman na Murja; shi ‘ kenan yaketa masifa”. Ta kece da dariya “Ahh yo in banda abin ka Sulaman, menene na fada? Lallai zakayi ‘kuskure, sunefa masu daura auran,ka.fasa ‘da Murjan ne?” Haushi ya kara kumeshi, ya balle murfin kofar dakinsu ya shiga, ya bankotavda karfi’.  Hajiya Suwaiba’ ta saki baki “Wu! Ango yayi fushi. In banda Suleman, wake fada da sarukai’? Toku kyaleshi, karwanda ya sake kula shi, tunda baya son ana -fadin”. Nasiru yace “Wai ‘dama da gaske ne Mamanmu?”
Tayi murmushi tace “Ai Babanku ne yace yana~masa riko, wata kila kuma wasane ya zama gaskiya”.
Suka wuce suna dariya. Khalid na fadin “Ai kuwa da mun sha biki”. ’Hajiya Suwaiha tacigaba da dariya. Ai kodai za musha biki! Kai ‘wadannan yaran?” Dariya abin kebata, don haka tacigaha da dariyanta. ‘-
Har suka fito daukar abincisu. Suna kan tebur Suleman’nata jagwalgwala nasa abincin ‘da cokali. Hajiya Suwaiba ta zura ‘masa ido kafin.Tace ‘”Waini Sule abincin ma yaki shiga ne? Ko a kira Murjar ne tazo tayi maka dure?” _ ‘ ‘
Duk suka kece da dariya. Suleman ya saki cokalin ya tashi da saurinsa, zai koma daki. Sai Alhaji ya fado da ‘sallama. ‘Suna’ dariya suna amsawa “Baba sannu da zuwa”.
Ya zuha masu ido yana ‘yar fara’a, “Me ya faru ‘ aketa dararraku?” Hajiya Suwaiba tace “Hhm! Shirmen yaran nan mana. Suleman keta bamu dariya”. me yayi”? Suleman din ya kwasa da sauri, ya shige daki yayin ‘ da take fadin. Wai baya son‘anace masa Suleman na Mur’ja._ ,Duk wannan hurahancin na masifane, shine nace kUnya zai baka, bayan karigada kayi masa riko” Alhajin ya hau dariya shima “Ai kuwa yayi’ — karya, gube-guben nan’ zan kaiwa Alhaji Bara’u gaisuwa. ‘ ‘ sai mugata tsiya kuma”. Ya wuce ya bude kofar dakin.
amma bai shigaba. daga bakin kofa. Yace “Ka jini ko baka jini ba? Gabe za’a daura auren in dawo da ita gidan nan. Dubi kansa kamar angon Murja”. ‘ ‘
Ya juya cikin falon, suna ta dariya. Shi kuwa Suleman haushi kamar ya kashe shi. Alhajin ya wuce dakinsa. Hajiya Suwaiba ta wuce kicin ta daukomasa abincinsa ta biyoshi dashi. Har yanzu fuskar ta dauke da dariya take, saboda daman a cike da férin-‘ciki take
“Ashe dariyarki zata kare yau”. Ta aje ‘tiren gefe’. Tace “Suleman iyaka ne, su kuma kome yajasu tsokanar tasa? Bakaga zuciyaba, kamar’ yayi bindiga”.
Yayi dan murmushi. Yace “Nima bari in kame
baki na, tunda ana min kawaici ko dama wasa nakeyi. Toya jikin? da alama yau ki na dan jin karfi’?” Ta rausaya kai tacé “Yau kam Alhamdulillahi!” Me suka ce  asibitin?” “Sunmin gwaje-gwaja, sun kara min magunguna”. Yace “Allah yasa a dace”. Ta amsa da “Amin”. Ta bude kula tana zuba masa abinci. “Lallai kina jin karfi,‘ girki biyu kenan, kikayi fa?”
‘ Tace “Eh mana, amma wannan‘ tuwon na albishir ne. cida yawa kasha labari”.’ya zuba mata ido “Ko? To tsaya kiganima kuwa”. ‘
Ya dauraye hannu, tana kallonsa tana murmushi, ‘ yana ta aikawa cikinsa tuwon “Miyar nan tayi zaki_ Madam, da alama albishir din ki mai zaki ne shima. Kin samomin bazawarar ne?
Fara’arta ta karu. Tace “Me yasa ka cinka? Ai kuwa saika bani gorona, tunda ban ceka cinkaba”. Ya kada kai. Yace “Bakici goro ba Suwaiba. don ban cinka ba
Hasali ma cewa nayi ki barni inyi shawara. kuma tun jiya nake fada da zuciyata, sabuda taki amincewa da shawararki. inda son samune, da Suwaiba ta dan karamin ‘lokaci akan maganar nan”.
,duqar dakai tayi qasa ta kada kai fuska yamutse. Tace “lta kuma bazawarar “nayi yaya da ita yanzu? Ya kamata ka gane cewa nan gaba kadan haihuwa zanyi, ko banza zan sami mataimakiya wajen kula da kai da yaranmu”._ ‘
~ Da yake bai fahimcetaba, sai ya murmusa. Yace
‘ “Duk naji, amma ayi min hakuri, haihuwar tazo,’ sai asan abinyi”. “Aita samu Alhaji”
“Mene?” Tace .”HaihuWar’ mana”Ban fahimcekiba?” Ta yi ‘yar dariyu. Tace “Ashe har da shigar ciki ke wahalar‘dani Alhaji”. Tuni ya tsame hannu daga abincin Waiwa keda shigar cikin?” Tace “Suwaiba!.”. Baki sake, idonsa a kanta tsawon lukaci bai iya kara mutsiba.‘ ,‘
Itama tabishi da kallo, tana dariya, “Kana mamaki ko? Ni kaina da‘Likitan nan ta gaya min ban yarda ba Alhaji”. Ta numfasa da ‘karfi, kwallar dadi ta zubo kuncinta sannan taci gaba da fadin
“Allah mai ikone akan duk abinda yaso, mai hakuri kuwa zai dafa dutse har ‘yasha romonsa. Hakuri yayi ’manarana. gashi Allah ya amshi addu’ar mu”. Kai! Alhaji Abdul-Rasheed fa ji yake tamkar mafarki yakeyi, shiyasa ya-kara tambaya.
Wai daga zuwa asibitin yau-yau, akace ciki ‘ gare ki?” Ta kada kai, tana gage kwalla; tasan kan Alhaji fa, ya kwance, saboda haka. Tace “Cigaba da cin abincinka’ Alhaji‘. Nasan bazaka yarda daniba. Amma maganar bazawara na kara maka kwana biya ka sake shawara. Ci abincinka, ka daina kallona’ Tsam! Kawai taga ya mike ya nufi bayi, jim kadan- ya fito,» duk gabobinsa da ruwan alwala‘ya nufi sallaya, ya kabbara sallah… Take nan hawaya suka tsunke masa. ” Lafiyayyun raka’o’i biyu ya kawo Sannan ya mika hannu sama. ‘ ‘ ‘ l ‘ Yayi ta zabga godiya ga Allah tare da fatan Allah ya sauke ta lafiya. Ya basu zuri’a mai albarka.-Tare suka ~ shafa’ addu’ar, yabi ta da kallo kafin ‘yasa hannu ya yafitota. ‘ ‘ Ta matsa kusa dashi. Ya tallafo kafadarta.‘ ‘Yace “Me kikeso goron albishir Suwaiba?”  ta dube shi, yasa hannu ya gage mata kwallarta “Ki gaya min duk abinda kikeso  lnsha-Allahu zan ,yi miki, muddin baifi karfina ba”. Tayi dan murmushi. Tace “Addu’a. Allah ya raba mu lafiya”.
Yace“Tun daga yanzu na fara, kuma zanci gaba dayi har zuwa lukacin fituwar abinda ke cikin ki. Amma .ki sani, bayan addu’a kin cancanci wani abu na ‘ tukuici daga gare ni”. Tace “dUk abinda kaga ya dace”. Yaja habarta. Yace “Nikuwa nasan abinda ya dace dake; sa ido, zan kawo miki da yardar Allah”
Tace Allah ya yarda”. Ya amsada “Amin”.’Yaci gaba da kallonta, fuskarsa bayyane da‘ farin ciki. Ji yake tamkar yau ya bareta a leda. Jim kadan ya numfasa’. Yace “To wane shawara suka baki a asihitin?” ‘
Ta zayyane masa komai. Ya kada kai kafin Yace “Dole kuwa a kula, don maleriya na tattare da illoli masu hadarin gaske. Nida son samu nema, su. baki gado ki zauna can gabansu, har sai sun tabbatar da sun fatattaki maleriyar nan”. Ta sake yin ’yar‘ dariya; Tace “Yanzu ana .cewa an bani gado, hankalin kowa zai tashi,gwara in zauna insha maganin, ’wani satin in koma a gwada kamar-yadda ‘  sukace’. Ya zuba mata ido “Kinfi’son’hakan?” Tace ‘ Karka damu. Allah zai tsare mu”. , _
‘ Yace “Na. yarda dake”. “Toya maganar .bazawarar?” Yace “.Jin baki yasaki wannan tamhayar. ‘ In. kinaso ki faranta min rai, kitambayeni abubuwan da ‘ bebina yafiso”. Ta sadda kai tana ’yar dariya. Shi kuwa kallonta yake  farin-ciki, kamar ya kashe shi.
lol
Alhaji baiyi kasa a guiwa ba, yana fitowa ya dauki mota. duk inda yaga mazaunin masu bara, saiya tsaya yayi sadaka, sannan ya wuce wani katon shagon sayar da kayan mata na kwalliya. ‘ ‘ .
Sanin Hajiya Suwaiba ,mai matukar son shadda ce, yasa ya danqaro mata tsala tsala kala uku. Ya koma bangaren takalma,~ ya zabo mata mai kyau. Yasa aka kawo masa manyan ‘mayafi guda biyu, ya cake kudi, ya amsa kayansa ya’fito.
Akwai inda ya Saba ganin masu ‘siyarda’kayan wasan yara a gefen hanya. Can yaja birki yayi kiran, mai kayan, ya’tasoda-‘sauri. Yace “Me zaka siya Alhaji?” Yace _”Kunada kacau-kacau?” ‘
‘ Ya amsa “Akwai Yallabai!” ‘Ya juya da sauri, ya kwaso su’kala-kala masu kyau. Ya gaya masa kudaden su, mai tsadar cikinsu Alhajin ya’dauka akan kudi Naira talatin. Daga nan bai zame ku’inaba, sai gida. Samarin gidansa na Zazzaune a koridon gidan, nan da nan suka” fara rige-rigan amsar kayan. Khalid ya mikamawa, don shine karamin cikinsu, domin Sulaman-ya bashi watanni takWas.
“Ka wuce min dashi dakina”; lnji Alhajin ya wuce, suka rufa masa baya. Bayan amsa sannu da zuwan Hajiya SUwaiba. Dakinsa ya shiga yin alwala, dun gabatar‘ da sallar’ magariba.
Karfe tara Alhajin ya shigu gida. Suleman na biye dashi da tiran kayan abincin‘da sukaci da‘ makwabtansa. Sun kammala kallontashar (‘NTA News),gaba dayanSu, sannan kowa ya nemi makwancinsa. Yana ta shirin kwanciya. Ta shigo dakin ta zauna gefen gado. Tace “Ina RUB dinka in gogawa kafafuwa na?”
.. Ya jawo dirowa,’yana fadin “Yau kuma kafafuwa ke ciwu?” Ta‘ce”‘Zugi suke min. Ta karba ta bude. ta fara mulkawa. Ya zauna gefe ya jawo ledar kayan nan. Yace “Sannu Maman twins”. Tana murmushi ta amsa; “Kaima’ sannu, Baban twins”: Yace “Dole in baki tukucin wannan kirari naki”;
Ya jawo leda, ya ‘dauko kacau-kacau, ya kada bisa fuskarta. Ta kyalkyale da dariya kafin. Tace “Amma dai Alhaji babu wanda ya kaika shiri‘rita. Kawai sai kaje ka siyo kacau-kacau?” Yace “Kawai ne? Abin wasan bebina, yafi karfin kawai; don haka ki. kimtsa bakin ki”:
Ta dan’ tabe baki. Tace “Na tuba”. To an yafé.’ bude wannan ‘ki gani”. Ta karbi kacau—kacau tana dariya tare da kada shi kadan -kadan. ‘ .
_ Ya zaru shaddojin ya dora bisa jikinta, ido waje take’kallon kayan. Yayin da yake ci gabada fiddo sauran kayan. yana’ laftawa’ a jikinta. Sannan ya dubeta. Yace “Goronki ne, ina fatan sunyi miki?” ‘ ‘
Ta sauke numfashi. Tace “Huunn…_… ,Wadannan kaya Alhaji? Lallai sun bayyana min farin-cikin ka. Tona gode. Allah ya‘ kara budi, ya kara rufa mana asiri!” Yace
‘ “Amin Maman twins!” Ta shiga da kayan tare da zuba
santin kyansu.
Kullum cikin farin-ciki suke. ‘Alhaji kuwa ya daura dammararrkula da Hajiya SuWaiba kwarai dagaske. Ba ta tsallake duk‘ wata dokar’ da Likita ya gindaya mata, shiyasa da taimakon Allah ta sami saukin maleriyar dake jikinta, ya zamana lafiya tazo sosai a jikinta, illa dan abin da ba’a raSaba. ” ‘
Yayin da ’yan uwa’ da abokan arziki ke ta zuwa masu murna tare da fatan Allah ya raba lafiya. A Cikinsu akwai Inna Mairo, wacce‘ ta kwana biyu a Kaduna,‘tana
– taya Hajiya Suwa‘iba dawaniyar gida. ,.
ltacema tazo masu da labarin rashin lafiyar Baba Liman. duk da dai tace zazzabi ne kawai, kuma’ ya Sami ,sauki. Hankalin Alhaji‘ Abdul-Rasheed yana‘ kan ‘mahaifinsa, dun haka yau karshen sati suka shirya tafiya duboshi.: Sun isa Dutsen Abba. Mansir ya dubi Suleman. Yace “Suleman .ga DutsEn Abba” Fuska yamutse ya .amsa. “To menene?” Yace “Me kuwa?” Daga gidan gaba Alhaji Ya sanyo baki, “K0 a sauke kune, idan kun ‘gaisa dasu, ku same mu a can?” ‘
Gaba daya su ukun suka amsa “Eh, a sauke mu Babe.” Suleman ya watso masu harara. yayin da Alhajin rage tayar motar har ya sauka gefen titi. Ya tura hannu aljihu ya fiddo kudi sababbin Naira hamsin hamsin ya mikowa Mansir, Yace”Ungo wannan, ku raba biyu. rabi ku basu, rabi kuma kuyi kudin motar zuwa Kaura”.
Ya karba yana fadin‘ “,to Baba” suka sauka Suleman ya kawo iya wuya. “kuce muna‘ gaisha su’.’ lnji Hajiya Suwaiba._Duk suka amsa banda Suleman. Alhaji yaja suka wuce, ha gaba daya lura Sulaiman baiso saukan ba. .
Suna tSaya suna jiran tsagaitawar motoci su samu su tsallaka titi. Mansir ya dubi Suleman yace”Naga kamar kana fushi ne Ya watso masa’harara yace”Ban sani ba”.
Duk suka zuba masa ido, yaja tsaki ya kauda kai. nasiru. Yace “Meya kawo tsaki?”‘Mansur yabada ‘ amsa,Bansan me‘ yasa Suleman baya Son shiga danginsa ba ……
Ya juyo da sauri ya katse .shi, “Ya’isa haka, dangin’ku ko nawa?” “Ba maganar fada bane suleman”. Inji Khalid. Mansir ya cafe “Don Allah rabu dashi  karya. akayi masa?”
Ya farke rafar kudin, ya shiga rabawa yana fadin “Wa yafi zuciya? .Ungo namka rike a hannun. ka, idan
in munje ka basu”. Ya karba a wulakance, ya tura a aljihu shima Mansur ya tura ragowar nasun aljihu. 11′
Babu wanda ya sake magana; ‘suka tsallaka Suka taka‘ har gidan su Suleman. “Ga Sule! ga Sule’ Haka kowa ke fadi. ‘Yaqe kawai yakeyi,
Bayan sun gaisa’da matan gida, suka shiga dakin Kakansa Baba Tanko. Tsohon na kwance, ‘ duk suka tsugunna suka gaishe shi. “Sule ‘Yan boko! Duk bokonne 
yasa aka gaiéheni a bankare?” . Yaqen ya sakeyi. Yace “Kaji Baba’ dai, tsufa ya
kama ka Baka gani sosai. Tomu mun gaishe ku, zamu wuce”. Yace “Haka da wuri? Wai ka taba zuwa ka kwana garin nan kuwa’?” Ya mike tsaye. ‘Yace “ai! saiku Baba, wa zai iya barci cikin duhu?”
Yana ‘yar dariya. Yace~”kaji dan butan da  ba’a‘cikin duhun ka taso ba? Samun wuri ko?” Ya dan tabe baki, ya zaro kudi a aljihu, gaba daya ya kirgi guda-biyar Naira biyar kenan, ya mika masa. “Karbi wannan, kaci . goro”. Ya dafe sababbin kudi. Yace “Wai har ka fara aiki
ne, kake fallo sabbin kudi haka?”
Yayi wani- saurayin murmushi. Yace “Zauna‘ nan”. .Yace “To; baka tambayi ’yan—uwanka ba, su‘ Balele?” “Suna ina?” Yace “Kasan .Kaka ce; sun tafi Zariya’neman kudi”. “business sukeyi?”
Yace “Tambayeni da hausa in gane”. Ya yi ’yar dariya. Yace “Kasuwanci na ke nufi”. Yace “A’a ga ruwa sukeyi. kafin damina ta tsaya su hada kudin aikin gona”. ‘
“Taf! Sunyi kokari.’ tomu zamu wuce”. Yace “To a gaida Alhajin da kyau da kyau. Ace ‘masa muna
‘ barar taki, idan ruwa ya sauka”.
Yace “Za’a’gaya masa”. ganin ‘yan kudin da Sulemah ya bama tsohon basu kai Sun kawoba’, yasa ManSur ya debi na aljihunsa guda guma ya kara masa. Bakin Baba Tanko har kunne yake‘ godiya. Shi kuwa Suleman tuni yayi waje, ya barsu suna sallama, sannan suka- biyo bayansa.
Yana tsaye tsakar’ gida, matan gida na fadin “Ko ruwa’baka shaba Sula?” Yace “Sauri mukeyi”. “Kai dai’baka son shan ruwan garin nan, koda yaushe kazo a
‘ daddafa kake , kamar . Ya dubi’ ‘yan’kananan yaran da sukayi cirko-cirko suna kallonsu: Ya fiddo naira biyu ya mika wa babban su.- Yace”’Kuje ~a raba maku; mu mun wuce, a gaida su Kawu”. “To Allah amfana, a gaida mutan gidan”. “Zasuji”.
‘ ‘Yace, yayin da Mansur’ ke kara wa yaran Naira biyar. Ya matsa wajen matan ya mika masu naira hamsin . ‘suka’ fito suna masu fatan sauka lafiya; Suna tafe takaddama ta balle’
“Wai Suleman kudin da na ha ka, ba sune Baba yace a basu dukaba?” Ya kyale bai tanka ba. “Baskiya hakan bai daceba, kuma ka san idan Baban, yaji ransa bazai masa dadi ba”. .
Yace “Ai sai ka gaya masa, yau ka fara?” Yace “Wannan dai ba dabi’a bane mai kyau, tunda Baba yace a basu rabin kudin. sai ka basu , bawai’ka rageba”. Yaja ya tsaya, ya dube shi ‘cikin zafi “Ban bayar dukanba. sai yaya yanzu?ko Kudin ‘ na Kawuna ne?” ‘
Mansur ya kawo iya wuya. Yace “Na kawunka ne, ai ba Sai kayi min goriba, kowa yasan na Kawunka – ne” Ya wuce sauran suka biyoshi. Sulaman yaja dagon tsaki, ya kwaso sauri, ya wucesu’ya riga’su zuwa bakin titi.
.Amma doleya jira suka shiga mota tare Suka koma. Mansur ya biya kudin matar, ba tare da ya sakE cewa Suleman uffan ba. Haka zalika su Nasiru, a takaice gaba dayansu rai bace suka iso Kauran Juli.
Gwaggo Atine ta tarbeSu da murna, tana fadin “Maraba da mazaje na! Amma ya ban ganku damanyan ladoji ba?” Duka suna dariya. Mansur yafara magana. “lna, wanda aka sauke a mota yanzu yanzun nan?” Tace
“To Allah dai ya sauwake. garda-Garda daku. babu cefane”.
Hajiya Suwaiba‘ta fito bayi,‘ ta aja butar gefe. Ta—ce “In banda gwaggo, ai duk tafiyar daya ce, kuma gaba
dayan cefanen: ,, ‘ Babansu ne ya fanshesu”. Duk suka amsa “Ah
kinji  To ku shiga ciki, tuwonku nanan na mulka maku”. SUlaiman ya Cafe “Haba dai tuwo? Wa zai ci tuwo. ana zaman lafiya‘?”
‘ . Suka Afada daki, tana fadin “Ashe zaku-wuni da .yunwa yau. ‘Karyan wofi kuke. Kowa dariya yakeyi, suka zazzauna gaban Baba Liman, suka gaishe shi, ya amsa cike’ da farin-ciki. Jikinsa yayi’sauki sosai! duk da haka tsokanarsa suke ta faman yi.‘
Wai sun ‘kusa ‘cin ‘gumba, Shi kuwa yana kishingide, hankali kwance yaketa zazzaro masu amsa.. Nan suka wuni zungur Amma. basu nuna alamun akwai sabani tsakanin Suleman da Mansur ba. hasalima tare sukaje ganin Inna Mairo. ‘ .
Duk da cewar abinda Suleman yayi. yana damun Mansur da sauran ‘yan uwansa’ kwarai da gaske, sam bai gayawa Alhajin ba, alhalin ya tabbata abinda Sulaman din yayi babban kuskure ne, wanda yake bukatar ayi masa fada. Sai dai ya san halin Suleman, yafi tsanar a. gayamasa gaskiy a rayuwarsa.‘shi yasa ya sharesa kawai ba tare Daya gayama alhajin ba
Sannu a hankali cikin Hajiya Suwaiba ‘ya girma sosai harya fito fili. Samarin gidan Suka ganshi. take
nan suka gaskata rada-raden da sukeji cewar Mamansu nada juna biyu. HaBa farin-ciki babu kama hannun yaro, duk suka kosa ta haihu. Amma duk kosawar’su, basu kai
Alhaji ba. da ita kanta uwar gayyar’. . ’KWanci tashi, a hankali ciki ya isa haihuwa.
Ranar juma’a karfe biyar’ na asuba ta haihu danta katon gaske, kamar dan larabawa a asihitin (Nursing home). Inda take yin awo  Awoyi tara ta kwashe cur! Akan nakuda, shi ya sa hankalin Alhaji dana- dukkan yaran ke tashe, har zuwa wannan lokacin da wata Nurse ta
fito masu da’sakan’ albishir.din Farin-ciki kamarsu zuba- ruwakasa susha.
Bayan sallar asuba. Alhaji dakansa ya nufi unguwar
.Shanu ya shaida masu Hajiya Suwaiba ta sauka lafiya.
Gida ya gauraye da shewa da murna mara misaltuwa. ‘ .Nan take mata uku suka bishi ya aje su asihitin,-
daga nan yaba direba mota-ya turashi Kauran Juli.- Kai~ farin-ciki baya kamantuwa. Haka Magaji ya dawo dauke da Gwaggo Atine da Inna Mairo. lta kuwa Mai-jegon da bebinta ba’a sallamesu ba, sai bayan sallar la’asar.
gida fa ‘dankare yake da jama’a koda yaushe . mata da maza kuma tun daga lakacin Mai-jegu keta samun alheri, musamman daga ‘abokan aikin Alhaji Abdul-Rasheed. ‘
Baba Liman da‘kansa’yazo  yayiwa yaro huduba .da sunansa, watau YUSUf  gefa guda kuma
. gagarumar walima angon karni ke shiryawa, wacce za’a
gudanar ranar suna.
Aliya’a kuwa zuwanta biyu daga Famheguwa kafin sunan, yau shine zuwanta na uku daya kama ranan suna.  Ta kuwa iske aiki kaca-kaca anatayi.
Domin dai wani durgujejen Sa yasha wuka. WaShe garin ranar suna, aka yanka raguna har hudu kosassu wadanda girmansu ya zama abin kallo ga jama’a, don girman nasu ya zarce misali. ‘ . ”
Ba’a maganar Mai -jego da . danta. Bayan saukowa sallar juma’a. Liyafar Alhaji’ Abdul-Rasheed ta maza zalla ta kankama a Hamdala hotel’, abin sai wanda ya gani.   bangaren Mai-jegoma, komai ya kankama abin, sai abin said Wanda ya gani Jama’a Sunci, sun sha har sun debi guzuri zuwa gidajensu, musamman ‘yan-uwa’ na mutanan karkara. .
Har washe garin sunan a‘nata hada-hadar abubuwa tare da kokarin gyaran gida, Sai dai ba’a samu kan gidan‘.ba’.sai‘ ranar litinin da kafa gaba daya ta dauke. Inna Mairo ke tare ‘ da .ita har’ zuwa kwanaki arba’in da biyu. Sannan ta koma gida tare da alheri mai dimbin yawa. ‘
Komai ya natsa.’Hajiya Suwaiba da Alhaji suka ‘dukufa kula da Yusuf (Imam), kamar yadda suke kiransa‘.
‘Kullum dare yana tare da Alhajin bisa shimfidarsa. Yayi
zuru yana kallun ikon Allah. Ya kan numfasa. Yace “Allah kaine Allah. Kai ka cancanci dukkan godiya”.
Hakika jinjiri akwai sha’awa, shi yasa idanuwan Alhaji basa daukewa daga kallon dansa, face barci ya kwashe shi. Soda kaunarsa tayi rassa a zuciyarsa kamar ya lashe shi, sabuda kauna. Shi kuwa mulka kiba kawai yakeyi. yana kara kyau.
Ta wajen bangaren samarin gidan; muna iya cewa daga Mansur’ zuwa Khalid rige-rigen daukarsa sukeyi, ba kamar Suleman ba, shi bai cika damuwa da yaraba, bawai kuma baya’ daukarsa bane.
Shi dai ra’ayinsa bamai son kula yara bane sosai haka Imam ya taso cikin gata da nuna tsananin
kulawa, mUSamman daga Alhaji. ‘ ***********

lol

www.Facebook.com/abdullahi.Ismail.salanke

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE