MALIKA MALIK CHAPTER 13 BY JANAFTY
MALIKA MALIK CHAPTER 13 BY JANAFTY
Kwabe Fuska tayi tana wani kif-kifta ido tace”Kamar ya marabana da tsirara kadan ne? Yo inace bakai ka kirani ba,kuma laifi ne don mace tazo Turakar mijinta tana kama da Tsirara kamar yadda kace..”,Tafada tana jifan Malika da wani matsiyan kallo na zakiji ubanki ne,ke kikafi bani haushi.
Wani miyau Saleem ya hadiye yana Fadin”a’a ni bance ba,kariso dama na kiraki ne, don kizo na gabatar dake ga malika na kuma taraku nayi muki nasihan zama lafiya da juna kamar yadda al’ada ya tanadar..”Tabe baki tayi kafin ta kariso tana wani jijjigen jiki kamar wata mara hankali,gefen gado ta zauna tana kada kafa,Fuskar na gefe tace”Ina jinka yi da jiki don inajin barci gaskiya..”
Daga Saleem din Har Malikan da kallon tababbiya suka bita,tun ballatana ma Malika wacce take ganin alamomin zahra kamar wata bakauyiya wacce batayi ilimi ba,Saleem ne yaga iskancin nata yayi yawa shiyasa ya hade rai kafin ya fara gabatar musu da juna,ya gangaro zuwa Nasihan su zauna lafiya,bangaren zahra ya juyo yana mata mgna da kakkausan murya inda ya Sanar da ita bai aurota don bayason matarsa ba😂🤔kuma bai auro ta don ya gaji da ita ba,ya auro tane don koyi da Annabin rahama sallalahu alaihi wsallam,kuma yayi mata mgana da zafin rai na kada ya kamata da Raina malika ko rashin kunya da rashin da gareta,ya gayamata koda ba domin tana uwargida ba,Malika ba tsarartabace ko banza agirme ta girmeta,so ta girmama ta kuma ta bita sau da kafa,daga karshe ya sanar da Malika sai tayi hakuri da Zahra kanwace gareta,Wani abun sai ta dinga Nusar da ita.
Malika bata bw Saleem kunya ba,tayi mgana cikin Hikima da natsuwa,itako Zahra saboda bakincikin kalaman Saleem na wai tabi Malika sau da kafa,yasa ranta taji yabaci da”aka nemi tayi mgana tana cin mgani tace”Naji duka maganganunku,sai dai Abu dayane bangane ba,Matarka Malika ce ta biya Sadaki ta auroni,ko kuwa kai kaine ka auroni da kudinka..? Tafada tana kallonsu dukkansu,Saleem yaji kawai ransa yabaci cike da kosawa yace”Wannan wata irin Tambayace? look zahra kingani nan dagani har matata bamasu son Rigima bane,indai ke rigima shine sana’arki to wlh bazamu Shirya ba..”Yafada yana Nurfafashin bacin rai.
Adage zahra ta kalleshi kafin tace”Au Allah,wato bakusan Rigima gani ni kuma Fitananniya,toh ni ba Fitinanniya bace gani nayi kana wani sanar dani nabi matarka Sau da kafa,alhali ko agida da za”a min nasihan zama da kai,wa mijina kadai ace nayi biyayyah baga wata katuwar gardiya ba..”Tafada tana wani mele baki,Ran Saleem yabaci saboda kalaman Zahra,yana kokarin mikewa ne Malika ta rikemai hannu tana Fadin”Plz don’t say Antytin…ba girman ka bane mallam..”
Tafada cikin sanyin murya,tana kuma kallonshi cike da sanyinta,Ganin yayi Shuru ne yasa takara damke hannunshi tana Fadin”Tadani na tashi,kasan ita amaryar so ce,so yar lallashi ne,don Allah Kayi hakuri kada ka biyemata yarinta ne ke damunta..”Tafada tana cije baki,zahra dake zaune ta zaburo tana Fadin”Eh naji yarinta ke damuna ai gwanda ni dana tashi sai na iyama kiruciyata banje na auri wanda yayi kusa da Sa’a na ba..”Tafada tana girgiza jiki lokaci daya tana sanya hannunta bisa kugunta,ko kallonta Malika batayi ba,Saleem ya taimakamata tatashi tana cije baki yana mata sannu,zaman myafin kanta ta gyara tana Fadin”Sai da safe Mallam,plz Amarya Kiyi hakuri fa,asha amarci lafiya..”Tafada hankalinta kwance kafin ta zame hannunta ana Saleem ta Fice daga dakin tana takawa dakyar saboda Nauyin datayi.
Tana Fita Saleem ya juyo ga Zahra yana Fadin”Tahaka zamu fara dake..? lalle ko ki chanza taku in ba haka ba wlh zamu samu mtsala cikin kankanin lokaci,don ni kingani nan na tsani mutum mara kunya da kuma girmama na gabanshi,uwa uba kuma rashin biyayya,ina mijinki wanda aka kawomin ke yau,ammh ina mgana kina maidamin da amsa kamar wani tsaranki ko? karki shiga hankali Allah zan saita miki kanki dinnan dake rawa bai zama daidai ba,mark my words..”Yafada kafin ya juya ya Shimfida darduma yana fadin”Ki Wuce kije ki sanyo zani ki kuma dauro alwala kizo zamuyi salla ne..”
Tsaye tayi tana kallonshi kamar zatayi mgana sai kuma ta fasa,Ganin irin kallon dayake mata,tana Tura baki ta Fice zuwa dakinta ta dauko zani ta daura bisa Rigar barcinta tadawo dakin,a tiolet dinshi ta Shiga alwala aranta tana fadin,ai bazan bari acuceni ba,daga yanzu har zuwa na cinye kwana bakwai dina adakin mijina zan dinga komai,ai itama ta shana,sai ta barni naci lokacina😂Koda ta Fito ta iske yana jiranta nan yajasu sallar Nafila Raka’a Hudu sukayi kafin ya sallame ya yi musu addu’a,Abun ya dauremai kai ganin duk tambayan dayayi mata game da addinta ta amsashi daidai babu kuskure,ammh ji Abunda takeyi sai kace batataba zuwa Mkrantar koyon Addini ba.
Nan kan Dardumar ta barshi ta haye gado,wai barci takeji,yana kallonta ammh takasa barci sai juye juye takeyi tana kallonshi,yana lura da ita yayi mirmishi cikin ranshi yana Fadin”hmm zaki samu Abunda kike nema,don wannan in ban bata Abunda take so ba,zuwa gobe zata iya kiran gida tace ban kusance taba,Tunda ya lura bata da cikakken Hankali.
Sai da yakoma Tiolet yayi bursh,kafin ya koma dakin,jallabiyan nashi ya cire yarage dagashi sai dogon bakin wandonshi ko vest bashi ajikinsa,ganin Faffadan kirjinsa awaje yasa take kara kallonshi kamar tajita kwance akan kirjin tana Shafawa,yana lura da ita ammh sai yayi kamar bai ganta ba,ya hayo gadon Agefe ya kwanta bayan ya saka hannu ya kashe hasken wutar dakin ya kunna Dumlight
Blanket din dake gefe yaja ya lullube rabin kafafunsa,dashi kafin ya tara duka hannunwanshi yana Addu”an kwanciya barci,Zahra na jinsa tayi lambo tana hadiyan miyau kamar wata mayyah,Tana ganinsa yashafama duka jikinsa kafin ya juya mata baya,ganin haka yasa wani kulikulin Takaichi ya ciyo Zahra,,yanzu kamar ita Ace Namiiji na juyamata baya,duk uban Tanadin datayi saboda shi,wlh bazata yadda ba,cikin sanyin murya ta kira sunanshi.
“Honey…Kayi barci ne..? Yana jinta yayimata banza,ganin haka yasa ta gangara zuwa gareshi ta Rumgumeshi ta baya tana sakin ajiyar Zuciya,bisa wuyansa ta zura hannunta tana Shafawa zuwa keyarsa tana Fadin”Honey Shine kayi kwanciyarka ka kyaleni ko..? Tafada cike da Shagwaba da sangarta,Ganin yaki mgana ne yasa,ta zura hannunta wajen kirjinsa tana Shafa gashin kirjinsa cike da salo,lokaci daya tana shafo Nipple dinsa,yaso ya Doje ammh jin abubuwan datakemai ne yasa dole ya Juyo yana rikota dakyau cikin wata irin murya yake Fadin”Kibar rawan kafa,Abun ba dadi ne dashi ba adaren Farko..”Yafada yana Shafa bayanta zuwa kugun hips dinta,cike da mugunta yake Sumbutar Wuyanta,yana kuma kara kaina da hannayensa cikin sassan jikinta,Tun Zahra na iya madamai da martanin salon wasan nashi haryazo ya kure Tunaninta musamman ma wajen dayake Tsotsan Nipple dinta,Bankare bankare tafaramai tana wani Numfashi sama sama,yafi minti talati yana Yana wasa da ita kafin ya fara neman hanyarshi,Zahra duk azatonta Abun mai dadi ne, sai da taji Wani abu na zungurinta kamar icce,kuma daya zungureta sai taji wani radadi,kamar an zubamata barkonu awajen,Jin Abun yana kara yawa ne yasa tafara mutsun mutsun kwace kanta,tana hade kafafunta,shiko Saleem da gayyah ya taleta dakyau😂ya kuma Rufe mata baki ya danna kai,Ai zahra ji tayi kamar ana sakamata reza ne ana caccaka wajen,gashi tana so tayi ihun ammh yatoshe mata baki,Tun tana iya motsu motsu har tazo jikinta yayi laushi Haka yake gurzarta kamar Allah ya aikoshi,dayayi Realising sai ya kara koma mata kamar wani maye,kuma ba komai bane ya jawomata haka sai shayen shayen mganuguar matar datayi,wanda dama akida in kikasha sukayi miki yawa toh ranar Mijinki zai Wuce mintinar dayake wajen saduwa dake yayi ta Abu daya ba gajiya,ke kuma nadama zata Shigeki sanda yayi raga raga dake,wajen neman ido ki rasa gira,koda yake basu nadamar haka sun gwammace suyita Shiga Ruwan zafi suna jinyar kansu,sudai burinsu ya cika Tunda miji yayita nanike musu ba gajiyawa.
Abagaren zahra kan tayi Nadama yafi cikin kwando Dubu don Allah kadai yasan yawan Allah ya isan data dinga lurama Saleem acikin zuciyarta,Jikinsa ko yasha yakushi da kunbunanata,kuka tayi shi har saida tagaji don kanta ta hakura,majina da hawaye suka dame waje daya,shiko Saleem bayama jinta caccakarta kawai yake jiyake kamar karfinsa na kara hauhauwa ne,kamar na doki,ga kuma mganin matan datayi amfani dashi wanda ya Yi sanadiyar Kara Fitar dashi daga hayyacinsa har sai da yayima zahra ci biyar Adare daya akuma lokaci daya,kafin ya koma gefe yana maida numfashi wahala,lokaci daya tambayan kansa anya Shine kuwa? domin yafi kowa sanin kanshi koda yake da karfin sha”awa bai da tsawaita kai Farmaki duk dadewarsa Minti talati koda malika ne,itama ta sani ammh kuma Abun mamaki Tunda ya hau kan zahra yaji yakasa control din kanshi d more zaiyi realesing d more,wata sha’awar ke kara zuwarma yayi mata Abunda ko Malika da zai yi Ramuwa akanta bai yi mata wannan cin haukan ba,Tundga nan ya fahimci akwai lauje cikin nadi,kuma yazama dole ya Tuhumi zahra kota gayamai gaskiya me yajawo haka?ko kuma wlh yaci ubanta la ada waje babu Ruwanshi.
Yana jinta tana Shesshekan kuka ya barta ya Shige tiolet ya sakarma kanshi yayi wankan tsarki ya Fito,yana tsane kanshi da karamin towel dake hannunshi ,yake kallon Zahra wacce ke kuka tana yarfe hannu,muryanta ta Dishe take Fadin”Wayyo momi,wayyo Abbana..Wayyo my best kuzo ki ceceni ya kashe ni Allah ya is Mugu kawai Azzzalumi wlh bazan taba yafe maka ba..”Wani haushi ya kamashi ya daka mata tsawa yana Fadin”Ai ke zan ma Allah ya isa da kika zalunceni Zahra,me kika sha? kika saka nayi Abunda ba halitta bace,duk Abunda ya faru dake kekika ja,kuma wlh hakan yayimin daidai domin Abunda keke nemane kika samu,kuma kin san da sani wlh gobe sai kin Fadamin wani banke banken hauka kikayi ma kanki,gashinan kinzo kina neman kissheni ni kuma kisa na kasheki..”Yafada yana Nunata da yatsa,tana jin Abunda yace ta Wage baki ta saki kuka,Ransa yakara baci haushi ya cikashi baisan sadda ya isa gaban gadon ba,cikin Fushi ya Fizgota sai gata ta Diro da kan gadon kafafunta suka daki kasa,wani kuka ta saki jin kasanta yadda yake turirin azaba kamar anzuba barkonu,ganin haka yasa ya dagata cak,sai cikin tiolet ya direta fuskarshi babu Fara’a yace”,Malama kibar kukan nan kiyi wankan tsarki ki Fito,kuma wlh kikayi yadda naji ko shesshekan kukan ki ne yadda kika batamin rai sai na Shigo har bayin nan nakara bayan nayi fatafata dake..”Yafada cikin kakkausan murya ganin yadda yake Huci ne yasa ta tsuge bakinta tana Sharan hawaye,tsaki yaja ya Fice da bayin.
.
Wutar dakin ya kunna,sai ya tarar da zanin gadon duk yabaci da jini hade da sperm tatarrashi yayi tana tsakar gasa jikinta taga yabude mota ya watso zanin gadon afusace yakoma,bayanshi tabi da kallo tana jin dadi aranta domin ko ba komai tanunamai Ruwa ba’asan kwando bane,ammh duk da yayi mata Abun cikin zalunci ne,ita da’akace mata Abun na da dadi,ammh ji Abunda Saleem yayi mata harda jini saboda mugunta,sai wata zuciya tace”Ke banza duk Dadinki ne yasa ya haukace miki yayi miki haka..”Jin haka yasa ta saki Dariyan jin dadi,duk ma sai taji azaban tatafi ta kara mikewa tana gasa kanta dkyau ranta Fes kare agado..😂
Shiko zanin gadon ya chanza,kafin ya koma ya kwanta Abun yaki barin ranshi,har Zahra ta Fito daga wanka tana Dafe dafen bango yana kallonta ta Dumligt din dakin aranshi yana Fadin”,Baki dafa bango ba,zaki dai ki dafa gobe da safe..’Yafada yana cije baki yayi alqawarin Sai ya koyama Zahra hankali in ma mganin mata tasha daga yau yayi mata alqawarin ko sadaka aka bata bazata karba ba.
Yana jinta tahayo gadon tana makyamayarta cike da Jin jiki,bai barta ba sai ji tayi,Yakara rikota Yana Shafa mata jiki,jikinta ne ya saki tafara matse kwallah,jin bai dauki wata hanya ba,yasa ta dan saki jiki,romancing dinta yashigayi da zafi zafi,tana jin dadin abu ya katseta ta hanyar Kara daidaita hanya,ai Sai Zahra ta haukace tana kokarin kwace kanta,ammh ina yayimata riko sosai ya danne bakinta danashi yashiga hakarta babu kama hannu yaro,Tun Zahra na iya motsi har tazo takasa kuka ma Rahama ne,haka takeji wani Siririn azaba na Fita daga kasanta ko kafin karfe 5 na asuba Saleem ya nemi Zahra yafi akirga,kuma lamarin nashi babu tsausayi sosai,har yaje sallar asuba ya dawo tana kwance tana kukan zuci,Kallonta yayi yana tsaye yake Fadin.
“Nasan haryanzu baki gaji ba kona kara ne…? Jin haka yasa Zahra tafara jan jikinta baya tana hawaye,harde hannuwanshi akirji yana binta da wani kallon banza kafin yace”Au ai na zata haryanzu dakarfinki ganin irin shayen shayen dakikayi tayi ke ga amarya ko,zaki gayamin abunda kika sha ko sai na kara zuwa inda na Fito yanzu…”yafada yana dora kafanshi daya bisa gadon,Zahra tayi Shuru da bakinta taki mgana don ita haryanzu batayi Nadama ba.
Ganin tayimai banza yasa yayi kamar zai haye gadon,da hanzari tadaga hannu tana Fadin”Don Allah kayi hakuri,Wayyo Allah na!Wlh in kakara zan iya mutuwa,don Allah kayi hakuri..”Mirmishi yayi kafin yace”Toh oya gayamin me kika sha ne haka,domin Abunda na aikata ba haka Karfin Desireta take ba..? Tana Sharbe hawaye tace”Magungunar mata nayi ta sha,tun ana saura wata daya bikinmu..”Tafada tana mtse kwallah,baiyi mamaki ba,dama hasashen shi ya bayyana Kada kai yayi yana Fadin”Gud,wato keda bakima Shigo cikin gidan auren ba,har kina tunanin yadda zaki sha mganugunar mata ki rikitani ko?ai kin Rikitani ni kuma nayi alqawarin nima sai na rikita ki,yadda zan Fitar da ra’ayin Shaye Shayen magungunar mata daga Zuciyarki,comon jere kitashi kije kiyi wanka kizo kiyi sallah…”Yafada yana kwanciya agefenta.
Zahra na kuka haka ta rarrafawa zuwa Tiolet tanayi tana cije baki,haka ta gasa jikinta tana kuka,ammh saboda taurin rai irin na Zahra babu Nadama aranta,sai ma dadi datakeji domin ta san duk wannan bambamin Fadan dayake Dadi ne yaji yamai yawa Shine yake borin kunya bayaso ya Fada,Harta Fito daga bayin da Rarrafe tafito tayi sallah kafin ta koma ta kwanta tana Sauke Numfashi,ammh azahirin batu taciyu iya ciyuwa wajen Saleem,kasanta ma bata iya hadeshi saboda azaba..
*******************
Saleem shima barcin gajiya ne ya kwasheshi sakamakon jiya bai sami barci na,saboda jarabar Zahra,sai da Malika ta kirashi awaya tana sanar dashi goggo Hadiza da zulai Sun Shirya zasu tafi,shi yatadashi ya Fito daga dakin yazo,ya daukesu acikin motarshi zuwa tasha suka hau mota zuwa Malumfashi,yayi musu godiya sosai kafin yayi musu alherin da zai musu ya juyo ya dawo gida.
Gabadaya malika takasa gane kan Saleem don daya dawo dakinta ya Shiga ya dinga barci kamar wani matacce,azahar da la’asar ma gameshi yayi lokaci daya,sai kuma alokacin yaci abinci,zahra ko,ko kofar dakinta bata Fito ba,Abincinta daga na Safe har Rana joda ne,tashigar mata dashi,wacce ke dunkule cikin bargo tana Jinyar kanta,Abunda ya bata tsoro ganin daren Ranar Saleem ya dawo mata irin na Jiya,haka Zahra ke kuka tana rokonshi ammh yaki Sauraranta,domin yana jin kamar manadigosu ne kejansa game da zahra,Sakamon shan magungunar mata da Zahra tayi kafin satinta ya Fita sai da ta gane Shayi Ruwane madara ake samai yayi kauri.
Kafin Satin ta rame ta lalace kamar ba Zahra ba Saboda wahala,daka ganta duk tayi Zuru zuru kamar wacce take amai da guduwa,Gashi kullum cikin gashin kanta take,saboda yadda Saleem ya maidata,kuka ko da Nadama tayishi kamar ba gobe,ammh Saleem bai ragamata ba,sai ranar daya gama bakwai dinshi ya koma dakin Malika,kuma Abun mamaki dasukayi Making love da Malika bai Wuce akidarsa ba,lafiya lau komai ya Gudana,Shiyasa gwara ka tsaya inda Allah ya ijiyeka da kaje kana ma kanka jaye jayen banza wanda baida amfani,daya gama kwana biyunshi yakoma dakin Zahra da kanshi ya iza keyarta ta Fito da duka sauran magungunar matan datazo dashi,abun yakusa bashi tsoro ganin irin Abunda Zahra ke dirkama kanta,shi ya Fita da mgungunar ya jefar abola yana tir da masu hali irin na Zahra,bai sauraramata ba,sai da ya tabbatar da Nadamarta kuma tayi mai alkawarin bazata kara shan wani mgani ba,wanda ya Wuce ka’ida,to lokacin ya dagamata kafa,kuma ya taimakamata ta kula da kanta,don ba laifi ta zazzagu har sai da ya kaita wani priver hopt aka bata mganunguna tazo tana sha tana kara Shiga ruwan zafi,sai ga Zahra duk Rawan kafanta,kan Saleem yanzu ta dainashi,ada batajin tsoronshi ammh yanzu dataji muryanshi sai gabanta ya Fadi,domin ba laifi taji maza,ballatana yayi mata mgana jikinta na Rawa zaki ga ta mike duk bai kara waiwaryata ba sai da ta warke ammh tsoron Abun ya darsu aranta,kuma Abunda da zai baka mamaki,duk surutun Zahra ko Nadira bata gayama Abunda ya Faru ba,taja bakinta tayi shuru kada ayi mata dariya.
__________________
Kwana bibbiyu sukeyi atsakaninsu Ranar da Malika keda girki joda ce keyi,Ranar da Zahra keda miji kuma ita ke girkinta da kanta,don daga malika har joda ko kallo basu isheta ba,wani lokacin sai dai in sun hadu afalo ita malika ta gaisheta,ammh zahra sai kiga ta amsa a wulakance,Wani abu mamaki in tana da miji Malika bata isa ta zauna afalo ba,don Shige da Ficen zahra cike da gayyah da kuma nuna isa,Ba laifi ta iya girki Tunda momi bata barsu sun zauna a sangarce ba,shiko yanzu Saleem aiki yayi mai yawa baya Wuni agida Sai dare yake dawowa kuma daya dawo ya gaji sai barci gari na wayewa 7 ya fita daga gida,wani lokacin in bai dakin Malika sai dai ya Tuntubeta ta waya su gaisa yaji kodawani damuwa
Abunda Zahra kema Malika ya Wuce misali,domin in zahra na Falo tana kallo babu wanda ya isa yazo yadau Remot din ya chanza tasha yanzu zai ga hayaniya da bala’i,shiyasa malika in taga zahra na Falon batama Fitowa Joda ce ke Fitowa tace bamai hanata Fitowa Falo ta gaji da zaman daki,kai ko kichen take tana aikin da zarar Joda ta Shigo zata ce Ta fita,ta bari in ranar girkin uwargijiyanta ta Shigo,Malika ke kwaban joda ammh da yanzu Sun raba hali saboda Abun na Zahra yafara batama Joda rai gaskiya.
Hardai wata rana data bangaje Malika har sai ta kusa Fadi,Allah ya taimaketa ta dafe kujera gabanta na Fadi take bin zahra da kallo,takan kawai ta Fito daga dakinta ita kuma ta Fito daga kichen zata Shiga dakinta,ita Malika bata ganta ba,ita kuma Zahra ta ganta ammh saboda mugunta da Iskanci ta bangajeta,wanda yakusa joda ta mareta don datayi mata mgana cewa tayi ita malikar bata da ido,da bata ganta ba,Ran joda ya Fadi suka Shiga sa’insa har zahra na mata gorin tana agolanci agidansu Malika kuma tazonan tana cin arziki ita da gidan mijin,wlh ba macen data isa ta hana ta yin yadda taga dama,Ko ita Malikar ma atafin hannunta take,tana jiran Ranar zata Shiga sabgartane wlh sai tayi Nadama.
Malika bata bari Joda tayi mgana ba tattarata suka koma daki,tana ba Joda hakuri tare da Nuna mata kada ta biyema Zahra don abokin mutuwa take nema,so take wani Abu ya faru tsakaninsu in Mallam ya dawo tace kece baki da gaskiya,kinga kuma ba dadi ace baraka yafara bullowa daga Barayinmu ki kyaleta mu hayaniya ba aikinmu bane,shiyasa kikaga bana son zama ako’ina sai adakina gudun Fitina.
Koda Saleem yadawo Zahra takasa kunne taji ko zata wata mgana bataji ba,duk ranar ko ita kedashi,jin shuru bai mata wani mgana yasa tayi kyafci aranta tana Fadin”Gaskiyan Saleema ce datace ni na kyalesu,da sannu duk zakuji ubanku daga ke har wacce kike zaune don ita..”itako Malika koda Saleem ya shigo da Safe Cikin uniform dinsa yana Sauri zai Fita koda ya tambayeta koda wani damuwa ne,cemai tayi babu,gaisuwan safe sukayi kafin ya sumbaceta abakinta yafice yana Fadin”Sai ya dawo,addu”ar dawowa lafiya tayimai koda ta rakoshi har kofar dakinta sai taga Uwar gayyah zahra ta cakare rike da jakarsa Ta brief case tana wani Mele baki kamar wata mai jiran cas,tana ganinta ta juya takoma ciki tana Dafe cikinta dataji ya juya mata,tana cije baki don ita ko abaya batayi hayaniya ba,balle yanzu datake kan Siradin rayuwa da mutuwa.
Tunda Saleem ya Fita Malika bata Fito ba,sai bayan datayi sallar Azahar,ta Fito tadan mike kafa,saboda sun kara kumbura,kuma tun Safe maranta ke ciwo tana dannewa,Ko joda bata bari ta Fahimci haka ba,bata zata haihuwa bane,don saura kwana 2 EDD ta yacika toh bata kawo haihuwa bace,falon babu kowa,shiyasa ta zauna akasa bayan ta saka Filon kujera ta dafe bayanta dashi Rimot ta dauka ta chanza tasha zuwa Arewa,ta iske sun saka wani Film din hausa,mirmishi tayi domin ba laifin zuwanta zamfara yasa tafara kalle kalle wanda ada ba Halinta bane.
Zahra ce ta Fito daga daki tana waya har tazo ta takama Malika yatsar kafa ta kuma tsalleta ta zauna bisa kujera tana cigaba da wayarta,jaye kafarta Malika tayi tana sosa inda ta takata cikin wani yanayi ta kalleta,kamar zatayi mgana sai kuma ta Fasa,ta kada kai ta maida hankalinta wajen kallonta,chan taji zahra ta Sheke da dariya tana Fadin”Wane ita,ai ina gayamiki ita da banza duk daya ,darajan cikinta jikinta kadai takeji Honey yasanar dani da zarar ta haihu zai kalata gidansu taje chan sucigaba da zaman Kunci ita da matar ubanta..”Tafada tana watsamata harara ta gefen ido.
Gaban Malika ya Fadi tabi zahra da kallo tana mamakin kalamanta,Kanta ya sara tayi jagale tana kallonta,da gaske ne Abunda take fada ko karya ne,bata gama mamaki ba kawai taji an Fizge Filon kujeran data jingina dashi,Tayi Baya ta dafa kujera tana bin zahra da kallon mamaki,itako kallonta batayi ba,sai ma ta dora kafarta kan Filon tana cigaba da lasta Wayarta bayan ta katse kiran.
Wani Fushi ya ziyarce Malika cikin kakkausan murya tace”Lafiyanki kuwa..? Me Filon yayi miki dana tare bayana dashi zaki Fizge,naga dai kina da iko dashi nima ina dashi ko..? Wani kallon Uku Saura kwata kafin ta yatsina Fuska tana Fadin”Nafiki iko dashi Tunda duk inda matar so take itace yar gaban koshin megida..”Tafada tana daga zaune,Wani iri Malika datayi nan da nan hawaye suka ciko mata ido,ta dade tana kallon Zahra kafin kawai ta kada kai ta dafa kujera ta mike dakyar tana Share hanci,Ganin haka yasa zahra ta saka dariya tana Fadin”Ikon Allah jimin mace toh ke in banda Abunki meye Abun damuwa,keda kika ga rashin so zahiri,ai ba babban Tozarci sai mijinka ya sakeka adaren Da’aka Daura maka aure bayan yayimaka fatafata,meyafi wannan Wulakanci,kuma wai mutum saboda dakikanci yana zaton haryanzu ana Sonshi ne..”Tafada tana kara saka dariya.
Cak malika ta tsaya tana jin wani kuka na taso mata daga kasan rai,juyowa tayi tana kallon Zahra kafin tace”Duk wa yagaya miki wannnan mganaganun dakike jifani dashi..?”Bude Zahra tayi kafin ta mike tana Rike kugu tace”jiki da wata mgana,wazai gayamin banda honey,Tunda shi aka cuta aka tilastama sai ya maidake dakinki,ke in ma zaki daina rawan kafa ki daina wai ke gaki uwargida bayan da bakinshi ya Fadamin tsausayinki yake babu Uwa asali mai kyau Tunda dangin Arna ne,uba kuma anyi Sanadiyar Shekawarsa da bakinciki,kinga ko ai inda imani ke abun atsausayane ga kuma ciki kinga sai ajira ki haife kafin kiyi gaba..”Tafada kai tsaye tana kallonta.
Malika dataji wani abu ya daki kirjinta ya gangaro har zuwa cikinta da maranta bata iya maidama Zahra da amsa ba ta dafe cikinta tana Cije baki cike da azaba lokaci daya hawaye na wanke mata Fuska,wata Shewa zahra ta saka kafin tace”Ji munafukar mata daga mgana sai ki dafe ciki kina kuka,Toh ni kam ban tabaki ba balle ace zan kashe rai..”Tafada kafin tayi tsaki tayi Wucewarta daki,
Malika taji hawaye suna zubomata basa yankewa ga maranta daya kulle cikinta na juyawa tama kasa daga kafa,tana kuka ta cije baki tana salatin cikin wannan Halin Joda ta Fito ta isketa cikin Tashin hankali ta isa gareta tana rikota take Fadin”innalillahi Anty malika,meya sameki,haihuwar ce..?
Bata iya mata mgana ba,saboda wani azaba daya Turnikota dafa joda tayi tana Sauke numfashi lokaci daya da kuka dakyar ta iya Furta”Ki ki..Kira maman Abba joda inaga haihuwar ce tazo..”Tafada tana cije baki,da sauri joda tatashi ta Shiga daki ta dauko wayan Malika ta kira Maman Abba ta sanar da ita,ita kuma tace tana asibitin yanzu haka,ammh gatan zuwa,kafin ta iso joda ta hada komai na haihuwan datazo sai su Koma asibitin tare dasu,aiko da hanzari joda ta Bude karamin akwatin Malika ta rinka jidan kayan haihuwanta tana sakawa aciki,kafin ta kulle ta zari hijabinta da hanzari ta kinkimo akwatin zuwa falo,koda ta Fito Malika ba yarda take,domin sai mukurkusi take tana kuka,Rikota Joda tayi tana mata sannu kafin tace”Na kira Maman Abba tace gatan zuwa mu je asibiti ko na kira Ya Saleem ne na sanar dashi..”Duk tana halin ciwo sai da ta girgiza mata kai alamun karta kirashi,rike joda tayi kawai tana nishi sama sama ga zufar datake ta Ketomata Malika girgiza kai kawai takeyi tana Tunanin kila ita kan tata ta kare,Sannu kawai Joda ke jerama,ammh ina batama jinta banda Sharban hawaye da Cije cijen baki babu Abunda takeyi,..
Acikin wannan Halin zahra ta sake Fitowa ta tarar dasu,kallon banza ta bisu dashi ganin Malika na wash wash tana zufa yasa ta rike baki tana yar Dariya tace”Topha Abun yazo ne…”Tafada cike da izgilanci,daga Malikar har Joda ba wanda ya kulata kichen ta Shiga ta dauko Tazo tazauna Afalo tana Sha hankalinta,kwance saima Rimot din Tibi data dauka ta chanza tasha,zuwa wata wacce ake wakokin Turanci harda kure Volume tana bi tana karkada kafa.
Maman Abba ce ta Shigo ahankalinta tashe ganin halin da Malika ke ciki ne yasa ta rude ta kamota tana Fadin”Kamota joda,haihuwace..”Riketa sukayi har zuwa motar Maman Abba suka sata abaya,kafin Joda ta koma ta dauko akwatin kayan haihuwan da wayarta data Malika,Zahra na zaune bisa kujera tana jijjiga kafa suka Fice daga gidan zuwa Asibiti
*********************
Saleem bai da masaniyar Abunda yafaru sakamakon yayi busy ko wayar dayake ma malika ma yau din kwata kwata bai samu yimata ba,har ya dawo gida wajen after 8,dayake zahra keda girki bayan yayi wanka ya sauya kaya zuwa jallabiya,sai ya Fito Falo ta Fitomai da abinci ta durkusa tana cikin Serving dinshi kenan ya kalli barayin dakin Malika yana wani nazari kafin ya kalli Zahra yana Fadin”Ina Malika,tana lafiya dai ko? don Tunda na dawo banji Duriyarta ba daga ita har Joda..”
Tabe baki Zahra tayi Daidai tana ijiyemai Filet din Tuwon shinkafan agabanshi tace”Bansani ba,nida naga wannan Nurse din ta shigo sun Fita da ita da Sauri,kamar dai kila haihuwan ce tazo…”Wani uban Zaro ido Saleem yayi yana Fadin”What..”!Haihuwa fa kikace zahra..? Kallonsa tayi cike da mamaki tana Fadin”Eh nake ganin kila haihuwan ne,nifa bansani ba don ba wacce tamin mgana da zasu Fita..”
Bai tsaya sauraranta ba,yasaka kafa yayi Fatali da kololin dake gabanshi ya mike yana Fadin”Ammuh ban taba ganin dabba Yarinya irinki ba yanzu ace Malika tafara nakuda har wata makociya tazo ta dauketa zuwa asibiti ki kasa kirana ki sanar dani,ammh don jakanki da rainin hankali har na dawo gida nayi wanka baki sanar dani ba,sai da ma na tambayeki,kuma kina sanar dani mganar banza..”Yafada yana Huci,mikewa tayi tana kallonshi,yadda yake kallonta kamar ya Rufeta da duka,bai tsaya sauraranta ba ya tureta tatafi ta Fadi bisa kujera yawuce dakinsa da gudu ya dauko wayarsa da makullin mota ya Fice da gudu yana cigaba da latsa wayar tasa.
“”Wayar Malika yake ta kira,ammh kuma gashi tana Ringing ammh kuma ba”a picking hankalinshi in yayi Dubu ya tashi,haka ya shiga cikin mota yayi zaune yana dafe kai,wayarsa ne ta dau Tsuwa yana dubawa yaga Wata Nombace agaggauce ya daga kiran yana Fadin”Hello…”
Joda dagachan bangaren tace”Hello ya Saleem Joda ce..”Jikinsa na rawa ya Fito daga motan yana Fadin”Joda,kuna ina ne,ina ita malikan? ta haihu ne? ko bata haihuwa ba..? Haka ya Shiga jeramata tambayoyi alokaci daya,cikin damuwa da alhini tace”Muna asibitin da Maman Abba ke aiki,kuma haryanzu Anty malikan bata haihuwa ba,sau biyu ana Saka mata Ruwan Nakuda,ammah haihuwar shuru,wlh Ya Saleem Anty malika tana Shan Wuya,yanzu hakama ana cukun cukun Turamu General hospital gusau ne..”
Dafe kai Saleem yayi yana Fadin”Innalillahi wa’inna Alaihirraju’un,ganin nan zuwa yanzu…”Yafada yana katse kiran ko cikin gida bai koma ba ya Fada mota ya tasheta asukwane,da Sauri ya dinga latsama Megadi hon,wanda ya Rugo da gudu ya Budemai get ya sulala zuwa waje da Gudu.
*******
Zahra ko tana zaune kan kujeran Da Saleem ya tureta bata iya tashi ba saboda takaichi da bakinciki,tana jin sanda yayi hon da kuma Ficewarsa lokaci daya,tsaki taja afali kafin tatashi tana tattara kololin daya watsar tana Fadin”Allah sa daga haihuwar ta mutu,basai naga karyan Tsiya ba..
ko Ajikinta bata damu ba,saima gyara zama datayi afalo tana chanje chanjen tasha ko ajikinta,saboda gulma ita ta kira Saleem tana Sanar da ita Abunda ya Faru,da kuma halin da’ake ciki,shewa Saleema tayi kafin tace”Kin min Daidai ta wajena,haka nakeson ki rika yin komai cikin taku,ni Allah yasa ma wajen haihuwar daga ita har Abunda ke cikin nata su Haura chan,sai mu fatan Allah ya kiyaye hanya mu sai munzo..”Dariya suka Sheke dashi atare kafin Zahra tace”Kamar kin Shiga Raina haka nace,….”nan suka cigaba da hiransu suna zagin malika da fatan kada Allah yasa ta haihu lafiya,su Fatan mutuwa suke mata,saboda yadda sukaji jininta arayuwarsu ta Duniya.
********
Koda Saleem ya isa asibitin har anbasu takardan izinin tafiya da malika Zuwa general hospital gusai so bai tsaya ba,suka sanyata amota Shida Joda da Maman Abba,wacce ta bar motarta anan asibitin BAyan ta kira Baban Abba ta sanar dashi Abunda ke Faruwa,yakuma amince taje har chan general hospital gusau din.
Saleem yayi gudu bisa hanya,sakamakon ganin irin kuka da salatin da Malika keyi tana Fadin ita mutuwa zatayi,duk inda hankalinshi yake toh alokacin atashe yake,gudu kawai yake tsulawa cikin lokaci sai gasu acikin haraban general din,maman Abba ita tafita ta gudu ta sanar Da Nurses su kuma suka zo da Gadon daukan marasa lafiya,ko kafin su kariso sai suka Hadu da Saleem ya daukota ahannunshi nan suka nuna mai dakin da zai Shiga da ita,nan ya Shiga da ita ya kwantar da ita kan wani karamin gado yana kallon Fuskarta yarda halittarta ta chanza Saboda wahala.
Korarshi sukayi waje,ammh da ya zauna kusa da itane ya rikemata hannu yana Lallashinta,Ranar dagashi har maman Abba da Joda babu wanda ya Runtsa saboda tashin hankali,har wajen asuba malika shuru bata haihuwa ba,ga karfinta ya kare,kawai sai likitoci Suka Nemi Saleem daya saka hannu zasu Shiga da ita dakin Tiyata,nan da nan ko ya rattaba hankalinshi tashe,daman ya gaji da wahalar da Malika kesha hakanan..
Sai bayan an Shiga da ita dakin Tiyata din ne yasamu sukunin kiran Abbi ya sanar dashi Abunda ke Faruwa,wanda yadinga salati yana kiran Sunan Allah,Koda yake sanar dasu Ummi da hajiya,wacce bata dade da dawowa daga kumo ba,don ko bikin Zahra da Saleem da akayi batanan,Suma salatin suka saka suna Fatan Allah ya sauketa lafiya,itako Saleema tanaji ammh sai ta nuna kamar bata sani ba,nan ko cikin ranta addu’a take kada Allah yasa Malikan ma ta rayu.
Joda kuma ta kira Hajiya Binta ta sanar da ita Abunda ke Faruwa,matukar tsausaya Hajiya ta tsausayama Malika,saboda tasani yau zataji Abunda kowacce uwa taji kafin ta haihu,Haka ta dinga mata addu’ar Allah yasa ayi aiki lafiya afito lafiya.
****************
Alhamdulillah Anyi Nasarar Yima Malika aiki kuma an Fito mata da kyakyawan yarinyarta wacce take kama da ubanta sak,sai dai ta debo hasken Fatan mamanta,Tuni har ankaisu dakin hutu malika bata Farfado ba,ammh an gyare bby tas gwanin ban sha’awa,Murna wajen Saleem ba’a mgana sai da yayi Sujjuda ya mika godiyarsa ga Allah (SWA) domin Shine ke badawa kuma Shike Hanawa.
.
Shi yayi ta kiran yan”uwa da abokan arziki yana sanar dasu anfito da malika lafiya kuma ansamu Babby girl,ciki harda Zahra wanda haihuwar kwata kwata bata mata dadi ba,sai ta nunama Saleem din don daya gayamata haka tayi Shuru taki mgana sai da yakara maimaitamata kana tace Allah ya raya ta yanke kiran,ya dade yana kallon wayar yana mamakin zahra yana so ya Fahimci wani abu game da yarinyar,wacce Tun Abunda tayi jiya ya gane ya bar Shiri Tun rani,ammh zai tambayi malika in takoma gida yaji wani irin zama suke gudawar ita da Zahra.
Malika bata Farfado ba sai da yammah,nan ta ci karo da Abunda aka Ciro mata,haka ta dauki yarinyar tana kuka,ba kukan komai take ba,sai kukan Mallam zai rabu da ita,acikin wannan Halin ya Shigo ya sameta nan ya hadasu ita da Bbyn ya Rumgume yana mata godiya,ammh abun mamaki Malika kanzil batace mai ba Tun yana ganin Rudin haihuwace da kuma aikin dake jikinta,ammh har washegari Batamai mgana ba,dayayimata zata kauda kai tana kuka Abun yabashi mamaki matuka,ammh sai ya kyaleta sai sun koma gida yaji meya faru kuma.
Sai Ranar yakoma Zamfara yabar Maman Abba da joda,koda ya koma Zahra kota tambayeshi ya maijego da bby,kuma koda yake chan Asibitin koda kuskure bata taba kiranshi taji ya ake ciki ba,sai dai inshine ya kirata,mamakinta kawai yakeyi,ammh sai bai mata mgana ba ya kyaleta yaga iya gudun Ruwanta,Ranar bai koma asibitin ba,saboda goggo Hadiza aka turo tazo daga Malunfashi don ta zauna da malika tana kula da ita,tunda dai joda yarinyace bazata iya ba,Maman Abba kuma ta dawo gida,washe garin ma kiran Ummi ya samu yana wajen aiki ta sanar dashi gasu asibitin basu ganshi ba,yace yana tafe,daga wajen aiki gusau din yakoma chan ya tarar da Ummi da Hajiya da Abbi sunce sunma dade da zuwa,sai wajen la’asar kana sukayi Shirin Tafiya inda Ummi taja Saleem gefe tana Tambayanshi”Ina abokiyar zaman malika da batazo asibiti ba,kuma joda ta sanar da ita makociyar Malika ce tazo ta taimakamata kwanansu biyu tare,bata tafi ba sai da goggon Malika tazo..?
Kame kame Yafarama Ummi Tundaganan tagane akwai mtsala,kafin yasamu karyar cemata zahran itama tana gida bata da lafiya,Ajiyar zuciya Ummi ta sauke kafin tace”gaskiya Abun baiyi tsari ba ka gyara zamantakewar gidanka,ai yakamata Tunda ba kwance take ba,ta biyoka yau tazo dubata ko? kansa na kasa yace ma Ummi ba daga gida yake ba,ammh insha Allahu gobe zasu zo tare,Ummi bata komai ba,sukayi musu sallama suka koma hanyar Abuja,su suka kawomusu kwando guda na coolers,cike da abinci sai kayan Fruits.
Mganar da Ummi tayima Saleem ta tsayamai arai har yakoma gida yana auna magarta inda yaga tabbas gaskiya ne,kuma Duniya na nan na Zaginshi akan Abunda Zahra tayi,ammh ba komai bari Malikan ta daawo gida zaiji dalili,Tun adaren ya sanar da Zahra cewa gobe zasu je asibiti da ita ta Duba malika,kodaga yanayin yadda tayi ya Fahimci batayi niyyar zuwa ba,aiko hakane gari na wayewa Zahra ta kwanta tana rawan sanyi tace bata da lafiya,mamakinta ya kamashi bai mata mgana ba ya sakai ya Fice,wanda duk Abunda tayi Saleema ce ta kitsa matashi,yana Fita ko ta kirata suna Dariya,nan Saleema ke sanar da ita gobe zata zo,su cigaba daga inda suka tsaya murna ta kama zahra tadinga Jin dadin zuwan Saleeman agobe.
Har Washegarin Ranar da Saleema zatazo Saleem bai sani ba,saboda Tun Safe yatafi gusau saboda yau din za”a sallamosu su dawo gida,koda yaje shiyayi cike cike da kuma biyan kudin wasu magungunar daba’a biya ba,kafin abasu sallama,shida kanshi yazo yana hada musu kayansu bayan su joda sun kwashi wasu kayan zuwa mota,Nan ne Malika ta kalleshi kafin tacemai tana neman wata alfarma ne,koda ya bata dama kawai sai tace don Allah yayimata alfarma barin ayi suna kafin ya saketa..”Mganar tazomai abazata zama yayi kusa da ita yana tambayanta shi bai gane ina ta dosa ba? waye yace mata Shi Saleem zai saketa..? kin amsashi tayi yayi mganar Duniyar taki magana daga bayama sai ta sakamai kuka,dole ya rabu da ita,ammh bawai don ya bar mganar ba,sai da yayi Shuru ne sai sun koma gida ya turketa yaji daga ina aka samo wannan iskancin.
Suna dawowa sukaci karo da Saleema ta iso,Saleem har ga Allah yayi mamakin ganinta,daya tambayeta meya kawota kuma yaushe tazo..? Sai tace bata dade ba,kuma tazo ganin mejego ne da kuma bby,Cikin mamaki yake tambayanta meyasa bata zo asibitin ba,sai tayi missing step tace wai Zahra tace mata yau zasu dawo gida,Yayi mamakin jin haka sabida ko zahra batasan yau za”a sallamo Malika daga asibiti ba? toh waya gaya mata..?bai maida mganar Serious ba,ya share kawai bai zauna ba yakoma wajen Aikinsa,itakuma goggo Hadiza ta saka Ruwan zafi tatara malika bayi tamata wanka ta gasata sosai duk ko achan asibitin tana gasata,ita kuma maman Abba ita tama bby wanka aka sanyata cikin kayan sanyi masu kyau da ban Sha”awa..”
Zahra ko Da Saleema wannan Haihuwa dai bata yi musu dadi ba,Har yammah basu shigo sun duba Maijego ba,kuma anajin dariyansu afalo,ammh kuma basu shiga ba,sai dare kana suka Shiga suka dauki yarinyar awulakance har zahra na Fadin tabiyo jar Fatan kakaninta Arna,Tafada tana dariya Saleema ko Fadi take,sai dai amata fatan Shiriya kinsan ana tsotson Iskanci da rashin tarbiya ajikin Nonon uwa..”haka sukayita fadar maganganu son ransu,Joda taso tayi mgana Ammh goggo Hadiza ta hanasu tace su kyalesu komai zasuyi kada su tankansu saboda su neman wanda zai tankasu ne suyi fada dashi,Haka akayi ba wanda ke bi takansu aiki ko ko changal basayi acikin gidan alhalin Saleema cewa tayi zatazo ta taimakama zahra da aiki,Joda ce da Maman Abba ke ta dawainiya da Malika suyi girki su gyara gida,su sakama malika Ruwan wanka,aikin goggo Hadiza kawai Yima Malika wanka da kula da ita ita da Bby,wacce ta samu Ruwan Nono sosai wanda yake taimaka jaririyar wajen samun Abinci sosai.
Saleem baida masaniyar Abunda ke Faruwa,don baya zama agidan in yafita Tun safe sai dare yake dawowa,kuma babu wanda ya Sanar dashi ga Abunda ke Faruwa,wanda Wuni suke suna zaune afalo suna Hiransu suna dariya,ko ajikinsu kuma adafa abasu suci suna wulakanci,Malika ko tana cikin damuwa bata cikin natsuwarta saboda ita harga Allah Ta yarda da mganar Zahra tana cikin Fargaban in Mallam ya saketa ya zata kare da rayuwarta,ammh ta gagara fadama kowa ta bar Abun acikin ranta.
*****************
Ranar bakwai din na zagayowa Ranar akayi suna jaririya taci sunan Ummi Aisha suna kiranta AYDA,Anyi sha’anin cikin Farinciki da murna,yan malumfashi sunzo harda yan Kumo ma sunzo ansha suna,wanda Su joda sukayi abinci kala kala agidan maman Abba,sun dafa white rice da Miyar nama,sai friede rice da Kuma jallof mai Cosslow,sai Soyayyan Naman kaji dana rago,Sunyi kunun aya,Sai alale na leda,wanda yaji kwai,kuma bayan lemukan da Saleem yasa aka sauke musu domin baki,Kuma su kadai sukayi duka aikinsu agidan Maman Abba,sai dai suka kwaso su cikin manyan kololi suka dawo dashi nan gidan
Malika ta Shiga ta Fita cikin kayan alfarma ita da Ayda,musamman maman Abba ta sake kiran Ummi mai lalle da kitso ta sake cakareta,bayan nan mai kwalliya tazo itama ta tsantsaramata kwalliya Abun sai wanda yagani,dayake simple make up ne tayi mata,sai ta Fito ras da ita,Abunka ga farar fata,dama gata da kyau ai sai kawai tashiga kyalli,Zahra ko da Saleema kamar su mutu saboda bakinciki domin ko sun sani wlh karfin hali kawai suke,ammh Malika tafi karfinsu dukkansu,domin ta Wuce da saninsu ta bangarori dama,Ranar sai ga Hajiya saratu momi da Nadira sun diro sunan wanda suka zo suna ta ma zahra Fadan bata sanar dasu malika ta haihu ba,nan tayi ta borin kunya tana Fadin wai ta kira wayarsu bata samesu ba,Nadira ce tace sunyi waya da Saleem yake sanar da ita jiya,yace kuma yau ne Suna,shine ta Fadama momi suka taho,duk da basu wani dade ba,ammh ko malika da basa shiri da zahra taji dadin zuwansu da zasu tafi momi ta bata 10k da kuma Atamfa guda biyu da kayan babys,ko Saleem basu gani ba,don Tun safe ya Fice sakon gaisuwa kadai sukabari agaya mishi.
Taron sunan baiyi wasu jama’a sosai ba,daga yan malumfashi ne sai yan kumo,wadanda suma suna gama cin suna suka koma,dama sunzo da motar gidane,sai yan group din *MALIKA MALIK PAID* Da yan *HAFNAN AND JANAF PAID GROUP* Da sukayi mata kara mota guda suka zo ma malika sunan Ayda wanda ta dinga mamakin daga ina suka samu lbrinta,nan Dotata Ladingo tayi dariya kafin tace”Karki damu da sanin ina muka samu lbrinki,domin mommyna Janafty ita take sanar damu lbrinki,kuma dukkanmu nan masoyanki ne,duk dabamu taba ganinki ba,muna kaunarki..”Jin haka yasa malika tayi murna sosai da Farinciki nan aka zubo musu abinci suka baje suna ci suna hira,su Sisina Aisha alto da Sahiba sai ci ake hannu baka hannu kwarya😂su mommyn Abdul me,su Rafi’atu,Fati sadi,mommyna khadija tame gari,momyna khadija bashir,Dijah Abdul,Dija muhd,Zuwaira Andijat,My besty halima,Fatima zahra,haleema,Ummi imran, Mmn useey,Ummi bilal,Fatima garba,mom sadiq,Suwaiba,shafa yola,Murja bagudu,Deejart,Mmn baraka,Mmn Amira,mm siyama,Ummu bilal2,Rouky niger,Azeeza,hadiza,Durling Rukayyah, Masoyiya takwarar malika,khadija Aliyu,khadee Noor,mmn Haneef,Mmn mama,yar Fulani,Nazeeha Ahmed,Saleema Hamza,Ayshert usman,Maman khairat,Bbyj,Asma’u Shehu,Ummah sabo,Zainab jega,Hafsart Umar,Fatima musa mamn Nabila,Mmn ummulos,Nafeesa Fee,jikar hajiya,Mrs Umar Faruk,Sardiya,Suna da dayawa wanda bakina bazai ya ambatonsu duka ba.
Sunsha Ankonsu cikin red din materila sunyi head da blue,abun sai wanda ya gani,malika tayi Farinciki ganinsu sosai haka sukayi ta daukan Hotuna suda malika da bby Ayda,Fatima zahra ko ana riketa tana abarta ta Shiga dakin Zahra taci ubanta😂🤔Dakyar Su Nazeeha da Ummi imran suka rirriketa suna bata baki kana ta hakura,Har sukayima Malika sallama bayan sun bata sha tara na arzikin da suka kawomata ,basu saka Zahra da Saleema a ido ba,ammh d Yawansu sun so su gansu koda tsaraban Harara ne su basu koda bazasu dake su ba,Saboda murna da godiya har bakin mota joda da Malika suka rakosu suna musu godiya suna dagama musu hannu har suka Fice daga gidan.😂
Anyi taro lafiya an watse taro,Ayda da mamanta sunyi goshi matuka domin Abbi 50k ya aikomata dashi Ummi ko akwati tayi Sir da kayan Babby da mamanta balle dataji ita akama takwara,Ya marwan ko Shima kayan yara ya turo dashi daga lagos,da kudi 30k akabama malika,haka shima Sadiq kudi yabata 20k Malika saboda Farinciki sai da tayi kwallah ta kira Abbi da Ummi tana musu godiya tana kuka,harta da Sadiq din da Marwan Saleem ya kirasu yabata tayi musu godiya sukace ai babu komai suma yarsu ce,Su Zahra da Saleema ba karamin mamaki sukayi ba da sukaji uban Dukiya da kayan da malika tatara,nan da nan hassada da haushi ya kamasu,nan Zahra taji itama tana son ta samu ciki itama ta haihu ataramata kudi,Niko nace banza abanza,ke keta Dukiya indai kudi ne Malika ta mallakeshi da wanda zai siyeki keda Mai zugakin gabadaya.
Shiko Uban gayyar bai siyan mata komai ba,illah wata sarkan gold mai kyau Sarka da Dankunne,Ranar daya kirata ya damkamata sarkan adakinshi ne,yana rike da Ayda ita kuma malika na Faman gwada sarkan gaban madubi tana washe baki murna ta cikata Fadi take”Wayyo Mallam wht a special gift,gaskiya am so hppy wlh Allah ya saka da alheri ya kuma rayamana Ayda cikin tafarkin islama..”Da Ameen ya amsa yana mata dariya Abun yayimai dadi yadda ta nuna murnanta afili,domin yasan cewa Malika ta mallki dubunsu kafin yanzu kuma ko ayanzu tana da Dubunsu ammh kalli yadda take murna akan kyautan da yayimata wacce bata Wuce yarwa abola ba indai awajentane..
Kwantar da Ayda yayi bisa gado ya taso yazo ta bayanta ya Rumgumeta duka kyakyaawan Fuskokinsu suka bayyana acikin madubi,mirmishi take sakin mai bayan ta dora hannuwanta kan nashi,cikin wani salo yayi mata Rada akunne yana Fadin”Ummi Ayda..”yafada yana Shinshinar Wuyanta Cikin kasalar daya saukarmata tace”Umhmm Abbu Ayda..”Mirmishi yayi har Hakoransa farare suka bayyana,Cikinta ya mtsana tayi yar ihu tana Fadin”Kai mallam wajen operation din nefa ka tabamin..”Tafada cike da Shagwaba Saurin juyo da ita yayi yana Fadin”Ayyh am srry..”Ya fada yana shafa kumatunta,Kafin yace”Tambayarki zanyi,kuma ina so ki sanar dani gaskiyan al’amarin..”
Hannayenta ta harde bisa kirji tana Fadin”yes ina jinka,Allah yasa na sani..”Gyara Tsayuwa yayi yana kallon cikin kwayan idanunta Yace”Mganar dakikamin a asibiti kince kada na sakeki sai mun dawo gida? waya sanar dake cewa nace zan sake ki bayan kin haihu..? Shuru tayi tana dukar dakai taki mgana,Ganin tayi Shuru taki mgana yasa yace”Kinga ki sanar dani waya gaya miki wannan mganar da bata da Tushe ballatana makama,in baki gayamin ba,zan kira goggo Hadiza yanzu,kila ita in ta tambayeki ki sanar da ita..”
Jin haka yasa ta riko hannunshi da Sauri wanda yake Shirin Fita,bisa gefen gado suka zauna kafin tace”Basai ka sanar da kowa ba,Bani son Tun bayan daidaitan al’amarinmu babu wanda ya sakejin kanmu kai baka alfahari da hakan..? kai ya gyada mata bai yi mgana ba,Sai tacigaba da cewa”Toh meyasa zaka kai karata? dama zan sanar dakai Wacce ta Fadamin ammh sai kamin alqawarin bazaka dau wani mataki ba,kowani hukunci ba..”zuru yayi mata da ido yana kallonta kafin yace’Banyi alqawarin ba,ammh ki fara sanar dani Abunda ya Faru..”,
Hannunshi ta riko ta matse cikin nata kafin ta fara bashi lbrin Abunda yafaru da ita da Zahra ranar,bata rage komai ba ta karishe cikin kuka tana Fadin”,Na shiga tashin hankali Mallam,wlh in ka barni banson ya rayuwata zata kare ba,ga Shi Daddy ya tafi ya barni bani da kowa sai kai,kai ne gatana,don Allah kada ka barni ka zauna dani koda bazaka kyautatamin ba,kazama bango Abun jingina gareni..”Tafada tana Fadawa bisa kirjinsa tana kuka.
Riketa yayi yana buga bayanta,idanuwansa sun kala sunyi jawur,Sai yanzu yake kara Fahimtar Abubuwan da Zahra ta aikata Tun haihuwar malikan,Ashe munafukace Mai Fuska biyu,kuma gulman nata harda mijinta aciki,lalle yazama Dole yayi gaggawan daukan mataki akan Zahra kuma sai ta sanar dashi wajen wa taji wannan mganr,Cikin sauri ya raba Malika da jikinsa ya mike yana Wuce ya Fice daga dakin atamanin,cikin Tsoro Malika tabishi tana Fadin”Mallam,tsaya kaji..Ka tsaya…”Tafada tana kokarin Fita sai kukan Ayda ya dakatar da ita ta koma da hanzari ta daukota ta sabata,ta bi bayan Saleem da Sauri.
Tundaga Falo ya ke kiran Sunan Zahra murya a kaukaushe..”Zahra!.Zahra..!
Zahra…Zahra…”!Yake Fada yana Bude murya cikin bacin rai,Zahra da Saleema dake kan gadon Zahra suna hira sukaji muryan Saleem yana kiran zahra cikin muryan bacin rai,atare suka diro daga kan gadon suna Rigen Rigen Fitowa daga dakin,Ba su kadai ba hatta joda dake cikin daki ita da goggo Hadiza suka Fito hankalinsu tashe,saboda jin kiran bana lafiya bane.
Zai Shiga dakin Zahran kenan sai gata tafito agaba Saleema na biye da ita,Tana Fadin”Lafiya hone….”Ji kake Tas!Tas!Tas!….”Saleem ya kwashe Zahra da maruka Zafafa guda uku atare,saboda gigita da zafin mari sai da Zahra ta wuntsila tayi baya zata Fadi Saleema ta tarota ta Fado jikinta,cike da mamaki suke binshi da kallo yadda yake nuna Zahra da yatsa yana Sakin Huci,daidai lokacin da Malika ta kariso idanuwanta duka awaje saboda karan marukan dataji zahra tasha….²⁶