MALIKA MALIK CHAPTER 18 BY JANAFTY
Www.bankinhausanovels.com.ng
“Lokacin da Bikin Saleema da Sadiq ya rage Saura Wata daya Takardan Transfer din Saleem ta Fito an maidashi Headquatersu ta Katsina, *POLICE HEADQUATER AIRPORT ROUNDABOUT KATSINA STATE* Murna wajen Malika ba”a mgana dama Tafison su koma katsina da Zama ta gaji da zaman Zamfara.
Nan da nan suka Fara parking din kayansu na Sawa,Domin komawa katsina,wanda Malika keta murna har Maman Abba na mata Tsiyan zata tafi ta barta,dariya tayi tace haba ai ko Birnin Sin ta koma suna Tare bazasu taba Rabuwa ba,Sati daya da Samun Tranafer din Suka gama duka parking din Abunda zasu dauka sukayi sallama da makota,shima Saleem din already yagama Sallama da Headquater nasu,bayan ya mika Sauran aikin zuwa ga hannu sabon Acp wato Shugaban wajen na yanzu.
Maman Abba ta zama kawar alqawari don da ita suka dumguma Zuwa katsina gidan da Daddy yabama Saleem wanda koda suka isa Hajiya ta tura musu su Dose sun gyara gidan,sun musu abinci,babu Abunda ya samu gidan,domin ana kula dashi Sosai,ga motocinsu guda biyar Nashi Biyu na Malika biyu wanda Daddy ya mallaka musu sunanan a mazauninsu Rufe da Tamfol,dama already makulayan motocin na hannun Saleem..
Malika da Maman Abba sun zaga lungu da Sako na gidan suna yabawa,Tare da jinjinama Daddy irin Kudin daya kashema gidan,komai na Zabinta an saka mata shi,harda Abunda ta Fiso arayuwarta Swimming Fool,Wayyo Dadi kashe Malika Duk da haka sai da tayi kwallar Tunawa Da daddyata ammh bai Hanata Nuna Murnan Tafi jin dadin wannan gidan Fiye da gidansu na Zamfara ba.
Maman Abba kwana daya tayi ta juya Zuwa Zanfara wanda Malika da Saleem suka Mata Sha tara na arziki don Ta nuna musu kara Sosai,Malika bata da Wata damuwa yanzu don Gata ga hajiya,ko banza tana jin kamshinta ba kamar da,da ko kamshin Wani na gida bata ji…
Saleem ya kai Trasafer letter dinshi Zuwa Sabon Headquater su,yayi wasu cike cike kafin Yafara Zuwa office cikin kwanciyar Hankali,dawowar Malika katsina yasa Hajiya ta dawo mata da Dose suna tayata wasu abun don Cikin malika yana da girma Sosai,Dawowarta katsina yasa tafara Zuwa Asibiti Awo asibitin Federal Medical centar katsina, Tunda da suna Zamfara maman Abba ke Zuwa har gida tana mata,Cikinta Watanshi Takwas yanzu ammh sai ka tsaya ka kara kallon yadda yayi Wani girma yana neman Rufe Malika gashi ya Kumburata Sosai Afuska da jiki,tafiya dakyar tashi Dakyar ammh kuma ahaka take Shirin Tafiya Abuja bikin Saleema,wanda Saleem yayi mata bakam Saboda yaga Malika bata da Hankali baisan ina zata da wannan Tulelen cikin ba taje tabama mutane aiki.
Malika batayi Shawara da Saleem ba Ta Turama Ummi Zunzurutun Kudi har Miliyan Talatin,wai gudummuwar bikin Saleema,dana ya marwan Tunda wanchan Lokacin bata bada komai,Sai ga Ummi ta kira Saleem yana office tana tambayanshi Cike da mamaki yake Sanar da ita bai sani ba,yana wajen aiki ammh in ya koma zai tambayi Malikar ita ko koda Ummi ta mata waya tana tambayanta wannan kudin na miye Dariya kadai tayi kafin ta Sanar da Ummi Gudummuwarta,Bakin Ummi bude take Fadin kudin Sunyi yawa,malika tace Allah Ummi basuyi ba,sai dai inda bazaki ki karba ba,Ummi kasa mgana Tayi, illah godiya datayi ta zubama Malika,shikanshi Abbi Dayaji yayi ta mamaki har yayi tama Saleem Fadan yazai bar malika ta dinga Wasa da kudi haka,yakamata ya zauna da ita su Tatauna Abunda ya dace su Dinga yi da Ribar Dukiyarta bawai Shanshanci ba,kaji Abbi😂.
Saleema dataji sai gata har katsina Tazo godiya,Malika bata bi takan Godiyar datake mata ba,sai ma Tambayanta datake wata irin mota take so kuma take Sha”awa Saleema bata kawo komai ba tace Vibe motar tana burgeta,gyada kai kawai Malika tayi aiko ko Sati basu da wannan mganar ba sai ga motar Saleema ta iso daga kwatano,Saleema sai da tayi kukam Dadi Saboda Farinciki Ummi da Abbi da hajiya sun kasa mgana,Shikamshi Saleem bai sanin Malika zatama yan gidansu kyauta sai dai yaji lbri daya yi mata mgana Sai tace Gift din Aure ne tabama Saleema da ya Nuna mata kashe Kudin yayi yawa sai da Malika ta maida Abun Fada,tana Tunanin Yanzu don ta bama Ummi yan kalilan kudade,kuma ta Siyama Saleema mota sai yazama Abun mgana,Bataji dadin haka ba,Dole Saleem ya kwaso Rantsuwa da magiya da lallashi ya Dora kafin Malika ta Hakura.
Saleem ya Fara Hawa daya daga cikin motocin da Daddy ya mallakamai Tun yana Raye prado din,Na Malika ko ya saka Aranshi zata koma hawa motar kanta,ammh sai dai ta koyi Tuki don Shi bazai yarda da Wani Direba don wannan ai Salon iskanci ne,kai kana nam Bude da baki wani gardi na gane maka mata,kowani kwalliya tayi yana ankare ta madubi yana Hadiyan yawu😂,Ammh bai sanar da ita ba ya bari sai Allah ya Sauketa lafiya.
*****************.
Biki na Saura Sati daya Bakin lagos suka Sauka Ya marwan da Joda,Ashe joda itama da dan matashin Cikinta har ya Fito,inaga Tun Haduwar Farko tayi gamakatar dashi akofar daki😂Malika na jin Joda tazo itama tace zata Tafi,Saleem yace kadama ta sa rai Joda ta Fita lafiya babu inda zata sai ana gobe Daurin Aure zasu Tafi tare,Ranar lahadi su dawo tare,don bazai barta tana yawo da wannan Abun cikin ba,Dole Malika ta Sadadu da,domin Ta tuna karonsu lokacin bikin Joda,shiyasa wannan karon bata Tada Hankalinta ba,in tayi Duba da gaskiya Saleem ya Fada tayi Nauyi da yawa koda Tama je daWurin babu Abunda zata iya,sai ma karama jama”a Nauyi.
Sai Ana gobe biki Malika tazo ita da Saleem wanda Hajiya wannan karon tazo tama Rigasu gaba da kwana Uku kafin suzo,Su merry malika tabari agida Tunda ba Dade zasuyi ba,Koda suka je sun iske ango ya iso Shida tarin tawagansa wadanda ya Saukesu A hotel,shima din ba dadewa zasu yi ba don In anyi biki Ranar asabar lahadi litini zai Wuce da Saleema wajen aikinsa don Bashi da Wani Hutu mai yawa.
Chan su Malika suka iske Ayda an zama yan mata,Ta kusa Shekara biyu,tana Tafiyanta ko”ina Gwanin ban”Sha’awa tana makale da Ummi ko Abbi ko Anty Saleema,ammh saboda wayon data keda shi tana ganin Iyayenta ta makale musu musamman ma Saleem wanda Tunda ya dauketa taki yarda ya Sauketa ko nan da nan chan,Dole yayi Hakuri yana Yawo da ita.
Gida ya cika da yan Kumo mata ammh banda maza dayake achan baban gidansu Daddy na kumon za”a Daura Auren,so su Abbi ne zasu Bisu chan wannan karon basu zasu biyo ba,Ranar daurin Aure Tun Safe Su Abbi suka kama Hanyar kumo tare da Saleem da Ya marwan da ango da tawagan abokansa,Sauran abokan Abbi da Wadansu wadanda aka gayyata Duk chan kumo zasu je,sai dai su Hadu achan.
Karfe 2:30pm Aka Daura Auren Saleema da Angonta Sadiq,Akan sadaki mafi daraja da kima,basu baro kumo ba,sai da suka tsaya sukayi Walima agidansu Abbi kafin su Dauko hanyar komawa Abuja cikin Rantattsun motocinsu.
Abangaren Gidan Biki kuwa ya cika Dakam da jama”ar kumo data Saleem da Jama”ar Ummi da Abbi Allah Sarki Harda yan malumfashin sunzo ma Ummi biki Mota guda,Wanda harda Matan Baffan joda Wato wanda yabada Auren Ba Ummi kadai ba Hatta Hajiya Taji dadi sosai Suka Dinga ina suka saka dasu saboda karramawa Ummi ko bak’inta kawayenta ne lauyoyi kowacce kagani babbar mace mai ji da ado da Dukiya mai yawa kunnawansu da hannayensu suna Kara kaina Zinare da Azurfa kamar ba kudi ake Sakawa Asiya ba.
Saleema ma taga jama”ar daba ta taba tsammani ba,Domin yawancin yan Sch din su na Buk yan Faculty su na medicine duk sunzo mata harda Wadanda sukayi Housemanship dasu,A Murtala Aminu kano,Abun mamaki Nadira ta cika alqawari wajen karfe 12 na Rana sai ga tazo Direba Dr Hambali ya saka ya kawota Saleema taji dadin Zuwanta haka ta Rumgumeta tana mata sannu da Zuwa dayake ita da yar Dr Hambalin tazo mai Suna Farha.
Takaita har Wajen Ummi sun gaisa ta mata Allah sanya alheri harda 5k dinta kusan Dama Nadira tana da wayau,tasan yadda zata kyautatama Mutum harda wata 5k din tabama Ummi tace inji momi tace ace mata bazata samu Zuwa ba,alhalin Momi da Zahra ma basusan Auren Saleema ya taso ba, Abbi ko hidima tamai yawa Bai kira Bukar Madan ya sanar Dashi ba.
Saleema dakin dasu Malika da Joda suke Dakin Hajiya Babban nan takai Nadira,sunyi mamakin ganinta ammh sai suka Shanye mamakin ganin yadda Ta nufosu da dariyarta da komai,gaisawa sukayi suna Tambayan Juna yaushe gamo,Malika sai kallon Nadira take ganin yadda takara kiba da Cika kamar ba ita ba lalle ta samu kwanciyr Hankali.
Itako Nadira Malika take kallo ganin yadda cikin jikinta yayi kato,sannu ta mata hartana Zolayanta da ko yan Biyu ne,Malika tayi Dariya kawai domin lokacin tana cikin Takaichi ne domin Kayan ankonsu da sukayi ita da Joda da Saleema da Ummi ,sunki Shiganta dalilin haka fa Ummi tace kada ayi mata Riga da Sikat ayi mata Doguwar Riga ne,ammh kwata kwata taki Shiganta,Har karba Ummi tayi ta kira mai dinki ta sake bashi ya dan Buda,ammh koda Malika ta sa,yadai Shigeta ammh kuma ya matse mata ciki Sosai tana Numfashi Sama sama,dole Ummi tace ta cire,Kuka ne kadai Malika batayi saboda takaichi Dole tana ji tana ganin kowa da kayan kwarai ita sai wata Doguwar rigarta ta sanya mai Roba na kamfanin Armani,ganin haka ne yasa Ummi ta bada Wata atamfa tace yanzu take so a dinkama Malika mai yalwa yadda zata samu ta Sanya.
Nadira sai after la’asar tatafi Malika ko da karfin Hali harda tambayan Zahra Nadira tace tana gida,mirmishi kawai Malika tayi tace agaida mata da momi da Zahra Nadira tace zasu ji,har wajen mota suka Rakota ita da Joda kafin suyi sallama su Fada mota bayan an basu kaya biki,har suka bar Haraban gidan Su malika Na daga musu hannu.
Yan Daurin Aure basu dawo ba Sai After sallar mangarib,sai gasu Sun Shigo,Falon gidan suka baje suna Sauke gajiyan Hanya Yan kumo na musu barka da Sauka,shikuma ango da tawagansa a hotel da suka sauka suka yada zango harda Shi Sadiq dinn,Ya marwan Dai matarsa ya nema ta bashi abinci don Yunwa yakeji koda Saleem yaga Uban garan da joda ta Hadoma Ya marwan kwabe Fuska yayi yana Tambayan Shi ina nashi,Ya marwan na mai Dariya yana Fadin”Ka kira matarka mana,nima ai matata ce ta gatantani..”Jin haka yasa Joda ta saki dariya tana Fadin”Ai ko ya kirata bazai jita ba yanzu tana chan tana kumburin Kaya ya ki Shiganta harda wanda Ummi ta bada aka Dinkamata yau din nan..”
kwalalo ido Saleem yayi yana Boye dariyarsa yake Fadin”Ke Da gaske..? Kice yau akwai danja kenan,ai ko bari na noke ya marwan yiman alfarma ci wajen wanda matarka ta kawo ma,Wlh yau In Malika ta ganni na zama Nama..”Dariya suka sakamai Shida Joda,sai ga Ayda ta Shigo da kuka Hawaye Shaba Shaba da majina,Joda ce tayi Saurin Daukanta tana Fadin”A”a Aydan Abbi waya tabaki..”Tana murje ido tace”Annie…”Dan ware ido Saleem yayi kafin yace”Tab yasin sai dai kiyi Hakuri Ayda ta,nima in naje Rama miki ai nakai kaina,Srry kinji zo nan kyale Annie..”Yafada yana mika hannu ya amsaheta Hawayenta yake Share mata yana Fadin”Ke ne Ayda kin cika Rigima kina ganin Annie naki ta zama sai a lallaba ammh sai ki dinga Zuwa kina damunta,Bakije wajen Abbi bane,ko baki ganshi bane..”Kai ta gyada kamar wata Babba kafin ta Washe baki ta tashi daga jikin Saleem ta koma ta Dane Bayan Ya marwan tana Kiran”Dadddi…”Rikota yayi yana Dariya yana Fadin”Aydata,ai na dauka yau ba’a ga Daddin bane..”Rikota yayi yana mata Wasan daya saba yana Cafata sama Tun tana jaririyarta yake mata Haka,harta girma data ganshi zata Nufeshi ya dauketa yana mata Wasa yanzuma Dariya take kyalkyalawa cike da Sha”awa Joda ko wayarta ta Fitar tana musu video tana aika musu da mirmishi Shiko Saleem bai biye musu ya jawo kulan Sinasir din da Joda ta kawoma Ya marwan ya loda uku A filet ya zuba miyar da akayita da Naman rago,ya ja gefe yana lodama cikinsa don Zahirin Batu yau din nan yasha Yunwa don ko a kumo bai wani tsaya yaci abinci sosai ba Saboda Shi haka yake bai cika Cin abinci agida ba.
Suna cikin haka Sai ga Malika ta shigo da tsinin Cikinta agaba hannunta Rike da Doguwar Rigar da Ummi ta kara badawa aka Dinka mata ammh Still taki Shiganta,Tana Shigowa Fuskarnan ba Annuri ta Nufi Saleem yana cin abinci sai ji yayi ta ta tsayamai bisa kai tana Tura baki dagowa yayi yana kallonta ganin haka yasa ya danne Dariyan dake neman kwacemai yace”Uwar biyu meya faru ne..? Na ganki kuma da Riga ahannu lafiya ke baki sa kayan bane,kiman kwalliyan dashi..?.”.Yafada yana kallonta mganar daya Fada kamar ya Tunzurata ne,kawai sai ta Fashe da kuka tana Fadin”Yaushe zan yi wata kwalliya da wannan cikin,Kowa ya saka kayanshi mai kyau ammh banda ni,shine kuma kai kana nan zaune ko ajikin ka..”
yana Danne Dariyanshi yace”Ashh,duka sunki Shiganki ne,Kai Abu baiyi dadi ba gaskiya,…”Tana Share ido tace”Wannan ma fa Ummi ta kara badawa akamin Dinkin Sauri itama bata Shigeni ba..”Ido ya zaro yana danne dariyarsa yake Fadin”Kai don Allah..? Kuma sai kace wata giwa ace Abu har an sake dinkawa ammh kuma yaki Shiganki..”Ya Fada yana Dan Ware ido kamar gaske.
Dariya ce takama Joda da Ya marwan wanda suke ta Danne ta kada ta Fito Tun Shigowar malika,Wani kallo ta Watsama joda kafin tace”Ke kuma wa kike ma Dariya..”Tafada cike da Haushi Ya marwan yayi Saurin tashi yana Rike Ayda yake Fadin”A”a fa kada ki Wuce kan matata,ga mijinki chan Shiya fara dariyan fa..”Yafada yana nuna Saleem da baki,wanda ke kokarin Rike dariyansa ammh kuma taki rikuwa sai da ta Fito Waje,Malika ta tsaya tana kallonsa cike da takaichi ,mikewa yayi yana Dariya ya Daga hannu yana Fadin”Allah ban miki dariya ba,Srry afuwan haba Malika ta,Haba yar Amanata,Kinfan san Nidake bata baci kada ki bari Ya marwan ya Hadamu fa..”Ya fada yana Dariya wacce takasa tsayawa.
Da Haushi ya kama malika sai ta bishi zata makamai Rigar hannunta tana Fadin”Zaka sani ne,wato ma Dariya kake,Tunda ni kamin ciki kabarni da aiki ko,ai akanka zan Wuce yasin kuwa..”Ganin tayo kanshi yasa ya haye gadon yana Dariya sanin dayayi bazata iya hayowa ba,itako ganin haka yasa tayi tsaye kafin ta saki kukan Shagwaba,Ganin haka yasa ya sauko daga kan gadon ya Rumgumeta ta baya yana Fadin.
“”Srry bari kuka kinji,nine ko..? Bazan karaba insha Allahu na bar dariyan.”Yafada yana Kamkameta ta gefe daya kuma ya zuro duka hannayensa biyu yana Shafa tsinin Cikinta,ya marwan da joda ko Tun Shagwaban Farko suka Fice dauke da Ayda suna Dariyansu Saleem,shiko dakyar ya lallashi yar rigimar nashi tayi Shuru,abinci ma sai abaki ya bata,yayi mata wanka ya Shafamata mai,Ranar dai bata sanya kaya ba ammh Washe gari Dole Saleem ya Fice Zuwa neman ma Malika wanda zai Dinkamata kayan da zai Shigeta kada Ta Cinyeshi danya da Masifarta.😂
Washegari ko Sai da Malika ta Sanya Wani leshi wanda Saleem yasa aka Dinkamata Riga da zani,rigar sai aka Budeta sosai har Zuwa gwiwanta,Dalilin daya sanya ta barshi ya Fita kenan ammh da tace wlh sai dai su zauna tare agida Tunda dai Shi yayi mata Abunda kaya suka Daina Shiganta,😂Saleem yaso su koma katsina Aranar ammh Ummi ta hana Dole suka bari sai monday,yan kumo da abokan Sadiq dai Aranar suka koma.
*******************
Ranar monday Tun Safe da karfe 10 am na Safe iyalan IG kabir kumo,suka Raka amarya Saleema da angonta Sadiq suka hau jirgi zuwa garin Abia inda Sadiq din yake aiki acikin masu rakiyan Harda Abbi da Ummi da Hajiya babba da Hajiya binta da malika da Saleem,da Ayda da joda da ya marwan,dukkansu suka rakasu har Filin jirgin Nnmadi azikiwe internationl Airport,suka rabu cike da kunci Saleema dakyar ta saki Abbi da Ummi wanda ta Rumgumesu tana kuka,hakama tama Saleem da Ya marwan Wadanda suma sunji ba dadi musamman ma Saleem domin Shine yafi kowa Shakuwa da Saleema,haka ta Rumgume joda da Malika tana kuka,wani karfin Hali ta rike Ayda wai sai tatafi da ita😂Malika ko tace ta bata Halas malak ta tafi da ita har Saleema ta fara murna Saleem yace Bazai yuyu ba ta bari ta kara girma lokacin,Sunzo ganin gida,sai ta tafi da ita,Dole murnan Saleema ya koma ciki Dakyar Sadiq yajata suka Shiga jirgin Tunda ana ta kiran Sunanyensu,Haka suka dawo gida jikinsu Duk yayi Sanyi musamman Ummi,Motar Saleema kuma Sadiq yace zai aiko Direba yazo ya dauka ya kaimata chan,Tunda achan zatayi Service dinta,kusa da mijinta.
Suna dawowa Daga raka Saleema,Su malika sukayi Shirin Tafiya,Ummi taso su tsaya ammh Saleem yaki,wai saboda wajen aikinsa,kuma bashi da alamun barin Malika dole Ummi ta bisu da Allah kiyaye hanya,Wannan karon Saleem yacema Ummi zasu tafi da Ayda bata hanasu ba Tunda yarsu ce,ammh sai Ayda ta watsa musu kasa a ido ta makale Ummi tana kuka Dole Saleem ya kyaleta,da Abbi yaji lbri dariya yayi yana Fadin”Su Saleem masu ya”Toh rigimar me yakeyi ga matarsa chan da wani cikin,ko kuwa Rashin kunya yaran zamani..”Dariya kawai Ummi da ya marwan sukayi tayi Sanin Halin Saleem din da Shi kanshi Abbi.
Tare da Hajiya Binta suka Wuto katsina sai aka bar gida Daga Joda sai ya marwan wanda sai Wani Sati zasu koma Lagos din,Su malika sun isa gida lafiya,hajiya kuma har gida suka kaita,koda suka koma su Merry sun gyara ko”ina na gidan,Saleem baima Zauna ba office ya wuce saboda an kirasa yana da baki itako Malika Suna dawowa Ta fada gado tana barci don ta gaji ga bayanta ya Rike kafarta kuma ta haye Saboda Zaman mota.
………….”Malika Da Saleem sun Cigaba da Renon cikin Malika wanda ya Shiga Wata na Tara ammh kuma yayi girman gaske gashi ta kara Hauhauwa in ka kalleta Sau daya bazaka ce Malika bane Dole sai kara kura mata ido kafin ka tantance itace ko ba ita bane.
Gabadaya ta rame tayi baki ta Rame,gashi Ta kumbura tayi Suntum,Tashi dakyar zama dakyar,shikanshi Saleem din Hankalinshi take yake da Tsausayin Malika,Sun Riga sun gama Shirin Haihuwa ganin Watan Haihuwan ya Shiga,ammh kuma haihuwan Shuru har Cikin Malika Ya haura Wata Tara ya Shiga na goma,ammh Haihuwa Shuru ganin hakane yasa Ummi tace Hajiya binta tazo ta Dauki Malika suje asibiti aduba agani in Haihuwan ta garara,kawai ayi mata operation,saboda wahalan tayi yawa ko itama Malika ta Wuta da wannan Wahalan.
Da Ummi ta kira Saleem Tana Fadamai Shawaran data yanke,sai ya nuna bai yarda A kai Malika asibiti aje akwakulo mata Nakuda ba,Su kara Hakuri Zuwa nan da Sati daya su gani,in bata ji komai ba,kuma bata Farajin Nakuda ba,sai a tafi asibitin ansan yadda za”ayi,Ummi bata ki Shawaranshi ta bar mganar haka,ammh kuma har Satin ya Shude wani ya Shiga Ba mganar Haihuwa,Dole Saleem ya yarda ya Dauki Hajiya Binta ita da Malika suka Nufi Asibitin datake awo Wato Federal Medical Center katsina.
Suna zuwa aka shiga da ita dakin Scanining,nan suka iske yan biyu ne acikin malika,don sai alokacin Allah ya gwada musu don ko da take Zuwa awo suka mata scaning Namiji daya suka gani Allah ya hanasu ganin dayan,dama toh ai karambani ne,Allah kadai yake da ikon sanin Abunda zai Faru yanzu ko anjuma,kuma Shike da ikon ganin komai,kuma Ya zartan yanzu kuma ya Faru,likitoci kawai wani lokacin Allah na basu dama ne,ammh sudin ba Allah bane basu isa su ga Abunda ya Halitta acikin mace ba,sai dai in Dan Allah yaso ya gwada musu da kanshi.
Yan biyu ne,ammh daya ya jirkice kafarshi tana wajen kan dayan,Shi dayan yana so ya Fito,ammh kuma kafafun dayan daya chanza wajen zama ita ta tokoreshi,koda dayan zai yi yunkuri Fitowa sai kafar dayan ta tokoreshi ta hanashi kuma shima so yake ya Fito,ammh kuma ta kafafunsa Tunda Ya jirkice,lalle ikon Allah,Shine Dalilin Daya sa Harta Wuce wattanin Haihuwarta bata haihuwa ba,da ace ta kara wasu kwanaki in suka yunkuru zasu Fito gabadaya zata iya Rasa Ranta suma yaran koda zasu Fito may be suma ba’a raye ba saboda sun Jigata aciki sosai…
Bayanin da Dr yayima Saleem da Hajiya kenan ya kuma umarci Saleem daya sanya hannu yanzu zasu Shiga da Malika dakin Tiyata Domin Cetonta ita da Abunda ke Cikinta,kuma suka bashi Umarnin yaje ya biya kudin aikin yanzu yanzu,Jikin Saleem na Rawa ya Rattaba hannu kafin ya kwashi Gudu yaje ya biya kudin Aikin da za”a ma Malika,Cikin lokaci kadan suka gama Shirya malika cikin kayan Tiyata suka gungurata zasu Shiga da ita dakin Tiyata,Lokacin Su saleem suna wajen Da hanzari ya karisa ga Malika ya riko hannunta haka ke Zubomata sha,ya sanya hannu yana Sharemata yake Fadin”Stop crying kinji za”ayi aikin lafiya insha Allah kinji..”Kuka ya kwace ma Malika ta sakeshi tana Shesssheka take Fadin”Mutuwa zanyi Mallam,ka yafemin don Allah..”Abunda ta Fada ya Kashema Saleem da Hajiya gwiwa bai samu zarafin mata mgana ba,Suka gungurata Zuwa dakin Tiyata wanda Hannunsu dake sarke da juna ya Rabe,har aka Shiga da ita suna kallon Juna Malika na Fitar da kwallah..
Kai Saleem ya Dafe yana kiran Sunan Allah,haka yaji Duniyar tayi masa kunci Bai Saurari Hajiya dake Fadin ya bar Damuwa Malika zata haihu lafiya,cikin mota ya koma ya Dafe kanshi da Sitiyarin mota yana Fidda Numfashi sama sama yana kallon idanuwan Malika suna Fitar da kwalla,tsigar jikinsa ne ya tashi sai yakeji kamar kallon bankwana tayi mai,Saleem har sai da ya Fitar da hawayen Tsausayin kanshi dana Malika,nan cikin motan ya cigaba da zama don baida kuzarin komawa cikin Asibitin yana ji wayarsa dake cikin aljihu tana Faman Ruru ammh kuma yakasa sanya hannu ya Cirota balle yaga kowaye mai kiran nasa.
Ummi ko dagachan Bangaren Hankalinta amatukar tashe yake ganin Tana ta kiran Wayar Saleem bai dauka ba,bayan kuma sunyi waya dashi Sanda zasu kawo Malika asibiti ganin bai daga kiran nata bane yasa ta maida akalan kiran nata kan Hajiya Binta ita ta dauka ta mata bayanin Abunda ke Faruwa,hankalu fa sun tashi sosai don nan Ummi take Sanar da Abbi wanda Shima hankalinshi ya tashi ammh sai suka barma Allah komai suka koma mata Fatan Allah yasa ayi aiki lafiya kuma afito da kai lafiya.
Shudewar Awa uku likitocin da suka Shiga da Malika sukayi kafin Su Fito,Kowanne Fuska ba Annuri Hajiya dake zaune awajen,tayi Saurin mikewa tana Tambayansu ya Malika..? Anyi Nasara kuwa..? Basu samu bata amsa ba illah tambayan Saleem da sukeyi ganin haka yasa Hajiya Binta tayi waje da Gudu,aharaban asibitin ta tsaya tana Neman Saleem bata ganshi ba,har masallacin shashen maza ta leka ammh bata hangoshi ba,ganin motarshi a parking space ne yasa ta karisawa ta Gudu ta kwankwasa glass din gaban motan tana Fadin”Saleem,Saleem malika..”…
Kansa na Bisa Sitiyari Barci ne ya fara dibanshi Harda Mafarkin An Fito da Malika ta Haihuwa lafiya kamar amafarki yaji buga glass,shi ya tadashi A Firgice yana bin inda yaji karan da kallo,dayake motar Tinted ne na waje baya ganin na ciki,shi ya Fara ganin Hajiya,ganin yadda Fuskarta ya Nuna damuwa ne yasa ya balle murfin mota ya Fito yana Fadin”Gani Hajiya lafiya..? Sun Fito da Malikar ne..? Hajiya Bakinta na Rawa tace”Eh nemanka suke..”Jin haka yasa ya Runtuma da gudu Zuwa cikin Asibitin Jikinsa na Rawa saboda Fargaba,itama Hajiya ta takemai baya.
Yana zuwa kofar Theater Room ya Gamu da likitocin bai jira cewarsu ba yafara Fadin”Hop d Operation is Sussesufull,…? Kallon Juna Sukayi kafin wani daga cikin Likitocin ya Dafa kafadanshi yana Fadin”Yes..d bbys are in good condition buH….”Saleem yaji Zuciyarsa na lukude ya Warce kafadansa daga hannu Dr yana Fadin”Buh waht…? Yafada Duka idanuwansa suna waje…
Kansa na kasa yace”Buh u lost her…”Zaro ido Saleem yayi cike Da firgici ya cakumo Wuyar wanda yace Malika ta Rasu yana Fadin”Kutumar ubanchan,Matar tawa ce zaka ce min bata,kana da Hankali kuwa,Wlh sai na kasheka nima…”Yake Fada da alamun ya Fita daga hayyacinsa,Hajiya data Fahimci Abunda ya Faru ta dora hannu aka tana kuka tana Fadin”Innalillahi wa’inna Alaihirraju’un..”Sauran likitocin ne suka Rike Saleem suna Neman rabashi da Wuyan wanda ya shaka,ammh sai Fuzge Fuzge yake kamar mahaukaci yana Fadin Shima sai ya kasheshi indai Bai Fitomai da matarsa ba.
Wani daga cikin Dr din ya Riko Kafadun Saleem da karfi yana Fadin”plz mrs man Cool down We know ur Feeling.buh am so srry to say u Wife iz Dead,we are Srry…”Zuru Saleem yayimai da ido yana kallonsa kafin yaji Duniyar na juyawa dashi kafin kace me, ya Sulale zai Fadi asume Dr din ya Rikeshi yana kwalama Nurses kira,nan da nan sai gasu da gadon daukan Marasa lafiya suka daukeshi Suka dorashi suka Shiga dashi wani daki.
Wata Nurse ne dake Dakin Tiyata ta Fito da Sauri tana Fadin”Sir She iz Breathing,…”Zaro ido sukayi atare kafin su Rankaya cikin dakin da hanzarinsu cikin gaggawa,shiko Saleem taimakon gaggawa akabashi kafin asamu ya Farfado aka yimasa alluran barci,Hajiya dake waje ban da kuka da Salati Babu Abunda takeyi tana cikin wannan Halin ne sai ga wani likita ya Fito daga Tiyata Room din daga ganinshi Musulmi ne,kallon Hajiya yayi yana Fadin”Mama kuyi hakuri da Abunda ya Faru lokacin da suka Ciro bbys din dake cikinta sai Numfashinta ya dauke,so sun zata ta rasu buh yanzu Numfashinta ya dawo komai ya Daidaita mun mata alluran barci zamu Kawota dakin Hutu ita yaran ta samu Twice,Duka Maza..”,
Hajiya Binta Tana washe Baki take Fadin “Alhamdulillah..Allah mungodemaka..”Take Fada tana Share kwallah,Daidai lokacin kuma wayar Ummi tashigo wayarsa nan da nan Hajiya ta daga bayan sun gaisa take tambayanta ya ake ciki..? Nan Hajiya Take Sanar da ita komai,Ummi ta Girgiza kai Tana Fadin”Ina Shi Saleem din..? Hajiya tace”Sun Shiga dashi ciki suma yayi lokacin da sukace Ba malika..”Ajiyar Zuciya Ummi ta sauke Kafin tace”Allah ya sauwake Allah yabata lafiya ya kuma Raya Abunda aka samu,Da safe muna nan Tafe..”
Dahaka sukayi sallama da Hajiya nan take Fadama Abbi Abunda ke Faruwa,ga murna ga damuwa sun tattara komai sai gobe in sunje sun gani kafin kace kwabo Haihuwan Malika ta zaga dangi,shiko Saleem sai da Daddare ya Farfado inda ya samu lbrin Malika bata mutu ba,sai lokacin yaji Abunda yamai Nauyi akai ya sauka,itako Malika bata Farfado ba sai Washegari,Dayake Hajiya ta kwana da ita Shikuma Saleem yakoma gida,Tana Farfado Abunda ta Haifa ta Fara Tambaya inda Hajiya ta mika mata su Duka biyu,kukan Farinciki Malika ta saki ta kamkame yaran,Kafin ta tambayi Saleem nan Hajiya ke Sanar da ita Abunda ya Faru,wani Farinciki ya Ratsata ganin Har Suma Saleem yayi Saboda Ance ta Mutu lalle ba karamin So da kuma muradi Saleem ke Mata ba.
Saleem Sai wajen 10 yazo,shi yazo musu Abun karyawa,shida merry yazo Saboda tataya Hajiya zama,Lokacin dayayi Arba da Malika agaban Hajiya ya Kamata ya Hadata ida yaran ya Rumgume yana Hawayen Farinciki,Malika na mai Dariya mai Suma,Keyarta ya make yana Fadin”Waya ce miki na suma..? Inda ace kin Mutu da nima binki zanyi Amanata,..”Kansa ta Shafa tana Fadin” Bazan Mutu ba Mallam,ina tare dakai Abadan,dakai zan rayu da kuma kai zan mutu..”Bakinta ya Sumbata cike da So Da kauna,hajiya dai Tuni tayi waje don Saleem dare dare kan gado yana ta Sumbatar Yaran,,yana kuma Hadawa da uwarsu,yana kuma ma Malika dariyan wannan karon ma yaci gari domin Gabadaya yan biyu kamaninshi suka debo,wannan karon ma Farar Fatar Malika kadai suka debo ammh har Shape din hancinsu,irin na Acp Saleem ne.
Ahaka su Ummi suka iso suka sameshi sai da Ummi ta Faffatakeshi waje kana Ya Fita,harda Rigimammiya Ayda aka zo,aiko nan taga Bbys ta makale tace bazata koma ba,Ummi tayi tayi Ammh Ayda ta makalema Malika tana Santin Kannenta,Dole su Ummi suka tafi suka barta wajen Hajiya,washe gari sai ga yan Malumfashi sunzo Duba Malika ,mota guda basu jima ba suka koma Dama ganinta sukazo yi,washe gari kuma sai ga yan kumo suma mota guda sunzo Duba Malika da zaratan magidantanta,wanda taji sauki sosai kamar ma ba”ayi mata aiki ba..
Joda ko da Saleema awaya suke kira suna ji kamar suyi tsalle suzo,saboda Zumudi ammh kuma duka mazajen nasu sunce sai sun Duba sun gani,ammh da Wuya su barsu suzo,Kwanan Malika 5 Aka sallameta ta koma gida Tunda taji Sauki sosai Dole Hajiya ta Dawo nan tana Kula da ita su merry na taimaka mata Tunda hidimar dayawa gata yan Biyu gata Ayda wacce ake Daga da ita sai ta Dauki Yan biyu,kuma ba dabam dabam ba,a”a so take abata ta dauka Duka biyu alokaci daya in ance bazata iya ba,sai tasaka kuka sai Babanta yazo ya Dauketa yayi ta lallashi ko yabata wayarshi ya Shigan mata game take Hakura..
Awannan karon ma Saleem ya Shirya Sunan Kece raini,Domin Sa guda Za”a yanka banda Raguna uku da kaji,Abun fa sai wanda ya gani,Ana gobe Suna Saleem yayima Yara Huduba da *KABIR* Da kuma *ABDULMALIK* Sunan daya Dadala Ran Malika Sosai Ganin yau ta Haihu da cikinta tama Daddylove takwara Shida Abbi,Abbi ma yayi murna Shima yayi bajinta Sosai,Maman Abba ma tazo ana gobe suna,Saleema ce Kadai ta samu Zuwa Joda kam tayi nisa dayawa,bama haka ba cikinta ya Tsufa mijinta yace baigama mata Shiri ba so yake in tazo to bazata koma ba sai bayan Ta haihu Dole ta hakura….
Sunan Zaratan mazan na Saleem an Shiryashi Domin Tun Ana gobe sunan Mota ta dinga sauke duk wani Nau’in Lemon sanyi na Sha da kuka sani sai da aka Saukeshi,duk kuma wani Ruwa na kowani kamfani Shima an Saukeshi Domin Taron gobe,Su Maman Abba da Saleema ko Tun daren Ranar suka Dinga Soye soyen Naman Raguna da kuma kaji,Domin bakin da zasu zo gobe yan Suna Duk da dai Duk yan”uwa ne da abokan arziki,Wannan karon ma Ummi akwati Hudu tayi na malika daya na Zaratan magidanta kuma Kowa daya daya,hakama Abbi yayi musu akwatina Shake da kaya na malika dana Takwaranshi da kuma mai Sunan Abokinshi.
****************
Washegari Ranar Suna,Baki na nesa dana kusa Duk sun Hallara Jama”ar kumo ma sunzo,Jama”ar Malumfashi ma sunzo mota guda Domin taya Saleem murna Shida Malika,wacce ta kece cikin Shigan ta alfarma Kafafunta da hannayenta sun Dauki Shekin lalle ja da baki wanda yakara Fito da ita sosai,yan biyu ko Wadanda akeyima alkunya da AYYAN DA AYRAN suma an cakare su cikin kayan alfarma gwanin ban’Sha’awa wadanda suke kama da Ubansu sak kanar yayi kaki ya ijiye,Mganar Abinci ko,Reataurant ne guda Saleem ya yi odarsu suka zo suka baje kolinsu Kowani Nau’in abinci akwai su Awajen komai kake bukata aikwaishi Sai dai kaje ka diba son Ranka babu mai hanaka ko yayi maka iyaka.
Wajen Misalin karfe 12pm sai ga Motoci har biyu cike da Mata,Da farko anyi mamakin ganinsu ganin yadda suka ci angonsu cikin wani Leshi mai Ruwan Hoda wanda keda zanen kwalliyan green ajiki,kowacce ta daka Uban Dauri ta chaba ado ba Raini,Akallon Farko zakayi musu ka gane ba Raini don ba yaku bayi ba ne😂,Sai bayan Sun Shiga ciki ne,Malika ta gansu sai fa Ta tuna su, Masoyanta ne daga *HAFNAN AND JANAF PAID GROUP* da kuma yan Amanata wato *MALIKA MALIK PAID GROUP* ,Nan da nan ta karbesu hannu bibbiyu ta hadasu da Maman Abba da Saleema tace aware musu daki na musamman,saboda bakinta ne,nan da nan ko aka Shiga ina aka saka dasu,Haka aka dinga jera musu Nau”o’in abinci da lemuka Kala kala gabansu bayan Uban Naman Rago soyayye da kuma Naman Kajin da suka dinga yi musu hy acikin manyan Filet din da aka Jirke agabansu,Tuni Su Sahiba Sarkin kwadayin Naman kaji,Tafara Hadiyan yawu kamar wata mayya ta mika hannu zata dauka Uwar dakina Chubado muhmmed ta kabe mata hannu tana Fadin”,Haba hafsy meye haka ki bari mana za”a baki kina Abu kamar baki taba ganin naman kaza ba,don Allah karki badamu mana Acp Saleem ya Shigo yaganki kina Halainiyar Naman kaza ya Rainamu..”tafada cike da yanga ammh itama cikin Zuciyarta da bakinta kwadayin Naman ne ke cinta ammt ta danne,itako Dotata ladingo kusan Abunka gamai ciki,😂😂miyanta har ya tsinke ta Kafe Ferfesun kayan cikin dake wajen da ido,Sisinah Aisha alto ganin haka yasa ta matso mata da kwanon gabanta tana Fadin”,Ci Abinki Diyarmu Shalelenmu ni da Janafty,kada ki kwari Jikanmu😂Fadin haka keda Wuya Dota ta fara Sharban kayan cikin nan ko jinta tasu Maman kausar da Fati sadiq da suke mata Tsiya bata yi ba,Su Nazeefa ko da Ummu bilal,ummu bilal2 da Ummi haneef,sune manya sai wani manyance suke suna tsara komai,ammah Abun mamaki da sun Fakaici indon mutane sai su Tura hannu cikin Farantin Nama su debo su Tura cikin wasu manyan jakunkunan da suka zo dashi kamar zasu saka kan mutane Ashe saboda suyi Satan Nama ne😂.
Hajiya Zuwaira ko da Kawa juwai,ko Suna barayin lemuka,sunfa sha har sunkusa amai ammh haka suka dinga Turawa har suna guzuri ajaka toh Abun ne dayawa Shiyasa babu Wanda yabi takansu,su Aisha amarya,su Aisha musa,su Amsopy,Asma”u Bafarawa,Asmau shehu,asmeey,Aisha usman,Bbj da bilkisu sani kuwa harda Fadan Fride rice,yadda kukasan basu taba ci ba😂Sai da su Dijah Abdul da fatima Musa,ta niger,fati sadiq,Fatima Xahra da fee sai jikar hajiya,haleem Sweetheart dina,jidda lawan,khadee Noor,Khadija muhd manga,khadija usman,khadija bashir,momy h,mmn Nabila,,mm Teema,mmn Useey,mmn kausar,Mmn bby,mmn khairat,mmn Nazeer,mmn Rabia,mmn Ummulos,mmyn Abdul,murja bakugu,suka rabasu Alhalin suma kowacce ta cika jakanta da Awaran kwai da aka kawo musu,Sata ce taci sata,ba wacce bata sata tayi cikin Jakanta dashi ba,ammh suna raba wasu fadan Hinkafa😂😛,Ai Ba Abun Haushi sai yadda su Besty ta da Nucy girl,Rafi”atu,yar Fulani,Saleema Hamza,Sardiya,Ummi,my Azeeza,deejart,Fatima garba,Hadiza,mmn basma,mmn sayeed,mmn Baraka,Malika masoyiya,mmn Amira,mrs umar,Durlig Rukayyah,mumy Halil,Rouky,Suwaiba,mmn Sadiq,Nafisa,mmyn sani,mrs zainab jega,Fatima umar uwaisu,Shafa yola,wasila,Rafiatu s Rimi,Khadijat usman,Bilkisu Duwan,Suka Dinga bi suna kulla Duk Abincin da suka rage aleda suna Turawa ajaka da Nama ne,dasu lemuka,da Zuwaira da Nazeefa,da su Ummi bilal sukayi musu mgana cewa sukayi abarsu su jida,gida babu,bikin irin na Malika kuma sai Rabo ya Ratsa makota kuma sai daidai😂😂Sun dai ci sun sha don ko Sunan yan biyu sun fa goge Wuya Da Naman kaji Abun ba Dama.
Sai dai kuma da suka tashi Tafiya basu bar Malika haka ba,Kowacce sai da ta bata dan Abun suna,kafin suyi musu sallama su Tafi bayan kowacce ta cika jakanta da abubuwa,Malika ta rakasu har Wajen mota tana yi musu Fatan Sauka Lafiya,amotarma ma fa Allah ya tsare da anyi Dambe don Mmn Sadiq,ce da Sahiba suka so su kasa hali kan cinyar Naman kaza da Sahiba ta sato acikin Sikat dinta😂Sai da Direba ya tsawatar yace kada wacce Ta kuskura tamai Fada amota kana kowacce ta Shiga taitayinta.😂😂😂😛😛😜😜😜
Anyi suna lafiya angama lafiya Washegari yan KUMO da yan Malumfashi suka koma,suma cike da kayan arziki,Suka tafi suna Malika da Saleem fatan alheri da Fatan Allah Shi raya Ayyan,da Ayran.