MALIKA MALIK CHAPTER 20 KARSHE JANAFTY

MALIKA MALIK CHAPTER 20 KARSHE JANAFTY 

              *KAR’SHE…*👏😰🙌

  …..”Full Address Din da Saleema ta Turo mata tabi da kuma tambaya sai gata abakin makeken get din gidansu Malika tana zuba hon da hanzari megadi yazo ya wangale mata get yana mata barka da Zuwa,yana zaton kawar Hajiya Malika ce.

Aparking space ta adana motarta kafin ta Fito tana Sanye da abaya doguwar riga baka ta kamfanin Armani Wacce ta yane kanta da karamin bakin gyalenshi, Kafarta Sanye da Cover baki,mai wani Fulawan baki Ajikinsa,sai karamar bakar jakarta dake hannunta Hade da key din motarta cikin Sha”awa take bin gidan da kallo kafin tafara taku Zuwa Wata kofar glass din da zai sadata da cikin Babban Falon gidan.

Tana sa kanta Falon Cikin Sallama Da karamar muryanta kamar ba Zahra ba, babu kowa a makeken Falon,sai karar Talabijin din da ta kusa cinye bangon Wajen Saboda Girma,tana kokarin sake Maimaita Sallaman nata ne Sai ga Merry ta Fito dauke da Aryan ahannunta yayinda Dose ke Tura Ayyan a wani karamin keke da alamun na koyon Zama ne… 

Da kallo Zahra ta Bisu dashi tana Mamakin Yaushe Malika ta Sake Haihuwa Domin ko ba”a Fada wannan ya”yan Malika ne da Saleem Saboda yadda suka kwaso kamanin Babansu da kuma Hasken Fatan Mamansu,Merry ce Tafara gane Zahra cikin Mamaki da doki ta Furta..”Anty….”Tafada cike da mamaki da Murna lokaci daya.

Mirmishi mai Sauti Zahra ta Saki kafin tace”Yes Merry..”Tafada tana mika hannu ta karbi Aryan daga hannunta tana Fadin”Ina Malika..? Ko bata nan ne..? Dose ta gaisheta ta amsa cikin sakin Fuska tana ma Ayyan wasa hannunta na dauke da Aryan,Da hanzari merry ta Haura sama ta kwankwasa dakin Malika,wacce Fitowarta wanka kenan tagama Shiryawa kenan cikin wata Atamfanta Riga da Sikat,tana Daura Dankwali tazo ta bude kofar ganin Merry yasa tace”Merry anthing..? Merry na Washe baki Tace”Anty Zahra ce tazo tana Falon kasa tana jiranki..”Cike da Mamaki Malika ta Furta”Wata Anty Zahra..”,

Merry tace”Wacce kuka zauna atare Azamfara Anty..”Cike da Mamaki Malika ta zaro ido tana Fadin”Zahra..!Sure..”Merry tana Dariya tace”Very Sure Anty..”Malika bata jira Cewar Merry ba Fito daga dakin ta Sauko kasa merry tabi bayanta cikin Sarsssafa Malika ke saukowa daga Steps idanuwanta na cikin na Zahra tana Saukowa ta karisa gareta tana Fadin”A”a Hajiya Zahra ce yau agidan Namu..? Tafada tana sakin mata murmishi lokaci daya kuma ta bata hannu suka Sarke cike da Farinciki Zahra tace”Wlh kuwa,Na sameku lafiya ya yara,ina Ayda nasan yanzu anzama yan Mata..? 

Tafada cike da kulawa,Dariya Malika tayi tana Fadin”Lafiya lau wlh,yara gasunan,Ayda kuma tana mkranta basu taso ba..”Tafada ta karisawa da Zahra bisa daya daga cikin kujerun Falon suka Zauna Zahra na Rike da Aryan,da hannu tama Dose alamun ta miko mata ayyan Duka ta Hadasu ta rike Tana Fadin”Masha Allah yan Biyu kyautar Allah..”Take Fada tana musu Wasa,Malika kuma ta umarci Merry data kawoma Zahra ruwa da Lemo nan da nan ko ta Shako mata Faranti guda da lemuka da Ruwa tazo taja karamin Center Table din dake Tsakar Falon ta ijiye akai kafin ta Zuba ma Zahra Ruwa ta mikamata ta karba tana Fadin”Tanque Merry..

Sai da tasha Ruwa kana suka kara gaisawa da Malika cikin Fara”a tare da Tambayan Yaushe gamo,malika ta Tambayi Nadira,Zahra tace da tare zasu zo,Ammh Mijinta ya hana Saboda tayi Nauyi baki malika ta rike tana Dariya take Fadin Allah ya Raba lafiya Kwata kwata Malika batama Zahra bakunta ba ko ta Nuna mata wani abu ba,Ta saki jikinta Sosai tana ta janta da Hira tana tambayan mutanen gidan,Cikin hiransu ne Zahra ta Fitoma da Malika katin bikinta ta Bata tare da Sanar da ita tana gayyyatanta,cike da Farinciki Malika tace insha Allahu zata zo indai Saleem ya barta,Shuru Zahra tayi kafin ta Sulale kasa tana Rokon Zahra gafara bisa Abunda ta aikata gareta Rikota Malika tayi tana Fadin”Wlh banta ba Rikeki ba Zahra,Da ina da yarda zanyi da Tuni Mallam ya dawo dake dakinki mun zauna tare,Ammh bani da yarda zanyi,har ga Allah Zahra banta rike ki ba har azuciyata ba..”Zahra na Sharan kwallah takema Malika godiya bata jima tace Zata tafi Malika ta Hanata tace ta bari ta kira Mallam yazo su gaisa,Ita kuma taki tace tafiya zatayi bataso tayi Dare ahanya,suna cikin mganar ne sai ga Saleem ya Shigo Shida da Ayda yana office ya samu wayar Shugaban mkrantan su Ayda an tashesu tun dazu ammh har yara sun gama watsewa Ba”a zo an dauki Ayda ba kuma yayi ta kiran Wayar Malika bata daga ba itako Zuwan Zahra ne ya Mantar da ita komai,kuma wayarta ta barota asama…

Shima yayi mamakin ganin Zahra,ammh sai ya Shanye mamakin ta hanyar Hade ransa itama Zahra gabanta na Faduwa ta duka tana Gaisheshi adakile ya amsa yana Shirin Haurawa sama Malika tace”Mallam zahra fa  gayyatanmu tazo yi zatayi aure upper week insha Allahu..’Bai waigo ba yace”Allah ya sanya alheri..”Daga haka ya Haye sama ya Shige dakinsa ko waigo,duk da Malika bataji dadi ba,ammh Sanin Halin gogan nata sai ta barsa,itama Zahra haka taji ammh sai ta Share ta bar Abun duk laifinta ne,kuma bata ga laifinshi ba,don ta chanchanci Fiye da Haka…

Girman Ayda ne da wayonta ya bata Mamaki haka ta dauketa tana Tambayanta Sunanta tace”My Name is Fatima Saleem kabir kumo,know as Ayda..”Baki Zahra ta rike tana mamakin Ayda Malika na musu Dariya domin Ayda akwai kwanya kuma dayake wani lokacin Duka iyayenta basu mata mgana da Harshen Hausa sai dai Turanci gasu Merry ma basu mata mgana da Hausa Sosai dat why tatashi dashi abakinta koda ta Shiga mkranta Abun bai bata Wahala sosai ba.

Zahra bata tafi ba Sai da Malika ta matsamata ta ci abinci kana ta rakota har Wajen mota suka rabu bayan Malika ta karbi Digit din Zahra da alqawarin insha Allahu zata lallaba Mallam zata bikinta da Yardan Allah,Zahran Tadai jita je,ammh ganin Yadda Saleem din yayi batayi tsammanin Zai Barta tazo ba,da zata tafi tabama Ayda 5k ita dasu Ayyan bayan Tarin tsaraban data zo musu dashi na Chaculate,suka rabu cike da kewa har motar Zahra ta bar Haraban gidan Malika da Ayda da su Merry suna Daga mata hannu.

Koda Malika ta dawo cikin gida Saleem bai mata mganar Zahra ba itama Sai ta Share bata Tankashi ba har Washegari kanzil bai Ce mata ba,kuma yana ganin Ayda ta saka Rigima da safe ita sai an saka mata chaculate din da Anty Zahra ta kawo mata cikin basket dinta,Yana jinta tana Fada da ita kan Shan zaki,sai ma tasowa yayi da kanshi ya kwashi Chaculate din ya Zuba mata cikin jakarta ya kama hannunta Suka Fice daga Dakin,da kallo Ta bishi kafin Ta murmusa,domin inda sabo ta Saba da Halin Miskilamcin Saleem.

Har Bikin Zahra Ya matso Saleem bai cema Malika komai ba,Ana jibi bikin Saleema ta kirata awaya, tana Tambayanta in zataje Zata zo gobe sai su Wuce Kanon Tare,Malika bata yanke mgana ba Sai da Saleem ya dawo da daddare take Tambayanshi Zuwa bikin bai ce mata komai ba,balle ta saka Ran Zuwa har Washegari Ta kira Saleema tace bazata samu Zuwa ba,Suka Rabu da Saleema kan zata Abuja aranar jirgi zata biyo gobe Direba zai kaita Kanon Tunda dai Tayi Ra”ayin Zuwa.

Sai da Daddare har sun kwanta yace gobe ta Shirya Zasu tafi Abuja gabadayansu Suyi Hutun karshen Mako daganan sai tabi Saleema su Tafi bikin Murna ta kama Malika har Sai da tayi tsalle ta Rumgumeshi tana Murna,gari na wayewa,koda 11 tayi tayi musu Abuja dama already ta kira Saleema tace ta jirata gatanan Zuwa tana Zuwa basu tsaya Ba,Direba ya kwashesu Zuwa kano,Ayda ne ta tsaya wajen Ummi da Babanta,Merry kadai Malika tataho da ita,saboda Kula dasu Aryan,Dose kuma an barta Wajen Ummi.

Koda Su Malika suka Isa gidan Su Zahra,Hatta da Momi tayi murnan ganinsu,balle ma Da Malika ta bata 50k Gudummuwar biki,tayi ta mata godiya  Sosai ballatana Zahra da Nadira Wadanda suka Rasa ina zasu sakasu saboda Murna da Farinciki kamar yadda Saleema ke Fama da ciki Haka Nadira ke Fama dashi Haihuwa yau ko gobe,Zahta tayi kyau Sosai in ka kalleta baka kirata bazawara ba,Saboda tana kyan jiki,kuma batataba Haihuwa ba,La”asar nayi aka kai amarya gidan Ya Nadir dake kusa da asibitin Murtala,tare ya Hadasu da matarsu,Zahra tasha Fada da Nasihan Hakuri da juriya,Zafin kishi kuwa Tunkafin wani yayi Mata Fada Duniya tayi mata,shiyasa yanzu taWatsar da komai ta kama Allah ta Shiga da Zuciya daya cike da alheri.

.

Su Malika basu samu dawowa Aranar ba sai washegari Saboda Dare yayi musu Gidan Nadira suka kwana,sai da Safe suka kamo hanyar Abuja bayan Sun Biya gidan,Zahra sun mata sallama suka Rabu cikin kararramawa da Farinciki,tare da alqawarin in Saleema ta Haihu zasu zo,suma sukace in Nadira ta sauka su Sanar dasu insha Allahu zasu zo.

Ranar da suka dawo sai yammah Suka Shigo shiyasa Su Malika basu koma katsina aranar ba Sai Washegari suka Wuce da Safe ita kuma Saleema jirgin yammah Tabi ta koma Don taso Sadiq ya barta ta zauna Har ta haihu ya nuna bai yarda ba kamar ma ya nuna achan yakeso ta Haihu,Allah barshi sai aturo wacce zata zauna da ita,ammh Bashi da Ra”ayin Ta dawo gida wanka,Dole ta Hakura ta koma bayan Ummi ta bata bakin in Ta haihu ita zataje ta zauna mata,Hajiya tace gata itama zata Dole ne,jin haka shiyasa Saleema ta koma Cikin Farinciki.

____________________

*BAYAN SHEKARU GOMA DA SUKA GABATA*

…..”Ashekarun goman da Suka Wuce Rayuwa ta gangara yadda Allah (SWA) ya tsara Abubuwa dadama na Farincikin da akasinsa Sun Fara acikin Rayuwar Saleem da Malika,Na akasin Farincikin Shine Shekaru biyar da  suka Wuce Sukayi Rashin Hajiya Babba Wacce Ta Rigamu gidan gaskiya Sai Fatan Allah ya jikanta da Rahma,mutuwar Data girgiza Iyalan Kumo gabadaya Saboda yadda Hajiya Babba take awajensu,ammh kuma basu yarda zasuyi Mutuwa tana kan Kowa muma ita muke jira.

Ababen Farincikin da suka Faru kuwa,Shine Shekaran daya Gabata  IG KABIR KUMO yayi Ritaya daga aikin yan Sanda,wannan Dalilin hakane bayan an samu chanjin gwannati aka Tsaga sunan SALEEM KABIR KUMO amtsayin IG Na kasa gabadaya,wanda Dama kafin lokacin yayi ya samu karin Girma yana mtsayin AIG ne.

  Rayuwa tayi kyau Fiye da Zaton mai karatu inda Zuru”a suka cika gidan Kabir kumo wanda Suke nan Zaune har yanzu agarin Abuja,Suko su Malika Sun baro katsina Suna Zaune a wani makeken gidan Da Saleem ya Siya Mai kama da aljannar Duniya,bayan Ayda da  Ayyan Takara Haihuwan Mata biyu Maza biyu,Ya”yanta Bakwai kenan,inda take da Saleema da Marwan,sai Abubakar Da Maryama,Ayayinda itama Saleema take da ya”aya biyar Cif Duka mata,Hamdiya,Hamida,Hafsart,Hadiya,Aneesa,Ya marwan ma Tuni ya”ya Sun lullubeshi shi da Joda ,ammh sukan suna Tsara haihuwan ne,Ya’yansu Uku Saleem,sai Saleema,sai Fatima wacce suke kira Ummi kenan.Ayanzu haka Sunbar lagos sun Dawo partacourt da zama Sakamakon Chanjin wajen aiki da ya marwan ya samu hakama Sadiq suma yanzu su suka koma lagos da zama sakamakon Shima ya samu karin girma Zuwa DCG,Sun tattara sun koma chan,sai dai duk bayan Wata uku suna kokarin Zuwa Abuja Hutu domin Ganin iyayen nasu da kuma Sauran yan”uwa.

 Abbi Da Ummi sun Fara manyanta Duk da Kudi da Hutu Suna Boye manyantansu nasu,ammh sun Kara manyata Sosai Saboda Shekaru yaja,ita kanta Ummi tayi Ritaya daga aikin lauyan datake yi saboda Shekaru Sunja kuma Jiki yayi Nauyi,Ganin yanzu Ummi ta Manyanta Shiyasa Suka sama mata masu kyau har Biyu wadanda zasu rinka Taimakamata,Ya”yansu suna kula dasu sosai musamman ma Saleem da Malika Wadanda ke kusa dasu,Kafin Rasuwar Hajiya Sai da Sukaje kasa mai tsarki dukkansu,ahalin wanda Malika ta biya musu Dukkansu sukaje kasa mai Tsarki suka sauke Farali,ita ko da Saleem da ya”yansu basu san adadin Hajji da Umuransu ba,saboda sun mai dashi kamar zuwa Abuja daga Kano ne

Hajiya Malika Wacce ke Amsa mtsayin Malika Abdulmalik Dankasuwa,ada Sunan Mahaifinta ne yake yawo Aduniya amtsayin Wanda ya Mallaki Dukiya mai yawa,ammh Zuwa wannan Lokacin Sunan Malika ne ke yawo a ko”ina Domin ta Samu Cigaban kasuwancinta Sosai,kuma da Taimakon Mijinta ta Maida hannayen Jarin Dukiyarta Zuwa kasashen ketare,Malika tayi kyau sosai Fiye da Tunanin mai karatu ta kera jiragen sama Sunfi guda goma,ta kire Jiragen kasa,suma ba adadi bayan Ta bude Wani kamfani a kasar America,na Kera motoci wanda da Farko hannu jari ta Hada dasu sai kuma Daga baya ta Siya wajen ya zama mallakinta,agida Nageria ta Budema Matasa Shaguna Kala kala domin Dogaro da kai,Riba kadai zaka bata awata sauran Kudin nakane,Malika ta abude Gidan Marayu agarin Malumfashi da kumo,wanda ke amsa Sunan *MALIKA ABDULMALIK ORPHANS* Bayan haka kuma ta na da Kungoyoyi na Taimakon al”ummah mussaman ma ya”ya mata marasa galihu expecially Kungiyarta na MALIKA MALIK FOUNDATION kungiyace data ke Taimakon Mata da kananan yara,wadanda basu da iyaye ko kuma iyayensu basu da karfin da zasu dau Dawainiyarsu ta bangaren karatu da Sauransu akallah ta Dauki Nauyin karatun yara mata da maza Wadanda batasan iyakarsu ba,ta Fita da wasu kasashen wajen wanda suma bata san iyakarsu ba,tana  DA office akaduna da Abuja,Tana da ma”aikatan na kusa da ita kamar Joda da Su Saleema Harta su Nadira da Zahra bata barsu ba,ta basu Mikamai acikin wannan kungiyar nata Suna taimakamata da abubuwa dadama,in wani Abu yataso zasu kirata Su Tattauna,duk da yanzu Dukkansu sun zama manya mata domin Nadira ma ya”yanta Biyar,sai Zahra dake da Hudu aciki harda takwaran Malika,harta Saleem din yanzu ya yarda komai an Dawo ana zumunci an zama Daya.

 Malika bata Shiga Siyasa ba ammh an Sha kawo mata tayin haka,kawayenta yanzu sune Matan Manyan Sojiji,da matan Sarakuna kowani yanki tare da Matar Shugaban,kasa da Matan Ministoci Duk da su suke Shige mata ganinta Macece da bata da kyashi ko kadan,itako tasan zaman data take da kowa,Lbrinta Babu inda bai Tsaga ba ko”ina afalin Kasar Nageria da ketare ba gidan Tibi da jaridan da bata hira da ita,ba gidan Radion da bai gayyaceta yayi Hira da ita ba,duk kuma wannan Abun bai samu ba sai da goyon bayan gwarzonta kuma bangonta Mijinta Uban ya”yanta Wato *SALEEM KABIR KUMO* Domin Shi ya bata duk wata dama na yarda zata Gudanar da Rayuwarta ta Hanyar Taimakon mutane da Dukiyar da Allah y bata,duk inda aka gayyaceta wani taro baya haufin barinta Tunda zatayi Shiganta na Mutumci taje,ya”ya kuwa Ayda tana Wajen Saleema Domin Malika ta cika alkawari ta bata,Su Aryan kuma suna gidan su Ummi,sai su Maryam wacce Suke kira Hajiya da Abubakar Wanda Suke kira Sadiq,sai Saleema Ummita,sai Marwan da Suke kira Khalipa,Su kadai ne yanzu agida Agabanta suma din sun girma ba yara bane,sun iya kula da kansu musamman ma Ummita da Sadiq Tunda Sune manya,Mijinta kuma bata iya hadashi da kowa matukar Suna gida Dukkansu to kashe wayarta take,musamman ma Ranar Weeked dukkansu basu Fita ko”ina sai dai in Wani kiran gaggawa ne ya taso,suna Makale da juna suna kara jadaddama Juna irin son da kowanne yakema Dan”uwansa.

Merry da Dose dukkansu sun Musulunta Merry ta koma maryam ita kuma Dose tace ita Sunan Madam take so Malika,ganin ko sun koma garinsu Danginsu Bazasu Amshesu ba yasa Saleem da Malika suke Rikesu tamkar ya”ya yanzu Haka dukkansu Sunyi Aure,ammh Maryam merry tana nan Tare dasu don mai kula da Gidan Gonar Saleem take Aure,suna zaune agida daya,wani lokacin in Duka iyayen basu nan,shashenta su Ummita ke Zuwa ta kula dasu har iyayen nasu Su dawo duk da Sun Dauko goggo Hadiza tana zaune dasu,in ma anyi Hutu kenan in ko Lokacin mkranta ne dukkansu Mkrantan kwana Sukeyi nan Nagerian Turkish acdmey,ita kuma Dose Malika tana kaduna tana Auren Wani Matashi suna daga cikin Wadanda Malika tabama Jari domin dogaro da kai.

 Malika ta Waiwayi Dangin Mahaifiyarta Dga Baya Tafiyar Datayi Shi Tare da rakiyar Mijinta Da Duka ya”yanta har Zuwa birin England,koda taje yawancin dangin Maman nata Duk Sun kare,saboda dama basu da yawa wanda suka rage kuma talauci da Taufa sun Rikitasu sosai,Dakyar ma wasu suka gane Malika Diyar Juliyat ne,suka Rumgumeta Suna kukan Murna,Malika tayi takaichi mai girma na yarda ta Fito daga wannan Tsatson ammh kuma bata da yarda zatayi wannan Shine zanen kadaddaranta,Sati daya sukayi kafin su dawo gida bayan ta cikasu da kudi Sosai da duk Abunda kowa Zai Bukata,kafin su taho da yawansu an samu Wadanda suka karbi Musulunci,Wasu anan ta barsu,wasu kuma ta taho dasu ta basu wajen Zama da aikin yi.Sai gashi Malika ta zama Abun alfaharin kowa,kowa na so yaji wani yace yana da alaqa da ita,kuma kowa na jin dama matar dana ne ko kuma dama kawar yata ce,saboda kyawawan Dabi”unta da kuma Yadda take kokarin Taimakon addininta da kuma Talakawanmu marasa karfi.

 ****************

 “”Yau din takama Weeked ne Ranar Sunday kenan,gashi suna cikin Hutu ne dagasu har yaran,Tun jiya da Daddare da suka dawo Daga kano,wajen Taron Na Malika malik Foundation inda ta gudanar da Bada Kudaden da za”a ma yara yanmata guda Hamsin kayan daki wadanda zasu aure ammh iyayensu basu da Hali sosai Shiyasa kwamitin kungiyar ta jahar kano Ta nemi data Taimakamusu,wannnan Shine Dalilin Zuwanta Kuma Alhamdulillah Ta taimaka Daidai gwargwardo,duk inda taje bata kwana Koman dare zata dawo,shima Saleem din bayanan ajiyan sunyi Taro Afadar Shugaban kasa,shima sai dare ya dawo Dukkansu Tunda suka kwanta sai barcin gajiya Dakyar suka iya tashi Sukayi sallar asuba suka koma suka kamkame juna suna cigaba da barcin gajiya.

Ummita da Sadiq Tun daren Jiya suka Hada kayansu Tsaf sukace wannan Hutun Sufa gidan Goggo Saleema zasuyi shi,su kuma hajiya da Khalipa suka ce ada sunzo zuwa gidan Ummi ammh Tunda su Yaya aryan na chan sun Fasa,yanzu Gidan Dadddi zasu je su gama Hutunsu achan,tunkafin Ranar suka Shaidama iyayen nasu ammh sai sukace su bari Weeked sai su Tafi,ammh gashi Weeked tayi Dukkansu basu Wuni agida ba,ga yau ma tayi ammh dukkansu babu Wanda ya Sauko kasa.

 Tun Karfe 8 na Safe suka Shirya kowanne ya jayo Trolley dinsa ya kame kan Kujera suna Jiran saukowan Iyayen nasu,kowanne ya kurama upstair ido yaga ta ina zasu bullo,Da ka kalli Fuskarsu zasu tabbatar da Ransu bace yake,gashi Tarbiyan da iyayen suka basu babu ta Shiga musu dakin barci indai basu tashi ba,Baba Larai mai aiki wacce Suka daukota daga Kumo tayi tayi suzo su karya kowanne ya Tura baki yana Fadin”Am ok..”Dayake yaran Sun taso cikin Tarbiyan iyayensu  suna da girmama na gaba dasu,sannan Saboda yadda bakinsu ya saba ko”ina sukaje ba kasafai suke mgana da Hausa ba,sunfi saka yaren Turanci abakinsu ta wani bangaren kuma suna jin larabci sosai saboda Abbansu ya iya Shiyake koya musu,balle kuma Malaminsu wanda ke koya musu karatu bayan sun Dawo Hutu Mallam Usman baya musu mgana cikin harshen Hausa Shiyasa suka iya,duk bangaren Daka tabosu basu da wasa.

goggo Hadiza ta kalli Ummita tana Fadin”Ummita Wannan Hade Fuska kuma Duk tamana yaji ne..? Tura baki Ummita tayi tana Fadin”Goggo Hadiza ,Su Mommy fa sukaki Fitowa,Alhalin kuma mun Fada musu zamu Hutu yau gidan Goggo Saleema…”Sadiq ya karbe da Fadin”Eh wlh,kuma lagos ba kusa ba,Ni addu”ata Allah sa ko Daddy ne yafara Fitowa da Mommy  kunsanta in tayi Tafiya ta gaji bata Fitowa da Wuri.”Baki khalipa ya Tura kafin yace”Ni fa na gaji da zaman gidan Allah bai kawo Wani light.”Yafada yana Cije baki Hajiya ce karamarsu yar Shekara Shida tace”Nidai ina son zama da Mommy da Daddy muyi ta hira..”Harara Ummita ta sakarmata tana Fadin”Ji wannan,Yasin ki ma kama kanki don Daddy bayason Hira da kowa sai Mommy su kule suki Fitowa mu su barmu da game ko kallo,gwara muje Hutunmu mu hade da Ya Ayda ehyyyyr…”Tafada tana Ihun murna,Goggo Hadiza da Baba larai na musu Dariya.

 Hajiya tace”Toh zan biku gidan Goggo Saleema..”atare Ummita da Sadiq suka taso suna Zaro ido lokaci daya suka ce”Ina….?,Waza ki bi..? lalle ma yarinyarnan kima kama kanki Tun Wuri don Wlh bazaki bimu ba,tabdijam ki Wuce kibi Khalipa gidan Daddi..”Jin haka yasa Hajiya ta bare baki ta saki Kuka harda buga kafa,Suko mai zasu yi banda Mata Dariya itako tana kukan Wlh sai ta bisu Gidan Goggo Saleema.

 Daga chan Sama Sukaji muryan Daddynsu yana Fadin”A”a Wa Yatabamin Hajiya da Safen Farin haka.?.”Dukkansu suka Kurama inda sukaji muryan Daddynsu ido,Dan matashin Dattaji ne yana Sanye da Jallabiya Mai Ruwan Toka,Idanuwansa suna lullube da Farin glass mai kara karfin gani,Kallon Farko zakama Saleem lokaci daya zaka Fahimci yafara zama Dattijo,domin har Farin gashi yafara bayyana a kansa,duk da Halittace dan kimamin Shekaru 50 aduniya ne ayanzu Bai kara kiba ba,sai sai yakara Murjewa da Kuma kara haske Saboda Hutu da kuma karin Jin Dadi.

Hannunsa na Sarke cikin na Malika Wacce ke Sanye da Wata abaya Doguwar Riga kirar Armani,Ta yane kanta da Wani jan Vail domin kwalliyan adon Kayan Red colour ne,Kyakywan Fuskarta wacce bata bayyana alamun Tsufa ta bayyana Sosai masu jere da Hakoran makka guda biyu,wanda suka karamata kyau,duk da Shekaru sun ja,ammh bazaka taba ganewa ba,saboda Hutu da jin dadi sun boye hakan sai dai zaka Fahimta da yanayinta Tunda ai jiya ba yau ba,

 Da gudu Hajiya ta ruga ta Rumgume iyayen nata dake kokarin Saukowa daga Steps,cikin hanzari Saleem ya Saki Hannun Malika ya Daga Hajiya Sama yana Fadin”Waya taba min ke..? gayamin yanzu na masa bulala..? Kwabe Fuska tayi tana kara Rufe ido Tace”Ba su Ya Ummita ba ne,da ya Sadiq bane suka ce bazasu dani gidan Goggo Saleema ba..”Tafada Tana kara Saka kuka,Dariya ta kama Malika tasa hannu ta karbi Hajiya suna karisawa saukowa daga Steps take Fadin”Wa ya isa..? Manta dasu ke kadai ma zaki Hutu wannan karon..”Tafada tana Dagama Ummita gira wanda suka kara Hade rai jin Abunda Momy tace.

 

 Goggo Hadiza sai dariya take Ganin yadda yaran suka kara Hade rai Suna kunkuni,suko iyayen nasu namusu Dariya ganin yadda sukayi ne yasa Hajiya dake hannun Malika ta hau ti musu gwalo,Zuciya ta Ciyo Ummita ta mike tana Hararanta,Saleem ne ya Daga mata hannu yana Fadin”Hy duk wannan Bata Fuska da Fushin na miye ne Ummitan Daddy..? Goggo Hadiza ce tace”Fushinku ne,nan fa duk jiran saukowanku Suke sun Shirya tsab yau sai Tafiya Hutu..”Sai lokacin suka Lura da manyan akwatun nasu dake Tsaye awajen Baki Saleem ya kama yana kallon Malika kafin su Gimtse dariyansu,Saleem ne ya zauna tsakanin Ummita da Sadiq ita kuma Malika ta zauna gefen Khalipa suka sanya ya”yansu atsakiya,Saleem ne yace”Duk ku tsaya yanzu kowa ya Fadi inda yake son Zuwa Hutu. “Da hanzari Ummita tace”Daddy ni da Sadiq Wajen Goggo Saleema zamu Hutu wannan karon mun barma su Ya aryan gidan Abbi..”Dariya yayi kafin ya kalli Khalipa yana Fadin”Babban yaya kai ina zaka..? Mirmishi yayi yana Fadin”Daddy gidan Daddi na zani nidai kasan bana chanji gidan Hutu..”Kansa ya Shafa yana Fadin”God boy,dama Ai Shima takwaran naka sonkai yake Nunawa,yafi son Zuwanka Fiye dana kowa..”Malika ne tace”Hajajju ke ina zaki Hutu ko zaki zauna damu..”Saurin girgiza kai tayi tana Fadin”No Momy gidan Goggo Saleema zani..”Da Sauri Ummita ta zaburo zatayi mgana Saleem ya dakatar da ita ta hanyar Rike ta yana Fadin”Ke wlh kin gado mai Sunanki sam baki da Hakuri..”Yafada yana Dungure mata kai,Kwabe Fuska tayi ta koma tana Hararan Hajiya,Malika ne tace”Toh Duk ku tsaya naga duk kuna Neman guduwa ne bamai tsayawa Wajen Goggo balle Wajen Anty Marym..”Dukkansu suka cuno baki suna bazasu tsaya ba,goggo Hadiza na Dariya tace”Allah Raka taki gona nima wlh na gaji da ku ku kara gaba gida yamana Shuru..”Malika Ta murmusa tana Fadin”Kyelesu goggo ai ke dama Uwar Malika ce,kinga duk zumudin nan da Sukeyi gidan Ummi zasu ci burgi don Jiya da daddare duka Daga gidan Goggo Saleeman har Gidan Daddi Marwan din Sun sauka gidan Ummi..”Jin haka yasa suka saka ihun murna Suna Fadin”Da gaske Mommy..”aiko amsa bata basu ba Suka mike kowanne ya Dauki akwatinsa suka Bi hanyar Fita suna Fadin”Daddy,mommy goggo,Mun tafi gidan Ummi,Achan zamu yi Hutunmu sai kunzo..”Suka Fada Suna Ficewa Harda Hajiya wacce ta Tashi Daga Hannun Malika ta bisu da gudu,Iyayen nasu suka bisu da kallon Sha”awa da kauna,Waje sukayi Dole Direba ya kwashesu amota Zuwa Gidan Ummi don sun matsu suga yan”uwan nasu musamman ma Ya Ayda Wacce ke Nesa,gwamma Su Ya aryan suna ganinsu in sunje Gidan Ummi ko kuma In su sunzo gidansu Duk da ba kasafai suke Zuwa ba.

 Da mirmishi afuskar Saleem ya Waigo yana Kallon Goggo Hadiza yake Fadin”Goggo ki Shirya in mun karya zamu Wuce gidan Ummi..”Mikewa tayi tana Fadin”Tohm bari na Hanzarta ai yan Wutar ciki Sun tafi Su..”Tafada Tana Dariya.

 Sai da ta Fita Afalon kana Saleem ya Manno Malika da jikinsa yana Shinshinar Wuyanta lokaci daya yana Shafa maranta Zuwa Cikinta,Dariya tayi tana Danna kanta bisa kirjinsa cikin Wani yanayi tace”Mallam,meka ke Bukata ne..”Akunne yayi mata Rada..”Ciki nake so nayi miki..”Ido ta zaro ta dago tana kallonsa cikin Mamaki tace”Ciki wani iri..?Kumatunta ya Shafa yana Fadin”Cikin Haihuwa mana Amanata,Hutun ai ya isa haka yakamata ama Hajiya kani ko kanwa..”Yamutsa fuska Malika tayi tana Fadin”Haba Daddy wani irin ciki kuma Ai ni gama kuma..”Wani kallo yayi mata kafin yace”Ko..? Saboda kinga na daga miki kafa kwana biyu ko..? Bari na Nuna miki har yau ina nan da karfina Insha Allahu kafin mu Tafi gidan Ummi yau sai nayi ajiya acikinki..”Yafada yana Kallonta ido cikin ido,Kwabe Fuska tayi zatayi kuka kawai taji bakinsa cikin nata,yana kissing dinta cike da kwarewa,itama Tallabeshi tayi Tana bashi Hadin kai,sai da yagaji don kanshi ya saketa yana Ajiyar Zuciya Kura ma juna ido Sukayi kafin Malika tayi Lum da ido ta koma Bisa kirjinsa tana Fadin” _Ina alfahari dakai Mijina…A komai na Malika malika kaci gaba da Ramuwa Har Abada.._…

 Dariya ya saki yana Sumbatar Saman kanta Kafin ya Mike ya Dauketa Cak ya Fara Tafiya da ita Zuwa sama inda Master Bedroom dinsu yake,Kallon Cikinta idonta yake yana Fadin” _*MALIKA MALIK SAI NA RAMA…Ammh bana Ramuwar da yawa Saboda Wani lokacin in Na rama ni nake Ramewa..*_  Dariya ta kyalkyalece mai dashi shima yana Tayata ahaka suka isa cikin makeken dakinsu da kafa ya Bude kofar suka ci burgi bisa Makeken gadonsu Cike da Kauna da Muradi mai girma Suke Gudanar da komai har abada bazasu gaji da juna ba,Kowani lokaci suka kebe kowannensu yana kokarin Farantama Dan”uwansa ne,wannan itace Kauna ta Gaskiya wacce ko man Tsufa bata yankewa har Gaban Abada.

 *TAMMAT BIHAMDULLAH*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE