MALIKA MALIK CHAPTER 4 BY JANAFTY

MALIKA MALIK CHAPTER 4 BY JANAFTY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

“”Washegari da misalin karfe 10 da wani Abu na Safe Saleem yadau hanyar katsina bayan ya kira Abbi yasanar dashi,shikuma yakira Alhaji Abdulmalik ya sanar dashi ga saleem nan zuwa.

Shi ya tuka kansa,shiyasa  ya isa akan lokaci domin dama Saleem akwai gudu amota kamar zai tashi sama,koda ya shiga cikin garin katsina bai sha wahalan gane gidan ba,sakamakon gidan Alhaji Abdulmalik Dankasuwa ba boyayye bane a katsina,cikin lokaci sai ga motarsa ta tsaya abakin makeken gidan,wanda yake kama da wata al’karya guda.

Hon ya zuba Kafin megadi ya leko yana Tambayansa sunansa kai tsaye yace”Saleem kabir kumo…”Bai yi watawata ba ya wangalemai kofar get din motarsa kirar 4matic ta sulala ciki domin dama Tuni an san da zuwanshi.

Aparking space ya Faka motarsa kafin ya Fito yana bin haraban gidan da kallo,wanda wasu tafka tafka motoci iya kallon ka mallam,sukama gidan kwanya gefe daya kuma excorts din Malika keta zagaye suna wani Mazurai Dan ware ido yayi yana bin benen gidan da kallo yana jinjinama fasahar bazanin da maginin harda wanda aljihunsa yayi kuka,domin duk Abunda yake zato,toh ya ganshi Fiye da Tunaninsa.

Komawa yayi ya jingina da motarsa Yana wasa da key din motarsa,sanye yake da Shadda mai Ruwan kasa wacce taji yarari da maiko,dinki tazarce ne yayi matukar amsansa,gefe daya kuma ya dora wata hula zanna bukar itama mai alaman zanen Ruwan kasa,hannunsa sanye da agogon Fata na kamfanin Rado,shima mai kalan Ruwan kasa,bayan takalminsa shima Rufaffafe ne na Fatar damisa,shima kalan Ruwan kasa,kallo daya zakamai kaji kakasa kara kallonsa saboda yadda kwarjinsa da haibansa ke tasiri a idon wanda ya kallesa 

mace kuwa komin Girmanta da ajinta,da isarta da takamarta da duk Abunda take takama dashi,in ta kalli saleem sai taji ta raina kanta da duk Abunda ta mallaka.

Bai Dade da tsayuwa ba,yaji muryan wata mace cikin hadadden Turanci wanda dagajinsa kasan mutum ba haye yayi ba,ya kware ne,daga gefensa kamar bazai daga  kai ba,sai yadaga idonsa ya Fada kan Malika wacce ke Tahowa daga bayan gidan Daga ita sai wani karamin mini sikat,da wata riga kai breziya ce ma,domin banda kokon nono bata tare komai ba gashin kanta ajike yake da karamin Towel akanta tana gogewa da hannu daya,dayan hannu kuma tana mgana awaya,fararen kafafunta da cinyoyinta awaje suna kyalli,bayan kafarta na sanye da wani Takami flat mai taushi.

Bayanta Merry ne da Dose,merry na Rike da robar Ruwansha,ita kuma Dose tana rike da wani karamin Towel din,dukkansu suna biye da ita kamar rakumi da akala,bai gama mamaki ba sai da yaga tabiyo ta gabanshi cikin wannan banzar Shiga ko ajikinta ta kuma ratsa ma,’aikatan gidan,wadanda suka kame mata kamar wata matar Shugaban kasa,Bayanta yabi da kallon Tir,yana jin wani takaichi aransa ganin yadda gabadaya idon kardawan arnan  samudawan ke kan Hips dinta wanda ke Juyawa kamar wanda ake controle dinsu.

Saurin Kauda kai yayi yana kiran Sunan Allah,wani Siririn tsaki yaja yana Fadin”Lalle yarinyarnan ta Wuce da Tunanina,ashe tsinanniyace ta karshe bansani ba….’Yafada yana rike haba,yana bin Kofar data bi da kallo,Bai gama mamaki ba,sai ga Alhaji Abdulmalik ya Fito da hanzari cikin Fararen kaya yana saba babban Riga ya kariso wajen Saleem yana Fadin”Am srry na barka awaje ko..?

Yafada yana kokarin mikasa hannu ammh sai Saleem yaki bashi hannu sai ya rankwafa yana Fadin”Ina Wuni Daddy…”Yafada yana sadda kai,Dagosa Daddy yayi yana Fadin”Ash Tashi Tashi mana,Saleem ko..’,?Yafada cikin Fara”a,

Gyada kai Saleem yayi yana Sadda kai,kafadansa Ya kama yana Fadin”Masha Allah…”Yana kallonsa murna da Farinciki sun cikashi ganin Saleem amtsayin Surikinsa koshi dayake Namiji kwarjinsa ya dakesa sosai,Yana Rike dashi Har zuwa Babban Falonshi na saukan baki,ya zaunar dashi bisa kujera,wanda Saleem din yayi saurin zamowa kasa yana dukar dakai.

Yar Dariya Daddy yayi yana Fadin”A”a Haba Saleem,maza tashi ka zauna da kyau nan ma fa gidanku ne,nima Abbanka ne ko Kumo bai sanar dakai bane..?”Yana duke ya murmusa yana Fadin”Ya sanar dani Daddy kayi hakuri kabarni anan…”Dariyan Farinciki Daddy yayi yana Fadin”Toh indai ka dauke ni a mtsayin Daddynka toh na baka Umarnin katashi ka koma bisa kujera kaji..”ba yadda ya iya,sai tashi ya koma bisa kujeran yana Kallon Cafet din daya karama Falon kyau.

Kallonsa Daddy yake ransa na Fari,Aransa yana ta Fadin masha Allah,waya ya daga ya kira Hajiya binta yace akawoma Bako Ruwa da lemo,ai ba’a dauki muntuna ba,sai ga Atika da Tire niki niki da lemuka da Ruwa ta ijiye gaban Saleem bayan ta duka ta gaisheshi,ya amsa bai kalli ma inda take ba idonsa na kasa.

Mikewa Daddy yayi yana Fadin”Bari na barka kasha Ruwa ka huta kafin nazo muyi mgana ko..? Mirmishi Saleem yayi baice komai ba har Dadddy ya Fice daga Falon jikinsa na rawa,Da kallo mai kama da harara Saleem ya bisa kafin ya saka hannu ya dauki Ruwan swan ya tsiyaya akofi yasha,Ajiyewa yayi yana sakin ajiyar zuciya Lokaci daya yana bin Falon da kallo Yana mele baki 

Bai jima ba,sai ga Daddy ya dawo yana ganinsa yayi kasa da kai kamar wani na gari,nan ko zaginsa kawai yake aransa,domin hardashi abada Gudummuwar Wulakancin da Malika tayimai,kusa dashi Daddy ya zauna yana Dafa kafadansa kai tsaye yace”Sannu da zuwa,hop kazo lafiya..?

Saleem ya amsa da cewa”Alhamdulillah..”Alhaji Abdulmalik yace”Masha Allah nasan dai mahaifinka ya sanar dakai komai ko..”,?Gyada mai kai kawai Saleem yayi,kafin ya cigaba da Fadin”Toh naji dadin hakan,yanzu Abunda nakeso dakai kamar yaushe ne kake bukatar ayi auren …?

Saleem yaji ransa Fes,ammh sai ya basar yana Kara sadda kai yace”Daddy duk yadda kuka tsara ni awajena Daidai ne..”girgizamai kai Daddy yayi kafin yace”A”a ba ahaka Saleem ai kaine zaka zauna da ita,kai ya kamata ka sanar damu zuwa yaushe kakeson ayi komai agama..”Shuru yayi kafin yace”nan da Wata daya yayi Ko…,?

Daddy yace”Yayi sosai ma,Allah ya nunamana yanzu kana wani aiki ne…? Saleem yace”Ina aiki a zamfara ne,karkashin wata headquter,a mtsayin Acp…”Washe baki Daddy yayi yana buga kafadansa yake Fadin”Wow Bravo…Ashe magajinn kumo ne,gaskiya am so happy to hear dat,Allah ya taimaka..”Yana mirmishi ya amsa da Ameen.

Gyara zama yayi yana Fadin”Kana da muhallin ma”ana wajen da zaku zauna…? gyada kai Saleem yayi kafin yace”Eh inada dan madaidaicin gida anan zamfaran…”Shuru Daddy yayi kafin yace”Toh babu laifi,ammh akwai Abunda nakeso na sanar dakai,bawai don zaka auri yata ba A”a don kaima kana mtsayin Dana ne ko ba malika zaka aura ba,zan maka dukkan Abunda yakamata..”

Saleem ya jinjina kai yana Fadin”Hakane Daddy…”Yace “Toh Abu na Farko Shine bani son ka kashe sisinka amganar auren nan bayan sadaki,duk wani Abun bukata,kama daga lefe da gidan da zaku zauna duk zan tanadar muku kaji..”Mirmishi Saleem yayi kafin yace”Ayi haka Daddy…’Kafadansa ya dafa yana Fadin”Karka damu Dukkanku ya”ya ne,so yanzu sauran mganr zamu tattauna da mahaifinka kaji ko,Allah yayi maka albarka yakuma baku zaman lafiya..”Afili ya amsa da Ameen ammh cikin ransa ba Ameen ba yake fadi  ba,yana ayyana yadda rayuwarsa zata Cutu matukar Allah yabasu zaman lafiya da wanchan tantiriyar yar iskan.

Mikewa Daddy yayi yana Fadin”Yanzu zaka Wuce ne,ko akirama ita ku gaisa ne?.”(Shima dai kawai ya Fadane kada Saleem din yagano ita malikar bata sani ba…) Saurin Girgiza kai saleem yayi yana mikewa yace”A”a Daddy rabu da ita,zan dawo insha Allahu,yanzu ma ina Sauri ne aiki yayiman yawa a office ni zan koma…”Daddy yace”Haba ka tsaya kayi lunch mana!Saurin girgiza kai yayi yana Fadin”ngd daddy…”

Bai hanashi ba illah Shiga ciki dayayi ya kira Hajiya binta suka gaisa,wanda itama ta yaba da Saleem din,kuma aranta tana ganin Malika ta samu daidai da ita,har bakin mota Daddy ya rakasa yabashi rafar kudi yan Dubu ammh Saleem yaki karba sai da yaga ya nuna baiji dadi ba kana ya karba,har ya Fice daga gidan yana dagamai hannu da Fatan Allah ya kaishi lafiya.

Saleem na tuki yana cin dariyan Ladabin karyan dayayima su Alhaji Abdulmalik,domin harga Allah baya wani ganin mutumcinsa,kawai yana mai na yan Duniya ne,ammh ina Abun girmawa anan wajen,yana babba ammh sam baida Tunani yabar yarinya na Abunda taga dama,ammh no wahala karshenta ya kusa zuwa,domin dama yace wata daya ne don ayi komai a Wuce wajen,Yaci burin yadda Adare daya malika ta chanzamai rayuwa,shima yayi al”kwarin chanzamata shi awannin goma ne bama sai an kai ga cikar dare ba,kudin daya bashi yake kallo yana harara,yana fadi afili,”Dole mana kabani kudi,Tunda za”a Tusa min Ragowar arna,yaga yaro shar zai makalamin tsohuwa,yo tsohuwa man wanda naba shekara daya,ai ta tsufa…”yafada yana sakin tsaki yana cigaba da hararan kudin kamar sune Alhaji Abdulmalik din.

   *****************

Saleem bai kira Abbi ya sanar dashi Abunda ya wakana tsakaninshi da Alhaji Abdulmalik dan kasuwa ba,shi da kanshi ya kira Abbi ya sanar dashi komai kuma yana kara yabawa da Saleem din,Ada Abbi yaso yayi Turjiya game da Cewar dayayi sadaki kadai yake bukata,ammh sai shi Alhaji Abdulmalik Dankasuwa ya nuna daga Saleem din har Malika shi uba yake garesu,saboda yana da hakkin yimusu dukkan Abunda ya kamata,nan yake sanar dashi ya tsaida mganar auren nan da wata daya,.

Abbi yaji dadin karamcin Alhaji Abdulmalik har ya nuna yana so yan”uwanshi baffanninshi da suka rage akumo zasu agabatar da neman aure,Alhaji Abdulmalik ya dakatar dashi da cewa basai sun zo ba ai duk Abun  na gida ne,su bari Ranar daurin Aure sai suzo tare da Sadaki,babu komai shi ya riga yaba saleem malika har Abada,da wannan mganar sukayi sallama cike da Farinciki.

Abbi baya da zabi illah sanar dasu Ummi halin da’a ake ciki,wanda Hajiya ce kadai ta nuna murnanta Afili ,ammh Saleema da Ummi Kamar su fasa ihu saboda bakinciki,Saleema ta bude baki tana Fadin”Haba Abbi yanzu Fisabillahi in yaya Saleem baida hankali da Tunani sai ka biyemai,yanzu don Allah duk matan Duniya yarasa wazai aura sai Wannan yar iskar…?

Tafada idonta cike da kwallah,hararanta Abbi yayi yana Fadin”Kul na sakejin kina kiranta yar iska,iskancin me tayi miki toh zan sabama miki wlh in bazakima dan”uwanki Fatan alheri ba juz keep ur mouth shout tunkafin na saba miki wawiya kawai…”,Yafada cikin Fushi.

Saurin mikewa tayi tana kuka ta Wuce zuwa dakinta,Ummi dake zaune batace komai ba,Hajiya ce ta kalli Abbi tana Fadin”Wai ni kabiru Meye dalilin da yaran nan basu son Auren nan,kodai ba diyar kirki bane…? Ummi tayi Saurin taran hajiya tana Fadin”Wlh bs diyar kwarai bace Hajiya,Yarinyar kwata kwata batayi kama da…”

“Aisha…..”Abbi ya katseta da tsawa yana kallonta,shuru tayi da bakinta tana Jin wani daci aranta,Bai kara mgana ba ya tashi ya haye sama ammh daga yanayin kallon da yayimata Jikinta yayi sanyi,tashi tayi tabi bayanshi batare data kara cema hajiya komai ba,.

Hajiya tabe baki tayi ta mike tana Fadin”Allah ya kyauta…”Daga haka ta shige dakinta Ranta fes Domin Dama babban burinta shine su Saleem suyi aure tagaji da ganinsu haka ba iyalai.

Shiko Abbi yana Shiga daki sai ga Ummi ta biyo bayansa tana Shigowa ya tasomata yana Fadin”Haba Aisha meyasa kike haka? ke yanzu Abunda kikayi Yayi kama da Abunda uwa tagari zata aikata,kada kimanta kema kinada Diya mace,in aka aibatata zaki ji dadi? kada ki manta Allah shi ke shirya wanda yaso ya batar da wanda yaso,nasan kuma kina da sani kan hakan bayan karatunki na Shari”a low kina da karatun Addini daidai gwargwardo,why kika aikata haka?

Yafada yana kallonta kur da ido ganin yadda jikinta yayi sanyi ne yasa ya juyamata baya yana Fadin”Kin bani mamaki Aisha,wlh ayadda na sanki mai hankali da hangen nesa banzata zaki ki bada goyon bayan Saleem yayi jihadi ba,baki Tunanin in ya aureta ya natsarta da ita,dani da ke dukkanmu munada lada? Gaskiya ban zan boye miki ba u already disoppoiting me Aisha…”

Yafada Yana jadda  kalamansa,Kukane ya kwacemata ta isa gareshi ta rumgumosa tana Fadin”Kayi hakuri yallabai,wlh nakasa sarrafa zuciyata ne na ganin Saleem ya auri yarinyar nan, da Duniya tagama saninta afannin rashin tarbiya da kamewa mezan cema yan’uwana da kawayena? wlh Abun kunya ne babban Amtsayinka na mai mutunci aji mun hada zuru”a dasu,sai ma afara zargin kila kwadayin Dukiyar mahaifinta ne ya Tsolemana ido…

Tana Fada tana Sheshshekan kuka waigowa yayi yana rikota gefen gado ya zaunar da ita yana Fadin”kalle ni nan Aisha..”kai tsaye ta dago tana kallonsa hannunsa ya mikamata ta kama kafin yace”Tun sanda kika zamo mata nake mika miki hannuwa na domin ki kama,yazama bango da majingini gareki,kuma har gobe zan cigaba da mikamiki ,Toh yau gashi na kara mika  ,mi ki ki kama ki damke yazama kariyarki har gobe kiyama ki kuma saka aranki indai Dan dani Kabir na haifa tare da Aisha ne bazai zamo gafalalle ba,sai da ikon Allah,na yarda da zencenki na za”a ce ko muna hangen Dukiyar mahaifinta ne,yes Alhaji Abdulmalik yana da tarin Dukiyar da baisan yawanta da karshenta ba,ammh wlh tallahi Aisha Dukiyarsa bata taba tsolenmun ido ba,mena nema na rasa,akwai Abunda bazan iya mallaka bane anan Duniyan…?Babu shi to kisa aranki Da zuciya daya na yarda da wannan auren,ki kuma toshe kunnuwanki daga zencen mutane,dama wasunsu dayawa basu son akullah alheri,ki kuma yi kyakyawan zato ga Danki,kinsan Abunda zai aikata da wanda bazai aikata ba,don Allah ki Cire wannan Tunanin azuciyarki kisama auren nan albarka kuma ki Rufe kofar da wani zai kawo kushen wannan Auren don Allah….,”

Yafada yana kara damke hannunta hawaye ne suke shatatamata kawai sai tafada kan kafadansa tana Fadin”Na yarda kuma na saka musu albarka…Allah ya sanya alheri,ka yafemin yallabai,Akullum ina alfahari da samun miji gwarzo kamar ka,lokacin da na nemi kauce hanya sai kayi saurin dawo dani,Allah yabani ikon Yima biyayyah har karshen Numfashina,Allah kuma ya Shiryamana Zuru”a….”Da Ameen yayi ta karba bayan ya sanya hannu yana Sharemata hawaye yake Fadin

“Toh bar kukan hakan,Fushi ya kare ko…”Yafada yana dariya Kirjinsa ta fada tana Rufe fuska wai ita kunya,yar dariya yayi yana Fadin”A’eesh dita har gobe bani da kamar  ki AISHATUL HUMAIRA…”Yafada yana Mata rada akunne,Rumgumeshi tayi itama tana mai rada akunni,nidai nayi waje Tunda dai naga ma”auranta sun daidata kansu dole na ja Siraran kafafuna zuwa waje😂

____________________

Tundaga Ranar Ummi ta fauwalama Allah komai ta karbi Auren saleem da hannu biyu,wanda harshi sai da takira tana mai Tsiyan yana Fushi da ita kwaso rantsuwa yayi yana bata hakuri,dariya kawai tayi tana sanyama auren albarka,aransa bai amsa da Ameen ba,don cewa yayi ai dama baki sakko ba Ummi,don ba auren gaske bane,na Ramuwa ne kawai na awannin kadan,ammh duk da haka bata makara ba😂

Saleema ko kwana uku takara takoma mkranta bayan taga gidan gabadaya anhada kai babu mai goyon  bayanta,Ummi ce toh itama yanzu tabi bayan mijinta,Hajiya kuwa batama sauraran mutum indai ta Fahimci zai kawo wata sukane game da auren Saleem,shiyasa ta tattarara kayanta Takoma mkranta,kuma tayi alqawarin ko bikin yatashi wlh bazata zo ba,indai da wannan Jinin Turawan ne.

Ita ta kira ya marwan ta sanar dashi,wanda yaji Abun kamar almara,nan da nan ya hau Shafin instergram,ya bude shafin Malik malik,nan yaga badala kala kala nata,Tunda abokan aikinsa sunsha Tuka jirgin data ke ciki ita da Amintattun Escorts dinta,ammh shi bai taba katari da shegiya ba,duk da yasan lbrinta ba boyayyiya bace,anan nema yake ganin Jiya da misalin karfe 2:00pm jirgin daya tashi daga Abuja zuwa Amurka tana ciki wai tatafi tarin karama yan kasuwa sani da Duniya gabadaya ta Shirya akasar ta Amurka,irin hotunan data daura da shigarta Abun ba kyan gani,nan da nan zuciya ta debi Marwan ya daga waya ya kira Ummi yana Kumfan baki tana gani Saleem zai auri wannan Shegiyar yar iskan yarinyar.?

Ashe Abbi na kusa yako karbi wayar yayima Marwan din Fata fata daga karshe ya bishi da Nasiha mai kashe jiki,shima din jikinsa yayi sanyi Domin yasani Shi da Allah ya Shiryar dashi bayafi sonshi bane,haka Allah yake Abunshi shi zai raya wanda yaso,kuma ya kashe wanda yaso,shi zai Shiryar da wanda yaso,Allah shike da ikon Umartan Faruwan Abu nan take kuma ya Faru ko ya kasance,ya sanar dashi ko ya manta kissan Annabin Allah Annabi Yunus wanda yayi Fushi da mutanensa ya baro garinsu zaiyi hijira ya Shiga jirgi sai aka ga jirgi na tangal tangal,nan masu jirgin sukace akwai wanda yayima Allah laifi acikin Jirgin,nan suka ganoshi suka jefasa cikin kogin,shikuma Allah nan da nan ya Umarci Kifi data hadiyeshi,ya sanar dashi Allah yace acikin alqur”ani mai girma ba domin Annabi Yunus yanemi gafarar Allah ba da ya dauwama acikin cikin kifin nan har ranar tashin kiyama.

Hakuri yayi ta bama Abbi,domin Hakika duk Abunda ya Fada gaskiya ne, domin sau nawa zamu dunga aibata yan”uwanmu da jifansu da  munanan kalamai a maimakon murika musu Fatan Shiriya tunda munsan babu mai batarwa,kuma ya Shiryar sai Allah,kuma hadisi ne ingantattace sau tari Mutum zai Fara aiki irin na yan Aljannah sai yana gabda mutuwa aikinsa ya juye yakoma na yan Wuta kuma ya mutu ya shiga Wutan,ALLAH YA KAREMU…Kuma sau tarin mutum yana ta aiki irin nan yan Wuta kwatsam sai yakoma aikin yan aljannah,kuma ya mutu alokacin ,sai kuma ya Shiga Aljnanah,to mai zamu ce da haka? musani Aibata wani mumina ba dabi”a mai kyau bane.domin babu wanda yasan tsakanin Ubangiji da bawansa…

_Allah ka shiryemu kabamu ikon sarrafa zuciyarmu ta hanyar mai kyau_

Yana zaune cikin Office dinsa aiki ya kacame mai Sargent musa ya shigo agabansa ya tsaya hannunsa asaman kansa yana Fadin”Weldone sir….”

Bai dago ba ya amsa da cewa”Weldon..Arm ya”aka yi ne Sargent musa..? Baya yaja yana Fadin”Yallabai kayi bako ne,yana waje yana son ganinka,ya shigo ne..?”Shuru yayi kafin ya dago yana Fadin”Bako kuma? Who…? Sargent musa yace” I don”t know sir buh kamar naga na gida ne”Tsaki yaja kafin yace”Let him in,buh dagashi bazan kara ganin kowa ba gaskiya a hv alot to do,koda wani ne yazo yana son ganina matukar iz not imfortant,plz tell dem bani nan ok…”saramai yayi kafin yace “Yes Sir…” Ya Fice da Hanzari,shiko yamaida hankalinsa kan karamar syestem din dake gabansa wanda da alamu dai Abunda yake yaja ra”ayinsa.

Sargent musa bai dade da Fita ya Turo kofar office din ya Shigo yana kwarara sallama.”Assalamu Alaika…”Aka Fada ana yar dariya,Dago kansa yayi ya Jefa cikin na mai sallaman,kai tsaye bayan ya dauki hannunsa wanda ke rike da pen yana sosa gemunsa dashi yana kara kallonsa kasa kasa,shiko Sadiq dariya Abun ya bashi ammh sai ya doje, ya karisa yana Fadin

“Haba Friend kuma shikenan don kazama Mijin hajiya sai azubamu akwandon shara,kuma ma don katon Wulakanci bayan Rejecting din call dina dakakeyi na baro uzirin gabana nazo inda kake ba mirmishin maraba balle abani wajen zama, ko..? Yafada yana zama cikin daya daga cikin kujerun da suke Fuskar Saleem din.

Wani bad look yamasa kafin yace”Ammh wlh kai kam indai aka leqa Wuta baka to kila ka makaleni,😝gulma da munafunci suna cin gindinka shege Bawan mata kawai…”Dariya Sadiq ya sheke dashi yana Fadin”Uhum sai ba kai ba,wai meyasa kasama rayuwata ido ne,badama nayi magana sai kace na cika gulma,kuma in an bibiya wlh gaskiya nake Fada..”Yafada yana kara saka dariya,

Tsaki Saleem yaja kafin ya tashi ya isa ga karamin Frigde din dake office din ya dauko Ruwa mai sanyi yazo ya ijiye agaban Sadiq,yana mai zama kujerar dake kusa dashi yake Fadin”Naji mallam,yanzu dai lafiya Tunda ga Abia ka bugo sammako,ko kana  bina bashi ne…? yafada Fuska Daure,dariya Sadiq yayi kafin ya dauki Ruwan daya ijiyemai ya bude ya kurba kadan kafin ya ijiye yana Fadin.

“Nazo yimaKa Allah sanya alheri ne,naji Abun alheri,ance ma ansaka ranar aurenka kai da Diyar Dankasuwan nan Alhaji Abdulmalik,wama take da suna…? Yafada yana Rike haba,kuri Saleem yamasa da ido kafin yace”Ok nagode yaushe kazo garin..? ya fada yana basar da zencen,Shiko Sadiq ya gyara zama yana Fadin”Jiya na iso,kuma yau nace kai zan dakama sakkko naji dadin ratayeni dakayi baka daga kirana,ko kafarama irinmu nisa ne Tun yanzu…”Mirmishi Saleem ya saki kafin yace”Eh duk yadda ka dauka hakane,ya aikin..?

Sadiq yace”Normal,ya shirye shirye…? tabe baki Saleem yayi kafin ya mike yana Fadin”Babu wani Shirye shirye daga wajena kabaro wajen da”ake Shirya komai ma”ana gidan Abbi…”Dariya Sadiq yayi kafin yace”Friend nazo ne muyi Serious tok dakai,wai don Allah meye ka gani jikin wannan watsatsiyar yarinyar da har ka makale sai ka aureta…? yafada Shima Fuskarsa nasa na rage Fara”a,ko kallonsa Saleem bai yi ba yace”Me ruwanka Allah yasa Tambadaddiyace ba watsatsiya ba,ni naji na gani,so plz and plz Sadiq stay out indai akan wannan mgananr ne, matukar kanason mu cigaba da zama a mtsayin abokai…”,Yafada babu wasa amganarsa.

Baki Sadiq ya rike yana Fadin”Haba Friend ina laifi don na gaya maka gaskiya,karka manta Ance mu zabama ya”yayenmu uwa tagari….”Cikin hargowa Da Fushi Saleem yace”Plz Sadiq i said stay out of it ko? kada ka Tunzarani nayi Abunda banyi niyya ba”Yafada idonsa yakada yayi jajir,kuma muryansa a kausashe,Shuru Sadiq yayi yana kallonsa kafin yayi ajiyar zuciya yana Fadin”Is ok,yanzu meye Shirinka akan shagalin bikin,bawani event ne,ko daga bangaren Amaryan…?

Saleem yayi kasake aransa yana Fadin”Kai Sadiq maye ne wlh,…? Fuska ba Annuri yace”Nifa ka ganni nan babu Abunda zanyi ko gayyata babu wanda nabashi aikin balle yazo ya wahala Saboda ni kai infact ma ni banda ku na gida babu wanda zai san da wannan auren nan,so plz mu chan wata hirar..”Yafada yana zama bisa kujeransa Fuskarsa kuma taki bada dama balle har Sadiq ya Fahimci wani Abu.

Duk yadda yaso ya bugi cikin saleem shiko yaki bashi dama,dole ya hakura suka shiga wata hirar,sai wajen la”asar kana yayi mishi sallama yakoma Abuja,bayan sun rabu kan gobe zai koma bakin aiki sai kuma Lokacin bikin na saleem in ya samu dama zaizo Daurin aure,shiko saleem yana mirmishi yacemai in bai samu lokaci ba kada ya takura kanshi,Abun yabama Sadiq mamaki,nan da nan kwalkwalrsa tashiga Tunanin akwai lauje cikin nadi,game da wannan auren na Saleem,ammh duk da haka zai cigaba da bibiyan al”amarin har ya gano gaskiya duk da Shi saleem din ya ki bashin damar Fahimtar hakan.

  _____________________

*BAYAN SATI BIYU*

Shirye shirye ta ko”ina ya kamkama,Abbi da kansa ya kira mutanen Kumo ya sanar dasu,tare kuma da sanar dasu lokacin biki,Hakama Ummi ta sanarma duk wanda yakamata yaji,ammh bata bada Fuskar wata mgana ta shigo ba,duk ba kasafai take iya sanar da wacece Shi Saleem din zau aura ba.daga ita har Abbi suna ta gayyan mutane da yan”uwa da Abokan arzuka ayayinda da ango da amarya basu san wainar da,’ake toyawa ba,Shi saleem bai yarda ya sanar da kowa ba,sai inspector sale,domin shine kadai yasan Shirinsa,ammh shikanshi baisan me yake Shirin aikatawa ba,kuma Tun bayan tafiyarsa baiji yanama sha”awar zuwa gida ba.

Shiko Alhaji Abdulmalik,Tuni ya kira chan Malumfashi ya sanar dasu,hakika sunji mamaki tare da al’ajabin jin wannan sangartattaciyar yarinyar zata yi aure? Abun tambaya wani dan asaran ne zai kwasan ma kanshi,haka kowa ya rayawa aranshi,Fatan alheri sukayi da murna,shima anashi barayin Shiri yake na mussaman Domin ana Saura sati biyu biki ya buga kayatattun katina,nashi dana Abbi wanda Direba guda ya tasa yakaima Abbi Abuja,akallon Farko kanama katin zaka Fahimci Abun na manya ne,mai fara fasa Abun Aduniya ba,saboda kada lbri yakai kunnann Malika komai ya tawarwatse.

Ana Saura sati daya bikin, kayatattacen ginin da Alhaji Abdulmalik ya sanya ayimai a anguwan GRA katsina ya kammallah wani gida ne upstair mai kyau da tsari bayan yaji makeken haraban mai dauke Da Fulawowi masu dadin kallo da ban sha”awa,wanda akallah zasu ji motoci fin ashirin basu san an ijiye komai ba,Tsarin gidan ko akasar Turai albarka,duk Abunda maleka ke so an ginamatashi acikin gidan,kama daga wajen wasanni,da kuma wajen wanka Swimming Fool,domin kusanta akwai shiga ruwa kamar kwado,Sai Tsarin kayan gida wanda kamfanin MAHARBA tazo ta baje kolinta acikin wannan gida kafin lokaci sun kawata gidan da kayansu na alfarma kalan Red and black duka kayan gidan komai da komai kalansa kenan,domin best colour ne na Malika,mai gayyah mai aiki,dakinta kuwa fadar yadda aka tsarashi bata baki ne,hatta da wasu ubansu sabbin kayanta wandanda take sakawa an Jeramatasu cikin wani makeken wardrope,mai kunshe da gilasai Abun sai wanda yagani.

Daki guda aka ware aka jeramata akwatunanta guda 40 wanda Mahaifinta ya dagi kirji ya bada kudi Hajiya binta taje Dubai tahado mata komai da komai na bukarar rayuwa,sai dai kash gabadaya kayan daga Atamfofi da lesuka sai material da kuma dogayen Riguna,babu Zabin Malika ko daya aciki,saboda ana Tunanin zata shiga kwaryan manya,Sauran akwatunan cike suke da kaya shake kama daga takalma,Jakukkuna,Kayan make up,sleeping dress,agoguna da Yan kunnaye Banda Zinare da Azurfa babu Abubda ke ciki,Abun fa sai wanda ya gani,daki ne guda ne aka ware musu suma kalansu Red and black ne,an jerasu gwanin ban sha”awa.

Shikanshi dakin Uban gayyar Acp Saleem kumo,kenan wanda ke upstair kusa da jerin dakunan Malika,An tsaramai shi,bayan yaji kayan more rayuwa shima Wardrope guda aka Cikamai da kaya kama daga Shadodi,da yadina babu na banza daga gezner sai yadi mai daukan ido,American Suit kuma na kowani kamfani akwai kama daga Hilfiger,Tommy,Armani,louls,Button Dolce,and Gabbana Bersace,DKNY,dukkansu kalan Bakake da masu Ruwan kasa.

Bangaren Turareka da lation kuwa Abun sai wanda yagani kamar za”a budemai shago,balla aje ga bangaren Takalma,gasunan ajere Reras,Kama daga sawu ciki zuwa Rufaffu na Fatar damisa ga jerun agogun nansa na Fata dana karfe na kamfanin Rado,Babu Abunda mutum zai nema ya rasa acikin wannan Dakin,domin duk Abun jin dadin Rayuwa da bukata akwai acikin dakin.

Daga haraban gidan kuma ya Faka musu Tafkakan motoci guda biyar Biyu na saleem,Uku na Malika na saleem Daya prado ce,sai dayar kuma matrix ce,sai ta malika Komferesor ce,607  kirar piagion,sai Accord,motocine na gani na Fada,kuma dukkansu sabbi ne, daga kwatano aka shigomai dasu diret kuma nan aka killacesu domin ma mallaka motocin sune zasu Shiga wanna kayatattacen gidan mai kama da Aljannah Duniya.

Lbrin Auren bai Fita waje ba,saboda tsoron kada lbri yakaima Malika tun tana chan,kuma jin hakan zai iya sakata taki dawowa gida ta Shiga Duniya yasan halinta sarai,shiyasa bai yarda gidajen Yan jaridu da sauran kafafan yada lbrai sunji batun baba,so yake sai bayan an daura sai afasama Duniya taji komai,Shiyasa Tun sauran kwana biyar da bikin Sukayi waya da Malika wacce daga Amurka,Babban birnin America ta Wuce U.S Taje kaima abokan karatunta ziyara,dagachan kuma england ta wuce wajen Dangin mamarta,Da sukayi waya sai ya sanar da ita tadawo gida nan da kwana biyu saboda akwai Suprise din daya Shiryamata bata kawo komai ba ta sanar dashi Visarta take jira,tana bisa hanyar Dawowa.

Ana gobe biki gabadaya duka bangarorin biyun gudajensu ya cika da yan”uwansu,na kusa dana nesa, Gidansu Saleem Tuni yan kumo suka hallarta mata anata shagali,ayayinda katsina kuma yan malumfashi kwansu da kwarkwatansu sun hallata mata da maza,saboda bikin dai zahirin batu za”a yi wadaka da abubuwa domin komai mota ke saukeshi kama daga ababen sha,da kuma snacks da sauran Abinci kuwa tun ana saura kwana uku da biki wani kayatattacen restaurant ke yo odar suna kawowa gidan,Abun sai wanda yagani 

Joda ma ta iso Tun jiya domin Amminta na sanar da ita tayi alqawarin kallo bazai Wuceta ba,so take ga shin waye mijin na malika,kuma ya malika zata kare matukar taji Abunda mahaifinta ke kulla mata? duk ta anada tambayoyinta ne shiyasa ta tadawo daga mkranta da hanzari domin ganema idonta Abunda ke Faruwa koma nace yana kan Faruwa..

Daga Amaryar har Ango sai daren Daurin Auren suka iso gidajensu,wanda suka tararshi cike da jama”a Saleem bai damu ba domin yana da masaniyar komai,Sadiq ne Maye Tun safe ya iso ya dinga jeramai wayar Shuru haryanzu bai ganshi ba,Shiko yayi niyar daga zamfara su hadu aktsina ne,Ammh ya kama damunshi yasa har Abbi na kiransa,Wani Abun mamaki bai dade da zuwa ba,sai ga ya marwan ya kariso shima,wanda kwata kwata saleem bai so ba,yaso ne kowa yayi zamanshi don zuwan fa harga Allah baida wani amfani,saleema dai tace ayi biki lafiya ammh bazata samu zuwa ba haka ta gayama Saleem shiko yace Gaskiya tayi Dabara don baya gayyatan irinsu dama.

Malika ko koda adawo taga dangin Abbanta bata wani damu kanta ba, domin tariga ta raina musu arxiki duk azatonta anzo Maula da cin arzikin da”a ka saba ne,shiyasa bayan sun gaisa da Abbanta ta Shige dakinta bata kara lekowa waje ba don bata son hayaniya sam,kuma ko aranta bata kawo wa ita aka taru ba, domin ko amafarki batata zaton hakan zai Faru da ita ba.

*WASHEGARI..*

  _RANA BATA KARYA SAI DAI UWAR DIYA TAJI KUNYA…_… Ayau Jumma”a 17/1/2020 Dubban Mutane suka Shaida Daurin Auren *MALIKA ABDULMALIK DANKASUWA* Da angonta *ACP SALEEM KABIR KUMO* Akan sadaki Naira Dubu Dari Hudu da hamsin wanda mahaifinshi ya biya da hannunshi ayayinda wani Baffanshi dake kumo ya karboma Saleem Auren,Itakuma malika Kawun mahaifinta dake Malunfashi ya bada aurenta,wanda ya gudana Ababban masallacin jumma”a dake garin katsina.

Daurin Auren daya samu hallartan manyan mutane,kama daga kusoshi agwannati,yan kasuwa manyansu da kananansu,kungiyar direbobi,kungiyar Kwadago ta kasa baki daya,Sevil defence,yan mofal,Yan sanda manyansu da kananansu sun samu katin gayyata zuwa wajen wannan Daurin Aure,sai bayan da”aka Daura aure ne, kana Alhaji Abdulmalik Dankasuwa yabama yan jaridu,da kafar yada lbria sanin Abunda ke Faruwa,ko kafin kace kwabo Tuni lbri ya zaga duniya ta ko”ina Kowani Shafi ka bude na wasop,instergram ne,Fbuk,twitter,duka lbrin zaka gani yana yawo da cewa” *WANI ABUN MAMAKI AYAU MUKA GA TARON DUBBAN JAMA”A WANDA SUKA HADA DA KOWANI MUKAMAI AFALIN JAHAR NAN ANA GUDANAR DA DAURIN AURE BAYAN AN SALLAME SALLAR JUMMA”A ABABBAN MASSALLACIN JUMMA”A DAKE  LAYOUT,SAI BAYAN KAMMALLAH DAURIN AURE NE, MUKA SAMU LBRI DAGA BAKIN SHAHARARREN DANKASUWAN NAN WATO ALHAJI ABDULMALIK DANKASUWA INDA YAKE SANAR DAMU DAURIN AUREN DIYARSA CE WATO MALIKA MALIK,TARE DA ANGONTA ACP SALEEM KUMA,WANDA D”A YAKE GA INSPECTOR GENERAL OF POLICE NA KASA GABADAYA WATO IGP KABIR KUMO,SHIN YAYA MUTANE ZASU DAUKI ABUN,ACE DAURIN AURE YA”YAN MANYA KAMAR IGP KABIR KUMO DA ALHAJI ABDULMALIK DANKASUWA BABU LBRI SAI BAYAN AN DAURA AUREN,SHN BAKU TUNANIN AKWAI LAUJE CIKIN NADI..*? Haka kowacce jarida ke wallafawa asaman Shafinta kama da leadership,Dailytruth etc.

Shiko Saleem yana gefe shida Sadiq da ya marwan,wanda dukkansu suke sanye da shadda fara taji kyau harda manyan Riguna da hulansu zannah bukar suna ta hannu da mutane,shiko ango tunda aka daura auren yaji wani Faduwar gaba da kasala duk karkashinsa,da wani zumarshi na ramuwa yaji ya Fitarmai aka,yana jin wani Abu mai kama da nadamar Abunda zai aikata ammh kuma bashi da yarda zaiyi domin bakin alkalami ya rigaya daya bushe,Bai ji faduwar gaba sai daya dinga samun waya ta ko”ina da sakonnin Fatan alheri,da kuma tsiyan yayi aure babu lbrin hatta abokan karatunsa da abokan aikinsa lbri yaje musu,Ya marwan ne yake sanar dashu lbri yazaga duniya don harda hotunanshi da Malika ansamu masu hadashi waje daya an dorashi bisa media akasa an saka *COUPLES OF D YEAR* Shi ahoton yana sanye da kakinsa na yan sanda ne,sanda Sadiq ke numai hoton wanda aka watsashi a Twitter,ya tuna sanda akayi hoton sanda Tsohon Inspector general ke sanya mishi Rank din karin girmanshi ne sanda ya zama ACP abuja akayi hoton,shine aka yanke IGP na lokacin aka hadashi da malika wacce ta ke sanye cikin riga da wando black and white kanta babu dankwal gashinta ta saki jelan ta baya,bayan ta tamke samanshi da band,kunnenta makale da waya,alamar kamar ma tana Tafiya ne,aka yanke hoton aka hadasu, sharrin Na”ura ace tare suka dauki hoton.

Kanshi gabadaya ya dau zafi,barin ma sanda yaga Abbi cikin mutane yana ta gaisawa dasu bakinshi har kunni saboda murna da Farinciki,suna wajen har mutane sukafara watsewa,yan jarida ko sunan suna haskawa abubuwan dake Faruwa awajen kai tsaye harshi sun so suji ta bakinsu ya daure Fuska yaki basu dama,Shiko Alhaji Abdulmalik bayan sungama Gaisawa da mutanen da suka gayyata sai gasu sun jero shida Abbi hannunsu sarke dana juna kowannensu yaci Farar shadda harda malum malum,Fuskarsu na bayyanar da Fara”a da kuma Farin cikin dasuke ciki.

Haka suka kariso wajensu,wanda dukkansu suka zube suna gaishesu,ammh banda saleem don Fuska yayi yaki bude baki gabadaya domin Gabadaya yanzu kowama haushi yake bashi,Alhaji Abdulmalik ne ya Umarcesu kafin su wuce Abuja zai gabatar musu da wani Abu,nan da nan suka shishshiga mota suda tawagarsu sai Gra.

Koda megadi ya bude musu get suka sulala ciki,da mamaki suka firfito suna bin gidan da kallo da alamun dai komai sabo ne kama daga motocin gidan yadda suke lullibe cikin tamfol,Daddy bai yi wata wata ba ya damko hannu Saleem ya zuramai makullaye har guda uku,Tsaye yayi yana kallonsa,shiko kafadansa ya daka yana Fadin”Kowa ya Shaida,Wadandan makullayen naka ne halak malak,daya makullin wannan gidan ne, inda zakuyi rayuwar aure kaida malika,Sauran biyun kuma keys din sabbin motocin dana siya maka ne Gift din Aure amatsayina na Uba gareka…”Gabadaya sai su Sadiq da marwan  da sauran mutanen wajen,suka dau kabbara,Shiko saleem suman tsaye yayi aranshi yana Fadin”Kash kayi gaggawa Alhaji,inda kasan Abunda nake shiryama yarka dabaka Bani wadanan kyaututtukan ba…”Ammh Afili ko fadawa jikin Daddy yana matse hawayen karya yana mai godiya,Bayansa yake dafawa yana dariya haka Abbi ma yayi ta godiya,ammh sai da ya nuna dawainiyar tayi yawa gaskiya.

Nan suka isa ga motocin aka bude suka gani harda na Malikan,jinjina kai kawai Sadiq yake aransa yana ayyana Dalilin daya sanya Saleem auren Malika saboda kudi ne,Ai basu saki baki sai da suka shiga gidan,daki by daki suka dinga shiga suna ganin Uban Dukiyar da”a Narkama gidan,basu tsinke da al”amarin ba sai da sukaga lefen dayayima Malika boutique Guda ne,aka tara,shikanshi Dakin Saleem din ya basu tsoro,kai Ai nan da nan Sadiq ya yarda da zuciyarsa na dama kwadayi ne da Auren jari yakai saleem ga auran malika Kai,babu shakka ya tsinci dami a akala.

Bayan sungama gani suka sanya albarka nan Daddy yake sanar dasu basai Saleem yazo daukan Amarya ba,shida kanshi zai kawo malika har dakinta,kana bai hanashi bayan sungama cin amarcinsu ba ya dauki matarsa zuwa wajen dayake aiki ba,in kuma zai barta nan ne,duk yadda yagani.

Saleem yaji dadin haka dama kuma Shirinsa kenan,domin adaren yau yake son dukkan wani Shirinsa ya kammallah zuwa waye garin gobe sai Dai aji bom din ya fashe shikuma kafin lokaci yayi nisa da jaharsa,kilama harda Kasar gabadaya.

Daganan gidan hanyar Abuja suka dauka,shikuma Alhaji Abdulmalik da danginsa suka koma gida,ko acikin motar,daga sadiq har marwan Zence suke tare da mamakin uban Dukiyar da aka batar suke,shiko Saleem ko baki bai tsoma musu ba illah danne dannen waya dayake tayi,ammh bayan lokaci kuma ana turomai sako ta waya kuma ya na maida reply batare daya bari wani cikinsu ya ankare dashi, ba Gabadaya zuciyarsa ta kekeshi,ba kamar dazu data nemi ta karaya ba,Abbi na gaba shida tawaganshi da sauran motocin yan uwa da sukazo daga kumo,suma lbrin arzikin da Saleem yatako kawai suke kowa aranshi yanajin dama shine saleem.

____________________

Malika ko tun daren jiya data Shiga dakinta bata Fito ba har gari ya waye,akayi ta hada hadar biki da kuma zuwa daurin aure batasan wainar da,”ake toyowa ba,tana kwance tana barcin gajiya sallar asuba ma,sai wajen 10 tayi bayan tatashi daga barcinta na asara,wanka kawai tayi,dama already Breafast dinta su Dose sun gama jera mata komai,Falo ta Fito daga ita sai wata yaloluwar riga Red colour,wacce da Kadan ta Wuce gwiwanta ,Wayace ahannunta wanda Tun jiya bata bi ta kanta ba,sakonni ta tarar bila adadin tare da kuma da kiran mutane,duk yawancin kiran na abokan kasuwancin Abbanta ne,na kasashen ketare,Abunda ya dauremata kai Shine sakonninsu ,mai dauke da *HAPPY MARRIAGE LIFE MRS SALEEM KABIR KUMO*

Abun ya Dauremata kai sosai,har ta zauna bisa daya daga cikin kujerun Falon tana sake cigaba da karanta sakonnin,Abun yabata mamaki ammh sai bata daukeshi wani Abu ba,tana tunanin kila kuskure ne,bata ji jikinta ya saki ba,sai da ta shiga shafinta na Twitter taga hotunanta dana Saleem Rututu ana Dorawa ,Friend dinta suna ta mata Happy marriage life.

Jikinta ne ya soma rawa,tafara Zargin wani Banza ne ya nemi bata mata suna aduniya kawai dare daya ya hada hotonta da wani kazami kazamin ma,wai wani Dan sanda,wanda basu iya komai ba sai lalacewa da shaye shaye,wai kuma da sunan  mijinta,Kutumar uba ne,lalle kowani Wulakantattace ne, ayau basai gobe ba  take son saninshi,taji dalilinshi na bata mata suna,da kuma yimata karya Aduniya

Fuuu tatashi ta Fice daga dakin dauke da waya ahannunta Falon Alhaji Abdulmalik dake sama Ta nufa tana kwalamai kira bata damu da Dimbin jama”ar dake falon kasa suna kallonta ba.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE