MARAICIN RAHMA 4

Hausa novels
MARAICIN RAHMA
 

                  Chapter 4

www.littafanhausane.com.ng
Wani banzan kallo ya watsa mata
tun daga sama har kasa,tare da
tamke fuska,har ga Allah yaga
tsananin kyan da kayan suka
mata,amma ya tamke,Sam ta
manta da kayan dake
jikinta,tsugunnawa tayi tace yaya
ina kwana,cikin kasaita yace da
ban kwana ba kya ganni,1:30
zakice ina kwana foolish
girl,rahma tuni ta shagala wajen
kallon tsabar baiwar kyau da
Allah yawa Ahmad,gashi da
tsabta ga iya daukan
wanka,kullum cikin kamshi,tsawa
ya daka mata yace wlh in baki
daina kallona kinje kinyi wanka
ba sai na mai dake kauyenku
yanzu,sha sha shar banza,dan
iskanci ina jiranki kina bata min
time,ai kafin ya kare magana sai
gani yayi tuni bata wajen ta ruga
da gudu toilet jin an ambaci
kauyensu,waje ya fice,da sauri
rahma tayi wanka ta kara yin
brush,wani dan cream da
Vaseline da suke bayarwa a hotel
 ta shafe jikinta dashi sai dan
kamshi takeyi,dama su rahma
bade tsabta ba,dama gashibade tsabta ba,dama gashinta
ranar da zata wajen me gari sai
da ta wankeshi tas har da gayyan
magarya,ta yanke farce,kamar
tasan ranar zata bar garin,da
kyar ta iya kama gashinta sabo
da santsinsa da tsayi,da wani
zaren buhu ta daure abinta,
Wajen sa bra ne ta kasa,kawai
pant ta dauka sabo ta sa,da
dogon tight dinta tasa doguwar
rigarta sky blue nd white,tayi
mugun kyau kai kace irin
cikarkiyar yar birnice,gyalenta
kawai ta Dora a kanta ta gyara
kayan dake ledar tasa short dinta
da singlet na bacci ciki,tsohuwar
atamfar da tazo da ita a jikinta
tuni na fada muku ramata ta jefa
su shara,yar ledarta ta rike abu
daya ne ya mata cikas takalmi
dan wani tsohon slifas ne a
kafarta,Wanda duk ya cinye haka
tasa,kwankwasa kofa yayi ta
bude wasu flat shoe ya watso
mata me kyau baki da ratsin
fari,yayi kyau,harkasa ta duka
tana godiya,kallonta yayi tun
daga sama har kasa,tayi kyau
ainun ya yaba kwarai,bai san
kyanta yakai haka ba sai yau,
Yace oya wuce muje,sumi sumi
zata wuce ya hango tabbazata wuce ya hango tabbas bata
sa bra ba kuma ya siyo
mata,juyowa yayi cikin fushi ya
fisge ledar hannun ta sai da ta
firgita,bincika ledar yayi ya zaro
bra fara kal yace oya je kisa
ballagazar kauye,kamar zatayi
kuka ga kunya tace banfa iya
sawa ba kuma ni bana sonta sai
kace yar iska,
Kin San Allah daya in baki sa ba
mota zan saki a mai dake
garinku,har gidan me gari zan
kaiki,wawiya kinfi so kowa yana
kallonki gazal haka,da sauri ta
rufe ido dan kunya,tace to ka fita
na gwada ko zan iya,tsaki yaja ya
fita,da kyar ta iya sawa hakan ma
duk hannun bra din ya fito ana
gani,kofar ya bude da Sauri tayi
kasa da kai,ala dole kunya,
Jawota yayi ya shigar da hannun
bra ciki ya gyara mata ya figi
hannunta sai cikin mota ba tare
da yace kala ba,itakam mamakin
iskanci da rashin kunyan yan
birni take,,
Gaban mota ya bude ya wurgata
ciki,ya dauki ledar kayanta ya sa a
baya,itakam sai kalle kalle
take,tace gwara na kalla na
more,hanya suka hau sosai,tun
tana kallo har bacci ya
kwasheta,juyowa yayi yaga tana
ta bacci,a ransa yace wannan
yarinya sai son baccin
tsiya,kamar kasa,gyalenta ne ya
zame ya fadi nan Ahmad yaga
zallan dogon gashi me kyau kal
kal dashi me santsi kamar
balarabiya,
Baki ya tabe daya ga gashi me
kyau amma an daure da zaren
buhu.tukinsa ya mai da
hankalinsa,sunyi nisa yaga ya
dace ya tsaya suci abinci danshi
baya wasa da cikinsa bai iya
zama da yunwa ba.
A wani makeken restaurant ya
tsaya Wanda da gani na manya
ne,jin an tsaya ne ya farkar da
rahma,fita yayi daga motar dan
sauri yake shi yasa ya musu take
away suci a mota dan dare ya
kusa,friedrice with chicken ya
siya musu sai yogourt da
juice,apple ya kara siyowa da
inibi,du a kusa da rahma ya
ajiye,mota ya tayar ya fara lulawa,
Izini ya mata da ta bude komai
su fara ci,ga nata daban nasa
daban tuni ramata aka fara
zuri,ko kallonsa batayi har Sosa
kunne da kai takeyi,rankwashi
Ahmad ya zuba mata,tare da
cewa naga ranar da zakiyi hankali
village girl,ko a jikinta,har ta
gama cin komi ta wanke hannu
ta windown glass, bayan ta
nutsu ta dauki apple da inibi tana
sha hankalinta kwance har rigar
ta fara batawa,kai kawai Ahmad
ya girgiza,dab da wani gari ya
tsaya a cikin motar yaci
nasa,sannan sukayi sallah suka ci
gaba da tafiya yana cin apple
dinsa,
An kusa zuwa ABJ kenan rahma
ta fara gyangyadi,tsawa ya daka
mata kina min bacci zan watsaki
ta window,tasan muguntarsa
dan haka tace kayi hakuri kamar
zatayi kuka,
Sun shiga garin ABJ,rahma ai
sakin baki tayi kamar zata jefa
kanta waje,bata kara shan
mamaki ba sai da taga an bude
get din wani wangalelen gida ya
kai girman rugarsu,kallon
motocin cikin gidan take,flowers
da komai ma,
Bayan yayi parking ledarta ya
miko mata da sauran apple da
inibi din gaba daya ya ja
hannunta suka shiga ciki,dan ya
gaji da kauyencin da take masa,ai
rahma ana shiga ciki ta rafka
salati tare da jawa su
obasanjo,goodluck Allah ya isa
akan sun kwashe kudin kasa su
basu dashi kuji min ramata da
karfin hali,su mimi ne a falo,ga
salma sai mum da dady,ai mimi
na ganin ramata ta jefar da
remote ta kwaso da gudu ta
rungumeta,tana Murna da ihu
sosai ta cika falon,tsaki Ahmad
yayi ya zauna sharab a
kujera,mum tuni ta gane rahma
ce ta kauye,dama dady ya Santa
sai dai bai San me ya kawota ba,
Ana haka sai ga su ammar da
autar momi amal,murna wurin
ammar ba a magana yaga
ramatansa,ahmad ne ya basu lbr
komai da komai har tarihin
rahma,su me gari da
sauransu,momi taji dadin
daukota da akayi,dady kuwa bata
rai yayi karfa ko su mai gari
gaskia suke fadi,amma baya
zargin yaransa da aikata komi da
ramata sai dai dama Dana garin
takeyi,ga zahiri tana kwana ita
kadai,kwana mace ita kadai a
gida ai sai hatsabibiya a
Nigeria,da wannan dady yaki
yarda da zancen ahmad,cikin
fada yace Ahmad ka dauketa ka
mayarda ita kauyensu bana son
gurbatattu a gidana,kar ta lalata
min yara,kowa yasha mamakin
maganar dady,momi ce ta fara
rokonsa amma ya dakatar da
ita,duka yaransa ne suka fara
rokonsa kan ya barta ta zauna
dasu,da kyar yace ya yarda amma
kwandalarsa baza tayi ciwon kai
ba a kan al’amuran rahma,ahmad
Wanda ransa tuni ya baci da
kalaman dady cewa yayi dad na
dauki nauyinta in,kafada dad ya
daga ko a jikinsa,tare da
tsawatarwa da mimi,salma,amal
,da ammar cewar in suka kashe
ko sisi kanta bai yafe ba,kuma
kar yaga wani yana mata
magana sai dai in maganar miko
min kaza,ko ina kaza,dole dai sai
da dalili har momi, bazai yafe
musu ba,dan yace me gari
mutumin kirki ne tunda har yayi
magana to da akwai kamshin
gaskia,dan haka ahmad daya
daukota shi kadai zai kula da
ita,ba sa hannun kowa yaje da
abarsa kuma wlh sai dai ta zauna
part din ahmad din,dan baza ta
bata masa yara ba,duk abun nan
da akeyi rahma hawaye ne
kwance male male a
fuskarta,ahmad kuwa kamar
ruwa ya cinyesa,bai taba zata zai
fuskanci haka ba in ya kawo
rahma,gashi ya dakkowa kansa
jangwangwama,taya zaina
kwana da ita part daya shi ba
muharramarsa ba,da ya sani da
nadamar kawota yayi,in ya
maidata garinsu ya zatayi,bashi
da zabi tunda dady ya amince
kawai zai taimaketa shi kadai
din,har ta samu miji ya mata
aure.
Rahma kuwa ta gama tsurewa
da kalaman dady,rayuwa kenan
yanzu tasan ta rasa iyaye,yanzu
tasan gatanta ya kare,yanzu
tasan bata da dangi masu
amfani,yanzu taga illar kin auren
da tayi da tayi auren wa zai mata
kazafi,yanzu taga laifinta na kin
zama da tayi gidan baffajo,yanzu
taga illar barin su ammar su
dinga shiga gidanta,ta tabbatar
tayi kuskuren zama ita daya a
cikin katon gida,da ace ko wajen
danginta ta zauna tana musu
share share ya fiye mata,sai
yanzu tsoro ya shigeta da take
iya kwana ita kadai dan miyagun
maza zasu iya mata fyade,domin
ansha kai mata hari
watarana,Allah ne ya kareta dan
har sau 2 akaje mata,naushi ta
musu da sanda tsira,sai yanzu
taga lefinta,ta tuno da taurin kai
da karfin hali irin Wanda tayi,tir
da Allah wadai tawa kanta,
Kawai tunani take hawaye na
kwarara,dady ne ya kira momi
cikin room suka kebe,zugata yayi
tare da fada mata ramata zaman
kanta takeyi,take momi taji itama
ta tsaneta amma ba sosai ba,
Haka duk su ammar suka bar
dakin cikin bacin ran da dady ya
jefa su tare da bawa rahma
hakuri,mimi ce ta tsaya ta karawa
ahmad kwarin gwiwar rike
rahma da amana,ya danji sanyi a
ransa,tashi yayi yaje dakin momi,
a zaune ya taddata tayi tagumi
gefen gado,karasowa yayi ya
kwanta cinyar mum,momi ce tace
ahmad kaga abinda ka jawo
ko,kasan babanku baya son
kowa ya zauna masa gida sabo
da kar tarbiyar yaransa ta
Baci,jiba abar da ka kawo,ahmad
ne ya mike tare da cewa mum
kema kin yarda ko,ke fa yau ma
kika Santa,haba mum me yasa
kuke haka,son Kaine
wannan,yanzu in mimi ko salma
haka ta samesu me zakuce,haba
mum wlh nutsatstsiyace ta
gari,why mum,why all this,mum
ce tace look ahmad ni na yarda
da babanku duk da ina
shakku,gargadina gareka ka
kiyaye kanka,ka kula,wlh kar inji
wani abu !!!!!! kanka sai ta bar
gidan nan,kuma kaje can da ita
wajenka nima ban goyi bayan ta
zauna wajen mimi ba,kuma ba
kai ba aurenta dan naga kana
wani damuwa akanta
Yar asali,nutsatstsiya zaka
aura,dauke min ita Ku wuce can
kai kadai na yarda kazo nan part
din cin abinci da komai,ita kam ta
tsaya can ka bata kayan girkinta
da kudinka tayi can,get lost,da
sauri ya fice cikin bacin rai,
Ramata kuwa kuka ake harda
majina,tsawa ya daka mata rufe
min baki,ki taso muje part dina
stupid kin tsaya kuka,duk
kukanta ya tsaya ganin tsananin
kyan part din ahmad yafi ko ina
kyau,2 rooms nd toilet kasa da
Palo, kitchen,sama kuwa
2room,toilet,sai Palo kawai,komai
ya tsaru,kayan coffee ne kawai
cikin kitchen din sai
indomie,corn flex, da kayan
tea,fridge biyu ne daya du kayan
gwangwani ne,sai nama,kifi
danyu,dayan kuma dankare take
da fruits,juices, fresh milk dan
ahmad watarana yana dafa
abinda ba a rasa ba,nuna ma
ramata komai yayi daga karshe
ya bata room daya cikin Wanda
ke downstairs, shi kam dama a
upstairs yake,godiya rahma ke
masa sosai,dakin ta shiga,tayi
wanka da sallah,kayan jikinta ta
mayar sannan !!!!!!!!? sannan ta kwanta tana
tunanin irin taimako,mutunci
,halacci da ahmad ya mata,take
taji sonsa ya mata shigar
sauri,itakam me zatayi wajen
biyansa taimakon daya mata,a
zuciyarta ta yanke shawarar yi
masa biyayyya da bashi matsayin
uba a wajenta sai yanda yayi da
ita,sai abinda yace zatayi,har kasa
zatana duka masa dan yanzu
wani girma ne da daraja dashi a
idonta,
Tabbas ahmad abin so ne,tana
cikin haka taji an buga mata
kofa,tasan bazai wuce shi
ba,tana budewa ya ballamata
harara tare da mika mata take
away na lafiyyan abinci,godiya ta
masa ya juya ya hau sama.
Wata yar uwar dady ce dake nijar
ta dira a abuja gidan su
ahmad,AMRATA kenan kyakkyawa ahmad,AMRATA kenan kyakyawa
me dan haske amma bata kai
rahma kyau ba,yar kimanin 25yrs
dan mimi ma ta girmeta
kadan,tunda taga ahmad take
sonsa, bata da buri sai na ta auri
ahmad ko ta dole ko baya so to
ita zata aura haka,ahmad kuwa
ba wacce ya tsana irinta dan bata
da kunya ko kadan, ga karya da
kuri, da bin maza manyan alhazai
masu naira.dady kuma ganin yar
uwarsa ce yake buri ahmad
dinsa ya aureta,momy kuwa bata
sonta,dan taga bata da ta ido.yau
da safe ta dira a gidan,Sam momi
da su mimi basuyi murna ba.
Amrata ta iso da safe sai yanga
take tana cika tana batsewa,su
mimi kawai binta suke da
kallo,bangaren su ahmad kuwa
rahma ce bayan tayi sallar asuba
da karance karancenta komawa
tayi bacci,sai 10am ta tashi
wanka tayi tare da tsaftace ko
ina na room din,daya doguwar
rigar ta dauka ta saka ta ebo
sauran kayan harda na baccinta
ta wanke tas,barin kayan tayi
cikin bocket tana jira in ahmad
ya tashi ta tambayeshi wurin
shanya,ahmad tunda yaje
masallaci ya dawo yake yin
baccin gajiya gashi yau Sunday
ba aiki,bashi ya tashi ba sai
wurin 12pm,dan yunwa harta sa
rahma kwalla,
Wanka ya fesa sanye yake cikin
wando 3quater black da Riga
armless brown,sai kamshi da
sheki yake,ya ma manta da wata
ramata kai tsaye part din su mum
yaje ya gaisar da ita da dady har
hira sukayi kan aikin
kauyen,amma cikin mum and
dad ba wanda ya tambayi
ramata,ko zancenta basuyi masa
ba,yana fitowa Palo yaga du
kannen nasa har ammar gaishe
dashi sukayi tare da tambayar
rahma,kawai tana lfy yace musu
ya wuce dining sai daya cika
tumbinsa,sannan ya koma wajen
mum da dady du so yake su
masa zancen rahma yaji ko sun
hakura amma shuru,dady ne ya
tamke fuska yace ahmad akwai
wani abu,
Cikin ina ina yace dady dama
ra..rahma,rufe mana baki
mutumin banza cewar
mum,rahma ai an bar maka ta
zama yarka komai na hanunka
cewar tashi ka bamu waje cewar
dady,yana fita mum da dad suka
Dora da hirarsu ta harkar nema Dora da hirarsu ta harkar neman
kudi,
Direct ahmad part dinsa ya nufa
cikin bacin rai da
zuciya,kwankwasa kofar rahma
yayi da gudu ta bude,jikinta har
rawa yake dan yunwa,gashi har
tayi sallar zuhr,durkusawa tayi
tace ina kwana yaya,lfy kawai
yace ya juya tare da cewa fito
muje,binsa tayi har Palo ya zauna
a kujera durkusawa tayi a kujera durkusawa tayi a kasa
kusa da kafarsa kamar yanda
takewa baffanta da,ni sawa
ahmad yayi sannan yace ke kinji
dai abunda ya faru ko,eh inji
rahma cikin sanyi dan cikinta ya
duri ruwa ko shima ya fasa
taimaka mata,nan zaki zauna ko
Ina a part din nan zaki iya shiga
kiyi amfani da komai banda
room dina indai ba gyarawa zakiyi
ko ki min magana na Neman
wani abu ba,duk wani abu da kike
so ni zaki tambaya,ga kitchen
nan zakina girki kullum ke daya
kici,abinda babu zan kawo miki
kitchen,ki kula da kanji,ki tsare
mutuncinki,bazan rikeki cikin
jahilci ba dole zan saki school kafin
ki samu miji in aurar
Dake,banson yawo,kawaye,kula
maza sai da yaddata Cewar
ahmad,tashi na nuna miki yanda
ake amfani da kayan
kitchen,ahmad kam ya sha
godiya har gajiya yayi yace daga
yau ban son yawan godiya ban son yawan godiya dan
Allah zanyi,da sauri rahma tace
to,nuna mata komai yayi
yakoma palo ya kwanta yana aiki
a laptop,wani kamshi yaji me
dadi ya cika palon,sai ga rahma
dauke da bowl na indomie da
soyayyen kwai,ga wani lafiyayyan
tea ta hada murtuk,dawowa tayi
palon ahmad ne ya mata
pointing dining amma tace ni
yaya nafi son kasa,ci gaba yayi da
aikinsa,tana zaune a center
carpet na Palon,
Da zafi take sharbar indomie ta
sabo da yunwa,jefi jefi yake
kallonta da gani Kasan yunwa
takeji sosai,tsab ta gama ci,ta
wanke kayan a kitchen,masu
share share momi ta kira ta
gargadesu da zuwa part din
ahmad domin gyarawa,wa ahmad domin gyarawa,wacce ya
kawo ta gyara masa wannan yar
kauyen ma ba ilmi tasan ahmad
yafi karfinta bazai taba sonta
ba,na birni ma ko kallo basu
isheshi ba bare wata ramata
cewar momi fa
Bayan momi ta hana masu aiki
gyara part din ahmad ta yadda
gwara ahmad ya auri amratu ahmad ya auri amrata yar
uwarsa akan rahma da sukaji
tana zaman kanta,kuma biri yayi
kama da mutum dan momi ta ga
Sam batayi kalar kauye ba dan
haka ta yarda cewar rahma yar
duniya ce kawai ta shigo gidansu
dan cin dukiyarsune,dady kam ba a
magana dan yafi kowa,
Bayan rahma ta gama komai nata
karfe hudu ahmad yace ta fito
zasu fita,ita dai bata San ina zasu
ba,wani makeken store suka
shiga inda ya siya mata dukkan
kayan abincin da babu a kitchen
har da Wanda ma ramata bata
sansu ba,bayan sun dawo shirya
komai tayi a store da kitchen
din,magrib na yi yace ta kuma
fitowa zasu fita,wani store ya
kuma kaita daban ya siya mata
kayan sawa wow zo kuga kayan
akwati uku ya shake mata da
kaya,atamfofi masu
tsada,lesuka,shaddoji,material
s,sai dogayen riguna ready
made,dasu Pakistan kala kala,har
English wears da
yawa,takalma,bags,mayafai masu
tsada,inner wears,kayan bacci ne
kawai ya siya mata kala
biyar,amma komai daga 10 sai
12,sai da suka zage 5
supermarket suna siye siye komai
na sawarta saida ya gama siya
mata,nan ma yasha godiya yace
ba godiya ba make sure gobe
around 8am kin shirya dan fita
za a sakeyi,ko kayan bata shirya
ba ta kwanta bacci,washe gari da
safe suna hanya wata noor
secondary school ya nufa private,a
time din suka mata komai ta
zama year ss1 dan har primary
certificate aka mata da jssce dan
ta danyi kokari ba laifi,schl din in
kaje tun 8 sai 2 za a tashi daga
boko,sunayin sallah da break by
3 zasu fara arabic sai 5 suke
tashinsu tunda hade take da
islamiyya,an bata uniform,books
da sauran material duk sanda ta
zama ready nan da 1week ta iya
fara zuwa,akan hanyarsu ya
tsaya ya kara siyo mata yadin
uniform dinsu ya bawa tela aka
gwadata yace a mata kala
biyar,canvas, sandals,bags na school
08035453572
duk ya siya mata kala uku uku
masu tsada,komai na schl shima
ya gama hada mata dan so yake
monday ta fara zuwa schl,
Yau ko aiki bai je ba sabo da so
yake ya gama da case
dinta,bayan sunci abinci sun huta
5 yace ta kwaso lesuka,atamfofi
,shaddaji,da material tazo akai
dinki,direct wajen telan su mimi
ya kai aka dauki measurement
dinta ya biya kudin dinki,gaskia
ya kashe dukiya sosai akan
ramata,har mamaki take,wucewa
yayi da ita wani kanti na kayan
cosmetic,sanin bata San komai
ba yake sashi dole shi ke zabo
mata,wash set din mayuka masu
kyau da kamshi da tsada ya siya
mata,powder,lips glow etc,duk
dai wani kayan kwalliya saida ya
siya mata kala kala,tsananin
mamaki yasa rahma kasa shirya
kayan,take taji ta rasa wanne
matsayi za ta ba ahmad,uba,yaya,
uwa uba,ko me,can dai tace my
mum my dad,
Bangaren su mum kuwa basu
San me ahmad keyi ba,amma dai
ba abinda ya fasa na zuwa part
dinsu da muamula,ammar da
mimi ne kadai ya basu lbr,sunji
dadi sosai,dan dady ya hanasu
kulatane ya musu baki akanta ya
za suyi,amma ammar shi ya bawa
ahmad shawarar ya daukowa
rahma me mata extra lesson dan
tafi ganewa,dan haka ya nemo
mata wata meena,ba zallar
bahaushiya bace amma in ka
ganta ka rantse bahausa ce,du
Saturday Sunday suke yi
4-6pm,gashi an karbo mata
dinkunanta na sawa Dana schl,ta
shirya room dinta,sauran kayan
amfani na gidan kuwa sai dai
taga ahmad ya kawo ya jera,su
roomfreshner, kayan wankin
toilet,su turaren wuta etc komi
akwai,
Amrata kuwa Ahmad ko kulata
bayayi,har yau Neman hanyar
shige masa take amma no
way,dan ko hi baya ce mata,duk
wani kissa tata taki aiki,gashi
sha’awar ahmad take ita,ko da
taga rahma Sam bataji wani
damuwa ba,dan ita sha’awarsace
tasa take son aurensa sai kuma
kudinsa, dan dady ya ce Tasha
kuruminta zai yiwa dad dinta
magana kan auren,dan ya zata
son Allah takewa dansa shi yasa
ma yace ya bata ahmad an
gama,tana jin wannan albishir ta
shirya ta koma nijar hankali
kwance taci gaba da
fasikancinta,
Yau ta kama Monday yaune
rahma zata fara zuwa schl.
Tun da asuba rahma ta gyara
part dinta tsab ko ina ya dau
kamshi,dakin ahmad ne kawai
bata gyara ba dan ko shiga ma
bata taba yi ba,tea tasha lafiyayye
da chips,sannan tayi wanka ta
shirya cikin uniform dinta Riga
fara iya cinya da wando baki sai
hijab fari da dankwali komai cib
dai dai ita,dama da dare ahmad
ya karbi littafan ya nuna mata
yanda zata dinga iba dai dai da
timetable nasu,dan haka ta shirya
schl bag dinta,dama tana son
canvas dan haka tasa fari wow
tayi kyau sosai,powder fara ta
shafa da lips glow,sabo da pink
lips dinta sai ta zama kamar tasa
pink lipsglow,fitowa tayi taga
yayanta abin sonta,abin
afaharinta mum and dad dinta
wanda takejin zata iya sadaukar
da ranta a kansa,ya shirya?
Amma shuru ta tafi zata hau
steps kenan domin yi masa
magana kar tayi late dan 7am
tayi,wani azababben kamshi ne
ya daki hancinta Wanda take ya
kara zuke mata jini,dan har
kasala takeji dan dadin
kamshinsa,
Sanye yake cikin wata tsadajjiyar
suit fara kal dai dai jikinsa kamar
a jikinsa tela ya dinka,abinka ga
fari dama gashi kamar bature,ga
gashin daya Tara sai sheki suke
tare da dan sajensa da gemu
kadan,abin sai Wanda ya gani
dan sai ka yini kana kallonsa ba
tare da ka gaji ba,
Da sauri ta durkusa yaya barka
da asba,ka tashi lfy,kallonta yayi
cikin kasaita da isa na Wanda
yake ji da kansa,ilmi,kudi,kyau,ga
Kyan hali ba laifi,da kyar yace am
fine kije parkingload ki jirani, I will
be there soon,ba ganewa tayi ba
amma ta gane kije ta gane
parking dan haka ta fahimci lalai
taje ta jirashi a wajen da ake
parking,murmushi tayi tace lallai
nima Ashe kwaruwa ce,ina jin
turanci,fitowa tayi taje wanjen
cars din,
Tana tsaye nan taga ammar ya
fito daria ya mata ya daga mata
hannu ya shiga motarsa ya fita
da alama aiki zaije shima,tana
tsaye mimi da salma suka fito
suma kowacce cikin
shiri,murmushi suka mata mimi
ta daga mata babban yatsa
daya,dan ba ikon magana dady
yayi baki,
Mumy da dady ne suka fito suma
suka hau mota daya su kam ko
kallonta basuyi ba,amma kallonta basuyi ba,amma du da
haka saida ta tsuguna ta
gaishesu ko kulata basuyi
ba,gwara mum ma ta
kalleta,rahma ce take tunani to su
kowa a gidan Neman kudi yake
ba yaro ba babba amal ce kawai
sai schl,bata fara ba,tana wannan
tunanin ahmad ya fito da alama
breakfast ya tsaya yi,wata
luntsumemiyar mota ya hau
baka,gaba rahma ta bude ta
Shiga dan a birni taga haka akeyi
in dai ba driver bane,7:30suka
dauki hanya,7:40 sunje coz ba
nisa,har ciki ya Shiga da ita ya
hada ta da manyan schl din idan
sunji kanwarsa na bukatar wani
abu ko matsala a nemeshi,anga
yar me kudi sai nan nan teachers
suke da ita a staffroom,
Kudi ya Ciro 1000 ya bata na
break,idan an tashi time din ya
tashi daga office zaizo ya
dauketa,idan da matsala ga
number ta cati ya miko mata har
2 daya numbersa da address din
office dinsa dayan kuma number
sa da address din gidansu,ya
nuna mata komai, ai kuwa ta
Adana komai a bag,har ss1A aka
rakata.
Du schl din kallonsa maza da
mata keyi har ya fita,direct office
ya wuce company da yake aiki,
ita kuwa student mata da maza
sai kallonta akeyi gata yar fulani
me kyau ja ja fara fara,ba abinda
ke basu daria irin hausarta da
bata fita saboda tafi jin
fulatanci,haka take hada haukan
turancinta tayi har daria ake
mata amma ita ko a jikinta, kuma
baza ta taba shuru ba domin tace
in tayi shuru ta zama jaka ta
karshe dole tayi magana tafi iya
komai da wuri kar a rainata.ga
yan ss3 sunga ahmad yayan yan ss3 sunga ahmad yayan new
student wasu da yawa suna
sonsa,dan haka suka dinga kula
rahma dan ta musu hanya ko
zasu sami shiga,haushin su ma
takeji har wani epizi take tana
sharesu dan sun bata mata rai
dan me zasu so yayanta.amrata
ta nijar tana can tana ta kiran
dady on phone tana kama kafa
akan aurenta da ahmad dan ta
matsu dady yayi maganar,Wanda
uban gayyar ahmad bai ahmad bai San
komai akai ba.dady da momi
kuwa kara kaunar amrata sukeyi
tare da kwantar mata da hankali
cewa in dai za ayi bikin mimi nan
da 8mnths da na amrata da
ahmad za a hada,murna wajen
amrata ba a magana.
Rahma dama an saba zuwa kiwo
tun safe sai magrib dan haka yau
gashi shine na farko da ta zauna
a schl tun 8am sai 5pm aka
tashesu ko gajiya bata ji tayi ba
dan dama ta saba,wajen gate
take so itama ta fita inda taga
student na fita dan so take ta jira
yayanta ahmad yazo daukanta,ta
taho hanyar waje kenan taga an
wangale gate din schl din motar
ahmad ta hango ya cinno
hancinta cikin schl din,mutane
caaa akayi ana kallo waye
wannan daukan student bazai
parking a waje ba sai ya shigo
ciki,
Da fara’arta ta karasa wajen
motar ta bude ta shiga wani
sanyi da kamshi ya daketa,har
lumshe ido takeyi,barka da
yamma yaya ya aiki,lfy kawai yace
yaja bakinsa yayi duf,suna zuwa
gida ta wuce part dinsa yayi
bangaren su mum,yana zuwa
jikin mum ya kwanta yana wash
na gaji,momi ce ta tabe baki tace
ba dole ka gaji ba ka dorawa
kanka wahala daukan nauyin
mutum azamanin nan kuma
marar asali ma,bata rai yayi tare
da ficewa daga palon cikin fushi
dan ko abincin ma bazai ci
ba,dakin dady ya nufa,da ammar
suka ci karo zai shiga palon
gaisawa sukayi suka danyi hira a
tsaye,bro ina zaka naga yanzu ka
shigo cewar ammar,ahmad yace
kasan su mum wlh na rasa me
yarinyar nan ta musu ni
tausayinta ma nake,ammar ne
yayi murmushi tare da jinjina kai
sai hakuri bro,kaci gaba aikin
lada kakeyi sosai kar ka
gajiya,bari naje wurin dady
cewar ahmad,ammar ne yace cewar ahmad,ammar ne yace ai
dady baya nan ka manta zaije Cairo
za a masa medical check
up,ahmad yace na manta ne nan
da 3werks zai dawo ai,part din su
mimi ya shiga ya duba su ko sun
dawo aikuwa du suna Palo zama
yayi cikinsu duk da shi bame
surutu bane na 30mnt ya mike ya
wuce part dinsa,momi kuwa
ammar na shiga ta tareshi tace
my son kalli bro dinka ya susuce
ya zama banza sai wahala yake
da yarinya,ba a isa a fada masa
gaskia ba sai yayi fushi ya fita ko
abincin bai ci ba,Allah shirye shi
ya ganar dashi dan sai
addua,ammar shi mum ma daria
suke bashi wlh amma haka ya
dingawa momi dabara da wayo
har hankalinta ya kwanta,tace to
shikenan ai sai yayi ta yi,dan na
daina masa ma zancenta sakaran
banza,a ranta kuwa tace ana
aura masa amrata zata kori
yarinyar daga gidan,dan tasan
amrata baza ta bar rahma gidan
ahmad ba.
Bangaren rahma kuwa tana
shiga part din uniform dinta ta
cire ta wanke su kal sannan tayi
wanka,ta shirya cikin wata
shadda dark pupple ba wata
kwalliya tayi ba powder tasa da
Jan baki ja kadan,dakin ahmad ta
shiga yau domin ta gyara masa
gaskia ya hadu dan ta kusa
suman tsaye dan kyan room
din,gaba daya kamshi ne ke tashi
komai Fes amma haka ta kara
kalkale saman ahmakalkale saman ahmad din
duk,komai kamshi yake da
sheki,sallar magrib tayi ta fada
kitchen,littafin koyon girkinta ta
dakko dan tun a kauye tana da
abinta wata da take zuwa birni
ce ta ke siyowa  dan haka
itama ta siya guda biyu daya na
abinci daya na juice,
Miyar kwai tayi tasha naman
rago da pounded yam,sai tayi
farfesun kifin gona ta hada fruit
salad,sunyi dadi sosai,komai
kadan tayi dan ahmad baya cin
nata,dama rahma akwai son a iya
abubuwan birni musamman
girki da kwalliya burinta kenan
shi yasa take cikin farin ciki tare
da godewa Allah da kuma yiwa
ahmad addua kullum,jera komai
tayi a dining dan tace itama ta
zama yar gayu yanzu. Sallar isha
tayi ta fito wurin dining zata ci
abincinta,ya ahmad ta hango
zaune a palon kasa yana latsa
waya abin mamaki bata ga yayi
wanka ba, har wajensa tazo ta
tsuguna tace yaya ga abinci ka
dandana kaji na iya Allah, shi
yanda take kwantar da Kaine ke
bashi ma daria,ya gaji da tayin
girkin da take masa bai taba ci
ba,gashi yau dama baici abincin
mum ba,yunwa yakeji gwara yaci
na rahman yau dan bazai iya fita
restaurant ba,danshi sai dole
yake cin abinci waje sabo da
kyankyami.
Umarni ya mata da ta zubo masa
ta kawo a gajiye yake bazai je
dining ba,cike da murna dining da
zumudi ta zubo komai daban
daban,fruit salad kuwa zuba nata
tayi a cup ta kawo masa jug din
gaba daya,jiki na rawa yau ya
ahmad dinta zai ci girkinta dan
bata da burin da ya wuce ta
faranta masa tare da
birgeshi,kadan ya fara ci yaji
wani azababban dadin dan
rabon da yaci girki yaji dadi haka
bazai iya tunawa ba,zagewa yayi
ya Lodi abincinsa,fruit salad
kuwa sai da ya shanye shi tas ya
masa dadi,yayi mamaki yarinya
15yrs da iya girki haka,sama
yahau yasha mamakin gyaran
dakin dan yasan rahma ce
tayi,cikin nishadi ya salla wanka
yayi nafila ya zura kayan bacci ya
haye bed sai bacci,rahma kam
wanke kwanukan tayi ta gyara
wurin da kitchen,ta shige
daki,wanka ta sake itama tasa
rigar bacci ta dauko littatafanta
tayi karatu,inda bata gane ba ta
barshi da safe ta tambayi ya
ahmad,
Bacci ta kwanta amma bacci yaki
zuwa mata sai tunanin ya ahmad
take tana daria ita kadai,a haka
har bacci ya saceta,washe gari
7am ta shirya tana jiran ahmad
dan yana part din mum kamar
kullum,a wajen ajiye motoci ta
jirashi,yau bai Dade ba ya fito sun
Riga kowa na gidan fita da
wuri,suna isa schl kafin ta fita ta
Ciro liffan inda bata gane ba tace
yaya dan gaya min nan ni ban iya
ba,wata uwar harara ya balla
mata yace u r very stupid rahma
muna gida daya same part ki
kasa daukowa na koya miki sai
now,sai ki jira Saturday Sunday
me miki lesson tazo ki tambayeta
ko wata ta koya miki a schl,sha
sha sha wallahi kinji na rantse
baki isa kisa nayi asarar kudi
ba,dole ki iya kisan me kike dole
ki kawo min good result,in ba
haka ba wlh garinku zan maidaki
ko na aura miki wani na
huta,aure zan miki kawai kuma
gate man zan aura miki,dakikiya
fice min a mota,idon rahma ya
cika tab da hawaye kallonsa tayi
rau rau zatayi magana yace get
lost,tsawa ya buga mata out.da
sauri ta fita tana share
hawaye,yaji tausayinta bai san
dalili ba baya son kukanta,amma
dole ya tsoratar da ita,
Yau rahma kawai dai tayi
karatune amma hawaye take ta
yi,ita ba fadan ne ya sa ta kuka
ba ta batawa yayanta rai,ita me
son sashi farin ciki ta sashi Bacin
rai dole ta faran ta masa,wata
student ce husna tana son
rahma,gata nutsatsiya ta
gari,wajen rahma tazo tace sister
lfy?ita dai rahma cewa tayi umh
umh yayana ne yake fushi dan
ban iya aikin jiya ba,murmushi
husna tayi tace wannan
baturen,me kyau?banza rahma ta
mata dan me za a yabi yayanta ai
ita ya dace ta yabi abinta. to fa
kaji su ramata,husna yar gidan
wani senator ce me ci akwai kudi
amma suna da tarbiya su uku
iyayansu suka Haifa,aiman,hus
na,nusaiba.
Husna ce ta koyawa rahma
komai ta iya sosai,har abubuwan
turanci take ta koya mata dan ta
iya,ta kuma yi mata alkawarin
koya mata English sosai,ai a
ranar suka kulla kawance da
husna,ko ina suna tare,husna ta
bawa rahma lbrn gidansu,amma
rahma kawai lbrn gidan su
ahmad ta bata kuma tace ita
daga kauye suka daukota ita yar
uwarsu ahmad ce,amma ahmad
yafi ji da ita .
Suna zaune a class rahma tanajiSuna zaune a class rahma tanajin
sauran yan class mata suna ta
lbrn period wato jinin
Al,ada,kowacce na fadan kalar
nata,can wasu sukace ai in
bakayi baza ka taba haihuwa
ba,take rahma ta shiga firgici,da
tunani domin gashi ta girmi
wasu yan class din amma sunce
suna period ita kuwa batayi,bata
taba ba,take
www.littafanhausane.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE