MARAICIN RAHMA 5

Hausa novels
MARAICIN RAHMA

                      Chapter5

www.littafanhausane.com.ng
Kanta a sunkuye dan tsoron ya
ahmad takeji ta masa laifi,da kyar
ta iya cewa sannu yaya ya
aiki,yau radau taji yace
alhmdllh,ta danyi mamaki,kallonta
yayi yaga hijab dinta ya karkace
bari daya,hannu yasa ya gyara
mata,rahma sai murna take a
ranta yayanta ya daina fushi da
ita,a hanya ya tsaya ya musu take
away na shawarma,hambugga
da kaji,suna isa gida ya bata
kayan yace kici iya yanda zaki iya
ci ba sai kinyi girki ba,Dama a
gajiye take taji dadi,part din mum
ya wuce can yaci abinci suka
taba yar hira ya kira dady a waya
shima,daga nan part dinsa ya
wuce,wanka yayi yasa jallabiya
fara kal ta masa kyau,saukowa
yayi kasa,rahma ya gani kwance
a kujera tana bacci hankali
kwance,tayi wanka sanye take da
doguwar Riga yar kanti marar
nauyi,yarinyar na birgeshi wajen
tsabta da kula da kai,agogo ya
duba yaga 6pm ta kusa,baya son
tashinta dan ta gaji yaga
alama,sallah ya fita yi ya dan
tsaya wajen ma’aikatan gidan ya
musu kyautar kudi,dama ahmad
akwai kyauta,yayi sallar magrib,a
hanya sukayi waya da frnd dinsa
shahid zai zo wajensa yaga yarsa
kanwarsa rahma dan ya fada
masa komai,
Bacci ya sameta tana tayi bata
tashi ba,gashi har sunyi sallah
tashinta ya fara yi ya dan bigi
kafarta,a hankali ta bude sexy
eye dinta Wanda yayi ja sabo da
bacci,da sauri ta mike yace hey
hey relax. Je kiyi sallah to kawai
tace ta wuce daki,sallah tayi ta
sake wanka dan jikinta weak
takejinsa shi yasa ma tayi
wankan,manta ta shafa,sai
powder ta shafa Vaseline a lips
Dinta ta dauko wani dan hijab
dinta me kyau kalar rigar ta sa,ga
a cuci anyi sai tayi kyau,Jakarta ta
schl ta dauka Arabic da boko ta
koma wurin ahmad,
Tana fita taga shahid sai hira
suke suna daria,a nutse ta karasa
dinining ta ajiye bag din ta karasa
wajensu rusunawa tayi ta gaida
shahid cikin nutsuwa,shahid sai
kallonta yake dan yaga baiwar
kyau ga hankali da
nutsuwa,kitchen ta wuce kamar
matar gidan ta hado masa drinks
da ruwa,shi kanshi ahmada ruwa,shi kanshi ahmad yaji
dadin abinda tayi,shahid ne yace
kanwar ahmad ya schl murmushi
tayi tace lfy lau,ya abokina amma
baya zaneki ko daria kawai
tayi,shahid sai janta yake da
surutu har sai da ta saki jiki
dashi ta fara bashi lbrn schl da
kawarta husna,shi hausarta ce
ma ke bashi daria dan fulatanci
tafi iyawa,
Tace kaga kawata fa daya,yace
why daya jal,to ai ya ahmad ya
hana yin kawaye fa,kuma hana yin kawaye fa,kuma ma su
bana sonsu,zaro ido shahid yayi
yace sabo dame?ai sune suna
damuna sai na hadasu da
yaya,kaga yan ss3 du sunce
sonsa sukeyi fa,ni bana musu
magana ma,tunda suke hirar
ahmad ya kafeta da ido a ransa
yace wannan daga ji mijinta zai
sha kishi,shahid kam ya fuskanci
tabbaas rahma na son ahmd ko
ba da yawa ba ta kamu,tabbas
ahmad zai iya sonta nan
gaba,yayi fatan haka ta faru dan
yarinyar na da hankali,
Shahid ne yace ta kawo books
nata suyi karatu,ya koya mata
abubuwa da ma,kuma ya
fuskanci tana da
kwakwalwa,shima ahmad yafi
kowa mamakin irin basirar
rahma,gata a kauye amma tasan
abubuwa da yawa,musamman
Arabic, yaji dadi kam.haka har
shahid ya wuce kowa ya wuce
room nasa bacci.
Rayuwa ta ja rahma yanzu tana
ss2 first term,tana kokari sosai
dan tana zuwa 3,4,ko ta 5 a class
Dinsu,gashi yanzu english ba laifi
ta iya alhmdllh,sosai ahmad ke jin
dadi baiyi asarar kudi,ba lafiya da
time daya bata kanta ba,islamiyya
kuwa hmm ba a magana tayi
zarra a bangaren ta 1 takeyi,ga
wani fari data karayi skin dinta ta
murje,har yar kiba tayi
kadan,yayin da hips suka kara
budewa tare da cukowar na
shanu,samari kuwa sunyo caaa
amma ko kallonsu batayi dan son
ya ahmad ne dankare a
zuciyarta,kullum a tunaninsa
take,tayi addua amma ina kullum
karuwa yake,su rahma an
waye,tayi fresh,daga kallonta
kasan tana hutawa kuma ana
mata abinda takeso,husna kam
tuni ta gano rahma son yaya
ahmad take,daga yanda take
nuna kishi karara bata so wata ta
kallar mata shi,shi kuwa ahmad
tuni ya samowa rahma driver shi
ke kaita da dakkota dan shi busy
yake yanzu,shakuwa sosai sukayi
da ahmad,sai abinda take so ake
mata,hakan bai hanata masa
tsananin biyaya ba dan ahmad
baya wasa da ita ko kadan bare
ta rainashi,Kawancensu yayi nisa
da husna amma tana tsoron
yayanta ta hana husna tazo mata
visiting gidansu itama taki
tambayar ya ahmad,bangaren su
mum kuwa har yau dady bai
sauko daga fushi da rahma
ba,amma dai ya rage dan yana
amsa gaisuwarta,momi ta rage
sosai tana kula yarinyar me
nutsuwa ce har murmushi tana
mata yanzu in zata amsa
gaisuwar,ba karamin dadi rahma
da ahmad keji ba,haka su ammar
ma,
Dady yaje nijar sunyi maganar
auren ahmad da amrata,Mimi ma
wani lawyer zata aura usman
matashi me kyau ga hankali ga
kudi,dan haka dady ya yanke
bikin Mimi za a hada da na
ahmad nan da 3months,ahmad
kamar ya hadiyi zucia sabo da
bacin rai,amma dole yayi
biyayya,rahma bata San zancen
auren ba,amma tana yawan
ganin ya ahmad dinta cikin
damuwa,tunani take taya zata
tambayeshi meke faruwa amma
ba hanya,shahid friend din
ahmad kam yana zuwa sosai sun
saba da rahma,me wa rahma
lesson meena tuni rahmalesson meena tuni rahma ta
koreta akan in yayanta ahmad ya
zo wucewa tana Kallar mata
shi,shi yasa tace ita ta iya komai a
sallami me lesson lol ,har yau
rahma ta gaji da jin lbrn period a
schl ita kam batayi,ta matsu tayi
amma shuru abin na damunta,
Kamar kullum yau drivern rahma
ya fadawa oga bazai zo ba zaije
garinsu ganin iyalinsa ba lfy bai
San ranar dawowarsa ba amma
zaiyi waya,kudi ahmad ya bashi
da yawa tare da kayan
abinci,rahma kuma ta kwaso
kayanta da taga zata iya badawa
ta bashi ya kai gida ko da masu
so,yayi Murna kwarai da gaske,
Cikin shirin makaranta take tana
jiran yayanta a palon
kasa,sakkowa yayi cikin wani
danyen boyel fari kal hula baka
da takalmi baki,yayi matukar
kyau,anan ta lakace tana kallonsa
har ya zo daf da ita bata kula ba
sai kamshi taji,let’s go yace da ita
kawai,firgit ta dawo tare da saita
kanta suka fita kowa ya gansu
yasan sun dace,
Tunda suke hanya ya ahmad ya
kula sai cije lips takeyi tana dan
rike ciki,ke are u okey?kai ta
daga tace yea,yace good rashin
jini ya motsa kenan,cike da
shagwaba tace a’a yaya,haka
kawai take jinta in tana gaban
ahmad kamar jaririya,shi ahmad kamar jaririya,shi yasa
bata San sanda take tabara ba,
Yana kallonta bai ce komai ba har
yayi parking a schl din yace make
sure in da Matsala kinkirani a
wayar wani teacher na baki kudi
ki siya recharge card kisa,ban
amince kiyi waya da kudin kowa
ba,zan siya mini taki very soon
sai time yayi dan ban son
shashanci shi yasa na hanaki
phone,kai kawai ta kada sai class,
Tunda ta shiga class mararta ta
rike,kuka take sosai,an kaita
chemist din schl din amma a
banza,dole ta bada number da
kudin kati wani teacher ya kira
ahmad ya fada masa,1pm yayi
sallar juma’a kenan kasansallar juma’a kenan kasancewar
Friday ce,da sauri ya bar
masallacin, ya taho schl din,sai
kuka take tana wash
yayana,marata yaya,salati kawai
take tana kiran yayanta,daukanta
kawai yayi cak ya sabata a
kafada,motarsa yasa ta sai wani
private hospital me tsadar
gaske,iya haduwa ya hadu,gado
suka bata suka dukufa aiki
kanta,shi kam gogan ya shiga
tashin hankali me tsanani,ya rasa
inda zaisa ransa babynsa ba
lfy,can wani likita ya fito ya
sameshi,yace ka kwantar da
hankalinka, ba wani ciwo
bane,period zata fara,maybe yazo
mata yau,gobe amma yanzu
munyi abinda ya dace ta munyi abinda ya dace ta samu
sauki bacci take,amma bazan
sallameku yau ba sai nan da 1wk
ko 5days,dan in ta koma gida da
matsala,kaje ka shirya jiyya
yanlabai,
Wani ajiyar zuciya ya sauke
sannan ya koma gida ya ciko
mata karamar trolley da kayan
amfani dai na me jinya,
Bacci take sha,kara fita yayi ya
cika room din da aka ajiyeta da
juice kala kala,milk,kayan
tea,fruits,nama gashashe,da
abinci laafiyayye,gida ya koma
yayi sallah ya huta, wajen
magrib yawa Momi da dady
karyar sun tafi kauyen su rahma
zai kaita ganin danginta,da yake
su gidansu akwai freedom ba
Wanda yace komai sai adawo
lfy.dady ne kadai yace son amma
flight zaku bi,in kaje ka duba
aikin nan ka gani ba
Matsala,insha’Allah yace tare da
jefa jakarsa a wata azababbiyar
motarsa tafi 12millions kudinta.
Su momi sun yarda ya tafi kauyen
su rahma sun San ahmad baya
magana biyu,gashi yace flight zai
bi sai addua suka masa,yana fita
direct hospital ya nufa da
jibgegiyar motarsa,ahmad kwai
zurfin ciki ko shahid bai fadawa
ba,a hanya ya tsaya ya siyi carton
din always pad me kyau sai kace
wacce ta haihu haka ya lodar
mata pad,tare da new panties
masu kyau da tsada,dakin ya
shiga ya tarar bacci take har yau
bata tashi ba,wata nurse ce ta
shigo tace sir a kula da ita zata
iya farkawa ko yaushe daga
yanzu,magun gungunan ta ajiye
tare da cewa anjima zan dawo
bata medecine Nata,ok kawai
yace,
Bata Dade da fita ba ta farka
bude idonta ke da wuya ta ga
ahmad zaune gefen
gado,hawaye ne suka gangaro
mata kawai ta tausayawa kanta
bata da kowa me sonta sai
ahmad,kusa da ita ya kara
matsawa tare da shafa
fuskarta,gwiwoyinsa ya sauke
kasa daga gadon yana share
mata hawaye dan ya gane me
takewa kuka,so sorry my little
sis,me kike so?waya tabamin
ramata ta,hannunsa ya Dora kan
mararta tare da cewa ke Mara ki
daina wahalar min da baby
ramata ta ki rasa wa zaki sa kuka
sai daughter na,ai bata San
sanda ta kama daria ba,kamar a
film,tana mamaki wai dama
yasan sunanta na kauye,amma
kamar baya ji,shi yanda yake
lallashin nata ne ma kamar wata
jaririya,ai take ta kara shagwabe
masa dama me kuka ne aka
jefeshi da kashin awaki sai yi,shi
ko sai fama yake da ita yana aikin
lallashi.
Tashi kiyi wanka baby ramata
make kafada tayi ni wlh yaya
bana son ramata,yace inye yar
gayu me kikeso to,ni little rahma
nake so,murmushi yayi yace
OK,yau kadai ahmad yawa rahma
wasa,kuma dukkansu sunyi
nishadi,
Little sis oya muje kiyi wanka kici
abinci,kar yazo,yaya waye zaizo?
Sam ya manta bata San meke
damunta ba,sharewa yayi yace
kafin doctor yazo dubaki I
mean,tace yaya wai me yasa
meni?yace kawai wai kinci abun
da bai karbi cikinki ba that’s
why,ohhh tace tare da shigewa
toilet,
Ai tana shiga ba jimawa ta tsala
ihu tare da fitowa da gudu daga
toilet,da kyar ma ta dauki towel
ta dauro tayo waje,jikin ahmad ta
fada tare da hugging nasa sosai
a rude take,jikinta sai rawa yake
shi kam gaba daya ji yayi duniyar
ta kife dashi ta masa daurin
butar malam,dan rungumenshin
da tayi ya jefa shi wani halin,ya
rasa dalili duk mata masu kyau
da gayu gasunan yana ganinsu
amma ko a jikinsa,amma duk
sanda ya kalli surar da allah yawa
rahma sai ya girgiza,sai yasan shi
namijine,bare gashi ta kai ga
cukwikuyeshi,da kyar ya
banbareta a jikinsa,lfy yace da
kyar tace wlh ina tsugunawa
nayo fitsarin jini,wlh yaya fitsarin
jini,shike nan kayan cikina sun
narke,hanta ta,ko kidney waya
sani ta karasa tare da rushewa
da kuka,
Shi kam ahmad bai San sanda ya
kwashe da daria ba,tsayawa tayi
tana kallonsa har ya gama,dariar
ta masa kyau,kasan kafarta ya
kalla ai kuwa jini nata diga,dis dis
daga kasan rahma,du tiles din ya
baci,tana gani ta saki wani
kukan,
Ahmad ne yace saurareni kiji
rahma ke baki San period ba
jinin haila da hukuncinsa wai?
daga kai tayi tace nasan
komai,yace to shine fa cutar
taki,ai sai rahma ta fashe da
daria tana ta tsalle tana
murna,kamar an mata bushara
da aljanna,ya ahmad kallon ikon
Allah yake kawai,kafadunta ya
rike ya turata toilet,pad ya Ciro ya
bude ya mika mata tare da new
pant,da ruwan zafi tayi wanka
tasa pad dinta cike da
murna,tana fitowa har cleaners
sun shigo sun mopping room
din tare da kara wanke toilet
kamshin dadi ke tashi kawai,Riga
da skert na atamfa tasa green
and yellow dagwas da ita,ta and yellow dagwas da ita,ta fesa
turare ta dane kan
gadonta,ahmad ya gyara jakar
kayan da kayan data cire,sallar
isha yaje yayi ya dawo,tea ya
hada musu da kansa yake bata
tana ci shima haka,har suka
koshi rahma sai murmushi takeyi
kasa kasa,yana kallonta,ya rasa
murnar da takeyi,itakam dadin ta
fara period take,itama ta fara period ,itama ta
girma,ba shegen da zaice mata
kwaila a schl,ga kuma dadin
yanda ya Ahmad ke tattalinta,ji da
ita,kuma ya daina daure mata
fuska kamar da itakam wannan
jinya ta mata dadi da haka ake
jinya da taso a dinga kwantarta da ita a
hospital tana kallon Ahmad dinta
kusa da ita kullum.
Dago fuskarta ahmad yayi yace
lfy kike kuwa little sis sai daria
kike,ko a kira doctor?kunya ce ta
kamata ta,kara kyalkyalewa da daria tare da boye fuskarta akan
bed.
Yau kwanansu 3 a hospital kuma
yaune husna tace zata zo
hospital dubiya,dan rahma ta
karbi wayar ahmad tasa number
husna ta kira ta fada mata,kamar
kullum yauma tun safe ahmad ya
tafi gidan frnd dinsa Hussain dan
acan yake wanka da komai
Hussain ne kadai a gidan that’s
yamma rahma ta zata gida yake
zuwa,4:30 bai dawo ba rahma ta
Shiga damua,sai ga sallamar
husna ahmad yana bayanhusna ahmad yana bayanta tare
suka shigo dan a hanyar
shigowa room din suka
hadu,rahma Sam bata kula da
shugowar ahmad ba ta kwala
ihu tare da kankame husna tana
frndy dan ubanki ke na
fara,husna ce tace me kika fara
au baki gane ba banza bakya ja
to ALHAJI me jar mota ne
yazo.nan husna tasan tabbas
bata da masaniya akan shigowar
ahmad rada mata husna tayi
yayanki na room din nan u have
to be very careful,watch ur
tongue, kalli kofa,ai kuwa ahmad
ya nade hannu daya a kirji ya
jingina da bango yana jinsu
amma sai yayi kamar waya yakeyi
ma yana hello yea ina jinka ya
fice daga room din a dole shi
waya yake,
Su kam sai murna Allah yasa bai
jisu ba,nan suka zube suna lbrn
schl,ahmad ne ya dawo gaban
bed din yazo ya sa bakinsa saitin
kunnen rahma yace me zaki ci?
itama rada masa tayi a hankali
tace naman rakumi,ya sake rada
mata yace am no
kidding,murmushi tayi tace du
abinda zaka ci,rada mata yayi
frnd naki fa?ta kara rada tace
same with us.tafiya yayi Wanda
husna tuni ta saki baki dan bata
ji me suke cewa ba sai mamaki
takeyi ko sun fara luv ne amma ta
share zancen suka Dora da
hirarsu.
Ahmad ne ya dawo har husna ta
mike yace abincin fa tace na
koshi driver na jirana tnx,haka ta
musu sallama ta wuce
Ahmad ne yaja nasa ya fara ci
rahma tace yaya yau baza kaci
dani ba,ALHAJI me jar mota yazo
ai sai kuci tare,kunya ce tasa
rahma kamar ta nutse
wajen,dama yajisu yaji abinda
tace amma ya nuna bai gane
ba,stop thinking and eat ur food
shugaban marasa kunya ta
Nigeria,
Nan fa ya hau masifa da
sababi,yanzu da wani gardin ne
ya shigo da tuni sunji kina period
ke bakya shuru ko? Ke ga
tantiriya yar makaranta,Allah
kaiki schl ki fadawa mutane kiga
yanda zan miki stupid
kazama.rau rau tayi yace oya eat
b4 I give u a dirty slap,fara ci tayi
tana kebewa tare da shidewa
zatayi kuka,tana saka loma daya
ta rushe masa da kuka me tsuma
zucia sosai,tausayinta yaji sosai
amma dole ta nutsu,ko kulata
baiyi ba sai kuka takeyi haka
doctor yazo ya dubata yana
tsokanarsu yau ya gansu a
rana,nurse ma haka,ita kuwa taki
cin abincin sai kuka takeyi,ita jin
dadinta da ya Ahmad tun ranar
da aka kawota hospital,amma du
3days din kawai ubanta yake
ci,da tayi abu fada zai mata sai
tsawa.shi kuwa tausayinta ne ya
mamaye zuciyarsa amma ya share
ya dakko waya yana latsawa
kamar bai San me takeyi ba,a
haka har bacci ya kwasheta sai
ajiyar zucia takeyi a baccin,bargo
ya rufa mata tare da gyara mata
kwancia yace rigimammiyata
kenan.
Yau sun cika five days a hospital
rahma kiba ta kara da kyau
tsabar yanda ahmad ke kula da
ita gashi kusa da ita kullum
hankalinta kwance,a yaune kuma
period din rahma ya dauke mata
dan haka tayi wanka Dana tsarki
ta tsantsara kwalliya tayi kyau
tasa doguwar rigar leshi me
tsadar gaske green and golden
tayi kyau ainun abun ba a cewa
komai naso kun ganta readers ta
dau jambaki red earing tasa
golden kawai ta fesa perfume,
tayar da sallah tayi ahmad ya
shigo room din cikin shigar wata
dakakkiyar shadda fara kal
dinkin da kadan ya wuce
gwiwarsa ga wandon dai dai shi
pencil na zamani ba kuma
tsukake ba me fadi ba normal
pencil na maza aka dinka,yayi
kyau sai kamshi kansa ba hula
sai sumarsa daya Tara amma
bata yi yawa ba da sajensa da
dan gemu yasha gyaran fuska
abinka da fari kamar bature da
ka ganshi kaga cikakken
wayayye,dan birni,dan kwalisa
dan gayu da tsafta wanda kudi
ya ratsa da hutu dan madara
wanda ke kwana a a.c duk inda
ya keto sai an kalleshi,mota ya
karbo daga carwash daga nan ya
karbo wankin kayansu daya
kai,tunda ya shigo room din yaga
rahma na sallah wajen doctor ya
koma ya rubuta musu
sallama,kafin ya dawo rahma ta
cire hijab din sallar da ta idar ta
linke tasa a jakarsu ta dauki gyale
golden dan dai dai da ita ta kafa
dauri kamar na gwagwaron
amare ta rataya gyalen,ahmad
sun shigo da doctor suna daria
ai ya kusa suma da yayi arba da
rahma yanda taci wanka kamar
wankin inji,doctor kuwa ido ya
kafeta dashi a ransa yana inama
inama lolx,ahmad ne ya kula da
kallon da doctor kewa rahma
yana lashe lips,da sauri ya ce little
sis anyi discharging namu je
waje wurin motar mu tana
parking space,to tace tare da
ficewa daga room din,bin
hospital din tayi da kallo tace kai
abuja tayi jiba hospital kamar
hotel har yafi hotel kyau,ahmad
ne ya bude booth yace get in d
car,ya hade rai yayi kicin kicin da
fuska. tofa ahmad lfy kuma?
A wani restaurant ya tsaya suka
shiga ciki matan ciki sai kallon
ahmad suke yayin da mazan suka
fi karkata ga rahma,wasu kuma
su duka ake kalla yanda suka
hadu dole a kallesu,
Ahmad yanda yaga anbi rahma
da kallo kamar a lashe mata
kurwa yasa ya fasa cin abinci
wurin,take away ya musu,sannan
ya shiga mall yayi shopping sosai
rahma tana mota ya hanata
fita,gida suka nufa a mota sai
tsaki ahmad yakeyi har suka isa
gida,direct part din momi yayi
itama rahma part din ahmad ta
nufa.zaune familyn ahmad suke
suna ta hira sosai kowa na palon
dady,ahmad ya mike zai wuce
part nasa dady ne ya dakatar
dashi kai ahmad ka fara shirin
zuwa Dubai domin hado lefen
aurenka da kayan dakin Mimi,yar
uwarka zaka aura dole kayi lefe
me kyau,momi ta kara da cewar
amrata gata yar gayu wayayyiya
kasan dole baza ta sa kaya
marasa tsada ba,to kawai ahmad
yace ya bar palon zuwa
sashensa,zazzabi me zafi ne ya
rufe ahmad,idonsa yayi jajir zallar
bakin cikine a zuciyarsa,dan ma
ahmad me addua ne da karatun
Quran. Ya rasa wa zai tayashi
kuka,wa zai fadawa ya samu
sauki,shi kam bai iya fadawa
frnds matsalar rayuwarsa
ba,mutum ne me sirri,da
kiyayewa tsakaninsa da frnds
hirar duniya kawai
tsakaninsu,gwara ma shahid
sunfi close yana iya fada masa
wasu.
Zazzabi yawa ahmad zafi a nade
yake cikin bargo me taushi yana
rawar sanyi,rahma kuwa tunda
ta shigo ta hau gyaran part din
nasu sai da ta gyara ko ina kal kal
sai kamshi ke tashi da kyalli,room
din ya ahmad ta nufa iya nan ne
bata gyara ba kuma shima ai
dole ta gyara mai,sallama tayi da
nocking amma shuru,kawai
turawa tayi tare da shigewa
toilet nasa,dan ta hango ya
ahmad kwance amma bata lura
da yana rawar sanyi ba zatonta
bacci yake sha kawai tunda tasan
lfy suka dawo,
Toilet ta kalkale masa
shima,sannan ta fito room din ta
share da mopping din ko ina ta
shirya komai inda ya dace,sai
kyalli da kamshi haka ta gyara
upstair ma shar bedsheet ne
kawai bata canja masa ba coz
yana bed din yana bacci,
Dai dai jikin bed din taje da ta
karewa ya ahmad kallo ko taji
sanyi a ranta,ko ba komai ta
dinga tariyowa tana kallan zallar
kyawunsa,
Tsayawa tayi gaban bed tayi
tsuru,daga baya ta gano kamar
fa vibrating yakeyi shi kadai
kamar Wanda akewa shocking
da wayar lantarda wayar lantarki kaf
kaf,lumfashi yake ja da kyar,ai da
sauri rahma ta yaye bargon
kadan,subhanallah tace tare da
sakin kuka marar sauti,yau farin
cikinta ba lfy,
Yayana?yaya?ya ahmad lfy me ya
faru,da kyar ya mata nuni da ta
dauko masa magani da
ruwa,drowar da yayi pointing da
yatsansa ta duba jiki na rawa ta
kawo masa ya sha ya
kwanta,zama tayi a gefen bed
din tana jira taga yaji sauki,kin
fita ko ina tayi duk sallolin ma a
room din tayi,tana idar da sallar
la’asar taga ahmad ya yaye
bargon daya rufa ya kara karfin
ac,da ganin haka tasan zazzabi
ya sauka,kitchen taje ta shirya
masa paten dankalin turawa yaji
hanta da kifi me ruwa ruwa.
sai
lemon tea data masa ta kawo
masa,yaci ya sha yaji dadin girkin
sosai,mikewa yayi ya Shiga toilet
kafin ya fito rahma ta canza new
bedsheet ta kwashe kwanikan
daya ci abincin wanka yayi ya shirya cikin
jallabiya baka ya fara sallar da
ake binsa,bayan ya idar Qur’an ya
karanta sosai tare da addua dan
yaji sanyi a ransa,kan bed ya
koma ya zauna yana tasbihi ga
wasu hawaye na fitowa daga
idaniyarsa,rahma ce ta shigo da
wani glass cup hadadde
kankana,apple,pineapple, ,inibi
da banana tayi blending tasa
fresh milk liquit ta kawo masa ko
zaisha,ganin hawaye a tsakiyar
fuskarsa yasa tai saurin karasawa
ta a jiye cup din,
Yaya lfy,me ya sameka,shi kuwa
da sauri ya goge kwallarsa kar ta
gani amma ya makaro,yaya me ya
bata ma rai?nothing kawai
yace,yaya ko nice?ya kada mata
tare da cewa no,ammar?a’a
Mimi?no su salma? no office? A’a
frnds?kada kai yayi alamar ba su
ba,tace momi da dady?yeah yace
mata a hankali,kamar wani dan
yaro
Yaya case din a kainane ko? Yace
ba naki bane,dadi taji tace eyya
yayana am so sorry iyaye sai
hakuri,dole a musu biyayya,ko
me sukai maka ba a fushi dasu
dole a bi su a hankali in dai har
bai sabawa Allah ba,haka ta
zauna ta dinga wa ahmad nasiha
kan girma da darajar iyaye,yaji
sauki aransa ya kuma samu
nutsuwa a ransa,lallai rahma
mace ce ta gari abar so,ga addini
komai ta hada gashi ta taso tayi
rayuwa ita daya,lallai Wanda Allah
ya shirya ko a INA yake ko a ya ya
taso tofa shiryayyene ga Wanda
suka taso ma cikin gata da iyaye
basu kai ta hankali da addini
ba,ga sanin ya kamata kai
masha’allah rahma du a ransa
ahmad ke wannan zancen a zuci,
Ita kuwa rahma tana zaune
gefen bed din fruits din ta mika
masa a cup ya shanye ko ba
komai ya samu saukin
zuciarsa,alwala ta dauro tace ya
ahmad taso muyi sallah na tayaka
addua,domin komai in zai zo
Allah ya kawo mana agaji da
sauki,
Allah yana son mutum me yawan
addua sai kaga ya canja ma
komai da mafi alkhairi abinda
baka zataba sai ya faru.mikewa yayi
ta tsaya bayansa sukai ta lafila da
yawa suna addua.
Abin mamaki sai kaga wasu
matsala ta samesu sun kasa bacci
amma sun gagara su mike da
salloli da karatun alqurani da
sauran aikin kwarai domin sukai
kukansu wajen allah, kaga
mutane da yawa musamman
mata baza su Dage da addua ba
ga matsala jingim,wasu ma sai
dai kaga sun kwashi kafa an
kaiwa bokaye malam tsibbu kuka
ayi musu duba da aiki,ga Allah
maji roko amma anki yin
addua,aji tsoron Allah mu daina
shirka jama’a wlh karyace a ciki
gwara ka ki rungumi Allah da
addua shine dai dai.to wasu ma
sallar farilla bata damesu bare
addua da nafila.
Bayan sun idar da sallolinsu
addua sukayi sosai rahma bata
San akan menene ba amma tayi
masa wadda ta dace sosai,tuni
ahmad ya samu jin dadi da sanyi
ransa,direct dakinta rahma ta
wuce,shi kuwa computer ya
dauko ya fara aiki ciki,da safe
kamar kullum baba driver ne ya
dawo daga garinsu.ahmad ne
bayan yaje wurin su dady ya fito
ya tarar da drivern rahma ya
dawo,wajensa yaje suka gaisa ya
masa umarnin yaje ya huta for
3days sabo da gajiyar hanya, sai
Monday yazo ya kai rahma yaji
dadi sosai godiya yayi wa ahmad
duk da haka ahmad sai daya
mika masa kudaden kashewa
gaskia baba driver najin dadin
aiki da su ahmad da
rahma,rahma CE ta fito da sauri
tana duba baba cikin shirin
schl,ahmad ya hakimce cikin
wata sabuwar dalleliyar Benz
tasa yana karewa rahma kallo
yanda yaga ta girma sosai breast
nata sun ciko sosai,ga hips nata
ya fashe abin kallo da
birgewa,fuskarta sai shining
takeyi Dama gata jar fata fara da
ita amma ahmad ya fita fari,du da
dankwalin data daura gashinta
ya fito ta gaban goshiya fito ta gaban goshinta
kwantacce da sajenta yabi ta
gefen kunnenta zuwa keya,baki
luf. Luf me sulbi
Hijab dinta ya kalla yaga da
kadan ya wuce kirjinta,horn ya
danna mata tare da sauke glass
kasa,daria tayi ta daga masa
hannu daga nesa,tace yaya baba
driver nake jira ta kwala da
karfi,da hannu ya yafitota, ta
karasa wajensa dauke da
murmushi harda tsallenta kadan,
yaya banga baba driver ba
kallonta ahmad yake sosai yawan
fara’arta na birgeshi sai kallonta
yake kamar ya lasheta dan me
kyau ce rahma,
Gaban mota ya bude mata yace
get in,shiga tayi ta zauna ya ja
mota,suna hanya ya dauko wani
karamin flask da cup karami ya
mikawa rahma yace tsiyayo min
abin,karba tayi ta tsiyayo sai taga
cuffee ne hadadde ciki,tsiyayowa
tayi ta rufe ragowar na flask din
ta mayar bayan sit,tace gashi
yaya taya zansha ina tuki rahma?
Tana so taji ahmad yace mata
rahma akwai dadi sai taji kamar
aljanune suke fada dan dadi,
A baki ta dinga bashi yana tuki
har tissue ce a hannunta kamar
wani yaro take bawa,ya rage
kadan ciki yace am OK, rike cup
din tayi ta dinga goge masa baki
da tissue,shi daria ma abin ya
bashi kamar wani
danta,murmushi yake sosai har
ta gama,cup din ta daga da
ragowar cuffee ta shanye sai
lashe pink lips nata takeyi irin
tasha ragowar ahmad abin
sonta,ahmad na kallonta ta gefen
ido yana kunshe dariarsa.
Juyawa baya tayi ta dauko flask
din ta tsiyaye ragowar a cup
gashi ahmad yayi parking a schl
dinsu,mika masa cup tayi wai
yaya sha wannan kaji yafi dadi
wai ita dole wayo ta masa dan
yasha ita kuma ta shanye
ragowar tasa,
Ya ahmad ne yace nafa koshi
rahma shagwabe masa tayi rahma shagwabe masa tayi pls
yaya ni Allah sai kasha,kadan ta
bashi ya kurba ta janye cup din
ta shanye sauran,tana ta murna
ta bude motar ta fita,ya juya
motar zai tafi ya tsaya ya mata
horn ta dawo,tana zuwa ya zuge
glass ta zira kanta ciki
tambayarta yayi me kike son ci
yau gashashshen kifi da
chips,kwadayayya ayi karatu
sosai jeki class.ya ja mota ya tafi
ita kuma ta wuce class cikin
nishadi.
Tunda aka kai rahma schl wani
malaminsu malam sagir ya nace
shi sonta yakeyi da ya takurawa
rahma,kullum sai ya kirata in an
tashi daga boko kafin su shiga
bangaren Arabic,
Ta tsaneshi bata masa magana
ko taje wajensa haka zai kari
surutu ta juya ta shige class,abin
ya dameta,so take ta fadawa ya
ahmad yaje Schl din ya masa
warning amma tana gudin kar ta
batawa yayanta rai shi yasa tayi
shuru,
Kamar kullum sun tashi daga
bangaren boko sunyi sallah sun
fara dinner kafin su shiga
islamiyya,malam sagir ya kirata
suna tsaye da sharbebiyar
bulalarsa,yau zai Zane jikin rahma
tunda taki karbar soyayyarsa,ga
wulakanci tana masa dan haka
yau sai yayi maganinta,
Tana tsugune gabansa yana
zabgarta da bulala tana hawaye,
ahmad kuma ya danno mota ciki
yazo kawo. Mata kifi da chips da
tace zatayi dinner dashi,itakam
bata zata schl zai kawo ba ta zata
a gida yake nufi tunda dinner
yace ba lunch ba,shi kam
surprise zai bata,shi yasa yace
mata dinner,
Rahmansa ya hango wani gardi
ya dame mata hijab yana
labta,take idonsa yayi jajir sabo
da bacin rai aiko
Ko gama daidaita motar baiyi ba
ya fito cikin kana nan kayansa
wando jean fari,sai Riga longslip
yayi kyau kamar bature,kowa
zuba masa ido yayi ana kallo cike
da kasaita da isa cike da izza ya
ke takawa ,yana zuwa wurin
malan sagir ya shaki kwalarsa ya
fesa masa maruka biyu a jere ya
shake malam sagir,idonsa shake malam sagir,idonsa yayo
waje kamar zai mutu da kyar
teachers suka kwaci sagir a
hannun ahmad,
Mutane yan kallo har yan waje
sun shigo schl din ana bawa ido
abinci,huci kawai ahmad keyi
yana masifa,wallahi duk Wanda ya
kara taba min sis a schl din nan
sai nayi kararsa cikin harshen
turanci yake magana,da kyar
principal ya lallaba ahmad principal ya lallaba ahmad yana
bashi hakuri dan ahmad yace
cire sis dinshi zaiyi daga schl
dinsu,hakuri akayi ta bashi har ya
hakura da kyar,tarzoma ta lafa an
settling case da student,har sagir
an masa last warning kan
students.
Komawa yayi wajen rahmansa
dake hawaye,tsaye ya mikar da
ita ya dauketa cak kamar jaririyita
yan schl sai kallonsu akeyi sun
birge wasu, wasu kuma sai kishi
suke da rahma suna son ya
ahmad,cikin mota a hankali ya
zaunar da ita ta huta sannan ya
shiga bata kifi da chips da kansa
yana kora mata da lemo me
sanyi,taci ta cika cikinta yace ya
jikin?rahma sarkin daria
murmushi tayi tace normal,
Je class har anyi nisa ana darasi
dan 4pm tayi,masallacin schl din
yaje yayi sallah ya koma mota
kida ya kunna yana ji ya lumshe
ido,kawai abunda yake tunowa
shi ke bata masa rai yanda ya
tuna malamin nan ya damewa
rahmansa hijab kirjinta ya fito
maza kowa na gani gashi a
bainar jama’a ya kunyata masa
ita yana dukanta cikin mutane.
Tsaki kawai yake ja,yana wannan
tunanin har yaga students sun
tashi yana duba agogo yaga
5pm,rahma da husna sai wasu
gun gun student suka taho wai
sai sun gaishe da yayan
rahma,amma wasu dan sukare
masa kallo suka zo,wasu kuma
suna sonsa,rahma ce ta bude
gaban mota tana wash yaya na
gaji hade da jefa littafanta
baya,husna ce tace yaya ina wuni
ya amsa da sakin fuska tabi
drivernta ta tafi gida,ita kuwa
rahma kishi yasa ta daurewa
sauran mata fuska sunzo kalle
mata yayanta,dan tasan sonsa
sukeyi da gulma,
Ahmad kuwa ko kallonsu baiyi ba
bare yasan suna wajen,rahma da
biyu taki rufe kofar su tafi ta
kama yiwa ahmad shagwaba
dan student suji haushi,yayana
kalla yatsana yanda ya ke min
zugi har nan ma ya shauda min
bulala kalla ta nuna masa
wuyanta tare da cire hijab,kamar
zatayi kuka tana lankwashewa
tana yarfe hannu,batasan ta iya
shagwaba sai yau,ta gama
kashewa ahmad jiki,biye mata
yayi yace sorry little na yana duba
wuyanta yana ta wani lallabata,ya
kwantar mata da kujera huta my
little,ta wani kwanta tana cewa
yaya bazan iya rufe kofar ba,da
Kansa ya rufe kofar,students
munafukai na ganin haka suka
watse kowa yayi hanyar
gida.itakam dadi ya kamata tayi
maganinsu shegu,
Suna isa gida yau ya gaji a
gurguje yaje part din momi ya
koma room wanka yayi ya
kwanta yana hutawa,rahma ma
hakan take.washe gari kuwa
suna dawowa ya shirya ya
fice,rahma taga ahmad yasha
wanka da yamma lis ya fice,ta
kasa zaune ta kasa tsaye karfa ko
ahmad zance ya tafi wajen
budurwa,kaji rahma da karfin
hali ta gumi tayi har bayan sallar
isha ta kasa cin abinci,tayi tagumi
kishi ne cike a ranta.
Shi kuwa ahmad shopping ya fita
daga nan ya wuce gidan su
shahid.sai 9pm ya dawo ya iske
rahma tayi tagumi,kaya ta gani
Leda leda a hannunsa,sabo da
kishi ko sannu da zuwa yau
batace ba.
Kallonta yayi yace lfy?lfy tace
kawai,zo yace mata kawai ya
haye sama binsa tayi a baya,har
palonsa na sama a kujera ya
zauna taje gabansa ta zauna a
kasa, naje wajen shahid yana
gaisheki,dadi taji Ashe ba zance
yaje ba,har ta saki rai fara’a ta
fara sosai,ledojin duka ya mika
mata,guda dayace tasa a
ciki.wata ledar ya karba wajenta
yace bari na hada mini
wannan,wata dalleliyar waya CE
ciki a kwalinta Gionee A1plus tuni
rahma ta washe baki,kan kujerarahma ta washe baki,kan kujerar
2seater wacce yake zaune ya
nuna mata kusa dashi yace dawo
nan ki gani,tana zaune kusa
dashi ya hada komai ya nuna
mata komai,rabi tana gani rabi
kuma du halittarsa take karewa
kallo tare da shakar kamshinsa
tana lumshe ido kamar ta kwanta
bacci jikinsa takeji,har wani
gyangyadin dadi takeyi,numbarta
yasa wayarsa ya kira tata wayar
yayi saving da my rahma,yayi
dialing number kiran ya shigo
wayar ya mika mata yace tayi
saving daga wayar dan kar ya ga
me tayi saving da tasa masa my
peace.su rahma an fada da
yawa…
Ledojin yace ta kwashe in taje
room ta duba,tana shiga ta baje
kaya wasu new design arabian
gaunt ne da cosmetics,sai kayan
gyaran gashi su mayukan
gashi,shampoo,hair treatment hair
spray ko wanne kala kala hair
hand drier,hair straightened,sa
koki da bangles,agogo kala 4,ko
wanne kala kala,komai shar,dan
shi ahmad ji yake da rahma
kamar yarsa dan komai a
hannunsa yake dole ya kula da
ita tunda su momi sunki yarda da
ita,kuma sun kasa gane illar
barinsa da ya mace kamar rahma
ya ajiyeta kusa dashi ba
muharammarsa ba ya jira yaga
ko zasu gane hakan ba dai dai
bane a musulunci amma Sam
harkarsu sukeyi,kuma sun kawo
wata zasu aura masa ai ganinsa
gwara a bashi rahma ya aura
duk da ba sonta yake ba zai
riketa.
Kamar kullum abubuwa nata ta
fiya normal wurin rahma yayinda
ahmad ke cike da kuncin aure
yana matsowa daf,inda Mimi take
ta gyaran jikinta da shirye
shirye,amrata ana nijar tana nata
dan ta matsu ta dandani zumar
ahmad ta dalilin haka take ci
gaba da fasikancinta abin nata
yawa yakeyi dan tunda ta taso
rayuwarta a bin maza ya
kare,anyi fada da nasiha amma
ina,tasan ko ta auri ahmad baza
ta daina harkarta ta yau da
kullum ba,duk abinda takeyi
ahmad ya San komai yana
bibiyarta ba tare da sanin
kowaba,shi yasa kullum cike yake
da takaici,
Amrat cikakiyar yar duniyace ta
gagari iyayenta amma dady Sam
baya ganewa momi kuwa tasan
amrata ba matar auren ahmad
bace danta baiyi dace ba ammma
a ganinta da ya auri wata ko
rahma gwara  amratu
Shi kam ahmad ya tabbata dady
tsofaffin da ne masu karancin
tunani ,abin na damunsa rashin
hangen nesa na dady,ammar
kuwa cewa sukai kauyece ke
taba daddy har yau,Mimi da salma
sukace ragowar miyar kuka ce a
kansa,momi kuwa sunce bin
bayan mijinta take sabo da
soyayya.dan sun tabbata tafi
dady ganewa,
Bikin ahmad da Mimi saura 3weeks
Wanda har yau rahma bata da
lbr,ga ahmad ya tafi Dubai hado
lefe da kuma kayan Mimi,inda
rahma tayi missing nasa sosai
har Takai yanzu a bed dinsa take
kwana.samun wuri su rahma
kwana har dakin ahmad bai sani
ba,saura 2weeks biki Ahmad ya
dawo gida,yana part din momi ya
zube musu akwatuna guda 9,sun
duba kaya yayi,sai na gida
Nigeria aka zuba suma akwati
sun zama 11.
Mimi kuwa an zamar da gidanta
kamar a turai yanda aka shirya
shi,su salma ba zama kullun
rabon I.v da gyaran jiki,
Shahid ne ke ta rabon na
ahmad,RAHMA baiwar Allah ana
ss2 sai karatu taga gida dai sai
shige da fice akeyi amma bata
San menene ba,
Yau kwana biyu da dawowar
Ahmad ko rahma bata San ya
dawo ba yana can ya kama hotel
yana hutawa kuma baya son
momi ta dameshi da zancen
bikinsa.
Amma yau ya yanke zai koma
gida kodan yaga rahmansa dan
kewarta yake sosai,karfe takwas
na dare ya je wurin mum a
gurguje ya tafi part dinsa,rahma
ta gama gyara gidan kaf sai
kamshi ke tashi,gashi tana ta
girki a kitchen,sanye take cikin
rigar atamfa 3quater da zani dai
dai ita caras da ita,tana zaune
tana kallo remote a hannunta
yayin da take jiran girkinta ya
karasa,
Sallamar ahmad taji ai da sauri ta
jefar da remote ta daka tsalle
tana murna oyoyo yaya…oyoyo
yayana ,sannu da zuwa yaya tana
wakar da yara keyi tana
tsalle,dariyace ta kwacewa
ahmad sosai,
Da gudu ta kwaso ta daneshi bai
zata ba wani shock Ahmad yaji ai
rigis suka fadi kasa,sai
tumurmusa takeyi kamar dai yara
kanana,
Da kyar ahmad ya kwace
jikinsa,ya koma kujera.durkusawa tayi baki har kunne ya ahmad
sannu da dawowa,kallonta kawai
ahmad keyi,dan ta birgeshi ta
sashi nishadi,Rabon da yayi daria
tun kafin yayi tafiya,
Abincinta taje ta sauke ta shirya a
dining kamar tasan zai dawo tayi
pounded yam da miyar egusi
tasha naman rago,ga farfesun
kaji tayi,ga kankana ta yanka a
plate,ta kawo ruwa da zobo me
sanyi data hada, yasha kayan
kamshi,
Riko hannun ahmad tayi sai
murmushi yakeyi, zaunar dashi
tayi ya dinga dura girki me dadi
cikinsa,Rabon da ya ci abinci me
yawan haka ya manta ranar.
Kwashe komai tayi ta gyara
wajen har kitchen,ta fito taga ya
ahmad ya fita,tana zaune taga
baba driver na shigowa da new
akwatuna masu kyan gaske,sai
da ya shigo da guda 14 falon,
Ahmad ne ya shigo hannun
rahma ya jawo ya zauna a kujera
itama ta zauna kusa dashi,bude
mata akwatuna yayi komai size
dinta ne har dinkunan su
atamfa,laces,shadda etc.yaya
wannan fa kamar lefe ta tambaya
zuciarta na bugawa karfa aure
zaiyi,take ta dinga tuno yanda
taga an kara gyaran gidan da
shige da ficen da akeyi
kullum,take jikinta yayi sanyi
murnarta ta koma ciki.
Ahmad yace little sis,kallonsa tayi
zuciarta na suya,aure dady
zaimin da wata yar uwata a
nijar,amrata sunanta,shine
damuata bana sonta dady ya
matsa min,ki tayani addua my
little ina ji a jikina da kyar in
auren zai yiwu.
Nan ya dai zayyanewa rahma
komai,ta tausayawa kanta da
kuma yayanta halin da yake ciki.
 Ai ranar rahma kwana tayi tana
kuka da addua,in tayi kukan sai
addua,kamar mahaukacia haka
takeyi,
Rahma har ta rame sosai ga biki
saura 5days,tawagar amarya sun
dira a gidan su ahmad
ango,anan za ayi shagalin biki,suna
part din mimi,
Ammar ne yaje wajen dady da
momi kan su yafe musu su
dingawa rahma magana,kudingawa rahma magana,kuma a
barta ayi shagalin biki da ita,sun
yarda kuma sun amince, murna
wajen su mimi ba a magana,ai da
gudu suka shiga part din
ahmad.jikin rahma suka fada kan
kujera,ahmad na zaune gefe
yana binsu da kallon
08035453572
mamaki,ammar ne ya fada masa
su momi sun yarje musu,yaji dadi
a ransa sosai,rahma ma taji
dadin su momi sun rage
tsanarta,nanfa aka baje koli ana
labarin biki,yayinda labarin
bayawa rahma dadi,haka ta
daure sukai ta hira,ammar sai
tsokanarta yakeyi,kusan yini
sukayi a part din ahmad yau,
Biki saura 2days a fara tuni
rahma ta saba da kawayen su
mimi,tare akeyi da ita,momi ta
fahimci rahma abar so ce kuma
me hankali,bata da aibu,ga ladabi
da biyayya,ga aiki da girki ba
kyuya ba ganda,momi ma ta fara
sabawa dan in rahma ta shiga
part din komai da ita akeyi,
Dady ma ba laifi ya kuma gano
rahma ta kirkice ga ladabin da
take musu kamar su suka
haifeta,ahmad najin dadin hakan
da sauran family,bangaren amare
amrata da frnds nata sun tsani
rahma yanda suka ga ahmad
shike kula da ita,sai zagi take sha
da tsinuwa kullum,tun
www.littafanhausane.com.ng

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE