MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 1
MATACCIYAR RAYUWA
Chapter 1
KANO
SANI ABACHA INDOOR STADIUM
Rufaffen dakin taron na sani abacha da akafi sani indoor
Cike yake da manyan mutane kama daga yan kasuwa, zuwa
manyan malama’i da sarakai da ma sauran jama’a.
Daga can gefe jerin dalibai ne mata kowanne cikin shiga ta mutumci da daraja, kusan dukkaninsu hijabai ne da su masu yalwa wad’anda . suka kai musu har kasa.
Daga can Bangaren maza suma suna cikin . shiga ta mutumci, yau ne ake shirin fidda gwarzon shekara akan musabaKar karatun alkur’ ani ta qasa wanda Kano ce keda masaukin baqi a wannan karon. “ ‘ ‘ . * ‘ . Ta Bangaren maza aka fara, in da gwaraza guda uku a ajin gasar karsh‘e suka yi karatunsu aka fidda gwarzo. ‘ ‘
‘ . Sai aka’komo ajinmata, mutum biyu sun fito sun yi karatunsu sai daliba ta qarshe FALMATA waccc ta fito daga jihar Maiduguri ta fito ta fara karatunta, muryar’ta da qira anta da yadda take bai wa kowane harafi haqqinsa ya sanya dakin ya dauki shiru tamkar babu kowacce
halitta a cikinsa.
Malamin da ke musu gyara ya yi tsai yana sauraron karatun dalibar wanda ya kasa zakulo gyara a cikinsa har ta kammala, aka dauki kabbara cike da mamakin baiwar da Allah Yai mata.
Ya dago kanshi ya yi mata kallo d’aya, wanda. ya haddasa masa abubuwa da dama, sannan ya maida kanshi gefe. Gaba daya jikin‘sa ya mutu murus ya samu kansa cikin rashin kuzari, sai dai muryar dalibar tana yi masa amsa kuwwa acikin kunnuwansa. ‘ ~
Haka nan dai ya daure ya yi ta ‘yanmaza ya ci gaba da abin da ya zaunar da shi a gurin.
” Kallon da ya yiwa Fahnata, anyi sa’a ita ma , a lokacin shi ta ke kallo, don haka
daurewa tayi ta karaSa gurin zamanta kusa da y‘ar uwarta Yagana. ‘
Ta dan yi qasa da murya tana fadin, “Yagana malamin nan mai darasi bai burge ki ba don Allah? Komai nasa cikin nutsuwa yake yin shi k0?”
Yagana-ta yi dariya tana fadin, “Yau kuma kin yi karo da namijin da‘ya burgeki kenan, ina ce kece kike cewa, me ye abin burgewa ga namiji kuma, sanda na taba ce miki Yaya Sani yana burgc ni?”
Ta ja bakinta ta gumtse don tasan Yagana ba
zata raga mata ba, sai dai ta kasa daina kallon malamin mai darasi, Wanda tun lokacin bai kuma kallon inda ta ke ba.
Har. aka tashi daga taron hankalinta yana kansa, ta rasa irin murnar da zata yi idan har ta zamo ta daya a cikin matan Nigeria, amma sanda aka sanar da ita sai tagaza murnar yadda ya dace, har saida ya zamana, Yagana da malamansu da sauran d‘aliban makarantarsu sun fita murna. Ita ce ta zo ta daya daga bangaren mata, yayin da Abdul-ra’uf
wanda “ya fito ‘daga jihar Kano yazo na daya a. Bangarcn maza.
An raba musu kyaututtuka har da kujerun Makka, shugaban kasa da gwamnoni ma sun cika su da kyauta har da su mota da tsabar kudi, amma wannan duk bai sanya Falmata murba sosai ba.
Yagana ta dan zungure ta tana fadin, “Na ga kamar ba kya murna, bayan burinki ya cika kin zamo ta daya, kin san Abba da Inna za su yi murna matuka da hakan fa”. ‘
Ta yi yaketa sunkuyar da kanta qasa tana cewa, “Nayi murba mana, me kika gani Yagané?”
Yagana tayi dariya kawai, amma ta fara gano inda qawar tata ta sanya a gaba.
Sun kammala komai ana shirye-shirycn tafiya gida, Falmata taso shiga cikin garin kano gidan wasu ‘yan uwansu da ‘akayi mata kwance, amma malamansu sun hana su matsawa k0 nan da ‘ can.
Ta isa gurin malaminsu Gwani Muhammad . ta durkusa kanta yana qasa cikin ladabi ta ce, “Malam zaka iya bani-dama na je cikin gari gurin wasu ‘yan uwanmu na dawo yanzu da wuri?” “Salon ki bata, ki jawa. mutane ‘tashin hankali?”
Ta’d‘aga kai da sauri, don‘ganin me yin maganar. Gabanta ya yanke ,ya fadi malam mai darasi ne da yazo gurin kufa-da haka. .
Gwani Muhammad yayi murmushi yana fadin “Kinji dai abin da shehi-yacc ki koma cikin ‘yan uwanki mun kusa daukar hanyar gida”.
Ta mike jikinta da sanyi ta koma gurin su Yagana ta cikin nikabinta ta kc qara kallon malam mai darasu, sai hira suke yi da Gwani Muhammad suna dariya.. Tana kallonshi ya wuce hannaunsa riqe da babbar robar swan water
“Falmata Gwani Abbagana”. Taji an kwala mata kira. ta waiga da sauri sai ta ga Alubura ce da suka taho tare. Alaburu ta kamo hannunta tana fadin zo kiji
Suka nufi can gefc suka tsaya, Alabura ta. dage nikabin fuskarta tana fadin “Kin caba Falmata, kinji yadda malamin can mai darasi ke batunki, ya ce kin burge shi matuKa, ina ma nina sami wannan matsayin, kin zamo tauraruwar
Elkanemi Bara’imul Iman, ina miki murna ta”. -‘Dage nikabita itama tayi cikin maganganun na malam mai darasu tafi yi mata dadi, ta kwantar da wuya tace“Kin ga ai yana da kirki k0?” Wa?”Alabura ta tambaya da hanzari.
Ta gano kwaBar da take son yi don haka da sauri tace GWani Muhammad mana” ..
” Alabura ta_dan_saki fuska, tace, “Au? Nayi zaton‘ malamin kike nufl..,Ni kuwa da zai aure ni da
na yarda”. Falmata tace, .“Ina son mutum mai ilimi k0 ke bai burgc ki ba nc? ’
. Alabura ta yi dariya, tace, “Kema da maza basu burgeki ya burge ki balle ni? Ni fa banda ina jin kunya’da na’ rubuta masa ‘yar takarda kafin mu tafi”.
_Yagana ta Karaso gurin tana fadin, ‘qulmar
me ake yi ne? An gama shirya’ komai ku zo mu wucc” .
** ** **
Taso ko sallama yazo ya yiwa malamansu kota
Qara kallonsa, amma abin ya faskara, tadinga
waige waige ko Allah zau sanya ta ganshi. amma
har motarsu ta tashi babu alamunsa.
Sanda motarsu ta d‘auki hanyar garinsu ta
lumshe idanunta cikc da takaici tana tunaninsa, tana jin yadda abokan tafiyarta keta surutunsu ba su damu da ita ba, koda yake ko ba don haka ba ma basu sanyata cikin surutunsu tunda sun san ita ba . surutun ta iya irin nasu ba, sau da dama idan ka ji ta yi magana to tabbatar abu mai muhimminci zata fad‘a, ko hirar akeyi ma sai dai ta yi murmushi idan abin murmushin yazo Sun yi nisa a tafiya, masu magana har sun ‘ gaji sun yi bacci, amma Falmata idonta biyu tunanin malam mai darasu ya h‘anata runtsawa, ga shi tasan babu wani abu da zai qara kawota Kano , balle ta sanya ran rara ganinsa, duk da ta sha jin a’na cewa, suna da ‘yan uwa a Kano amma koda wasa ba a taBa cewa za a kai su ba, don haka koda ta ji a nan za su yi musabaka ta qarshe a Kano ta dami mahaifiyarta akan ta yi mata kwatancen gidan ‘yan uwansu a Kano idan ta sami dama taje, amma bata sami damar hakan ba.
MAIDUGURI ‘
Malam Abbagana‘yana zaune bisa kujera mai cin mutum uku a cikin Kayataccen falonsa mai girma da fadi, wanda ya sha kujeru na zamani.
Daga jikin bango Tv ce irin ta zamani plasma, da qaramar’video da receiver a bisa dan wani tcbur na ‘ tangaran baki.
‘Dakin malale yake da jan kafet ta mai taushin tsiya,‘ can daga kusurwar’ gabas babbar drower ce cike da littattafan addini kala-kala, da kaga dakin kasan na shahararren malami ne, kuma mai arziki. ‘
Hajiya Iyami ta shigo dauke da faranti wanda ke shaqeda tufa ta shigo da sallama, mace mai kwarji da cikar kamala wa’cce ba zata wuce ‘ ‘ shckaru arba’ in ba. Ta nufi mai gidan nata cike da farin ciki, ta zauna kusa da shi gami da Janyo wani tebur na glass ta dora yankakkiyar tuffar.
‘ Hankalinsa yana ‘kan talabijin wacce yake kallon Saudi 2, ya. waigo ‘yana qoqarin rage maganar ‘da’ linzamin rage magana (remote control)
‘ “Yaya kin gaya wa Falmata saqon nawa -kuwa?”
Ta dan yi murmushi, “Kai ma kasan dole na isar da sakonka, ita ma dokin haduwar taku ta keyi, don fa jiya’ma ni na hanata zuwa gurinka nace dare, ya yi a bar wa yau kuma, amma da tun daren zaka ganta .
Ya yi dariya yana fadin,‘ “Ai dole ta yi murna, kin san fa yanzu itace zata wakilci matan
Nigeria a gasar musabuqa ta kasa, wacce nake kyautata zaton a Saudia za ayi, Allah Ya shi mata albarka, ta gado gida,itama nasan .duk cikin diyoyina mata tafi kowa qokari, amma sai a dinga jin haushi don ina nuna mata. kulawa da ba ta kyautuka. Shin zan yarda na bai wa masu zubda min daraja gida kyauta ne
Ya qarasa maganar muryarsa amo takaici ya bayyana qarara akan fuskarsa. .
Iyami ta dan kwantar da murya, .tana fadin, “Malam ban son kana fadin haka ya’yan nan duk Allah ne’Ya ba ka, akan me zaka dinga nuna kafi , son wani Bangare? Su da kake ganin suna yin abin da bai dace ba ai addu’a ya kamata kAnayi musu ba~ kyara ba, tunda kaga iyayensu sun kasa yarda da gaskiya, bayan tana bayyane…”
“Addu’ a ta nawa Iyami? Ai ke shaida ce, amma yaran nan sun yi kunnen uwar shegu da tarbiyyar daba basu, wai ace diyoyina ke zuwa, tadin dare, kamar ni da ake girmamawa a garin nan wa ’adinsu ya kusa cika, sati hud‘u ya rage duk wacce ba ta kawo miji ba cikin almajiraina zan samo mata wallahi…
Maganar tashi ta katse saboda :shigowar Falmata, wacce ke sanye da doguwar riga har qasa da karamin hijabi ma’abociyar nutsuwa da sanyin
jiki Ya maida hankalinsa garcta, yana amsa sallamar cike da fara’a.
“Yauwa diyata, shigo ga guri zauna”.
Ya nuna mata kusa da Kafafunsa.
Ta isa fuskarta cike da farin ciki, ‘ta durkusa cikc da ladabi tana fadin, “Abba ina wuni?”
‘ “Lafiya lau diyar Abba, ko na ce mutanen Kano ko?” . ‘ Ta Kara sunkuyar da kai cike da kunya, ya yi dariya yana fadin, “Yau dai duk abinki sai kin ba ni labarin tafiyar nan da abubuwan da kika gani a ,hanya” . . Hajja Iyami tabe fuska, “Lallai zaka . kwana a nan kana jira, yarinya kamar ba a yanka ‘mata fatar baki ba, sai dai ta yi ta yaKe maka hakora kamar me tallan makilin, wallahi idan zaka ‘ wuni da yarinyar nan a daki ba zata ce maka uffan ba, Abba”.
Ya yi dariya yana fadin, “To me ye amfanin surutu ratata? Ai a nan ake samun rarar zance, ni daman tsokanarta nake yi,’ai malaminsu ya ba ni labarin komai, da duk alkhairin da ta samo. Yanzu sai ki sanar da ni abin da kike so nayi miki auta, domin kin faranta min, kin qara daga martabar gidana a idon duniya, kuma na Kara alfahari da
haihuwarki kamar kullum Falmata, Allah Ya yi miki albarka, ina jiranki ki sanar da ni abin da kike so, uhum!”
Ta Kara duqar da kanta tana wasa da yatsun hannunta, ta dai daure tace “Abba ni ba na bukatar komai, sai dai ka mini addu’ar biy’an bukata kawai”.
‘Suka kalli juna da mamaki, sannan suka kalli diyar tasu, Abban ya daure yace . “To sai ki gaya mini buqatar taki na biya miki mana, ko a gurin Allah kike nema Falmata‘?”
Ta daga kai alamar eh, abin da ya sanya shi shiga damuwa, yace, “Falmata ba zaki iya sanar da ni abin da ke damunki ba, nasan ki da zurfin ciki, ko wani abu‘ yan uwanki ke miki ne‘?”
Ta daga kai da sauri, ganin yadda hankalin mahaifin nata ya tashi, tace, “Abba babu komai wallahi,dama zan yi addu’, a ne don na roki Allah cikawa da imani, kasan ba ni da matsala da kowa Abba ” .
Ya yi ajiyar zuciya, hankalinsa ya kwanta ya yi dan murmushi, “To shi kenan zan rubuta miki, kin ji k0? Amma idan wani abu yana darnunki ki sanar dani kinji ko? Tashi kije. Allah Ya shi miki albarka”.
Ta tashi ta nufi waje, ya kalli Hajja Iyami yace “Me kika fahimta da Falmata? Kamar tana da
damuwa fa”.
Ta tabe baki, “Kana son wahalar da kanka
ta ya ya za a gane damuwar Falmata? Kullum a haka ta kefa. .”. ‘
_ Ya yi dariya, yana fadin, “Kai ni dai da an sani da ba,a haifar mini Falmata a ta fari ba, duk anbi a _ tsangwame ta haka? Idan tana da matsala ma ai ba z‘ata iya sanar da ke ba da kin ganta sai ki kama wani
ciccin magani kamar za a yi dambc da ke.
Suka yi dariya su duka biyun a tare.
. Kai tsayc ‘Falmata dakinta ta wuce ta fada , gadonta ta kwanta, .idonta yana kan silin ta kasa. mantawa da suffar malam mai darasu, k0 bacci ta ke mafarkinsa ta ke. Idan tana ido biyu kuma ya
‘dinga yi mata gizo. ‘
Shin idan ta yi addu’a a-kansa ta yi laifi ne? Mutum mai ilimi da daraja irin haka ai kowace mace zata so shi matuka. Tabbas idan ba ta same shi ba ta yi asarar mutum mai alkharii’, ba tasan meye so ba, tunda ba ta taBa yiwa wani ba, sai dai ita a yi mata, amma da alamu abinda takeji a kansa shi ne so, shifa? shin yasan so k0 bai sani ba? ‘Shin matansa nawa ma, diyoyinsa nawa?
Gabanta ya yanke ya fadi, tasan abu ne mai
Hmmm me zai faru 🙂
Bari mu dakata a nan mu tara domin ci gaba da sauraron wannan qayataccen littafin