MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 11

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 11
Dauko amarya mu kam gaskiya’ an .sha damu, ai’ munYi zaton sai mun kara’ cashewaa a~ Kano 
Yayi ‘dariya, gamida fadin ‘Haba Hajiya; don akin daurema bidi’a gindi, ni .yanzu maganar kayan da za,a ‘hadawa Fatima ne ma ya kawo ni, tunda anyi abin cikin gaggawa kamar nawa» kikaga ya dace a kashene? 
’ta kumayin dariyaa cike da farin ciki, wai ,yau Mukhtar ne ‘ke maganar ‘zai ’ hadawa wata’ kayan aure; mutumin da ada idan kamai maganar mace kamar ka watsa  mishi garwashin wutane lallai idan da rai da rabo‘ 
Tace kaga kamata .yayi mu rubuta duk  abinda za,a ‘siya sannan-a ‘lissafa k0?” 
“‘Ya. katseta,‘ ‘Kai Hajiya  yaushe za a yi haka kawai’ ki kimtaci abinda kike ganin zai isa,
Basai a karo daga bayaba ko
Tayi dan jimm kana tace to ai shi kenan
Inaga dubu dari uku zasu isa a hada daidai na talaka
Ya karkace ya zaro kudi na cikin Aljihunsa na gefw sa gefe bandir din yan dubu dubu yana fadin, “Daman dubu dari biyar na taho da shi, idan sun isa shi kenan, idan ba su isa ba sai ki sanar dani ki sanya duk abin da ya dace Yayata, kin san amaryar ‘yar gayu ce”. . 
Ta yi dariya har da shewa, “Lallai wannan amarya taci fas, ashe da ranmu zamu ga wannan rana Mukhtar? T o Allah Ya nuna ‘ mama ranar da zamu ga ‘yan ‘ya’yanka suna yawo akan qasa, amin”. 
Ya dan hade rai, don bai son yanda suka tsangwami Fatila akan rashin haihuwa, shi gani yake don ba ta haihuwa me ya sanya suka sanyata a gaba, ya mike yana dariya qasa-kasa, “Ku kuma kun j i matsalarku kenan Hajiya, bari na wuce ni, sai na ji ki a waya”. 
Ta mike ita ma tana fadin, ‘Ahaf, ai an taBo ‘yar gwal din taka ka mike mana, ni kam Allah ‘Ya fidda Falmata daga sharrin Fatila, don nasan ba zata dauki abin a kaddara ba”. 
‘ Ya yi gaba yana fadin, “Ni dai kinga tafiyata, Allah Ya huci zuciyarki”. 
Ta yi dariya sanda ya gama fita tana fadin, “Oho dai k0 a yau ka rabu da Falmata mun nunawa Fatila iyakarta, muguwa kawai”. 
Daga nan gidan kai tsaye gidansa ya wuce, sai dai abin da ya ba shi mamaki bai wuce ganin Fatila bata nan ba, ransa ya baci matuka, to ina ta tafi ba tare da ta tambaye shi ba? Ya fara neman layukan wayarta, lokacin tana durkushe gaban boka Barbushe kamar zata yi masa sujjada don biyayya, tana jin kiransa ta dan tsorata ta kalli bokan ya kalle ta yace
“Shi ne yake kiran wayar taki k0?” 
Da sauri ta ce, “Eh shi ne boka, watakila yaje gida bai ganni ba ne, ni sam na manta na tambaye shi ma saboda Bacin rai, cewar zan fita unguwa”. 
Bokan ya fashe da dariya yana fadin, “Ai haka ake so,ai duk wani abu da zaki saBa masa ake son ki dinga yi, idan har kina tambayarsa idan zaki fita to aikinmu zai iya karyewa, na ‘ gaya miki mijinki malami ne da yake yawan karya mana aikinmu, don haka sai kina taimakon shaidanu da basu‘ gudunmawa akan duk wani abu da suke so, kamar satar fita da -yawan labe, da daukar duk kudacdensa, duk wani abu da zai dinga sanya shi Bacin rai dai. domin sai ransa ya baci sannan zasu samu 
damar aiwatar da ayyukansu akan shi, kin gane k0?” Ya fadi yana zare idanu. 
Da sauri ta cc, “Eh boka”. 
. Ya kara kallonta, “Ki dauko wayar ki kasheta yanzu, idan kin koma kada ki ba shi _ hakuri, kuma duk yanda zaki yi ki takale shi ku yi fada, muddin ransa ya baci to ki tabbatar a daren yau aikinmu zai fara tasiri a kansa. Ga wannan kuma” . 
Ya mika mata wata kankana wacce ta sha wani irin zane da rubuce-rubuce duk an huhhudata yana ci gaba da fadin. 
“Ki je ki binne a kasa, ki tabbatar ramin ya kai kamar kamu goma, ki kuma tabbatar kin binne cikin makabarta da daddare, idan ta kwana kikoma ki gano yanda ta zama, sai ki sanar dani. Ga wadannan layun ki watsa su a kanta, amma fa kada ki manta inda kika binne kin ji k0?” 
Da sauri tace, “Insha Allah…” 
“Ke… Ke ya ya zaki fara karya mana aiki? Kada na kuma jin irin wannan kalmomin a bakinki, ai dasu ne yake karya mana aiki shi 
“To boka, yanzu me za mu baka ne?” Hajiya Kumatu ta tambaya tana daga gefe a tsugunne, ita da Diyana manyan mata. 
–. Ya kalle su ya bushe da dariya, sannan yace, “Ai dole sai dodo ya sha jini, don haka muna bukatar jini, sannan na gaya mata duk ranar litinin da juma’a ba zata yi sallah ba, kuma babu sallar safe da ta isha’i, duk ranar da ta kuskura ta yisu to aiki ya lalace kenan”. . 
Hajiya Kumatu ta kara kwantar da kai tana fadin, “To ai boka kasan bamu san inda zamu samo jinin ba, sai dai mu baka abin da za a biya yara su samo a taimake mu boka Barbushe jikan Tsanburbura”. 
Ya gyada kai yana wani muzurai, yace, _“Shi kenan, ku bada dubu dari da hamsin…” 
Jikin Fatila yana rawa ta zuge jakarta ta zaro kudin ta mika masa. Ya amshe ya watsa bayansa cikin wasu layu kamar marasa amfani. 
Da haka suka bar gurin nashi, shi kuwa yana can gida ya kufula, domin a rayuwarsa bai son matarsa ta dinga yawo mara kai, idan akwai abin da yake hada shi fada da Fatila bai wuce 
yawonta ba, duk sai ya damu ya kasa yin 
komai, saida yaji shigowar sako a waya ne ma sannan ya tuna da Falmata 
Yana dubawa kuwa‘ yar halak din itace, da sauri ya kirawota. 
Tun daga jin sallamarta hankalinsa ya kwanta, ya lumshe ido wani sanyi yana kwarara a ransa. 
Ba ta shigo gidan ba sai gab da sallar magariba, yana falo a zaune ya cika fam kamar zai fashe, sai dai abin da ya kara kular da shi bai wuce ganin ta zo ta shige ba tare da ta k0 kalli inda yake ba. Bai yi niyyar kulata ba, domin yana da matukar hakuri, me yasa ya kyale ta, sai dai wannan rainin wayon da ta yi masa ya hasala shi matuka, ya mike rai a bace yana fadin. 
“ke malama daga ina kike, kuma kina ganina kika wani share ni, bayan kin fi kowa sanin zunubin da yake cikin satar fita?” 
Ta kalle shi sama da kasa domin ta kular da shi, tace, “Bani da lokacin magana da kai, ka ji k0?” 
Ya kuma kufula, sai dai can tunanin abin da ya yi mata jiya na game da auren 
Falmata ya fado masa, don haka sai ya sanyawa zuciyarsa sanyi ya koma kujera ya zauna ya dafe kai. 
. Sam ba haka ta so ba, domin hasalarshi yana cikin shirinsu na farko, amma ba ta karaya ba taci gaba da magana. 
“Kuma fita ma yanzu na fara yin’ta, idan mutum ya isa ya yi maganin abin mana”. 
Ya daga idonsa yana kallonta, yana ta tausar zuciyarsa da yi mata uzuri domin kishin Fatila yasan zai iya sanyata yin komai, sai ma ya kwantar da kai yana fadin. 
“Fatila ki kula da nauyin da yake kanki, bani ne na dora miki ba, Allah ne Ya dora miki, amma tunda haka kika zaba shi ke nan…” Yana kaiwa nan ya mike da sauri ya nufi hanyar waje domin an fara kiraye-kirayen sallar magriba. 
Hankalinta ya tashi matuka don yana neman karya mata aiki , sai ta nufi dakinta da sauri, babu batun sallah dama. Diyana ta fara kira, bakinta na rawa tace. 
“Diyana nazo na tarar da shi a falo da farko kamar zai biye min na bata masa rai, amma in gaya miki daga karshe sai ya koma 
lallashina, kin san halinsa da shegen hakuri kamar wanda kecin naman damo, yaya zan yi ne yanzu?” 
Diyana taja tsaku cike da takaici, tace
“Ke fa banza ce, ke yanzu har sai an gaya miki abin da zaki yi? Kawai ki shiga dakinsa ki nemi kayansa da yafi so ki yayyaga su da reza ki watsar tsakar falon naku, sannan ki fasa talabijin da rediyo ki watsar a falon, sai ki dauko jakarki ki bar gidan a haka, nasan duk iyakacin hakurinsa dole ne ransa ya Baci, dole zai nufi dakinki da zummar yi miki masifa ya tadda ba kyanan, nasan zai kwana ransa a Bace sai kuma shaidanun aljanunmu su kwana aiki a kansa, a daren sai muje mu binne kankanar kiyi zamanki har gobe a gidan da zummar yaji kika yi, idan muka je muka ga yanda ta koma sai ki sanar da tsinannen sai ya sanar da mu abin da zai faru kuma a gaba, amma dole sai mun tashi tsaye tunda kinga yace yarinyar nan ita take .a_ tsaye don har tafi Mukhtar dinma addu’o’i na kariya”. _ 
Fatila tace, “Lallai kam haka ne, bari naje na fara aikata abin da kika ce din ma”. 
Ta kashe wayar ta nufi dakin Mukhtar. Wasu yadikansa da ya siyo daga Dubai da mai ruwan madara da fari kal kudinsu ya .kai kusan dubu hamsin-hamsin, ga shi an yi musu wani dinkin hannu‘mai kyau. A can baya babu abin da ta keso illa ta ga ya sanya wadannan kayan don yana komawa kamar’wani Saraki, shi ma kansa yana son kayan matuka, su ta yayyanka gutsi-gutsi ta watsar a falon, ta faffasa duk plasma T.B da ke gidan da sauran kayan kallon ta bar su barbaje a falon ta nufi dakinta ta hada kaya cikin jakarta tau wucewarta abinta. 
Shi kam bai dawo ba sai da ya yi har da sallar isha’in sannan ya nufo gidan. Ya jima cikin .raka’,arsa ta karshe yana addu’ar neman zaman lafiya a gidansa da iyalinsa. 
-Sai dai me? Yana shiga gidan ba tare da sani ba ya taka glass wanda ya shige kafarsa ya rike Kafar da sauri yana fadin. 
“Subhanallah”. 
Sa- alokacin idonsa ya kai kan barnar da ke cikin falon, gaba daya ”sai ya tsaya cak kamar an dasa shi, yana karewa dakin kallo. 
Wani irin Bacin rai ya baibaye shi, domin cikin ‘yan sakwanni kwakwalwarsa ta sanar da shi abin daje faruwa, ya maida takalminsa ya nufi cikin dakin da sauri, kai tsaye gurin kayansa da ta yayyanka ya wuce. 
Ya daga kayan zuciyarsa tana kuna bai san sanda ya nufi dakinta kai tsaye ba. Tabbas mai hakuri bai iya fushi ba dama, sai dai me? Dakin nata a datse ya ganshi alamun bata nan. Ya Kara tura kofar don ya tabbatar, ransa ya kuma Baci ya nufi dakinsa kai tsaye, ya yi zaune bakin gado tallafe da kumatu, ransa yana suya. 
Wace irin mace ce Fatila? Shin kishi hauka ne da  har zai sanya ta yaga masa kayansa ta fita ba da izininsa ba? Ya kyale ta shi ne kuma ta yayyaga masa kayansa har da yi masa rotsen kayan kallo? 
Tabbas dole ta gane kurenta a wannan lokacin’, idan ma yaji tayi yayi’ alkawarin ba zaije bikonta ba sam, idan ta gaji da yajin ta dawo don kanta. 
Haka nan ya kwanta ransa yana suya, k0 
abinci-bai sami arzikin ci ba ya kwanta. Can 
dabarar kiran Falmata ta fado masa sai dai yayi rashin sa’,a wayar tata a kashe take, don haka dole ya hakura. 
A can Bangarensu kuwa Diyana ta yanke shawarar gidan Haj. Kumatu zasu kwana, ta . yiwa maigidanta karyar Kaduna zata gaisuwa, haka ta tsallake ta barshi da ‘ya’yanta biyu domin su je su binne abin da boka .ya basu. Karfe dayan dare suka fice suka nufi makabarta basu ji tsoron Allah ba, balle aljannun dake yawonsu a daren ba. 
_ , Can gefen makabartar suka haka rami 
suka binne kankanar da sauran layun suka yi  shaida yanda .zasu gane gurin, sannan suka : juya gida. 
***************************************
Koda gari ya waye. kai tsaye gurin masu aiki ya nufa ya tadda su har sun fara fentin gidan, daga nan ya wuce ofls dinsa kai tsaye, sai da rana ‘ta d’aga sannan ya kirawo layin Falmata. ~Ya yi sa’,ar samunta kuwa, donhaka suka shiga hira mai dadi, sai dai a Bangarensa gabansa sai yawan faduwa yake yi.Haka suka 
yi sallama ya hada tagumi ransa yana zafi ya san abin da Fatila ta yi masa ke damunsa, duk da yana son ya ga ya manta da abin amma ya kasa. «. Sai yamma Iikis ya bar ofls dinsa kai tsaye gidansu ya nufa, ya tadda gidan a cike ana ta kallon kayan da Hajiya Safiya ta hado, kaya ne na  gani na  kowa sai sanya albarka yake yi
sai da suka matsa masa sannan ya dan kalli kayan, duk da ba sanin kayan mata ya yi ba, kayan sun burge shi, daga gani kuma an kaso kudi masu dama. Ya kalli yayar tashi yana fadin. 
“Nawa ne kuma cikon Hajiya?” 
Ta yi dariya ta ce. 
“Cikon babu yawa, su ma don an sai mata awarwaro na gwal ne, dubu ashirin da tara ne, amma ka barsu shi ne gudunmawata”. 
. Ya ji dadi matuka, yace
“To an gode, bari na wuce gida”. 
Mahaifiyar shi ta tare shi da maganar Fatila, tana fadin, “Ina fatan ka gaya wa matar taka k0?” 
Gabansa ya fadi, Bacin ransa ya dawo, don ko sunanta bai son yaji an ambata, amma dai sai ya dake yace
“Eh na sanar da ita Hajiya”. 
“To ai shi ke nan, ni dai na gaya maka ka dinga neman magungunan tsarin jiki, kana takama kai malami ne amma ilimin zamani ya lalata ku, bakwa nemawa kanku tsarin komai, kada ka yi tunanin don kana mahaddaci asiri ba zai kamaka ba, yafi kama irinku masu sakaci ma”. Cikin ladabi yace Insha Allahu zan kiyaye”. . 
A ransa kuwa mamakin yanda_ suka dauki Fatila yake yi, yaushe zata yi masa wani asiri, su ba su san irun son da take masa ba, banda wannan maganar ta Falmata ta ratso ma shi zai ce bata taba bata masa rai ba, kullum takan yi duk wani abu da zai faranta masa ransa ne, amma dai dole ya bisu da to don a zauna laflya. Da haka ya wuce ya bar gidan. 
Baiwar Allah Falmata tunda almuru ya kawo kai ta ji ranta yana baci, zuciyarta tana ta tafasa, ga wani irin faduwa da gabanta ke yi, da 
yake ita din malama ce sai kawai ta dauko qur’ani ta fara karantawa har aka yi sallar magriba. 
., Shi ma can yaji duk abin da falmatan keji, amma sai ya dauka a Bacin ran abin da Fatila ta yi masa ne, don haka kai tsaye wata majalissar abokansa lakcarori ya wuce, can gefen Gwauron Dutse suke zama, duk da har lokacin ran nasa a bace yake sai ya dan ji dadin hirar, ya yi kokarin boye abin dake damunsa suka yi ta hirarsu anan suka yi jam’in sallar isha’i, sai wajen takwas suka watse kowa ya kama gabansa, shi kam sai da ya biya gidan sayar da abinci ya sayi na taflya ya sanya a motarsa sannan ya wuce gida. 
Amma da ya isa gidan sai ya kasa ci, ya dinga juye-juyen tashoshi Arab  yana son kiran Falmata ya ji muryarta, amma kuma zuciyarsa taqi ba shi hadin kai, sai yake jin zafinta a ransa matuka. A nan falon bacci ya dauke shi ba tare da ya shirya ba. 
Su kam shedanu wajen karfe daya na dare kamar jiya suka kara komawa inda suka 
binne abin nan suka kuma tonawa, gabansu ya 
fadi ganin ba su ga komai ba, ga shi dai sun tabbatar nan ne suka binne, sai alamar kwallaye na Kankanar, amma ko fatar babu. Suka dinga kallon juna a tsorace amma sun kasa magana, sai da suka isa cikin mota sannan suka iya yin magana. Fatila ce ta fara magana 
“Momy kada ace aikin nan ya lalace dana shiga uku na kuwa”. 
Hajiya Kumatu ta yi dan qarfin hali ta ce. 
“Anya? Mu dai kirawo wayarshi muji”. 
Da sauri ta kirawo layin nasa, bugu biyu ya dauka, bakinta yana rawa tayi masa bayanin abin dake  faruwa, maimakon ya yi magana sai taji ya fashe da dariya. Gabanta ya ci gaba da faduwa, sai zare ido ta ke yi. Su kuma sun zura mata nasu idanun cike da tsoro da fargaba, sai da ya yi ‘dariya son ransa sannan yace. 
“Yarinya ki godewa aljani Ifritu domin aikinsa ya yi kyau ina mai miki albishir da yanda kankanar nan tabi kasa babu ko alamunta, to haka maganar auren mijinki tabi ruwa har abada ba zai kuma maganarta ba, kin yi nasara, saura kici gaba da yiwa Aljani biYayya akan abin da ya d‘ora ki”. 
‘Ta yi wata ajiyar zuciya, sanda take kashe wayar, cikin rige-rige suke tambayarta abin da yace. Bakinta kamar gonar auduga tace, “Momy yace mini yanda kankanar nan tabi kasa haka maganar aurcn nan ta bi ruwa”. 
“Kai amma naji dadi yau zan yi barci har da minshari”. 
Farin ciki ya cika musu zuciya, suka nufi hanyar gida cike da farin ciki suna maida yanda aka yi. Hajiya Kumatu ke fadin. 
“To bari kwana biyu mu Kara komawa ya yi mana wani aikin, wanda ko da an yi masa irin wannan auren take a nan zai saki matar ma, tunda ita tsinanniyar uwar tasa mun kasa samun galaba a kanta, koda yake ai ba ta dame mu ba, gwara ma a yi komai ba da son ranta ba, don ina son ta yi ta hadiyar bakin ciki har ranar da zata koma kabarinta, ai mu duk wanda ya Ci tuwo da mu miya ya sha wallahi”. 
Tunda Mukhtar ya farka da asuba yake jin zuciyarsa sakayau kamar an sauke masa wani abu. sai dai kuma da soyayyar Fatila ta cikata, har yake jin kamar idan bai je inda taje ba komai zai iya faruwa da shi Cikin hanzari 
Tofa wai meke shirin faruwane?????? 😀😀

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE