MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 13

MATACCIYAR RAYUWA

CHAPTER 13

cuci yarinya, idan abin ya fad‘o mata har kwalla ta ke yi.
Falmata kam abu wasa-wasa tana dan ciwon kai da zazzaBi sai ga ciwo ya kwantar da ita magashiyan, mahaifiyarta ke fadan wai idan harta sanya namiji a ranta zata mutu a banza.
Ita kam kuka kawai take yi don ita kadai tasan abin da ta keji a. ranta game da Mukhtar, ga kuma azabar ciwo, su Hajja Yakolo kuwa murba ake ta yi da shewa, domin bokayensu sun tabbatar musu da a haka auren zai lalace, ba zata taba tarewa ba.
Abba Gana ya shiga damuwa musamman sanda aka ce masa Falmata babu lafiya, dama kwana biyu da ba taje gaishe shi ba duk ya damu, da kansa ya-nufi dakin nata, lokacin tana ta kelaya amai kamar ‘yan hanjinta zasu yo waje, mahaifiyarta tana tsaye a kanta cike da tashin hankali.
Kallo daya ya yi mata ya Kara shiga damuwa, cikin sauri yake fadin.
Subhanallahi Falmata ashe haka jikin naki yayi zafi
Ya maida dubansa ga mahaifiyarta yana ci gaba da fadin.
“Garin yaya kukayi sakaci har jikin nata ya yi haka Iyami?”
Ta dan kwaBe fuska tana fadin, “Ni fa na yi zaton kawai tunanin mijinta ta sanya a ranta ban yi zaton ciwon na gaske bane
Ya dan hasala yana fadin, “To idan ta yi tunanin mijin nata ai ‘ba ta yi laifi babe k0 kin manta yau wata uku kenan da daura mata aure, duk ‘yan uwanta sun tare ita kuwa tana zaune, ai dole ta yi tunani da kika ga haka ai dacewa ya yi ki lallasheta ba wai ki tsangwame ta ba k0?”
Ta kwantar da kai tana fadin, “Tabbas na yi laifi, a yi hakuri malam”.
Ya dan sassauta murya yana fadin, “Shi kenan maza shiryata mu kai ta asibiti kada ciwon zuciya ya kamata a banza… Koda yake bari na yiwa Dr. Ibrahim waya idan ba shi da aiki yazo ya dubata”.
Ya zaro waya ‘ daga aljihunsa ya fara neman wayar Dr. Ibrahim, dai-dai lokacin da mahaifiyar tata ke gyara gurin da ta Bata.
Minti talatin Dr. Ibrahim ya shigo gidan, Malam din da kansa ya yi masa iso har dakin Falmata ya yi mata ‘yan tambayoyin da suka dace. Ya ce maza  taje ta yo fnsari ta kawo masa. Bayan ya auna fitsarin ya yi mata allura da magunguna, sannan ya koma ya duba fitsarin ya yi rubutu bisa wata ‘yar farar takarda, ya nufi falon da Malam da Hajja Iyami ke zaune suna jiran sakamakon ciwon nata.
Dai-dai lokacin da Hajja Busma da Yakolo suka karaso dakin, tsegumi me ya kawo su. domin sun ga shigowar Dr. Ibrahim sun san babu lafiya ke nan, murna ta cika su, Hajja Yakolo ke fadin, “Allah Ya sanya ciwon zuciya ya kamata kowa ya huta, ai sai muga Karshen diyar so k0?”
Suka yi dariya suka tafa, sannan suka nufi sashin domin su ga kwaf, da sallama suka shigo fuskokinsu da damuwar Karya, Hajja Basma ce ta fara magana.
“Malam waye babu lafiya, yanzu  take fada mana wai Dr. Ibrahim yazo ya shiga sashin Iyami, waye babu lafiya?”
Ya kalle su ganin yanayin da fuskokinsu suka nuna ya dauka har cikin ransu haka abin yake, don haka ya fara kora musu bayanin abin da ya faru. Hajja Iyami kam ba ta so hakan ba, domin tasan ba don Allah suka shigo ba,
munafurci ne ya shigo da su Yana tsaka da bayanin Dr Ibrahim ya
shigo dauke da takardar a hannunsa.
Malam ya mike da sauri ya tare shi yana fadin, “Yaya dai likita ba wani abu ne yaso taba zuciyarta ba k0?”
Likitan ya mika masa -‘yar takardar yana ‘fadin, “Malam ai abin murba ne, babu wani ciwo a tattarc da ita, illa laulayin da mata suka
saba yi… “Laulayi? Kada dai kace ciki ne da ita?”
Hajja Basma ta katse shi da sauri. . ..
Dr. Ibrahim ya juyo ya kalleta da ‘mamaki, domin yasan Falmata matar aure ce. tunda shi ma yana daya daga cikin wadanda suka shaida d‘aurin ‘auren amma sai ya gaza cewa komai ganin malam ya daka mata wata
uwar harara.
Ya kalli malam din yana fadin “Akaramakallah, ni zan wuce,Allah ya bamu alkhairi” .
Malam ya sanya hannu a aljihu yana zaro kudi yana fadin, “A’a malam Ibrahim tsaya ka amshi wannan ka zuba k0 da mai ne cikin
motarka”. Bai waigo ba yace, “A’a ka barshi kawai
malam, a yi mana addu’a”. Ya fice da sauri. Duk da hankalin Malam din a tashe yake bai hana shi daurewa ba ya‘hau Hajja Basma da fada, “Dake ake magana k0 dani? Wato rashin tarbiyyar sai kin nuna shi a ko’ina k0? To ku wuce ku bar; gurinnan. Suka wuce sumi-sumi kowacce tana cike .da mamaki da murna, sun dai san Falmata ba ta tare .ba, kuma mijinta bai taba daukarta sun je wani guri ba. Kai koma shine ya dauke ta suka jewani guri har ya yi mata ciki ai anyi abin ‘ kunya, ‘balle suna da tabbacin ba cikinsa ba ne, sai gasu kowacce tana addu’a a ranta wai Allah ya sa cikin ya zama na shcge ne, in yaso suga karyar tarbiyyar da kullum ake kirawa Falmata,
su ‘ya’yansu da kullum ake kira marasa tarbiyya ba su kwaso abin kunya ba.
Suna fita Hajja Iyami ta fashe da kuka gami da faduwa ta bar cikin kujera tana fadin, “Na shiga uku ni Iyami, wane labari ne nake ji ‘haka mai muni . da daga hankali? ~Amma Falmata.ta cuce ni, ashe duk tarbiyyar dana bai wa yarinyar nan zata iya cutata taje tayo-abin kimya?” .
Malam Abba Gana yace, “kin ji ki da ‘wata maganar banza, kina tunanin Falmata zata iya cikin,shege ,ne? Duk fadin zuri’ata nasan Allah ba zai jarrabe ni da wannan mummunan abin ba, domin na kiyaye dokokin Allah, na tsarkake zuciyata, Allah ba zai taBa jarabtata da wamnnan mugun abu ba insha Allahu, muje gurinta muji abin da zata ce
Duk da hankalinta ya dan kwanta da kalamin mijinta, amma gabanta bai daina
faduwa ba har lokacin da suka isa dakin
Falmata. …
Tana kwance bacci ya fara daukarta, da kakkausar murya mahaifiyarta ta yi kiran sunanta abin da ya sanya hankalima mugun
tashi ta bud‘e idon ta babu shiri, ganinsu su biyu ya kuma fadar mata da gaba ta mike da hanzari, sai dai kafin ta kai ga cewa wani abu hajja Iyami ta rigata. da“Uban waye ya yi miKi ciki Falmata…” Falmata dafe da kirji cike da tashin hankali tana fadin, “Ciki kuma Hajja a jikina?” “To karya zan miki amma. kin cuce ni Falmata…” Sai ta fashe da kuka, Malam ya daga mata hannu yana fadin.
“Kada ki Kara cewa komai Iyami”: Sannan ya nufi gefcn gadon da Falmata take kwacce ta waro ido waje a gigice kamar zata fasa ihu ya zauna ya kwantar da murya cikin ran shi yaje  fadin.
“Falmata na baki tarbiyya mai kyau nasan ba zaki bani kunya ba ki gaya mim . gaskiya. Cikin jikinki na waye?”
Sai ta fashe da kuka ta kama rantsuwa, “Wallahi Abba ban taba bin wani namiji ba, nasan yanda kuke fadin illar ‘zina ka kawo kur’ani na dafa, idan na taba bin wani namiji Allah Ya tsine…”
Ya daga mata hannu, “Ya isa, nasan daman ba zaki taba bin wani namiji ba, ba kuma za ki bishi ba har abada, sai dai ina son ki gaya mini gaskiya, k0 kin taBa zuwa wata unguwa da Mukhtar ne?”
‘ Ta yi duru-duru da idonta, wannan shine _ ga koshi ga kuma kwana da yunwa, da kunya tace da iyayenta ta bishi, amma kuma fadin hakan ne zai wanke ta, taci gaba da kuka ta kasa magana. Abin da ya kuma tayarwa da mahaifiyarta hankali ke nan, da ace su Hajja Basma basu ~ji ba.ma da sauki, har su san yanda zasu yi .da Cikin, kamar daga sama ta jiyo muryarsa yana ci gaba da lallashin diyar tasu, abin da ke Kara kular da ita, ita kam da zai kyale ta ta rufeta da duka tafu fadin yanda akayi
“Ki yi tunani a nutse, tun daga sanda aka daura muku aure har kawo yau, k0 kin taba fita, ko kebewa da shi, ki kwantar da hankalinki ki gaya mini, Mukhtar mijinki ne da duniya ta shaida, babu wani wanda zai zarge ki akan komai, kin ji k0 Falmata?” Cikin rarrashi yake maganar.
Ta dan tsaida kukan tace, “Sanda ina gidan Yaya Bulama lokacin Anti Shafa ta haihu, yazo yace na raka shi gidan su zai gyara, har Anti Shafa ya tambaya tace muje kuma…” Ta kasa karasa maganar saboda kunya._
Malam din ya yi wata ajiyar zuciya yana fadin, “Masha Allah kin dai tabbatar da hakan k0, kuma Shafa ce shaidarki k0?”
Ta daga kai da sauri alamar eh.
Malam ya dubi’ Hajja Iyami, ya ce, “Ki kirawo mini lambar Shafa’ atun mana” .
Da sauri ta nufi dakinta ta dauko wayarta ta dawo, ta fara neman layin wayar Shafa’ atu, ta yi sa’a bugu daya ta shiga ta mikawa malam
din. ‘Daga can Bangaren Shafa’atun ke fadin;
“Hajja ina kwana, ya ya yara?” Malam din ya katse ta yana fadin, “Ba Iyami bace nine Abba. Na bugo ne na yi miki
wata tambaya”. Sai Shafa ta Kara nutsuwa tana gaishe
shi, ya amsa sannan ya dora da cewar, “Sanda Falmata tazo gidanki, wai mijinta yazo ya dauke ta ‘har sunje gidansa k0? Ki gaya mini gaskiya Shafa’atu, domin ina cikin tashin hankali ne yanzu”.
Tuni Shafa ta gano abin da ke faruwa. Tunda dai ita din ba yarinya bace ba, daman tun kwanaki ta kula da Fa’mata na da ciki, sai dai ba ta son ta gaya mata ne hankalinta ya tashi, tafi so sai ta tare a gidan mijinta da ake ta sanya rana kullum ana dagawa. Da sauri tace
“Tabbas haka ne, Mukhtar yazo ya dauke ta a nan gidan da zummar zata taya shi ’ gyaran gidansa, har dare ya yi suka kwana a can, k0 yayanta ma ya sani ai”.
Malam din yace, “Masha Allahu, shike nan, na gode Shafa’atu, sai an jima”.
Ya kashe wayar. ya kalli Hajja Iyami, “Kin ji abin da nake gaya miki, kafin ka fara aiwatar da komai kayi bincike, kin dai ji da kunnenki k0?”
Ta yi ajiyar zuciya hankalinta ya fara kwanciya, da yake wayar a hannu bude ta ke, ya maida hankalinsa ga Falmata dake kuka, ya ce, “Kinga daina kuka, nasan ba zaki taba aikata abin da ba dai-dai ba bane ba, bari na
kirawo Muktarin”. Ya fara neman layin
‘ Mukhtar. Yana ofis dinsa yana tsaka da‘aiki,
kwanansa daya da dawowa daga tafiyar da yayi Sudan kiran malam ya shigo wayarsa, kunya mai tsanani ta kama shi. ga shi ba zai iya kin daukar wayar ba, don haka ya dauka hannunsa yana raWa, cike da kunya ya gaishe da malam din. . Babu wani sauyi a muryarsa ya amsa, ya dira da cewar, “Malam Mukhtar, daman
matarka ce babu lafiya har likita yazo ya dubata, yace tana da juna biyu shine na bugo na sanar da kai, k0 kaima ka sani ne?”
Kunya ta sake kama shi, ya kasa cewa kOmai har sai da malam Abba Gana ya sake
maimaita masa tambayar da fadin.
“Shin k0 ba cikinka bane Mukhtar? Ka sanar dani: gaskiya”
Nan da nan ya dawo hayyacinsa. da sauri yace, Malam ayi hakuri tabbas cikina ne. ‘nayi kuskure ne kada aga laifinta, nine mai laifin, .amma babu makawa nine mutum na
farko data taba sani a rayuwarta”.
Hankalin malam ya kwanta ya yi wata .
wawuyar ajiyar zuciya yana fadin.
“Masha Allahu, kada ka damu, ai ” ‘ Falmata matarka ce komai kayi babu mai ,,
tambayarka, ai daura aure shi ne gaba da
komai, ka dai yi kokari ka kammala gidan ta tare ta haihu a dakinta, ka ji k0?”
Da sauru’ yace, “Insha Allah malam, a kara yin hakuri dai. Ita ma a bata hakuri zan shigo cikin satin nan insha Allahu”.
Da haka suka yi sallama ya kalli Iyami ’
da hankalinta ya kwanta, wani irin farin ciki ya rufe ta, ya ce.
“Kin ga abin da nake gaya miki k0? To ki kula da ita”. Ya maida dubansa ga Falmata da kunya ta hanata daga kanta, cikin farin ciki yake fadin.
“Ki kwantar da hankalinki ki daina kuka,
ba ki yi wani abin kunya ba, zan Kara neman ” mahaifiyarsa mu yi magana sosai, Allah Ya yi .,
miki albarka ameen” .
Ya sa kai ya fice, hajja Iyami tayi dan Jim kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa tabi malam din da sauri.
A falo ta tadda shi yana shirin ficewa tace, “Abba ina da magana”.
Ya tsaya gami da juyowa, ta karaso kusa ‘ da shi da ladabi a muryarta, tace
“Ya dace a sanar dasu Hajja Basma halin da ake ciki, domin kada a sauyawa maganar fahimta”.
Ya girgiza kai yana fadin, “Wannan haka yake, zan tura a kirawo su yanzu, ki taddani a sashina kema, amma ki fara bata magunguna ta sha”.
Ta amsa da toh, sannan ta koma dakin da Falmata ta ke, ita kam Falmata cikin kunya da nauyi ta amshi magungunan ta sha, bayan fitar mahaifiyarta ta koma gado ta kwanta, amma ta gaza lallashin kanta, tausayin kanta da rayuwarta ya cikata ta yaya ta yi sakaci har wannan abu ya auku a kanta? Ta toshe kanta cikin filo ta fashe da kuka, domin ba ta son mahaifiyarta ta jiyo sautin kukanta, sai da ta yi mai isarta sannan ta shiga bandaki ta wanke fuskarta tana cike da fata da addu’ar kiran Mukhtar a kowane lokaci.
Ta dawo ta zauna tsakiyar gado ta zurawa wayarta ido jira take ta ji ya kirawo ta cike da murna da doki domin dai bai taBa haihuwa ba, tabba’s dole zai yi murna .da wannan cikin, wata kila zata iya cin darajarsa ma ya yafe mata laifin da tayi, wanda ba ta sani ba. Sai dai ga dukkan alamu baShi da niyyar kiran nata.
Shi kam yana can ofis murna ta cika shi, da gaske Falmata tana da ciki? Tabbas da ya kasance mutum mai sa’a idan har ya samu da a wannan lokacin da ya fidda rai da shi. Ya janyo wayarsa da sauri da zummar kiranta, amma sai wani haushi da tsanarta ya cika masa ransa, ya rasa laifin da ta yi masa yake jin haushinta haka, tabbas yana neman taimakon Allah a kanta. Ya tashi ya kama sintiri a ofis din nasa gaba daya ya kasa yin komai, amma ransa ya cika da soyayyar abin dake cikin Falmata ko waye ma haka ya dinga zagaye dakin.
Daga karshe sai ya fara ambaton sunan Allah, domin Ya kawo masa dauki a bisa Wannan halin da ya shiga ciki.
************************
Malam da kansa ya kirawo Hajiya Mariya cike da tsananin kunya ta dauki wayar, kafin yace wani abu ta fashe masa da kuka cike da tashin hankali ya fara fadin.
“Subhanallahi, Mariya me ya faru haka?”
Cikin kuka ta ce, “Tabbas tsinanniyar matarsa ta‘yi mugun aiki a kansa, ta yi masa farrako, domin daya daga cikin masu aikinta ta tabbatar min da hakan. Ban san yaya zan yi da ita ba, kunya ta sanya na kasa kiranka kullum addu’a nake yi malam, amma abun Kara gaba yake yi”.
Malam yace“Ashsha, ki daina fadin haka, ina ce a baya ne ma kika ce ya yi auren ma yaKi yi, ai kuwa addu’a tayi aiki, ki daina fadin irin wannan maganr kada kiyi sabo. Yanzu ma bugowa nayi na gaya miki tasirin da addu’ar ta yi, domin babu wanda ya isa ya hana Allah ikonSa. Yanzu haka Falmata tana dauke da cikin Mukhtari, zuwan da ya yi kwanaki ya dauke ta suka fita, ashe har rabo ya shiga tsakanin…”
“Kana nufm ciki ne da Falmata? Kai masha Allahu, alhamdu lillahi, malam ku shirya kayanta jibi zamu zo mu tafi da ita, domin jiya na je gidan nasa na sanya a kammala duk abin da ya rage. Sam ban san ya dawo’ba ma tunda bai neme ni ba kwata-kwata, amma ina nan tafe jibi insha Allahu”.
Hankalin Malam din ya kwanta, yace “To Allah Ya kawo ku lafiya, amma ku bi komai a sannu, ni ma a nan zan yi wani dan kokarin insha Allahu”. Da haka suka yi sallama. .
Cikin kwanakin nan biyu aka gama shiri ganga-ganga domin tafiya babu fashi da ikon Allah’ inji Hajiya Mariya, malam ya dukufa addu’a kamar yanda matansa su Hajja Basma suka dukufa bin bokayensu da malamansu, suna gani maganar tariyar ta tashi, amma Allah ya fito da ita. _
Tun da sassafe ‘yan daukar amarya suka iso, domin jirgi suka biyo, mutane shida ne nan da nan aka fara. shirye-shirycmen karrama su. Falmata kam labarin bai yi mata dadi ba, domin tasan ba da yawun Mukhtar aka zo daukar nata ba,

Hmmm su hajja basma sun takura fa shin zasuci nasara a wannan karon ko kuwa mu tara domin ci gaba da sauraron wannan qayataccen littafin

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE