MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 15

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 15
Shi kam kai tsaye dakin da aka yiwa Falmata masauki ya nufa. Tana kwance akan gado rigingine kunnenta sanye da headphone ta . lumshe ido tana sauraron, karatun Sheik Sudeis cikin suratul Rahman karatun  ke ratsata, tai tsam kamar tana bacci sai dai rabin hankalinta yana ga tunanin mijinta ne. 
Ya dade a tsaye yana kallonta gaba daya ta sauya masa, kirjinta ya kara cika, fuskarta ta yi haske, Rugunta ya Kara fadi, sai yake ganin kamar ba Falmatansa ba, komai nata ya sauya 
zuwa na cikakkiyar mace. ‘ Ya isa da sassarfa ya sarkafo ta, abin da ya sanya ta bud‘e ido a razané zata kurma ihu, kenan sai dai tuni ya toshe mata baki. Ta waro ido waje cike da tsoro sanda ta ga shi ne, ya kura mata ido wani abu yana sauka a ransa mai sanyi. 
Ta runtse idonta cike da kunya mai tsanani, amma gabanta faduwa yake yi kada wani ya shigo ya tadda su a haka. Sun d‘auki tsawon lokaci a haka kowa ya kasa ccwa komai, da kyar ta daurc ta ce. 
. “Kasan kowa yana iya shigowa dakin nan fa”. 
“Sai me idan an shigo, ko kwartanci na shigooyi? Ashe haka kike Falmata ba ki da kirki?” Yana kokarin janye ta daga jikinsa suka tashi zaune. 
Da sauri ta ce, “Lah! Me na yi maka? Ka yi hakuri don Allah”. 
Ya yi dariya, “Ai kin san laifinki, kullum sai na shigo gidan nan sau uku k0 hudu amma anKi barni na ganki, ke kuma kika Ki satar jiki ki fito mu hadu, ga wayarki kin kashe, haba Falmata kin kyauta mini kuwa? Ina‘ son na ji , numfashin diyana amma kema kin biyewa Hajiya k0 kuma fushin kike yi dani?” 
Ta sunkuyar da kanta wani abu mai sanyi yana ratsa jikinta, irin kalaman da ta ke bukata daga mijinta ke nan, ashe har. yanzu yana sonta? Farin ciki ya sanya idonta ya fara zubda hawayen dadi Sai dai ta runtse ido kam, ta kasa bud‘ewa, ya dinga bin hawayen nata yana lashewa a hankali. Gaba daya ya kashe mata jiki ya dinga yi mata wasu abubuwa dake Kara narkar mata da zuciya ta ma manta a inda suke
sam, ta shiga duniyar bege da soyayyar mijinta, ganin abin nashi na neman wuce gona da iri, ya sanya ta farkowa daga duniyar da suka shiga, don zata ji kunya wani ya taddasu a wannan halin. 
Ta yi kokarin kwace kanta amma ya rike ta gam, ta kama kici-kicin kwacewa da ‘wata . raunanniyar murya da ta shagala yace “Ki barni don Allah na shaqi numfashin diyoyina, ba ki tausayina Falmata? Haba Falmata kina son sanya ni a wani hali ne ko’?” 
Yanda yake maganar ke kara kashe mata jiki, da kyar ta iya ta maze ta ce, “Kasan fa . muna gidan Hajiya, don~Allahka kyale ni kada ta ji ka shigo dakina ta yi mini fada”. 
Sai kawai ta fashe masa da kuka. 
Ya kasa janye jikinshi daga gare ta, kamar yanda ya kasa lallashinta. Shi dai duk sanda ya hadu da yarinyar sai ya ji komai yana sanya shi farin ciki, tabbas wata baiwa ce ita  a gare shi, ganin kukan yaqi karewa ya sanya ya janye ya koma gefe ya zauna ya zuba mata ido, ya yi tagumi da hannuwa biyu, duk kunya ta cikata kamar ta nutse a gurin. Yanayin 
yanda yake kallonta ke kuma tsoratata, ya kwantar da kai yace, “Sai me? Ai na cika ki Ta kasa cewa .komai cikin kwantar da murya, yace “Fatima kina jin Hajiya tana son rabamu bayan muna son juna., don Allah ki daure ki ‘cire kunyarki kice mata kina son mijinki yanzu a cikin gidan nan akwai wanda za ki so sama dani ne? Ni fa ta sanya duk haushin mazan gidan nake ji ma”. 
” ‘Dariya taso Kwace mata, lallai wannan mutumin idan yana wani abu sai ta ga kamar ba malam mai darasun Ba  gaba daya ya sauya mata, ta dai kasa cewa komai. 
Ya daga ido yana kallon agogo sha daya da kwata, ya dafe kai cike da fargaba, domin dai yasan duk inda Hajiyar take ta dawo gida kenan yanzu. ‘ 
Da tsoro yace “Fatima kika ki gaya min dare ya yi na gudu tun Hajiya ba ta rutsani ba, ‘ yanzu dai gaya mini zaki sanar da ita kina ‘sona?” 
Ta dan saci kallonsa tana cike da mamakinsa, cike da takaici, yace“Wai ke
kurma cc ne? To idan ba zaki ce kina sona ba ma ki ce akai ki gidan mijinki ta haka zata fuskanci kina sona”. 
. Dariya ta so kamata yaushe zata iya irin wannan rashin kunyar? Ya matsa kusa da ita cikin kinnenta yace, “Shi ke nan zan yi ta zuba rashin kunya, idan suka ga ciki guda biyu ai sa kai mini matata, bari na gudu kada Hajiya ta kai karshe, sai da safe, ki yi mafarkina fa Fatima na . 
Ya fice da sauri yana waigenta, ta bishi da kallo tana girgiza kai cike da murmushi, ‘wani irin dadi yana bin gabobin jikinta, ashe dai mijinta yana sonta, sai ga ta tana daga hannu sama tana godiya ga Allah, sai ta ji kamar ta kirawo Yagana a waya ta sanar da ita abin da ya faru, domin ta -barota cike da damuwa ita ma, amma dai bari gari ya waye. 
Gogan kam ya fita sadaf-sadaf da sandaaa. cike da farga‘ba yana ta addu’a Allah Ya sanya Hajiya ba tasan ya shigo ba, tana daki. Sai dai me? Kicibus ya yi da ita a falo tana kallo, ya tsaya turus cike da fargaba kamar ba zai ci gaba da tafiyarba, can ya dake ya ci gaba da tafiya 
yana shafa gemunsa. Tabbas da akwai wata kofar da ta can zai wuce. 
Sanda ya iso inda take ya daure yace, “Barka da hutawa Hajiya”. 
Ta daga kai ta galla masa harara cike da takaicin yanda ya hurewa Falmata kunne, domin k0 minti goma bai yi da shiga ba ta dawo, samarin gidan ke gaya mata zuwansa, tayi zaune tana jiran ta ga fitowarsa, ko kuma ta ‘ ga Falmata ta fito a zuciye, sai dai shiru hakan ya nuna mata ya riga ya gama’ kama wuyanta, abu mawuyaci ne ta bata hadin kai su ci gaba da wajiga shi. 
’ Ya yi kasa da kansa ganin irin hararar da take wurga masa, ta ce, “Mutumin kawai, dube ka da gemu kamar mutumin kwarai, amma idan aka tona cikinka Kuda ba zai ci ba. Yanzu to me kake nufi? Ina ce cewa ka yi ba ka son yarinyar nan na je na daukota da zummar ta haihu shi ne ka.fara shiga kana hure mata kunne k0?” _ 
Ya yi kasa da kai cike da ladabi yace “Tuba nake Hajiya, wallahi ban taBa jin kin Fatima a zuciyata ba, k0 dana second guda ne, 
sai dai nasan na tsinci kaina cikin wani kunci da takura a kwanakin da suka gabata, don Allah ki yi haquri ki ci gaba da mini addu’a kamar yanda kika saba, akwai shaidan cikin ‘lamarina da ita, amma tabbas ina sonta, ki yi haquxi”. 
Tausayinsa ya so kamata, amma ta dake don batason badakai dawuri,tace,“Kaga shige ka bani waje,‘ ni ba Falmata bace da zaka yaudare ni‘da zakin bakinka. Ai daman Hamisu ya ce duk mai son a binne shi da ransa k0 a sanya zuciyarshi karaya ya saurari lafazinka, nasan da hakan ma ka yaudari diyar mutane, wuce ni ka bani guri ka ji k0″. 
Sumi-sumi ya fice cike da fargaba don ~ yasan halin Hajiyar tasu akwai ta da jajircewa akan abu, yana fita ta mike ta nufi dakin Falmata waccc ke kwance cike da nishadi da farin ciki, bude kofar ya sanya ta waigawa da sauri, suka yi ido biyu da Hajiya, duk sai kunya ta cikata, kamar kasa ta tsage ta shige da kyar ta iya daurewa tace
“Ashe kin dawo? Sannu da zuwa…“ 
“Yaushe za ki san daman na dawo? Ana 
nemar miki martaba gurin mijinki kina yadda 
da yaudararsa, kece kika ce yazo bana nan k0? tana sane ta yi mata haka
Da rawar murya Na rawa tace “Wallahi ba ni bace ba, kawai gani na yi ya shigo… ina ta cewa “ya fita ya kiya, don Allah kiyi hakuri”. 
Dariya ta kamata, mace da mijinta amma take wannan rawar jikin, amma ta dake ta cc, “A’a ke ya dace na bai wa hakuri. Ai ban san kina son mijin kiba, ki shirya gobe za a kai ki gidan mijinki kowa ma ya huta”. Tana kaiwa nan ta fice
Hankalin Falmata ya tashi gaba daya, ta dafe kai tana fadin, “Na shiga uku, malam ya ja mini jidali yanda Hajiya ke kokari a kaina ya ja ta ga gazawata, har tana tunanin ni na kirawo shi a waya, da sam tama manta da ta yiwa kanta‘ alkawarin daina kiran wayarsa ta kirawo shi. 
Ya shiga harabar gidansa ya ji kiranta, Allah Ya sanya bai dade da cireta daga diverd  ba, da sauri ya faka motar ya dauki wayar har da kwantar da kujerar yana kashe murya, ya ce, “Hello amaryata yaya aka yi?” 
.Sai ya ji ta fashe da kuka, tana fadin, “Ka cuce ni malam, ka sanya Hajiya tana ta yi mini fada, yanzu ma tace gobe dole za a kai ni gidanka, wai ta yi fushi da ni mai tsanani”. 
Wani irin dadi ya kama shi kamar ya taka rawa ya ce, “Au to, me ye abin kuka? Ai ni gaba ta kai ni, da na san hakan zata ce ma ai da tuni na yi inrin haka din, kwantar da hankalinki, yarinya gidan masoyinki .za a kaiki na yi ta baki nama da juice a baki, k0 ‘yar amaryata?” 
Wani malolon takaici ya tokare wuy’anta,‘ sai kawai ta kashe wayar da sauri tana ci gaba da kuka, ya biyota tana ta ringing amma ta Ki d‘agawa; daga karshe ma sai ta kashe wayar gaba daya ta yi wurgi da ita. Ta fada gado tana kuka, da wanne ido zata kalli ‘yan gidan da safe idan suka ji abin data aikata? Mutanen dake karramata da muumtata,.ita kam ta ga ta kanta, dole ta kirawo Yagana da sassafe ta gaya mata abin da kc faruwa. ‘, 
***********************
 Washegari tun da safe Hajiya ta fara yiwa ‘yan uwa waya‘tana sanar da‘su. Ita kam
Falmata ta kule a daki abin duniya duk ya isheta, ‘yar hirar da take fitowa suyi da Hajiyar ma yau dai ta kasa saboda kunya,_ ita kam Hajiya dariya kawai ta keyi a ranta,. da kuma kara jin soyayyar Falmata a ranta, tana ganin wannan ita ce mace ta gari da take yiwa danta fatan samu. 
Shi ma Malam mai darasu yana ofis yana tsaka da aiki ya fara jiyo kiran Hajiyarsa, da sauri ya dauka cikin ladabi ya fara gaisheta, ya so ya shiga da safe ya gaishe su amma yana tsoron kyaran da zata yi masa, don haka dole ya samawa kansa lafiya ya wuce ofis din kawai. 
“Ka je ka gyara gidan yau da daddare za a kawo maka matarka sai na huta da rashin kunya”.’ , 
Tana fadin haka ta kashe wayar da sauri, malam mai darasu ya rasa wanneya dace ya yi murna k0 takaici domin dai a yanda Hajiyar ta yi masa magana ya kula kamar a kule ta ke yi, amma dai yasan ta bata da wuyar saukowa, don haka dai farin ciki ya dace ya yi. Ji ya yi kamar ya doka tsalle amma da yake manya ne sai ya daga hannu yana yiwa Allah godiya. 
Sai ga malam ya fara tattara takardunsa zai bar ofis din, sai da ya fara biyawa OflS din abokinsa Dr. Shamsuddin yana dariya yace Kai malam zan wuce’gida, domin yau ina da sabuwar amarya a sabon gida”. 
Dr. Shamsuddin ya fashe da dariya yana fadin, “Mai darasu a ji tsoron Allah, amaryar nan fa abar tausayi ce, ya dace ka sallami diyar mutane tun Fatila ba ta nakasata ba”. 
Ya yi dariya yana fadin, “Kai dai ka sani, zan gayawa Fatila kana cikin ‘yan adawarta, don tunda na auri Falmata kake mimi”. “Ka yi. ta fada din, an gaya maka ina tsoronta ne, gidanta ma ba zuwa nake ba balle kace, ihe!” Da daga murya yake fada don ganin Malam mai darasu ya wuce da sauri, shi kam dariya ya kama yi yayi gaba. 
Cikin wunin nan ya dinga zirga-zirga da gyare-gyaren gidan, gab da sallar magriba ya nufi gidan nasu domin doki ya hanashi sakat. Ya dinga leke-leke ko zai hango Falmata amma ko keyarta bai hango ba, sai abokan wasansa ne. ke tsokanarsa. Hajiya kam cewa ta yi, “Yauwa  daman ina son magana da kai, zo nan”. 
Da saurinsa ya bita, a zatonsa fada zata yi masa, amma k0 fadan ne ya sanyawa ransa ba zai -ji haushi ba, domin yau ranar farin ciki ce a gare shi, sai ya ji maganar ta sha banban. Cikin kwantar da murya take magana. 
“Ga Falmata nan amana ce na baka, ka dubi yanda mahaifinta ya girmama mu ya yi mana halacci ya ba mu ita, don Allah ka riketa da amana da daraja, kada ka ga auren hadi ne ka. wulakantata, sannan bana son ka sanar da matarka batun tarewar a yanzu saboda akwai wani shiri da nake yi, ka sanar da ita tafiya zaka yi har kayi sati dayan, duk sanda zaka je gidan Falmata ko sanar da ita tafuya zaka yi, kada ka sake ta sani har sai zuwa lokacin da ya dace ta sani din”. 
Mamaki ya cika shi, don wannan doka ta Hajiyarsa ya rasa abin da suka dauki Fatila, shi dai yasan tana kishi mai tsanani wanda kuma yasan tsabar sonsa ne ya sanya ta ke kishinsa, amma yasan Su daukarta suke yi a mai asiri, shi kuwa ya san ba ta yi sam. 
Haka ya fice daga gidan cike da zanccn zuci, sai ya ji duk ya kagu yaga Falmatan, 
amma ganin babu fuska kuma dai yau za a kai masa ita ya sanya ya hakura ya fice kai tsaye gidansa ya nufa.
‘.Su Fatila anci kwalliya an shirya’girki mai dadi na tarbar miji, daya daga abin dake kara sanya ta shiga ransa, akwaita da gyara da kula da duk wani abu da yake so abinci kam ta iya girkawa kala-kala, koda yake ai ‘yar gado ce. . ‘ 
Tana wata kwarkwasa ta tare shi, har ranshi yaji dadi, don haka ya bata kyakkyawar ‘sumba. Sun jima a haka sannan suka wuce dakinsa. Yana cire kaya ya d’an saci kallonta, yace, “ansan abin dana samu? Wai visiting  lacture a jami,ar Abuja, sai dai na gaya musu ba lallai ne su dinga samun yanda suke so ba, yanzu haka wani aiki aka tura ni a makaranta wai har Dubai sai yau ake sanar dani, ga shi karfe tara jirgin zai tashi ma”. 
Babu damuwa a ranta domin tasan duk ci gaban mijinta ne, sai ma ta tashi tana taya shi cire kayanshi har gindin motarshi ta raka shi. har ya fice daga gidan tana d’aga masa hannu, tafiyar tafi komai farin ciki a gare ta,
domin duk wani abu da zai hada shi da ‘yan uwansa ba ta kaunarsa k0 miskala zarratin. 
************************
Hajiya kam ta shirya Falmata yanda ya dace da kayan tsari ‘da komai, domin kuwa tasan k0 wace ce abokiyar zamanta, ita kam tunda aka fara shirin kaita ta ke kuka, domin tana ganin kamar ba ta kyauta ba abin da ta yi, sai da Hajiya ta lallashe ta tana sanar da ita, ta kwantar da hankalinta, tsokanarta ta keyi, fatan dai bai wuce ta zauna da mijinta lafiya ba, sannan taci gaba da yin addu’o’i na tsari da ma’,aiki ya bada, ta kauracewa jin kide-kide marasa kan-gado, wannan ne ya dan sanyaya ranta ta rage kukan, har aka fice da ita daga gidan. 
Suna fita Hajiya ta daura alwala ta fara sallah tana sanar da Allah halin da take ciki na bakin cikin auren danta da Fatila tsawon shekaru goma sha hudu. 
Shin
WACE CE FATILA NE? 
Mu tara gobe donjin ko wacece ita

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE