MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 16

MATACCIYAR RAYUWA

CHAPTER 16

Asalin Hajiya Kumatu mutumiyar Katsina ce, sai dai aure ya tsallako dasu Kano, ita da maigidanta Alhaji Sada mai kwai, sana’arshi ke nan sayar da Kwai tun yana garin Katsina, ‘yan uwanshi basajin dadin aurensa da Hajiya Kumatu domin ba mutumiyar .arziqi bace ba, sai dai yanda ta mallake shi ya sanya kowa ya kyale shi, tunda iyayensa sun jima da rasuwa sai yayye domin shi ne karami.
A unguwar Tarauni suke zaune Allah Ya sanya masa wasila a harkar tasadon haka ya gina katon gida yana“ wadaqa da iyalansa. Hajiya Kumatu tana. mulkinta yanda ta so a gidan, cikin wannan halin Allah Ya doro masa karayar arziki ya zamana yau da kwai gobe babu, da yake Hajiya Kumatu ta karanci fannin girki har tayi diploma .ya sanya ta fara sana‘ar kek da yambal da meat pie da sauran dangin wadannan, kayan, wannan ya-sanya suka dan sami rufin asiri tunda ta fara a sa’a, shi kuma yaci gaba da fita yana zagawa kasuwa yana dan samo abin da ba za a rasa ba,
‘Ya’yansu uku ne‘ Fatila ce babba sai kannenta Hassan da Usaini sai Lariya wacce
Hajiya ke riko ‘yar Kanwarta, amma dai ba ‘yan biyu bane ba, duk wanda ya kwana ya hantse a unguwar yasan yanda Hajiya Kumatu ke mulki a gidan, sai abin da tace za a yi a gidan, gidan kuma sai ya kasance wata matattara ta samarin da basu da mafadi saboda su Hassan kam babu dama ne, ita kanta Fatila halinta kamar Hajiya kumatu ta yi kaki ta tofar ne, har ma kamanninta. Sun taso a shagwaBe, domin babu kwaBa balle hantara, tsakaninsu da gidan su Mukhtar gidaje hudu ne, sam babu wata mu’_amala a tsakaninsu, kasancewar su gidansu na malamai ne, don haka ake zaman doya da manja. Kusan duk unguwar ma haka suke zaune da gidan ‘Hajiyar Fatila.
Ita kam Fatila ta taso irin ‘yammatan nanne masu shegen girman kan tsiya da yanga, ga shi koda yaushe shigarta irin ta ‘ya’yan Turawa ce, hakan ya sanya koda yaushe zaka ga nigogin samari suna sintiri a kanta zuwa Unguwa a motar samari ba wani abu bane a. gurinta, sukan zugata da suna Fatila Senior hakan kuwa yana fasa mata kai
Sai dai ita tunda ta tashi Allah Ya jarrabe ta da Kaunar Mukhtar, wanda ko kallo ba ta ishe shi ba, ya taso nutsattse mai cike da tarbiyya, a nan B.U.K yake karatunsa na Islamic Studies dai-dai lokacin da Fatila ke karatunta a F.C.E, duk yanda ta so yiwa Mukhtar shisshigi ya kulata a banza hakan yana na kona mata rai a wannan hali ya kammala karatunsa na digiri na farko ya sami gurbin karatu na biyu a Jami’atul Madina, ya wuce abinsa ya bar Fatila da ciwon zuciya.
Wani hutu ya dawowanda ya yi dai-dai da shekararsa guda a Madina fatarshi ta murje ya yi kyau ya ajiye dan karamin gemu da saje wanda ya kara haskaka fuskarsa, har lokacin yana nan a dan gayensa, zaka yi zaton yana karantar medicine be ba Islamic ba saboda gayu. ‘ Wata rana ya fita daga gidansu da wani yammaci yana sanye da blue din wando jeans da farar T. Shir wacce aka rubuta da koren launi a gaban rigar, ‘I’am pround to be a muslim’, kansa ya sha taza da sajensa. Yana sanye da farin tabarau sai Kamshin turare ke tashi daga jikinsa. Gidan abokinsa Sani zai je dake makota da gidan su Fatila, suka ci karo ta fito ta dauki wankan yamma da wani dogon siket da ya kamata daga kugunta da’ kasa,~ kuma ya bude sai wata ‘yar mitsitsiyar body hug da ta kamata, fara kal mai kwalliyar zaiba a jiki ta yafa siririn gyale da ya tsaya a kafadarta ta hau bisa dogon takalmi mai tsini ana tafe ana yada hannu.
Ta tsaya turus tana kallonsa, gabanta yana harbawa da sauri da sauri, shi kam kallo daya yayi mata ya dauke kansa, ita kuwa cikin rawar jiki tace.
“Yaya Mukhta: ina wuni?”
Ya juyo ya kalle ta da mamaki akan fuskarsa sosai, domin yasan ba abokiyar maganarsa bace ba, amma sai ya dake ya yace Lafiya lau”. Kawai ya wuce da sauri.
Ta bishi da kallo kirjinta na ci gaba da bugu kamar ta ruga da gudu ta kamo shi ta rungume, wani irin azababben so take yiwa Mukhtar wanda ya kulla shekaru k0 kusa ba ta gabansa, sai ta ji ba zata iya zuwa inda ta yi niyyar zuwa ba ma, don haka ta koma gida da sany’in jiki.
Hajiya Kumatu ta dame ta da tambayar abinda ya dawo da ita, sai ta ce kawai kanta ke mata ciwo, ta fada dakinta ta cusa kai cikin filo, dama zata iya yin kuka da ya fiye mata sauqi.
Kusan kwanaki uku kullum sai ta labe ta ganshi, wasa-wasa ciwon soyayya ya kwantar da ita, hankalin mahaifiyarta ya tashi matuka domin ‘yar lelenta ce.
Da wani yammaci ma suma ta kama yi, aka kwasheta sai asibiti, anyi mata duk gwajegwajen da ya dace, likita ya tabbatar jininta ne ya hau, idan kuwa aka yi sake zuciyarta na gab da kamuwa da ciwo, wannan labari ya dagula wa Hajiya Kumatu hankali ta tsare diyar tata har da kuka tana rokon ta sanar da ita abin ke sanyata wannan tunanin.
Fatila ta fashe da kuka tace, “Hajiya son Mukhtar ne ya haifar mini da wannan ciwon, na kula shi kuma ina cikin mutanen da yafi tsana da alama ko kallona baiyi ma”.
Hankalin Hajiya Kumatu ya kuma tashi, tace “Waye wannan Mukhtar din da har yake yawo da hankalinki, dan gidan uban waye da ba ki sanar dani an nemo miki sonshi k0 ta gurin boka bane?”
Cikin kuka tacc, “Momy babu abin da boka zai iya yi masa, domin dan gidan malam mai darasu ne, kin san gidansa gidan malamai ne…” Sai ta kuma fashewa da kuka.
Hankalin Hajiya Kumatu ya kara tashi, lallai sun dauko ruwan dafuwar kansu, amma dai ai sai an gWada akan san na kwarai. Ta taBa jin an ce wasu irin malaman nan anfi jin dadin yi musu asirin ma, domin sunfi maida‘ hankalinsu ga taimakon mutane ba kansu ba, balle shi Mukhtar da yake kamar dan boko, kuma wanda ake tsoron mahaifin nasa ya kwanta dama, don haka bai dace lokaci guda su sare ba. Ta dinga lallashin diyarta tana nuna mata babu abin da zaifi karfin .boka, zata je ta Sanardashi halin da ake ciki.
Sunyi kokarin buga.duk wani tsafinsu, amma a banza bai yi k0 kyas a zuciyar Mukhtar mai darasu ba, haka ya koma hutunsa ya bar Fatila da ciwon zuciya kamar zata haukace bai san tana yi ba.
Shckara daya ce da watanni zai kammala karatun nasa, don haka a cikin wannan shekarar kam Fatila bata sami kwanciyar hankali ba, don ta sha carry over ma a makaranta, hankalin Hajiya Kumatu ya tashi matuka, duk wata
hanya da zata kulla zumunci da gidan marigayi malam mai darasu ta bi, amma a banza, domin sai hali yazo  daya ake abota.
Da wani’ yammaci Hajiya Mariya tayi sallama cikin gidan su Hajiya Kumatu, Hajiyar taji abin a bazata ta mike har da rawarjiki tana fadin, “A ’a Hajiya  a gidan namu? Sannu da
zuwa”. ‘
Hajiya Mariya ta sami guri ta zauna suka gaisa a mutumce, ta dora da cewar, “Daman Baba ne zai dawo jibi daga tafiyar da yayi karatu, shine nace bari na shigo idan badamuwa da saina baki kwangilar yi masa spring rolls da ‘cak ranar, juma,a zai dawo”.
Wani irin dadu ya kama Hajiya Kumatu domin wannan wata dama ce a gare ta. Da sauri tace mezai hana haba Hajiya, ai Mukhtar d’ana ne, k0 ranar kika sanar ma ai sai a yi masa, kamar na tiya nawa ne zai ishe shi?”
Hajiya Mariya ta rike baki “Kai har tiya? A’a rabin tiya ma ai ya ishe shi, haka ma kek din, na gode, a nawa kike yi ne?”
Hajiya Kumatu ta Kara gyara zama, lokacin fara cusa kai yazo, ta karkata kai ta ce.
“Haba dai ba zan amshi kudinki ba, zan yi masa da kaina, zan shigo da safiyar ranar ma na kawo masa, ki bar kudinki kawai”.
Mamaki ya kama Hajiya Mariya, a ranta take ayyana a darin gamme kuma, amma a fili sai tayi dariya ta ce, “A’a ai ba za a yi haka ba, kema ai ba kyauta ake ba ki kayan ba, ga wannan”. Ta ajiye ‘yan dubu-dubu guda goma don tasan kudin dai ba zai wuce haka ba.
Hajiya Kumatu ta mike dai-dai lokacin da Hajiya Mariya ta mike tana fadin, “Haba Hajiya nifa nace ki barsu, don Allah…”
Hajiya Mariya ta katse ta, “Kada muyi jayayya dake don Allah, sai anjima”. Ta nuflli kofa da sauri.
Hajiya Kumatu ta koma ta zauna tana Kirga kudin, duk abin da zata yi koda na
siyarwa ne ai ba zai wuce dubu hudu zuwa biyar ba, amma ga shi an ajiye mata dubu goma, lallai dole tasan yanda zata tura diyarta ‘ wannan gidan da suka gaji arziki da ilimi‘. Sanda Fatila ta shigo gidan ta ji abin da ya faru, sai da ta. doka tsallen murba ta rungume mahaiflyar tata tana fadin, “Kai Momy amma na ji dadi don Allah yanzu ki dage‘ ki nemo min soyayyar Mukhtar don Allah, don tabbas idan ban aure shi ba mutuwa kawai zan yi”. Hajiya Kumatu ta fashe da dariya, tana fadin, “Kwantar da hankalinki kamar kin zama matarsa kin gama, yanzu ma don yamma ta yi ne, amma a gobe zan tafi gun’boka na sanar da shi duk yanda muka yi. Da kanshi zai zo yace yana kaunarki, dole ne ma ya gaya miki. Dadi ya cika Fatila, daren ranar kam kasa bacci ta yi, burinta bai wuce ta dora idonta akan Mukhtar a gobe ba, duk lokacin sai ya yi mata tsawo. ’ Ranar da zai dawo kam tun asuba suka kama Kiri-kirin aikin shiryawa Mukhtar cak da spring rolls wanda aka barbade shi da magungunan gurin boka, kafin Rarfe goma na
safe sun kammala, aka shirya cikin wasu kwanuka masu hakorin Hajiya irin na da can, Hajiya Kumatu ta dauko da kanta ta nufi gidan da kudirinta a zuciyarta.
Hajiya Mariya kam da murnarta ta tari Hajiya Kumatu, sanda ta buda ta ga yanda aka tsara kayan kuwa kasa godiya ta yi don murna, kusan duk sanda zasu yi sabga a gidan Hajiya Kumatu suke kai wa kwangilar kayan snacks amma ba ta taba tsara shi irin wannan ba, nan fa ta dinga godiya da sanya albarka. ‘
Dadi ya cika Hajiya Kumatu sai ta share gindi aka kama hira tana ba ta labarin ai ita daman girki ta karanta, tun lokacin ba a bai wa karatun mata muhimmanci ba. Hira dai ta miKa sosai har take tambayar Hajiya Mariya k0 ya kusa aure ne Mukhtar din.
Hajiya Mariya ta taBe baki tana fadin, “Wannan dan tsurfar duk matar da ya gani sai yace batayi masaba aikinsan shikam ya fita daban a gidan nan, ga shi da karatun addini a kansa kamar me, amma akidunsa irin na Turawa ne, mutum da k0 kaya bai sanyawa balle rubutu, zanzaro mafa har yau sau’ nayi da
gaske yake dainawa, Allah Ya taimake ni tunda farko malam akan karatun addini ya dora shi, da karatun boko ne kam irinsu ne masu cewa tirinrin girki ke ‘dunkulewa ya zama hadari. a sauko da ruwa, ga shi duk gidan nan babu wanda yafu shi haddar karatun tunda da ka zai karanta miki duka qur’ani da tafsirai kowa yana ganin shi ne ya gado karatun malam, amma ban da dabi’ ar malam sam” .
Wani irin dadi ya kama Hajiya Kumatu ta gyara zama ta karkatar da kai, tace,“Lallai kam kice irin halinsu daya da Fatila, ita ma yanda kika san diyar mangora akan boko, haka ta ke…”
Ta Kara rage murya, “To me zai hana muyi tuwona maina Hajiya‘?”
Hajiya Mariya ta gumtse fuska da sauri tana kallon Hajiya Kumatu da mamaki akan fuskarta tace “Ban gane abin da kike nufi ba Kumatu
Jikinta ya danyi sanyi ganin yanayin da Hajiyar ta nuna, amma sai ta dan dake tana karanta lamarin da boka ya bata, tace Da…
dama ina nufin wai mu hada Mukhtari da Fatila aure…”
“Aure kuma? Ai kin san Fatila ba dai-dai auren Mukhtar bace ba’ Kumatu”.
Ran Hajiya Kumatu ya dan fara Baci, tace “Ban gane abin da kike nufiba, shin muni gare ta k0 baqin tabo ne da ita, k0 kuma shi dan naki dan gwal ne da za,a ce yafi karfin diyata iye?” Ta karasa maganar a hasale.
Hajiya Mariya ta ce, “K0 daya amma dai ai kin san Manzon Allah ‘yace, ka nemarwa’ ‘ya’yanka uwa ta gari, yanda Fatila takw kuwa ai sai irin ta niga, ‘sannan ina ganin yanda mahaifinta ya zama hotiho ai ba zan so nima,, dana ya zama haka ba, kiyi hakuri amma”.ba
Hajiya Kumatu ta hasala matuka, ta miqe jikinta yana rawa ta ce, “Ai dama duk gulmarta da ake yi a layin nan yana dawo‘wa kunnena‘, kuma aure tsakanin Mukhtar da Fatila babu ‘ fashi muddin ina raye wallahi, sai dai duk abin da Zakiyi ki yi ehe”.
Mamaki ya cika Hajiya Mariya kamar
da wata a Kasa, amma da yake ita mai ilimi Ce sai ta ce, “Allah ke kaddarawa idan Fatila
matar Mukhtar ce babu wanda ya isa ya hana, amma zan nemar masa tsari da wannan muguwar kaddarar insha Allahu mace ta gari wacce ta  fito daga gidan daraja zai aura insha Allah”.
“Mu zuba ni dake dan halak ka fasa”.
Ta fice cike da Bacin rai tana huci, Hajiya Mariya ta rike haBa cike da mamaki, sai ga Hajiya Babba ta shigo dakin (uwargidanta).
Ta kalle ta tace,“Lafiya Mariya yanzu naga Kumatu ta fita rau a Bace tana masifa  ko amsa gaisuwata ma ba ta yi ba?”
Hajiya Mariya ta yi ajiyar zuciya, tace, “Bari ke dai Yaya, tsautsayi zan ce ya kai ni nan ta kwashe duk yanda aka yi ta sanar da ita. Hajiya Babba tace“Cabdijan, lallai na yarda da ake cewa Kumatu tana da taBin hankali, banda haka ina gamin Muhammadu da wannan fitsararriyar diyar tata? To gaskiya ki tashi tsaye kin san yaran yanzu da sakaci da addu’a, ga shi dai sun sani din amma aiwatarwa sai ya zama aiki, Allah Ya raba mu da sharrin Kumatu tunda dai ba tsoron Allah take ba
Hajiya Mariya tace “Ke ni kek din nan
da spring rolls din nan ma ban yarda da shi ba,
bari na bada a kaiwa almajirai, domin naga
ab‘i’n daman kamar ta shirya masa, Allah kadai Yasan irin kulle-kullen da ta keyi”.
“Gaskiya kam, ki amso masa take away gidan abinci kawai”.
Da wannan maganar suka share zancen aka baiwa almajirai,  ta bada aka yo masa take away “aka ci gaba da shirin tarbarshi. ‘
Karfe hudu yayansa Malam Hamza ya isa airpozt don hudu da kwata jirginsu zai sauka, sai dai har karfe biyar yana airport din amma bai ganshi ba, ga shi ya kira lambarsa ta can Madina an tabbatar masa da lallai tana rufe alamar ya daina amfani da ita, haka ya hakura ya nufi gida ya sanar da su halin da ake ciki.
Hankalin Hajiya Mariya ya tashi, domin ya tabbatar musu da lallai yau zai iso, amma dai ta‘dake tana ta addu’a tunda ba shi ne zuwansa. na farko ba balle ace bata ya yi. Malam Hamza ne ya kwantar musu da hankali yace, yana tunanin makara yayi jirgin ya taso, amma zai
bincika idan zuwa washegari bai iso ba, da wannan hankalinsu ya dan kwanta, Hajiya Mariya ta zubawa kayan da ta shiryamasa ido cike da takaici.
Shi kam Mukhtar karfe hudu ya iso Nigeria daidai, a airpor tayi yaci karo da Hassan wanda ke bin Fatila suka gaisa a mutumce. Hassan ya ce.
“Daman kai muka zo dauka ga mota can”. Ya nuna motar wani abokinsa, babu musu Mukhtar ya nufi motar yana godiya. A motar ya dinga’ jan Hassan din da hira yaron kam abin har lokacin mamaki yake ba shi, domin tunda Hajiyarsa tace yazi airport ya dauko Mukhtar a motar abokinsa ya cika da mamaki ya ce, _“Momy meye kuma hadinmu da shi da zaki ce muje mu dauko shi, su da suke da motoci kala-kala a gidansu?”
Cikin fada tace, “Ni dai abin da nace maka ke nan, kai ba ka san shi zai auri yayarku ba, tun daga can ya yi waya don ya ce ita yake bukatar ya fara gani kafin ya ga kowa”.
Da farko ya dage yana musu sai da ta matsa sannan ya yarda ya tafi cike da mamakin
sanda aka kulla soyayya tsakanin Mukhtar da yayarsa, sai kuma ga shi Mukhtar din da ko magana ba sa yi sosai bayan gaisuwa yake janshi da hira.
Shi kam Mukhtar yana sauka a Nigeria yaji gaba daya kansa ya juye babu abin da yake buKata illa ya ga Fatila, da kanshi ya dinga mamakin kansa, meye hadinsa da yarinyar? Sai ga shi yaci karo da Hassan kuma, yaji idan bai bi shi ya ga Fatila ba zuciyarsa zata iya tsagewa aikin boka yayi kenan).
Daman an kammala shirya masa girki, abinci wajen kala hudu Hajiya Kumatu ce da kanta ta tare shi cike-da farin ciki tana fadin
“Marhabin malam Mukhtar sannu da zuwa”. . Wani irin farin ciki da kaunar matar ya dinga shigarsa, cike da ladabi ya gaisheta ya sami guri’ ya zauna, tabbas banda aikin asiri babu abin da zai kai Mukhtar wannan gidan domin tunda yake baifu sau uku ya shiga gidan ba shi ma tun yana yaro lokacin mahaifinsa Yana:yana aikensu rarraba zakka ga makota, ne amma yau sai ga shi a gidan.
Hajiyeir ce da kanta ta dinga kawo masa
kayan abinci, sai dai ya kasa Ci, domin har lokacin zuCiyarsa tana cike da mamakin abin da ‘ke faruwa, amma ya kasa tunanin dai-dai, sai da tace “Haba Mukhtar ka ci mana, ai da nan da gidanku duk daya ne, k0 ba ka son wannan a ‘sake girka maka’wani ne?” . Da sauri ya ce,”‘A’a”. Ya kama Ci, sai “dai ‘zuciyarsa sai azalzalarsa take yi akan Fatila, babu abin da yake so illa ya ganta, suna sane suka Boyeta saboda cika umarnin bokansu
la’,ananne. . Ya kasa daurewa yace“W’ai ina Fatila
ne Hajiya’? . ‘ Wani irin dadi ya kamata domin ta tabbatar aiki ya yi kyau, ta kyalkyale da dari’ya
sannan tace . ’ ‘ “Tana ciki, bari na kirawo maka ita ku
‘gaisa”. , ‘ ‘ Ta mike jikinta yana rawa ta nufi dakin .Fatila cike da zumudi ‘
Fatila tana can a daki tana jin duk abin da suke fad’a, tana jin shigowar Hajiyar tata ta doka tsalle ta rungumeta tana fadin.
“Kai Momy na gode, dame zan saka miki wannan abu da kika yi min? Wai yau Mukhtar ne a gidan nan har yake tambayata, tabbas wannan hatsabibin boka ne”.
Hajiya Kumatu tace, “Kinga ki yi sauri ki je, domin na ga ya matsu ya ganki, ina fatan kin sanya kwallin nan da turaren da boka ya ba ki?” _ . _ . .
, “Duk na sanya momy, bari na je naga yanda ‘zamu kare”.
Ta nufi tsohon falon nasu da sauri, wanda a can baya cike yake da kayan alatu a yanzu kuwa sai tsofaffin kujerun da suka ci duniya da tsohon kafet da ya kukkurje ya koke don wahala.
Tunda ta nufo kamshin turaren da ta sanya ya fisgi zuciyarsa matuka ya kurawa kofar da zata ,fito ido, ta fito tana kwarkwasa. amma cikin shigar mutumci, domin boka ya kafa musu sharadin dole ta guji duk wani abu  da

Kut  wannan hajiya kumatun fa hatsabibiyace mai zai faru?
Idan naga comment dari biyu 200 daga yanzu zuwa 10:00am na safen gobe zan kawo muku daga inda muka tsaya har qarshen book 📚 2  zabi ya rage naku 😀

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE