MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 18
MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 18
tana asibiti ciwo zai warke, amma ana dawowa da ita gida jikin zai kuma rikicEwa,
Hankalin duk wani mai Kaunar Samira ya tashi, ganin irin azabar da ta ke sha ya sanya da kanta Hajiya Mariya ta je ta gaya musu tana jin matar Mukhtar ce, wata kila idan aka fasa auren zata warke. Ai kuwa ana cewa an fasa ’auren ta warke garau da ita, daga nan kam da Hajiyar ta dawo akan a daura auren su ma iyayenta suka ba shi hakuri akan suna tsoron kada a kashe musu diya.
Tun daga‘ sannnan duk’inda zai némi aure ba a ba shi, ko da an ba shi za a kai labarin matarsa, iyaye su cc sun fasa sai ya hakura da neman auren, ga shi babu haihuwar kuma da zarar mahaifiyarsa ta fara maganar gajiya da aurensa, sai yayita bata hakuri.
Allah Ya sanya tana da imani tace ba zatace ya saki matarsa ba, tunda itama tana da
‘ya ’ya mata, sai dai ta yi ta masa addu,a Allah Ya yanke masa wahala. ’
‘ A haka aka kWashi shekaru goma sha hudu abin ya ishe ta ganin kowa ya zubawa Fatila ido tana tsula tSiyarta, shi ne fa ta nufi
garin Maiduguri gurin Abbagana har aka aura masa Falmata, to zamu gani shin ita zata zauna ko kuwa ita ma zata hadata da irin abubuwan da take hada sauran matan ne?. .
************************
Falmata tana kan gado taci kukanta ta more, kowa ya watse ya barta kamar daga sama, ta jiyo sallamar malamin nata, ta kasa daga . kanta saboda wani shauki da ke ratsa jikinta, .a hankali ta iya amsa sallamar
Ya jima a tsaye jikin kofa yana kallonta, Kamshin dake tashi daga jikinta da dakin yana rats’a shi, da wani shaukin soyayyar Falmata; Ya taka a hankali ya isa kusa da ita ya durkusa ya dago gyalen da aka rufe fuskarta cikin sanyin murya ya ce. . .
“Fatimatul Zahra, yau kuma kunyata ake ji kenan k0?”
Ta runts‘c ido wani irin shauki yana shigarta, da zata .iya‘ jikinsa zata fada ta rungume mijinta saboda yanda sonsake ratsatA, . ko ina na jikinta. Ya Kara matsowa kusa da ita ya janyota jikinsa ta yi wata doguwar ajiyar
zuciya, ya lumshe idonsa yana lekenta kamar mage cikin kunnenta yake fadin.
“Falmata kin yi kewata ke nan kema? Da Hajiya ta raba mu tabbas da an tauye mini rayuwana kin kuwa san irin son da nakeyi miki? Tabbas da zan iya bude miki zuciyata zaki ga sonki ne ya cikata fal, ki taimakeni Fatima ki ci gaba da rayuwa dani“.
Shauki ya sanya idonta ya fara zubda ruwa, babu abin godiya sai Allah, tabbas Allah Ya sanya tana daga cikin mutane masu sa‘a data zamo wacce Mukhtar keso.
Yau ga ta cikin gidan mijinta mai sonta me yafi wannan dadi? Ba ta taBa zaton kuma zaiyi dokinta irin yanda ya yi yanzu ba, koda yake ai Hajiya ta gyarata matuka. Sunyi wani irin bacci da zai zama tarihi a cikin rayuwarta
Da safe da kansa ya kaita bandaki duk da nauyin cikin da ke jikinta.
Tabbas Falmata ta yarda mijinta yana sonta, domin a tsawon kwanakin bakwai da yayi tare da ita ya nuna mata matukar kulawa da soyayya, sai dai ta kula duk sanda yaji karar wayar Fatila jikinsa bar rawa yake yi gurin
amsawa, yakan kaucewa duk wani abu da zai nuna Falmata na kusa dashi.
Domin akwai sanda ta shigo tana tambayarsa abu ba tasan yana waya da ita ba, sai hankalinsa duk ya tashi ya kuma d’aga mata hannu alamar ta koma, domin kwanansa biyu a gidan Falmata ya kirawo Fatila yace mata ya dawo, amma yana Abuja don kada tsautsayi ya sanya ta kira wayarsa ta shiga.
Ta tsaya sororo cike da mamakin abin da yayi mata, sai tagashiko ajikinsa yaci gaba da Wayarsa abin ya tsoratata matuka, ta koma falo ta zauna ta yi tagumi, ta sanya ran idan ya gama wayar zai fito ya. bata haKurin gwasalewar da ya yi mata, amma sai ta kula shi k0 ajikinsa, bai san ya yi mata laifi bama shi.
Abin nan ya tsaya mata a ranta, tun daga wannan lokacin idan ta ji ya fara waya da Fatila sai ta bar gurin, domin sukan shafe awanni suna hira, sai dai takan yi mamakin rashin zuwa gidan Fatila da ba yayi, duk da kusan dake tsakaninsu.
Ranar da ya cika kwanaki bakwai ya fara Shirin tafiya gidan Fatila. Gaba daya hankalinta
ya tashi matuqa, don tana ganin idan ya tafi kamar bazai dawoba, sai dai tadanne’a zuciyarta taqi nuna masa, amma ta kula shi kansa hankalinsa kamar a tashe yake»
Lokacin da dare ya yi har gurin motarshi ta raka shi, ya matse ta a jikinsa yana tsotsa kamar ba zai sake taba, a lokacin kam kuka sauran kiris ya kwacc mata, cikin kunnenta yake fadin. .
. “Fatima ki kula mini da kanki, kada ki kwanta ba kiyi addu’a ba kin ji ko”.’
Ba ta magantu ba, sai d‘aga kai da ta yi alamar to.
“Sannan ki dinga kwantawa da wuri kada ki bude kofar duk wanda yazo in dai dare yayi, dole ce zata sanya na tafi na barki, bana son na zama azzalumi ne shi ya sanya zan je gurin Fatila, ki kularmin da kanki kinji k0?”
Cikin rawar murya tace“A dawo lafiya, Allah Ya tsare”.
Ya jima yana kallonta sannan ya danne ya shiga motar tana kallonshi har maigadi ya dage masa kafa ya fice sai a sannan taji kuka
ya kwace mata, ta koma cikin gida da sauri tana kuka.
Ta jima a kwance idonta kam babu alamun bacci, ga wani irin saboda Mukhtar yayi mata na lele da kulawa, har lokacin da take nafilarta yayi, ta mike ta dauro alwala ta fara gabatar da sallar. Bayan ta idar ta dauki kur’ani mai tsarki ta fara karantawa, sai ta ji ranta yana mata sanyi, can kamar almara ta juyo wayarta tana kira. ba ta raba daya biyu Mukhtar ne don ~ haka cikin sauri ta yi sadakallahul azim ta’ dauki wayar, tana kallon agogon bango da ya nuna karfe biyu da kwata na dare, cikin sanyin murya ta yi sallama.
Daga can Bangaren ya amsa muryarsa kasa-Kasa kamar mai rada, hakan ne ya nuna mata lallai labewa yayi a wani guri ya kirata.
Maganarsa ta katse mata tunaninta, “Falmata kema kin kasa bacci kamar ni kenan?”
Ranta ya yi sanyi, tace, “Au kana nufin har yanzu kai ma bakayi bacci ba malam?”
Ya yi dan dariya yace, “Ina ce nace a daina ce mini malam din nan k0?”
Ta kwantar da kai kamar yana gurin tace “Ayi hakuri na manta ne”.
Ya yi dariya yace “To gaya mini me ya hanaki bacci?”
Ta yi ‘yar dariya kasa-kasa cike da kunya kamar yana gabanta cikc da shagwaBa tace “Kai to me ya hanaka baccin, sai ka fara fadan naka sannan zan gaya maka nawa” .
Daria ce ta kama shi sosai, yace, “Iye Fatima na ashe kina da wayo haka? To ni bari na gaya miki, sonki ne ya hanani bacci, duk kusurwar da na juya sai na ganki, Fatila ta gaji da tambayar abin da ya hanani bacci har ta yi baccinta zuciyata ta kamu da tsananin sonki, tabbas kullum zan dinga rayuwa cikin kewa idan har bana tare daje to na gaya miki ni abin da ya hanani bacci, saura ke ki gaya mini naki dalilin”.
Ta dinga dariya kawai, har yace, “Kefa nake saurare Fatima”.
“Bazan-iya fada ba… amma…
“Amma me? Kiyi magana don Allah
Fatima ki gaya mini abin da zai sanya ni yin bacci”. . .. Ta yi shiru sannan tace, “Ni ma kewarka nake yi, kuma…” Sai ta yi shiru ta nutse kai tsakanin cinyoyi kamar yana gabanta, ya dinga dariya yana kiran sunanta. Da kyar ta maida wayar kunnenta ta amsa.
Ya ce,”‘To ki kwanta ki yi bacci kinga bake kadai baCe ba k0?” Ta daga kai alamar eh, sai kace yana gabanta, sai da ya cika mata zuciya da dadadan kalamansa sannan ta samu ta yi bacci mai cike da dadi da mafarkin mijinta.
Washegari tunda sassafe tana made a gado ya shigo gidan ya jima yana kallon
yakkyawar fuskarta kafin ya shiga cikin bargon ya rungumota. A tsorace ta farka tana
ganin shine ta kama dariya tana ture shi tana fadin‘ ‘babu kyau fa”.
Sai da ya gama tandeta kamar wata alewa sannan ya fito yana maida numfashi
yana kallonta, duk ya yamutsa kayansa sai da ya sake wasu kayan da kyar ya wucé ofis din
Dai-dai lokacin da ya tashi ma sai da ya biya gidanta sannan ya wucc gidan Fatila.
.Su Hajiya Fatila an ci kwalliya ta daukar magana. ransa kam ya yi wasai da ganin kwalliyar tata, amma a ransa yana tuno kwalliyar Fatima mai sauki da tsari bata fiye ranbatsawa kanta kayan ado ba.
Sai daime? Wani kallo ta yi masa hankalinta a tashe kamar ta ga dodo a gabanta jikinsa ya dan fara Bari yace “Nan fa yaya dai aka yi Hajiya?” ‘
Ta yamutsa fuska tace “Kai ya dace na yiwa ”wannan tambayar, na ga ai bada wannan kayan ka fita da safe ba?”
Ya kalli kayan a firgicc sam ya manta ya sauya kayan gidan Falmata, yayi duru-duru, Allah Ya taimakce shi dabara ta fado masa, yace“Ahaf ashe ba kiji sanda na dawo ba lokacin kina wanka na sauya kaya, domin sai dana fita na ga wadancan ashe ruwan batir ya dan zuba a gefe, mai wankina ma na baiwa”.
Ta dan saki fuska ranta ya yi sanyi, sannan ta taroshi tana fadin.
“Mijina ai dole kasan nayi taka tsan~ tsan da kai, domin ‘yan matan wannan zamanin ji suke yi kamar su figo namiji yana tafe a titi, muje ka yi wanka ka huta.
Shi kam tuba yake ta yi a zuciyarsa na karyar da ya zabga, amma yana godewa Allah da Ya sanya yayi wannan dabarar Allah Ya sanya ya yi ne don a zauna lafiya.
“””””””””””””””””””””””””””””””””
Haka nan ya dinga tafiya gidan Falmata yana yin kwanaki biyunsa a zuwan ba ya garin gaba daya. Rannan sun rabu da Fatila akan ya tafi aiki sai washegari zai dawo, kwanansa daya sai ga Kawarta Diyana ta iso gidan a gigice.
Ta kalli Diyana tace “Ke lafiya kuwa na ganki duk a wani firgice?”
Diyana ta zauna tana haki tace am“Ina Mukhtar yake?”
Ta kalli Diyana cike da mamaki, tace, “Ban gane ba, Mukhtar mijina kike nufi ko wa‘?” _
“Shi nake tambaya, yana ina?” Diyana ta kuma tambaya.
Fatila ta ce, “Ba ya garin, yana can gurin aikinsa kin san ya sami aiki a…”
Diyana ta katseta da hanzari, “Ya sami aiki a ina, ko yana gidan matarsa Falmata…”
, Fatila ta mike a gigice ta dafe kirji tana . fadin, “Na shiga uku, Diyana bana son irin wannan ‘wasan, ai sai ki sanya zuciyata ta buga, don Allah ki daina mini haka bana so”.
Diyana ta cc, “Au ba ki yarda bane? To wallahi Mukhtar ya yi aure, yau kusan watan matar uku da tarewa, naje gidan Aunty Siyama take ce mini na rakata kusa da gidansu wata amarya ce ta tare,wajen wata biyu yaranta suna shiga, to sunce yau ba ta da lafiya sanda muka shiga na hango Mukhtar yana shiga wani daki, da farko na yi zaton ko idona ke mini gizo, na kasa sukuni har muka fito, na kama tambayar Anti Siyama sunan
mijin da dan ina ne, bata rage komai daga adireshin Mukhtar dinki ba, har ta dora da cewar, mahaifiyarsa Hajiya Mariya ce ta shiga da kanta ta bata. amanar yarinyar mai suna Falmata ma. ‘ ‘ ‘ Ashe auren dai da aka daura a baya yana nan, don haka zama bai ganmu ba, don ciki gare ta harya fito ma”.
Tunda ta fara maganar Fatila ke tsaye ganin taKi magana ya sanya ta dafata, sai gata ta fad’i jaBar a sume. A rude ta debo ruwa ta yi kanta tana yayyafa mata.
Tana farkowa ‘da kuka ta farka tana fadin. . .
“Karya ake yi, ace zan yi tarayya da wata mata a son Mukhtar, ki tashi mu je gidan dole na kashe yarinyar, domin ci gaba da wanzuwarta a duniya babban hatsari ne a rayuwata, tunda duk aikin da muke yi a kanta bai yi tasiri ba”.
Diyana ta mike, “Hakan nima na yanke shawarar yi, kin ga ma har da guzurin gubata na taho, idan kuma acid zamu watsa mata to?”
“Idan muka watsa mata acid kowa zai gane mune, gwara dai mu tura mata gubar, taso muje”. Haka nan suka mike idanuwansu sun rufe, sun manta rayuwar ba daya bace ba.
Hmm lallai su fatila fa sunyi nisa basajin kira
To jama,a anan muka kawo karshen MATACCIYAR RAYUWA book 📚 2 mu tara cikin littafi na uku domin ci gaba da sauraron wannan kayataccen littafin