MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 19

MATACCIYAR RAYUWA

BOOK 📚 3

CHAPTER19

Falmata tana zaune a falo ta gyara komai sai kamshin turare yake, kewa ta yi mata yawa, tunanin gida kawai ta ke yi, don haka ta kira Abbanta suka gaisa, suna tare da Innarta a lokacin don haka ya mika mata suka gaisa. _
Hajiya Iyami cike da kunya ta amshi wayar Malam Abbagana yana tsokanarta, ta so ta tambayi Falmata halin da ta ke ciki, da yanayin ‘ zamanta, amma kunyar Abbagana ta hanata, don ‘ haka bayan gaisuwa sai ta mika masa wayar kawai. Ya dinga yi mata dariya yana zolayarta.
‘ Yace da falmata, “Da fatan babu wata matsala k0?”
Ta yi murmushi, tace, “Abba babu, sai dai mugayen mafarkai kawai da nake yi, wani lokacin kuma sai cikina ya tokare ni na kasa bacci kwata-kwata”.
Ya yi dan murmushi yana fadin, “Kowacce mai ciki haka take ji, sai dai kiyi ta addu,’a Allah ya rabaku lafiya. Maganar mafarkai kuma ki dage da yin addu’a kamar yadda na sanar dake Allah dai Ya shige mana gaba, idan
na bullo ta Kanon zan shigo na ganki”
Da jin dadi ta amsa, “To malam, na gode, Allah Ya Kara girma”.
Ta kashe wayar cike da kewar mahaifan nata, sai kuma Yagana ta fado mata a rai. ‘Yan boko kenan, don haka ta fara neman wayar Yagana. Bugu biyu ta dauka da sallama ta fara.
“Wai me ciki uhum ga ni nan tafe, mai ciki, wallahi ba ni son sunan nan”.
Falmata ta fashe da dariya tana fadin. ‘
. .“Wallahi yarinyar nan ba ki da dama. To ya ya karatu?”
Yagana ta yi danyi jim, tace
“To alhmdu lillah muna nan muna cin kwakwa matuqa wallahi, ga kashe kudi, don ma Abba ya dauke min komai, hatta kudin motar makaranta duk sati sai ya bani, abin dai sai godiya babu abin da zance da Abba wallahi, rashinki bai sanya ya manta da hidimar karatuna ba. Lokuta da dama nakan ji ina ma ace muna tare, naso kwarai ki ci gaba da karatu Falmata don irinku masu kwakwalwa ake so a jami’a”.
Falmata ta yi ajiyar zuciya tana fadin.
“Niga babban karatuna kicin din oga…”
Shigowar da wasu mata masu siffar ‘yan duniya ya sanyata yin shiru. Yagana ‘ke tambayarta, “lafiya’?” Cikin rawar murya tace
“Ina zuwa, zan kiraki anjima, na yi baki”.
Ba ta jira jin ,abin da Yagana zata ce ba, ta kashe wayar da sauri ta‘ mike tsaye tana fadin, “Sannunku da zuwa”.
Suka tsaya rike da kugu suna karewa dakin kallo. Tabbas babu ko tantama wannan matar malam ce, cikin dake jikinta ya fito sosai, hankalin Fatila ya kuma tashi matuka, ta Kurawa
falmata ido kamar zata fashe da kuka.
Falmata tace, “Ku zauna mana, kun tsaya? Ban ma game kuba…
“Ke rufe mana baki shegiya, mayya” .
Muryar Fatila ta katse ta, ta dora da cewar.
“Wato duk irin. gargadin da aljannuna ke miki sai da kika yi karambanin shiga gonata k0? To ki sani don ni kadai aka halicci Mukhtar, wannan cikin dake jikinki dake da shi sunanku matattu, sai dai ki haife shi a lahira, yau zan nuna miki ba a shiga gonar Fatila a zauna laflya”.
Tsoro mai tsanani ya kama Falmata, ita ba abin tayi  ihu ba babu mai jiyota ma, babu kuma‘ damar kiran wayar wani, kuma babu damar fita dakin ta kullo. Ta tabbatar dai kwananta ya kare domin a yadda taga alamun Fatila da Kawarta babu tsoron Allah kwata-kwata a tare dasu, za su iya aikata komai.
Idonta ya ciko da kwalla, ta kwantar da murya tana fadin, “Kuji tsoron Allah, ku sani Allah shi ke aiwatar da komai, an riga an rubuta jikin allon lauhul mahfuz ni matar malam ce, shin mutum ya isa ya hana abin da Allah…”
“Ke rufe mana bana shegiya ‘yar boka”.
Fatila ta kuma katseta.
“Kin yi nasarar auran Mukhtar kamar yadda shegen ubanki ya so, amma ba ki sami sa’ar zama da shi ba, ba zan raga miki ba wallahi, wannan karatun naki yafi dacewa da yara ‘yan aji daya na firamare bamu ba”. Cewar Fatila tana huci.
, Diyana ta ce, “Ni fa ban ga amfanin wannan surutun ba. ya kamata mu fara kaddamar ‘ mata kawai…”
Falmata tana jin haka ta nufi daki a guje, amma tuni Fatila ta kamo rigarta ta baya ta
janyota. Falmata ta fasa wata irin Kara cikeda tausayin kanta, Fatila ta wanka mata mari’ guda uku,sannan ta gwara kanta da bango wanda a take a lokacin ya fashe.
Ta kuma sanya ihu tana dafe da goshin. Diyana ta ce, “bari na samo wuka a kicin dinta, don duka zai wahalar da mu”.
“Maza ki yi sauri ki samo”. Cewar Fatila wacce ta nufi Falmata ta kamo gashinta ta fincikota.
Falmata ta fara kokanrin kwatar kanta ta hanyar kai wa Fatila duka, amma ba ta sami damar hakan ba, domin daga yanayin kirarsu ma tafi ta jiki nesa ba kusa ba.
Tuni Fatila ta sanya kafa ta daki cikinta, Falmata ta rike cikin tana ihu da kuka, ta kuma nufarta da sauri ta daga kafa da zummar maka mata a ciki, sai dai salatin da ta ji da ihu ya sanyata waigawa da sauri, dai-dai lokacin da Diyana ta fito da wuqa rike a hannunta.
Gaba daya jikin Fatila ya yi sanyi, fargaba da tsoro suka kamata ganin Hajiya Marya a tsaye.
Haji a ta karaso da sauri tana Kokarin
Daga Falmata‘ tana ci gaba da salatin da sallallami. Ta daga kai tana kallon Diyana da ta taho da wuka tace.
“Subhanallah, kashe musu diya kuke niyyar yi ke nan ban da Allah Ya kawo ni? Tabbas mafarkina bai gaya min karya ba, daman jiya da dare nayi mafarkin kin zo gidan Falmata zaku kashe ta, ashe Allah ne Ya nuna mini ba rabon muji mugun labari, amma yanzu zan yi maganinku”.
Ta dauko waya a jakarta ta fara neman wani layi jikinta har rawa yake yi. Su kuwa sun kasa aiwatar da komai, kiran na shiga tace.
“Hashim maza shigo cikin gidan nan, Allah Ya kaddara ba za,a tadda gawar Falmata ba, kayi hanzari ka shigo….
Kafin ta kashe wayar ma sai ga Hashim ya bayyana a falon, danta.ne na biyar, daman kuma ‘ gashi kakkarfa da taurin zuciya.
‘Ta kalle shi da kulawa tace
“Abin da nake so da kai ka tsaya mini a bakin kofar nan, ka ciro bclt dinka duk wacce tayi yunkurin fita a cikinsu ka zane mini ita, sabawa haka din zai iya sanyawa na tsine maka .
Daman mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, ya tsani Fatila matuKa, don ko magana ba ya yi mata, don haka ya zaro belt dinsa yana muzurai.
Hajiya ta kuma kiran wayarta ta kara a kunnenta, daga can Bangaren Malam ya daga cikin sauri ta ce.
“Maza ka zo gidan Falmata bana son ka wuce nan da minti goma, komai kake yi ina gidan yanzu haka”.
A gigice ya fara tambayar abin da ya faru, ba ta tsaya ba shi amsa ba saboda kukan. da falmata keyi, tana rike ciki ta kashe wayar da sauri ta dauki wani ruwan swan dake kan dan tebur da kofi, ta fara tofa addu’o’i a ciki
Diyana da Fatila kam sunyi mutuwar tsaye, sun kasa aiwatar da komai, kamar an dasa su a gurin, sai satar kallon Hashim suke, fatansu bai wuce su sami kofar guduwa ba. Sai dai ganin yadda Hashim din ke tsaye yana huci yana wulwula belt sun san babu damar dosar kofar fita, don haka ba su da sauran zabi illa murguda baki da suke tayi tamkar za su rufe Hajiyan da keta tofawa Falmata addu’a a cikin ruwan da duka
ko kadan babu nadama ko dana-sani a idon  Fatila sai takaicin kasa cimma burinta ma.
Hajiya ta kammala tofin ta bude bakin Falmata ta fara zuba mata, sannan ta shafe sauran a cikinta. Taci gaba da tofa mata addu’o’i da yi mata sannu.
Hashim ya dalla musu harara, yace
“Hajiya ki bani dama na kirawo police, don ya dace su shigo cikin maganar nan”.
Hajiya ta ce, “Duk abin da ya dace kayi., don wadannan azzaluman sun cancanci kowannc irin hukunci”. Jin an ambaci Police ya sanya Diyana
sakin wuqar dake hannunta, tabbas sai yanzu ta tabbatar da sun yi wauta. Ta durkusa a qasa tana rokon Hajiya ta yi hakuri.
Hajiya ta kalle ta a wulakance tace, “Yan iska irinku bai dace ku yi saurin ‘karaya ba, kamata ya yi kuci gaba da tsayuwa kan kudirinku, wannan karon kun tabbatar ku shegun kaya ne, masu halakakkiyar rayuwar da babu tsoron Allah a cikinta, azzalumai…”
Shigowar Malam Mukhtar ta katse mata maganar, mamaki mai tsanani ya cika shi, sai ya
kama kallonsu yana zazzare idanu. Fatila sai ta sanya kuka cike da tsananin
tsoro da fargaba
Hajiya ta mike tsaye a fusace tana fadin.
“Yau zaka yarda matarka azzaluma ce k0? Allah ne ya kawo ni gidan nan sakamakon mummunan mafarkin da nayi tana cakawa Falmata wuka, yanzu Hashim yana shigowa nace ya kawo ni naga halin da yarinyar nan ke ciki.
Muna isowa tun daga harabar gidan na fara jiyo ihun Falmata, na karaso a gigice. Ina zuwa na tadda tsinanniyar matarka tana dukanta ta daga kafa tana shirin maka mata a ciki, na zabga salati sai ga shegiyar kawarta ta nuna Diyana ta fito da wuqa a hannu daga kicin alamar da ba mu zoba
kasheta za su yi”. Hankalin Malam Maidarasu yai kololuwar
tashi, ya kuma kallon Fatila dake kuka, jikinsa yana’kyarma yaxe. “Fatila wane irin mugun labari ne wannan, ~me kike shirin aik’atawa, kisa?
Ta daga jajayen idanunta da karfin hali, tana fadin, “Eh ai laifinka ne, kai ne munafuki, har kayi aure ka tare da matar ka baka gaya min ba
Bai barta ta kai karshen maganar tata ba ya wanketa da mari har ‘guda uku, yana fadin.
“Ban san dabba nake aure ba sai yau. Ban san baki da hankali ba sai yau, don haka ki tafi gidanku na yanke igiyar aurena a kanki guda daya. Sannan duk wani abu daya sami Falmata ki tabbatar sai na sanya an kama ki, azzaluma”.
Fatila ta fashe da kuka har da dora hannu a kanta, yau ita Mukhtar ya saka? Tabbas ta shiga uku, ina zata tsoma ranta?
Ya nuna Diyana da yatsa yana fadin. “Kema shegiya azzaluma zan yi maganinki wallahi, sai dai ke ma ki tabbatar duk abin da ya sami matata kotu ce zata raba mu…”
“Ka ga don Allah bar batun wadannan kama Falmata mu wuce da ita asibiti a duba lafiyarta, cuta dai an riga an yi mata”.
Da hanzari Fatila da Diyana suka fice daga falon ganin Hashim ya dan kauce tunda ya cika aikinsa, ya bisu da harara yana fadin.
“DakiKai sai kuma abi wani sarkin k0?”
Ba su saurare shi ba, domin sakin da MUkhtar yaiwa Fatila ya firgita su matuKa
Cak Ya sanya hannu ya dauko Falmata don ma tunda ta sha ruwan addu’ar cikin ya dan yi sauki. sai dai kawai barazanar zogi.
Hajiya Mariya tana biye da shi suka fice, dai-dai lokcin da Fatila ta kunna motarta da niyyar ficewa daga gidan, amma gano Falmata rungume a jikin Mukhtar ya sanya ta kara rushewa.da kuka, ta kasa tuka motar, sai. da Diyana tace
“Kinga malama ki tuka mu wuce mu bar gidan nan, ci gaba da tsayuwar tamu ba zai haifar mana da da mai ido ba” .
Sannan ta tuka suka fice amma zuciyarta tana tukuki tamkar zata faso kirjinta ta fito don bakin ciki.
Suna zuwa asibitin dai yake na kudi mai k‘yau aka amshi Falmata duk wasu gwaje-gwaje an mata, Allah Ya taimaka an sami komai lafiya lau, ‘yar buguwa ce kawai aka ba ta magungunan rage zogi, sannan aka yi mata dressing  ga goshima suka nufi gida
A hanya Hajiya ke bashi umarni ya wuce
gidanta dasu. Ya dan juyo kadan yana kara tambayarya
“Hajiya kamar naji kince gidanki k0?”
Ranta a vace, tace “Ashe dai kai ba kurma bane kaji abin‘da nace don ba zan yarda na maida diyar mutane babu wani mataki da aka dauka a gidan ba su’ kara zuwa su cutar da ita, domin sun tafasa har sun kome”.
Gabansa ya fadi tabbas sun ballo masa ‘ ruwa, shi kanshi ya kasa tsira daga fadan Hajiya tamkar shine ya aikata laifin basu ba, ‘don dai a zauna lafiya din ya wuce can babban gidan da su.
Fatila kam Allah ne kadai ya kaita gidan su tana kuka ta sami guri tai parking ta fada gidan kamar an wurgata Diyana tana biye da ita.
Hajiya kumatu an yi zaune akan kujera ana kallon tasoshin larabawa cike da’ tsananin farin ciki-na rashin damuwa kawai ta ga diyar tata ta shigo a fusace kamar an jehota tana kuka, ta mike tsaye a kidime taha tambayarta.
“Lafiya Fatila, meya faru, k0 Mukhtar meya mutu?” ‘
Cikin kuka ta ce, “Ai gwara ace mutuwa _yayi Hajiya da cin mutumcin da ya yi min yau, Mukhtar ya mareni har sau uku, ya kuma hada mini da saki.
“Saki kika ce fa? Kan uban nan”. Ta kai dubanta ga Diyana dake karasa shigowa tace “Diyana da gaske ne wannan labarin da Fatila kc fada k0 kuwa shiryawa ta yi?”
Diyana ta yamutsa fuska tace, “Wallahi da gaske ne hajiya, mari uku ya yi mata a gabana, ya kuma hada mata da saki, bayan shi ne mai laifi da ya dace ace an mara”.
Cikin kidima tace “To duk me ya janyo ya mata wannan wulakancin da cin zarafin kuma?”
Diyana ce ta iya warware mata duk yadda abin ya faru, tun farko har karshe. Ta dora da ccwar.
“Idan da gaskiya ai haquri ya dace ya bata tunda ta kama shi da laifin cin amanarta da yake, .tsinanniyar uwarsa tana nan ya bita da mari har da saki”. .
“Kc tafi can sakaryar banza sokayen WOfi, ‘ kullum ina gaya muku yarane ku, baku san ta kan duniya ba”. Kumatu ta katse ta ta dora da cewar. I
“Da kunzo kun sanar dani ai da na san ta yadda zamu Billowa abin, waye yake irin haka
kai tsaye to yanzu ‘ribar me kuka ci? Ta karkashin kasa ya dacc abi, idan ma kasheta ya dace ayi sai a yi a huta..
Cikin kuka Fatila ta daga kai tace, “Hajiya Momy na ga ciki ne da ita, alamar ya jima da aurenta, k0 kuma tun sanda aka daura auren farkon ba a warware ba daman kamar yadda muke zato, kuma fa Momy ba ki ga gidanta da komai nata ba….”
Sai ta kuma sanya kuka tamkar ranta zai fita.~  Hajiya Kumatu ta ce, “Kinga kwantar da hankalinki tamkar tsumma a randa, sakin da yayi miki da shi da babu duk daya ne Da kafarsa sai yazo gidan nan ya ba ki hakuri muddin ina raye, sannan ita shegiyar da aka sakeki saboda ita nayi alkawari k0 zan yi yawo tsirara sai na ga bayanta, sakin da aka yi miki daya sai an mata uku. Wannan cikin da suke takama da shi kuwa ba’ dai a haifi dan mutum ba, sai dai a haifi dan kadangare ko mushen jaki, bari na kira boka na sanar da shi tun yanzu ma ba sai gobe ba”.
Ta fara kici-kicin neman wayarta.
Tana fadin, “Haba yanzu ai naji
magana, ai mu duk wanda ya ci tuwo da mu wallahi miya ya sha, zamu ga Karyar matar so”.
Bugu daya bokan nasu ya dauka cikin fushi, ta zayyane masa duk abin da ya faru ya fashe da dariya, yana fadin.
“Rayuwarta da mutuwarta .duk tana hannunku, duk abin da kika ce shi za’a yi, ku dai ku tabbatar kun tanadar wa aljani dan amaro jinin sabon jariri da zuciyar kiyashi, da hanjin kuda da dan Zakanya haihuwar lokcin, da majinar Giwa. Tabbas idan kika tanadi wannan zaku ga aiki da cikawa, hahaha… Ya fashe da dariya.
Hajiya Kumatu ta ce, “Boka ai wannan duk aikinku ne, mu dai za mu taro da ruwan kudi kawai sai a bai wa yaran aljannu su samo. Gobe asubar fari zamu kawo maka ziyara”.
Ta kashe wayar‘ tana shafa kan Fatila tana fadin. .
“Ki yi shiru don Allah, Mukhtarin me? Me jiya ta yi ma balle yau? Muddin da kudi da shaidanun bokaye ai wallahi ya yi kadan”.
Da wannan aka samu aka lallashi diyar so, sai dai duk sanda ta tuna yadda Mukhtar ya
rungumo Falmata, ta kuma tuno cikin dake jikin ~
Falmata sai taji wani’ abu mai ciwo ya tokare zuciyarta, wato bayan ita ashe Muktar yana kadaicewa da wata?
Baqin cikinta bai wuce sanin irin soyayya da tattali na mai darasu ba, yanzu duk haka yaje yiwa shcgiyar yarinyar nan? Tabbas k0 saki dubu ya yi mata bata huce ba, domin ta dandani zumar da take baqin cikin kowacce diya ta dandana, ta kuma sab a duk sanda yarinyar ta ta tuno da Mukhtar sai ta yi dariya da farin ciki,. domin ta san ba shi da na biyu, babu tamkarsa a gare ta, a haka ta wuni cike da bakin ciki da takaici.

*** ** ****************
Tun da suka iso gidan Hajiya ake ta lelen Falmata kamar kwai, kawai sai Hajiyan ta kasa yarda da hukuncin su zauna haka, domin tafi kowa sanin halin su Kumatu, yanzu zasu dauki mataki akai, kuma tunda suka san da cikin nan ‘ komai zai iya faruwa Don haka wayar Malam Abbagana ta fara kira, bayan sun gaisa ta kece masa.
“Malam daga gidan Falmata nake yanzu,
don har na taho ‘da ita gidana, cikin nata ke ciwo ga kuma yawan munanan mafarkai da ta keyi, duk ta rame ba ta iya cin abincin yadda ya dace shi ne nace bari na sanar da kai don Allah a taimaka mana da addu’a matuqa, idan akwai wasu lakanai na karya sammu ma duk a bamu, don kasan halin abokiyar zaman nata”.
Sarai Malam ya fuskanci abin da take nufi, wato sammu ake jifar diyar tashi da shi, amma da yake macen kwarai ce ba ta sanar da’ shi kaitsaye ba, ta yi ‘yan dubaru.
Ya yi murmushi yace, “Babu matsala za a dinga taimako muku da addu’a, amma bai wa falmatan na gaya mata abubuwan da zata yawaita yi da yardar Allah za tafi qarfin sammu irin na mutum harna shaidanun aljannu ma”.
da hanzari Hajiya ta miqawa Falmata wayar, Malam ya dinga gaya mata ayoyi da surorin da zata dinga karantawa daman Hajiyar ta miko mata takarda da biro, don haka yana f‘ada tana rubutawa. Bayan ya kammala kuma ya dora mata da nasiha yana fadin.
“Falmata ki dogara da Allah. shi kadai zai isar miki,_kada ki yi_taqama k0 ki dogara dani

Hmm su hajia kumatu fa anyi nisa ba,ajin kira mai zai faru!!!!?  Kudai ci gaba da biyoni cikin tsanaki

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE