MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 2

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 2
wahala acc wannan kamilallan mutumin ba shi da mata hud‘u, sai ta ji idonta ya ciko da kwalla, gabanta ya hau bugawa. 
Tabbas ta hadu da mugun ciwo da ta sani da ba ta je Kano ba, ta sha ayyanawa idan ta zo ta daya a gasar musabaka ta gama cika burinta na duniya, sai dai ta roki cikawa da imani, sai dai a yanzu ta yadda burikan dan Adam ba sa cika harya koma ga Allah, amma dai zata tsananta addu’a idan ta je makaranta ma zata Kara tambayar malaminsu wata addu’ar . 
ELKANAMI BARA’IMUL IMAN 
Falmata ce tafe da Yagana sun taso daga makarantar islamiyya ta Elkanemi Bara’imul Iman suna rike da kur’anai. 
Yagana ta dan daki kafad’ar Falmata tana fadin “Ya Ustaziyya’, duk kin zama shiru kwana biyu na kasa gane kanki tunda muka dawo daga Kano fa kika koma haka, k0 kina tunanin malam mai darasu ne?” 
Falmata ta tsaya da sauri tana kallon Yagana, gabanta yana faduwa, don Yagana ta gama gano laqonta, amma sai ta danne tace. “Yaushe na gaya miki haka?” 
Yagana ta. yi dariya tana fadin, “aiba  sai _ 
kin gayn min ba. yanayinki kawai ya isa ya gaya min, Koba dazun  naji kina  tambayar gwani Sale ya ba ki addu’ur biyan buqatu ba?” Tana maganar tana dariyu. 
Fulmata ta yi wuki-wuki amma me sai tayi gaba da sauri cikeda borin kunya, tana fadin, “Haka kuma kika koma? Tabbas kin wuce sanina”. 
Yagana ta bita da gudu tana dariya, tana cewa. “Tuba nake mu bar maganar Malam mai darasu, mu koma wata. Yaushe ya dace mu shiga islamic Techcology ne, mu amso resue dinmu? Na gaya miki Malam Bukar ya kirani ya sanar dani results  dinmu ya fito,amma kinqi kice  komai, na rasa gane kanki, ko aure kike so ne yanzu kin fasa karatun?” 
Ta waigo ta harari ‘Yagana da keta babbaka dariya, don tasan iskanci kawai ta ke mata. Yagana ta ci gaba da dariya tana fadin “A to meye laifin wanda ,yace yana sonka? Ni fa ban ga aibun Malam Bukar ba Falmata, Allah da gaske nake ya dace ki ba shi dama”. 
Ta shige gidansu da sauri dai-dai sanda suka zo qofar gidan, don idan akwai maganar da ta tsana ba ta wuce ta malam Bukar ba. Yagana taci gaba da dariya kafin ta wuce ta nufi gidansu dake makwabtaka da nasu Falmalan Sai dai gidans‘u bai kai qeruwar nasu Falmam ba. 
A harabar gidan Falmata ta ci karo da Yakwari ana ta gyara damarar bel da alama wani guri zata. Falmata ta bita da kallo cike da mamaki, sanda ta ga ta zaro doguwar riga (after dress) ta dora akai, wato sai taje zata_cire, wai wannan diyar babban malamin dake fad’a a ji ke irin wannan shigar. 
Caraf suka yi ido biyu da Yakwari tasan kwanan zancen, don haka sai ta nufi cikin gidan da sauri. Amma tuni Yakwari ta sha gabanta tana wata girgiza, ta nunata da yatsa. 
“Munafuka, algunguma, na ga kina wani kallona, to wallahi koda wasa na ji wannan magana a gurin Abba ki kuka da kanki, domin nasan hali, an yi gadon gulma da mugun abu ta ko’ina, mtssss Taja tsaki gami da wucewa ta barta a nan tsaye
Falmata ta girgiza kai cike da takaici a ranta, tana fadin “Allah dai Ya shirya, sai na rasa dadin me sukeji a zubarwa da gidan nan qima”. 
Ta kada kai ta shige cikin gidan tana tuno maganganun Yagana tana murmUShi. 
ELKANEMI COLLAGF. OF ISLAMIC TECNOLOGY 
A hankali motar ta yi parking, Yagana da Falmata suka fito daga gidan baya cikin shigar 
mutumci. Yagana tana sanye da dogon hijab iya gwiwa, ta sanya shadda a ciki, yayin da Falmata ke cikin shigarta ta gado, wato doguwar riga har qasa ‘yar Maroco, ta nannade kanta da gyalen rigar irin nadin Larabawa, da medicated  glass a idonta don -tana _da matsalar ido, idan ta ga rana ta kalla sai ta sanya shi k0 idan zata yi karatu. Har sun dan yi gaba direban ya fito yana fadin “ Malama Falmata zan jiraki ne k0 .kuma zuwa zanyinadawo?” .. 
“Ka Jiramu mana, ai ba Jimawa zamu yiba”. 
cewar falmata. 
Yagana ta. kalle ta tana qunshe da dariya, don tasan dole ta sanyata shigowa makarantar, sai da ta hadata da mamansu ma sannan ta yarda suka shigo. .* 
Tace“Anya ya jira mu? Gwara dai ya je ya dawo 
 A qule Falmata tace “Eh, da yake kwana zamu yi k0, kin ‘san Allah zan komawata cikin mota Allah kuwa”. 
‘ “A ’a, bani na kar zomon ba, rataya aka bani Wuce mu je”. 
Suka wuce cikin nutsuwa suna tafe Yagana 
*na zuba, yayin da Falmata ke binta da eh ko a‘a 
Ko rirgiza kai da take ita ba ma’abociyar ?zance bace
Ran Falmata ya yi wasai ganin harsun kusa kammala abin da zasu yi ba su hadu da Malam Bukar ba, wanda shi kuma Allah Ya doro masa qaunarta kamar ‘ya hadiye zuciya ya huta Ita kuma k0 miskala zarratin ba ta qaunarshi sam baya ranta, ta tsani k0 had‘uwa suyi. 
Sun kammala komai sun fito cike da murna domin sakamakon nasu ya yi kyau matuka, suna da damar neman gurbin karatu a jami’a. 
Suna gab da isa inda motarsu take suka jiyo ana kwala musu kira,‘ sarai Falmata ta ji shi, kuma ta gane k0 waye-don haka ta qara sauri, sai da Yagana tace
“Kina ji Malam Bukar yana kiran mu; ki tsaya bai dacemu wofintar da kiran malaminmu ba k0?” ‘ . . 
Da wann‘an dabarar ta shawo kanta ta tsaya, amma gaba daya ranta ya cunkushe ta rasa irin Kin da take yiwa malam Sadik, shi dai ba muni ne da shi ba balle munin hali, ammn tunda ya ambata yana sonta ta ji bata ko kaunar ganinsa. A can baya takan girmama shi matuka, don yana cikin malaman‘da tafi qauna. da‘ngane da aikinsu, am‘man tun suna gab da zasu fara jarabawar WAEC da ya bayyana mata abin da ke ransa ta ji tana jin haushinsa har
takanqi halartar darasinsa da yake musu na share fagen jarabawa. 
Shi kam ya kasa fushi don sone yake mata na gaskiya, mai kuma zafinnan da nukurkusar zuciya, irin son da komai zaka yiwa mutum ba ya jin haushi bare ya daina ganin wanda yakeson“ da qima. 
Ya iso inda suke yana haki saboda saurin da ya yi, gaba daya hankalinsa yana kan Falmata, wacce ta sha kunu matuKa kamar an aiko matada -sakon mutuwa. ‘ 
‘ Suka .yi cirko-cirko su dukkansu kamar .zakaru aka rasa wahda zaice da dan uwansa wani ‘abu. 
Yagana ce ta yi saurin durqusawa tana fadin, “Malam ina wuni” . 
Abin da ya sanya ita ma Falmata ta yi saurin durqusawa ke nan tace “Ina wuni”. 
Da ’sakin fuska ya amsa, bakinsa yaqi rufuwa saboda murnar ganin Falmata. 
Yana kallon idonta yake fadin, “Yagana babu daidaia ‘me ya kawo gaba ace har ku shigo makarantar nan amma ku kasa nemana mu gaisa, kamar na yi “wani laifi
Yagana ta kalli idon Falmata don tasan da ita yake, ta ce “Ka yi haquri Malam, da yake
dircba yana jiranmu ne shi ya sanya muke ta sauri”. 
Ya matsa gaban Falmata don ya kula bata da niyyar yin magana, yace Hajja Falmata, rannan ina ta turo saqo shiru babu amsa, ni na kasa gane laifin da nayi miki Falmata”. 
Ta sunkuyar da kai, shiru tayi ta kasa cewa komai. Yagana kuwa sai tayi saurin barin gurin ta nufi motar, ta bi Yagana da kallo cike da takaici kamar ta bita da gudu, amma tasan ba zata iya yiwa Malaminsu haka ba, don haka ta ci gaba da tsayuwa tana wasa da zara-zaran yatsun hannunta. 
“Uhm! Ke nake saurare, idan akwai wani laifi da na yi miki ki sanar dani, domin dan Adam ajizi ne  tana iya yiwuwa na aikata wani laifi ne wanda ni a gare ni nake ganin ba laifn bane”. 
Cikin qosawa da zancen shi, Tace “Nifa malam babu abin da ka yi min, kawai dai, uhm… uhm…” Ta kasa qarasa abin da ke ran nata. 
Ya kwantar da kai cike da tausayin kansa, yacc, “Kawai dai me? ko kina nufin kawai dai sona ne ba kyayi?” 
Ta daga kanta da sauri suka hada idanu, ganin yanayin da ya shiga duk sai ya ba ta tausayi. tayi saurin kawar da kanta gefe tana fadin. ‘ 
“Ni fa ba haka nake nufi ba Malam”. . 
“To me kike nufi Falmata? A tunanina 
soyayya bata zama qiyayya, haka kawai Allah Ya jarrabeni da matuqar sonki, shin wanda yace yana sonka ya yi laifi? Haba Falmata MENE NE LAIFIN ZUCIYA don ta ga abu tana so? Ki kalle ni da kyau kin sani ‘yan mata nawa ke sona a makarantar nan, amma ni kuma ke Allah ya dora mini sonki, ke kuma kina wulakanta ni. Don Allah ki tausaya min mana Falmata, ko ba ki san zafi da radadin so banc?” 
Matukar tausayinsa ya kamata, amma kuma ba ta jin k0 digon sonsa guda daya a cikin zuciyarta, tabbas acan baya ba ta tausayinsa k0 miskala zarratin, don tana ganin zakewa ce kawai irin tasa. Sai dai a ‘yan kwanakin nan da ita ma ta gamu da irin ciwon da ya harbe shi ta ke tausaya masa, domin ta fuskanci zafi da radadin so ba abu ne mai sauKi ba. 
Cikin kwantar da kai, tace da shi. 
“Malam ka gama mu zamu  wuce dircba yana jiranmu”. ‘ 
Wani abu mai ciwo ya tsaya masa a makogwaro, wato duk abi‘n da ya fadi a banza ma ke nan? Amma dai fushin fari ba nashi bane dole ya bi komai a sannu yana ganin watakila zaici ‘riba a gaba, don haka ya karkata kai yana fadin. 
“Shi kenan Falmata. kuje kawai. amma don 
Allah idan na kira a dinga daga wayata, kin ji k0?” 
Ta daga masa kai alamar to, sannan ta wuce da sauri tana ajiyar zuciya. Tana jinta kamar akan qaya take daman. 
Ya bita da kallo yana girgiza kai, a ransa kuwa addu’a yake Allah Ya, sanya Falmata matarsa ce uwar ‘ya’yansa, domin Allah Ya jarrabe shi da sonta matuka. 
                    . …………. 
Kai tsaye ta wuce sashinsu ta shige dakinta ta sillo wanka, ta fita cikin wata doguwar riga mai yankakkcn hannu, kanta da ya sha kitso qanana irin na bare-b‘arin usuli ta sanya’ hula mai kyau irin ta mata. Kai tsaye kicin ta wuce ta fara zubo abinci a cikin faranti ta nufi falo. 
Ta tarar da mahaifiyarta zaune akan kujera tana kallon tasoshin Larabawa, ta isa kusa da ita tana fadin. 
“Hajja, sannu da gida”. 
Mahaifiyar tata ta dan kalle ta, sannan tace “Yauwa, har kin dawo? Ina sakamakon naku? Allah dai ya sanya ya yi kyau”. 
Ta yi dariya tace “Yana daki, yunwa ce ta 
gigita ni har na manta ban dauko ba. Bari na dauko miki shi…” 
“A’a, gama cin abincinki tukuna, abin da ba guduwa zai yi b,,,,, 
Ta sami guri ta zauna bisa kujera ta fara cin ‘abincin nata tana kallon film din da Babar tata ke kallo a tashat MBC 4, ita dai tana son fina-finan Larabawa ita da Abbansu, k0 don suna jin Larabcin nc? Oho! ‘ 
Hajja Iyami ta kalli diyarta tana fadin, “Kece ‘yar sarkin son zuwa  Kano, to yau dai Allah Ya kawo Hajiya Mariya, sai hankali ya kwanta k0?” 
Wani irin dadi ya cikata kamar ta shide ta dire farantin abincin tana fadin, “Kai Hajja, da gaske? Kai amma na ji dadi, kin san na so zuwa gidanta sanda mukaje, amma malaminmu ya hanani, bari naje na gaisheta. Tana ina?” Duk dadi ya cika ta. 
Hajja .Iyami,ta kalleta cikc da mamakin yadda take zakwadi duk ta wani gigice ta rasa irin son da takeyiwa Kano haka. Tayi dan murmushi tana fadin
“Ina zaton tana can sashen Abbanku, ki bari ta shigo nan mana sai ku gaisa”. 
Ta yi dan jim, sannan tace“Don Allah Hajja ki kyale ni naje na ganta, ina son mutanen Kano ko dan ni yadda ake ba ni labarinsu?” 
Uwar tabw baki tana cewa, “Sai kin dawo, amma dai ki shiga a hankali kar ki bugeta garin wannan rawar kan naki”. 
Ta yi dariya gami da nufar dakinta ta d‘auko qammin hijab dinta ta nufi sashin mahaifm nata. 
Sai dai me? Sanda ta isa tana gab da shiga ta jiyo alamun kuka da magana, ta tsaya turus cike da tsoro, don ba ta raba daya biyu muryar bakuwar da tazo ce Hajiya Mariya ke kukan, ta yi kamar ta juya ta koma, amma abin da take fadin ya dauke mata hankali. 
Gaba daya hankalin Malam Abbagana ya tashi jin kukan da Hajiya Mariya ta ke yi. 
Ita kam kukan shibe mafita a gunta, cikin kukan ta ke fadin. 
“Yanzu Abba don qasa ta rufe idon malam sai ace ba mu da wani mai tsaya mini akan lamarin yaron nan, mutum idan ka kalle shi kamar mutumin kirki, amma sai ,kayan haushi, yana zaune da yarinya _tsawon shekaru tana juya shi ita ba haihuwa take yi ba, balle ace rabo ne rabon dai  wahala, ku kuma kun zuba ‘mini ido? Sau nawa nake sanyawa ya yi aure sai komai ya kankama sai ta rushé maganar?” 
“A’ a Mariya, banda zargi abu ne mai muni a addininmu, tunda kin sani zato zunubi ne k0 da ya 
Kasance gaskiya ne”. 
“Wallahi mallam babu zargi a cikin wannan batu, da kanta take aiko min da wai na daina asarar kudina shi da aure sai dai a lahira idan har ana yi, k0 kuma ba ta raye. Gwara na tsine masa na bar wa duniya don ita na haifawa”. 
“Subhanallahi, abin har ya kai ga haka? Lallai ta yi nisa, ki yi hakuri, ki kwantar da hankalinki insha Allahu ni da kaina zan yi maganin abin, ki daina zaton don malam ba shi da rai zamu zubawa iyalansa ido suna watangaririya, ban san matsalar Muktari ta. kai haka -ba, amma ki sha kuruminki, ki daina’ qokarin yi-‘masa baki, insha ‘Allahu za -a warware komai, ba dai aure kike son ya yi ba? Sai dai ki yi imani da Allah Shi ne mai bayar da da, ba wai zamu yi masa aure ba ne don matar tasa ba ta haihuwa ba ne, sai dai muna son nuna mata ba -ta isa ‘ta ja da ikon Allah ba. Shi kuma ya sami nutsuwa da sauki a rayuwarsa, domin irin wadannan matantashin hankali ne matuqa, kedai ki dage ki yi ta addu’a. 
Idan kin koma kuma kada ki gaya masa yadda muka yi da ke, idan na kammala shirina zan neme ki a waya na sanar dake shi kuma zab kira shi mu yi maganar, amma don Allah ki daina ambaton tsinuwa, tunda ita din ai ba gyara take yi  sai dai qara lalata abu”. 
“Na godc Malam Abba daman nasan kai kadai ne zaka iya share mini hawayena”. 
“Babu komai, Allah dai Ya shige mana gaba, kuma ina tunanin cikin yaran gidan nan zan samar masa matar auren, zan yi istihara dai nu“ gani”. ‘ 
Falmata dake labe ta dafe qirji cike da tsoro da faduwar gaba, sai taji kamar ita za aba wa Muntarin da akc fadi lallai da an kashe ta, ita da ta gama burin ta bi Hajiyan Kano ta yi ta binciken masoyinta, k0 ta samu ta dace yace yana sonta, gaba daya Sai murnarta ta koma ciki, ta ma fasa shiga don kada tsautsayi ya fada kanta, don haka ta juya sumi-sumi tabar gurin. 
. Harta nufi sashinsu sai kuma ta tuna abin da zata ceda Hajjanta ya hanata shiga, sai ta Wuce kai tsaye ta yi wajeta nufi gidan su Yagana. 
Sai da aka yi sallar magriba sannan ta dawo gidan. Tana shiga mahaifiyar tata ta hauta da fada. 
“Ina kika shiga keda kika ce za ki je ku gaisa da Hajiya Mariya, ta shigo tun d‘azun tana nemanki?” 
Ta kwantar da Kai, tace, “Hajja na nufi dakin na ji suna hira da Abba, to don kada na katse musu hirar tasu ya sanya na wuce gidan su Yagana”. 
Ta yi ajiyar zuciya, “Ai shi kenan, sai kije tana wajen Hajja Kaltum ku gaisa”. 
Ba kamar dazu ba da take cike da muma ta fice,mahaifiyar°tata ta bi ta da kallo tana saka wani abu a ranta. 
Ta d’an jima kofar sashin Hajj: Kaltmn. ~ saunan ta daure ta shiga da sallama. ‘ 
Hajiya Mairo ce ta fara waigowa, sai ta saki murmushi tana fadin, “Duk yadda aka yi wannan . ce Falmata k0?” 
‘ Hajja Kaltu‘m ta saki murmushi, tace “Yaya kika gane ta?” ‘ 
Ita ma ta yi murmushin, ta ce, “Ai kamar haka Abba ya auro Iyami tana ‘yar kucilarta su Yakolo suna ta mita da tashin hankali kamar a kanta aka fara yi musu kishiya”. . 
Hajja Kaltum ta yi dariya, tana fadin. “Yakolo ke nan, sai addu’a ” . 
Falmata ta shiga ta durkusa gaban Hajiya Mariya tuna fadin, “Hajiya ina wuni?” 
“Lafiya lau, ya ya karatu Falmata?” 
“Alhamdu lillahi’.
Hajiya Mariya ta dubeta tana fadin. 
“Ashe haka ku ka sha Kano ba a kawo mana ko
ziyara ba Falmata? Sai yaushe za, azo mana, ko sai an kammala karatu?” 
Gaban Falmata ya yanke ya fadi, amma sai ta kasa cewa komai, sai duqar da kai take, tana yaqen dole. 
Hajja Kaltum cw tace, “Ai ba ki ga takaicin da ta sha ba, ta kuma kammala karatunta, kin san tun bayan su Zanna da Sani ba a samu mai koqarin Falmata a gidan nan ba, kin san tana cikin wadanda zasu wakilci Nigeria a gasar karatun qur’ani ta duniya, jibi za su tafi ma”. 
“Kai masha Allah; ai yarinyar da gani akwai nutsuwa”. har Hajiya Mariya tana kallon Falmata cike da sha’awa; a ranta tana addu’ar Allah Ya sanya malam Abba ya zabarwa Mukhtari ita, domin diyoyin Yakolo ma ba su da wani banbanci da matar tasa, amma dai ba zata yi azarbabin magana ba, za dai ta yi ta addu’a kawai a zuciyarta idan rabonsu ce Allah sai Ya ba su ita. 
Haka nan ta tashi ta bar dakin sumi-sumi cike da kunya da faduwar gaba, don jin yadda Hajiya Mariya ke ta zuzuta halinta. 
Bayan ta fita, Hajiya Mariya ta dubi Hajja Kaltum ta ce, “Hajja Kaltum me ya sanya Yakolo ta yi sakaci da tarbiyyar yaranta haka, kinga dana shiga sashinta wani irin kallo da suka dinga mini
kamar sun ga kashi, sai da tace su gaida ni fa sannan suka gaishe ni da shigarsu kamar ba diyoyin me fada aji ba babban malami . Ita kuwa ‘yar kadifire Basma sai wani harare-harare ta ke yi ‘yar kora, ashe har yau halin nan dai nasu yana nan, ‘ babu abin da suka sauya?” 
Hajja Kaltum ta tube baki, ta ce, “Kema dai Hajiya Mariya ai an ce idan kun jima baa kaga mutum ba in kun had‘u tambaye shi wani abun ba halinsa ba yakolo bata tunanin abinda zaije yazo bayan ita ya dace tafi kowa taka tsan-tsan ita da Allah Ya bai wa ‘ya’ya mata amma ta watsar da duk tarbiyyar da Abba ke basu, ita kam Basma ai batadakaico tunda batada kuda agidan ko?Idan kin ~yi magana tace an tsane ta ita da ‘ya’yanta, kinga k0su Bulama na hana su yiwa ‘ya’yanta fada domin tace sun tsanesu saidai nata su hanasu  , gidan matansu kuwa babu abinda suke yi sai hada gulma a-zo nan ayi ta dambarwa, wani lokacin ki ji wai bar da dambe, to me ya yi zafi lamarin dai sai addu’a 
ai”. Gaba daya sai jikin Hajiya Mariya yayi,sanyi  tabbas idan tunanin Abban ya fada kan diyoyin Hajja Yakolo an yi badi babu rai kenan k0 ace b, a rabu da Bukar ba an haifi Habu. Amman sai wata dabara ta fad‘o mata ta gyara zama tace
Hmm yanzufa aka fara mezai faru mu tara domin ci gaba da sauraron wannan danbarwan

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE