MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 22

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 22
ya QULu yaCe “Yaya Malam mota fa muka rasa, da kyar muka samu motar data dawo damu. gidan, sauran kiris ’nayi waya can babban gida nace a kawo mana mota ta dauke mu ma”. 
Ya kalli Hashim da sauri, yace“Saboda baka da hankali, ai niya dace ka yiwa wayar ma idan kun rasa motar ba can gida ba”. 
Yana sane ya fadi haka, don haka yace “To ai na ji kace kana da unguwa mai muhimmanci ne kada a sanya ka taho ba ka gama abin da kake yi mai muhimmanci ba”. 
Tabbas ya-kula magana Hashim din ke gasa masa. don haka yace “Ka ga malam wuce dakinka ka kwanta dare ya yi, sai da safe”. 
Hashim ya wuce yana dariya kasa kasa don yaji dadi da ya amayar da abin dake ransa. ita kam Jidda tun kafin yace mata wani abu ta wuce dakinta da sauri. 
Ya kalli Falmata sai yaga duk ta sauya. Ta kumbura tai wani iri, sai yaji duk tausayinta ya cika shi, ga kuma kunyar data rufe shi ta abin da ya aikata din, domin bayan ya fita din ya tsinci kansa da tunanin abin da ya aikata bai dace ba. sai Ya fara tunanin kuma  wacce irin mota zasu
hau kada suje wani abu ya Same su, sai yaji duk unguwar da zaije din ta fita daga ransa. daman wata ziyara ce zai kaiwa wani abokinsa, don haka bai wani jima a gidan ba ya juyo ya zauna a gida yana ta addu’ar Allah Ya dawo da su lafiya. domin bai ma san da Hashim suka tafiba. 
. Ya dan kwantar da murya yace “Ya ya kuka yi da likitan? naga katin naki”. 
Ta isa ta dan durkusa ta bashi cike da ladabi, ta sami guri ta zauna. . 
Ya amsa ya fara karantawa ya daga kai da sauri yana dubanta, yace, “Kamar jininki ya dan hau k0?” 
Tana wasa da yatsunta ta ce, “Eh haka ne daman na gaya musu bana samun bacci ga yawan ciwon kai shi ne suka yi mini awon jini suka ce jinina ne ya dan hau kadan, amma sun rubuta min magunguna da dokokin da zan bi”. 
Ya tsareta da ido cike da fargaba yace, “Fatima me kika sanya a ranki da har ya sanya jininki hawa haka? Gaskiya ban ji dadin ganin wannan sakamakon ba, to tsaya ma wai me ya sanya jininki hawa k0 wani abu nake miki?” 
Wani malolo ya tokare wuyanta, wato shi
 ‘ duk abin da yake mata bai sani ba ko ta so tace ch, amma gudun rigima ya sanya ta girgiza kai ‘ alamar a’a. 
Ya tsareta da idonsa, “Kinga ba kada kai zaki yi ba, baki zaki bude ki yi magana, ni kam duk kin tayar mini da hankali wallahi”. 
Ta yi shiru tsawon lokaci tana son ta gaya masa abin da ta gaya masa kwanaki sai dai tana 
. tsoron kada ya balbaleta da fada don haka tace, “Ni fa babu komai”. 
Ya kada kai, “Shi kenan, amma don Allah kada ki sanar da Hajiya kina da wannan matsalar, don ba zata taba yi mini uzuri ba”. 
Ita dai kawai “To”. Ta cc masa, sai dai a daren ta ji dadin yadda ya dinga ba ta kulawa kamar zai maida ita a cikinsa. A ranta ta shiga addu’ar Allah Ya sa hakan har zuciyarsa ne kuma ya sanya ya dore ya koma mata kamar can baya. 
*** ** 
Da safe gidan babu kowa sai ita daya, ‘yan makaranta sun tafi  Malam shi ma ya tafi aiki, sai ita kadai tana kwance akan kujera ta 
kunna ‘tashar Saudi Sunna tana bin karatun kur’ani da suke yi cikin Suratul Bakara, taji ana kwankWasa kofar gidan, da yake kullewa takeyu
Ta yunkura da kyar ta mike ta nufi kofar tana tambayar, “Waye”. 
Daga can waje ta ji ana cewa, “Nice
Mamaki ya kamata don ba ta shaida muryar ba, kuma tun bayan zuwan su Fatila gidan ba ta barin gidan a bude take kulle kofarta sai taji waye sannan ta bude, amma dai tayita ‘yan maza tana addu’a a ranta ta bude. 
“ Wata mace ta gani da kullin kaya a kanta, sam ba ta san matar ba,kafin tai magana matar ta rigata. 
‘ “Sannu da gida Hajiya,atamfofi da lesika nake siyarwa ko zaki siya?” 
Gaban Falmata ya Yanke ya fadi, sam ba ta yarda da matar ba, sai take Jin muryarta wani iri kamar ba ta mutaneba, amma sai ta dakc tace
‘ “A’ a, Allah Ya bada sa’ a mijina ke siyowa’.’
Matar tayi dariya tana fadin, “KO zaki
sammin ruwa don Allah na sha‘?” 
Falmata tace “Me zai hana? Shigo na ba ki mana”. 
Falmata ta juya ta nufi cikin falon, matar ta dunkule hannunta ta nuna Falmata da shi gami da binta cikin falon kai tsaye, sai dai tana shiga sautin karatun kur’anin da ya cika falon ya doki dodon kunnenta, sai ta janye hannun nata da ya fara fidda wani‘ haske ya nufi jikin Falmata, kai tsaye ta dafe kanta, kan kace kwabo ta bace daga gurin Bat babu ita. 
Falmata da ta nufi kicin kai tsaye ba ta kula da abin da ya faru ba, don haka ta d‘auko ruwa da kofi ta dawo falon, sai dai ta ga falon wayam babu matar, kofar tana rufe har lokacin. Mamaki mai tsananiya cikata ta kama waige waige tana fadin. 
.“Baiwar Allah ina kika shiga ne? Baiwar Allah!” 
Ta nufi kofar da sauri tuna leqe, sai dai abin da ya bata mamaki bai wuce ganin kofar shigowa gidan babbar kofar a kulle takeba, babu alamar an budeta wani ya shigo, kuma babu matar sam. Tsoro ya kamata matuka, to kodai ba mutum bace? 
Sai ta fara karanta ‘ayaturkursiyyu a fili cikin daga murya ta koma cikin gidan da sauri, amma bata kulle Kofar ba ta nufi kujera ta zauna sai taci gaba da bin karatun suratul Bakara din gar tana lumshe ido, sai ta ji duk wani tsoro da fargaba sun fita daga ranta tsawon lokaci tana wannan halin, sai da ta tabbatar ta sami nutsuwa. 
Kamannin matar suka fara bijiro mata, ‘ ‘ 
tabbas ba ta yi kama da irin mutanen da ta saba gani ba, duk da ba wani abu na muni a tattare da ita, amma yanayin idonta da kallon da ta yi mata da muryarta ya sha bamban da na mutane. Ba taga kafar matar ba sam, haka dai. ta wuni tana addu’a da jin karatun kur’ani har zuwa sanda . Jidda ta dawo sam ba ta sanar da ita abin da ya faru ba, ta barwa .cikinta komai. ‘ . 
Aljani Kusugu ya isa gurin boka a gigice yana nishi ya fadi yai gaisuwa a lokacin Hajiya Kumatu da Fatila da Diyana suna durkushe a gabansa suna jiran dawowar aljanin Kusugu da boka ya tura gidan Falmata wanda ya sauya halittarsa zuwa ta mutum, kuma mace har da kayan talla domin ya dauko abin dake cikin 
Falmata din;
Duk da ba sa ganin aljanin, sukeba am‘ma suna jin numfashinsa duk a tsorace suke domin a gabansu aka aike shi din.
Boka ya daka masa tsawa yana fadin, “Yaya na ganka hannu babu dan cikin nata, bayan mun baka jinin tsohuwa mai kusumbi ka tsotse?” 
Cikin nishi aljani Kusugu yace “Ran boka ya dade yarinyar nan tana tattare da abubuwa masu dama da ba zan iya tunkarar jikinta ba, sanda naje ma karatun Kur’ani ta ke saurare cikin surar da ke saurin halaka mu, suratul bakara, don haka na kasa yin komai na bace, tabbas da na ci gaba da wanzuwa tare da ita da babu abin da zai hana na kone kurmus kamar yadda dan tsito ya kone”. _ 
Ran boka ya Kara baci matuka, ya cika fam kamar zai fashe, yace “Yanzu kana nufin ka sha jini a banza ke nan Kusugu?” 
Aljani Kusugu yace “Ba haka nake nufiba boka, ina son dai a Kara ba ni lokaci zan yi ta bibiyarta har zuwa lokacin da zata fara nakuda da lokacin da ta ke cikin jinin al’,ada’ nasan a wannan lokacin ba ta da tsarki sannan ibadunta za 
su ragu, sanda take tsaka da nakudar sai na sauya abin da ke cikin nata, sanda take jinin biki kuma zamu iya samun damar aiwatar da duk Kudirinmu a kanta”. 
Boka ya yi ajiyar zuciya, yace “Lallai wannan magana taka magana ce  abar bi, tashi kA tafi ganin Shema ka aikata sauran aikinka kafin faduwar rana ka dawo min nan”. 
Nan da nan ya bace, gaba daya nishin da sukeji sai ya daukw dif, sai a lokacin suka saki ransu, amma da duk a rude .suke
Boka ya kalli Hajiya kumatu ya fashe da dariya. 
“Kin ji abin da aljani yace kamar yadda na sanar da ku yarinyar tana da kariyar da duk wanda muka tura ba ya iya zuwa kusa da ita ma sam balle ya yi tasiri a gare ta, sai dai mu jirayi lokacin da aljani Kusugu ya ambata mana, kada ku damu za a dace fa”._Hajiya Kumatu ce tayi Karfin halin yin  magana. ,To boka maganar komen nata fa, har yanzu fa mijin nata baice komai bai ga shi ta kusa 
kammala idda. domin ta kwashi wata har da doriya a gida”. 
Boka ya‘cc, “Shi aikinsa tsaurinsa kadan ne akwai lokutan da mukw nasara a kansa, musamman sanda yake tare da abokansa suna yin hira, don haka kada ku damu ba da kanku kuka ce kullum sai yaje gidan Fatilan ya kwanta a gadonta ba? To a hankali ma sonta da kaunarta zai dawo masa ransa sabo dal! Har yafi na farko ma, ku dai kara hakuri har zuwa wa’,adin da na dibar muku, kuci gaba da amfani da magungunan da na baku”. 
“Shi kenan boka, mun gode ga wannan”. 
Ta damKo damin kudi ta zube masa a gabansa, ya amsa ya watsa a bayan bukka Allah Ka shirya mu, Ka raba mu da irin wannan MATACCIYAR RAYUWA, amin). 
*** **
Tunda satin nan ya kama Falmata ba ta jin dadin jikinta, ciwon mara yafi matsa mata, amma da yake tana da tsananin hakuri haka take dannewa tana cijewa taKi nunawa kowa halin da take ciki, ga shi ba ta son zuwa asibiti, domin tunda suka ambata yi mata operate (operation take jin tsoro. domin ta kan ji yadda ake bada labari, don haka take addu’a Allah Ya sauke ta lafiya. ya sanya ta haihu da gidanta  lafiya.  Yau da daddare tana tsaka da bacci taji ciwo ya tsikareta, daman tunda zata kwanta take jiyo ciwo sama-sama don haka ta sha magunguna na ruwa ta kwanta. 
Haba ciwon fa karuwa yake yi, kamar. ana caccaka mata allura jikinta, ta mike ta fara sintiri tana zagaye dakin tana yarfe hannaye da ambaton sunan Allah. 
Malam dai yana gado yana ta baccinsa bashi da masaniyar abin dake faruwa. Tun tana iya zagaye dakin da kafarta, har karfinta ya tasar wa ‘Karewa, ta durkusa ta riqe gado tana nishi. 
Sai dai me? Wasu irin halittu ta ga sun fara zagayeta‘ masu kama da_ kadoji suna kawo mata barazana da karfi, kuma karkashinta suke neman caka, wato inda dan zai fito._ 
Cikin karaji ta fara kiran sunan Mukhtar, abin da ba ta taba yi ba a rayuwarta. Ya farka a tirgice cike da mamakin kiran, sai dai da ya hango Falmata durkushe gaban gado ya dira daga gadon da hanzari yana tambayarta abin da ya faru. . .. 
Cikin azabar ciwo ‘tace, “Ka kunna mini rediyo suratul Bakara, sannan ka zauna kusa dani ka yi ta tofa mini ayatul kursiyyu don Allah…” Sai ta fara yin wata irin kara cike da tsoro ganin 
kadojin sun nufota a fusace, ga‘ shi ba ta da ikon yin karatun saboda azabar ciwo. 
Da sauri Malam ya kunna radiyon dakin anyi sa,’a suratul bakara dince a kai, don haka amon’ karatun ya fara fitowa cikin muryar Sudeis. 
Shi kuma’ ya dawo kusa da ita ya riKe hannunta ya fara karanto ayatul kursiyyu da sauran addu’o’i yana tofa mata kamar yadda tace
Cikin ikon Allah, sai ta ga wadannan kadojin sun fara wata irin burgima suna ja da baya suna wani ihu. Can kuma sai ta ga gaba dayansu sun bace, sai dai gunjinsu kawai da ta ke jiyowa da kukansu daga can bayan gidansu. 
Duk da ciwon ya qaru a lokacin sai ta ji zuciyarta ta fara samun nutsuwa, ta fara karanta . sunayen Allah, sai da ta kai su har karshe ‘tun daga Arrahman har zuwa Karshe sannan ta . fara fadin summa sabila yassara. ‘ 
Can ta rirrike hannun malam tana wani nishi kamar za a zare ranta, shi kam ji ya yi kamar qartu uku ne suka matsc shi, tsananin tausayin Falmatan ya shige shi, jikinsa sai rawa yake yi, kawai sai ya jiyo karar abu facal! A kasa dai-dai lokacin da falmatan ta kara kankame; shi katamau? 
Kafin kace kwabo ihun jariri ya cika dakin, 
sai ya ji rikon yasassauta matuka, ya koma irin na Falmata ba kartu uku da yake hasashe ba. 
Ya mike da sauri yana fadin, “Sannu Falmata, kin haihu, matsa gefe kada ki danne danki”. 
Da kyar tace, “Ba zan iya ba, kama ni”. 
Ya kamata da sauri ya janye ta gefe ya zaunar da ita cikin ikon Allah har da mahaifar (mabiyar) suka fado. Katon yaro, sai kuka yake tsalawa, yana cilla kafafu da hannu. Malam ya matsa kusa da shi cikin rawar jiki yana fadin; “Masha Allah, alhamdu lillah, me zan yi masa ne Falmata.” 
Ta yi murmushi, tace, “Ka yanke masa cibi ‘ mana”. 
Ya waro ido waje cike da tsoro yace “Ba zan iya ba, ya ya ake yi?” 
Ta cc, “Zaka iya bari na gaya maka yadda na ga Hajja tana yi idan ta haihu, bude cikin waccan lokar akwai reza da zare, ka nannade zaren kamar sau hudu ka yanke, ka daure sama da kasa, sai ka daure can kasan cibiyar, amma kada ya kure ka auna da karamin yatsanka, sai ka raba awon da 
kayi gida biyu ka daure tsakiyar kamar sau UkU, sai ka yanke 
Ya matsa yana kallon yaron yayi yadda tace din sai dai bayan ya saure tsakiyar awon da yayi ya dubeta ta yace “Dai-dai ina zan yanke kuma?’
Tace, “Dai-dai awon da ka yi tsawon Karamin yatsan naka zaka yanke
Ai kuwa ya Kara matsawa ya yanke ya tsaya yana kallon yaron. Ta yi murmushi ta ce, “Ai shi kenan, sai ka ‘dauke shi ka dora shi akan gado, bayan ka nannade shi cikin zanin da tawul”. 
Da sauri ya bude sif dinta ya dauko zani da tawul ya nannade yaron sai fuskarsa kawai ya bari ya dora shi akan gadon, ya juya ya kalle ta ya ce, “To sai me kuma? Kin san na zama unguzoma”. 
Ta yi murmushi tace “Kaje ka taso Jidda sai ta gyara gurin, kai kuma sai ka dora mana ruwan wanka a babbar tukunya kan kuka gas (cooker gas)”. 
Da sauri ya fice kiran Jidda ya kwankwasa mata kofa yana fadin, “falmata ce ta haihu”. ‘ 
Ta bude kuwa da gudu ta yi dakin, yaron ta fara kalla yana ta cilla jafa sama, ya daina kuka. Ta kalli Falmata tana dariya, tace, “Anti Falmata kin haifo mana Yaya Malam wallahi”. 
Falmata ta yi dariya, tace “Kinga ki gyara 
gurin kada jinin ya bushe kisha wahala”. 
Da dariya Jidda ta kama gyara gurin ta ficc da mabiyar a cikin leda da safe a binne. Kafin asuba sun yi wanka sun gyara tsaf, dayake J idda ta iya wankan jajirai ta wanke yaron tsaf kamar wata uwar mata, dakin aka kunna turarcn wuta. 
Tun gari bai gama haske ba Hajiya Mariya da abokiyar zamanta suka taho ganin yaro, domin tunda ta haihu ya sanar dasu murna kam ta ‘cika wa kowa ciki, suka dinga kallon dan ana yiwa Allah godiya da tasbihi, yau dan Mukhtar ne a duniya, waye ya zaci haka? 
Sai dai Hajiya tace dole sai anje asibiti an duba lafiyar mai jegon da d‘an. Hakan kuwa aka yi, an yi sa,’a ko da aka je likita ya tabbatar lafiyar Falmata kalau. k0 Kari ba ta samu ba, suka dinga mamaki da jinjina mata, ganin ta haifo wannan qaton dan, amma ba taji ciwon komai ba, haka shi ma dan lafiyarsa kalau. 
Kafin kace kwabo ‘yan uwa da abokan arziki sun cika gidan, kowa sai kallon dan yake da mamaki yau ga dan malam a ‘duniya. Shi kam angon kauri sai shige da fice yakse baki ya qi rufuwa, yana tambayar abin da za, a kawo, sai da’ Hajiya ta kore shi tace komai akwai ya ba su guri 
kawai sannan ya wuche. 
Malam Abbagana ne yayo waya yana tambayar halin da ake ciki, Hajiya tana dariya tace “Wato har ya sanar da kai ke nan ko? ” . 
Malam ya yi dariya, yace Eh ya sanar da ni an sami takwaransa Muhammad, zuwa gobe zamu zo ni da yayata Furera, wacce zata zauna a gurinta”. ‘ 
Hajiya taCc, “Haba malam wallahi ba za a yi haka ba; ai da an yi suna zan dauketa mu koma can babban gida har sai ta yi arba’,n sannan na dawo da ita, kada ka damu ba sai ka kawo wata mai zama ba sam”.rab
imam Abba‘ ya yi wasai, domin dama yana tunanin yadda zaije ya zare Furera daga cikin iyalanta domin tana da yawan “ya ya, ga kuma jikoki da taje rik‘o, don haka kawai sai ya dinga godiya da sanya albarka. 
Su Hajiya Yakolo kam tayi tsammanin ita Malam din zai .tura zaman dabaro, don haka ta kammala tanadar dukkan matakan da zasu dauka har zuwa ganin bayan auren ta yadda ba za a gane da hannunsu ba, ta kuma ci burin yadda za ta yi sakaci Falmata ta lalace yadda ba Mukhtar ba, k0 wani namijin ma ba zai iya zama da ita ba, sai dai ta Allah tasu ba. 
Abba ya sanar da su yadda suk‘a yi da Hajiya Mariya» sai a lokacin ma suka gane k0 da za,a je din ma ba sune za su je ba, don haka sun cika da takaicin karyewar kudirinsu matuka. 
Sanda su Hajiya Kumatu suka sami labarin haihuwar Falmata lafiya, kuma lafiyayyen da hankalinsu ya tashi ainun, ai basu Bata lokaci ba suka isa gurin boka da kokensu, sai dai a wannan_ karon kam sun yi fata-fata da boka, don suna ganin cutarsu kawai yakeyi, karya ne, duk da yai musu bayanin iyakacin kokarin da aljanin da ya tura Kusugu ya yi akan ya sace dan abin ya faskara. Baram-baram dai suka rabu ba kare bin damo. 
Daga nan ba su hakura ba suka shiga bin. ‘ wasu malaman ko naCe bokayen gadan-gadan, sai dai abin da suka kula babu wata nasara zuwan da Mukhtar keyi a gidan F atilan ma a kowanne dare yanzu ya daina gaba daya, ya tattara hankalinsa ga dansa da matarsa kacokan abin dake faranta ran mahaifiyarsa ta tabbatar da addu’o’in da take akan dan nata Allah Ya amsa. 
Saura kwana biyu a yi suna ‘yan Maiduguri suka iso, Hajiya Yakolo da Hajja Kaltum, sai H’ajja Basma suna cikin ‘yan tawagar duka ‘yan uwanta Sun taho saidai duk sun zo ganin kwaf ne baya 
Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE