MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 24

MATACCIYAR RAYUWA 
CHAPTER 24
masa, da ace ya hadu da fitsararriya sai sun hau sama amma babu komai zata san abin yi. 
Ta jima tana rarrashin Falmata kafin ta fice. 
Washegari ma irin jiya ya shigo, sai dai yau ya ce da Falmata zai koma, don yana gudun kada yaqi zuwa ne ma mahaifiyarsa ta yi fada babu laifi dai ya dan saki ransa yau ba kamar jiya ba, amma ga duk wanda ya sanshi yasan ba a cikin walwala yake ba. 
A falo ya tadda hajiya tana kallo, ya zauna ya gaisheta fuskarsa babu yabo ba fallasa, ta amsa ita ma ranta a hade ganin haka ne ya sanya ya mike yana fadin. 
. “Bari na shiga mu gaisa da su, don ina da 
aiki da dama a gida”. 
Har ya mike ta dakatar da shi, da kakkausar murya taje magana. “Dakata malam, ina son yin magaba da kai”. 
Ya koma ya zauna jikinsa a sanyaye, don ya tabbatar ta gano komai. 
Ta kuma zabga masa harara, tace “Wanne laifi Falmata ta yi maka?” 
Gaba daya sai ya dururuce, ya nemi dauriya ya rasa, yana-kamw irin na mara gaskiya
“Wallahi ba tayi mini komai ba Hajiya, ni babu wani abu da ta yi mini sam”. 
Ta kuma tsare shi da ido irin na tuhuma, wanda kan sanya ya ji kamar yana gaban alkali ne, tace “To amma kake mata wannan kuncin da shan kunu? Ina ce sai mutum ya yi laifi ya dace a yi masa ‘irin wannan horon, wallahi Malam ka ji tsoron Allah, kada don kaga ka sami salihar mace ya sanya ka dinga cutar da ita, Allah zai tambaye ka yadda ka zauna da ita. 
Ya kama sosa keya ba shi da mafita, sai dai haushin Falmata ya karu a ransa, domin ba ya raba daya biyu ita ce ta sanar da mahaifiyar tasa komai. To me ta ke nufi? Ta kawo Kararsa ne don ta haddasa masa jidali da tashin hankali k0 me? Amma ne sai ya Bige da bai wa mahaifiyar tasa hakuri tamkar gaske, har da karyar shi ma haka ya kejin zuciyarsa babu dadi kwana biyu. 
Wannan furucin nasa na karshe ne ya ankarar da ita wasu abubuwa da dama, wanda har ya sanya ta dan sassauto ta ringa fadan da fadin. _ 
“Shi ke nan, sai ka dage da addu’a da neman tsari, babbar matsalarka bata wuce sakaci ba”. 
Shi _-ai da ya samu ya tsira daga fadan nata 
ya mike yana fadin, “baru na shiga na gansu”. ‘ 
Mahaiflyar tasa ta bishi da kallo da tausayi a ranta ~tana masa’addu’ar Allah Ya raba shi da kaidin su Hajiya Kumatu, domin ta tabbatar ba za su barshi haka ba sam. 
Muhammad din yana gado yana bacci lafiyar Allah, domin jikin nasa ya yi sauki, ita kuma tana ta linke kayansa da  jidda ta wanko masa cfazun. 
Ya shigo da sallama yana wani cika yana batsewa, tamkar bajimin Sa ta waiga ta kalle shi gabanta yana faduwa, a duk sanda ta ganshi sai ta ji gabanta ya yanke ya fadi. 
Ta amsa sallamar da sauri ta dora da fadin “Sannu da zuwa, ina wuni”. 
Ya yi mata wani kallon banza, yace, “Ashe ke dama munafuka ce ban sani ba?” 
Ta dago kai da sauri hatta hanjin cikinta sai da suka kada, wannan wacce irin kalma ce mafi  muni da mijinta ya jefe ta da ita? Ta shiga ukunta! 
Bai bari tace wani abu ba, cikin Bacin rai ya ci gaba da bambaminsa. 
‘ “Ban da tsabar munafurci ni ban miki komai ba ki hada ni da mahaifiyata, to me kike nufi?so  kike ta tsine min ko so kike tayi gaba dani
Ta fara‘ rantse-rantse cikin kokarin kare kai. “Wallahi tallahi ban sanar da ita komai ba. na ga abin da ta sani daga gare ka, kuma don Allah ka yi hakuri ka dubi halin da nake ciki, ina bukatar tallafi da taimakonka. Ya dacc idan har na yi maka wani abu da ya sosa zuciyarka ka sanar dani don Allah”. 
Idonta ya fara zubda hawaye, amma maimakon yaji tausayinta, sai ma haushinta ya kuma cika shi. A ganinsa ba komai bane hakan illa wani salon munafuncin. Ya dinga fadansa babu k0 sassauci, abin da ya dinga kona mata zuciya sai dai ta ja bakinta ta yi gum, domin ta kula a duk sanda ta yi yunkurin kare kanta sai ya kuma hasala, don haka ba ta da zabi da ya wuce ta yi shiru din, sai da ya yi mai isarsa sannan ya yi shiru. 
Mamaki mai tsanani ya cikata, k0 wani ne ya bata labarin Mukhtarinta haka’yake da fada zata musa, amma yau ita ga shi ya yi mata, mutumin da take gani mai sanyin hali da hakuri ke balbala wannan fadan yau? 
Sai da ya ga babu Sarki sai Allah sannan ya kade rigarsa ya fice babu k0 sai da safe. Ta bi shi da kallo tana son ta yi kuka k0 ta ji sanyi a ranta‘ amma zuciyarta na gargadinta, don kada uwar mijinta ta kuma yi masa fadan dake
janyo mata cin kashi, don hak sai kawai ta ajiye linkin kayan ta dauko qur’ani da yake tana da tsarki, don jinin bikin ya dayke mata, ta kama karatu fatanta sanyi da salama su sauka a zuciyarta, ta yi dacen hakan kuwa, domin shi alkur’ani maganin komai ne, waraka ce har sai da ta ji ranta ya yi sanyi, sannan ta kwanta tana tunayo abin da ya wakana, abin kamar a mafarki. 
Shi kam daga nan gurin’ Fatila ya koma, domin shigar da ta yi yau ta yi ne don ta tsokane shi, ta kuma samu yadda ta keso don, girki ma sai da aka yi masa kala uku, wanda aka zuzzuba asiri a ciki, don haka ya saki jiki ya cika cikinsa, gaba daya duk Fatila ta rikita shi, sai wani karairaya take yi masa. Da kyar ya iya kammala cin abincin ya kamota, ta zille tana masa dariya tana fadin. Ka manta a gidanmu kake?” 
Haka dole ya hakura yana kallonta 
*** *** 
Kwanakin da suka biyo baya babu abin da ya sauya sai dai Falmata tana Kokarin binshi a duk yadda yazo, ta kuma bar wa cikinta komai, inda Allah Yasa tana da masu debe mata kewa a gidan, da tabbas dole ciwon zuciya ya kamata. 
Sai dai tsananin son Mukhtar ke nukurkusarta kullum, Allah Ya jarabeta da tsananin sonsa, wanda har ta fara zargin kanta da shi me ya sanya ya ke mata komai ta damu
Gare shi kam ba shi da damuwar komai, domin kullum yana tare da Fatila, yana son ya ce ta tare a gidanta, yana shakkar abin da zai biyo baya, yana kuma tsoron tunkarar mahaifiyarsa da batun, don haka suka ci gaba da tafiya a haka, su da kansu ba su damu da ta koma dinba,~ sai sun kammala shirye-shirye tsaf. . 
Kwanaki arba’in da biyar hajiya ta kammala gyara Falmata tsaf, ita da kanta ta gyara kanta da tsarabar da ‘yan uwan mahaifibta suka kawo mata musamman kayan kamshi da ya tsumata, a ranta tana son ta koma k0 domin ta samu mijinta ta ji abin dake damunsa, sai dai tana fargabar irin zaman da za a yi a gidan, kullum dai cikin gayawa Allah halin da ta kc ciki take
Sanda aka sanar da shi batun komawarta ya yi murna matuka, don ya gaji da sintiri a gidan nasu, yana kuma kallonta ta cika tayi bulbul gwanin sha’awa, sai yake jin wani abu na darsuwa a ransa. daya nuna ce ta faranta ran 
‘mahaifiyar tasa aka shiryawa Falmata kayanta sai 
‘ gidanta, a lokacin Jidda ta tafi gidan Yayar Malam din data haihu don ta taya ta aikace-ai‘kacen da yake hutu suke yi. Don haka bayan ‘yan rakiyar ta sun watse ita kadai tai zaune a d’aki sai ka ce irin sabuwar amaryar nan, daga karshe dai ta tashi ta fara gyaran gidan nata da kayan kamshi na tarar maigidan nata. 
Sai dai shiru-shiru har wajen karfe sha biyu bai iso gidan ba, yana can tare da Fatila hankalinta ya tashi mamaki,ya cikata amma ta dake a ranta tai ta tilawa. ~ 
Su Fatila sun yi shiri mai girma, domin suna da labarin yau ne ranar komen Falmata din, sun kuma yarda ba za su yi nasara akan Falmata ba, domin k0 sun yi tasiri a kanta bai jimawa take karya musu’, hakan ya sanya suka fi maida hankalinsu akan Mukhtar din. 
Bai samu damarshigowa gidan ba sai wajen sha biyu da wani abu na dare, duk dokin da yake kuwa a kanta sam babu shi a yanzu  ransa, sai ma wata gajiya da kasala da aka dora masa, don haka kai tsaye dakinsa ya wuce ya fada gado. 
Ta jima tana jiran shigowarsa domin ta ji 
alamar tsayawar motarshi amma har aka kusa awa 
daya ba ta ji alamarsa ba, don haka ta fitar da‘ rai zai shigo din, amma abin ‘yayi mata ciwo arai ainun,sai dai zuwa yanzu ta fara sabawa da halin da mijin nata ya tsiro da shi, tayi alkawarin yin hakuri harta ga Karshen abin. 
Da safe ma bai neme su ba, don haka ita ta neme shi, bayan ta kammala shirya masa abin kari, sai dai abin da ya dan faranta mata rai bai wuce cin abincinta da ya yi ba, duk da ba wani sakar mata fuska ya yi ba, da kyar ma ya amsa gaisuwarta, abin da dai ya daure mata kai k0 kallon yaron bai yi ba balle yaji yadda ya kwana, abin kam da mamaki, domin tasan yana matukar kaunar dan nasa. ‘ 
Abin da ba ta sani ba tun bayan da aka ‘ tabbatar ta haihu lafiya dan kuma yana raye, suka ce sai sun raba shi da dan, idan don shi ne ma za a yi musu akin da k0 shege ne sai haka irin kiyayyar da zai numa masa, don ‘haka sanda suka koma gurin boka karo na biyu har da wannan aikin 
suka yi. Ya yi kuma tasiri akan yaron da uban, don ba ya jin kaunar dan k0 miskala zarratin a cikin zuciyarsa. 
“haka suka dinga zama kusan sati biyu ba ya 
shiga huruminta, sai dai zai ci abinci ya fuce, dawowar Jidda ne ma ya sanya yaje dan sakar mata fuska a gabansu, don bai son su gano wani abu su sanar da mahaifiyarshi, ita kuwa tana kokarin shanye duk wani abu da yake mata. 
Kamar da ta cika kwanaki goma sha biyar da dawowa tana falo a zaune tana bai wa yaronta , mama, tana yi masa wasa ya shigo gidan, ya dawo daga aiki ba ta motsa daga inda ta ke ba ta yi masa sannu da zuwa. Kamar an ce ya waiga ya kalleta, caraf idonsa sai ya sauka a kanta 
Yadda take baiwa yaron mama da yanayin yadda jikinta ya murje ya fisge shi, ya tsura mata ido kyar kamar ranar ya fara ganinta. 
Ta kula da hakan, amma sai ta nuna kamar ba ta ganshi ba, ta kauda kanta ranta ya damyi sanyi, domin ba ta jin dadin yadda mijin nata ya maidata tamkar wani gardi ba ya nuna wata sha’awar kallonta sam. 
Kome ya tun numa, sai ya wayance cike da kunya sanda suka hada ido, ya wuce yana fadin
“Ki kawo mini abinci a dakina a can zan ci”. 
Wani irin dadi ya sake kamata, yaushe rabon da ya yi mata maganar da ta kai tsawon haka? Sai dai ya a fito falo ya kama cin abinsa kawai yana kallo, baya ga ko a’a idan ta yi  magana ba ya cewa komai. 
Ta kira Jidda ta bata Muhammd’ ta koma dakinta ta kara sanya tumre mai dadin kamshi ta nufi dakin nas‘a da abinci hannunta, tana ta addu’o’i. 
Yana zaune da alama har ya watsa ruwa don daga shi sai doguwar riga da gajeran wando, yana zaune a gefen gado ta shigo da sallama da sanyin muryarta. Ya daga kai ya kalle ta’ sai ya ji wani abu ya damm ransa, wanda ya jima bai ji shi a rai ba, ‘ 
Ta durkusa ta ajiye abincin a gabansa ta yunkura da nufin tashi ya tsaidata da fadin. 
“Ina kuma zaki, sai wani sauru’ kike yi, ko kina da aikin yi ne?”. 
Abin tamkar a mafarki ta ji abin, ta mike da sauri ta zauna a kusa dashi tana fadin, “A’a, ba haka bane, ba ni da abin da zan yi”. ~ 
Yana cin abincin yana kallonta. Kamshin dake fita daga jikinta yana dan shigarsa kadan‘kadan. ita kam kanta yana kasa tana ta wasa da yatsun hannunta. Tana ta addu’a Allah Ya sanya wannan shine karshen matsalarsu. 
Can bayan  tsawon lokaci ya ce “Dazun
Hajiya ke min maganar tafiyarki‘ Maiduguri, wai yawon arba’ in meye ra ’ayinki?” 
Tai tsam cikc da farin ciki,tabbas ta jima tana son tace zata je ganin gida, ammma ba ta san ta inda zata fara ba, don haka ta ji tamkar’an =yi mata albishir da gidan aljanna Da sauri tace
“Duk abin da kace ai ya yi, ni ba ni da ta cewa tunda kai ne mai bada izinin tafiyar”..
_ Ya ji dadin abin da tace din kuwa, ‘don haka 
‘ya’ yi munnushi, ya ‘ce’, “Shi ke nan zuwa karshen wata idan an yi albashi kya tafi lOkacin kudi sun samu an yi musu tsaraba k0?” 
Ta daga kai alamar eh, ranta kam har lokacin’cike da dadi yake, yaushe rabon da ya yi irin wannan doguwar hirar’ da ita’?’Tun tana kwanaki ashin’n da wani abu da haihuwa, rayuwa ke nan. ~ 
, Ya dinga janta da hira tana biye masa. Can yace, “Wai ke me ya sanya ba kya son zuwa dakina ki kwana ne?”. 
° Lallai anzi gurin, ta tabbatar kallon da yake mata. dazun daman da wata a kasa, ita da dama tana buqatar mijinta, cikin dariya tace. 
“To ai na ga kamar dama kai ke zuwa 
Dakina… kuma.. kuma… ’ ‘sai tayi shiru Kuma me? Ai daman kafin
Please kuyi haquri da wannan gobe zan muku fiye da yaddah nake kullum afwan

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE