MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 26

MATACCIYAR RAYUWA

CHAPTER 26

duk yadda zata iya amma abin kamar ma kara gaba yake yi kullum, daga karshe dai ta yanke shawarar sanar da Allah halin da take ciki, domin ta tabbatar shine kadai zai fiddata daga halin da ta shiga.
Kwanaki biyu bai leko ba, bai kuma kira wayarta ba. ita ma ba ta k0 gwada kiransa ba ta kyale shi ta ga iyakacin gudun ruwansa, dan kudin da ta samo daga garinsu shi ta sanya a gaba take cefane da yin duk wani abu da ba za, a rasa ba.
Fatilu kam tafi kowa murna dajin dadl da abin dake faruwa, domin ta san daga haka auran zai mutu itama ta huta gaba daya
Randa ta cika kwana hudu da yamma bayan sallar isha’i tana zaune a falo tana kallo taji kamar karar tsayuwar mota, ta mike da sauri jikinta yana rawa ta leka Ai kuwa shine sai ta tsinci kanta da wani tsananin farin ciki, ta rasa wanne irin so ne take yiwa malam a rayuwana, duk abin da ya aikata mata data ganshi sai taji ya wuce, ta san ita daman mutum ce mai saurin afuwa da yafiya ga duk wanda ya cusguna mata. amma yadda take saurin yafiya ma  k0 bai tambayeta ba daban ne dana saura
Tana tsaye tama rasa me zatayi Takaicinta daya da batasha kwalliya baTa jiyo bugun kofa
Da sauri ta nufi kofar ta bude.
Yana tsaye kikam tamkar mutum mutumi, fuskarsa a dame kamar bai taba dariya ba.
Duk da gabanta ya yanke ya fadi, amma bai
hana ta kwamar da murya tace masa, “Sannu da zuwa ba. ‘
Ya zura mata ido yana son tuno wasu abubuwa, amma ya manta, daga karshe ya kutsa cikin gidan kai tsaye  sai dai yana shiga ya toshe hancinsa.
Mamaki ya cikata, me ya’ sanya shi toshe hancinsa haka? Ta dan bishi hardakinsa da ya nufa, daman ta gyara dakin tas, sai dai me? Yana shiga dakin amai ya kufce masa.
Ya dinga kelaya amai kamar hanjin cikinsa zai fito, ta rude matuka ta tafi ta dauko abin goggogewa da ruwa tana ta yi masa sannu. a maimakon aman ya’yi sauki sai ma abin ya karu. Can kamar wanda aka tsirawa allura sai ya zabura yayi waje da gudu bai tsaya ako inaba, sai da ya isa kofar gidan’ Mamaki mai‘ tsanani ya kamata’, tabi shi da sauri ta” tadda shi “zaune kan baranda yana maida numfashi. Ta isa ta mika masa ruwan dake hannunta tana fadin Da ka dauraye bakinka ‘.
Bai yi musu ba ya amsa ya kama wanje bakinsa, sai da ya gama sannan ya ‘miKa mata robar.
Ta kura masa ido tana fadin, “bannu”.
Kamar ta tsikare shi ya daga kai a fusace yace“Wacce irin kazama ce keda har zaki bar gidanki yana wari haka tamkar an ajiye mushe a ciki’? Tabbas kin dauki alhakina”
Abin sai ta ji shi kamar ba‘a, tace “Amma dai da wasa kake ko Malam?”
Ya galla mata harara yana fadin. “Kina nufin zan yi wasa har da lafiyata ne? To ldan har ba kya jin warin dake fita daga cikin gidanki ya tabbata kina da matsala a hancinKi. Kiyi
gaggawar ganin likita”
‘ Tayi sororo ta ‘rasa abin cewa domin ba jiddah ba hatta hashim daya shigo cin abincin dare saida ya dinga fadin kai anty falmata kin iya sanya turare mai kamshi idan har zanyi aure ke zan kawowa matata ki fada mata yaddah ake hada kamshi
Tayi daria lokacin cike dajin dadi saidai wanda tayi dominsa yace wai warin mushe ma gidan yakeyi gaba daya yanzu meya dace tayi
Ta kwantar sa kai hawaye na gangarowa saga idanunta
tace“Don Allah ka yi hakuri insha Allah hakan ba za ta kuma faruwa ba”.
Ya mike yana fadin “k0 da na hakura ba zan iya kwana a cikin gidanki ba,-gwara na kwana . a motata”. Ya mike ya nufl motarsa.
Ta bi shi da kallo cike da tashin hankali, wannan wacce irin masifa ce? K0 a littafin labari ba ta taba jin irin wannan matsalar ba, sai dai tana ganin bai dace ta bar shi ya kwana a motar ba, don haka’ta bi shi da hanzari tana fadin
. “Don Allah ka yi hakuri ka komo gidan ka kwana…”
Ya juya a fusacc tamkar ta watsa masa ruwan zaf’i yace “Wato na koma ba amai ba idan kashe ni warin zai yi baki da asara ko? To baki isaba. Ya karasa cikin motar yana huci.
Ta tsaya cak! Kukan yaqi yazo sai ajiyar zuciya. Wato shi kansa kukan rahama ce kenan, tana ji tana gani ya shige mota kujerar baya ya yi kwanciyarsa, da taga tsayuwar ba ta da amfani ta koma gidan cike da damuwa.
Yadda b‘ai yi baccin dadin rai. ba, haka ita ma ta kwana tana kuka da damuwa.
Washe gari’ daga masallaci bai dawo gidan ba ya wuce gidan Fatila abinsa, sanda Fatila ta
ganshi ta yi tsalle ta rungume shi tana ihu, ita kuwa wanne irin dadi ne yafi wannan a gurinta?
F almata baiwar Allah sam bata san ya tafi ba, ta shirya girki da sauri ta,.zuzzuba ta fice da zummar kai masa ya karya, ta lallaba shi k0 Bangaren Hashim ya tafi, sai dai tana f1ta tilin gurin ta gani babu kowa, tsoro da takaici suka cikata, tabbas ta shiga uku, yanzu ina mijinta zai je yaci abinci? Haka ta koma gidén gwiwa a saBule.
Sunakari ne Hashim ke fadin, “Anti Falmata  jiya naji kamar karar motar Yaya Malam?”
Ta yi dan murmushi, tace “Shi ne, da asuba ya fice wai yana da wani aiki” .
Ya waro ido waje yace“Kai shi Yaya Malam ya ‘cika matsawa kansa da yawa, yau fa
. Sunday ranar hutuce.
Ta yi wuki-wuki saboda yadda yayi saurin
gano ta, amma ta dake tayi murmushi kawai.
Suna kammala cin abincin tace, “Yau lallai kwalema za ayi a gidan nan kowa ya shirya”.
Tunda suka fara da safe sai da suka kai la’asar, komai na gidan sai da suka fiddo da shi, na wankewa suka wanke, na gogewa. suka goge sannan ta bada turare kala-kala a gidan. ai kuwa
gidan ya d’auki kamshi tamkar kamfanin saida turaruka. Su Jidda kam suka dinga santi da surutun yadda gidan ya yi kyau. A zuciyarta addu’a take Allah ya sanya yadda suka yaba shi ma idan yazo‘ ya yaba din.
Sai dai me? Abin da ya faru a daren jiya yau ma shi ya faru, ya iso gidan ya fara kwankwasawa tana zaune daman jiran tsammani take don haka da sauri ta mike ta ci uwar kwalliya daman ta bude masa’ kafar tana yi masa sannu da zuwa ya shigo kamar
gaske, sai dai yana shakar iskar falon ya fice waje yana nishi, ta biyo shi tana kuka tana fadin. “Tabbas Malam kaje a duba ka kana da matsaIa, amma wallahi hatta bakin da nayi d‘azun sun tabbatar gidan nan yana Kamshi mafi  dadi”. Cikin t‘sawa ya ce, “Ai kin san zan yi miki karya ne k0 Fatima? Toki kula kamarki ba ki isa nai miki karya ba”. Ya sanya hannu cikin aljihunsa ya zaro kudi ya mika mata.
“Amshi nan kiyi cefanen duk abin da babu, amma indai baki gyara halinkl na kazantar nan ba, wallabi ba zan kuma shiga gidanki ba har abada”.
Ya nufi mutarsa tana kallo ya shigeya tafl. Har saida ya bacewa ganinta  sannan ta koma cikin
gida tana kuka, ta hada kai da gwiwa a tsakiyar gadon tana kuka sosai, wannan wacce irin masifa ce ta shiga? Tabbas ta had’u da jaraba mai wahalar hayewa, amma duk da haka zata.ci gaba da kaiwa Allah kukanta, domin ta san Shidin ba Ya bacci.
Daren ranar kam idan tayi bacci, to sai dai Garawo da ya dauketa, amma tabbas ta kwana zuciyarta tana zogi da radadi, wanda ta ke jin har kanta yana juyawa, ga Muhammad kuma ya dinga tsanyara mata kuka cikin dare, duk abin da tayi masa yaKi yin shiru Ga shi yaki kama mamansa, sam ta rasa abin dake damunsa, kawai sai ta sanya shi a gaba ita ma ta kama kukan, domin dai ba ta san me zata yi masa ba.
Shi da akayi kiran sallah sannan bacci ya dauke shi, ta samu ta yi sallah ta kwanta ita ma.

***
Tabbas F atila tana cikin matan da suka dauki rayuwa da zafi, har suke gudanar da rayuwarsu a cikin MATACCIYAR hanya ba tare da sun ankara ba, domin ita yanzu gurinta ko albishir din aljanna aka yi mata ba zata yi murna irin haka ba, domin Malam gaba daya ya tattara ya dawo gidanta da kwana. abin da take fata‘ domin an
tabbatar mata fitar Falmata sai a hankali don haka duk sai tabi a sannu, hakan ya sanya take ganin samun wannan nasarar kamar tsani mlne na kaiwa ga babbar .nasara, sai dai tana matukar Kin Muhammad a cikin ranta, bata taba ‘ganin yaron ba, amma tana jin tamkar ta aika a sato mata shi ta kashe shi ta huta da bakin cikinsa. Sai dai mahaiflyarta ta lallashe tace, komai dadewa yaron zai dawo hannunta sanda suka kori Falmata, a sannan sai su yi masa duk abin da sukaga dama, babu wanda zaice don me
Shi kam malam bai taBa ganin aibu k0 laifin abin da yake aikatawa ba, domin a ganinsa yana da cikakkiyar hujjar da ta sanya ya daina kwana a gidan nata. wacce yake ganin ko a addini yana da hujja.
Wannan ya sanya yake zaune daram kan ra’ayinsa, duk bayan kwanaki uku k0 hudu yakan je kofar gidan da daddare ya yi mata hon k0 ya kira wayarta idan ta fito ya mika mata kudin cefane har da gargadi mai kaushi na idan ba ta gyara halinta na kazanta ,ba to shi kam ba zai iya kara shiga gidanta ba har abada
‘ Jidda ta lura da halin da Antin nata take ciki, domin ita din ba yarinya bace duk da
Falmata na kokarin Boye komai amma sai da ta gano, sau da dama har hawaye ta keyi idan ya iso ya yi kiran Falmata a waya, sai ta wayance da bari naje mai wanki ne ya iso. Tun Jidda na yarda har ta sha jinin jikinta, rannan dai ta bita taji maganganun da Malam ke fada mata.
A daren kam ta kwana mamaki, sai da ta zubar da hawaye don tausayin Falmata.
Abin dake daure mata kai bai wuce jin da ta yi wai Mukhtar na cewa da Falmata kazama, ba zai kara zuwa gidanta ba sai randa ta gyara gidan ya daina yin wari, tabbas wannan wani abin mamaki . ne a gare ta, domin idan lissafin masu tsafta k0 da a gasar duniya ne F almata zata iya daukar na daya, balle aje ga batun wari k0 bandakinta ba ya wari saboda yadda ake sanya turarukan bandaki kalakala balle jikinta, ti shin wai me Falmata ta yi da ya zama kazanta’?
Ta jima tana mamakin wannan lamari, sai ta fara jin tsoron maza matuka, domin idan mace kamar Falmata da ta hada komai na tsafta da gyara da kuma kyau zata iya fuskantar matsala a hannun namiji, to ina ga su kuma‘.’
ta bar abin yana ci mata rai kamar yadda yakc ciwa dalmata rai kullum idan ta yi tunanin ta sanar da Hajiya halin ‘da ake ciki. sai kuma ta yi tunanin kada maganar ta fito ace ita ce malam ya tsaneta k0 ma ya koreta gaba daya, ko kuma a dangi ace sanya musu ido ta keyi, don haka ta bar abin a ranta.
Shi kansa Hashim ya kula da rashin zaman yayan nasa a gidan, sai dai kullum dare yakan gaji shigo da motarsa a tunaninsa a gidan yakc kwana ya fice da sassafe k0 da asuba, da yake karatu yai masa zafi, kusan sati uku ma ba ya kwana a gidan, sai dakin makaranta, domin suna gab da fara yin jarabawa.
Da wani dare Falmata tana karatun qur’ani tana hawaye domin ta kasa bacci, idan ta kwanta baccin sai ta dinga mugayen mafarkai, sai dai muryarta rawa ta keyi matuqa, duk wanda ya ji sautinsa zuciyarsa zata karye matuja.
Jidda ta farka daga bacci cikin dare kamar ‘ an tasheta, sautin karatun Falmata ya doki kunnenta, ta yi tsam cike da tausayi sai ta mike ta nufi dakin Falmatan ta wundo ta leka ta hangota zaune bisa sallaya tana ta karatu. amma idonta yana zubda hawaye tamkar an saki famfo, wani irin tsananin ‘ ‘ sanyi ya kamata, da kyar ta iya komawa dakinta tayi zaune a tsakiyar gadonta, sai ta ji
kuka ya Kwace mata. Tabbas idan taci gaba da barin Falmata cikin wannan halin, Allah zai tambayeta domin ta kula Falmatan ta yi niyyar fansar da ranta ga wannan baKin cikin ba ta da niyyar sanar da kowa, don haka kwana ta yi tana sakawa da kwancewa, tunani daya hanyar da zata bi ta taimaki Falmnata ta fita daga wannan yanayi. Take
Ta yi dace week end din nan Hashim ya shiga gidan don ya dan huta bayan sun gaisa da Falmata ya dan zolayeta ya wuce sashinsa, Jidda kam sai da ta saci ganin Falmata ta fice ta nufi dakinsa.
Yana tsaka da cire riga ta fada da sallama. Ya waiga yana kallonta, ganin-yadda yake ya sanya duk kunya ta rufeta, ta koma baya da sauri domin yanzu sun fara wasan ‘yar kunya, kwarai yake nuna mata sonta yakeyi. abin da ta dauka da farko wasa ne amma daga baya ta kula da gaske yake yi, don haka ta fara jin nauyinsa da kunyarsa.
Shi kam sauri yayi ya maida rigar tasa yana dariya ya leka sai ya hangota tsaye can nesa da kofar dakin nasa. Ya yi dariya yace
“Ke budurwar kauye meye na Wani gudu kamar kin ga dodo? Zo nan ki gaya mini abin dake tafe dake dariya yake maganar.
Ta kauda kai cike da kunya kamar ba zata karasa ba, amma muhimmancin abin dake tafe da ita ya sanya ta nufi dakin nasa tana wani sunkuyar da kai. . Yana tsaye a bakin kofa ta iso shi ta shiga. Ya bita  a baya yana dariya, ta zauna a gefen kujera jikinta sanyi kalau. Ya iso ya durkusa a gabanta yana fadin.
“Yarinya na jima da gano ki, son dan yaron ‘ nan Hashim kike yau kin cika kinzo gaya mini k0?”
Kai Hashim mugun dan zolaya ne, ji tayi kamar ta nutse don kunya, amma sai ta dake tace
“Ka ga malam, ni ba wannan ta kawo ni ba, maganar Anti Falmata ce ta kawo ni”.
Ya ‘nutsu sosai tare da gyara zama yace, “Eh  ina jinki, wani abu ke damunta k0? Tabbas na kula kwana biyu duk ta rame ba ta da walwala kamar’baya”.
‘ Ta gyara zama tace. “Eh to, laifln dai duk na Yaya Malam ne kasan bai kwana a gidan kuwa?”
Ya waro ido cike da mamaki, a tsorace yana fadin, “jidda kada ki gaya mini maganar karya. Yaya Malam ne zaki ce bai kwana a gida. ina kike zaton zaiJe ya kwana kenan? Kullum fa sai na ga ‘ motarshi ya shigo da daddare sai dai kice bai zama sosai a gida dai kamar baya”.
“Hum Hashim, daman na san kowa zai yi mamakin hakan, amma wallahi Yaya Malam bai kwana a gidan nan kusan wata daya, kai tunda muka dawo daga Maidugun’ sai dai yazo ya bata ‘ kudin cefane yai komawarsa’”.
Ya kura mata ido cike da tsananin mamaki da damuWa, ya daure yace  “Jidda idan Yaya Malam bai kwana gidan nan, to a ina yake kwana kcnan? Meye dalilin da ya sanya kuma bai kwana a gidan?”
Kamar ya sosa mata inda yake mata kaikayi, tace “Oho, shi yasan inda yake kwana, amma najj yana fadin wai saboda gidan yana wari shi ya sanya ya daina kwana a cikinsa”.
Ya sake Fito da ido waje har da saurin zabura ya mike kamar wanda aka tsikarawa takobi yana fadin, “Wai me kikeson sanar dani ne Jidda? Falmata ce ke wari k0 gidan ke wan’ k0 me?”
Ta tabe fuska. “Kai ma kace wallahi jin kunne na naji yana fada har sau uku. ita kuma ta kasa sanar da kowa ta bar abin a cikinta yana shirin halaka ta. Banda cuta da zalunci Mace kamar
Falmata za a kirata da kazama? Ni fa ina zargin Yaya Malam gurin Fatila yake zuwa shi ya sanya yake yiwa Anti F almata wannan wulakancin dacin Kashin, ya kuma san ba zata iya sanar da kowa ba”.
Hashim ya kai ya kawo cike da tsananin mamaki da bakin ciki, ko da wasa aka ce masa yayansa zai yi haka zai musa, malam mutum mai tsananin tsoron Allah, ma’abocin taka tsan-tsan, tabbas in dai hasashen Jidda ya kasance zai iya kiran mace da shaidaniya kuwa, ya waiga ya kalli J idda da ta tsare shi da ido. Yace
“Ke yanzu ya kike ganin za muyi Jidda? Tsananin tausayin Falmata ya cika ni, yarinya kamarta mai karancin shekaru ba ta cancanci shiga taska da tasku irin wannan ba, tabbas duniyar nan akwai abubuwan mamaki masu girma”.
Ta kwantar da murya tace“Duk da na tabbatar da abin da na sanar da kai, amma ina son ka gani da idonka, yau kwanakinsa biyu bai zo gidan ba, ina zaton yau zai iya shigowa. Idan ka gani sai kaje ka sanar da Hajiya, domin ita kadai ce zata iya maganin matsalar nan”.
Ya gyada kai cike da gamsuwa da bayanin nata, “Tabbas wannan ce kam mafita amman da Yaya Malam _yaji Bunya. Mutum kamar shi ~mai nusar da wasu abin da za su yi da inya shiga haKkin wani amman shi yake aikata wannan abu?”
“Kada fa kayi mamaki, sharrin mace ya .wuce da haka, balle kowa ya san Fatila ba kanwar lasa bace. Jidda ta tunasar da shi.
Sun jima suna tattauna maganar abin yana basu tausayi matuka.
A daren kam Hashim ya dinga zuba ido k0 zai jiyo kukan motar Mukhtar, amma shiru Malam ya ci shirwa, har bacci ya dauke shi. Da safe yake tambayar Jidda k0 yazo? Ta tabbatar masa bai zo ba, don haka daren yau ma ya fara baza kunne sai wajen sha daya saura kwata ya jiyo shigowar shi, ya zagaya da sauri ya labe can gefc yana hango sanda Mukhtar ya yi kiran waya bayan kamar minti biyu sai yaga Falmata ta fito. Abin ya ba shi mamaki matuka, sai kace irin rubutun littafi k0 kuma a film” Wai yau yayansa ke aikata haka, duk ’ da bai jiyo abin da yake gaya mata ba ya kula ‘ maganar mai zafi ce, domin gaba daya yanayinta ya sauya zuwa damuwa, sai ya ga a hankali tana ja da baya daga jikin motar, shi kuma kawai sai yayi ribas ya fice daga gidan a guje. Falmatan taci gaba da kallon motar cike da fargaba da damuwa tsawon lokaci. sannan ta nufl cikin gidan tana goge
fuskarta alamar kuka ta keyi.
Wani irin tausayi mai tsanani ya cika shi, wace irin mace ce Falmata mai tsananin hakuri da zurfin ciki haka? Wato ba dan sun gano ba ta gwammace ta mutu a haka da ta sanar da wani abin dake damunta?
Da kyar yar ya iya jan kafa ya koma dakinsa, dan dare ma ya yi da yanzu zai wuce gidan nasu ya sanar da mahaifiyarsu , sai dai ya barwa washegarin.
Ai kuwa washcgari k0 shigakari bai yi cikin gidan ba ya wuce babban gida, Jidda tana ta kwala ido ta ga shigarsa shiru ba ta gani ba, can ta kasa hakuri ta dubi Falmata sanda suke kari, ta ce
“Anti Falmata yau dai mutumin naki dadin bacci yake ji, kinga har yanzu bai tashi ba, balle ya nemi abin kari”.
Falmata ta danyi murmushi, domin ta riga taharbo jirgin nasu, ta ce “Toko za kije kitaso shi ne?”
Da sauri Jidda tace “Eh mana, sai naje na . taso shi  don kada ya huce k0?”
Falmata tayi dariyar da bata shirya yinta ba. tana fadin. “ke Jidda abin har ya kai haka kenan? T0 hashim ya fice, ina jin karar babur dinsa tun dazu ya fice”. Kunya ta kama Jidda ta rufe fuska tana fadin“Kai Anti wai saurayina, inji wa?” . Falmata taci gaba da zolayarta har sai da’ta tashi ta falla daki da gudu tana dariya.
A can gidan su Hajiya, Hashim ya isa ransa
a Bace ya tadda Hajiyar tasa tana karyawa, sabon tuwo aka tuka miyar ayayo, don haka yana shiga, tace
‘ “Ayya yau ga malam Hashim ga tuwo; yau dame zaka karya kenan kai daba kason tuwo a rayuwarka‘?”
Ya yi yake ya zauna yana fadin “Ai dole kuwa hajiya a samar min abin da zan ci, don yunwa nakeji wallahi. Ban k0 karya ba na flto”. Hajiya ta mike sa sauri ta leka gurin masu
aiki, ta ce su soyawa Hashim dankali da kwai da
Ruwan shayi, ta dawo ta zauna suka ci gaba da hira.
tana cin abincin kada ya katse mata ya sanya
bai sanar da ita ba, ya dake suka ci gaba da hira har
sai da aka kawo masa kayan kaeinnsa, yaci ya koshi
sannan ya gyara zama yace
“Hajiya nifa Karar Yaya Malam na kawo”. Mamaki ya cikata tace “Hashim yau kuma kaika kawo karar yayan naka? Lallai abin babba ne me ya yi maka ne?”
Ya sunkuyar da kai kasa, yace “Ba ni ya yiwa ba, illa Falmata da yakE zalunta da sababbin halayen da ya samo…” .
Da hanzaei ta katse shi, “Alhamdu lillah yana daga cikin dalilin daya sanya ma yarda ku zauna’ a gidan domin kada a cutar da diyar mutane sanar dani me ya faru ne?”
Ya kwashe duk abin da ya sani da wanda ya gani ya sanar da ita.
Mamaki da tausayin Falmata suka shige ta, ta ‘kuma tafa hannaye tana sallalami cike da damuwa ko a cikin satin sai da ta tsare Falmata da tambayar abin daje damunta, tace babu komai, sai tayi zaton k0 tana cikin irin jinsin matan nan ne da ake cewa suna da tsoron tsotso, don suna shayarwa sukan rame, _
Ta kalli Hashim a fusace tace “Amma mai ya sanya tsawon wannan lokacin ba ka sanar dani ba sai yau?”
Yadda ta balbale shi da fada tamkar shine ya yi laifin
Ya kama‘rantse-rantse yana fadar “Wallahi Hajiya nima a shekaran jiya Jidda ke sanar dani na sanya ido’na kuma  tabbatar shi yasa nazo na fasa miki,
amma dana sani tuntuni da wallahi na sanar daje
Ta yi shiru ta cika fam. takaicinta bai Wuce  a ina.Mukhtar ke kwana ba, ba dai yaronta mai tsantsani da tsoron Allah Ya lalace ba? .
Ta kalli Hashim jikinta ya yi sanyi, tace “To hashim a ina kake ‘zaton yana zuwa ya kwana? K0 ya fara bin matan banza ne?”
Idonta ya cika da Kwalla, tabbas idan hakan ta kasance taga ta kanta, wannan shi ne ana kukan targade kuma sai ga karaya ta samu.
_ Hashim ya yi shiru bai son tabbatar da zargin da mahaifiyarsa keyi, domin duk gidan su babu wani dake irin wannan mugun halin, balle malam dake da tsantsani da tsoron Allah, wanda ake ganin shine ya gaji mahaifinsu a komai. ya ‘ daure yace ’
“Hajiya ba na zaton yaya Malam zai bi matan banza, sai dai wani abin ba wannan ba ina kyautata masa zato insha Allah. Ubangiji ba zai jarrabeshi da wannan mugun aikin ba”,
‘ Sallamar haajlya Babba ya katse musu hirar tasu. Ta shigo a rude tana kwadawa Hajiya Mariya kira. Hajiya mariya dake zaune ta mike tana fadin.
“Yaya ‘gani nan, yanzu nake shirin shiga
sashin naki kika shigo, karaso kiji wani mugun labari da Mukhtar keyi kuma”.
Hajiya Babba ta Karasa shigowa tana fadin.
“Au k0 kin ji abin da nazo gaya miki miki ne game da Muhammad din?”
Hajiya Mariya tace “Me kuma ,ya faru Yaya? Yanzu dai Hashim ya shigo yake sanar dani wai bai kwana a gidansa, ashe kema kin sami labari ne?”
Hajiya Babba tace“To yaushe zai kwana a gidansa timda ya tattara ya tare gurin waccan shegiyar yarinyar Fatilar…”
Hajiya.Mariya ta dafe kirji tana fadin, “Na shiga uku, ba dai a gidansu yake kwana ba Hajiya Yaya? Ina fa gidansu? Ai tuni ashe ya maida ta, a can gidansa yake kwana, muna nan mun saki baki ashe sun jima da komawa”. Cewar Hajiya Babba.
Hankalin Hajiya Mariya ya tashi matuka, idonta ya cika da hawaye tace
“Mukhtar abin da kayi mini kenan? Abin
da ka yi mini Allah Ya… ‘ . Hajiya Babba ta katse ta da sauri, tace don Allah kada ki yi masa baki, kin sani sarai duk abi. daje faruwa ba yin kansa bane addu‘a ya dace muyi masa amman tabbas abin akwai mamaki

Hmmmm su fatila fa karensu sukeci kawai babu babbaka🤗
Masu nadar post dina Suna turawa groups da pages bada izni na ba bazan muku baki ba amman inajin ciwon hakan typing da wuya fa

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE