MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 28

MATACCIYAR RAYUWA
BOOK 📚 4
CHAPTER 28
Ita ko daren yau yafi mata ko wanne muni, wato haka zata yi ta 
cinye darare cike da bakin ciki kenan? 
Tabbas ban da babu kyau mace ta nemi saki 
ita kam yau da ta ce ya sauwake mata ta huta, Allah ne ya kaita wayewar gari lafiya. 
daga wannan ranar ba ta kuma mannarin zuwa d‘akinsa ba, ta yi alkawarin ko kewarsa zata kashe ta ba zata Kara binsa ba, a haka suka ci gaba da zama. 
Hajiya, ce ta dauke Muhammad domin a ganinta shi yake hana Falmata Kiba, ga shi. 
. daman a Iokacin ya yi wata ashirin da biyu, kwara ace ta yi kiba, abnin da ya bawa Falmata mamaki ko da ya ga bai ganin yaron bai tambaye’ta yana ina ba duk da tasan zai ganshi gidansu, abin kam yana girmama mata, wacce irin kiyayya yake yiwa yaron nan? Ita ‘kam Hajiya da taga ba ya kula yaron sai ta yi zaton ko irin alkunya ce ta d’an faei, don haka bata kawo komai a ranta ba. 
Yau ya shigo gidan yana sauri ya dauki
wani fayil dinsa da ya manta ya duba dakinsa bai gani ba, sai ya nufi dakinta, lokacin ta cire rigarta tana shafa wani maganin ciwon nono na hausa da Hajiyan ta aiko mata saboda kumburan da maman nata ya yi, har ya zuba mata’ zazzaBi, idan ta shafa maganin kuma tana jin dadi ga shi idan aka shafa shi maman mace bai zubewa, ya turo Kofar dakin ya shigo. Kai tsaye idonsa ya tsaya akan maman nata ya tsaya turus yana mata wani kallo, wani abu ya ji ya soki ransa Ta kula da haka don haka ta ja rigarta da sauri ta rufe, ya shigo dakin jikinsa ba kwari ya kama binciken abin da yake nema, yayi sa’a ya same shi kuwa ya dauka ya fice, sai dai tunda ya je ‘ofis din take masa gizo. Ita ma ya barta da tunani yaushe rabon da mijinta. _ yayi mata irin wannan kallon? Ta kula mak0 kallonta ba ya son yi, sai ta tsinci kanta da godiya ga Allah. Da daddare yana dakinsa yana ta juyi amma ya kasa kiranta, da zarar yafita waje sai yaji sha’awar matarsa ta kama shi, amma
idan ya shigo gidan sai yaji duk babu. Daga karshe sai ya mike ya tafi can wani saki da ake ajiye inji can bayan gidan, ai kuwa sai ya ji gaba daya ta dawo ransa ya kira ta .a wayarsa ya ce ta tadda shi dakin inji. . 
Abin ya ba ta mamaki tana jera kayan wanki. ne cikin sif, ta ajiye ta sanya hijab dinta ta nufl dakin injin. 
. Wani abin mamaki, tana shiga ya ja ta jikinsa, wannan fa shi ne ikon Allah, mutum da gidansa an hana shi kusantar matarsa a ciki . .saboda rashin tsoron Allah. Tun tana mamakin abin har yazo ya fara ba ta tausayi, don kuka ya dinga yi da idonsa, wannan shi ne abin mamaki. 
Sai da ya kammala ya ce, ta wuce d’akinta. Bayan ta isa daki ta dinga mamakin wannan lamari, tabbas ta yarda wani abu aka yi aka rabata da mijinta, zata ci gaba da gaya wa Allah. 
Ashe wannan haduwar tasu rabo ne, don karshen wata ba tayi al’ada ba, tun daga .sannan ta kama laulayi. shi kuma in dai yana 
bukatarta sai dai ya kirata can, abin dake ba ta mamaki a can din sai yayi ta tausarta bisa sunna ta Allah da bakin bai bai k0 damuwa, tabbas Allah sai ya saka musu, ita kuwa F atila tana da tabbas shi da ita har abada, haka ciki ya girma. 
Sai dai tunda cikin ya shiga wata bakwai ya daina kiranta d’akin inji, abubuwa sukafi baya rikicewa, ita dai tana ta gayawa Allah halin da ta ke ciki, domin ta san shi ne 
zai fiddata. . 
‘ Yau ma ta je awo ita da Jidda kamar da wasa sai ciwo ya kamata a can, tana shiga likita yace, “Ai nakud’a ce maza jidda ta je gida ta hado kaya, ai kafin Jidda ta dawo ma hat ta haihu an samu katon da, don haka sanda_ Jidda ta dawo ta dinga tsalle ta kira wayar Hajiya da Mukhtar ta sanar dasu. ‘Kafin ka ce meye wannan asibitin ya cika damkam da dangi, kowa yana murna yaron kamar su daya da Muhammad. 
Mukhtar kam ya yi matukar farin’ciki. ya d’auki yaron ya yi masa huduba da sunan 
Abba, yadda ya dinga rawar kai abin har mamaki ya bawa Falmata sai dai yana ambaton an sami Abba ta ji wani farin ciki ya cika ranta, haka suka kwasa aka yi gida. 
. Sai dai tunda suka koma gidan abin jiya ya dawo, Falmata ta jima da kula da duk wani abu da aka yi musu na sammu yana cikin gidan nan, domin in dai za su had‘u a waje zai yi ta nan-nan da ita, amma da zarar sun shiga gidan magana ta kare. 
. Su Fatila kam da ta sami labarin Kara 
haihuwar Falmata suma ta yi don bakin ciki, a kuma lokacin suka kuma bazama neman asirin da za a farrakasu har abada, boka har kasar India aka tafar musu. 
Ai kuwa komai na suna Mukhtar ya yi kamar bai san ciwon kudl ba, sai dai ranar suna wani kudiri ya shiga ransa, ai kuwa an kammala suna lafiya an ci an sha an yi hotuna cike da farin ciki mai jego ta fito daga wanka tana goge jikinta ya shigo, bai ce mata komai ba ya mika mata takarda yana fadin
“Dama baki da iddata don haka sai kuzo ku kwashne kayanku gobe, na kula zamanmu ina cutar dake”. 
Mamaki da tsoro ya kamata, ta kasa cewa komai har ya fice, sai ta fashe da kuka, Allah Ya sanya wannan karon Yayar babarta ‘ da Yakura ne kadai suka zo sunan, don Abba ya hana kowa, ai kuwa Innar tata ta shigo da gudu tana tambayar abin da ya faru, ta mike. mata takarda tana kuka. 
Ta amsa ta karanta saki ‘ne guda daya, nanta kama sallallami ta yi da Hausa ta yi da barbarci,‘ Hajiya Babba tana gidan ta shigo don jin hayaniyar ta yi yawa, nan ita ma aka nuna mata ta kama salati da sallallami ai kuwa sai ta kira wayar hajiya Mariya. 
Hajiya ta iso gidan a gigice hankalinta ya tashi ainun, sai ma ta rasa me zata yi, sai ta fashe da kuka kawai. Da kyar aka dinga rarrashinta tayi shim, Falmata kam sai ta ji ta fitausayin Hajiyar ma a kanta. don Allah su dakata har ta yi waya da Abbagana tukunna. 
Shi kam Malam daga nan kasa komawa gidan Fatila ma kawai yayi sai ya wuce ofis ya yi ‘ zugum cike da tunani da Bacin rai. 
Ya yi zaton idan ya saki Falmata zai nemi damuwar da yake ciki ya rasa, amma sai ya ji komai ya karu ma, haka nan ya dinga kaiwa da komowa yana sake-sake. 
Sanda malam Abbagana ya ji abin da ya faru ransa ya baci matuka, hankalinsa ya tashi domin bai taba zaton Mukhtar zai iya yi masa haka ba, rokon da Hajiya ta yi na ya bar Falmata a hannunta yaci tura ya ce ta yi hakuri gwara dai Falmata ta_ komo gida, kada kuma ta dauka hakan zai kawo yankewar zumuncin tunda ga 
‘ya’ ya sun Kara hadawa, dole Hajiy’a Mariya ta hakura ranta a bace
Washegari tunda sassafe suka ‘sauki hanyar Maiduguri,Fa1mata kam Kunshe kanta ta yi cikiri hijab ta dinga kuka, yau za ta bar garin da take matukar so da kauna a
rayuwarta, ganrin masoyinta Mukhtar Mai darasu da yake sonta. Shin zata kuma dawowa Kano kuwa? Ya ya zata yi da yaranta wadan nan tunanin su suka dinga damunta, ta dai tabbatar Mukhtar ya yi mata wulakancin da har ta mutu ba zata manta da shi ba sam, amma duk da haka ta yafe masa, ba zata kullace shi da komai ba. 
*** *** 
Sanda suka iso. Maiduguri hankalin Hajja Kaltum da mahaifiyarta sunyi matukar tashi, su Hajja Yakolo kuwa murna har da zuba ruwa a kasa a sha, domin a cewarsu Allah ne ya saka musu akan cin kashin da ake musu. Ita kam Falmata jin duniyar ta ke gaba daya ta yi mata zafi, sai da Abba ya dinga tausarta da kalamai masu sanyi ya nuna mata komai na duniya a tsare yake gurin Allah, tunda Allah Ya kaddara rabuwarsu da Mukhtar babu sauran tsumi balle dabara. Cikin ikon Allah ta dan saki ranta ta ci gaba 
da rainon yaronta dake kama da mahaifinsa sak. 
Mukhtar kam komai ya tsaya masa, musamman sanda ya iso gidan Falmata yaga babu komai. Sun kwashe, abinsu hatta Hashim ya fice daga gidan da J idda, baiwar Allah kam da kuka daman suka rabu da Falmata sai ya tsinci kansa cikin mugun bakin ciki, ya zauna dandariyar kasa sai ya kama kuka kamar ba namiji ba, yana tambayar kansa laifin da falmata ta yi masa ya dinga tariyo rayuwarsu yana tunanin cin kashin da ya yi mata amma ba ta taBa sanar da wani ha, shin ina zai tsoma ransa. 
Tun daga wannan ranar bai kuma samun kwanciyar hankali ba, mahaiflyarsa kam bata kula shi idan zai wuni a durkushe ba ta sauraronsa, duk irin wanda zai shiga maganar ya shiga, amma ta ce ta tsame shi daga ‘ya’yanta ta barwa Kumatu. 
Su kam su Hajiya Kumatu duniya sabuwa dal, domin suna ganin bokansu ya gama musu koma Fatila tayi alKawarin k0da
zata yi yawo tsirara babu mijinta ba wata mace, don haka ta kuma bude faifan asiri kala-kala, duk da zamanta da malam din ya sauya matuka, ba sakin jiki da’ faram-faram kamar kullum cikin tunani yake. . 
~A haka watanni shidda suka shude, tunda Falmata ta komo gida mahaifinta yake ta yi mata fafutukar samun gurbin karatu na jami’a. An yi sa’a kuwa an samar mata a islamic University  0f  Madinag, bai sanar da ita ba sai da aka karnmala komai har da ranar taflyar. 
Hankalin Falmata ya tashi matuka, jin zata taf1 ta bar yaranta musamman mai shan nonon da duka-duka watanshi shida ‘ da kwanaki, amma da yake mai ladabi ce sai ta kasa musawa, shi da kansa Abba ya lura da halin da ta ke ciki, ya taddata har dakin mahaifiyarta ya dinga tausarta da nuna mata hakan shi ne kadai gatan da ya rage ya yi mata. Tausayin mahaifinta ya cikata, mutum mai tsananin sonta da farin cikinta, ta wani Bangaran ma ai ta huta da habaici da yada maganar su hajja yakolo
Hmm labari dai na tafiya yaddah ya kamata fatila kam dai tace koda zatai yawo tsirara ba mijinta ba wata mace su falmata kuma za,a shilla qasar larabawa shin me zai faru!!!? 🤓 tunda bakwason yin comments bari a rage yawan post din naga kamar bakwason a kammala da wuri nima kun hutar sani😄

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE