MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 30
MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 30
yana sonta, ai da ta more matuka.
Sanda ya iso dakin Hajja Iyami duk sai ya ji kunya ta rufe shi, tabbas iyayen Falmata mutane na gari, don ba su nuna masa komai a fuskarsu ba, hakan ya sanya kunyarsu ta rufe shi, duk da Hajja Iyami tana ta jansa da .hira, amma ya kasa sakin jiki da ita, burinsa bai wuce ya ga Falmata k0 ya jiyo sautin muryarta ba, amma har suka kammala hirar . bai ganta ba, dole yayi musu sallama ya koma masaukinsa, akan gobe zai zo su yi sallama ya wuce gida
A can d’akin Hajja Yakolo Yakura ce ta tsare mahaifiyarta da korafin malam mai darasu.
“Hajja ni fa gaskiya Muhammad ya yi mini, irinshi na jima ina fatan na aura’Zubaida ta ce, “Amma kin manta mijin kanwarki ne Yakura?” Yakura ta gallawa Zubaida harara tana
fadin “A da ba, yanzu kam ina da damar auransa, babu haramci a yin hakan”.
Zubaida ta gyada kai, tace.
“Cabdijan, amma da an ji kunya
wallahi”. , Tana maganar tana zumbura baki, alamar tsananin kishi da baKin ciki ya bayyana akan fuskarta, domin ai ita ma tana son malam din, sai dai ita har yanzu auran nata bai mutu ba, kuma ba ta koma ba, shi kuma Abba ya zuba musu ido yaga’iyakacin ‘ gudun ruwansu. ‘ ‘ ~ .
Hajja Yakolo dake kallonsu ta yi ajiyar zuciya cike da Bacin rai, tace, “Wannan ba magana ba ce mai yiwuwa Yakura k0 da shi ya amince yana sonki, mahaifinku ba zai yarda ba, shi fa burinsa bai wuce shegiyar yarinyar can Falmata ta koma gidansa ba, don haka sai dai kiyi hakuri hakan ba zai yiwu ba”.
Yakura ta kufula cikin tsananin bakin ~ciki, tace.
“Hajja ya kike fadin hakan, idan har Mukhtar ya amince zai aure ni, ko babu amincewar Abba sai na aure shi”. Yakolo ta harare ta cike da bakin ciki, ranta yana suya tace.
“Don Allah Yakura ki bar wannan maganar, kada ki ci gaba da Bata min raina, ni fa lamarinku ya fara isata, kullum magana daya, kin Ki fidda irin mijin da nake so, kina kallon yadda ake min gori a gidan nan, yanzu kuma kizo da wata banzar magana?”
Yakura ta ,,,,,, cike da’ bakin ciki, tace.
“Ai kuwa wallahi Hajja sai dai kowa ya rasa, don ba zan yarda falmata ta koma gidan Muntari ba, Allah”.
Hirar tasu dai yau kam baram-baram ‘suka watse, domin ita Yakolo hankalinta a tashe yake saboda zuwan Mukhtar, ga kuma ‘ Yakura tana neman sanyata cikin wani tashin hankalin.
a. ransa, ya dinga ayyana kamanninta da irin yanayin zamansu, sai ya Kagu gari ya waye yaje ya ganta.
Kwana ya yi yana shirya kalaman da zai dawo da zuciyarta cikin sonsa; sai ya tsinci kansa da kasa bacci a’ranar, ya‘ kwana yana sallah da rokon Allah Ya kawo masa komai da sauki.
Karfe goma ya isa gidan Abba, a falon Abba na cikin gida aka yi masa masauki, sai dai yayi rashin sa’a, Abba ya tafi jana’iza cikin gari, don haka da Hajja Iyami kawai suka gaisa ta fice ta barshi da yaransa da suka ci kwalliya cikin wata shadda mai taushi da ;tsada. Ya dinga kallon .yaran da sha’awa, da kuma soyayya, shigar tasu ta yi masa kyau matuka, sai ya tsinci kansa da tambayar waye ‘ya yi musu wannan dinkin wanda ya dace ace shi ne ya yiwa ‘ya’yansa? Shi kam Abba da yake mai son jiki ne a jikin uban nasa ya lafe yana tsotson hannu.
Malam ya janyo Muhammad ya rike hannunsa, yace
“Muhammad ina Ummanku take ne, tunda nazo ban ganta ba?”
Cikin gwaranci yaron ya ce.
“Ummanmu ba ta nan, ta tafl can‘ wani gari cikin mota, kullum sai na tambayi Hajja ta ce ba ta nan”. Yana maganar yana dariya.
Sam bai gano inda maganar yaron ta dosa ba, yafi yarda da shirmen yaron ne kawai. Ya . jima zaune yana sakawa da kwancewa k0 tashi zai yi ya shiga gidan kai tsaye ya tambayi Hajja Iyami? Amma dai yaga ba zai iya ba, dole ya hakura ya tura yaran cikin gida. Sai” dai abin mamaki, sai yaran
.suka kama kuka, dan wunin da ya yi da su kwana biyu wai har Sun saba da shi, da kyar ya kirawo Ahmad kanin Falmata ya shige da su cikin gida suna .kuka, don Abba har hannu ya dinga mikowa sanda aka shiga da su cikin gidan Wannan abin ya tsaya a ran Mai .darasu; ‘ Har yana tafe a hanyar komawa Kano yana jiyo sautin kukan yaran nasa yana masa
amsa kuwwa a cikin kunnuwansa, sai yake jin kamar ya koma ya dauko yaransa, wannan ne ya kuma kwadaita masa dawo da Falmata gidansa, duk da bai sami ganinta ba.
Wannan karon ya san insha Allahu zai dace ta amince ta koma dakinta, da wannan tunanin ya isa Kano.
Bai isa Kanon ba sai dare, amma duk da haka bai wuce gidansa kai tsaye ba, babban gida ya wuce.
Su Hajiya suna falo suna kallo ita da autanta Hashim, Mukhtar ya shigo ta daga kai tana amsa sallamarsa’ da mamaki akan fuskarta, don ba ta zaci da ya dawo zai yo nan ba, domin ta san da maganar dawowar tashi yau ta bakin Hashim.
Ya sami guri ya zauna fuskarsa a sake, ya ce.
“Kin ganni sai yau ko Hajiya, mutanen naki‘ yan rigima sun hanani dawowa, yau ma da rigima muka rabu, sai da Ahmad ya shige dasu cikin hajiya mariya ta yi murmushi cikeda farin Clki taCe. “Kace maigidan nawa Abba ya fara
gane mutane ke nan?”
Ya y’i murmushi, ya ce, “Sai gwarancin tsiya, shi kuwa Muhammad kaudl kamar zai tsinke maka kunne”;
Hajiya Mariya ta dinga dariya cike da farin ciki, lallai jikokin nata suna cikin koshin laflya ke nan. Ta saki jiki suka yi ta hira da_ Mukhtar, kamarba fushi ta keyi da shi baTa kula yana son ya sako mata maganar Falmata, yana shakka, ita kuwa sarai ta san Falmata ba tagarin ammataKi sanardashi, tayi’ aLkawarin ba zata taba yi masa maganar Falmnata ba sai dai idan shi da kansa ya yi zancen Da ta kula ba shi da niyyar taflya, ga shi sha daya na dare ta wuce, sai ta ce masa.
“Ya dace ka wuce gida ka huta tunda dare ya yi”.
Haka nan ya mike ya nufl gidanshi ba don ya so ba, domin ya so ya dan ji wani abu game da Falmata, amma ransa cike da farin ciki yake ganin mahaifiyarsa yau ta saki jiki da shi, yau sun sha hira.
INA LABARIN FATILA?
Fatila kam, tunda Mukhtar ya tafi Maiduguri bata cikin nutsuwarta, kullum‘ cikin kuka da damuwa take, ga shi idan ta kira wayarsa ko da ya daga bai wani sakin jiki su yi hira, kamar yadda suka saba. Don yau da safe ma bakin ciki ne ya sanya ta datse kiran nasa, domin tana masa magana ta jiyo muryar Muhammad yana ta ba shi labari, sai . zuciyarta ta ayyana mata Falmata tana gefensa a zaune tunda ta jiyo muryar yaranta, wannan ya sanya ta kashe wayar ta fashe da kuka sosai. Ji takeyi a wannan lokacin kamar ,ta hadiye zuciyarta ta mutu ta huta, ga shi Hajiyarta ta ce ta gaji da lamarinta, sai dai ganin diyar tata tana ta ramewa don bakin ciki ya sanya ta nufl gurin boka, ya ba su abin da ya saba basu, da Karyar da ya saba yi musu ta kawo diyar tata da sunan wai a zubawa malam oil abincin da zai dinga ci, hakan zai sanya ya manta da Falmata da yaranta. Da ace suna da hankali da ya kamata su hankalta su gane abinda Allah Ya kaddara zai faru babu wanda ya isa ya hana shi faruwa.
Tana tsakiyar gado ta kudundune cike da takaici, ta jiyo bugun kofarsa. Tayi kamar ba zata bude ba, sai kuma ta ga rashin dacewar hakan, tunda tana son ya dinga cin abincinta ko asirin ya yi tasiria kansa, sannan kuma Hajiyarta tace dole fa sai ta dinga haDawa da kissa da kisisina yanzu ta kuma . rage zafin kishi hakan zai sanya su san halin da yake ciki da Falmata don su san yadda za su dinga Billo mata, _
Har ya dan fara kufula saboda ba ta bude kofar da’ wuri ba, amma ganin tana goge ido ya sanya yayi zaton ko_bacci ne yayi .nisa ba ta ji shi ba.
Ta yi kokarin kakaro murmushi tana fadin.
“Sannu da zuwa Hubbyna, ina nan ina ta kewarka”.
Duk da maganar ba ta wani burge shi ba, amma ya dan saki rai yaceYauwa, ya ya gida?”
Yana wucewa cikin gidab
Ta bi shi a baya tana kallonsa da baqin ciki, sai ta ke ganin kamar wani abu ya shiga tsakaninsa da Falmata, sai dai ta danne zuciyarta ta bi shi dakinsa.
Amma abin da ya qara kona mata rai bai wuce ganin bayan ya watso ruwa ya haye gado ya kama bacci ba, har da munsharin gaji’yar tuki kuwa, duk yadda ta so ya kusanceta ya basar, sai taga kamar bai kula da kwalliyar da ta yi ba ma sam, haka ta dinga kallonsa cike da bakin ciki, kishi yana tsikararta, ban da tana tsananin son Mukhtar da ta shake shi da ya mutu ta huta da wannan bakin cikin da yake kunsa mata.
Da safe ma suna gurin kari ya dame ta da labarin Abba da Muhammad, duk da tana jin kamar yana watsa mata ruwan tafasasshiyar dalma ne a duk sanda ya ambaci sunan yaran nasa, amma ta dan ji dadin ganin yadda dage yana cin abincin, hakan ya Sa take ganin ta kusa yin nasara a kansa.
sai dai ba ta san wannan malam din ya sauya daga wanda ta sani a baya ba, yanzu ya dage da addu’o’i na karya sammu ba.
Haka nan ya kammala cin abincin ya wuce ofls dinsa, a can din ma hiran shi daya ta yaranshi, ya dinga bai wa Dr. Usman labarinsu yana dariya, hakan kuwa ya yiwa Dr. Usman dadi Ya tabbatar sammun da aka yiwa abokinsa na raba shi da ‘ya’yansa ya karye, domin ya yi bincike sosai ya gano ba Karamin asirin farraku aka yi tsakanin abokin nasa da yaransa gami da matarsa ba, hakan ya sanya kullum sai yakaWo masa ruwan addu’a duk da yasan abokin nasa ma ya iya, amma yana ganin yana da sakaci don haka ya judiri aniyar taimakonshi.
ISLAMIC UNIBERSITY 0F MADINAH Yau kam a gajiye tibis suka dawo daki, Falmata ta cire nikaf din dake fuskarta da hijab din dake jikima, ta watsa a gado sannan ta fada tana haki tamkar wacce ta yi tseren gudu.
Ammi ta kalle ta tana dariya tare da fadin.
“Yarinya na gaya miki rashin sinadarin aure ya sanya kike saurin gajiya., ni kinga da yake Isofu yana zuwa duk wata yana bani bana gajiya kamar ke”
Falmata ta wawuro filo ta wurga wa Ammi suna dariya, ta ce.
“Wallahi ke yar iska ce, ni kam babu
ruwana da wannan maganar”.
Ammi ta mike ta rike kugu tana fadin.
“Kan ubancan, ni ce ma ‘yar iskar? Don nayi miki maganar aure, to wallahi sai na kira wayar mai darasu nace ga ki nan kina ta kuka da kewarsa”.
Ta nufl gurin wayar Falmata da gudu, sai dai kafin ta je Falmata ta dauke wayar ta Boye a cikinta, nan suka kama dambe, wai sai ta kwata, duk da Falmata ta sake layi amma ta kasa goge lambar Malam daga wayar idan ta yi kamar ta goge sai ta ji ta kasa, don tana ganin kamar ta aikata laifi ne mai girma‘, hakan ya sanya duk lokacin da Ammi ta so tsokanarta sai ta ce sai ta kir lambar Malam din.
Suna tsaka da kokawa wayar ta fara kara, Falmata tana dariya ta ce.
“Don Allah ki dagani na amsa, wallahi kiran Hajja ne”.
Hakan ya sanya Ammi ta dagata ta koma gefe tana kallonta tana kuma yi mata dariya.
Falmata ta danna gurin’ amsa kira. sannan ta kara wayar a kunnenta. Daga can Bangaren Hajja Iyami ta yi-mata sallama, ta amsa da ‘sauri gami da gaisheta cikin ladabi tamkar Hajjan tana gabanta. Bayan sun gaisa
ta fara tambayar Hajja mutanen gida. Hajja ta ‘ dinga ba ta amsa, Muhammad yana gefe yana tSalle yana cewa.
“Ke Hajja ki bani Umma na yi mata magana mana.
Hajja ta mika masa tana dariya tare da fadin. ‘
“Dan kare mai shegen surutun tsiya, amshi uwar taka ka kama zanina ka cukwikwiye kada ka balle min shi”.
Falmata ta fashe da dariya cike da jin dadi tana fadin.
“Ai kuwa da na fasa siyo” masa game dinda na ce zan siyo masa”.
Dai-dai lokacin da ya amshi wayar ke nan, da sauri yace mata.
“Ki yi hakuri Ummana, na daina kuma ina yin karatu yadda kika ce a gurin Abba, har na fi shi lyawa”.
Falmata ta yi dariya cike daJin dadi,tace
“To shi kenan, amma ba ka yi wa Hajja kukan banza k0?”
Ya ce, “Bana yi mata, sai‘rannan sau daya da Babana yazo daga wani gari a mota ya kai mu yawo ni da Abba, ya siyo mana kayan dadi, shi ne da zai taf1 muka dinga yin kuka, shi ne kawai ranar da nayi kuka”.
Ba ta taba kawo Malam ba, tafi zaton Yaya Kabir wanta ne, don yana son yaran. don haka ta ce.
“To kace da Hajja ta sanya Ahmad ya
kai ku gidansa ku kwana mana, ko ba Uncle
Kabiru ba ne?”
Da sauri’ ya ce, “Ba shi bane, wannan
sunanshi Abba Malam na Kano, haka Hajja tace mini, kuma ta ce shine Babana ni da Abbanki…”
Gabanta ya yanke ya fadi, da gaske Malam ne yaje Maiduguri ganin yaransa? Lallai abin da tsananin mamaki da yake wayar a handsfree take duk Ammi tana jin abin da suke fada, ganin jikin Falmata‘ya yi sanyi ta
rasa abin cewa ya sanya Ammi ta warce wayar da sauri tana fadin
“Dana Muhammad yaya motar nan taka daka ce zaka kai ni Makka da Madina cikinta?” . ’
Muhammad ya fashe da dariya cike da jin dadi yace
“Aunty Ammi, yanzu Abba na Kano ya siyo mini wani Katuwa ma, da ita zan kai ki idan kuka zo gidan Hajja, ba kin ce mini zaki zo ba?” Ammi tace“Eh haka ne, amma bani Hajja mu gaisa k0?”
Da sauri ya mikawa Hajja wayar, ya fice yana ihun murna wai zai kai wa Abbagana labarin abin da ya faru. Cikin sakin fuska suka gaisa da Ammi da Hajja, domin sun saba a wayasosai, kuma Hajja ta yaba da
hankalin Ammi duk da ba ta ganta a zahiri ba, a waya kawai ta santa.
Bayan sun ‘gama gaisawa ta kashe wayar ta nufi gurin Falmata da ta zauna gefen gado ta yi shiru tana tunani.
Ammi .ta kalle ta da kulawa tace
‘ “Wai don Muhammad yace babansa yaje duk kika damu haka, k0 ciwon son ne ya taso?” ‘
: Ta karasa maganar tana yi mata dariya.
Falmata ta harareta tace.‘ ,
“Ni ba wannan -ne damuwata ba.. Ina ‘tsoron kada Mukhtar ya ce zai kai wa Fatila ’yayana,ne tunda ya fara zuwa gurisu komai zai Iya faruwa”.
Ammi ta yi dan jim, sannan tace “Ba na jin Hajja da Abba za su yarda su
bai wa Mukhtar yaran nan a yanzu, ko da sunso ba shi ma Hajiyar Mukhtar din ba zata yarda ya kaiwa Fatila su ba”.
Ta dan sha kunu ta tsére Falmata da ido, tace
“Falmata Allah na kula kina son Mukhtar da yawa, don haka zan sanar da Babana ya yi aiki akan komenki gidansa. hakan zai sanya’hankalinki ya kwanta”. Falmata ta dafe kirji tace
“Don Allah kada ki soma, kina nufin sai na yiwa Mukhtar asiri zab koma gidansa, ashe mun zama daya da Fatila ke nan, duk da na san aurena da Mukhtar ba aure ne na so ba,‘ aure na irin na biyayya ba na fatan na koma gidansa ba da son ransa ba, a can baya abin da ya ja min duk abin da ya faru saboda ya aure ni bada son ransa bane”.
Idonta .ya ciko da kwallah, ta kauda kanta gcfe idonta’yana zubda hawaye ta ce.
“Ammi ba na fatan na koma gidan Mukhtar har abada, muddin yana tare da~ Fatila. Ni kadai na san irin azabar da na sha.
duk wani abu da za a iya kiransa da wulakanci da tozarci Mukhtar ya yi min shi ‘ lokacin zaman aurenmu, sannan na sha shafe darare ina kuka saboda bakin ciki, na kuma sha fad’a _da aljanu akan’ auren Mukhtar, don haka ba’na fatan na komawa aurensa har abada .ko da Abba ba zan iya yi masa biyayyar dana yi masa a baya na koma gidan’ Malam ba Na kyalewa Fatila shi, dama karambani da kuma zabo ya sanya ni shiga tsakaninsu”. ‘
Tausayin F almata ya cika Ammi, daga yadda ta ke magana ka san tana tsananin’son ’ Malam, amma tsoron Fatila ya sanya ‘ta’sadaukar da soyayya ta hakura da shi, ‘ ta kauda kai gefe ta ce.
“Falmata na gama gano Fatila ce‘ matsalarki da Mukhtar, don haka ki yarda don Allah ki, .ba ni kwanaki uku, wallahi sai ta bar gidan Mukhtar ko da tsiya k0 da arziki, ai babu -laif1 don an gumawa mai gumawa, ke a gurin Allah ba mu da laifl hakan”.
Yadda take magana ka san har zuciyarta abin da ta ke nuf1 kenan.
F almata ta dafa kafadarta ta ce.
“Idan har zamu yi sanadiyyar da Fatila zata bar gidan malam mun zama daya fa kenan. Ina son ki yi hakUri kamar yadda na yi, kada mu yiwa Allah shisshigi, mu barta kawai idan mutum ya aikata mugun abu a gare ka kai kada ka biye masa. Idan ka biye masa duk kun sabawa Allah, ki ci gaba da taya ni da addu’ar neman zaBin Allah a rayuwata shi ne abin da nafi bukata, abu daya zan iya yarda yanzu a yiwa Mukhtar, a taimaka masa a karya duk sammun da aka yi masa, wanda kuma za a yi masa a gaba kada ya yi tasiri a kansa, domin ina tausayawa rayuwarsa yadda ake -wajiga rayuwarsa da yadda kullum yake cikin saBani da mahaiflyarsa., wannan kadai shi ne taimakon da zan iya yarda a yi masa, don haka babu laifl idan kin sanar da Baba wannan, duk da na san kin sanar da shi a baya, na kuma san dukufar da Baba da su Abba suke yi gurin yin addu’o’in ne ya sanya shi ya fara dawowa cikin hayyacinsa tunda ga shi har yaje ya gano yaransa, har da sai musu kaya. Yaushe rabon da ya kallonsu a matsayin ‘ya’yansa, k0 zai yi musu magana sai dai ‘yace ‘ya’yanki, bai taba danganta su da shi ba. balle ya ambaci su‘nansu. K0 hakan aka tsaya na godewa Allah matuka”.
Kusan wunin ranar akan maganar Malam suka yi shi, sai dai can’kasan .zuciyar Falmata farin ciki ne ya cikata, don da tana
tausayin yaranta yadda za su tashi mahaifinsu bai damu da su ba.
KANO
Duk wata dauriya da malam zai yi ya yi, amma daga karshe zuciyarsa ta gaza, tsananin son Falmata ya cika masa zuciya, har ta kai komai yakeyi ita yake gani, sai ya tsinci kansa da bai son kallon fuskar Fatila. Kansa yana suya a duk sanda yake tare da ita, har yana mamakin yadda aka yi ya aure ta a can baya. bai san abin da ya ja hankalinsa ga aureta ba, amma yana kokarin danne abin a ciikin’zuciyarsa.
da kyar ya iya yin kwanaki goma a Kano, ya fara shirin komawa Maiduguri a wannan karon ya ci burin sai ya ga Falmata, ko da ba zata kula shi ba, ganinta kadai zai iya faranta ranshi.
Sai ga shi yana ta siyowa yarama kaya, hankalin Fatila ya kara tashi matuka, ganin irin kayan da yake shigowa da su kwana biyu, duk da bai ambata mata ‘zai je Maiduguri ba ta san shirin da yake yi na taf’iyar ne, don haka ta sha jinin jikinta, domin ita yanzu abin ya fara ba ta tsoro, ta kula duk wani asiri da suka yi yanzu sam ba ya tasiri a kan malam din, sai abin ma ya zama kamar suna masa tiri ne, don haka take lallaBa shi ganin yadda yake bude mata wuta, amma ta sanar da Diyana komai.
Diyana tacw ta lallaBa shi da kissa ta sanya ya dauko yaran, domin su fara aiwatar da mugun nufinsu a kan yaran kamar yadda boka yace dole sai an rabo yaran da gidan kakansu Sannan aikinsu zai fara tasiri a kansa. A ‘cewarsa wai gidan Abba sammunsu sam ba ya aiki a gidan, don haka yau da daddare yana zaune yana kallo ta tunkare shi da maganar
Ta kalle shi da kissa, murya a sanyaye tace
“Hubby na kula da yadda kakc tsananin son yaranka, me zai hana ka kawo mana su nan kusa damu, inu ganin hakan zai sanya hankalinka yafi kwanciya”.
Ya d‘aga’kai ya dubeta tsawon lokdci, ya ce.
“Kin san Allah kamar kin shiga zuciyata kin ga abin dake cikinta. Tun shckaran jiya wannan tunanin ya darsu a raina, sai dai ina ganin kamar muhaiflyata. ba zata yarda. na dauko su ba”.
Jin ya ambaci sunan mahaifiyarsu taji kamar ya. caka’mata mashi a qahon zuciyarta, amma ta dake tana yake hakora tace
“Ai ba cewa zaka yi zaka dauko .suba kenan, dabara zaka yi mata kace zaka zo dasu ne su kwana biyu, ‘kaga idan ka samu ka taho da su idan aka ce ka maida su sai kace aisun dawo kenan, ina ganin idan kabi wannan hanyar zaifi maka sauqi ‘Ya‘ yanka sun dawo kusa da kai’saika basu duk tarbiyyar da kake
Hmm su fatila tanan aka bullu kenan lallai akwai aiki gaba😀