MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 32
MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 32
magana wai za kiyiwa Yakura aiki, wato ni na mutu kenan? T o wallahi sai dai a yi mutuwar kasko kowa ma ya rasa”.
Yakura ta mike a fusace tana nuna Zubaida da yatsa tana fadin.
“Wallahi ba ki isa ba, shegiya ‘yar bakin ciki, sai dai takaici ya kashe ki”.
Zubaida ta murguda baki tana yiwa Yakura kallon banza tace
“Banza a banza wallahi nafi karfinki ni, sai dai ki yiwa Falmatan, kek0 kunya ba kyaji, wai mijin kanwarki kike so don abin kunya…Kafin ta kai Karshen zancen nata Yakura ta wanka mata mari, ai kuwa ba ta yi sanyi gurin ramawa ba’ ita ma,Yakura ta rike kunci jikinta yana rawa tace.
Tabdijan, ni kika mara? Wallahi yau , sai jikinki ya gaya miki”.
Sai ta nufi Zubaida da duka, ai kuwa sai dambe ya’ sarke a tsakaninsu, Hajja Yakolo da ‘ Hajja Basma suka mike suka kama rabo. Da jyar suka raba fadan.
Hajja Yakolo ta kalli Zubaida tana huci tace
.“Shcgiya mai bakar zuciya, kina bakin cikin ‘yar uwarki ta sami abu har kin lf1 kaunar Falmata da ita, to wallahi sai dai ki mutu, aurenta da Muntari ba fashi, ke kuwa ki karata a haka, ba zani kuma kashe kwabona a kan wannan matsiyacin almajirin mijin naki ba, na gaji, shegiya mai Kashin tsiya tunda kika zo gidan nan duk wasu hanyoyin samuna suka toshe sai fatara da talauci ke damuna”.
Zubaida ta fashe da kuka tana fadin.
“Ai dama na jima da sanin tsoron Yakura kike yi Hajja, ni dai an cuce ni, an raba ni da gidan mijina anzo ana ci mini ‘ mutunci, wallahi sai Allah Ya saka min”.
Ta wuce dakinta tana kuka..
Hajja Yakolo ta bita da kallo a fusace tana fadin. ‘
. “Wato ni kike yiwa Allah Ya isa ke nan mara kunya fitsararr’iya, to idan kin isa ki koma gidan mijin naki shegiya, ai ga hanya nan waye ya hana ki?” ‘
Yakura tace, “Don Allah Hajja rabu da ita, mucii gaba da abin da zai fishe mu”
Hajia Basma tace “Da dai yafi don na kula kamar sammun su Iyami ya fara kama Zubaida ma mu kam munci dubu sai ceto wallahi .
Haka sukaci gaba da saka mugayen kudurorinsu na sharri ga bayin Allah.
Yagana kam tana isa gida jikinta har rawa yakeyi ta kirawo wayar Falmata. Tana dagawa ta kama dariya ta ce. Yammatan Maiduguri, yau an tuna damu kenan
Yagana tayi dariya 1ta ma tace
“Ai dolw na tuna daje Falmata, kin san kuwa Malam yana garin nan yazo biko’.’” Gaban Falmata ya yanke ya fadi,amma sai ta dake tace
“A banza wai talaka ya girmi Sarki, kin gaya masa nayi masa nisa dai yazu ko””
Yagana ta sake yib dariya tace“lye kawata yaushe kikayi baki haka.’ Lallai Ammi ta koya miki rashin kunya
itama Falmatan ta sake yin dariya tana kallon Ammi dake ta sabgar gabanta tace
“Wallahi babu ruwan Ammi, duniya ce dai ta koyar dani halinta, ke kina zaton zan yarda na Kara komawa gidan Malam ne Yagana? Ai sai yanzu nake godewa Abba da ya raba ni da kasarku mai cike da rudani da tashin hankali”.
Yagana tace “Au qasar mune mu kadai ke? To dadin abin dai k0 da zaki shckara dubu sai kin dawo garin dai”.
Suka yi dariya a tare. Yagana ta ci gaba da cewa. . . . ‘ “Don Allah ki sassautawa malam. wallahi baki ga yadda ya shiga damuwa ba‘ na san zai kira wayarki ma…”
Cabdijan, kika ba shi lambata? Wallahi koya kira bazan daga ba, kuma zan rama wallahi, ‘yar rainin wayo bayan kin ‘ tabbatar min ba zaki taba ba shi lambata ba shi ne yanzu kika ba shi‘.’”
Yagana tace wallahi k0 kece kika ga yanayin daya shiaga zaki ba shi, ai fadan masoya hutu ne na san zaki huce nema…”
F almata ta yi tsaki, tace
“Kin san Allah in dai zaki Kara bugo min waya akan maganar malam zan daina daukar kiranki. Ke yanZu ma sai an jima”.
Ta kashe wayar da sauri zuciyarta tana zafl.
Ammi dake kwance tana ta chatting da lsofu ta kalli Falmata tana dariya, tace
“Lallai kice mun kusa shan biki a Najeriya, ai da gaskiyar Yagana”. Tana magana tana dariya, ai kuwa ta wurga mata filo tana kuma cika tamkar har ance sai ta koma gidan Malam dinne yanzu.
Shi kam malam dakyar ya iya kai kansa masaukinsa, gaba d’aya hankalinsa ya tashi, don yana yanin kamar zai rasa Falmala ne har abada, sai yaji gaba daya garin Maiduguri yayi masa zafi tamkar babu AC a dakin da yake ya dinga kaiwa da komowa Cike da tsananin tashin hankali. can ya zari wayarsa ya fara Kokarin nemo layin Falmata. sai dai wani abu dabai sani ba tun bayan kammala wayarsu da Yagana tayi bidding din lambar Malam din gaba daya.
Don haka k0 da ya kira wayar tata sai akace anyi diverting din kiransa, hakan ya sanya ya‘ fuskanci boye lambarsa Falmata ta yi, hakan kuwa ya Kara daga masa hankali, tabbas yana cikin tsaka mai wuya, a daren nan dai da kyar ya samu ya runtsa, ai kuwa washegari da sassafe ya fara shirin barin garin Maiduguri, bai sake komawa gidan Abba ba, ya dai daure ya yi masa waya cewar ana nemansa a ofls da gaggawa, don haka zai wuce sai wani lokacin zai dawo.
Duk da son da yake yaga yaransa Bacin ran da yake ciki bai ba shi sukunin tunanin ya je gidan Abban ba, Allah ya sanya ma da safe da zaije ya tafar musu da duk siyayyar da ya yi musu.
K0 akan wannan tsarabar ma sai da abin ya zama rigima da tashin hankali gurin su Yakolo, domin yadda aka tsani kakarsu da babarsu haka su ma aka tsane su, don haka basu isa su flto harabar gidan wasa da kayan ba, sai an make su, k0 a lalata kayan. Hajja Iyami kam sai dai ta yi murmushi, tace, “Allah Ya shirya”. Kawai.
INA LABARIN FATILA MANYAN MATA?
Tun ranar da Malam ya tafl Maiduguri ta kulle kanta a daki ta yi ta kuka, wanda ya haddasa mata tsananin ciwon kai, abin kamar wasa sai ga ciwonkai ya kwantar da ita warwas, da kyar ta iya yiwa mahaiflyarta waya ta sanar da ita halin da ta ke ciki, hankalinta a tashe HajiyaKumatu ta iso gidan, yadda ta tadda Fatila hankalinta ya kuma tashi domin da kyar ta ke iya shakar numfashi, kirjinta sai sama da kasa yake yi, ba ta ma cikin hayyacinta sam, ga shi ita ba iya tuka mota tayi ba balleta tuka su su tafl asibitiba, dole sai fita ta yi a rude ta taro adaidaita sahu ta tallafo Fatila suka tafl asibiti, gwajin farko likita ya sanarda ita jinin Fatila ne ya hau matuka, don ba don tayi gaggawar kawota asibiti ba komai zan iya faruwa da ita, haka nan aka sanya mata Karin ruwa da allurai da za su sanyata dogon bacci.
Hajiya Kumatu ta shiga damuwa matuia ganin zata rasa diyarta akan wata bama can, domin bata raba d’aya biyu ta san taf’iyar Mukhtar Maiduguri ne ya haddasa wa Fatila wannan ciwon, kuma abin da ya kara kona mata rai tsawon wunin da suka yi a asibitin nan Mukhtar bai kira ya ji ya ya ta,ke ba, hakan ya Kara tabbatar wa Hajja Kumatu lallai ba ya yin ta diyar tata, ta kuma yi imani asirin aka yi masa a can Maiduguri a ganinta, hakan ya sanya hankalinta tashi, sam ba ta yi niyyar kiransa don ta yi fushi mai tsanani da shi, sai da Diyana tazo tace ai dole a kirawo shi k0 don ya dawo dole domin zaman nashi a can abin bakin ciki ne a ganinsu. Sai dai tun da safe suke neman wayar tashi ba su samu ba, saboda tunda ya dauko hanyar Kano ya kashe wayoyinsa gaba daya, saboda tafasar da zuciyarsa ke masa, don ma yana ta ambaton Sunan Allah a ransa
Sai dare ‘ya iso gidun, sai dai abin daya
ba shi mamaki bai wuce tadda gidan nashi a kulle ba, bai kawo komai a ransa ba illa kawai Fatila ta tafl yawo kawai, wannan ya sanya bakin cikin ya kuma Karuwa a ranshi, ya gama yanke hukunci da zai yankewa Fatila ya gwammace ya zauna shi kadai da wannan bajin cikin da Fatilan take cusa masa. Haka ya kwana a gidan shi kadai.
Da sassafe ya shirya ya fara nufar Babban gida bayan sun gaisa da Hajiyarsa ya kwantar da kai yace
“Hajiya ashe Falmata tana jami’ar Madina karatu tsawon lokaci amma baki taba gaya mini ba?”
Ta yi masa kallon banza tamkar ya sosa. mata inda yake mata kaikayi, tace
“Akan mezan sanar da kai? Aurenka ne a kanta ko kuma wani hadi ne tsakaninka da ita da dole sai an sanar da kai?”
Ya sunkuyar da kai sosai ganin ta dauki zafi, yace
Gani nayi kamar an yi gaggawar tafiyar tata, domin an san…”
Ya yi shiru ya kasa karasa fadar abin da yake shirin fada saboda hararar da take galla masa. Cikin hargowa ta ce.
“An san me? Kana nufin sai ta zauna zaman jiranka har sai randa ka gama wulakancin ka matarka ta ba ka izini sannan ka maidata k0? To tsaya ka ji na gaya maka a can baya naje na nemar maka auren Falmata, amma yanzu wallahi ko cikin sahun masu bada hakuri ba zan shiga ba. Kai tsaya ka ji ma addu’a nake mata kullum Allah Ya bata miji na gari da yafi ka, don ba zan yarda ta kara dawowa gidan ka ba har abada, domin ‘ duk wani abu da za a iya ambatonsa da wulakanci k0 cin zarafl ka yiwa Falmata, sai dai ka tafi wani gurin ka nemi aure kaji yadda kowa yake Ji gurin neman aure, domin wancan an yi maka a sama ne”.
Ta inda take shiga ba ta nan ta ke fita ba, har ya ji dama ya sani bai yi maganar ba, wannan shi ne azaba kan azaba, kunama kan gyambo. Shi a ganinsa ai tausaya masa ya dace a yi ba cin zarafi ba, ko don shi ba shi da bakin korafl, dame zai ji? Da bakin cikin da Fatila ke tusa masa k0 da wannan na Falmata da ake sanya shi?
can kasan’ ransa ji yake kamar zuciyarsa zata yi bindiga ta fashe, yana mamaki ina Fatila ta tafl ba ta Sanar da shi ba har ta kwana? Sai ya tsinci kansa da zarginta, wato idan ya bar gidan ya tafl wani guri zai kwana ita ma ficewarta ta keyi.
Ya jima cikin motarsa bayan ya fito ‘daga gidan nasu ya kasa tuka motar yana sakawa da kwancewa, can wayarshi ta fara Kara, ya daga ya ga kiran Fatila ne, don hak ya katse shi da sauri saboda babu wani abu da zata ce masa ya yarda. Sau uku tana kira yana katsewa, daga baya sai Diyana ta kira da ’ wayarta..
Ganin bakuwar lamba ya sanya shi dagawa, daga can Bangaren Diyana tace.
“Ni ce Mukhtar, dama na bugo na sanar ,da kai Fatila tana kwance a asibiti yau kwanaki biyu ke nan, muna ta neman wayarka bama samu ne”. Sai yaji hankalinsa ya tashi, yace
“Wanna asibitin kuke?”
Ta sanar da shi asibitin har da lambar dakin da suke. Ya kashe wayar ya yi shiru yana tunani, sai ya ji zuciyarsa tayi dar sanyi, abin da ya kudurce akan F atilan sai ya ji duk ya bar zuciyarsa. A hankali ya tuka motar ya nufi asibitin da Diyana ta sanar da shi. A can asibitin kam hankalin Hajiya Kumatu ya Kara tashi, ganin duk sanda F atila za ta farfado ba ta farkawa cikin hayyacinta, sai dai ta yi ta buge-buge da surutai tana ‘fadin
“Ina Mukhtar din yake? Ya tafl gurinta k0? Wallahi ba zan yarda ba sai na kasheta… Ke Falmata ki kyale mini mijina”.
Sai ta kama buge-buge, dole sai an kira likita .yayi mata allurai sannan zata koma ‘baccin. ‘
Mukhtar ya iso asibitin cikin ‘yan mintuna ya tadda Hajiya Kumatu da Diyana zaune a gurinta: Diyana ce ta yi masa bayanin abinda ya faru, ita kam Hajiya Kumatu ta cika ta batse tana ganin shi ne sanadiyyar jefa diyairta cikin wannan matsala’. Allah dai ya taimaka wannan karon ta farfado cikin ~hayyacinta, sai dai tana ganin Mukhtar ta fashe da kuka, tausayinta ya cika shi, ya matsa kusa da ita yana lallashinta har ya samu ta yi shiru.
Kusan tare da shi aka yi jinyar tata, wannan ya san faranta ranta, abin da ya bata mamaki kuma bai wuce ganin tunda ya dawo bai kara yi mata zancen Maiduguri ba, wannan ya sanya take tunanin k0 asirin da suka yi ne ya fara cinsa, ta kula ko maganar Maidugurin ma ba ya son a yi masa.
Kwanakinta hudu aka sallameta, jikin ya yi sauki matuka, sai dai an kafa mata dokoki da sharudda da dole sai ta bi su zata sami saukin ciwon nata.
Shi kam malam ciwon Fatila ne ya dan dakatar dashi, amma tunda aka sallamota ya koma ‘yar gidan jiya, idan ya je ofis dinsa yakan wuni tunanin mafita, daga karshe dai ya yanke shawarar siyan wani layin ya kirawo Falmata da shi, ita kam kamar ta san shi ne don haka in dai taga sabuwar lamba ba ta dagawa sam.
Tofa! Ciwon so ya kama malam, mafita kawai yake nema, daga karshe wani tunani ya fado masa, akwai wani lokaci da jami’ar da Falmata ke karatu suka nemi daukarsu aiki, bayan sun kammala karatunsu amma kishin Kasarsu ya sanya suka Ki amsar aikin sai yaga yanzu ba shi da mafita baya ga ya Kara neman aiki a makarantar, hakan ne kawai zai ba shi damar haduwa da Falmata yadda yake so, don haka a take a nan ya kunna na’ura. mai kwakwalwa (computer ya fara binciken jami’ar ta Madina.
MADINA .
Sun fara jarabawa wacce daga ita ne za su sami hutu, sai dai Falmata ba ta son komawa gida kwata-kwata, domin ta san tunda malam ya fara bibiyarta, tana komawa gida Malam zai iya matsa mata ta koma gidan Mukhtar din, abin data Ki tsana a rayuwarta kenan, domin yanzu karatu shi ne abin da tafi bukata. .
‘ Tana tsaka da wannan tunanin Allah Ya kaW‘o mata mafita, domin Isofu ya ce, Ammi ba zata koma gida ba, a nan zata zauna a Madina gidan Ambassador garinsu abokin Babanta, domin ya Ji rade-radin da ake yi, cewar mahaifiyarsa tace in dai ta dawo sai ta matsa masa’ ya saketa, domin ta gaji da auren ‘nasu, don tana ganin kamar an mallake mata danta ne, daman bata kaunar auren kwatakwata, wannan ya sanya yace ta yi zamanta a gidan. , .. . ‘ Ammi kam ta shiga damuwa bata san yadda zata zauna dasu ba domin ita din damisa ce qi Sabo, ta dinga rokon Falmata akan .su zauna tare a gidan.
Falmata ta ji dadin hakan kuwa, sanda suka yi waya da Abba ta sanar da shi mijin Ammi ya ce su zauna gidan tunda hutum ba mai tsawo ba ne, Abba yaJi dadin hakan, yace ta zauna din, shi ma idan ya sami lokaci zai kawo mata ziyara.
Don haka ana yin hutu suka tattara kayansu sai gidan Ambassador Jibrilu, ya amshe su da daraja,gidan nashi babban gida ne na gani na fada, sai dai basu da yawa a gidan, daga shi sai matarshi da ‘ya’yan samari guda biyu, hakan ya sanya kowanne yana da Bangarensa daban. Falmata da Ammi ma kowa daki guda aka ba shi, duk da sun so a hada su daki daya amma Falmata taKi yarda tace, idan Isofu yazo fa? Gwara ta ware dakinta daban ba za a yi rashin kunya a gabanta ba, don ta gaji da rashin kunyarsu, hakan ya sanya suka raba dakin.
Rayuwar gidan Ambassadem Jibrilu rayuwa ce ta ‘yanci da wayewa, tamkar suna kasar Faransa ne, ‘ya’yansa biyu ne Abdulkadir wanda suke kira da Kader sai kuma Abdul kareem wanda suke kira da Karim, mahaifansu suna bala’in sonsu, k0 don su kenan ‘suka haifa? Dukkaninsu sun kammala karatunsu na jami’a a can Kasar
Hmm wato so babu abinda bai saka mutum malam dai nason biyo falmata madina shin mai zai faru? 😀