MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 33

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 33
Faransa ne, don haka suje da wayewa da dabi’u irin na Faransawa, sai dai suna da ilimin addini dai-dai gwargwado, hakan ya sanya’ suka rage wasu abubuwa irin na fitsararrun turawan faransa. 
Zuwan Ammi da Falmata a gidan ya sanya Hajiya Khadija cikin farin ciki, domin ‘ya’yanta duk maza ne, gari yana wayewa suke ficewa gurin aiki suda mahaifinsu, yanzu kuwa ta sami masu tayata hira har da girki ma duk da tana da masu yi mata aiki, amma ita ke girkinta da kanta. Zuwansu ya sanya suka dauke mata komai. 
Daman dan zaman da Falmata ta yi da Ammi ya sanya ta fara sabawa da irin girkunansu masu dadi babu abin da ke mata dadi Sama da ordeuBre, yanayin girkin da al’adarsu tana burge ta. 
Sai dai wata al’ada da suke da ita wacce ta ke jin nauyinta ita ce, yadda ake haduwa gurin cin abinci da ‘ya’yan da mahaifansu da su, ita kam Ammi da yake ta saba sam ba ta damuwa, Falmata ce sai taji duk ta takura ta kasa sakewa, su kam ba sa kulawa da ita sai su yi ta cin abincinsu suna hira da shewa, wani abu dake Kara takura mata ma bai wuce yawan kallon da Kadir ke mata ba, sai ta ji kamar zata nutse a kasa, ta kula komai take yi sai Kadir ya sanya mata baki. 
Yau suna daki ita da Ammi suna hira, tana gyarawa Ammi gashi domin gobe Isofu yace zai zo, duk Ammi ta gigice Falmata tana ta gyaran gashin ta jiyo muryar Ammi tana fadin. 
“Falmata me kika fahimta game da Kadir ne?” 
Falmata ta hase rai,_tace
“Kamar yaya? Ni ban fahimci .komai ba, wani abu ne?” 
Ammi ta yi dariya ta ce. 
“Kin san Kadir abokin Isofu ne, tare suka tashi, wannan ya sanya ‘muka shaku. sosai da shi, har bai iya Boye mini damuwarsa tun muna kwanaki biyu ya dame ni da tambayarki, nace masa kina da aure bai yarda ba ya kira Isofu a waya ya tambaye shi, shi ne 
ya sanar da shi gaskiyar baki da aure. Tun daga wannan ranar ya matsa mini da zancenki, har mamansu ta san maganar fa”. 
Falmata ta saki kan Ammi da sauri ta dafe kirji tana fadin. . 
“Na shiga uku, kina nufin kowa a gidan nan ya san wannan maganar Ammi?” Ammi ta yi dariya ta ce. 
“To me ye? Ke kunyarki ta yi yawa, sai dai na sanar da Kadar gaskiyar labarinki, ina sonki da Mukhtar amma kuma ina tausayin yadda Kader ya mace a kanki, sai ki zaba ki darje”. 
Ta karasa maganar tana dariya. Falmata ta yi shiru cike da damuwa tace
“Wallahi za kisa na gudu daga gidan nan Ammi, ai kin f1 kowa sanin ba ni da lokacin soyayya yanzu, balle Kader hadadden saurayi me zai yi dani bazawara? Don Allah kice musu ina da aure 
‘ Ammi ta fashe da dariya, tana cewa “Wallahi baza, a shirya wannan karyar dani ba ki dai san yadda za kiyi da Kader kawai”. 
Falmata ta mike tana fadin “Sai ki nemi wanda zai karasa miki gyaran kan, ba dai ni ba wallahi”. 
 Ammi ta mike da sauri ta marairaice tana fadin. 
“Ki yiwa Allah kawata ki karasa mini, na tuba don Allah”. 
Falmata ta zabga wa Ammi harara tana zama a gefen gado duk ta damu Ammi ta fashe da dariya tace
‘ “Sai an yi magana ku ‘yan Najeriya kuce kunfi kowa wayewa, amma da saurayi yace yana sonku duk ku rude, wallahi mugayen Kauyawa ne ku”. T ana maganar cikin zolaya. Falmata ta dalla mata harara ta ce. 
“Za ki sami daidai ke a garin nan wata . rana, Allah dai ya kai ki garin, amma yadda kika kulla mini wannan tuggun wallahi ki warware shi tun muna shaida juna da arziRi”. 
Ammi kam dariyarta ta ke tiqawa, har da rike ciki. 
Da daddare kowa ya hallara a tebirin cin abinci babu Falmata, Mama ta kalli Ammi ta ce. Ya ya ban ga F 
almata ba?” Ammi ta ce.
“Wallahi Mamma na yi yin duniya ta flto wai ta koshi”. 
Kader ya mike da sauri yace
“Haba dai, me ta ci ta koshi, bari na je ‘ na flto da ita”. 
Kafin wani ya ce wani abu ya nufi hanyar dakin nata da sauri. 
Ammi ta bi shi da kallo tana runtse baki lallai yau Falmata zata nutse ke nan don kunya, Kader ya yi maganinta kenan. 
Ambassador  ya kalle shi har ya kule yana dariya ya ce. 
“Na ga alamar yaronki ya zama d‘an Amow’eud‘(dan soyayya)”. Hajiya Khadi tayi dariya tace, “Yau ne ka fara ganewa ke nan charic (abin sona)”. 
Suka fashe da dariya gaba dayansu. Karim yace
Baba yaronka bai iya soyayya ba, kace ya biyani na koya masa yadda ake amour (so)”. 
Suka kuma Kwacewa da dariya, Ammi ‘tace, “Kuma na gaya maka Karim yadda yake dan kauye haka nan Falmata take ‘yar Kauye f1tik, har ma ya fita wayewa…” 
Ambassador  yace “Shi ke nan an yi daidai, amma zan so ganin hirarsu. Kowa dan kauye ke nan” 
Haka nan suka dinga hira tamkar kawaye. Falmata tana zaune a gefen gado tana . kallo, ta ji an turo Kofa da sallama. Kafin a yi sallamar ta yi zaton Ammi ce sai dai jin sallamar ta gane Kader ne, nan da nan ta wawuro gyaleda kekan gadon ta yafa a jikinta, tana amsa sallamar. 
Kadir ya shigo ya tsaya a kanta ya zuba hannuwa cikin aljihu yana kallonta, gaba daya sai ta dururuce gabanta ya hau fad‘uwa ta kasa daga kai ta kalle shi. Ya kula da halin da ta shiga, ya yi 
murmushi, abin dake burge shi da Falmata ke nan, tamkar ba ‘yar jami’a ba, tana da kunya ainun, halayensu sun sha bamban da na Ammi gurin kunya da kawaici, wannan ne ya ja hankalinshi da zuciyarshi ga tsananin sonta. 
Yayi gyaran murya yace, “Amma dai na san da wasa kike yi Bintu da kika ce kin koshi k0?” Sabon sunan da ya rada mata ya sanya ta daga kai da sauri ta dube shi, domin mutum daya ke gaya mata Bintu, ita ,ce kakarta da ta mutu, wacce aka sanya mata sunanta, wacce ita din Binta din ake ce mata. 
Amma ganin irin kallon da yake mata ~ ya sanya ta yi saurin dauke kanta da sauri, gabanta yana ci gaba da faduwa. . 
Ya yi murmushi yaci gaba da fadin, “Na kula tun tini ba kya son kallona, ko da mun hada ido da’ ke sai ki yi saurin dauke kanki Bintu, ni kuma na kan ji dad‘l a duk sanda na’ kalleki, yau dai dauriyata ta iare gani nazi da kaina, ina sonki da yawa Bintu”. 
Shi ke nan ta faru ta kare an yiwa mai dami daya sata, abin da take gudun kada ya fada ya fada din, amma ai tana da sauran abin cewa, ba ta kalle shi ba ta ce. “Amma Ammi ta Boye maka wani abu da ba ta sanar da kai ba. Ni fa ba budurwa ba ce, ina da yara biyu, sannan kuma mijina…” Mijinki me?” Ya katse ta da sauri, ya dora da cewa. Ba kiyi kama da wacce za ta yi min karya ba, Ammi ta sanar da ni komai, ta gaya . mini kina da Abba da Muhammad, anma baki da miji, ki taimaka Falmata, wallahi ban taba jin son wata mace a raina ba saike, ki dube ni da girmana ba yaro bane ni, shekaruna talatin da biyar, mamma ta damu nayi aure, amma rashin ganin wacce nake so ya sanya na kasa cika mata burinta, amma da na ganki na sanar mata ta yi murba sosai”. Ya daure ta da jijiyar jikinta, ta ma rasa me zatace masa, ganin ba ta da niyyar magana tsawon lokaci ya sanya yace
“ida kin yarda da abin dana fada sai ki taso muje ki ci abinci k0?” Cikin siririyar murya tace “Ni fa na koshi da gaske” . 
Ya yi dariya yacw “Na ga dai alamar kunyar Mamma da Baba kike ji, bari na dauko nawa da naki nazo  muci, amma don Allah ki saki jiki dani Falmata muyi hirar soyayya, domin ban taba  aoba sai a kanki”. 
Kafin tace wani abu ya juya da saun’ ya fice dauko-abincin, ta bi shi da kallo cike da tsananin mamaki, shi babu ruwansa baya jin kunyar iyayensa, yanzu sai yace musu tare za suci abincin. 
Yana fita ya fara tarkato abincin yana hadawa guri guda, iyayen nasa da Ammi da kanin nasa suka bi shi da kallo, ya daga kai ya kalle su yana murmushi yacw
“Ku taya ni muna na fara samun shiga, amma kunyarku ta ke ji, gwara na kai mata abincin a can, kun san ita malama ce fa”. 
Ambassador  ya yi .. murmushi yana fadin, “Ai na ga alama, amma dai ka bita a cab kada ka bata kunya faYa yi dariya yana wucewa da abincin tare da cewa. 
“Kai dai Baba ka taya ni addu’a kawai, idan na fito za ka sha labari”. Suka Kara fashewa sa dariya, suna tsokanarsa har ya wuce ciki. 
Falmata kam ta cika da mamakin wannan dabi’a tasu tamkar turawa ba sa jin kunya sam, sai ga shi ya shigo tsulum sai dai duk yadda ya yi zaton-Falmata ta wuce nan, domin ya yi juyin duniyar nan ta Ki cin abincin har idonsa ya cika da Kwalla don magiya, daga karshe tace masa, sai dai idan ya tafi zata ci. Ya marairaice yana cewa, “Kin yi alkawari za kici k0?” 
Ta daga masa kai alamar eh zata-ci, sannan ya fice ya barta. Yana f1ta ta janyo abincin ta fara ci, daman tana jin yunwar ya leko ta taga ya ga tana ci sai ya ji ransa ya yi sanyi, ya yarda samin mace mai kunya irin ta Falmata za a jima tabbas. 
                 ****
Duk wata hanya da Kader zai kafa kansa a zuciyar Falmata sai da ya bi, tun tana jin kunyarsa da kamewa har ya samu shiga, domin shi din mutum ne mai iya barkwanci 
~ sosai, sai ya zama abokin debe mata kewa“ musamman da Isofu yazo garin ya dauke Ammi suka tafl Jamus ta yi masa rakiya wani aiki da zai tafl, sai Kader ya zama shi ne dai abokin hirarta, duk inda zata suna tare, iyayen kam sun yi murna matuka da wannan soyayyar tasu, domin sun yaba da hankali da 
. tarbiyyar Falmata, ba su damu da wai tana bazawara ba, wannan abin ke burgeta mutane wayayyu da ba su da duhun kai, ga ilimin bokO da na addini. ‘ 
Malam kam yana cikin tsananin damuwa da tashin hankali, ya dinga  sintiri ‘ a Maiduguri, wai k0 zai samu Abba ya yi masa maganar Falmata amma abin dake ba shi tsoro ko zancen Falmata ya fara sai yaga Abba ya wayance ya sanya wata hirar, wannan abin kw karya masa gwiwa, ga shi ya yi applying din da yayi har yanzu ba a bashi amsar komai ba. Rannan kamar da wasa yaje Maiduguri suna hira da Abba ya sanar da shi aikin da yake nema a jami’ar Madina sai Abban .yace ya turo masa da takardunsa ta email dinsa zai tuntuBi abokinsa Sheik Uzair Ibn Abdallah, domin yana cikin iyayen makarantar, kwanaki kuma ya ji suna cigiyar malamai. Da haka suka rabu ya tsananta addu’a, Allah Ya sanya ya dace. 
Kwatsam Falmata suna daki ita da Ammi ‘suna ta hirar Isofu, lokacin kwanansa guda da komowa’bayan sun dawo daga tafiyar da suka yi, wayar Abba ta shigo yana sanar da ita ya iso garin Madina. Ta ba shi kwatancen’ inda suke  dadi da murna suka cika ta mike ta doka tsalle tana fadin 
“Ammi Abbana ne yazo, yana cikin garin nan, wai mu sanar da shi inda muke, muje don Allah gurin Baba mu sanar da shi” .
Ambassador  da Mamma suna hira a falo, Ammi da Falmata suka iso. Ammi ce ta Sanar dasu zancen Abban, Ambassador  ya amshi lambur Abban a gurin Falmata yace zai sanya Kader ya dauko shi yanzu k0 Karim. 
Ana tsaka da maganar sai ga Kader din ya shigo gidan, Abmbasada yace“Yauwa amshi wannan lambar Abban Falmata ne ya iso, kaje masaukinsa ka taho da shi yanzu”. 
Dadi ya cika Kader ya amshi lambar ya fice yana fadin, “Sai na riga kowa ganinsa”. Ya fice suna masa dariya, Falmata kam baki yaKi rufuwa, kamar mai tallan makilin. 
Abin mamaki, sanda Abba ya iso sai suka ji ya ambaci sunan Ambassador  yana fadin
“Alhaji Jibirilu daman gurinka su Falmata suke?” 
Nan fa hirer yaushe gamo ta Barke ashe sun san juna sai da aka gaggaisa sannan Ambnasada ya kalli Falmata ya ce. 
“Ai malam malamina ne tsawon lokaci, tun daga can Kasarmu nake zuwa gurinsa idan ina da bukata, wani yayana ya hadani da shi, abubuwa ne suka yi yawa na kwana biyu ban je ba, tunda na zama Ambassador  a kasar faransa daga can kuma nayo nan, ashe ke din diyata ce shi ya sanya tunda na ganki na yaba da hankalinki”. Falmata ta sunkuyar da kai cike da 
tsananin kunya, tana dariya Kader kam dadi ne ya cika shi don yana ganin kaya ne suka tsinke a gindin kaba. 
Ambassador  yaso Abba ya zauna a gidansa, sai Abban ya ce ai yazo ziyartar kabarin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallamma ne da wani aiki, don haka zaifi bukatar ya zauna kusa da masallacin domin akwai wasu addu’o’i da zai yi, wannan ya sanya dole Ambassador  din ya hakura. 
Kwanakinsa goma sha shida a garin ya yi musu sallama, daga Karshe ma Abba yace su yi zamansu a gidan Ambassador  din ba sai sun koma dakunan makaranta ba hankalinsa zaifi kwanciya idan a nan din suke, duk da Falmata ba ta so hakan ba, domin tana ganin kamar Kader zai sami damar da zai ci gaba da takura mata ita da take murna sun kusa komawa hutu ta koma 
makaranta ta huta, amma ya ya ta iya ba zata ja da hukuncin Abba ba. Shi kam Kader sai ya ji kamar an yi masa gafara, daman da Abba yazo ya dinga shige masa sai dai sam Abban bai kawo komai a ransa ba. . Abin da ya bai wa Falmata mamaki bai wuce jin Abba har ya koma bai yi mata maganar Mukhtar ba, wannan abin ya ba ta mamaki kwarai da gaske, ta san yadda Abba yake ji da malarn amma ya gaza yi mata maganarsa, k0 zancensa ta kula Abba ba ya son su yi hakan sai ya jefata cikin tsananin tunani. ‘ 
Abba ya kira malam a waya bayan ya koma ashe takanas abin da ya kawo shi garin Madina ke nan, bayan ya yi ziyara a kabarin Manzon Allah ya tafl gurin abokinsa Sheik Uzair Ibn Abdallah, sheik din yace, ai tuni ya tura masa da sakamako, yanzu abin da ya rage ya turo yaron nasa a yi masa jarabawar gwaji, idan ya cancama shi kenan, don haka Abba Yana komawa ya sanar da malam din 
Cikin zumudi malam ya fara neman bisa, Allah Ya taimake shi bai sha wahala ba ya samu. 
Ya isa garin madina da d’oki,‘kwanaki biyu ne zai yi a garin ranar da aka sanya ta ganawar tasu ta cika, don haka a masallacin manzon Allah ya ke wuni addu’a yana kuka da rokon Allah Ya sanya ya dace. 
Cikin ikon Allah ya yi sa’a kuwa yana cikin wadanda aka zaba, domin bayan ya yi jarabawar gwajin ya yi ta baza kunne bayan ya dawo watanni uku kuwa sake yi masa sako ta email dinsa, yana cikin wadanda aka dauka aiki. , 
Ya fara shirin taflya Madina cike da murna da farin ciki, Fatila tafi kowa murba domin a ganinta mijinta zai yi nisa da Falmata idan suka tafl sai ta Allah za su dawo, sai dai tsiyar da ya yi mata ya ce ba tare .da ita zai yi taf1yar ba, sai yaje yaga yanayin zaman nasa zai dawo ya koma da ita. 
Abbagana da hajiya Mariya kam sun gama gano malam din, yana ta wannan yakin 
Hmmm za,ayita fa ga mukhtar ga khader
Su fatila kuma murna ta koma ciki wa kuke supporting ne nidai ina team mukhtar😝😝😝muje zuwa

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE