MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 34

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 34
ne domin ya sami damar had’uwa da Fahnata, haka ya tattara ya bar Najeriya Fatila tana cike da baqin ciki
Bayan ya isa jami’ar sai ya yi rashin sa’a Bangaren da aka kai shi ba Bangaren su Falmata bane, ga makarantar da girma ta ina zai samo Falmata bai sani ba, amma da yake kusan abin da ya kai shike nan sai ya shiga binciken Bangaren da Falmata ta ke, har ya yi sa’a‘ya samo inda ta ke. Daga nan ya fara neman ta yadda zai’samu ya zama saya daga cikin masu daukarsu darasi,‘ abin nashi kamar mai tafe da wani sihiri sai ga shi yana daga cikin‘wadanda za su dinga koyar da su karatu, sanda suka shiga aji na, biyu. Wannan labarin yafi komai yi masa dadi, tun bayan zuwanshi jami’ar tsawon watanni takwas. 
” Ranar da ya fara shiga ajin nasu abin tsoro ya bai wa Falmata matuka, Allah ya ‘ sanya akwai nikaf a fuskarta, tafseer ya fara yi musu wanda hakan ya nuna mata shi ne abin da zai koyar da su, sai ta dinga ganin abin kamar a mafarki, sai da ta mintsili jikinta ta tabbatar ba bacci ta ke yi ba, Mukhtar ne dai ya zama malaminsu a Islamic University  of Madina, duk karatun da yakeyi ba ta fahimtqr komai. 
Shi kam malarn tun bayan daya gabatar da kansa ga daliban nasa, ya fara gabatar da darasin da zai dauke su, sai dai rabin hankalinsa yana kan daliban yana son ya gano Falmata domin yawancin daliban suna sanye da nikaf ne. Can ya hango Falmata zaune kusa da Ammi da kwayar idonta ya ganeta, abin da ya bata tsoro ganin yadda ya tsareta da ido, ya sanya ta gane ya gano ta, gaba daya sai ta dururu ce, farkon haduwarsu ya fado mata a indo stadiyum ta Kano. 
Bai ankara ba har lokacinsa ya cika, sai ya ji kamar kada ya fita, bai san dalilin da ya sanya yake son falmata irin haka har ba ya iya rike kanshi ba. 
K0 da suka koma gida bayan an tashi daga makarantar, Ammi ta dami Falmata da labarin sabon shehinsu na Tafseer, ita kam Falmata bata ce komai ba sai dai um kawai take cewa, sai ta ji gwara ta yarda da batun Kader k0 ta huta da maganar Malam, domin daga yanayin kallon da yake mata tasan komai zai iya faruwa, kuma Yagana tana sanar da ita komai a waya, na game da yadda yake sintiri a Maiduguri. 
Tsawon lokaci Malam yana neman hanyar da zai samu ya kula Falmata, amma ya rasa domin ya gano ba a cikin dakin kwanan dalibai dake makarantar take zaune ba, ko da a ciki take ba sai da halin shiga ba, bai kuma san lokacin da suke taf’iya ba, don bai san adadin darasin da suke yi a kowacce rana ba. Abin yana damunsa, hakan ya sanya ya yanke shawarar daukar wani mataki yau, don haka tun bayan da ya kammala darasinsa, ya sami guri ya zauna yana jiransu. Darasi daya suka yi bayan nasa suka tashi, akwai direba da Ambassador  ya ajiye saboda daukarsu da kawo su kawai, mutumin kasar Najcriya ne, da suka tafl can zaman shahada. Sun nufl motar suna hira, Falmata taji ana kiranta daga baya, sarai ta gane muryar malam ce, amma sai ta kara sauri’ tana rike hannun Ammi, yayin da Ammin ta waiga tana fadin, “Ke kiranki ake yi, kuma malamin tafsirinmu ne, a ina ya samo sunanki har ya san ki haka?” Falmata ta ce, “Oho, ni ban yarda da shi ba, kallon da yake mini dama ya ishe ni, don Allah zo mu wuce”.
Ta Kara flzgar hannun Ammi. Sai dai Ammi ta dage ta ce, “Gaskiya bai dace mu yi haka ba, mun hada ido da shi kuma bai kamata ace malaminmu yana kiranmu mu qi tsayawa ba, hakan bai dace da dalibai masu neman albarka ba”. 
Falmata ba ta tsaya cewa wani abu ba, don tana gudun kada ya tadda su ta wuce da saurinta ta bar Ammi a gurin. Da sauri Mukhtar ya karaso ya kalli Ammi yana mata larabci don ya yi zaton balarabiya ce, amma sai ya ji ta amsa da hausa, mamaki ya cika shi, yace“Kice ‘y’ar uwata ce ‘yar Najcriya har nake miki Larabci?” 
Ammi ta yi murmushi ta cikin nikaf dinta tace “Eh to ‘yar uwa ce amma ‘yar Nijar ce ni malam, ya ya aiki? Na ji kamar kana ambatar sunan kawata ne”. 
Ya yi murmushi ya gyara tsayuwa yace “Don Allah kawarki ba ta sanar dake komai a kaina ba, na san tun ranar dana fara daukarku darasi ta gane ni”. Ammi ta cika da mamakin jin abin da ya fada, ta ce. Ba ta sanar dani komai a kanka ba, ina jin ba ta sanka ba, k0 kuma ba ta gane ka ba, da tana da wani labari a kanka da nice wacce ya dace ta fara sanarwa malam”. 
Ya yi yake ya ce, “Ta sanni taqi sanar dake komai daya shafe nine don tana jin haushina, k0. Falmata ta makance ba zata manta da muryata ba, amma bari na tambaye ki, bata taBa ba ki labarin Muhammad Mukhtar Mai darasu ba don Allah, koda kuwa agun labari ne?” Ammi ta sake cika da tsananin mamaki. ta dube shi da kyau, tace. Kada kace mini malam kai ne tsohon. mijin Falmata baban Abba da Muhammad?” Ya yi murmushi cike da jin dadi yace“Ni ne, na san watarana ta taba ba ki labarina, ni mai laifl ne gurin falmata, amma na san halinta tana da hakuri da yaflya zata yafe mini, ba zan Boye miki komai ba na nemi aiki a garin nan saboda Falmata ne, ki taimaka ki sanar dani inda kuke baiwar Allah don Allah”. Ammi tayi murmushi tace, “Ka yi hakuri malam, wallahi ban san yadda zan kwatanta maka inda muke ba, da yake mu‘ baqi ne, amma na yi maka alkawarin tambayar ‘yan gari, sannan sunana Ammi tare muke da Falmata tsawon lokacin da ta kwashe a garm nan, muna zaune a gidan, Ambassador  na Nijar ne, wanda ya kasance’ dalibi ne ga Abba ma”. 
Mukhtar yace, “Naji dadin wannan bayanin naki, da na taho da abin hawana dana bi ku a baya, amma babu komai zan jiraki, 
na gode Ammi”. 
Haka suka rabu da Ammi ta nufl gurin motarsu ya yi tsaye yana hango Falmata can cikin mota a zaune tana kallonsu, mamaki ya cika shi’ wai yau shi Falmata take gudu, har sai da ya ga motarsu ta tashi sannan ya sami damar juyawa. Ransa ya cika da farin ciki, yau ya sami wani abu da ya shafl Falmatansa. 
A cikin mota kam fada aka kama yi da Falmata da Ammi, yayin da Ammi ke ta yi mata dariya tana fadin, “Lallai yarinya kya Ki kula kowa, ashe haka malam din naki yake mutum mai ilimi irin wannan dole ya siye zuciyar ‘yar yarinyar nan mai zurfin ciki”. 
Falmata kam sai ta kuma Kuluwa. kamar zata nutse a Kasa, ta rasa me ya sanya Ammi take mata haka, ta maidata tamkar kakarta gurin tsokanaeta. 
Lokacin zangon karatu ya kare, Falmata kam wannan hutu a gida zata yi shi, domin yazo daidai da lokacin bikin Yagana da angonta Auwal, malami ne a jami’ar Maiduguri, Allah Ya hada su yana matukar son Yagana, yana da mata da yara biyu farfesa ne. Da farko Yagana tana tsoron aurensa saboda ganin abin da ya sami kawarta, amma dai daga baya ta dake ta bar wa Allah komai, don tana tsananin son Farfesa Auwal. ~ Kwatsam su Falmata suna zaune a falo suna hira Ambassador  ya aiko wai Falmata ta je yana son ganinta, dama Mamma tace musu yana da bako da Abba ya turo daga Najeriya, k0 kusa Falmata ba ta yi zaton Malam ba ne, tafi sanya rai da daya daga 
cikin yayyanta ne Abba ya turo su ganta, don haka k0 da. aka aiko kiranta da doki ta tafl. Sai dai .abin da ya ba ta tsoro bayan ta isa bai wuce ganin malam ba, jikinta ya yi sanyi kalau, ita ba abin ta koma’ ba. Ambassador  ya mike yana fadin
“Ashe kina da yaya a makarantar taku ba ku sani ba, sai da Abba ya turo shi sannan ya san acan kuke karatu, ga shi nan ku gaisa ya baki sakon Abban”. Ya wuce ya nufi Kofa. 
Falmata kam ji ta yi kamar ta nutse don bakin ciki, ko ta yi layar Bata ya daina ganinta tace don Allah ka yi hakari ka rabu da rayuwata na yi kokarin mantawa da kai, da duk wani abu da ya shafe ka, kada ka zama azzalumi ka sanya ni a uku ba don Allah”.  Idonta ya ciko da kwalla muryarta ta .kama rawa kamar zata kurma ihu. 
Jikinsa ya yi sanyi sosai, hankalinsa kuma ya tashi yau shi falmata ke ambata da tashin hankali, lallai yasan ya Batawa Falmata rai matuka, tunda har ta yi fushi da shi haka. Hankalinsa .ya Kara tashi, yau Falmata k0 gaishe shi ta qiyi, cikin sanyin murya ya ce.
“Falmata idan ban sami komai daga gare ki ba, ki daure ko gaishe ni kiyi don Allah”.” . Maimakon ta yi abin da ya ce din, sai ta fashe da kuka, don ganin Malam yana tuna mata abubuwa da dama, yana kuma tsoratar da .ita abubuwa masu yawa, cikin shesshekar kuka ta fara magana. “Nayi ~ nisa da kai da rayuwarka Mukhtar, domin na sami sauyi da ‘yanci a rayuwata, meya sanya ka biyo ni? Don Allah ka Kyale ni ka sanar da kanka gaskiya, zamanmu tare da ba komai bane illa hanyar cutar da ni, hakKina da ka dauka na baya bai wadatar da kai ba sai ka kuma cutar dani… don Allah ka barni Mukhtar… Ka bar ni!” 
Jikinsa ya dauki rawa, zuciyarsa ta dinga tafasa lallai ya yarda zuciyar Falmata ta kekashe ba ya ga sunansa da take ambata yau karara har kuma da Kokarin maganganu ta ke gaya masa masu zafi, tabbas ba shi da sauran kalamai ko hanyar da zai iya lallashinta, shin ya ya zai yi? 
Kafin ya kai ga tunanin mafita, ta mike da sauri tana goge idonta. Ya mike a fusace yana Kwala mata kira, amma k0 waige ba ta yi ba, ta shige ciki da sauri, ya yarfe hannaye cike da damuwa, tabbas yana da sauran aiki a gabansa ke nan, Falmata ke gudunsa haka? Ya jima tsaye yana kallon kofar yana ganin kamar zata dawo, har ya yanke ya nufl Kofar fita a .can harabar gidan ya tadda Ambassador  zaune a kan’kujera yana karatun jarida, suka yi sallama ya wuce. 
Duk yadda Malam ya dauki abin ya wuce tunaninsa, domin falmata taqi ba shi fuska kwatakwata, daga makaranta har gidan ko’ ina babu dadi. 
Sai wani abu da ya gano ya kuma sosa masa rai, soyayyar dake tsakanin Kader da Falmata, yawan zuwa gidan da yake yi ya sanya shi ma ya zama dan gida, musamman da yake jininsu ya hadu da Karim, yana zuwa can masaukinsa daukar darasi, Kader ne dai . sai gaisuwa sama-sama domin kowa ya gano dayan yana son Falmata, sai daga baya Ammi ke sanar da Kader ai mijin Falmata ne na baya Mukhtar din, duk da yaji gabansa ya fadi, amma bai tsorata ba, don yace yanzu Falmata ta zama allura cikin ruwa mai rabo zai dauka. 
A haka aka yi hutu, Falmata ta fara shirin tafiya Kano, a sannan ne hankalin Kadcr ya tashi, domin yana ganin kamar idan ta 1afi shi kenan ya rasata, domin ya kula da yadda Malam ke neman yi masa ci da karfi, amma shima ya kudurci binta Kanon a yi 
Duk wacce za a yi. Bai taBa zuwa Najeriya ba, amma saboda Falmata ya shirya zuwa k0da Birnin Sin ne. 
Tare. da Ammi suke yin shiri, domin Ammi ta ce da ita za a yi bikin Yagana, ko da wasa ba ta sanar da malam tafiyar tasu ba, sai da suka tafl yazo gidan Mamma ta sanar da shi ai sun tafl. 
Ya yi mamaki matuka, amma ya ya ya iya, dole ya bi su can. 
Kader kam yana ta fafutukar yadda za a yi ya sami hutu yabi Falmata Najeriya. 
*** *** 
Sanda Falmata ta isa gida mahaifiyarta ta cika da mumar ganin yadda diyar tata ta zama, su Hajja Yakolo kuwa kamar su ce ina wuta su jefa Falmata, Yakura tafi kowa tashin hankali da shiga damuwa, a zuciyarta tana ta addu’a Allah Ya sanya ba zasu taBa had’uwa da Mukhtar ba, ka ji hauka da son zuciya, zuwan Falmata dai ya Kara tadawa ‘yan gidan hankali, domin Falmata ta yi kyau har ta gaji, komai nata ya koma irin na Larabawa, daga shigarta har bakinta ta riga ta saba da Larabci, sai ta zama kamar wata bakuwar Jakara. 
Zuciyarsu ta kitsa musu komai, -don haka sun Kulle kansu da muguwar shawararsu. 
Kwanakin su Falmata biyar Malam ya iso garin, kwanansa daya kacal a Kano ya yo hanyar Maiduguri, don yace da zafl-zafi akan doki karfe, ba ya samun ganin Falmata ‘saboda sabgar biki da suke yi, kullum suna tafe siyayya, amma haka yake ta naci, Falmata kam tana ba shi wahala yadda ta so, shi kuma ya jure. 
Kwatsam sai ga Kader ya iso garin, hankalin Falmara ya tashi .matuka, ta dinga fadin, ta shiga uku. Kader kam bafaranshe ne bai Boye komai da ke tsakaninsa da Falmata har a gurin Abbagana kuwa kai tsaye yake shiga d‘akin Hajja Iyami ya zauna yayi ta surutu, ita dai sai dai ta dinga cewa uhm, sai Amina kanwar Falmata dake hutu yanzu a gida ke biye masa, domin bana tayi candy da yake makarantar kwana ta ke yi. An yi bikin Yagana cikin ‘kwanciyar hankali da farin ciki, daman suna da komai na .. kayan daki da Abba ya ba su na Falmata, har kuma lokacin ba a daina yayinsu ba, da yake kaya ne masu tsadar gaske, don haka da su aka kai ta, sai sauran siyayyar da aka yi mata. 
Abba ya yi musu halacci da Falmata babbar kawa, Yagana da mahaifanta har sai ‘ da suka yi kukan dadi, domin babu wanda zai ce Yagana ba diyar wani ba ce, saboda yadda aka shirya mata gidanta, da yake ba tare suke da kishiyarta ba. 
Su Hajja Yakolo an kuma bazama neman asiri, domin zuwan Kader ya Kara daga musu hankali,~suna ganin k0 sun raba Falmata da malam ga wani ma, sun je wani surKuKun kauye can. gurin wasu arnan kan dutse an ba su wani tsafl da za su binne. An tabbatar musu in dai har suka binne shi shi ke nan har abada Falmata ba zata kara lafiya,ba haka za tayi ta fama da jinya har ta mutu Sun dawo gida cike da tsananin murnar cikar burinsu, don suna ganin da sun yi wannan aikin sun huta, idan shi Malam ya ga Falmata ta sami ciwo zai iya yarda Yakura ta auri Mukhtar din za kuma su yi masa dabara da cewar zata aure shi ne don ta rike ‘ya’yan ‘yar uwarta, idan ya so bayan Yakuran ta shiga sai su yi jojarin fidda kishiyar tata, wannan shirin da suka shirya tamkar suke da rayuwar. 
Ita Falmata abin duniya yabi ya ishe ta, domin har ta fara tunanin da zarar an kare bikin za su koma, gwara su karasa hutun can gidan Ambassador , Kader ke ba ta kunya k0 tana gaban waye bai jin kunyar binta duk inda take yana biye da ita, wannan abin ke
Dagawa. Malam hankali har ya fara sarewa. 
dan yana ganin kamar yanzu Falmata tafi son Kader din fiye da shi. domin lokuta da dama zai tadda su suna hira da dariya, wani abu da bai sani ba shi Kadcr sarkin barkwanci ne, shi kuma taki yarda su kebe ma sai gudunsa da take yi, duk wata hanya da yasan zai ba ta 
Hmmm bari mu dakata anan naga alamun khader nason kada mukhtar da ga kuma su hajiya yakolo anje an samo asirin da za,a jwantar da falmata ciwo harta mutu
Shin me zai faru🤓🤓🤓 muje dai zuwa

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE