MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 35

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 35
haKuri ya kuma lallasheta yabi, amma duk a banza, amma dai bai yi fushi ba, don ance mai hakuri yana tare da samu. 
Abba yana cikin falo a zaune shi da Hajja Kaltum dake dama masa fura, tana tsokanarshi. 
“Abba shan furar nan taka ya yi yawa, anya ba fulani ne suka sanya maka hannu ba?” 
Ya yi dariya yana fadin, .“Ni ma dai hakan nake zato Kaltume, don ina mamakin yadda bana iya yin bacci idan ban shata ba”. 
Suka yi dariya a tare. 
Hajja Kaltum ta dan nutsu ta ce, “Abba anya haka za muyi ta zama a gidan nan dasu Yakolo, kullum ana girma ana kara cin kasa, ba ga rashin tarbiyyar yaran diyanta, sun raina kowa a gidan nan, jiya fa yarinyar nan Falmata suna ta shirya ‘yan mata cikin mota za a tafi kai Yagana kawai Yakura tahe tana bala’i, wai ta ajiye kudinta a dakinta an sace mata, kuma taga Falmata ta shiga gidan da ‘yan mata don haka bata raba daya biyu sune don haka dole a fito mata da kudinta. 
Duk hakuri irin na Falmata sai da ta biye mata suka fara sa’in’sa don kasan sharrin sata ba Karamin abu ba ne , Allah Ya sanya Yayansu yazo gidan sai shi ya fita rabon fadan da Amina ta sanar da shi, Falmata ta sha kuka saboda kazafin da kunyatar da ita Yakura da ta yi, abib nasu kullum sai karuwa yakeyi maimakon ya ragu”. 
Abbagana ya yi shiru cike da damuwa, yace “tabbas kowanne bawa da irin jarabawar da Allah yake masa, hajjia Yakolo da ‘ya’yanta sune jarabawata, Allah Ya bani ikon hayewa, amma dole zan dauki mataki a kansu, don na kula abin nasu kullum karuwa yake yi…” . 
Sallamar Zubaida ce ta katse musu hirar tasu, suka amsa a tare. Zubaida ta shiga ta sami guri ta zauna ta sunkuyar da kanta kasa ganin kallon da Abba yake mata, tamkar kallon tsana. 
. Cikin tsawa yace, “Yaya aka yi kikazO klka sanya mu a gaba, iye?” Bakinta yana rawa ta mika masa wani abu kulle cikin leda tace“Daman su Hajja naji suna maganar za . su binne wannan abin da suka amso gurin malamansu wai don Falmata ta yi, ta ciwo sai Yakura ta auri Muntari…” Abba ya gyara zama a flrgice yana fadin, “Subhanallahi me kika ce Zubaida? Me ye wannan din?” Ya janyo ledaI da sauri ya fara budewa, wani irin abu ne mai kama da bushiya jikinsa duk gashi-gashi abin gwanin ban tsoro, ga sunan Falmata nan an rubuta da wani jan fenti. . 
Hajja Kaltum ta kama sallallami cike da tashin hankali, tace. 
“Abin nasu Yakolo ya wuce kaina da Iyami ya koma kan falmata kuma? Shin yaushe su Yakolo za su hankalta ne a duniyar nan?” 
Abba ya jima yana kallon abin, ya taBa karya wani sammu da aka yiwa wata mata . waccc ta shekara kusan ashirin tana fama da 
cuta, har ta koma kamar mai ciwon kanjamau, babu irin maganin da iyayenta ba suyi ba amma a banza, har mijinta ya gaji ya saketa sai da suka zo gurinsa Allah ya sanya ya karya sammun. Bayan haka irin wannan abu da yayi a kasa tabbas yau sun kai shi Karshe, zai iya lamintar su yi masa komai, amma ba _ zai lamunci cutar da ‘ya’yansa ba, don haka da sauri ya dauki wayarsa ta cikin gida ya fara kiransu, a lokacin suna zaune a tare kuwa, yace maza suje har da Yakura. 
‘ Sannan ya kira hajja Iyami yace ta je ita ma da Falmata, ya kalli Zubaida yace
“Na gode da Allah Ya shirya ki har kika tona Wannan mugun abin da mahaiflyarki tayi ‘niyyar kullawa, tabbas da sun kai‘ ga aikatawa da sun cutar da Falmata harda ni ma”. . 
Su Hajja Yakolo suka shiga a tare sam ‘ ba su kawo komai_ a ransu ba, Hajja Iyami ta iso it’a ma da falmata, ganin su‘ Hajja Yakolo ya nunar mata lallai ba lafiya ba, suka sami guri suka , zauna suma Abbagana ya mika wannan abin asiri ga Hajja Yakolo da Hajja Basma yana fadin. 
“Me ye wannan?” Suka waro ido a tsorace kowacce gabanta yana faduwa, Hajja Yakolo ta kalli Zubaida a firgice, ta tuno abin da tace musu bayan sun dawo daga gurin malaminsu. 
“Hajja ya kamata mu daina mugun kudiri ga wadannan bayin Allah, domin kullum mu Allah ke kunyatawa, su kuwa suna ta samin daukaka, ku dubi darasi daga kanmu ni da Yakura, ita kanta Salima zaman da take gidan mijinta ba na dadi bane don dai ta fara haihuwa ne ta hakura, Zahra ce kadai ke jin dadin gidan aurenta, ina ganin komawa ga Allah ne kadai mafit a gare mu…” 
Hajja Yakolo ta daka mata tsawa tana fadin. 
“Wuce ki bamu guri munafuka, annamimiya, shi ya sanya da zamu tafl ba mu neme ki ba, don na kula kinf1 kaunar Iyami da ‘ya’yanta a kanmu. To wallahi ko zaki mutu sai mun aikata abin da muka yi niyya, wuce ki bamu gun’”. Wato ashe da suka ajiye abin kafin gobe suje su binne shi ne ta dauko? 
Tsawar da Abbagana ya daka musu ce ta katse mata dogon tunanin da ta tafi“Da ku nake magana kun tsaya kuna ‘ zare mini idanu”.Hajja Yakolo ce ta yi saurin yin magana. 
“Abba ai ba mu gane abin da kake nufi . bane meye wannan din?” 
Hajja basma ta ce, “Ina shirin magana kika riga ni, ni ma ban san ko meye ba”. 
., Abba ya qulu cike da bakin ciki yace, “Bari to nina sanar daku tunda kun kasa fada, asiri ne kuka amso zaku binne domin ku raba Falmata da laflyarta da kwanciyar hankali, sannan ku rabata da Muntari…” Hajja yakolo ta fara sallalami tana tafa hannaye ta ce. 
“Injiwa Abba? Wallahi ko waye ya gaya maka karya yake yi, ni…?” 
Ta dafe jirji ido waje. Hajja Basma ma firiricewar tayi, wai bata san maganar ba. Abbagana ya galla musu harara yace. 
“Duk abin da kuke yi ina sane da shi, ina kyale ku ne saboda na san nafi karfinku, Allah Yana kare ni, amma tunda kuka fara bin kan ‘ya’yana da asirinku to ba zan yarda ba, Zubaida ba zata yi muku Karya ba, don haka na gaji da zama daku Basma da Yakolo, don haka na yanke igiyar aurena guda-dai-dai a kanku… 
Sai suka fashe da kuka suka fara rokonsa, Falmata da Hajja Iyami kam mamaki mai tsanani ya cika su, wacce irin kiyayya ce wannan matan ke mata? _. 
Sai dai , duk yadda suka baiwa Abbagana hakuri bai saurare su . ba, daga karshe ma yace su fice su bar masa gidansa. Ya kalli Yakura yace. . ‘ “Ke kuma daga‘ yau na baki kwana goma kacal ki fito da miji ki bar mini gidana, idan ba haka ba sai dai kibi uwarki can gidansu, don ba gaji dan bazan kara karanbanin aura miki kowa ba, ki fito da miji da kanki ko ki bar mini gidana”. 
Ya kalli Zubaida yace. 
“Ke kuma Yaya maganar mijinki, kina bukatar ki koma ne?”
Zubaida ta daga kai tana fadin Wallahi na tuba Abba ba zan Kara ba, ina son komawa dakina”. 
Ya ce, “Shi ke nan, zan kira mijinki gobe mu yi magana yadda muka yi da shi zan sanar da ke, daman na zuba miki ido ne naga iyakacin gudun ruwanku ke da uwarku, amma tunda Allah Ya ganar da ke shi ke nan, Allah Ya Kara shirya ki”. 
Ya dubi Falmata yace, “ke ma daman ina son yin magana dake yaron nan da ya biyo ki ya sanar dani son aurenki yake, na sanar da shi ke bazawara ce babu damar na ce ga wanda za ki aura, sanda nake da damar aurar dake na yi miki din, amma yanzu kece kike da damar zabar mijinki shi kansa Muntari na san tsananin kunya ya sanya shi ya kasa yi mini maganar, don haka a cikinsu 
saiki zaba, gobe ina jiranki ki sanar dani wanda kika zaba, ranar juma’a zan daura miki aure kafin ki koma makaranta, ina son ki koma da aurenki, hakan zai sanya hankalina ya fi kwanciya”. ‘ 
Hankalin Falmata ya tashi matuka, shi ke nan anja mata, ta ga ta kanta, waye za ta zaBa  tsakanin Malam da Kader? Tabbas ta shiga tsaka mai wuya. Bayan ta koma daki ta sanar da Ammi abin dake faruwa, Ammi ta yi mamaki kwarai da gaske, domin abin da su Hajja Yakolo suka aikata ko a film ba ta taBa gani ba, ta tausayawa Falmata yadda ta ga ta shiga damuwa, ta tsareta da ido ta ce. 
“Falmata tsakaninki da Allah a cikin Mukhtar da Kader waye kika f1so?” Falmata ta yi shiru idonta yana zubda hawaye tace
“Idan kina maganar sone Ammio har abada ba zan hada son Mukhtar da na kowa ba, shi ne wanda na fara so, shi ne kuma ya koya mini duk wani abu da za a kira da so, amma a halin da nake ciki a yanzu zan iya rayuwa da kowanne namiji ne ko da ba na sonshi, domin ina tsoron komawa auren Malam don nafi kowa sanin halin dana shiga 
na wahala da azaba, bana fatan na koma‘ masa. 
Ammi tayi shiry tace, “To Kader ne kenan zabinki k0?” 
Falmata ta yi shiru cike da damuwar data fi ta farko, ta ce, “Ammi ina son Kader k0 domin yadda ya ji ya gani zai aure ni duk da ya san ni bazawara ce mai ‘ya’ya biyu, amma ina jin tsoron auren nasa, domin watarana zai iya ji a zuciyarsa shi saurayi ne ya auri bazawara yana kuma da wani hali na rashin kamewa da kauda kai, wannan ya sanya make shakkar auransa, don haka cikin su bani da na zaBi, da ace Abba zai kara mini lokaci da na fldda wani mijin, wanda zuciyata zata yarda amma na san Abba ba zaiyi hakan ba, idan ya yanke hukunci babu wanda ya isa ya ja da shi”. Hawaye ya fara zubowa daga idonta na tausayin kanta
Amina ta shigo dakin tace da Falmata hajjansu tana kiranta. Bata raba daya biyu maganar da Abba yayi mata ce zata nisamata, don haka’ ta mike tace da Ammi tana zuwa
A  cam uwar daki’ ta‘ tadda hajjan tata tana zaune cike da tsananin. damuwa; ta samu guri ta zauna daga, Kasam kafet kusa da‘ kafafuwan mahaidiyar tata tana. 
“Gani Umma Amina tace. kina kiranaHajja Lyami ta gyara zama tace Akam magabar da Abba yayi miki dazun, duk ya baki zabi nasan a ransa bazai rasa zabinsa ba ke meye ra,ayinki wa kikeso cikin ranki?  
Falmata ta sunkuyar da kanta tace ina rsoron komawa auren mukhtar domin har yau yana tare da fatila wacce zata iya aikata komai a kaina na rashin imaninta
Hajia iyami tayi ajiyar zuciya tace kina nufin kin zabi kader din kenan ko? 
Da sauri tace shima yanada wasu abubuwa da na ke shakkar zaBarsa domin, ina ganin bai dacw dani ba sam”. 
Hajja Iyami tajinjina kai, tace
“Kin gano abin da na gano kenan, tabbas Kader yana sonki, amma ina ganin ba shi da magana irin ta Mukhtar, duk da Mukhtar yana da nashi matsalar, amma ina ganin’ shi yafi dacewa ki komawa k0 domin ‘ya’yanki kada ki dinga ganinsu a gabanmu kina jin dadi, duk randa aka wayi gari kinyi aure Mukhtar ba zaibar mama yaran nan ba, kuma dai shi da kansa ya gano tuggun da matar tasa ke shirya masa, don .haka ba zai yi sakaci irin na baya ba, kuma k0 don soyayyarki da Hajiya Mariya ya dace ki komawa Mukhtar. Tana yawan zuwa gidan nan bayan ba kya nan tana zuwa ganin jikokinta, tana kewarki, koda yaushe amma shawarace nake baki ba tilasta ki nake yiba, sai kije ki yi tunani ki zabi wanda kike so,zaki iya taflya Allah Yayi miki albarka Ya zaba miki mafl alkhairi amin”. Ta mike sumi sumi cike da tsananin 
 
Hmm karku damu bazan sake cewa kuyi comment ba idan kun ga dama kuyi idan kunga dama ku karanta ku wuce inanan ina shirye shirye domin ganin na kawo karshen matsalar komai da lokacinsa ,,,,,,,  aita shan karatu lfy 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE