MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 4

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 4
Alfahari dake har abada, ko da ace anan kika tsaya wato gurbi na biyu, balle ma muna fatan ki zamo garzuwar duniya gaba daya, ki kwantar da hankalinki ki sanya a ranki ko kin ci k0 baki ciba ‘ baki da kaico sai lada domin ba caca bace aikin Allah ne, Allah Ya yi muku albarka ameen”.” 
Duk bayaninsa yafi na kowanne yi mata dadi, ba wai don yafisu iya kalamai ba, a’a don dai shi ranta ke ganin yafi din.
Har aka basu.umarnin su tafi ba ta sani ba, sai da Yagana‘ ta dan zungureta sannan ta farga’ suka fice. 
Koda suka isa daki bakinta yaqi rufuwa, kowa zai iya ganewa farin cikita yafi na kullum, 
‘Yagana kam bata buqatar fashin baqi Alabura ce ma ta ishe ta da magana kamar zata tsage mata kunne
“Anya kuwa Malam mai darasu bai Kyasa ba? Nifa ina ganin yarinyar nan kin tafi da imanin Malam Muhammad mai darasu , kai ina ma nice, kin ga wani kallo da yake yi miki? 
Hmm Kin san Allah bani da sha’awar auran ustazan nan amman  irin yau  Kin gansu tsaf-tsaf babu abin da za a nuna musu na wayewar rayuwa, ga bokon .ga arabic din. Dan gemunsa cas bai fiye tsayi ba. ga  kwantaccen saje, ya kuma iya tsara kwalliya kamar za shi gasar shigar gargajiya ta Afn‘ca”. 
Suka dinga dubanta da mamaki, Yagana tace, “Kc Alabura har kika iya tsayawa kika yi masa wannan kallon kurullan yanzu?” 
Alabura tace, “Ke rufa mini asin’, babu wani kallon kurilla a kallo biyu na gano hakan” 
Suka fashe da dariya gaba dayansu, Falmata na fadin,”‘To ai-kallo daya ne ya halatta ba biyu ba, Alabura”. 
Ta ce, “Uhmm Allah dai Ya yafe mana, amma mutumin ya hadu Allah kuwa, idan kika matsa zai ambata miki yana sonki, don irinsu suna da wuyar sha’ ani wallahi, amma idan mace ta kama su a hannu ta dace, wallahi”. 
Yagana ta dan daki kafad‘arta tace“Kawata k0 dai shi ne sintirin da ake ta yi harami babu dare babu rana?” Tana dariya. 
Falmata ta yi shiru ba ta amsa mata ba, don ba ta son fasa sirrin zuciyarta, tafi son ta barwa ranta sirrinta zaifi mata sauqi fuye da komai, musamman ma gudun muguwar fassara. 
Ta gallowa Yagana harara ta rasa mai ya sanya duk abin da ta yi take ganota nan da nan. Koda yake Allah Ya baiwa Yagana wani irin kaifaffar kwakwalwa da duk abin da ka yi sai ta gane ka, ta nufi gado ta fada don ba zata iya da
halin Yagana ba. 
Suka dinga tiqa mata dariya harta qulu ta lumshe idanuwanta wai bacci take amma tunanin malamin ta ke ashe sunansa Muhammad ma, wato m’ai darasun lakani ne da ya maye sunan nasa na gaskiya ke nan? Sai ta ke suffanta kamanninsa kamar yadda Alabura kefadi, sai ta ga tabbas haka din ne, ta tsinci kanta. da addu’ ar Allah ya sanya Malam mai darasu yana cikin qaddarorin da Allah Ya tsaro mata. 
Ita kam ta kuma samun Kwarin gwiwa, k0 ba komai tana son.ta sanya Malam mai datasu farin ciki tunda tasan yana gurin, don haka ma kusan kwana ta yi tana roqon Allah ya ba ta nasara. 
RABITAH ISLAMIC WORLD LEAKUE. ~ 
Yankin filin da ake taron gasar musabaqar 
na Saudia mai suna a sama yayi cikar kwari. Malamai, larabawa da bakar fata kw jere a mazauninsu na alkalanci, bandakalmomin larabci babu abin da ke fitowa daga-gurin, sai sanyayyen Kamshin turaren almiski  da ya gauraye gurin
Falmata tana can inda aka tanada domin su. Bayan an yi addu’a aka fara gabatar da musabukar kamar yanda aka saba, Hanna ‘yar qasar Saudia aka fara kira ta yi karatunta cikin qira, ar hafsi, 
wacce ta karade gaba saya dakin taron da ya yi tsit, har ta kammala ta amsa duk tambayoyin da aka yi mata. ‘ . ‘ . Daga nan aka koma kan Falmata ta yi karatunta cikin sanyayyar muryarta mai cike da kwarjini, har ta kammala ba a yi mata k0 gyara daya ba. Sai Ayush da ta yi nata karatun, wacce ita ce ta qarshe daga nan alkalan gasar suka dukufa fidda sakamako. 
Daga qarshen musabakar Alkalan gasar sun tabbatar da sunanta a wacce ta zo ta daya, wato gwarzuwar duniya’ ke nan a Bangaren mata. Yayin da Hamia tazo ta biyu daga Saudia, sai Ayush da tazo ta uku daga Misra, a Bangaren maza kuma Saudia ce ta fidda gwarzon shekara. 
‘ Sun koma masaukinsu cike da kyaututtuka da yabo, dadi ya cika ta don tasan zuciyar malamanta da Malam mai darasu ta yi haske da farin ciki. Abbanta ne ya fara kiranta ya yi mata murna da sanya mata albarka, sannan ‘yan uwanta ma’za ‘suka dinga kiranta suna yaba mata, arziki naduniya kam ta same shi darajar karatun alkur’ani har sai take ganin tafi kowa farin ciki. 
Tunda suka fito daga babban d‘akin taron musabakar RABITAH ISLAMIC WORLD LEAKUE 
ta dinga rarraba ido ko zata hangi malam 
mai darasu, amman bata ganshi ba, har suka isa masaukinsu, hakan ya dan taba ranta sai dai ta dake. ‘ 
Har suka fara haramar komawa Nigeria bata kuma ganinsa ba, sai daga baya neta ke jin Ya wuce Jami’atul Madina shi da wani Malami, don za su gudanar da wasu ayyuka, su daga, baya za su taho gida. 
Ranta ya d‘an sosu har sai da ta makale a bandaki ta yi kuka, domin ko babu komai ta so tayi masa kallon karshe, don tasan idan ta koma gida babu wani bata lokaci za a aurar da ita ga wanda ba ta sani ba ta kuma tabbatarwa da ranta da baya sonta, baijin komai game da ita magana ko sashen Alabura da Yagana ba gaskiya bane, da gaskiya ne da bai tafi bai neme ta ba, da k0 sallama ya tsaya su yi, k0 ya yi ‘mata jinjina kamar yadda sauran malaman suke yi mata. Wasu ma har da kyaututtuka suka ba ta. 
Dole k0 ta so k0 ta ki ta cire shi daga ranta, shi ne samun maslahar rayuwarta, 
. Haka nan suka tarkata suka dawo gida Nigeria kowa yana cike da farin ciki, ita kam yake ne yafi yawa a fuskami, sai dai ba kowa ke gane hakan ba tunda miskila ce ita. 
                                NIGERIA 
Shugaban kasar Nigeria ma sai da ya shirya babban taro da aka bai wasu Falmata kyaututtuka, bakin mahaifinta da ‘yan uwanta yaqi rufuwa. Falmata tazame musu diyar da zasu yi alfahari da ita duniYa da lahira; 
_Wani abu da ya fiyiwa Falmata dadi shi ne daukar‘ nauyin karatunta’ da kasar Saudia ta yi na jami‘a har Zuwa sanda za ta kammala. Wannan -‘abin’ ya yi mata dadi, sai dai mahaifin nata yace, sai idan ‘tayi aure mijinta ya amince sai ta tafi saboda’haka murnarta .ta koma ciki, don tana ganin 
‘ zata iya amfan’da wannan damar ta karatunta a ‘ Jami’atul Madina, tunda malam mai darasu yana da alaqa dacan ‘din 
Kwanakinta uku da’ dawowa mahaifin nasu ya kuma tarasu gabanta yana faduwa ta isa dakin. Kowa ya hallara tana shiga su Yakura da Hajja Yakolo suka dinga yi mata wani kallo na banza, domin suna takaicin irin abin arzikin da ta samu‘, kuma Abban ‘ba shi da wata magana sai tata a gidan. Ta sami guri ta rakube cikc da fargaba. 
Abbagana ya gyara zama sannan ya fara magana. ‘ . 
“Kamar yadda nake ta fada, ina cikin matukar farin ciki na abin da Falmata tayi, domin 
ta kuma samowa wannan gida daraja da d‘aukaka ba kamar yadda sauran ke neman zubar mini da darajar gida ba. 
Wannan abu ya sanya mutane da dama sun nuna sha’ awar na basu auren Falmata, ciki kuwa har da sarakai da attajirai da ace kuma hakan kukayi koyi da hali irin nata bazan yi ta baku lokacin fito da miji yana shudewa ba idan baku  manta ba a can baya na sanya muku watanni suka shude ba ku cika umarnina ba, na kuma baku sati daya wanda dalilin tafiyar Falmata musabaka ya Kara sanya lokacin ya tashi har izuwa wata guda, amma a banza kuna ganin kamar wasa 
nake. Sai dai kun fi kowa sanina babu wasa cikin . ‘ 
‘ lamarina, don haka a yau ne nake son  sanar daku ranar juma ’a mai zuwa za a daura muku aure da mazajen da na tanadar muku!. 
Gaba daya hankalinsu ya tashi, zuciyar Hajja Yakolo tsai hanqoro ta keyi tamkar zata fashe, gani take kawai an shirya haka ne domin a tozartata a idon duniya. . 
Cikin zafin rai tace “Gaskiya Abba idan aka yi haka ba a yi min adalci ba, ai kai kanka ba ayi maka irin wannan auran ba, kai da kazo a wancan zamanin ma balle wannan zamanin. Kawai dai ana son a wulaqanta mini ‘ya’ya ne
Allah Ya ba ni ‘ya’ya mata, ai na jima da gano ba kaunar ‘ya’yan nan kake yi ba, kafi son maza, na ga ai ba ni na baiwa kaina ba…” Sai ta fashe da kuka. . ‘ 
Ran su Yakura da Zubaida ya yi. sanyi, gwara ta kwatar musu ‘yancinsu ko saji dadi
Shi kam yake ya yi, wanda ake kira yafi kuka ciwo, sannan ya fara magana. 
“Tsakanina dake za a sami wanda bai qaunarsu, don ni dai nasan Allah Shi ke bada mace da namiji, ya‘ragega dan Adam ya yi musu irin tarbiyyar da ta dace, domin tarbiyya ke nuna da na gari ba jinsi ba. Tunda aka haifi yaran nan nayi ‘qoqarin ba su nagartacciyar tarbiyya da ilimin da ake yayi : a wannan zamanin, domin su sami nagartacciyar rayuwa, amma sai da kika yi kutunkutun din da kika lalata musu tarbiyya har suke kallona a dan qauye wanda bai san rayuwa ba, suke ganin rayuwar Bature ita ce ta dace da su, har ya zamana samarin da suke tarawa marasa tarbiyya da na kore’su kika ce ina korarwa ‘ya’yanki samari, don suna da farin jini. Yanzu kin gano abin da nake guje musu ko‘.’ 
Samarin arziki sunga na banza sunqi zuwa. yayin da na banza suka gaza amfana muku komai, sai dai magana ta ta qarshe ki sani umami ne nake
yiwa ‘ya’yana, idan idonki zai iya gani to, idan ba zai iya kalla ba qofa a bude ta kc, don bazan iya lamintar abin da na laminta a kanki a baya ba”. 
Ta kuma rushewa da kuka tana shirin yin magana ya daga mata hannu, yaci gaba da magana. 
“Ke Zubaida akwai malam Mu’azzamu, limamin masallacin juma’a ne kamar yadda kika sani, shi ne mijinki don sadakinsa zai iso da daddaren yau. Ke kuma Yakura Alhaji Isa mai sumunti ne mijinki. Ke kuma Salima Hassan dalibin nan nawa da yazo daga Sokoti ne mijinki. ‘Kekuma Falmata Muntari dan abokina Abbas shi 
ne mijinki insha Allahu.. 
. “Wallahi wannan son kai ne, ta ya ya za a baiwa Falmata Muntari? Ai a dakina ya dace a yi 
, masa mata idan dai gaskiya ne” . Hajja Yakolo ta 
katse shi a harzuke tana ci gaba da kuka. Su ma 
‘ya’yan nata duk ‘sai suka saka kukan. 
‘ Hajja Iyami ta kwantar da murya, tace “Malam idan kana ganin hakan zai zama rigima ka bai wa Yakura ko Salimar Muntarin mana,ita Falmata k0 wa ka bata ai zata yi murna da godiya ne. 
Falmata kam ta yi wuki-wuki tana ganin duk wanda aka ba ta ita babu wani gwara, su suka wani damu da Muntarin Kano, ita da za a yarda ai
da an cire ta daga wannan tsarin auren, amma tasan ba ta isa ta ja da maganar mahaifinta ba, don haka taja bakinta ta tsuke tana jiran hukuncin da za a yi. Abbagana ya harzuka matuKa ya kalli Iyami, yace “Kina ji ba wai na taraku na nemi shawararku bane, a’a, umarni no make bayarwa kowa ya tashi ya ba ni guri, sai ku sanar da ‘yan ‘ uwanku ranar jumna’a’daurin auren ‘ya’yanku, saura kwanaki takwas ke nan”. ‘ Haka nan suka tashi kowa da abin da yake sakawa a cikin ransa. ‘. . 
A dakin hajja~ Yakolo, Hajja Basma keta ‘ ‘ qara ingizata wanda da ace tana da hankali da ta gane domin duk abinta ba ta cewa uffan gaban Abbah, wai dole ita nan mai kirki, ya riga ya ganota amma sai ya kyaleta yake kallonta kawai. 
“Wallahi wannan shiryayya ce don cuta, ace duk an hada‘ yan dakinki datarkace, sam da sake’? . inji Hajja Basma 
Yakura ta dago jan ido tana cewa, “To wai ni Momy_ina aikin da kika ce malam ya yi aka ba mu magani da turare muka yita dirka, amma ace maganar nan ta tashi daga kanmu?” , ‘ 
Hajja yakolo tayi saurin amshewa, “Ya zama asara, ai na jima ina aiki akan uban nan naku amma a banza, tun ba kawoku duniya ba nake neman 
fada ta hanyar malamai da bokaye, sai dai tamkar ina shuka dusa, na ma rasa yadda zan yi da rayuwata”. Ta qarasa maganar cike da tsananin takaici. 
_ Zubaida ta amshe, “Ni kam guduwa zan yi, gwara na bi duniya idan ya huce na dawo, don wallahi ba zan yarda kamarni mai digiri a hada ni aure da wani wawan almajiri ba, ba zai yiwu ba”. 
“Keki kiyayi kanki, wallahi malam ya yi miki aikin shashatau ki zama mara hankali da dai ace kin jawo masa wannan abin kunyar, ki shiga taitayinki wallahi, kuma kina tunanin idan kika qi yarda da auren nan zai kuma yarda ki zauna masa a gidansa ne? Akul na kuma jin wannan maganar, ku dai ‘ barni da shi, akwai‘ wani hatsabibin boka dake’ tsafi, gobe zanje na same shi, komai zai zamo daidai dole ma kuwa”. Yakolo ta qarasa tana hura hanci.
Wannan ya sanya sauran yaran suka dan kwantar da hankalinsu, don sun san Babar tasu Boss ce. . , 
ita kam Falmata abin ya tsaya mata a ranta, sai dai ba ta son mahaifiyarta ta fuskanci hakan, don haka dole ta fito babban falonsu ta tattara qannenta tana ta koya musu karatun Alqur’ani mai girma, hakan ne ya dan sanyaya ranta. Can da aka 
jima ta tambayi mahaifiyar tata ta shiga gidan su Yagana. 
Ta bata izinin shigar domin ita kanta tana tausayin diyar tata, ta riga ta gano ba ta maraba da wannan auran, amma tsananin biyayya ya sanya taqi nunawa koda akan fuskarta. 
‘ Sanda ta isa gidan su Yagana suna kebewa a dakinta ta fashe, da kuka mai ciwo, hankalin Yagana ya tashi matuka, ta dafe Kirji tana fadin
“Subhanallahi, Falmata me ya yi zafi haka? Don Allah ki kwantar da hankalinki, nasan dai ba zaiwuce maganar malam mail darasu da kuma auren da Abba ke shirin yi ba” .‘ 
Ta dago kai idonta jajur ta ce “Na rasa yadda zan yi da raina Yagana, addu’ ar da Abba da Gwani Muhammad suke ba ni duk na yi amma kullum son mutumin nan kuma karuwa yake yi a raina, babu kuma abin da yafi mini ciwo illa za, a aurar da nine ga, mutumin da bai son auran, fa shi da bashi da lokacin wata diya mace ma bayan matarsa da ta mallake shi. Yarizu kina zaton akwai wani jin dadi da kwanciyar hankali a auran irin wadannan mutanen’.’ Tabbas Abba ya yi shirin auren na huce dani, Wanda nasan karshensa kuma wulakanci da dana-sani ne, dama na amince tun farko na fara Sauraran Malam Bukar da duk hakan ba ta faru da ni ba. Ni kam na ga ta kaina a rayuwata”. 
Tausayinta ya cika Yagana domin ta bata labarin abin da ya hanata bin Hajiya Mariya Kano, wato ta yi gudun gara ta fada gidan Zago kenan, amma ya ya ta iya? Haka nan ta dinga lallashinta har ta dan kwantar mata da hankali tana fadin. 
“Nasan Allah Ya amsa addu’arki, domin bakinki mai albarka ne, bakin da ya saba karatun littafi mai girma Allah ba zai wofintar da shi ba. Nasan wallahi Allah Ya amshi du’a’inki, sai dai ba mu sani ba a duniya zai cika miki shi, k0 kuma zai sanya miki cikin mizaninki na can ne wanda nasan sai kinfi farin biki idan kika riske shin ‘ Kece fa kece  mini wannan duniya wani ‘,d‘an taqi ce mara dorewa, k0 kin manta hadisin ma’aiki , duniya kurku ce ta mumini, kuma aljana ce ta fasiki, don haka ki kwantar da hankalinki, ki dauki duk batun aurenki da Muntari a matsayin ibada, wacce zaki yi fatan ta kai ki aljana, ki yi kuma ta addu’a Allah Ya musanya miki halinsa da na matar tasa sa su zama masu alkhairi”. 
Da wannan ta dan sami nutsuwa da sassauci a cikin ranta har suka ci gaba da hirarsu. . 
Sai da ta ga magriba ta doso sannan ta yi haramar komowa gida. Gidansu yana kallon gidan su Yagana, ita kam iyayenta ba su da shi don 
karatunta ita da sauran ‘yan uwanta duk Abbagana ke daukar nauyu. KUSan rabin hidimar gidansu ma shi neke yi, sai dai Yagana ba ta fiye shiga gidan su ba sosai saboda wulakancin su Yakura, domin su ba su harka da diyan talakawa, ita kuwa Falmata babu ruwanta tunda ta taso suka shadu da Yagana ba ta taba jin wani fifiko ko dana digon kwayar zarra a ranta game da ita ba, wannan ya sanya mahaifiyar Yagana ke matuqar sonta da yaba mata. 
Shakuwarsu’ ta kai ko d‘ankwali Malam Abbagana inzai dinkawa Falmata sai ya hada da Yagana, hatta Hajja Iyami ma, domin ita kanta ta ‘yaba da tarbiyyar Yaganar kusan babar Yagana Hajja Fatime ma kawarta ce,’ko muce aminiyarta. 
Tana shiga harabar gidan nasu can daga qofar sashin da zai sadaka da sashin Abbansu ta hango su Yakura da Zubaida suna ta haqa rami. Tasa musu ido cike da tsananin mamaki, tana kallonsu har zuwa sanda suka zaro wani abu daga cikin _laffayar Zubaida suka sanya a ramin suka maida da sauri suka rufe, har da dandabéwa. Ita kuwa tsananin mamaki ya sanya ta kasa motsawa har suka kammala. 
Sanda suka hangota tana kallonsu sai da Suka firgita matuka, amma da yake zuciyar ta taurare sai suka dake suka nufota da saurinsu, ganin 
ta dauke kai tana shirin Shigewa Kofar da zata sadaka da ainihin gidan. 
Zubaida ce ta fara magana, “Magulmata makwanzama masu zuwa lahira da kokon dambu, . wallahi mukaji wannan maganar a bakin wani sai kin gwammace kida da karatu, munafuka”. 
Yakura ta amsh “Kc ba ki ga har wani rawar kai ta ke ba, don ita an mata kyakkyawan zabii, to yarinya bar murna karenki ya kama zaki, mu nan zamu yi maganinku, banzaye”. 
Ita dai ta wuce da saurinta ta nufi sashinsu, ~ domin ta riga ta saba da wannan halin nasu, tunda ta taso tana yarinya ta ke shan wahalarsu da shegen . ‘yan ubanci, da ace dane ma sai sun hada mata da 
‘ duka. ‘ 
” tana isa sashinsu ta wuce dakinta, ta dauro ‘ ‘alwala ta jima gurin sallah tana gayawa Allah, amma kuma _dai ta gaza samun nutsuwa tana ganin kamar wani abu zai iya samun Abban nasu. Ta kuma yarda duk abin da ya sami Abban nasu da kamashonta a ciki, tunda dai ta gani, amma kuma tana tsoron sanar da wani don tafi kowa sanin ’halin masifar Hajja Yakolo da ‘ya’yanta, sai ma ta lauya abin ya koma kansu. Tana mamakin butulci irin na su Yakura, duk irin hidimar da mahaifinsu yake yi musu, amma har su yarda su cutar da shi. 
Ta gaza jure abin da ke cin ranta, don haka ta mike da saurinta ta nufi dakin mahaifiyarta, ta tadda ita tana linke kaya tana sanyawa cikin sif, ta shiga da sallama. 
Mahaifiyar tata ta daga kai tana kallonta, tana nazarin yanayinta, ta gano tana cikin damuwa amma sai ta dake ta ce 
‘ “Ya aka yi na ganki haka Falmata?” 
Ta sami gefcn’ gado ta zauna kanta yana kasa, tace “Hajja wani abu na gani yanzu da bazan iya hakuri da shi ba” . 
Mahaifiyar tata ta bar linke kayan ta zauna gefen gadon ta tattara hankalinta a kanta domin tasa‘n duk abin da ya sanya diyarta magantuwa ba qarami bane domin itaidai bata gulma duk abin da zaku yi a gabanta sai taga dama zata daga kai mata kalle ku balle har tasan kana yi taje ta gayawa wani, domin kuwa duk irin cin zarafin da ‘yan‘ uwanta ke mata ba ta taBa gaya mata ba, sai dai idan ita ta gani da idonta. 
Falmata ta kwashe duk abin da ta gani ta sanarwa mahaif’iyar tata, ta dora da cewa, “Hajja ina tsoron kada su cutar da Abba, nasan akan maganar Muntari ce dai”. 
Hajja lyami ta yi murmushi, tace, “Kada ki damu an jima ana ruwa qasa tana shanyewa. 
Mu tara domin ci gaba da sauraron wannan qayataccen book din

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE