MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 8

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 8
juyewa zuwa irin na namun daji, idan ruwa ya taba jikinsa, to sai dai na sama. 
Sai da ya gama dariyar sannan yace, “Aljana Zulzaliyya da muka aura mata Mukhtar ta kashe auren, domin ya gama konata da karatunsa, duk da tace tana iyakacin kokarin nisantar shi idan ta ga zai fara karatun nasa, amma da yake yakan yi babu lokaci ya sanya yafi karfinta. Aikinki mai wahala ne Fatila, amma duk da haka nakan tura aljani Sharmilu ya dinga yi masa labe; 
Tabbas kina cikin matsala, domin mahaifiyarsa tana nan akan bakanta sai ta yi masa aure… 
Ta dafe kirji a tsorace, “Na shiga uku, boka yanzu ya ya za a yi kenan?” jikinta sai rawa yake tamkar mazari ko wadda ake kadawa ganki a filin bikin shan kabewa. 
Ya yi ihu sannan ya watsa Kasa ya yi wani zane-zane, sannan yace “Abu daya zaki yi, dole ki dinga yi masa girki duk wata da jinin al’adarki, har abin shansa. Sannan dole ki daina sallar asuba da ta isha’i idan kika yi haka aljani Sharmilu zai taimakeki ya ci gaba da kudundune zuciyarsa ya kasa kula wata mace, ya kuma kasa biyayya ga mahaifiyar tasa sai abin da kika ce. Aljani Sharmilu yace a gaya miki ko bayan ranki bai isa ya yi aurc ba, sai 
dai ya rungumi kabarinki a matsayin matar aure”. 
Wani irin farin ciki ya cikata, ta gurfana kamar mai yin sujjada tana fadin, “Tsinuwa da tambadewa su tabbata a gare ni da kai, wannan boka mafi girma da daraja. Zan yi duk abin da kace me ake buqata kudin kayan aiki?” 
“Ba ma son komai illa koriyar Giwa da kashin Kiyashi, sai fitsarin Zakanya mai goyo”. 
Ta kuma gurfana, “Wannan aikin sai ku la’ananne; ga kudi a bai wa aljanun su sawo”. Ta zaro damin kudi a jakarta na dubu dari da hamsin ta ajiye masa. Ya dinga dariya yana fadin, “Ku tashi ku fice da baya, Aljani Sharmilu yana godiya, yana kuma Kara la’antarku da haka ‘zaku zama masu nasara a duniyar nan”. 
Haka suka fice da baya da baya suna ihu kamar yadda suka shigo. 
A mota suna hanyar komawa gida Fatila ta cike da damuwa ta’na fadib“Diyana ba ki da matsala irin tawa, sau nawa nake yin aiki yana karya mini, har sai yaushe zan yi aikin da zai zauna tsawon shekaru a jikinsa ne?” 
Diyana ta tabe baki tana fadin, “Hakan ma ba ki gode ba kenan, guri nawa muka je kafin mu sami irin haka? Ina ce akwai sanda muka rasa Wanda zai iya aikin da zai yi tasiri a kansa, banda 
kissa da kisisina da ladabin da kike masa da tuni ba. ya yi waje da keba? Tunda dai mijinki malami ne, sai hakuri, don mafa wai ba mai kauce hanya bane ba, keda irin su Malam .jatau mai garada neda suke hadawa da kauce hanya da ai ba ki isa kiyi masa irin wannan aikin ba tare da ya gane ba. Kedai ki kwantar da hankalinki kiyi duk abin da ya dace, da haka wata rana sai ki ga aikin yana dadewa a jikin masa”. 
Hankalinta ya-dan kwanta tace “Ai shi kenan, amma ina son ganin wannan lokacin”. 
Haka nan suka dinga muguwar hirarsu har suka iSa gida. 
** ** ** ***************
Cikin satin gaba daya hankalinsa ya yi gurin Falmata, k0 bacci yake yi ita ce ke masa gizo, wani irin sonta Allah Ya dora masa mai zafi sai ga shi kwanaki tara da dawowarsa daga Maiduguri ya kuma fara shirin komawa can. Sai dai Bauchi yace da matar za shi, ita kuwa har ta yiwa bokanta waya tunda ya ambata tafiyar, ya gaya mata wai taro ne zasuje na malamai, hakan ya dan sanyaya mata rai, tana ganin lallai ita mai nasara ce. 
Don haka koda ya fara shirin tafiya har da taya Shi Shirya kaya, domin yace mata kwanaki 
uku zai yi a garin. 
Tun daga hanya ya kira Falmata yace mata, ga shi nan zuwa. Dadi ya cikata, gashi tana gidan yayanta Bulama, domin matarsa Anti Shafa’atu ta haihu yau ma ake taron suna, kwananta biyu a can gidan. 
Duk ta rude ta ma rasa ina zata tsoma ranta don dadi sai ga ta ta shige kicin din Anti Shafa’atu ta fara kacaniyar hada masa abin da zaici. Tana gamawa ta zuba su a wammcrs ta koma ta zubawa waya ido, duk bayan awa daya sai ya kira har ya shigo garin Maidu’guri ana kiraye-kirayen sallar magruba, ai kuwa bayan ta yi sallah ta salla sabon wanka. ‘ 
Shi kam masauki kawai ya nema a gidan mahaifibsu na garin, don tun bayan da aka daura auran kafin su koma mahaifiyarsu taje da ‘yan uwansa suka gyara gidan don su sami gurin sauka idan sunjc. Sai dai gidan yayi qura, doki kam ba zai iya barinsa ya gyara ba, don haka jakarsa kawai ya ajiycme ya watsa ruwa ya yi sallar magruba da isha’i ya saka kaya ya fito ya dauki hanyar gidan Bulama. 
A falon saukar baqi ya tarar da ita, duk ‘yan suna sun watse kowacce ta tafi gidanta, an shirya masa abinci’ mai rai da motsi, biski ne da miyar taushe yasha man shimu da kaji. sai kunun lafiyayyar gyada, shi kam duk ya qosa yaga amaryar tasa, don haka idonsa yana kan kofa. 
Can sai ga ta nan ta shiga, kamshinta gaba d‘aya ya cika shi, ya kura mata ido tana sanyc da wani ubansun matcriyal da aka yi masa dinkin riga da siket. Ya kamata tsam gashinta ta daure shi ta tura cikin band don haka da tayi dan juyi sai ya zauna das a kanta. Ta yafa dan qaramin gyale wanda Anti Shafa’atu tace dole shi zata sanya, ita kam duk jinta ta keyi a takure, domin ba ta saba sanya qaramin gyale irin wannan ba, daga shigarta ta Larabawa sai dogon hijabi su ne kayanta, don haka ta shiga tana ta takurewa ta sami guri ta zauna. 
Gaba daya jikinsa ya mutu, ya koma ya kwanta jikin kujera yana mata wani duba qasaqasa, bakinsa yaki rufuwa. 
Da kyar ta daure tace Sannu da zuwa Malam, ka sha hanya ko?” 
Ya yi dariya yana fad‘in A’a, gama dai yangar da yaukin sannan ki yi mini magana, ko da yake kin san kin yi kyau, ai dole ki yi Yanga”. 
Kunya ta kuma rufe ta, kamar ta tsaga kasa ta shige, musamman saboda irin kallon da yake wurga mata, da kyar ta daure tace 
“Ni fa ba haka bane ba, ka tambayi Anti ma ban iya yanga bafa, haka dai Allah Ya halicce ni kawai”. Ya sake yin dariya, wani irin nishadi yana shigarsa, yace, “Ki ce lallai zan more. Ai ana son. mace ta kasance mai irin wannan suffar ta yanga da yauki. Hakan ya .kansa kullum mijinta .ya dinga ganinta kamar wata ‘yar budurwa”. 
Cikin kunya tace “Don Allah kaci abinci Malam, nasan ka kwaso gajiya da yunwa, k0 ruWa fa baka sha ba”. 
Ya noke kafada tana ‘yana fadin , “Baki so naci abincin naki ba, da kin zuba mini, ko kina zatonna 
iya zuba abinci da kaina ne?” Ta mike da sauri ta kama zuba masa.a
faranti a ranta tana ganin shirmen da tayi, shaf! Ta manta ma ko shaukin ganin nasa ne ya mantar da. ita? Oho!
Bayan ta zuba masa ya bita da kallo, sanda. ta komo gurin zamanta. Yace, “A’a, ya ya kika. koma? Tasowa zaki yi muci tare ai”. 
Ta zaro ido waje cike da kunya tace “Don Allah ka yi hakuri, wallahi naci abinci tun dazun, a koshe nake. 
Yace “To shi kenan, matso ki bani a baki, idan ba haka ba bazan ci ba”. ‘Ya fadi yana dariya 
don yasan ba zata iya ba. 
Ai kuwa kanta ta Boye tsakankanin cinyoyinta tana dariya, don tana ganin ba zata taba iya yi masa hakan ba, ya ja farantin ya fara cin abincin yana dariya, don yasan ya gama bata ‘ kunya. Shi kam bai taba ganin mace mai kunyar Falmata ba. Tabbas zai sha wahala da ita, komai ita abin kunya ne. 
Sai da ya kammala cin abincin sannan yace “To dago kanki na kammala, amma fa ina kallo kina satar kallo na k0?” 
Ta kuma Boye kan nata tana dariya. Da kyar ta sake suka yi ‘yar hira, sa‘nnan yace, yana son ta raka’ shi can gidansu ta taya shi gyarawa, don ba zai iya ba. Gabanta ya yanke ya fadi, amma tasan ba zata iya yi masa musu ba, don haka tace “ko na ‘kirawo Anti Shafa ka gaya mata, kada ta ji shiru ban dawo ba?” 
Yace “Hakan yayi kyau, ai ya dace ma na shiga naga boy, k0 zaki yi mini iso ne?” ‘ 
Tace, “Toh, bari na sanar da ita”. 
,Ta mike ta nufu cikin gidan, ya bita da kallo, wani abu yana mintsininsa a zuciyarsa, minti biyu suka dawo tare da Anti Shafa, Falmata tana rungume da yaron, kai tsaye shi ta mikawa yaron, ita kuma Anti Shafa ta sami guri ta zauna, a 
mutunce suka gaisa dashi yayi mata barka, ya dora da cewa.‘ 
“Ina son ki bani aron ‘yar gidan naki ta raka ni mu gyara wancan gidan, yayi kura da yawa ne”. 
Anti Shafa tace “Haba Malam Mukhtar, ai ba sai ka nemi izinina ba, abin da matarkn ce?” 
. Ya yi dariya yace, “Ai Abba a hannunki ya santa duk abin da ya same ta ke za, a tuhuma tunda bai danka min itaba’ko’?” . 
Suka yi dariya, sannan tace “to ai k0 bai danka maka ba, duk wanda yaji tana tare da mijinta babu abin da zaice bari na koma kada kuyu
Dare ko yace hakane ungo yaron fatimatul zahra  mika mata shi 
Falmata ta tashi ta amshi yaron daga hannunsa hannunsu ya gogi juna kallon da yake mata ne ya nuna mata sa gayyah yayi hakan saida ya daura bandir fin dari biyu wanda jikin takardar tasu aka rubuta dubu hamsin
Anti shafa,atu ta amshi yaron falmata ta bisu tanace masa
Bari na dauko babban gyale mu tafi yace ok ki tarar dani can waje a mota sanda suka koma cikin gidan antt shafa,atu ta dauko wani maganin a mulmule kamar bonvita
kama ta kuma kwayar dawa ta miqa mata guda uku tace “Maza shanye wannan, ga wannan kuma‘kije bandaki ki tsuguna a kai”. 
’ Ta bi Antin da kallo cike da mamaki, Antin 
tata tace, “Kiyi yadda nace idan kika dawo zan yi miki bayani, kinga yanzu sauri yake yi, kada ki Bata masa lokaci”. . . Jikinta da santi ta amsa, ta yi yadda tace din Bayan ta dawo daga bandakin ta mika mata wata hadaddiyar humra tace ta shafe-jikinta gaba daya, ta kuma ba ta wasu turaruka sannan tace ta gyra fuskarta.
Hatta lafayar da zata nade sai da aka fesheta da wasu Turaruka irin nasu na ‘yan Maiduguri masu dankaren kamshi, sai ga Falmata ta qara fitowa tana walkiya da kamshi, haka ta nufi gurinshi fabanta sai faduwa yakeyi. 
. , Yana mota a zaunc ta iso, ya qura mata ido 
tana .tafe kamar. tarwada, komai nata burge shi yakc yi, tabbas ya yi sa’ar mata, sai dai ya yi ta yiwa Allah godiya. 
shine ya bade mata Bangaren ma‘I zaman bunza ta shiga ta zauna, gaba daya kamshi ya cika motar  ya lumshe ido sannan ya bade ya kalle ta yace, “Fatima kin iya tukinmota ne, don duk kin kashe mini jiki, kada na karawa wani”. 
Ta kauda kai waje tana dariya, tace, “Ni ban iya mota ba, sai dai idan zaka hakura ka kwana a nan kawai”. 
Ya yi murmushi yana kokarin tayar da motar yana fadin, “Lallai da an kai ni taska ace ga wani ya kwana gidan surukansa”. 
“me ye kuma taska malam?” 
Sai da ya fita daga gidan saboda tuni maigadin ya wangame kofar, sannan yace, “Ashe fa keba ‘yar Kano bace ba k0? Wani shiri ne da ~ake gabatarwa a gidan rediyon Kano, idan kika tare zan dinga kamo miki kina ji kullum, abubuwa kala’kala ya dace’ma fa mu kai musu labarin aurenmu k0? Auré mai cike da mamaki, muka hadu a Kano ‘muka hadu a Saudi, amma muka Ki kula juna, ashe mu mata da miji me bamu sani ba. ,Ya ya kika ji a zuciyarki yanzu Fatima?” 
Ta kauda kai da sauri tana dariya. Ya qurawa titi ido yana fadin“Wai ke waccc irin kunya ce haka? K0 kin manta ni mijinki ne iye? To idan ba ki daina jin kunyata ba zamu yi fada, kuma kada ki kuma ce mini malam daga yau”. 
Ta marairaice “to ai niba zan iya fadin sunanka bane, Allah kunya na keji, to zan dinga ce maka yaya, hakan ya yi?” ‘ 
Yasha kunun wasa, “A’a bai yi ba, aini
masoyinki ne ba yayanki ba, kin san me Fatila kece mini?” 
Gaba daya annurin fuskarta ya dauke, jin ya ambaci matarshi, wani irin kishi ya shige ta, wato ita ce karkatacciyar kuka mai dadin hawa ko‘? Amma sai ta Boye damuwarta ta sunkuyar da kanta ta kama wasa da yatsun hannunta. 
Ya kula da yanayin da ta shiga, amma yasan kishinta irin na halak ta keyi, ba irin na Fatila ba, don da ita ce ya‘ ambaci sunan wata mace da babu zaman lafiya. Ya yi kokarin share waccan maganar ta hanyar ba ta labari. . 
“Wani abokina ne matarshi kejin kunyar fadar sunanshi, Sai take ce masa DL, rannan suna zaune a majaliSa sai Wani yaro yazo wucewa, sai daya daga cikin abokanshi yace, kai na ga randa yaron nan zai yi wayo, wallahi DL ne. Sai ya kalli abokin yace, meke nan? kana so kace darling akece masa? Sai suka kama yi masa dariya, suka cc, ai DL yana nufin DOLO. Sai ga gogon naka ya tashi yana huci ya nufi gida, sai ga rigima shi da matar wai tana ce masa dolo…” 
Dariya ta kama Falmata harda  toshe baki Ya kalleta cike da sha’awar dariyar tata, yace. “Don haka a sunan da zaki rad‘a mini~ban da DL. gwara ma kice Dee k0?” 
Ta kuma fashewa da dariya, kai wannan mutum ya isa sanya mutum nishadi. Ta ayyana a ranta, a haka suka isa gidan
Suna shiga taga gidan tabbas yayi kura, ta kama koqarin fara gyaran k0 lafayar bata .cire ba, amma sai ta ga ya dauko wata she ta da dogon wando cikin kayansa yana fadin
“Amshi wannan ki saka kada kayanki su baci, bari naje na dawo”. 
Ta amsa ta shige daki ta sanya ta hau gyaran gidan, shi kuwa tafiya ya yi ya siyo kayan shayin da zai yi amfam’ da su da safe, har da su risho da duk wani abu da zai bukata a wani super market Sanda’ ya dawo taci karfin aikin, don haka shi ma ya cire babbar rigarsa ya fara tayata aikin, ita kam duk ta tsargu da kallon da yake yi mata. Sai ta ji kamar tace ya fice zata yi ita kadai kawai, amma dai ba zata iya ce masa-hakan ba. 
Sai da suka kammala gyara k0 ina sannan yace “Bari na shiga na yi wanka, kema shiga ki yi a wannan toilet din ta dan”,  sunkuyar da kai qasa tace, “Ni dai da ka maida ni gida nayi a can, ka ga dare yana yi”. 
Ya tsare ta da ido don ya kula sai ya yi da gaske, domin tuni zuciyarshi ta sanya masa darasin daukota tuni,,,, ,
 yace, “Kiyi wanka, ki dawo harda alwala bana son gardama fa”. 
Ta kalle shi a tsorace, tace“Na fayi sallar isha’i a gida, kada Yaya Bulama ya komo ya yi fada, ka yi hakuri don Allah” 
Ya kuma Bata rai, yace“Shi kenan kici gaba da gaddama, amma ai kina da ilimi, kin san hakkin miji akan matarsa k0? K0 kasar nan zan iya bari daje a yanzu domin kedin matata ce k0?” 
Ta sunkuyar da kanta cike da takaici, tace, , “Kayi hakuri zan yi din
Ya sa kai ya dice ya barta a nan gabanta yana faduwa, domin tana tsoron irin fad‘an da Yaya Bulama zai yi mata, amma don ba zata iya sabama maganar malamin nata ba, mutum mai daraja haka, don haka ta shiga band‘akin ta fara yin wanka da saurinta. Ta fito ta fara kokarin sanya kayanta sai gashi ya shigo tsagal kamar an hankado shi. Wata irin kunya ta kamata, domin tana shirin sanya rigarta ya rutsa ta, amma sai ya d‘auke kanshi ya matsa can cikin d‘akin ya shimfid‘a sallaya ya zauna ya kama lazimi. Da sauri ta gama sanya kayan ‘ jikinta har rawa yakeyi, taji dadi kuwa da bai kuma waigowa ya kalle ta ba daya kintaci bayan ta kammala kimtsawa ya ce. 
“Kizo mu yi sallah ta nafila ce
Ba tayi musu ba ta iso  gurin daidai lokacin 
da yake tayar da sallah, sai dai hankalinta gaba d‘aya a tashe yake, domin ta fara gano take-takensa, idan ba ta manta ba ai malamansu suna yi musu bayanin irin wannan sallar ta makaranta. Sai ta tsinci kanta a‘ sujjadarsu ta karshe tana rokon Allah Ya sanya ba abin da ta ke zato ne zai faru ba, domin tasan ba zata iya yiwa malam mai datasu musu ba san. Suna yin sallama ya juyo ya kama addu’a. 
. Gabanta ya ci gaba da fad‘uwa har zuwa sanda ya kammala, ya mike tsaye daman tana nannad‘e cikin lafayarta don haka ta mike da sauri tana fadin
“Kazo mu tafi, dare fa yayi sosai, kada Yaya Bulama ya yi mini fada, ban taba kai wa dare irin haka a waje ba 
Ta yi kwal-kwal idonta ya ciko da Kwalla kamar zata fashe da kuka. 
. Ya yi murmushi ya nuf‘i wata katuwar leda da ya shigo da ita da ya dawo daga super marke ta yace, “Kinga danyi hakuri ki kwanta a nan, kinga daré ya yi, sha biyu da kwata fa yanzu”. 
Hawayen daya ciko mata a ido ya fara zubowa, ta marairaice murya tana fadin, “Don Allah kayi hakuri‘ Malam, me kake tunanin Yaya Bulala zai dauka” Don Allah ka maidani”. 
Ya sha kunu matuka, yace “Kin ma ba ni mamaki Fatima, kamar ba mai ilimi ba? Yanzu ‘yan uwanki da aka yi muku aure ba suna gidansu ba? Ban da Allah Ya kaddara, sai anyi haka aida yanzu kina gidana”. 
Yana magana yana tafiya har ya isa kusa da 
ita, jikinta sai rawa yake kamar ana kada mata gangi, idonta kuwa sai zubda hawaye yake, ya kamota ya riketa a jikinsa cikin lallashi ya ci gaba da magana. _ “Fatima kina da ilimi fa, kada ki yi aiki irin na jahilai, kin san nasan duk hukuncin da ya hau kan musulmi mumini,’da nasan abin da zan aikata ‘a gare ki illa ne da ba zanyi ba. Ki yarda Fatima ban taBa aikata’ irin wannan abin ba ta gurBatacciyar hanya ba, sai ga iyalina da Allah Ya halatta mini su. Ke halak dita ce kuma Allah Ya jarrabe ni da sonki, idan kin amince kin bani dama saina nuna miki irin sonda nakeyimiki.ina tunanin hakan ne zai rage mini wani abu mai nauyi da ke yawo a zuciyata. idan kuma baki yarda ba bazan matsa miki ba, zan kyale ki duk da kyalewar taki nasan zata janyo mini abu buwa da dama. Ki yarda dani Fatina”. 
Yadda yake maganar gaba d‘aya ya kashe mata jiki, wata irin kunya da sonsa ke kara ratsata 
har taji ba zata iya yi masa musu ba, tabbas ta san abin da yake shirin aikatawa ba hararnun bane sai dai ya ya zata yi da kunyar su Anti Shafa’atu da .yaya Bulama? Amma dai ba zata yarda wannan ya sanya ta bijirewa mijinta ba, domin ba tasan halin da zai shiga ba. 
Jin ta yi shiru ya sanya ya Kara magana cikin rada da wata irin murya mai rawa da ta kuma ratsa kwanyarta. 
fatina kin amincc dai? Bana son nayi miki dole, nafi bukatar yardarki kafin na kusance kin 
Cikin kunya ta daga kai alamar eh, wani irin ‘ dadi ya kama shi, a fili ya dinga fadin, “Masha’Allah, alhamdulillah”. 
Washegari da safe kunya da ciwon jiki suka hadu suka hana Falmata ko da motsa yatsanta. Shi kam malamin nata tunda asuba da ya tashi yaje masallacin dake cikin layin ya dawo ya zauna ya keta tilawar karatun qur’ani, kusan tunda ya fara ta tashi take saunaron karatun nasa cikin qira’ar Hafsi, muryarsa mai dankaren dadi, kai kace Sudeis ko Shureim ke rera karatun. Tunda asubar ya tasheta ta yi wanka da sallah, sanda zai fice yana sauri don haka da ya dawo ya tarar da ita a kwance ya yi zaton ta yi sallar. Ita kam tsoron mikewa ta 
Hmm su muntari manya daga zuwa taya gyaran gida sai ayima yarinya wayo,,,,,,,,  ka bada maza😀

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE