MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 9

MATACCIYAR RAYUWA
BOOK1 THEND QARSHE
Ta mike ,sai takejin kamar faduwa zatayi saboda azabar ciwon data keji. 
Saida gari yayi shaar sannan ya tashi daga kan sallayar ya nufi gadon, saidai daya daga bargon sai yaga a yadda ya barta  haka taje  Da sauri yace “Subhanallahi, Fatima ba kiyi sallah ba kenan?” 
Fuskarta tana Boye cikin filo, muryarta da alamun kuka, ta ce, “bazan iya tashi bane
Ya daga kai da sauri yana fadin “Subhanallahi, yi hakuri ina sauri  kada jam’i ya wuce ni, bari ki gani”. 
Saiya nufi bandaki da sauri yayi sa’a heater din bandakin tana aiki,don haka da wuri ya hada mata ruwan wanka cikin baho ya koma dakin. 
Cak! Ya dauke ta kamar wata ‘yar jaririya, kunya ta sanya ta kasa bude idanunta. Yau dai Malam ya gama tsiya, domin batun kunya ta qare, shi neya sille ‘yar amaryar tasa, wani farin ciki yana Kara cika masa zuciya, k0 yaqi k0 yaso Falmata ta banbanta da sauran mata K0 kusa ba zai iya ajiyesu aji daya da Fatila ba domin daga kirar jiki har ta baiwa ta fita. Bai taba samun kansa cikin halin daya samu a daren jiya ba don ma dai yana tausayin Falmatan ganin ta daure, amma bai kyaleta don ya gamsu Tabbas yasan 
kyautar Allah ce kawai a gare shi Falmata. 
Sai da ya dawo da ita d‘aki sannan ya fice yana fadin Ki shirya kafin na gama had‘o miki abin da zakici”. . . 
Ita dai ta kasa k0 iya daga kanta balle ta kalle shi, domin tsananin kunyarsa ta keji, to daman ya ya lafiyar Kura balle ta yi hauka? 
Ba wani abu mai nauyi ya shirya musu ba, wainar kwai ce da shayi da biredi, amma duk da haka ita kam mamaki takeyi yadda akayi duk ya iya komai. Mutum mai daraja kamarsa bai cancanci ya dinga wannan aikin ba-a ganinta. Sanda ya kai abincin a gabanta kasa k0 da loma d‘aya ta yi, ya yi dariya yana fadin’. 
“Fatima nayi zaton ‘kunyar  raguwa zata yi, tunda yanzu mun zama daya. Amma sai ta kuma karuwa, don Allah ki rage kunyar nan kada ki dinga cutar da nifa”. 
Ta kasa dai motsawa, sai da ta ga‘ya mike yana fadin “Bari dai na baki a bakinki”. Sannan ta fara matsowa da sauri ya dinga yi mata dariya yana tsokanarta. . 
Gaba daya kuma hankalinta ya yi ‘gida tana jin nauyin yadda zata iya hada ido da Anti, Allah ma Ya taimaketa ba a gidansu ya daukota ba, da abin kunyar sai yafi haka. Shi da kansa godiya 
yake yiwa Allah da Ya sanya daga gidan Bulama ya daukota, domin da daga gidan sune bai isa ya kusanceta ba, dole ya maidata a daren nan koda kuwa abin da yakeji din zai kashe Shi domin zai ji kunyar idon Abba ace ya kwana gida daya da Falmata bata tare a gidansa ba. 
Amma tsananin kunya ya sanya ta kasa gaya masa amman tsananin kunya ya sanya ta kasa gaya masa abinda ke ranta  yace mata, “Kinga ki kwantar da hankalinki, Yaya Bulama tun jiya na sanar -da shi . kina gurina, kuma a nan zamu kwana. Yanzu ma mun yi waya da shi yanzu Antinki zata zo, don ba zan maidake baki gama jinya ba, dole sai kin warke sumul, babu wanda yasan muna tare bayan su”. 
Ta daga kai da sauri cike da fargaba, suna hada ido ta yi saurin maida kanta tace, “Gwara dai mu tafi gidan don Allah malam…” 
Ya yi dariya, “Yarinya kuma ai sai kiyi, sai kin warke zan maida ke gida, gwara ma ki saki ranki, kuma ki daina ce min malam din nan fa tunda ai ni ba malaminki bane Gwani Ahmad ne malaminki k0? Ni sai dai kice min DL k0?” 
Dariya, da kunya suka kamata, ta Boye kanta cikin filo. Karae wayarsa ce ta katse musu hirar ya daga da sauri yana fadin “Kin karaso ne?”. 
Shi ne ya je ya bude babbar qofar Anti Shafa ta shigo da motarta ta sami guri ta yi fakin, sannan suka shiga tare, shi kam k0 a jikinsa, namiji kc nan duk halinsu daya. Ita ce ma ta dan dinga jin nauyinsa. 
Falmata kuwa na jin sallamarta ta janyo bargo ta kudundune kanta, don ba zata iya hada ido da Antin tata ba. Anti ta shiga daga ciki ta zauna gefen gado tana murmushi ganin ta kudundune har kanta, k0 iska ba ta Shaka. 
Malam Mukhtar kam tsayuwa ya yi daga bakin kofa ya harde hannaye a kirji yana fadin
“Kin ganta nan, ni ban taba ganin mace mai kunyarta ba, haka kawai ta sanya mai jego fitowa ba ta shirya ba” . 
Anti Shafa ta yi dariya tana fadin “Malam ai kasan qanwar tawa special ce, dole tayi kunya k0?” 
Yace “Ai shi ke nan, bari na baku guri k0 ta gaya miki abunda ke damunta, tunda ni nayinayi taKi magana”. 
Sai ya juya ya fice ransa fcs! Kamar an yi masa albishir da gidan aljanna. 
Anti Shafa ta yi dariya tana fadin, “To ai sai ki bude fuskarki, wanda kike jin kunyar ya fice”. 
Maimakon ta bude sai ta kuma
Bai jira jin amsarta ba, ya fice da saurinsa. 
Anti Shafa tace “Kinga ki gaya mini sauri nake yi, na baro babyna fa a gida”. 
Ta mike da sauri tana fadin, “Allah Sarki Shahid boy dina, dama kin taho da shi”. 
Ta marairaice murya tana kwantar da kai, “Ni dai’ Anti ki ce kawai dani za ki tafi don Allah, babu fa abin da ke mini ciwo sai jikina fa”. 
Ta mike, “Shi kenan haka ake so ai, nasan malam mai ilimi ne daman, ba zai miki yadda za ki ji ciwo ba. Kada maki sanya rai za ki bini, domin sun gama magana da yayanki sai gata ma zai maida ke can gidan…” 
Ta waro ido waje “Gata Anti? Don Allah ki tadi dani, wallahi…” Sai ta yi narai-narai idonta ya ciko da kwallah, don ba zata iya fadin abin da ta keson fadin ba. 
Anti Shafa ta koma ta zauna ta dafa kafadarta,tace “Falmata ki nutsu ki nemo wa kanki soyayya a gurin mijinki, kin san bake kadai bace, kina da kishiya, mutumin da ya tsallake matarsa wacce ake ta rade raden bata da imani, k0 kallon mace bai isa yayi ba, har yazo ya kusance ki ai kin san kin karya alkadarinta, don haka ya rage naki ki kuma nemo gurin zama daram a cikin zuciyarshi, ki kwantar da hankalinki baBu wanda yasan kuna tare, kuma bazan gayawa kowa ba, ina 
sane na baki abin da zaki qara rikita shi, domin mu tabbatar mun karya alkadarin Fatila da qaryarta, kin san gidan Anti Kubra yayarsa ta sauka, ta sanar dani komai, ki yi hakuri har zuwa gatan kin ji k0?” 
Jikinta yayi sanyi ta daga kai alamar toh kawai, taci gaba da magana bayan ta dauko wani kulli daga cikin jakarta. 
“Ga wannan ki dinga sha da madara, wannan kuma a ruwan zafi za ki dinga sanyawa kina zama, zai rage miki radadi ki daure ki samo mana boy don Allah, damin mu ‘karya camin din Fatila”. 
Kunyar tata ta ‘dawo ta fada gadon ta kudundune tana dariya, Anti Shafa ta nufi Kofa tana cewa, “Shi kenan, sai gatan. Ki kula da kanki sosai, ki kuma bai wa mijinki hadin kai”. 
Har ta ficc bata iya dago kanta ba tana dariya dai, amma maganganun Antin nata sun yi tasiri a ranta, sai taji dama ta tambaye ta wace ce Fatilan da yadda take, domin tun sanda taji kadan daga halinta a bakin surukarta ta tsoronta, wato don ta tabbata ke nan. 
:::::::::::::;;;;;;;;;;;;::::
Cikin kwanakin nan da suka yi ta more 
soyayyar mijinta, ita kuma ta bashi hadin kai matuka, tabbas Mukhtar mutum ne mai tsananin iya gwadawa mace soyayya, sai dai yana da buqata da yawa, don haka sai ya zame .mata kamar cingam. Tun tana yakice shi tana tsoro har ta saki jiki. 
Sai da suka yi kwanaki biyar sannan ya fara shirin kai ta, shi ma din ba don ya so ba, sai don ya koma gida ya fara shirye shiryen tarewarta, kuma ba ya son a gane suna tare. 
Sanda ya fara tattara kayan da ya-sissiyo mata cikin wata akwati, sai taji duk hankalinta ya tashi, tana zaune tsakiyar gado ta yi tagumi tana kallonsa. Wani irin sonsa yana kara shigarta, Malam Muntari mutum ne mai kwarjini da cikar kamala, dole ya sacc zuciyar kowa, dogo ne sosai, yana da kiba, amma ba sosai ba. 
Yafi kama da yanayin Fulani, wato kamannin mahaifiyarsa, don haka ya kasance fari tas, mai dogon hanci. Gcmunsa kamu-daya ne da saje abin da ke burge ta ba a yin awa biyu sai taje gemun d‘an kuwa da madubi daga aljihunsa ya kama gcmun ya taje, yadda gemun ke shan gyara dole ya yi sheki da sulBi, gwanin sha’awa, ita kam bata taBa ganin mutumin da gemu ya yi masa kyau kamar Mukhtari ba. 
Har ya gama shirya kayan sannan ya juyo ya 
kalleta yaba murmushi ya nufeta ya hau gadon ya janye hannayenta yana dariya, da fadin
“Ya dace fa mu tashi muyi tsere k0?” 
. Ta kalle shi da sauri, “Tsere kuma mal…” Sai ta yi shiru ganin irin kallon da yakeYi mata, sai ta fashe da dariya, “To yaya”. 
“Kinga tashi na maida ke gida, nima zan dinga ce miki Malama k0 Anti shike nan mun yi duro k0?” ‘ . 
Ta Iangwabe kai, “Ka yi hakuri na daina”. 
Ya mike yana daukar jakar, “Taso mu tafi, 
ina son na shiga cikin gari kafin na wuce gobe amma dai ina son na rage wannan tunanin, Mukhtan’ naki ne, mijinki nefa, ina komawa zan sanya a yi fenti nan da kwanaki hudu za ki tare insha Allahu”. 
Haka nan ta mike jikinta sanyi kalau, sai take jin kamar kada ta bar gidan, dama za a biyota da kayan jeranta acetayi zamanta anan. 
A mota ma shi ne ke kokarin yin magana, to daman ya ya lafiyar Kura bare tayi hauka, daman ba ma,’abociya maganar bace, balle a yanzu da take cike da alhinin rabuwa da masoyinta. 
Bai shiga gidan Yaya Bulama ba ya ajiyeta yace zaije ya dawo. Haka nan ta shiga gidan, jikinta duk ya yi 
Sanyi. Anti Shafa tana falo a zaune ta jiyo sallamarta, ta mike da gudu ta tarota tana fadin, “0yoyo maman baby, kin dawo‘?” 
Ta rufe fuska tana dariya, tace, “Ni fa ba, haka bane don Allah Anti ki daina fada, babu komai fa”. 
Anti Shafa ta yi da’riya, ‘Ai na sani shiga to maza ki hada kayanki, Abba sai fada yakeyi wai kin zo kin yi zamanki ba tare da an nemi izinin mijinki ba, ban gaya masa kuna tare da shi ba. Maza shirya direba ya kai ki a qarasa soyewar a gidan Abban”. ‘ 
Ta falla daki da gudu cike da kunya tana dariya. Ba ta‘so tafiya ba don tana jin dadin zama da Shafa’atu wadda ta maye mata gurbin ‘yan uwa mata, tunda su ‘yan uwan nata ba sa qaunarta, don haka duk wata damuwarta daga Anti Shafan sai yagana sune abokan shawararta. 
Har ta isa gida tana cike da alhini na rabuwa da masoyinta, tana tafe a hanya ta tura masa da sakon ta koma gida idan ya tashi a can ‘zai-same ta. 
Tunda ta shiga mahaifiyarta ta kula tana cikin damuwa, amma da yake tasan halin abarta ba tace mata komai ba, bayan amsa gaisuwarta. Ta nufi dakinta tana shiga ta jiyo hayaniyar Yagana a falon. Tayi dariya tana kokarin cire kayanta, ta 
shiga ta watsa ruwa. 
Yagana ta fada dakin da sauri ta tsaya tana yi mata wani kallo taba dariya, tana fadin, “Kai amaryar malam kin ga yadda kika koma kuwa? Kin yi wani bulbul, lallai gidan Anti Shafa ya amshe ki k0 dai can zamu maida ke ne? Amma fa k0 malam ba zai ganki ba”. 
Ta galla mata harara tana wucewa cikin bandakin, Yagana ta yi dariya tana fadin, “Bari na duba kayan na ga irin tsarabar da aka kawo mana kawas” . 
Kusan tare suka wuni, tunda suka shiga kicin, Falmata ta fara shirya girlki, Yagana ta fara tsokanarta tana ‘dariya, “Lallai’ kice malam yana garin, shi ya sanya na ga kin yi wani sharrr daje, iye amaryar ba?” 
‘Ita dai dariya kawai take yi. Sai da aka yi kiran sallar magruba, sannan Yagana ta koma gidansu akan zata dawo su gaisa da malam din. 
Shi kam Dr. Mukhtar tun gab da magriba ya iso gidan, sai dai ya tsaya a masallaci ya yi salla, tukunna suka wuce falon Abba tare, aka dinga kawo abinci kala-kala, shi kam bai saki ciki ya ci ba don yasan gimbiyar tasa tana shirya masa dabge. sai da ya yi sallar isha’i sannan ya sami shiga gurinta. 
Sanda suka had‘u kamar ta yi tsalle ta rungume shi don murna, kullum kara burgeta yake yi, saboda ya iya tsara kwalliya, wata dakakkiyar shadda ce a jikinsa riga da wando, sai ya sanya irin rigar nan ta sarakai a ciki, sannan ya dora malummalum akai, kansa ya sha hula zanna-bular da ta zauna das a kan nashi. Gcmun nan nasa sai walkiya yakeyi, ya sha mai da gyara, fuskarsa ma’,abociyar haske da annuri, sai haske ta keyi. Ita ma taci kwalliya cikin sauka dinkin atamfa super, sai dai rigar ba ta cika tsayi ba, yau ma dai an yi sa,’a dan karamin gyal‘e ne ta yafa, koda yake ai ta fara rage jin kunyar tasa. Kamshinta gaba daya ya cika dakin, kai tsaye gurinta ya nufa sanda ta Shigo, sai ta yi sauri ta zauna ta durkusa don ta gano abin da yake shirin yi, cikin sanyayyar muryarta tace. 
“Ina wuni?” 
Ya zauna yana dariya, “Lafiya lau, wato nan gidan Abba ne ba za a dan gwada mini love din ba k0?” Ta yi dariya tana boye fuskarta, domin dai ya riga ya gama ganota. Sun sha hirarsu ta soyayya, rigima ba ta tashi ba sai da ya tashi yin sallama, ta yi narai-narai da ido sai ga kwallah, wani irin tausayinta mai tsanani ya kama shi. Tabbas ya riga ya gano irin dumbin son da take masa tuntuni 
cikin kwayar idonta, don haka tsam ya tashi ya nufe ta. Yayi mata irin rikon da yake mata kamar: ‘yar mage cikin kunnenta yake fadin
“Meye na kukan? Inace nan da sati guda insha Allah kina gidana? Ki kwantar da hankalinki kinjiko Fatina? Ko kinaso nima nayikukanne?” 
Da saurita girgizakai alamar a’a, wannan shagwaBar ke qara  ruda shi, zuciyarsa ta dinga kissima masa abubuwa da dama, can cikin kwanyarsa ya jiyo ta tana fadin
“Ammadai basau daya zaka dingakirana ba k0?” 
Yayi dariya don ya gano kumallon matan ne ya motsa, amma irin kishinta m‘a yana burge shi, yace, “Kiyi haquri zan dinga kimnki duk sanda na ‘ sami lokaci, na miki alkawarin na daina kiranki sau daya, kedai ki kwantar da hankalinki kinj i k0?” 
Ta kuma daga masa kai, da kyar suka rabu, shi kam banda gidan surukansa ne da ya nunawa matarsa irin son da yake mata, da kuma yadda yae jin kaunarta. Sai take jin ita ma kamar ta bishi, banda tana jin kunyar abin da-zai biyo baya da ta bishi, ta kuma taya shi kwana. 
A d‘akinta kasa bacci ta yi, sai juyi take a gado tana tuno malam dinta da dumbin soyayyarsa I gare ta, malam ya iya soyayya mai ratsa
zuciya, daga qarshc dai miqewa tayi ta fada toilet ta dauro alwala ta dawo ta dinga nafilfili da lazimi da yake gwana ce a gurin yi. . Shima kusan hakane takasance dashi, gaba daya Falmata ta dagula masa lissafi, harya ji ba shi da wani samin shakka akan sonta. Ya kuma shirya tunkarar Fatila da maganar kai tsaye don zai iya rabuwa da kowa ma akan Falmatn, domin sai 
yanzu ya gane meye so, ya kuma san son gaskiya yake,,,,  Kai Falmata daita tsaya aranshi. Da safe kafin ya tafi saida sukasha hirar soyayya a waya kamar wancan lokacin, don tunda suka kammala lazimin asuba suke abu daya wato hira. 
Sai dai yau gidan nasu Falmata da rigima aka tashi, domin tun daman jiya Malam Mukhtar yake gayawa Abban Falmatan nan da kwanaki bakwai iyayensa zasuzo  domin tafiya  da Falmatan. Ammn kada a tafi da komai saboda kada jigilar kayan yayi yawa, shi zaiyu mata komai. ‘ Abba yace a,a bai yarda ba yanason daidai shima yayima diyarsa wani abu  amman dai zasu bari sai anje can kanon saisu siyi komie domin kuwa tafiya da kauan kam jigila ne 
Da safe bayan ya karya ya tara matan nasa yana sanar dasu  shawarar daya yanke kamar haka , “
“Jiya mijin Falmata ya sanar dani nan da kwanaki shida zai turo ‘yan uwansa su daukar masa matarsa, yace ba ya son komai domin idan akace za,ayi jigilar kayan akwai wahala ni na yarda da shawararshi, amma na nuna masa ina son ita ma na yi mata komai kamar yadda na yiwa ‘yan uwanta. Don haka idan zaku tafi ke Hajja Kaltum zan ba ki kudin komai ki siya mata a can Kano. Wadannan kayan kuma na  zance da mahaifin Yagana su turo su diba, domin dai ba mu da sauran ‘yanmata da zamu sa ran a ajiye mawa k0 ya ya kuka gani?” 
Tunda ya fara maganar Hajja Yakolo da Hajja Basma suka hade rai, domin tun jiya da suka ji Mukhtat yazo hankalinsu ya tashi musamman ‘da suka ga bai bar gidan ba sai can wajen sha biyun .dare. Sun san sun gama dai-daita kansu ke nan. ‘ ‘ 
Hajja Yakolo ce tayi tsagal tana fadin, “Gaskiya malam wannan zalunci ne, kudin da zaka kashe a sayi wasu kayan ai ba su kai yawan kudin da za akai kayan Kano ba, idan dai ba wata dabara ce aka fito da ita ba domin a ware diyar gwal ba, mu kam ba mu yarda ba ko Basma?” Ta kalli Basma wadda tayi saurin daga kai tana cewa. 
“Ni a su wa? Ai mu ‘yan kallo ne, harka ce ta masu ‘ya’ya. Amma dai kowa yasan wannan salo 
ne na a raba kan yara dai”. 
Yayi dariya, idan da sabo ai ya saba da halin matan nasa, ya sake gyara zama yace “Ai ba maganar kashe kudin kawai ake miki ba, maganar wahalar kai kayan daga ni har shi Muntarin ai ba mu da takaicin kudi. Kuma don kudi nane duk abin da zakuce ba zai dame ni ba, domin duk ‘ya’yana daya na dauke su, tunda ni na haifi abina”. 
Ya mike tsaye, “Ni ‘ina da gurin zuwa, sai anjimanku”. Ya nufi kofa da saurinsa. ‘ 
Hajja Yakolo ta mike ta yiwa sauran kallon banza tana fadin, “Oho dai, duk munafurcin dodo  Na mai shi ne, kuma a yi mu gani idan tusa zata hura wuta”. Sai taja wani dogon tsaki ta wuce Hajja Basma ‘yar koro tana biye da ita, su kam sauran abin dariya ma ya ba su. 
A can d‘aki bayan sun kule Hajja Yakolo ta yi tagumi tana fadin, “Ai ni daman nasan da gayya aka shirya wannan auran, domin ki duba tun washegarin da aka kai su Yakura suke min waya suna kuka, banda Zahra wacce ta sami gidan zama mai kyau? Ai ke kinje kin gani, ita kuma Falmam har wani shiri ake mata, kina kallon yadda mijin nata ke bin iyayen nata kamar zai musu sujjada, to wallahi bazan yarda ba, duk dan da ya hana uwarsa 
bacci shi ma kuwa ba zai runtsa ba, dole nayi duk Wani abu da zan ga bayan auren nan, muddin ina raye Falmata ba zata taba tarewa a gidan Muntari  ba, balle har su sami abin da suke so”. , 
Hajja Basma tace, “Ahaf! Ai daman kallonki nake yi, haka kawai kin zauna kina kwasar bakin ciki da arziqin kanki da komai, gwama ki mike ki nemarwa ‘ya ’yanki da ke kanki ‘yanci wallahi. Ni da ace ina da‘ ya ’ya ai da bazan yarda a 
yi min wannan cin kashin ba”. Ta dinga zuga Hajja Yakolo tana hawa har
ta yanke shawarar ziyartar bokanta a gobe don yayi mata maganin abin. 
Hmmmmmm to masu iya magana dai sukace sannu sannu bata hana zuwa mun kammala littafi na daya
Admin yace, “Allah Ka shirya, Ka raba mu da matacciyar rayuwa”). 
Mu hadu a na biyu. 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE