MATAR SHEIKH COMPLETE

MATAR SHEIKH COMPLETE

SOMIN TABI.( something like_prologue or so😂💔).4 2014. Kano, Nigeria. Kallon kwalaben da ke gabanta tayi amma bata iya karanta komai daga jikin su. Idanunta sun kada sun yi ja wur, kanta har wani juyawa yake tana ganin abubuwa uku uku. Hannu tasa ta dauki wata kwalba da babu komai a cikinta, ta bude wata da bata ma iya karanta sunan ta zuba rabi a kwalbar da babu komai ta ajiye hannun ta na rawa. Wata kwalbar ta bude ta hade da wancan rabin ta jijjiga sannan ta shanye duka. Cikin mintuna kadan ta sake buguwa sosai kasancewar magungunan sun ratsa mata jiki sosai. Duk da a yanayin maye ta ke, tana iya tuno dalilin da yasa ta fara shaye-shaye. Zafafan hawaye ne suka zubo daga idonta tana dana sanin rayuwar ta. A haka dai tana tunane-tunanen hankali da shirme da ma wanda magungunan ke kitsa mata su, bacci ya dauke ta. **** Hoton dake hannunsa ya ajiye yana ajiyar zuciya. Har izuwa yaushe ne zai manta da matar sa, Jamilah? Anya zai manta da ita kuwa? Jijiga kansa yayi hawaye na neman zubowa daga idonsa. Qarar wayarsa ne ya katse masa tunani. “Ya Sheikh, jiranka akeyi.” Yaji Sheikh Usama ya fada. Sannan ya tuna ashe ana jiransa zasu je da’awa a wani qauye. A gaggauce ya shirya ya fice yana kewar matar sa da ta rasu shekaru goma baya. **** Sheikh Muhammad Salim shine sunan sa. Babban malami wanda ake ji dashi saboda tarin ilimin da yake dashi. Toh amma kafin ya zama abun da yake a yanzun, ya aikata abubuwan da yake da na sani akan su sosai da sosai. Zamu iya cewa rayuwarsa ta baya akwai matsala a cikin ta. Domin kuwa ya dauki alhakin mutane da dama. Ya muzantawa mutanen da ya kamata ace yafi kyautatawa…. Abubuwan da yawa sai kawai mu zuba ido mu karanta a cikin littafin…. Salmah Bello sunan ta kenan. Mai shaye-shaye a miskilance ba tare da ansani ba. Sai dai an ce komai yana da dalili. Ko meye dalilin da yasa ta fara shaye-shaye? Yaya zata kaya a yayinda na tsinci kanta a matsayin matar Salim wanda bata san komai game dashi ba? Yana da tabo a rayuwarsa. Sai dai kuma na ta tabon ya taka nashi ya karya! Taya wadannan biyun zasu zauna tare? Taya Salmah zata yi haqurin zama MATAR SHEIKH bayan ta fahimci zaman da Salim yayi da matar sa JAMILAH? Labari ne daban, me tarun darussa da yanayin tafiyar da rayuwar yau da kullum. Zamu yi dariya, zamuyi kuka, zamu dauki darasi in sha Allahu. A tafiyar zamu gamu da mutane kala-kala zamu leqa labarin rayuwarsu domin mu tsinci abun tsinta, mu watsar da marar kyau. Daya daga cikin tiyatocin jami’ar cike take dan’kam da dalibai suna ta kai komo. Kowannan su yana harkar gabansa. Wasu kuma suna zaune a gefe suna danna wayoyinsu, wasu suna hira da abokansu wasu kuma sunyi shiru suna jiran isowar manya manyan malamin garin. Wani taro na qarawa juna sani a kan addinin musulunci zasuyi da kuma qara fadakarwa da waye wa jama’a kai akan abubuwan da su ka musu duhu. Zaune take ita da qawayen ta suna ta hira abunsu. Daya daga cikin su ce take ta tsaki tana duban agogo. Ita Allah ya gani bata son taro irin wannan. “Wai dan Allah malaman nan ba zasu qaraso bane? Nifa na gaji.” Ta fada tana bin qawayen nata da kallo. “Hmm ki bari kawai nima tun dazu baya na ya gaji da zama.” Dayar ta bayar da amsa. “Ke dalla malama kina jin mu amma kinyi shiru duk ke kika jawo muka zauna fa.” Dayar ta buge kafadar Salmah. Salmahn ce ta dan sosa wajen kafin ta ajiye wayarta a cikin jaka ta kalle su.+ “Toh ni yanzu da kuka kafe ni da ido me kenan? Ban fa ce dole ku zauna ba nima saboda bin umarnin Ummah zan zauna.” Ta tabe bakin ta tana mayar da idonta kan mutanen da suke shigowa. “Kullum maganar kenan, sai ta dinga yi kamar wata salaha, kamar irin ta fimu sanin Allah amma kuma duk kanwar ja ce.” Qawarta ta mayar mata da magana, taja hannun dayar suka fice suka bar ta. Ko ta kansu ma bata bi ba ta cigaba da kalle kallen ta. Duk kanwar ja ce… Abun ya dawo ya tsaya mata a wuya. Tabbas ba qarya bane to amma me yasa zaiyi mata ciwo? Jijjiga kanta tayi cikin dana sani da kuma cewa ina ma zata iya mayar da hannun agogo baya. Ta na cikin tunani, sai ji tayi ko ina yayi tsit, kafin ta ankara taji ana gyaran murya a lasfika. “Bismillah, wassalatu wassalamu ala rasulillah…” Tun kafin ya qarasa taji lallai tana son ganin fuskar mutumin nan amma bata samu damar hakan ba saboda mutanen da suke gabanta sun kare ta. Haka dai ta zauna don dole tana jira a gama ta tafi. Tsawon awanni biyu ne suka shude kafin malaman su tafi ba tare da taga ko daya a cikin su ba. Ita dai taji wannan me muryar da taja hankalinta yace sunan shi SHEIKH MUHAMMAD SALIM. ***** Sauri sauri takeyi ta qarasa gida saboda ta huta. Yau tayi bala’in gajiya. Tana shiga gida ta tarar Abba yazo gida, ta gaishe shi zata wuce kenan sai taji ya ce ta dawo, sai da gabanta ya fadi kafin ta sunkuyar da kai ta nemi waje ta zauna. “Ina kika tsaya?” Ya fada idon shi a kanta. Yana daga cikin qa’idojojinsa akan lallai sai mutum ya dawo daga makaranta akan lokaci. Qarin minti sha biyar kadai ya bayar. “Ah, ni nace ta tsaya ta saurari lakcar da malamai zasu yi akan addini.” Ummah ta fito daga kicin tana goge hannunta da wani tsumma kafin ta nemi waje ta zauna. Wata ajiyar zuciya Salmah tayi kafin ta miqe ta bar wajen tunda an bashi amsar tambayar sa. “Wannan tsaurin da kake mata fa bashi da wata rana.” Ummahn ta fada tana kallon Abban da kamar ba hankalin sa ba akanta ya ke ba. Numfasawa yayi kadan. “Kullum haka kike cewa amma ni na fiki sanin wacece Salmah.” Ya miqe tare da daukar hular sa da ya ajiye a kan tebur din tsakiyar falo domin fita sallahr Maghreb. “A dawo lafiya.” Ta fada a taqaice tare da barin wajen itama. Jim kadan, sai ga Muhammad ya shigo da abokanan sa suna ihu. Bangaren sa ya wuce da su suka kunna talabijin. Tana kamawa aka kai tashar ball. Kafin mintina biyar, gaba daya sun cika gidan da hayaniya suna ta ihu. Salmah ce kwance a dakinta tana qoqarin yin bacci amma sabida hayaniyar su sai ta kasa. Shikenan ace duk daren duniya sai an ishe su da ihu, tab lallai yau kam sai tayi musu magana. Hijabin da ya tsaya mata dai dai gwiwarta ta saka ta nufi falon da suke kallon. “Yaya,” ta kwalla masa kira amma kamar ma be ji ta ba. Tsaki tayi ta nemi inda rimot din yake, sadaf sadaf ta dauka sai ji sukayi an kashe TV. “Ke! Kina hauka ne?” Ya daka mata tsawa har sai da gabanta ya fadi amma ta dake. “Barci fa nake ji amma kun ishe ni da ihu. Ni gaskiya…” Katseta yayi. “Dalla malama bani remote dinnan tun kafin ranki ya baci.” A sanyaye ta miqa masa tana qunquni. “Bace mun da gani.” Ya yi mata nuni da bakin qofa ta juya zata tafi. “Woooo maza kana wuta wallahi.” Daya a cikin abokan ya daki bayan sa. Duk suka kwashe da dariya. Hawaye ne ya taru a idonta, nan da nan ya fara zubowa. Ita kam a duniyar nan ta tsani a ci mata mutunci a cikin mutane sannan ayi mata dariya. Toh yau ba abin da Muhammad yayi mata bane ya bata mata rai, sai dai kawai ya tuno mata da abunda ya taba faruwa da ita wanda duk gidan babu wanda ya sani. Saboda shima abun, anyi embarrassing dinta ne sosai da qasqantar da ita. Juyi takeyi a kan gadon baqin cikin yana qara taso mata. Ta rasa inda zata kanta. Sai kawai ta tuno wani abu. Ta dauko jakar ta a qarqashin gado ta fiddo da wasu kwalabe tana qura musu ido. ‘Kar ki sha!’ zuciyar ta ta raya mata. ‘Ki sha kiji sauqi a ranki.’ Wata zuciyar ta ayyana mata. Runtse idonta tayi tana tunani wace zuciyar zata bi. Kusan minti biyu tayi tana nazari kafin ta bude kwalbar ta kwankwade qwayar dake ciki. Babu bata lokaci, ya gwaraye mata jiki, taji yana fisgar ta. Ba shiri taji duk wata damuwar da ke damun ta ta bace, driving her out of the real world. A world, full of deceits! **** A hankali jikinta ya fara motsi, tana jujjuyawa kamar jikin nata ciwo yake. Hasken rana da ya bullo ta windo ne ya haske mata ido hakan yasa ta kasa bude idon nata da wuri. Sai da ta dan bude daya a hankali, sannan ta kalli hannunta wanda taji yana mata zafi zafi sai ta ankara ma allurar qarin ruwa ce a jikinta. Zumbur ta tashi a tsorace tana kallon gefen ta inda wata mata itama take barci. Me ya kawo ni asibiti? Ta tambayi kanta tana kalle kalle kamar wacce ta samu tabin hankali. A hankali ta fara tuna abun da ya faru. Runtse idonta tayi cikin fargaba. Allah yasa dai ba’a fadawa su Ummah dalilin sumar ta ba. Tana cikin wannan tunani ne zai taga an bude kofa. Likita ne, wani saurayi kyakkyawa da zai wuce shekara talatin ba ya qaraso wajen ta yana dan murmushi. Kau da kai tayi domin ita a duniyar nan babu wanda tafi tsana kamar namiji. Musamman ma idan yana nuna mata kula Sai taji duk ta tsani mutum. “Sannu ko? Ya jikin malama…?” Ya qarasa tambayar yana neman yaji sunan ta. “Lafiya lau. Ina su Umma?” Ta tambaya ba tare da ta bashi amsar tambayar ba. Kafin ta sake yin maganar sai ga iyayen nata sun shigo. “Alhamdulillah. Likita me ka gani a test din?” Ummah ta tambaya gami da rungume Salmahn. “Gajiya ceh, depression, da kuma…” Sai ya mayar da kallonsa zuwa Salmah. Kallon da yake mata ne yasa ta sha jinin jikinta. Bata ankara ba taji zuciyarta na dukan uku uku a lokaci guda. Yau idan likitan nan ya tona mata asiri ya zatayi? Tab lallai yau tana cikin matsala. Itama kallonshi ta shiga yi tana me roqon sa ta idonta. Murmushi yayi, haka kawai sai taji hankalinta ya dan kwanta. Allah dai yasa bazai kwafsa ba. “Sai kuma wataqila rashin barci. Amma ga magunguna da zaki siyo a waje Ummah.” Ya miqa mata wata takarda. Da sauri Ummah ta karba tayi waje ya rage daga Salmah sai likitan sai wasu masu jinyar kuma. Zagayo wa yayi, ya duba gudun ruwan da ake kara mata kafin ya gyara muryar sa. “Me yasa kika sha qwaya?” Ya tambaya cikin wani irin salo da yasa jikinta ya fara rawa. Bata taba samun wanda yayi mata wannan tambayar ba kuma ba tajin zata iya bayar da amsar tambayar ko da kuwa tilasta ta za’ayi. Kallon ta yayi, ya tabe bakin shi kafin ya sake magana. “Idan baki fada ba fa zan gaya wa Ummah saboda naga alama kamar basu san halin da kike ciki ba.” A razane ta daga kanta tana kallon shi. Gaba daya ma ta rasa ta yanda zata yi mishi magana. Itakam ta sani cewa idan Ummah taji labarin nan kwanan ta ya qare. The day Ummah will find out that she was using drugs was her biggest nightmare. She would do all it takes taga cewa ta boye wannan halin nata. Gyaran muryan da likitan yayi ne ya saka ta dawo daga duniyar tunani. Toh yanzu shi me yake so tace masa? “Ehmm, daman… Dan Allah ko zaka iya mantawa da wannan tambayar?” Ta fada a hankali. Shi kuwa likitan kallon fuskarta yakeyi sosai yana mamakin me zai saka kyakkyawar yarinya kamar ita shan qwaya. “Da alama dai so kike su Ummah suji labari. Then, it will be easier.” Ya juya zai fita sai ga Ummah nan ta shigo. Hadiyan yawu Salmahn tayi tare da hade hannayan ta biyu a boye tana roqon shi. Gyada kai kawai yayi ya juya ya fita yana tausayin ta sosai. STORY CONTINUES BELOW “An gaya miki boko ba addini bace amma kin qi ji. Shin yaushe zaki dena karatun hauka ne? Ko sai kin kai kanki kabari kafin lokacin ki ne?” Ummah tasha yi mata fada akan zaman daki wanda take tunanin idan Salmahn ta zauna to karatu takeyi. “Ummah idan na fadi kuma fada zakui min fa.” Ta fada a shagwabe tana turo baki. Ita kam Salmah tana sane da duk abinda takeyi. Wasu lokutan ma sai ta sha qwayar ta ta kwanta, sai ta kifa littafi akan fuskarta dan ayi zaton ko karatu ne ya saka ta barci. Lokuta da yawa kuma rike littafin take hannu. Ita kuma Ummah da ta leqa dakin ta ganta da littafi, sai tausayinta ya kamata. If only she knows the truth. Sun danyi shiru ne, aka turo kofar dakin a hankali. Gaba daya suka mayar da kallonsu zuwa qofa. Anty Samirah maqociyarsu su ka gani ta shigo da manya manya filasai da alama abinci ta kawo. Anty Samirah mace ce mai kirki da son taimako. Ita daman bata da da ko ya ko daya, da wannan dalilin yasa take son ko wani yaro ko yarinya. Sannan kuma idan taga mutum babu lafiya tana iya qoqarin ta taga ta taimake shi. “Anty Samirah ina wuni.” Salmah ta gaisheta bayan sun gama gaisawa da Ummah. “Lafiya lau, ya jikin?” “Da sauqi.” “Toh Allah ya qara sauqi.” Ta fada tana zuba musu abinci. A haka sukaci suna hira. Da yamma tayi aka sallami Salmah ta tafi gida. Amma fa kafin ayi musu sallamar sai da likitan yayi dabara ya karbi nambar Salmah. Ranta bai so ba amma saboda kar Ummah tayi magana ya sa ta bashi. **** Bayan kwana biyu Salmah ta warware sarai har ma taje gidan kitso ta dawo. Suna zaune suna cin abincin dare neh sai Muhammad ya gyara murya yace. “Ummah misali ace wadda nakeso tana shan qwaya zaki barni na aure ta?” Duuum. Salmah taji gabanta ya fadi musamman ma da taga kallonta yake. When you’re guilty… You know. Lol. Ummah ceh ta buga salati sannan ta riqe haba tace, “Er qwaya! Tazo tana maka maye a gida? Allah ya kiyaye.” “Toh misali ace yaudarata tayi sai bayan na aureta na gane. Kuma ko a gidansu ma ba wanda ya sani fa?” Wai meye hakan ne? Me yasa yake son ci mata mutunci ne? Shi babu rufin asiri a lamarinsa? Salmah’s heart was literally burning and threatening to break it’s confines. “Wallahi sakinta zaka yi babu ruwana domin ba zaka gurbata tarbiyan yaranka tun wuri ba.” Ummah ta fada tana gatsine. Salmah ce ta gaji da jin zancen. A masife ta fara magana bata sani ba. “Haba dan Allah dan annabi. Ku ka san ko meye zai kasance dalilin shiga halin da take? Ko kuwa littafin qaddara a hannun ta yake? Gaskiya Ku sake tunani.” Har ta ida maganar numfashinta yana sama sama. “Ke kuma meye na tsarguwa?” Muhammad din ya jefe ta da tambayar da ta sa hantar cikin ta ta kada. “Ni ban tsargu ba. Kawai akwai wadda na sani ne… Amma kar ka damu ba sai kaji labarinta ba.” Ta fada gami da miqewa tabar abincin a wajen.1 The place suffocates her! Tana shigewa daki, ta zauna ta fara rusa kuka har barci yayi gaba da ita. **** Washe gari Salmah tayi iya qoqarin ta ta tabbatar basu hadu da Muhammad ba ko a wajen cin abinci. A gaggauce ta shirya ta fice saboda daman lakcar safe ce da ita. Tana zuwa makaranta ta tarar da qawayen nata zaune a qasan wata bishiya suna hira. Tayi mamakin ganin su bayan kamata yayi ace suna aji a wannan lokacin. STORY CONTINUES BELOW “Yoo girls!” Ta qarasa tana daga musu hannu. “Kunji sabuwar sallama daga wajen uztaziyar cikin mu. Yoo Salmah ya kike?” Sa’ada ta tambaya in a sarcastic way. Salmah ce ta harare ta kafin ta zauna. Ita ta rasa me yasa Sa’adatu take yi mata irin wannan abun. “Ya kuka zauna anan?” Ta tambaya tana kallon gefe inda taga wasu fuskokin da ta sani. “Ai an fasa lecture yau. Kinsan ashe malaman nan basu tafi ba. So, yau ma zasu sake lakca karfe goma shine muka fito nan saboda ana can ana yiwa tiyatar kwalliya kamar wanda za’ayi wani biki. Hmm.” Raudah ta bayar da amsa tana dage girarta hade da yatsina fuska. Salmah wadda ta ji dalilin ne ya saka kawai ta tsinci kanta cikin farin ciki. Tabbas ko Ummah bata tilasta ta zama ba tana son zama. “Yanzu wannan sheikha zata ce sai mun zauna.” Sukayi wa Salmah gatse. “Babu dole fah. Zaku iya tafiya.” Ta fada ranta a bace. “Salmah matso kiji dan Allah.” Matsawa tayi kusa da Raudah tana jira taji me Raudah zata gaya mata. “Ko kina da abun?” Tsaki Salmah tayi ta zata ma wani abun kirki za’a gaya mata. Sai kawai ayi mata zancen syrup. Ita Allah ya sani ba’a son ranta takeyi ba kawai saboda ya riga ya zame mata jiki ne. “Dallah malama ki rabu dani.” Ta tunkude kawar ta ta. “Ke da anyi maganar abun sai ki kama turbune fuska. Ni na dora miki?” Wasa wasa sai fada ya barke tsakanin su har ma da sauran. Baram baram sukayi dasu. Salmah barin wajen tayi tana sharar qwalla. Ji tayi kamar ta fasa ihu a lokacin amma sai ta danne zuciyarta ta wuce masallaci ta zauna kafin lokacin zuwan malaman yayi. *** Kamar wancen lokacin, yau ma an cika maqil ko ina mutane ne. Wannan karan kuwa Salmah a gaba ta zauna. Ba a jima ba malamai suka zo suka fara gabatar da kansu a karo na biyu. Sunyi lakca me ratsa zuciya sosai har yasa da yawan mutane suka share hawaye. Salmah kuwa ji tayi gabadaya duniyar batayi mata dadi. Malamin da ta tun a wancen karan ya birgeta wato SHEIKH MUHAMMAD SALIM ya dade yana magana. A qarshe ya fara karanto suratul mu’uminun yana fassarawa. “Allah yace qad aflahal mu’uminun wato lallai mumuninai sunyi nasara. Allah dai tsaya a nan ba sai da ya fada mana su waye mumunai. Ya jama’ar wajen nan ku bani hankalin ku kuji ko kuna cikin mutanen nan.” Ya fada yana kallon ko wace fuskar da idon sa yake iya gani. A hankali idonsa ya fada kan Salmah wadda da ka kalleta kasan hankali ta a tashe yake. Sadda kanshi qasa yayi ya cigaba. “Allah ta’alah ya qara da cewa Alladhina hum fi salatihim kashi’un. Wannan ayar ba wai ta tsaya kan maganar masu yin Sallah ba. A’a, idan kana sallahr kana yin ta da tsoran Allah? Ma’ana idan kana yi kana qaddarawa a gaban ubangiji kake? Shin kana tara hankalin ka waje daya ko kuma kawai yi kake kana tunanin abun duniya? Ya dan uwa, minti biyar kacal ya ishe ka kayi sallah raka’a hudu. Idan har zaka iya awa biyu kana hira me zai rage ka idan ka cire minti biyar? Wasu sai ka ga ma Sallahr kawai yi sukeyi dan kar ace basuyi ba.” “Idan kana Sallah, kana nutsuwa kaji karatun sallar na ratsa ko wacce kofar jikinki ko da kuwa baka gane abunda kake cewa? Shin idan kana Sallah kana karatun a nutse ko kuwa karatu kake kamar sautin injin markade, birrrrrrrrrrr birrrrrrrrr.” Dariya aka kwashe da ita kafin ya cigaba. “Wallahi akwai watarana na fito zanje masallaci na tarar da wasu samari a gefen titi suna hira. Har na je na dawo. Ko da na dawo na tarar basu tashi ba sai nayi musu magana. Nace kunyi Sallah kuwa sukace basuyi ba. Na tambayi dalili. Wa’iyazubillah. Kun san me suka ce min? Wai customer sai da bashi. A lokacin sai da naji wani ciwon kai. Wato a duniyar nan akwai wanda yake tunanin in yayi Sallah saboda jin dadin Allah ne. Shin bamu san cewa Sallahr nan da duk sauran ibadu kan mu mukeyiwa ba?1 Har takai ta kawo wani idan kana masa wa’azi kana cewa yaji tsoran Allah ce maka zaiyi wai no space. Dan Allah wannan wace irin lalacewa ce haka? Muji tsoran Allah mu gyara tun kafin lokaci yayi halinsa. “Allah ya qara da cewa Wallazina hum anilagwi mu’uridun. Wadanda suke basa kusantar munanan kalamai.” “Yan uwana musulmai, muna cikin wani hali a wannan zamanin. Zagi, ashar, batsa duk sunyi yawa kuma an dauke su ba komai ba. Yanzu sai ka ga wani ance masa ubanka amma dariya zaka ga yana yi. Kaji ana fxck you amma cika zai dinga yi yana botsewa a lallai shi ya burge an kira shi da shege. Me yake faruwa? Ina muka bar tarbiyar mu? Shin bama so mu kasance cikin muminai wadanda sukayi nasara?” Ya fada muryar sa na rawa yana neman ya fara kuka.1 Nan da nan dalibai suka fara Allahu Akbar kafin ya cigaba. “Yanzu kuma ya zame mana jiki. Muyi gulma, muyi annamimanci, munafurci, cin naman mutum duk ba tare da jin komai ba. Abun har ya kai ga kaga yan uwan juna, uwa daya uba daya suna gulmar junan su ina ga bare? A hakan muke so mu shiga aljanna? ‘Yan uwa ku tuna cewa ranar alkiyama Allah zai iya yafe maka wani abun wanda ya ke tsakanin ka dashi amma banda haqqin wani. Yau idan akace kaci naman mutum yazo yaqi yafe maka ya zaka yi? Mu sake tunani ayyuhal ikwaat.” Ya matse kwallarsa ya cigaba da fassara har sai da yazo qarshen bayanin siffar muminai. Yace ” Lallai wadannan da muka lissafo sune magadan aljannah firdausi. Sune wadanda zasu shige ta har abada. Ya dan uwa, yanzu zabi ya rage naka. Ka zauna kayi tunani. Kai mumini neh? Idan ka ga kana da wata matsala sai kayi hanzarin gyarawa tun kafin lokaci ya qure domin idan lokacin mutuwar rai tazo Allah baya qara ko da kuwa sakan daya ne.” A lokacin da ya rufe lakcar tashi hawaye yake sosai har sai da ya samu wajen zama. Salmah kuwa gaba daya mutuwar zaune tayi domin gaba daya abunda ya lissafo babu wanda takeyi. Eh toh, tana Sallah amma banda kamar yanda ya kwatanta ba. Dungure dungure takeyi. Wasu lokutan ma tv na gefe tana Sallah tana jin abunda ake fada. Wasu lokutan kuma Allah Allah take ta idar ta koma kan gado. Yanzu ya zata yi? A hankali dai lokaci ya qare malamai sukayi jawabin bankwana suka fara fita. Salmah wadda qafarta tayi sanyi ne, ta bisu a hankali ta samu sheikh din da ya fi burgeta. “Ya sheikh.” Ta fada. Ai kuwa tayi sa’a yaji ta. Gaisawa sukayi kafin tace tana buqatar number sa saboda zata so yin magana dashi akan wasu abubuwa. Bude jakar sa yayi ya ciro wasu kati guda biyu ya bata. “Ya sunan malamar?” “Salmah.” Ta fada a taqaice tana jin wani irin yanayi a zuciyarta. “Salmah.” Shi ma ya fada. Har tsakiyan kanta taji sunan. Ya fade shi tamkar a bakin sa aka tsara sunan. Ko wani harafi sai da ya bashi haqqinsa. Ita kam bata taba jin dadin sunan ta ba sai yau. “Nagode ya sheikh.” Gyada kai yayi ya tafi. Yana matsawa sai taga ya yarda wani koren littafi me ban sha’awa. Dauka tayi ta bi bayan sa da zimmar bashi sai ta neme shi ta rasa. Bude fejin farko tayi taga wani rubutu mai kyaun gaske. Suna na Jamilah wadda aka fi sani da MATAR SHEIKH wannan shine tarihin rayuwa ta tun daga farko har zuwa aurenmu da sheikh. Gudun zuciyarta ne ya qaru tayi saurin rufewa gami da jefa shi a cikin jakarta. Har ta koma gida tana tunanin lakcar yau da akayi da kuma koren littafin dake Jakarta. ****** A kwance yake, idon shi na kallon sama ya na nadamar ko wacce rana a rayuwar zaman aurensa da Jamilah. Ko kadan bei kyauta mata ba har ta koma ga mahallicinta.+ Ko zuwa yaushe neh zai ji sanyi a ransa? Oho. Tashi yayi, yayi alwala yayi raka’a biyu kafin ya dauko laptop dinsa ya shiga site din su na malamai inda ake turo musu tambayoyi anonymously. Site din baya nuna sunan mutum. Tambayar farko ya fara karantawa. -Ya Sheikh na kasance tunda nake ban taba Sallah ba. Idan na fara yau Allah zai gafarta min? Fara typing amsa yayi yana me yiwa al’umma adduar shiriya. Ya dade yana duba wa yana amsawa. Nan ya dada jin kewar matarsa. Yau da tana nan ita zata karanto masa kuma duk da haka ba godewa zaiyi ba. Ina ma zata dawo ya gaya mata yayi appreciating efforts din ta. Ina ma! Wani saqo ne ya ja hankalinsa. -Ya sheikh inaso na kashe kaina saboda ina ganin kamar bani da wani amfani. Tsayawa yayi chak, ya dauke hannun sa daga kan laptop din yana tauna maganar da zai bayar a matsayin amsa. Wannan me yayi zafi haka? Har ma mutum yake tunanin daukar ran shi. Number sa ya rubutawa me saqon yace a kira suyi magana. Yana gamawa, ya dauko jakarsa yana neman littafin da Jamilah ta rubuta amma ko sama ko kasa ya nemi littafi ya rasa. Ya duba, ya bincika amma littafi yace dauke ni inda ka ajiye ni. Yaji babu dadi, domin karanta littafin ne ya ke rage masa kewarta. Dama ta bar yara neh toh, da sai ya dinga kallonsu yana jin dadi. Toh babu, kuma duk a sanadiyar lefin sa ne. Kash, shi kam yayi wa rayuwarsa tabo mara goguwa. But unfortunately no traces of her left except the one lingered to his memory. Haka dai ya cigaba da zaman kadaici na kusan awa guda. Ya shiga wannan tunanin ya fita. A qarshe dai ya yanke shawarar zuwa wajen mahaifiyarsa. Shiryawa yayi cikin kananan kaya yayi kyau sosai. Mukulin motar sa ya dauka ya fice. *** Ko da ya isa gidan, tarar da maman tashi yayi tana hutawa. Gidan yayi shiru sosai yau babu yaran maqota da suke leqo mata saboda duk ta aurar da yaranta. Gida ne dan dai dai. Da bishiyar mangoro a tsakya, gefe kicin. Daya gefen bandaki sai daki guda biyu. A soro kuma kafin ka shigo akwai kejin da take kiwon kaji da tattabaru. Ita kadai take zaune. Wasu ranakun kuma idan an samu wuta sai ta kulla qanqarar siyarwa ko dan ta dinga jin motsin rai. Rediyonta ta kashe da ta ga shigowarsa. Gayshe ta yayi ta amsa masa a daqile. “Lafiya Hajiya?” Ya tambaya duk da kuwa yasan bai kamata ya tambaya ba. “Da ba lafiya ba, zaka ganni haka?” Sosa kai yayi. “Naga kamar kina mura?” “Kalau nike.” Ta bashi amsa tana hararrrasa. Duk da kuwa tace qalau take sai ya miqe ya fice don ya siyo mata magani. Ya kasa gane wani irin zuciya ne da mamansa. Ace abu shekaru dayawa amma taqi sakin jiki dashi? Tace ta yafe masa amma shikam bai ga alamar hakan ba. Wasu lokutan sai yayi tunanin mayar da ita garinsu cikin yan uwan ta. Amma idan ya tuno yanda sukayi zaman a baya sai ya fasa. A haka dai ya shiga cikin unguwa domin neman mata magani a kemis. Duk kemis din unguwannin ya zaga bai samu ba hakan yasa ya shiga mota zuwa Lamco pharmacy a gyadi gyadi. 1 STORY CONTINUES BELOW **** Ta dade a kwance tana tunanin duniya. Shikenan haka ita zata qare rayuwarta? Zama tayi tana kallon mudubi. Kallon kan ta takeyi a mudubi tana mamaki. Kallon yanda fuskar ta ta chanja launi, idon ta ya kada ya soma chanja kala daga fari zuwa ja-ja. Wannan wace irin rayuwa ta daukarwa kanta? Tana matuqar nadamar halin da take ciki sai dai baya bazata taba gyaruwa ba. Shin yaushe neh zata dawo cikin hankalin ta? Sau da dama tana tunanin ta bar mugun halinta amma da an kwana biyu sai ta cigaba. Wannan masifar har ina? Ita kam gara ta kashe kanta kawai ta huta da baqin ciki. Hakan yasa ta dauko wayarta ta shiga site din da ta gani a katin da sheikh ya bata. Da sauri ta rubuta saqon ta tura tana hawaye. Ba’a jima ba aka bata amsa. Nambar malamin ta gani. Kwafa tayi a wani littafi sannan ta mayar jakarta. A sannan ne ma ta tuno da wannan koren littafin. Hakan yasa ma ta dauko shi. Tayi kamar minti biyu tana wasiwasin budewa kafin ta bude. Feji na biyu ta bude. Zata fara karantawa kenan taji an bude kofar dakin ta. Sauri tayi ta ajiye. “Zo ki siyo mun magani a Lamco.” Ummah ta bata umarni. Gyada kai tayi tana murmushi. Neman hijabin ta tayi har qasa ta saka. Ta nemo niqab dinta shima ta saka. Ita Allahn da yayi ta ta tsani kallo haka kuma bata cika son magana ba. Da yake wajen saida maganin a bakin titi yake, shiyasa ta rufe fuskarta. Tana fita ta tarar da majalissa kala kala. Idon kowa a kanta yake har sai da taji tana harhardewa kaman zata fadi a qasa. Kafin ta wuce taji yace ‘ko yau kuma wani munafurcin ne ya sa ta saka niqabi oho’. Wani ne ya bashi amsa da cewar wai tsabar munafurci ne. Ita dai bata tanka musu ba kawai tayi wucewar ta. Tana zagayawa har ta iso kemis din. Shiga tayi ta siya abunda zata siya. Har ta juyo zata fito taji ana mata magana. Mtsww, dan masifa ma mutum ya saka niqab baza’a kyale shi ba. Ta fada a ranta gami da juyowa. “Kin yar da chanjin ki ne.” Wani ya miqa mata. Juyowa tayi a hankali. “Nagode.” Kallon idonta yayi. Nan take yaji wani abu a zuciyarsa. Ita ma kallon sa tayi ta dauke kai. Ita bata gane cewa sheikh dinnan bane haka nan shima bai gane ta ba. Suna tsaye wata mota ta zo wucewa da gudu ta fesa musu ruwan cabi. Ay kuwa farar rigar da sheikh yasa duk tabi ta baci. Tsaki Salmah tayi gami da zagin wanda ya wuce. “Allah yana tare da masu haquri. Kiyi haquri. Ko kinsan inda zan samu ruwan wanke rigata?” Ohhh! Wai shi mutumin nan bazai fahimci cewa bata san yin magana da shi bane? Kai! “Muje.” Kawai tace, ta fara tafiya ba tare da ta duba ko yana binta ko baya binta ba. Hanyar gidansu ta fara bi, shi kuwa yana binta a baya yana mamaki hali irin nata. Nan take ya gane bata san magana kuma idan tayi maganar a fadace ta keyi. What a girl! Sautin takun sa ne yasa ta tabbatar ya biyo ta din. Tana zuwa qofar gida ba ta ce komai ba nan ma kawai ta shige. Sai da ta jima sannan ta fito da butar ruwa da omo ta ajiye a gabansa ta juya zata koma. “Haba Khair sai ki taimaka mun ai.” Khair? Wacece Khair kuma? “Wai dani kake?” Ta tambaya tana nuna kanta. “Eh mana. Ko ba alkhairi bace ke, umm?” Ya dage mata gira. Dauke kai tayi. Ba dan ranta yaso ba sai dan kwarjinin da yayi mata yasa ta tsaya har ya wanke rigar a jikinsa. “Ba za’ayi mun iso cikin gidan ba? Ko ba’a so na gaisa da ummahn mu?” Dafe kanta tayi kawai ta juya zata tafi. “Ko ki ban nambarki ko kuma in yi ta zama anan har sanda baban mu zai dawo.” Kyale shi tayi ta shige. Bayan minti goma ta leqo ta ganshi a zauna. Gabanta ya fadi ras! Idan Abba yazo yana mata fada fa? She’s so gonna kill this man! “Au da gaske kake?” Ta tambaya. “Eh tunda kin fi son hakan.” Ganin dai bashi da niyyar tafiya banda ma gyara zama da yayi yasa tace, “Ga nambar.” Miqo mata wayar sa yayi ta saka. Bata jira me zaice ba ta bar shi a wajen. Shi kuwa nan take zuciyar sa ta amince da me niqab wadda ya laqaba wa sunnan Khair. A ganin sa indai yayi nasarar samun soyayyarta ai ya samu komai.2 Da wannan shaukin, ya juya ya tafi inda motar sa take. **** Kai Yaya!” Salmah ta fada tana dariya. Yau kam duk sanda mutum ya gifta zaiji dariyar ta saboda Yaya Farouq yazo hutu. A jami’ar dake Sokoto yake karatu kuma a halin yanzu saura zango daya ya kammala.+ Shine wanda jininsu yazo daya. Wanda take jin zata iya fada masa komai da komai. “Bari in wuce masallaci.” Ya dubi agogonshi gami da miqewa. Murmushi Salmah tayi tare da cewa idan ya dawo yayi mata magana su cigaba da hira. “Yau baki har kunne.” Ummah ta qarasa shigowa falon tana tsokanar Salmah. Bata tanka ba saidai yar dariya da tayi kafin ta wuce cikin daki. Tana zuwa tayi alwala tayi sallah. Tana idarwa wayarta ta fara ruri. Dan tsaki tayi kafin ta sa hannu ta dauka. “Ranki ya dade.” A ka fada daga dayan gefen. Wani tsaki taji yazo mata amma ta hadiye shi. Ko duba waye ya kira batayi ba amma daga jin kalaman farko tasan likita ne. Wai shi meye damuwarsa da rayuwarta?4 “Hello? Bana ji.” Ta katse tun kafin yace wani abu. Ace mutum sai naci? Ita kam ta tsani irin haka a rayuwa. Kowa kawai yayi rayuwarsa ba tare da ya takurawa wani ba.2 Let everyone mind their businesses without poking nose in the affairs of others. Urgh! Was that too much to ask?1 Girgiza kan ta tayi ta haye saman gado. Ita gabadaya ranta ma ya baci sai taji bata son fita falon. Dama ita fushin ta a kusa yake. Zaman kusan mintuna da yawa tayi ta juya wannan ta juya wancan. A take ta tuno da littafin nan. Yau kam babu wanda zai hana ta karantawa. Kofa taje ta rufe, ta dawo ta janyo jakar ta inda littafin yake. Daukowa tayi ta sake hayewa gado ta kishingida kafin ta bude fejikan taga yawansu. Gani tayi littafin a cike yake taf. Lallai yau tana da aikin yi a gabanta. Kamar me shirin karanta Qur’an harda wata bismillahr ta da jan dogon numfashi. Assalamu alaikum warahmatullah. Page 1: The beginning of it all. 1998. Watarana ne dai ba zan iya tuna kwanan watan ba amma dai nasan a watan September ne sanda muka zo hutu Nigeria. Mun yan Nigeria ne ciki da baya. Asalin yan Katsina ta Dikko. Kasancewar Abba yana aiki da wata kungiya yasa aka yi masa transfer zuwa Brighton. Temporary transfer ce saboda shekara biyar kawai zamuyi. A lokacin ina yarinya yar shekara sha hudu.2 Nice ta biyun qarshe a gidan mu. Yaya Nasir ne na farko, sai Yaya Fiddausi, sai ni Jamilah sai yar autar mu Ilhaam. Tsakani na da Ilham akwai tazara sosai hakan yasa nakeji da shagwaba sosai ba kadan ba. Ranar kuwa munje gidan Hajiya, kakarmu ta wajen mahaifin mu a Katsina. Bayan mun gaysa sai na fice waje domin ganin gari. Ba wuya abun naga wasu yaran maqwabtan ta kamar sa’anni na zasu tafi talla. “Dan Allah zan bi ku.” Na roqe su. Abun mamaki sai suka fara musu, ko wacce tana cewa ita zan bi. Wadda tafi su tsafta na kalla nace nikam ita ce kawa ta. Bani da kyamar kusantar talaka amma kuma bana son kazanta ko kadan. Farantin gyadar ta ta sauke ta bani ta ce idan ina so na dauki kulli daya kafin mu tafi. Tambayar ta nayi idan babu matsala a hakan tace iyi. Duk da hakan dai nace zan biya in mun komo gida. Ganin muna tafiya a jere gwanin sha’awa yasa nace don Allah nima a bani faranti na riqe tawa gyadar. Babu musu kam suka bani. Tafiya muke yi muna asiye gyada har muka iso bakin titi inda na ga da mai mota ya sauke gilashin motar sa za’a fara guje guje. STORY CONTINUES BELOW Bazaka taba ganin irin wannan a Brighton ba. Asali ma idan aka ga mutum yayi kamar bara yake ko talla akan titi kama shi a keyi. A gaban wata mota muka tsaya inda mai tuqin yayi kiran mu. A guje na qarasa shiyasa na dan dafa motar ina haaki. Abunka da wadda bata saba ba. A haka dai cikin lokaci kadan muka siyar da gyada muka koma gida. Na sha fada sosai har ma an kusa duka na amma ban damu ba because I had a lotta fun out there. I didn’t care about what Ummah and Abba did to me. Ko da mukazo tafiya sai naji dama a barni. Ko yunkurin tambaya banyi ba saboda nasan ba abu ne me yuiwa ba. A haka muka tattara muka koma. Rayuwa ta cigaba da tafiya har na kammala high school. A lokacin ne na tayar da rigima sosai nace ni akan dole a Nigeria zanyi jami’a idan ba haka ba kuma zan kai qarar mahaifana nace sunyi violating rights dina. Dama qawaye na sun sha gaya mun da ace sune suke rayuwar gidan mu da tuni sun mutu saboda takura. Wasu acikin su su ka nuna min cewar zan iya kai qara idan aka takurawa rayuwa ta. Da wannan dalilin yasa Abba kawai yace zaifi dacewa a mayar da ni Nigeria gidan kakata saboda da alama idan na cigaba da rayuwa tare dasu kuma na girma zan yi fitina. Domin kuwa ina shiga shekara sha takwas zan buqaci a ware mun gida. Ba abi ta abunda Umma zata ce ba aka tattara mun komai nawa sai Nigeria. Murna kamar inyi me. Wani abun haushi shine duk wadannan masu tallar sunyi aure sun dena talla. Wasun su ma har yara sun ajiye. Ban ji dadi ba amma dai haka na haqura. Duk sai naji kuma bana jin dadin zaman saboda kaka ta ba mai magana bace. A haka dai a ka fara fafutukar samo min admission a jami’ar da ke nan Katsina. Na samu na fara zuwa inda nake karantar mass communication. A lokackin kuwa SHIEKH malami ne. Yana koyarwa a department na Islamic studies. Lokacin yana tashen quruciyarsa, saurayi ne kyakkyawa na ajin farko don kuwa yan mata tururuwa suke yi akan sa. Shi kuma kamar ba malami ba, yana da kallon mata da kula su. Hakan yasa gaba daya nikam naji na tsane shi. Gashi kuma yana da gadara da nuna isa. Taya na san hakan koh? Aminiyata Hadiza tana bala’in son shi. Kullum takan fito kofar department dinmu ta zauna ta jira ya fito daga faculty dinsu ya wuce a motar sa. A lokacin mutane da dama basu mallaki mota ba musamman ma malaman makaranta. Naji ana cewa mahaifinsa mai kudin gaske ne. Toh da wannan haukar Hadizah, rannan sai ta yi masa girki taci kwalliya sosai tace nayi mata rakiya zuwa ofis dinsa. Ban tsaya musu ba saboda nasan ba zata sauya ra’ayinta a kan shi ba. Bayan mun gama lecture muka shirya mukaje. A bakin qofa muka tsaya Hadiza tana ta faman addua kamar babu gobe. Nice ma na kwankwansa kofar yace mu shiga. Ko da muka shiga wasu mata biyu muka gani suna ta fari da ido suna dariya shi kuma yana aiki a laptop dinsa. Tabe baki nayi na samu gefe na kame a wata couch. Hadiza ce ta gayshe shi. Nikam ko kallan sa banyi ba. “Ya akayi ne?” Ya tambaya yana wani yatsina fuska. “Emm, Malam daman… Nace ko wadannan zasu iya bamu waje?” Ta fada tana nuna yan matan da suke zaune a gaban teburin sa. Harara suke shiga aika mata ita kuwa ko kula su bata yi ba. “Ke kuma ofis din na gidan ku ne da kika samu waje kika zauna? Ko na baki izinin zama ne?” Yi nayi tamkar banji ba. Lallai ma mutumin nan yana ji da wulaqanci. Duk Hadizah ce ta janyo mana. Littafi na na cigaba da dubawa har ma wani lokacin ina tuntsurewa da dariya kamar irin na tuno abu. Kunsan yanda dariya take da cin rai. “Get out of my office!” Ya wani daka tsawa. Ko gigau banyi ba. “Zaki fita ko sai rai ya baci?” Hakan da ya fada neh ya saka wata er dariya ta zo min. Rufe littafin nayi a hankali sannan na kalle shi. “Wai da ni kake?” Na tsare shi da idanuwa kamar yanda naga yana kallo na shima. Kafin yace wani abu, nayi bakin qofa na tsaya. “Dalla malama dauki lalataccen abincin ki kiyi gaba. Da fuska tamkar ta biri.” Ya jefi Hadizah da wadannan kalaman. Eh toh, ta bani tausayi saboda haka naga idonta ya fara ruwa yayinda hannun ta ke ta rawa. A hankali ta dauki flask din tana neman fita inda ni kuma na tsaya a bakin kofar ina sake tattauna maganar da ya gaya mata a cikin raina. Taka wa nayi har inda yake da niyar masifa. Yan matan da suke zaune ne suka gaji sukace zasu tafi. Ko amsa bai ba su ba. “Kai waye da zaka zagi halittar Allah?” Na fada ina nuna shi da yatsa na. “Ki sauke hannunki. Bana son raini.” Ya fada cikin muryar da take nunawa cewa umarni yake ban. “Sai ka sauke idan zaka iya!” Na fada cikin tsiwa. Kafin na qarasa rufe baki na, har yau kama hannu na ya matse. Hadizah ce tayi saurin qarasowa daidai inda muke. “Haba…” Ta fara magana. “Stay out of this Hadizah.” Na fada cikin raunanniyar murya domin kuwa na fara nadamar rashin kunyar da nayi masa. Yayi mun riqo mai zafin gaske. Da kyar nake riqe hawaye na. “Kisan wa da wa zaki dinga yiwa rashin kunya amma banda ni!” Ya kafe ni da idanuwan sa wanda sai da nayi da na sanin kallan cikin su. Ya bani tsoro sosai. “Fita!” Ya sake ni yana nuna kofa. Kamar wacce ake kunnawa da batir, haka na nufi kofa ba tare da nayi musu ba. A hankali naji yayi wata ‘yar dariyar mugunta. Ban kula ba, na kama hannun Hadizah muka fice. Salmah ce tayi ajiyar zuciya tana yar dariya. Ashe ma kurin Jamilahn na qarya ne. Nisawa tayi da zummar cigaba sai wayarta tayi kara. Kamar kar ta duba sai kuma ta dauka. Baquwar number ta gani. Sallama tayi ta kara a kunnenta. “Hehehe kina tunanin bana iya binciko duk inda kika shiga a fadin duniyar nan?” Kamar wadda aka zubawa qanqara haka ta daskare a wajen. Ba zata taba mantawa da mai wannan muryar ba. Innalillahi wa inna ilaihirajiun. “Kina mamaki ko? Zan zo har gidan da kike gobe.” Kafin tayi magana, ya kashe wayar. Wani wahalallen kuka ne ya kwace mata. Yau kam ta shiga uku. Wanda ta gujewa shekarar da ta gabata shi yake son dawowa. Wanda ya zama sanadiyyar hargitsewar rayuwarta. Yanzu ya zata yi idan su Ummah suka ji? Dafe kanta tayi tana kuka mai tsuma zuciya. Kamar ko da yaushe ji tayi tana da buqatar ta sha syrup ko ta samu sauqi. Da sauri ta sauko daga kan gado tana neman inda ta ajiye. Wayar ta ce ta qara yin qara ta duba taga Salim neh yake kiranta. Wanda take karanta labarin sa mintuna kadan da suka wuce ba tare da ta sani ba saboda sam har yau bata fahimci shine wannan sheikh din ba. Daukar wayar sa tana matuqar faranta mata rai. It has started becoming her new addiction, which she was oblivious to. “Assalamu alaikum.” Ta fada gami da komawa saman gado. A hankali ya fahimci tana cikin damuwa. Haka yayi ta Jan ta da hira har dare yayi sosai. Lokacin kuwa, Salmah ta manta da wani kiran waya da ya firgitata. Bayan sati daya, Salmah da Ummah suna sirfa waken da zasu yi alala aka yi sallama. Zaune suke gaba dayan su babu wanda yake magana. Kowa kawai yana tunanin abunda yake ran sa ne. Idan mutum ma ya hango su daga nesa sai yayi zaton ko babu wata alaqa a tsakanin su. + Mayafan su dake gefen su suka yafa sannan suka bayar da izinin shigowa. Wani yaro ne da bazai wuce shekara bakwai ba ya shigo kafar sa babu takalma. Gefen wandon shi daga hagu ya yayyage gashi fuskar sa fututu kamar an haqo shi daga qasa. Da dukkan alamu dai almajiri ne. “Wai ance ana sallama da Salmah.” Da rana tsakar nan? Salmah ta dubi fuskar Ummah kafin ta kalli yaron. Wani tsaki ne da bata san da zuwan sa ba ya kufce mata. “Ke kenan kullum cikin tsaki kamar wata tsaka. Allah ya shirye ki.” Umma ta fada sannan ta mayar da hanakalinta kan yaron. “Ka ce tana zuwa.” Ummah ta riga ta bayar da amsa. Shiru tayi tana tunanin to waye wannan din. Idan da Sheikh ne cewa zaiyi ana sallama da Khair. In kuma likita ne cewa zaiyi kyakkyawa. Yawu ta hadiye kafin ta gyara zaman mayafin akan ta sannan ta fice. Tana fita ta hango wata mota baqa. Sai da kirjinta ya buga da qarfi daga ganin motar. Eh toh, bata taba ganin wani a ciki ba amma daga ganin qirar motar, ta san me ita. Haka kawai jikinta ya bata cewa shine. Shine wannan wanda bata mafarkin sake haduwa dashi. Jingina kanta tayi da bango hade da sanya hannun ta a cikin ta tana jiran ikon Allah. Fitowa yayi daga motar, yayinda ita kuma ta dauke kanta daga gun motar. A hankali ya qarasa takowa inda take. Turaren da ya fesa ne yasa tayi saurin dagowa ta kalle shi. Gefen mayafin ta ta duqunqune sannan ta toshe hancinta da shi. Ba wai turaren bashi da kamshi bane sai dan yana tuna mata abubuwa da dama. Abubuwan da, da a baya suke saka ta nishadi. Yanzu kuwa tuna abubuwan kadai yana saka ta jiri har ma taji kamar zata shide saboda takaici. Fuskar nan a tamke take, ga baqin gilashi ya sha shi. Dan gayu ne na gaske. “Sweetheart,” ya fada tare da dago habarta. Kallon sa tayi har cikin qwayar idonsa tana jin tsantsar tsanar sa da tayi. Bata ankara ba taji zuciyarta ta raunana. Hawaye ne suka fara zirya akan kumatun ta. Taso ta riqe su amma ina… “Mu shiga mota ko? This place is too hot for my liking.” Ya fada yana gatsina fuska. Da ace wani ne da tuni ta buga masa tsaki tayi shigewarta cikin gida. Har ma yana da idon cewa nan yayi masa zafi da yawa? Bayan ya bace kwatsam rana daya ya dawo mata tamkar bai aikata lefi ba? Shi wai wani irin mutum ne da ya fiya son zuciyar sa? Me yasa ba ya damuwa da halin da mutane suke ciki? “Mansur wai dan Allah dan annabi me kuma zanyi maka? Ha’an! Dan jaraba sai da ka biyo ni nan bayan duk abunda kayi mun? Me yasa ba zaka rabu dani ba? Wulaqancin da kayi mun a baya bai isa bane ko me?” Ta fada a masife, zafafan hawaye na sauka bisa fuskarta. A hankali kalaman da ta binne a qasan kwakwalwarta suke fitowa. Hannu yasa ya goge mata hawayen. A nata bangaren kuwa, so take ta make hannun nasa sannan ta hada shi da mari amma kuma tana tsoron abunda zai biyo baya. Lokaci da dadewa ya dasa mata tsananin tsoron sa a zuciyar ta. “Kiyi haquri yanzun na zo ba baki haquri ne.” Ya fada yana rausaya murya. Salma bata san sanda wata dariyar takaici ta kufce mata ba. Wai dama shi yasan kalmar haquri ne? Ashe dama ya san yayi lefi? Ai ta zata shi bai san meye lefi ba a rayuwarsa. “Haquri? Haquri akan me? Haquri akan ka cuceni? Haquri akan ka saka ni a mayunwacin hali? Haquri akan ka sa na fara shaye shaye? Ko wani irin haquri kake magana akai?” Ta fada tana nuna shi da yatsa. Taso ace ta riqe kukan da yazo mata amma abun sai ya gagare ta. Taso ta nuna masa cewar bashi da waje a zuciyar ta balle ma ya sanya ta jin wani abu. Tayi zaton cewa babu fagen Mansur a zuciyar ta sai gashi ganin sa kadai ya saka ta zubda hawaye. Wani dattijo ne ya tsaya yana kallon ikon Allah. Salmah tayi saurin goge hawayen ta da bayan hanunta sannan tayi doguwar ajiyar zuciya. Tabbas tayi kuskure da ta bar shi yaga hawayen ta. Kuskuren barin sa ya gane cewar har yanzun ita raguwa ce. Amma bata makara ba- ta nuna masa cewar ita ma jaruma ce. Itama tana da zuciya mai zafi Mansur kuwa tsayawa yayi yana kallon duk motsin da takeyi. Ran shi ya baci sosai. Har ita wace da zata daga mishi murya? Toh shi kam bai saba da hakan ba. Dan ma ta samu ya tako har inda take shine zata nuna masa ita wata ce? Ji yayi kamar ya kama ta karfi da yaji ya wulla ta a mota ya tafi da ita. Shi fa sam bai iya rarrashi ba. “Wuce ki shiga motar can idan ba haka ba kuma wallahi kin san ba qaramin aiki na bane in shiga cikin gidan nan in sanar da Ummah…” Girgiza masa kai tayi sannan ta fada cikin gida. Tasan idan ta qara ko da minti daya ne, zai iya yin nasarar karkata mata tunani. Wani abun takaici da baqin ciki shine kukan da ta keyi. Amma kam ba zata bari Mansur yafi qarfinta ba. Shigewa tayi hade da banko masa kofa. Sai dai duk abunda zai faru ya faru! In ma shigowar zaiyi, ya shigo. Karshe dai tasan ko me za’a yi mata, ba za’a kashe ta ba. Furzar da iska Mansur yayi ta bakinsa sannan ya saki naushi a iska yana mai jin haushin rashin nasarar da yayi. Mota ya shiga, yaja ya bar gun yana jin haushi. A zafafe ya shiga kiran abokinsa a waya. **** Tun ranar da malamin nan yayi mana rashin mutunci, Hadiza ta sama wa kanta lafiya ta dena bibiyarsa bayan nayi mata fada sosai. Ni a rayuwata babu abunda nafi tsana irin naga ana wulaqanta mutum a wuri sannan shi kuma ya qi yin zuciya.+ Rayuwa haka ta cigaba da tafiya, kullum muna zuwa school in an tashi, direba ya dauko ni ya mayar gida. Ranar wata Laraba, ba zan taba mantawa ba. Ba’a zo dauka na ba har na gaji na fito titi ina neman abun hawa. A na qwalla rana sosai ga azumi a baki na. Ji nake kamar na zube a qasa tsabar gajiya da qishirwa. Gashi ni kadai ce, su Hadiza duk sun tafi. Tsaye nake da littafi a hannuna wanda nayi wa kaina rumfa dashi daga ranar da take gasa ni sai naji qarar horn din mota. Ban ko juya ba, na cigaba da tsayar da abun hawa amma ban samu ba. Injin motar naji an tayar, ta qaraso inda nake nayi saurin dauke kaina daga saitin motar. A kan kunne na naji sautin kashe motar da kuma rufe qofa. “Yan mata,” dagowa nayi. Idanuwa na suka fada akan wannan wawan da be san abunda yake ba. “Sannu,” harara na banka masa na juyar da kaina. Yana malami a bangaren musulunci amma bai iya sallama ba. Lallai ashe zai bushe a nan. “Assalamu alaikum.” Tabe baki nayi na amsa ciki ciki ina kallon shi ta gefen ido na. Ko me zaice mun oho. “Au dama ka iya sallama da zaka ce min wani sannu? Ko aiki kaga ina yi?” Na tambaya ba tare da na kalle shi ba. Inada wata matsala guda daya kuma itace, in dai magana tazo baki na bana iya danneta. Sai na fade ta nakejin dadi a rai na. Kuma babu ruwa na da ko zata yiwa mutum ciwo ko akasin haka. “Wa’alaikumus salam zaki ce. Kuma gashi sai aikin tsayuwa kikeyi a rana.” “Toh naji. Wa’alaikumus salam.” “Yauwa kinga har kin samu lada, masha Allah.” “Ni fa ban san ka ba…” Nasan duk wanda yaji yanayin da nayi magana zai gane qarya nake. Kallon sa na shiga yi. Sanye yake da wata shadda fara qalqal da ita sai qamshi me sanyi yake fitarwa. Oh wasu dai kamar su sukayi kansu. Duk ranar nan da akayi kwanakin nan bata taba shi ba. “Banyi tsammanin jin haka daga gare ki ba amma dai bari na gabatar da kaina. Sunana Muhammad Salim dan gidan Alhaji Abdulhamid Bunza.” Tun kafin ya qarasa na gane wanda yake nufi. Alhaji Abdulhamid wani me kudi ne sosai. Wanda ake ce ma me kudin talaka kuma gidan sa ma kullum a cike yake da mutane masu neman alfarma. Zai cigaba da bayani nayi saurin katse shi. “Jamilah. Ni ba yar gidan kowa bace kuma bana taqama da dukiyar kowa. Dukiyar da a duniya zamu tafi mu barta haka zalika bazata amfane mu ba ranar qiyama. Sannan kuma Allah ne me bayarwa kuma yake bawa wanda yaso daga cikin bayinsa ya hana wanda yaso. Wannan shine dalilin da yasa ko dukiyar mahaifina bana taqama da ita kuma idan an tambaye ni sunana nake cewa Jamilah kadai saboda ni Jamilah ce kawai.” Na fada ina qarashe magana ta hade da Jan numfashi. A hankali na lura kamar jikinsa ya danyi sanyi. Ko ma meye dalilinsa shi ya sani. Ni dai na san gaskiya na fada ba komai ba. “Kinyi gaskiya. Kuma kin burgeni da hakan. Ni kuma dai an fi sani na da Sheikh. Saboda bani da burin da ya wuce naga na zama babban malami ina zagayawa a duniya.” STORY CONTINUES BELOW Caraf na cafke maganar tasa. “Au ashe ma kenan burin naka na wofi ne. Tunda ba jihadi kake son yi saboda Allah ba. Saboda duniya ta sanka kenan? Lallai kana da aiki. Allah ya ida nufi.” Shiru yayi yana bina da manyan idanuwansa wanda kallonsu ke saka mata suji suna san shi. Bazan boye ba, nima kaina sai da naji wani abu a rai na. Gani nayi Sam baiji dadin yanda nayi magana ba. Karkacewa yayi tare da saukowa daga saman booth din motarsa sannan ya dungule hannun sa. “Wai ke haka kike da surutu kamar aku?” Nace a raina haka dai ka gani. “Ni kawai gaskiya nake fada.” Na bashi amsa ina tunawa ita fa gaskiya daci ne da ita kuma ba kowa ne yake son jinta ba. Asali ma yanzu a zamanin nan mutum ya fi so ga gaya masa qaryar da zata faranta masa rai akan gaskiyar. Haka kuma yanzu ta kasance aminan juna ma qarya suke a tsakanin su saboda qaryar ta fi dadi. A yayin da mutum yace zai fadi gaskiya to a sannan mutum ya zama abun kyama. An manta da cewa ita qarya fure takeyi kuma qarya tana daga cikin manyan lefuka wanda Allah baya so. Sai dai kawai nace Allah ya shirye mu. “Hakane.” Ya dan sosa qeyar sa. “Toh ko zaki zo na dauke ki ne? Naga har yanzu baki samu abun hawa ba.” Girgiza kai nayi alamun a’a. Jinjina kansa sheikh yayi wanda ya sa na fahimci abunda yake nufi ko da kuwa bai fada ba. Nasan kawai yana mamakin hali irin nawa ne. “Toh ko zaki bane address dinki?” “Me karbar haraji ne kai ko me?” Na tambaya ina neman kaucewa daga abunda ya ke nufi. Sarai na fahimci abunda yake nufi amma na basar. “Kin cika abun dariya.” Ya qarashe maganar tasa da yar dariya. Haka kawai sai na ga yayi kyau sosai domin dama shi din me kyau ne. Naji kamar ba shi bane wannan malamin da ya mana rashin mutunci. “Kallon na meye?” Zaro ido nayi. Wayyo Allah, ya akayi na bari ya gane ina kallon sa? Shikenan zai raina ni. “Kaga ka hana ni samun abun hawa. Bari na wuce.” Na matsa dan gaban titin. Kamar wadda yayi wa addua, na dade a tsaye amma ban samu babur din hawa ba. Haka dai yayi ta min dadin baki har na haqura na shiga motar sa tare da dora hannu na akan murfin kofar. Ni kawai ban yarda da shi ba. A haka dai na dinga nuna masa hanya har ma ya shiga ya gaida Maami, wato kakata. *** Muhammad Salim (SHEIKH). Tuqi yake a hankali bayan ya sauke Jamilah a gida. Gaskiya yau ya sha mamaki. Domin kuwa ba’a kure shi a rayuwarsa. Sai gashi yau Allah ya hada shi da wadda take da amsar duk kalmar da ya fada. Wani abu kuma shine yayi mamaki da ya sauke ta domin wani tafkeken gida ya gani. Cikin gidan ma ya fi nuna kyaunsa da kudin da aka zuba. Kuma a haka wai gidan kakarta ne. Ita kuwa wace irin macece Jamilah? Which type of woman’s she? Girgiza kansa yayi, a sannan har ya qarasa gida. Bude gareji akayi, ya shiga ya faka. Ko da ya fito, sai ya hangi me gidan zaune a kujerar qarfe da yar rumfa a samanta. Ga wani farin tebur a gabanshi inda wani kwalban lemo take. Sai kofuna guda biyu. A russune yaje wajen ya durqusa har qasa sannan yace, “barka da dare Abba.” Mutumin ne ya sauke jaridar hannun sa sannan ya dan murmusa. “Muhammad Salim.” Ya fada, yana dafa qafadar Salim. “Sannu da hutawa Abba.” Salim din ya maimaita idonsa na kan mutanen da suke yawo a cikin gidan. Yawancin su, ma’aikata ne. “Yauwa. Dama I’ve been wondering ko yaushe ne zaka je Danja?” Salim na ji ance danja ya fara sosa qeya yana nema ya fara kame kame.1 He doesn’t like the said topic at all. “Abba kaga aiki ya danyi yawa shi yasa amma nan ba da jimawa ba.” Ya fada gami da gyara durqusan sa. “Kullum haka kake cewa. Shekara biyu kenan.” Alhajin ya fada yana dan rufe idonsa domin ya tuna. He thinks it’s even more than two years ago. “Abba banyi sallar magariba ba fa…” Ya miqe saboda da alama in bai tashi ba za’a saka shi abunda baiyi niyya ba. “A hakan zaka zama Sheikh din?” Dariya Salim yayi sannan yayi wuf ya bar wajen. **** Kwana biyu Salmah ba ta je makaranta ba haka kuma yar maganar ma da takeyi ta dena. Har ma dena fitowa tsakar gida tayi saidai in an kira ta ta yi shara ko wani abun, tana yi zata koma daki. Ummah tayi mamaki ganin canjawar Salmah lokaci daya. Gaba daya babu walwala a tare da ita kuma babu dan wannan murmushin da ta saba duk da daman baya kaiwa zuci. Muhammad ma yayi mamaki domin duk takalar ta da fada da yayi bata kula shi ba sam. Ummah ta tambayeta me yake damunta. Da farko tace bakomai, daga baya tace ciwon kai. Haka akan dole aka saka ta shan magani.+ Abba kam yayi tafiya wajen kasuwancin sa wato Cotonou saboda haka bai san abunda yake faruwa ba kuma Ummah bata yi yunqurin fada masa a waya ba. A kan gadonta wanda zama akan sa ya zaman mata al’ada take. A can qarshen gadon ta takure waje daya tare da runtse idonta tana jin wani radadi yana zagayawa dukka sassan jikinta. Idan ba zata manta ba, irin wannan abun taji ya saka ta fada halin da ta ke ciki. Yanzun tunani kala kala take yi a ranta. Ji takeyi kamar ta dauki ranta kowa ma ya huta gaba daya. Idonta a rufe ta fara laluben wayar ta har sai da ta ji ta taba ta sannan ta janyo ta zuwa gabanta. Har yanzu bata bude idon ba. Domin gani takeyi kamar idon ta budesu, babu wanda zata gani illa fuskar da tafi tsana a duniya. Wato fuskar Mansur. A lalube ta danna number Salim ta kara wayar a kunnenta. Wataqila yin magana dashi yasa taji dadi. Wataqila ya fada mata kalaman da zasu sanyaya mata zuciya. A haka dai har wayar ta tsinke bai daga ba. Sai a sannan ta daga kai ta duba agogo. Karfe bakwai da rabi ta kusa. Dai dai lokacin sallar isha bayan ita a lokacin ma ko sallar magariba ba tayi ba. Tunawa tayi da abunda wannan SHEIKH din ya gaya mata tayi. Ta tuna sanda ta tura masa saqo nasiha yayi mata doguwa. A lokacin ta shiga hankalinta yanzu kuma nasihar ta bi dayan kunnen ta ta fice. Ya gaya mata a duk sanda take cikin damuwa, ta samu tayi sallah ko raka’a biyu ce zata samu sassauci. Idan ba zata iya hakan ba, ko iya alwalar ce tayi. In itama ta gagara, to ta karanta qurani ko kuma ta dinga salati ba adadi a cikin ranta. Salmah ce ta dan yi murmushin takaici a lokacin. Dan ko sallar farillar ma ba’ayinta yanda ta dace ina kuma ga nafila? Sallah ita ce farko a rayuwar mutum. Ita ce abu na farko da za’a fara dubawa a littafin mutum ranar hisabi. Sallah ita ce ta farko a shikashikan musulinci bayan shahada. Kenan idan mutum baya sallah ya zama ba shida babancin da wanda ba musulmi ba. Sannan an bayar da misalin wasu mutane wanda zasu tashi a cikin wuta ranar qiyama idan aka tambaye su dalilin shigar su wuta, zasu ce— mun kasance cikin wadanda basa sallah. Qalu lam naaku minal-musallin. Sallahr nan dai ita take hani daga mummunan aiki. Innas-salata tanha anil fahsha’i wal munkar… Yayin da mutum ya ga rayuwa bata tafiyar masa dai dai yanda yaso, abu na farko shine ya fara duba yanayin sallar sa; tun daga tsarki zuwa alwala. Ance sallah itace mabudi ko mukullin aljanna, mabudin sallah kuma shine tsafta da tsarki. Ashe kenan idan alwalar mutum bata yi kyau ba, sallar ma ba zata yi yadda ake so ba. Salmah har yanzu bata fahimci haka ba. Bata gane cewa ya kamata ta gyara sallarta ba, tayi ta cikin nutsuwa da lumana. Kawai dai jefi jefi tana tuna lakcar da ta zauna rannan. Toh idan ta tuna sai jikinta yayi sanyi. Ajiyar zuciya ta sauke tana jin wani irin ciwon kai na damunta. Daurewa tayi, sannan tayi saurin saukowa daga saman gadon ta shiga bandaki tayi alwala domin yin sallar farillar da bata yi ba ma tukun. Ta idar da maghriba kenan taji an turo kofar dakin. Ummah ta gani tsaye da kwanon abinci a hannun ta. Ganin Salmah akan dadduma ya saka Ummah ta danji dadi a ranta. “Ga abinci kici. Gone zamu je asibiti a duba lafiyarki.” Zare hijabin jikinta tayi, ta linke sannan ta zauna a gefen gado. “Ummah ni fa ba sai anje wani asibiti ba. Gobe ma zanje makaranta domin na ji sauki.” Ta fada tana tabe baki sannan ta qaqalo wani murmushi ta sanya a fuskarta duk dan Ummahn ta yarda da ita. “Toh shikenan. Allah ya qara lafiya.” Gyada kawai ta samu tayi tare da juyawa daga saitin fuskar Ummah. “Sai da safe Ummah.” “Ki tabbatar kinci abincin nan fa. Zan zo anjima naga ko kinci in ba haka ba kuma na turo miki Muhammad ya gamu da ke.” Yar dariya tayi. “Zanci.” A takaice ta fada tana kade gadonta. “Ana karkade gidan ne?” Ummah ta fada a sigar tsokana. “Gida kuma Ummah. Wani gida?” “Ga shi nan kina kadewa. Ai ke gado ne gidan ki. Inaga ko a tsakiyar titi aka ajiye miki gado kwanciyarki zakiyi ba tare da kin gane a kan titi kike ba ma.” Dariya Salmah tayi. Ita ma Ummah ta danyi kafin ta juya. Har ta fice daga dakin sai kuma ta dawo kamar ta tuna wani abun. “Salmah!” A firgice Salmah ta dago kanta. Idanunta wanda har sun canja kala tun da jimawa, ta sauke akan na Ummah. “Na’am Ummah.” Sai da ta hadiye wani abu kafin ta bayar da amsar. Shiru taji Ummah tayi. Ita kuwa Ummah tunanin abunda zata fada takeyi. Kar taje ba zaiyiwa Salmah dadi ba saboda ita kawai na mace ce mai son fada ba. Amma yaro sai da fadan lokaci zuwa lokaci saboda tsaro. Yaro idan ya tashi bai saba da fada ba, yana zamantowa mai wata iriyar hallaya. Kowa ni mahaifi yana son dansa kawai daurewa yake yayi fadan ko dan tarbiyar dansa ta inganta. Tuna hakan ne yasa ta yiwa Salmah da alamar tazo ta zauna kusa da ita. “Me yake damunki?” Kamar yanda Ummah tayi tsammani, girgiza kanta tayi. “Ki dena ce min babu komai bayan kwayar idonki taqi gaskaka hakan. Abunda fuskar ki take nunawa baiyi daidai da abunda bakin ki yake furtawa ba Salmah. A ina matsalar take?” Hawaye ne suka taru a idon Salmah. Duk yanda taso ta boye su, sai da suka zubo. A zafafe ta share su. “Ana miki wani abun da bakya so ne a gidan nan? Nice? Muhammad ne? Ko Abba? Ni bana so naganki a cikin halin nan sai naga kamar bana kyauta miki. Tun da kin dage ba zaki fada min me yake faruwa ba inaso dan Allah ki dena damuwa. Ko sai na kira Yaya Karime ne?” Jin an ambaci wannan sunan yasa Salmah saurin yankare haqoranta. “Ummah dan Allah ki bari. Kalli kiga, na miki alqawari ba zaki sake ganin hawaye na ba amma karki sake min maganarta.” Murmushi ne ya kufce wa Ummah. Dama tana sane ta fadi hakan. “Toh yayi kyau. Allah ya qara lafiya.” Ummah ta fada tana miqewa domin ta fita. Ta san ruwan zafin da ta dora zata sha kunu ya tafasa. Har ta fita sai ta hango wata kwalba ta gangaro daga qarqashin gado. Har zata wuce sai ta dawo. Ta dauki kwalbar. Salmah kam ta mayar da idonta rufe sai jin muryar Ummah tayi. “Salmah meye wannan?” Zuciyar Salmah sai da ta kusan fitowa. “Laa Ummah wani man gashi aka ban a ciki fa,” a tsanake take maganar saboda sai da ta tattaro duk nutsuwar ta kafin ta fara. Karkata kanta Ummah tayi alamun bata gamsu da amsar ba. Haka kawai zuciyar ta take kitsa mata wani abun daban. Ko me ta tuna oho, sai kawai ta ajiye. “Nayi mamakin ganin ta daga qarqashin gado…” “Ai tara su nake zan mayar wa da mai siyarwan.” Salmah ta bada amsa tana matsowa inda Ummahn take. Cikin dabara ta tura qafarta qasan gadon ta matsar da wadda take akwai abu a ciki. Tana yin hakan, zuciyar ta na karye wa. Yaushe zata dena ne? Ita kam ta san dole abun nan yanada illoli marasa lissafuwa. Tsoranta daya, kar ace mafi muni a cikin illolin ya afka mata. Ba haka ba ma, idan su Ummah suka gane ta san ai ta gama yawo. Kwana biyun nan, tana iya qoqarinta taga cewa bata sha ba. Ko bayan zuwan Mansur ma bata kalli kwalba ba. Amma ji take kamar ta fasa ihu sannan ta bude kirjinta tayi musanyen zuciya da wani. Ko dan ta samu farin ciki ko da kuwa na sati daya ne. Kafin ta san Mansur, a cikin damuwa take. Zuwan Mansur sai tayi tunanin duk wani kuncin rayuwa ya qare mata ashe zuwan Mansur, zuwa ne wanda yazo ya dora mata baqin ciki daga inda aka tsaya. Bayan abunda ya faru tsakaninsu, sai ya zamana abun ya qaru har ya kaita ga fadawa halin da take ciki. A yanzun da za’a mayar da ita jaririya wadda bata san komai ba da yafi mata. Kawai a lallabata tayi barci. In taji ba dadi tayi kuka, a rarrashe ta an bata abinci. Gara kawai ta zauna a hakan amma tasan hakan ba me yiuwa bane ko sama da kasa zata hade. Idan kuwa hakan ta faru, toh ranar raqumi zai iya shiga ta qofar allura. Da ajiyar zuciya Salmah ta kalli inda Ummah ta fice. What an escape! **** Yau da gobe sai Allah. Shekara tazo qarshe yanzu Salmah tana aji na biyu a jami’a. An sha dogon hutu ba lefi. Yau take ranar da za’a koma makaranta saboda haka tun da tayi asuba take shirin fita saboda zumudin ganin qawayen ta. Wajen shida da rabi ta gama shiryawa, ta gyara dakinta tas sannan ta fito falo inda nan ma ta fara shara. Nan da nan ta gama da yake falon ba me girma bane sosai. Tana gamawa take kicin tayi wanke wanke. A sanda ta gama jera kwanukan cikin kwando sannan Ummah ta tashi. “A’a ba dai har kinyi shirin makaranta ba. Banda abunki yau ai ranar komawa ce.” Ummah ta fada tana leqa kicin din inda ta ganshi fes fes. “Ummah ina kwana.” Ta fada tana russunawa kafin ta sabi jakarta ta rataya a kafadarta sannan ta zura hijabi. “Lafiya qalau allazi boko. A dawo lafiya dan nasan ma ko na yi magana me tsawo ba fasa zuwa zakiyi ba.” Duba filas din shayi Umma takeyi. Nan ma ta tarar da ruwa a ciki. Kwana biyun nan mamaki kadai ta ke sha. Gaba daya Salmah ta chanja. “Ummah sai na dawo.” “Allah yayi albarka. In kin dawo baki same ni ba zanje Kabuga. Ko kuma ki same ni a can tunda ba nisa daga makarantar.” “Amin. Sai yadda ta yuiwu dai.” Ficewa tayi wani murmushi na kwance a fuskarta. Wayarta ta zaro ta sake kurawa saqon da aka turo mata jiya da daddare ido. ‘Shi dai wannan Salim din ya iya tsara magana wallahi.’ Ta fada a ranta. Nambar sa ta budo ta danna kira yayin da take qoqarin shiga adaidaita sahu. “Assalamu alaikum gimbiyata.” “Wa’alaikumus salam,” ta fada da sauri kafin ta qara da cewa; “Ba dai barci kake ba?” Murmushi yayi me sauti. STORY CONTINUES BELOW “Wallahi wayar ki ce ta tashe ni.” “Na zata kace min zaka fita qarfe bakwai da rabi.” Miqewa zaune Salim yayi sannan ya jingina da pillow a bayan sa. “Eh wallahi kinga fa ai da sauran duhu. Kuma wallahi barci nakeji.” Ya fada da muryar yara yana tabe fuska kamar tana ganinsa. “Wannan muryar fa. Duba lokaci ka ga.” Ta fada tana guntse dariyar da tazo mata. “Innalillahi. Kinga sai anjima, ki kula mun da kanji kinji? Kar ki bari kowa ya bata mana rai. In kinji babu dadi ki kira ni memakon ki zauna fushi kinji.” Ya fada da sauri sannan ya kashe wayar yana me dirga daga kan gadonsa. Da sauri ya shiga wanka ya watsa ruwan sanyi ya fito yana rawar dari. Kafin ya bushe ya shafa mai ya saka kaya. Salmah kuwa bata kula ba sai ji tayi me adaidaita ya fara masifa wai an zo kuma yana ta mata magana ba taji ba. Ita kam ko haushi ma bai bata ba saboda ta dade bata ji zuciyar ta tana mata tsalle a qirjinta ba irin wannan. Murmushi me sanyi ne yake ta bayyana a fuskarta wanda ko kadan bai kai abunda takeji a ranta ba. Wai ya sunan wannan yanayin ne? Ita dai bata da amsa. Kudi ta ciro daga jakarta ta sallami me adaidaitar kafin ta shiga cikin makaranta. Fitowar Sheikh Salim daga daki zuwa kicin kenan Jamilah ta fado masa a rai. Kallan teburin abincinsu yayi inda kwakwalwarsa ta fara masa gizo ga kwanuka nan kala kala a jere. Ba tare da ya ankara ba ya lula tunani; tunanin abunda ta rubuta a wannan koren littafin. Lumshe idonsa yayi hawaye na sauka akan kumatun sa. **** Jamilah. 2002. Page 3; Disapproval. Hmmm, ba sai na tsaya baku labarin irin soyayyar da ta shiga tsakani na da Salim ba wanda yake da laqabin sheikh amma soyayya ce wadda aka dade ba’a yi irinta ba. Har ma qawaye na cewa suke asiri ya min. Don kuwa wataran ana cikin lakca zanji ina son ganin sa. Haka zan fita na tafi zua ofis dinsa musha hira. Idan na gaji sai in koma. Na sani son da nake masa yafi wanda yake min kasancewar akan sa na fara soyayya. Babban kuskurena shine barinsa da nayi ya gano hakan. “Matar Sheikh!” Na tsinci muryar Hadiza na kira na. Wani murmushi nayi wanda duk wanda ya kalleni sai ya gane farin cikin da kalmar take saka ni. Tun kafin na san sheikh, dama suna kira na da hakan saboda daidai gwargwado ina da ilimin addini kuma suna tunanin in dai ba sheikh na aura ba toh zan raina mijin nawa ne saboda ba zan yarda ya fadi ba dai dai ba. A farko, da yawa sunyi tunanin ban san komai ba tunda nayi rayuwa a qasar waje. Basu san cewar malaman can ma sunfi na nan. Ina zuwa islamiyya, ana zuwa har gida a mana karatu bayan isha. Kuma ina zuwa halqa. “Matar Ibro!” Na tsokaneta. Yanzu Hadiza kam tayi aure. Ta auri Ibrahim dinta. “Wata muhimmiyar magana nake so muyi.” Shiru nayi ina nazari kafin na ce ina jinta. “Amma ina fatan ba zaki ji haushi ba. Gani nayi idan nayi shiru akan abunda zan gaya miki, na ci amanar qawance.” Shiru na sakeyi saboda tun da nake da Hadiza, ban taba ganin tana mun magana a irin yanda take mun yanzu ba. Na yi mata sanin da ko kanwata ce sai haka. Gashi muna shakarar mu ta qarshe a makaranta yau tazo mun da baqon yanayi. “Ina jin ki Hadizata.” Murmushi tayi. “Dama jiya da daddare muke hira da habiby…” Dakatar da ita nayi. “Waye kuma habiby?” Sarai na san abunda take nufi fa. Harara ta kawai tayi ta cigaba da magana. “Allah ni bana sauraron ki in dai baki fada mun waye habiby ba.” Tsaki tayi. STORY CONTINUES BELOW “Toh Ibrahim shikenan?” “Au toh yanzu naji batu.” Na bayar da amsa ina dariya. Wai ashe da gaske aure yana canja mutum ban taba yarda ba sai da naga yanda Hadizah ta canja gaba daya. Tayi wani hankali da mugun nutsuwa. Har rage magana ma sai da tayi. Ni dai nasan babu abunda zan fasa. “Toh shine yake fada min cewar ya san shi kuma kowa yasan ba shi da halin me kyau. Mu’amalar sa da mutane abun…” Ban bari ta qarasa ba na daga hannu na sama. “Haba Hadizah wannan wacce irin magana ce mara fataha balle kisra. Kin san me kike cewa kuwa?” A masife na fadi hakan ina neman na tashi daga wajen ma gaba daya. Ban taba sanin Hadizah na cikin wadanda suke min baqin ciki ba sai yau. “Shi yasa nace kar ki ji haushi. Dawo ki zauna.” Ta riqe hannu na. Fisgewa nayi na kalle ta. “In dai kinsan zaki sake min irin wannan maganar to ki sani cewa ba zamu sake zama tare ba.” Ban jira amsar ta ba na wuce ina jin haushinta. Wannan sunan dai sai na tabbatar ya zama gaske. Ma’ana sai na zama MATAR SHEIKH ko suna so ko ba sa so. **** Qarshen shekara ne sanda yan uwana suke zuwa Najeriya gidan Maami. Muna zaune a daki ne kowa na harkar gabansa sai Ilham tayi magana. “Didi!” Daga kai nayi na kalle ta. “I heard about the great news.” Murmushi nayi. Yanda ta fada ne ya min dadi domin kuwa duk yan uwana ba wanda yake bin bayan zabi na. Abun mamaki har Abba. “Yeah Ilham. I can’t wait to be his wife.” Na bata amsa ba tare da na ji kunyarta ba. Saboda maganar gaskiya na qagu naga an gama maganar auren mu. “Amma kinsan no one likes him. Abba has found out that the dude is a terrible person.” “No one knows him more than me. I don’t care akan abunda mutane suke cewa akan sa. Okay? Dan qarya ne? Wawa ne? Ba shi da hankali? Duk be shafe ni ba. Hakan nake son shi.” Na mayar mata da amsa da tazo da abunda yake raina. “You’re a goner didi!” “You’ve no idea Ilham.” Mamaki nake yanda kowa yake cewa wai Salim ba mutumin kirki bane. Wai bai kai matsayina ba. Sanda aka yi bikin yaya Fiddausi shekarar da ta wuce babu wanda ya mata baqin ciki sai ni don kawai an ga zan auri dan me kudi sosai kuma yaro me hankali wanda yake da burin zama SHEIKH na gaske wataran. Tsaki nayi sannan na sauka qasa inda na tarar da Maami tana cin abinci. Abba da qannen sa Hajiya suke ce mata. Ni kuma na zabi Maami. Rungemeta nayi ta baya, ina lilo da jikinta. “Zagayo tanan. Akwai maganar da zamuyi da ke.” Na san tatsuniyar gizo ba zata wuce ta qoqi ba. “Akan yaron nan Salim.” “Ina son shi a haka.” Girgiza kanta Maami tayi. “Ni babu abunda zan ce. Tashi ki bani waje.” Fuska a turbune na tashi na bar wajen. Da na koma daki na tarar Ilham tana karatu. Ban bi ta maganar da take min ba, na haye gado sai hawaye. If only I knew that more tears are yet to come. If only I knew i was putting myself in trouble… Da na san abunda zan fuskanta a gidan sheikh da banyi abunda nayi ba! **** Bugun da ake yi wa qofar falonsa ya sa ya duba lokaci. Qarfe takwas da rabi ta kusa. Dafe goshinsa yayi ya fice bai ci komai ba. Ko ina littafin da ta rubuta oho? Ya karanta littafin yafi sau a kirga. Ya haddace ko wacce kalma da yanayin yanda Jamilah ta rubuta ta. Amma zai so ace har yanzu littafin yana nan. Yaso ace a lokacin, shima wani me hankalin ne. Yaso ace bai bi zugar abokanai ba. Bai kuma bi san zuciyar sa ba. Da tuna Jamilahrsa tana nan. Damn! ***** Sanda Salmah ta qarasa tiyatar da aka rubuta zasui lakca, tarar da ita tayi har malami yazo. A hankali tayi sallama ta shiga. Babu mutane da yawa kasancewar ranar itace ta farko a sabon zangon karatu. A can qarshe ta hangi yan tawagar ta. Haka kawai taji bata son zuwa inda suke. Gefe ta zauna daga qasa ta zaro littafinta. Sai da awa daya da rabi tayi sannan malamin ya fice. A guje Saadah ta qaraso ta rungume Salmah. “An dena ganinki. Ko yar wayar nan ma baki kiran mutane.” “Da yake su mutanen kirana suke.” Ta murguda baki yayinda suke gaisawa da sauran qawayen nata. Idanunta ne suka fada kan wasu baqin fuska. “Kiyi magana mana.” Raudah ta buge ta. “Naga bakin fuska.” “Yan direct entry ne.” Gyada kai Salmah tayi gami da danyin murmushi. “Wannan itace Zainab. Maman Amirah kenan.” Raudah ta fara gabatar dasu sannan ta nuna dayar me baqin mayafi. “Ita kuma itace Jay. Sunan ta Jiddah.” Miqa musu hannu Salmah tayi suka gaysa. “Wannan ma yar clique dince na ganta da hijabi?” Inji Jay. “Ai wannan nata daban ne. A miskilance take abun ta.” Saadah ta bata amsa. “Naga alama. Amma tsaf tsaf da ita.” Inji Maman Amirah. Salmah dai bata tanka ba. Fatanta daya shine Allah yasa kar wadannan din su koya. Amma daga ji ma suma sunayi. Don’t judge a book by it’s cover! “Kar ki damu muma irin ki ne. Ko wacce da kike gani a cikin mu tana da nata dalilin shaye-shaye. Ni maman Amira ba a son raina na fara ba. Amma yanzu bana jin zan iya rayuwa babu syrup.” Jay ce tayi wani murmushi sannan ta yi magana a yangance. “Ni kuma wayewa ce ta saka.” “Maman Amira bakya tunanin Amirah ko babanta su gane?” Salmah ta tambaya. “Ba zasu gane ba ma.” “Ni dai na dena. Yau wata guda kenan rabona dashi.” Salmah ta sanar dasu a lokacin da suke tafiya zuwa masallaci. “Ke don Allah!” Raudah ta fada a gatse. “Kice kin uztanzance.” Wata ta fada. “Kunga da gaske nake. Kun sani dai na son abun nake ba.” Raudah ce ta bude jakarta ta ciro robar lemo ta miqa ma Salmah.+ “A ajiye dai saboda emergency.” Wulli Salmah tayi da ita. “Kar ki tilasta mata.” Inji Maman Amirah. “Nima fa babu abunda nafi tsana irin wannan. In an kwana biyu na aminta da ku, zan baku labari na.” Ko da suka isa masallaci sun tarar babu ruwa. Sai Salmah tace zata je siyowa. Tana fita neman ruwa taci karo da shi. “Salmah!” Ya fisgi hannun ta. Sai jinta kawai tayi a cikin motarsa. ******** Ta rufe idonta kenan tana jira taji yaja motar sai taji shiru. Abubuwa da yawa ne suke yawo a kanta. Har wadanda ta manta dasu. Zuciyarta ce ta fara bugu da sauri sauri. A hankali ta bude idanunta ta sauke su akan na Mansur. “Wai meye damuawarka ne?” “Kin san me nake so Salmah. So nake ki zo muyi aure!” “Aure fa kace Mansur! Kanka daya kuwa? Wai tsaya ma. Bibiyata kake yi duk inda nake ko toh wallahi tallahi ka fita a idona. Kar ka ga wai wancen karan nayi kuka ka zata I’m not over you. Ya kamata ka gane cewa baya ta wuce kuma ba zata dawo ba!” Tsayawa yayi kawai yana kallon ta.+ Shikam bai san ta a haka ba. Ganin hankalinsa kamar baya kanta ne yasa tayi dabara ta bude kofar ta fice. A guje kuwa ta qarasa masallaci inda Mansur ya fito shima ya biyota. Wayarta kawai ta dauka bata ko jin abunda qawayen nata ke cewa. Sheikh take kira amma waya taqi shiga. Zuciyar ta tafasa takeyi a lokacin kuma Salim kawai take son yi wa magana. Har ta koma gida ranta gaba daya a jagule yake. **** Jamilah Page ;4 Ummah’s trick. Duk wanda ya zaunar dani zai mun magana in dai akan sheikh ne to daga ranar na dena masa magana. Har Hadizah ma sai da muka koma idan na hango ta, canza hanya nake saboda kar ta min magana. Abun haushin shine ni sam ban yarda gaskiya suke fada min ba balle ma na duba lamarin ko na shiga bincike da kai na. A haka na kafa, na tsare ni fa dole shi nake so. Yau ma kamar kullum ina faculty dinsu muna hira sai nace masa akwai abunda nake son gaya masa. “Dama ce min akeyi wai ba mutumin kirki bane kai…” Ban qarasa ba ya katse ni da ihu. “Ai dama na sani! Na sani akwai wanda zasu dinga zuga ki. Wato kin fara daukar zugar mutane ko? Shi kenan babu dama mutum ace yana da abun duniya sai a fara masa sharri. Toh kin kyauta. Nace kin kyauta da kika fara daukar maganar mutane.” Ban san bakina a bude yake ba sai da naji kuda na nema ya shiga saboda mamakin da nayi. Ko tsayawa yaji bayani na baiyi ba fa ya hau ni da masifa. Lallai wannan babban al’amari ne da ban taba cin karo da shi ba. Mota ya shiga ya tayar yayi gaba abunsa ba tare da yace mun komai ba. Kallon qurar da ta tashi nayi sannan na girgiza kai na wuce ajinmu. Dama fitowa nayi. Ko da muka tashi nayi mamakin ganin motar sa a qofar department dinmu. Da saurina na qarasa ina murmushi. “Kiyi haquri na miki fada dazu. Dama raina a bace yake ne.” Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyata. Sabon qaunar sa na qara yaduwa a ko ina na zuciyata. Dama na san sheikh dina mutum ne na qwarai. Nasan ba zai mun fada haka kawai ba. “Dama banji haushi ba.” Na fada da qarfi. Bayan a gaskiya dazun raina ya baci sosai kawai danne zuciyata nayi saboda ina neman na masa uzuri tunda bai saba yi min haka ba. Na qara da cewa; “Amma dai kasan babu kyau fushi ko? Kamata yayi ace duk sanda kake cikin fushi to ka gaya min sai na dan nisanta kaina da kai har sai ka huce. Inda ruwan sanyi a kusa ma, sai na baka ka sha.” Sosa qewarsa naga yayi sannan ya kalle ni cike da soyayya. “Haka ne sarauniyar zuciyata. Ina matuqar sonki wallahi saboda hankalinki. Ga kyau ga hankali. A idon sheikh fa kinfi ko wacce mace kyau a duniya.” Kunya ce ta rufe ni yayinda naji dadin kalamansa sosai. STORY CONTINUES BELOW “Ka fiya zolaya!” Na fada a shagwabe. “Toh yanzu a zo a tafi gida ko?” Kai na daga masa ina boye murmushi na. *** Ko mai bahaushe sai yace kamar yau ne. Ban taba yarda da hakan ba sai yau da naga ina shiryawa zuwa bikin kammala makarantar mu. Abun mamaki wai har na gama karatu. Tsaye nake a gaban mudubi da Ilham a baya na tana daure min igiyar riga ta. Farar riga ce wadda suka taho min da ita daga can. Tana gama daurewa, ta rufe min zif din siket dina yayinda na dauki gown na saka. Hular ta miqo min nan ma na saka na kalli mudubi ina murmushi. “Kinyi kyau sossai.” Jinjina kai nayi ina tafiya kamar wadda bata son taba qasa. A haka na sauka zuwa falon Maami inda na tarar da su Abba da Ummah duk sun shirya suna jirana mu tafi. “Ka ga manya!” Abba ya tsokane ni. “Wannan sunan da saura. Sai na fara masters tukun.” Na fada ina duba qaramar waya ta da bata daukan hoto. A lokacin ita ma tsada ne da ita. Kemarar Abba na dauka muka fice ana hira. Ansha shagalin biki an ci, an sha kuma an dauki hotuna. Bayan na karbi kwalin shedar kammala karatu sai na kasa tsayar da hawaye na. Abun gabadaya mamaki yake bani musamman ma na fita da first class. A haka nayi ta kuka ana min dariya har muka isa gidan Maami. Ko da mukaje sai Ummata ta bukaci na bi su gidan da suke zama kafin su koma. Ni ban wani shaqu da ita sosai ba dan ko sanda muke can nafi zama tare da Abba. Ba don raina ya so ba, na hada kaya na set biyar muka tafi gida. Ance gida yafi ko ina dadi amma gaskiya na fi son gidan Maami. Rabona da gidanmu na dade. Bayan Isha’ muka isa gidan a GRA. Gida ne dan dai dai misali. Da mutum ya shigo harabar gidan, zai ga wani dan qaramin gini a ciki daga gefen hagu. A nan wata mai aiki da mijinta da yaransu suke zaune saboda gyara gidan idan su Abba ba sa nan. Gefen dama kuwa fulawowi ne birjik masu daukan ido sosai. Da alama ana kula dasu sosai. Sai tsakiya inda main ginin gidan yake. Inda su Abba suke zaune. Falo uku ne da dakuna hudu. Sai kicin da bandakuna. Bayan nayi sallah na watsa ruwa ina shirin shigewa qasan bargo na kira sheikh tunda shi bai kira ni ba sai Umma ta shigo. A wata kujera da ke gefen qofar dakin ta zauna kafin ta kira ni. “Jamilah magana zamuyi idan kika mun tsiwa ko wannan rashin kunyar naki to wallahi zan saba miki.” Wani abu na hadiya saboda nasan halinta. Babu wasa in dai tayi magana da irin muryar da tayi mun yanzu. “Umma ba zanyi ba,” na fada ina lashe lebena wanda naji a lokaci daya har sun bushe. “Ki ma yi dan Allah.” Rufe fuska ta nayi da hannuwa na wai ni naji kunya. “Dama nayi bincike akan yaron nan da kike so kuma ban gamsu da yarda na samu bayanai akan sa ba. Eh ba dan iska bane, baya sata kuma amma dai akwai abunda ake cewa Aadab da Aqlaq duk a cikin wadannan ko namba daya ba zan bashi ba. Kin san ance idan kana so ka san halayyar mutum da dabi’unsa, toh kayi tambaya akan sa ba ka tambayeshi ba.” Kallo na tayi taga nayi wuqi wuqi da ido. Ga kuma bayyananniyar rashin yarda a fuska ta. Bata ce komai ba. Dama haka take. Umma bangaren karantar hallaya da dabi’un mutane da ya danganci kwakwalwa (psychology) ta karanta shiyasa ban yi tsammanin jin haka ba. “Amma ina so ki cire son da kike masa ki gaya min abubuwan da kika fahimta a kansa.” Anzo inda nake so. Nan ba fara zubo mata bayani har qarshe amma ban gaya mata wulaqancin da yakewa mutane ba. Ban kuma gaya mata masifar da ya min rannan ba. STORY CONTINUES BELOW “Kin boye min wani abu, ga alama nan a idonki. Ina so kice yazo ya gayshe mu gobe in har da gaske yana sonki din kamar yanda kika fada.” Bata jira amsa ta ba, ta wuce abunta. Sauke ajiyar zuciya nayi ina murmushi. Sai yanzu naji dan dadi dadi. Ko ba komai Umma zata bashi dama. Sam ni ban gane ashe so take ta karance shi ba lokaci daya. ****** Jikin Salmah babu qarfi ta koma gida tana waige-waige. Ita fa tsoro Mansur dinnan yake bata sosai ba kadan ba. Kwana biyu ta canja sosai, amma da alama Mansur yana neman ya dawo da ita ruwa. Ya zata yi? Juyi take a kan gado har aka kira magariba. A hankali taji buqatar shan syrup dinnan gashi bata da shi. Ragowar da take dasu duk ta zuba musu ruwa ta zubar. Wanda Raudah ta bata ma tun a wajen tayi wulli dashi. Zuwa kicin tayi ta taya Umma girki. Umma ta kula yau din Salmah sai a hankali amma sai ta kyaleta. Komawa dakin da zata yi, aka yi sallama. Raudah ce ta shigo. Sai da suka gaisa da Umma sannan suke wuce dakin Salmah. Bayan sun zauna, Salmah ta kawo mata ruwa da cincin, sai Raudah ta sauke ajiyar zuciya. “Mun shiga damuwa fa ganin yanda kika bar makaranta babu shiri. Qalau dai?” “Lafiya ta qalau. Ciwon kai ne ya fado min a lokacin.” Salmah ta bata amsa tana sanya murmushin da be kai zuci ba a fuskarta. “Ayya sannu. Bari na tafi tunda qalau kike.” “A’a ki dan zauna mana ko bayan isha’i sai ki tafi.” Raudah ce ta miqe tana duban wayarta. “Baby na jira na. Dama icecream zamuje sha shine nace bari na zo kafin ya qaraso.” Duba lokaci Salmah tayi sannan tace toh. “Ga damuwa nan a fuskar ki Salmah. Sai dai kiyi wa wanda be sanki ba qarya. Ga wannan,” ta ciro kwalbar coke ta miqa mata. Daga Raudah da Salmah babu wanda ya san ba coke bane zalla. “Na gaya miki na dena fa.” “Miqo su kawai.” Janyo jakarta tayi ta zaro dari uku ta bawa Raudah. Wani murmushin mugunta Raudah tayi. Ita fa ba zata bar ko wacce ta dena ba saboda ita ma ta kasa denawa. Gara kawai a cigaba da damawa tare. Kuma uwa uba, ta cigaba da samun kudi domin a farashi mara tsada take samo su ta siyar wa da mutanenta, taci riba. “Kin san dai bana son damuwarki sam. Amma idan baki sha ba to wallahi zaki iya haukacewa. Gara kawai ki dan dinga sha jefi jefi sai rayuwa ta tafi sumul. Kar ki damu zamui aure a haka ba tare da an gane ba in har kina tunanin waye zai aure mu. Kinsan duniyar nan sai ana yi mata dabaru idan ba haka ba sai ka mutu. Kar na cika ki da surutun da nasan rabi ba ji na kike ba, bari na wuce.” Salmah bata ce komai ba tayi wa Raudah rakiya har soro sannan tace ta gode. Abinci ta zuba taci, ta kora ruwa. Har lokacin, tana wasiwasi akan robar lemon da Raudah ta bata. Zuciyarta na gaya mata kawai ta je ta zubar a rariya. Wata na saqa mata cewa in fa bata sha ba, ba zata ji dadi ba. Ba zata iya barci ba kuma. ‘Idan kika sha kuma, kin koma baya. Ki tuna sabawa Allah ne zakiyi. Ki tuna kuma baqin cikin da kike ji na sabawa Allah bayan kin dawo hayyacin ki.’ ‘In kuma baki sha ba, rayuwar ki ta baya ce zata yi ta miki yawo a kai. Ki sha abunki kawai kiyi istighfari shikenan.’ Abunda zuciyarta ke saqa mata kenan. Dauka tayi tana kallon robar, idanta na hasko mata wani ruwan itatuwa a ciki da koren abu sai fuskar matar da ko sunan ta bata son ji. Ajiyewa tayi a qasan bargo ta fita falo inda Muhammad yake. Gara kawai ta rage zaman kadaici ko abun ya fita daga kan ta ma gaba daya. Zuwanta yayi dai dai da shigowarsa shima. Kafin tayi magana ya riga ta. “Ke zo nan.” A hankali taje. “Wace wadda ta fita dazu?” “Qawata ce.” Ta fada a qasan maqoshinta. “Qawarki? Ashe baki da hankali?” Tas, taji ya waske ta da mari. Tuni hawaye suka shiga saukowa. Mari fa? “An gaya miki irin wannan qawayen ake ajiyewa. Jibi kalarta kalar marasa tarbiyya. Toh wallahi ba zaki bata mana suna ba a nan kamar yanda…” Be qarasa ba Umma ta shigo tana tambayar abun da ya faru. Ko wannen su baiyi magana ba sai Salmah da ta ruga a guje zuwa dakinta. Tana zuwa ta banko kofar ta sa mukulli ta sulale a jikin kofar sai hawaye. Zuba suke ba qaqqautawa. Wai me yasa ya tsaneta haka? Me yasa rayuwa bata mata adalci? A daddafe ta qarasa kan gado. Ta zaro robar ta kafa a bakinta. Bata sauke ta ba sai da ta shanye tas. An koma ruwa…😓 **** Bayan mun gama magana da Umma, bamu cigaba da hira ba nayi sauri na tashi ina jin raina duk wani iri amma daga baya sai naji sanyi. Nasan sheikh dina zai basu mamaki duk kansu. Ina shiga daki, na watsa ruwa nayi sallah na haye kan gado. Waya ta na zaro a kasan filo inda daman nan ne mazauninta. Nan take zuciyata ta fara tsalle a kirjina ina jin dadi. Na juya na juya na rasa ta ina ma zan gaya masa ana son ganin sa a gidan mu. Ni dai gaba daya farin ciki ya hana ni wani tunani mai kyau. Danna kiran kawai nayi wataqila idan ya dauka na samu abun cewa. Har ta kusa katsewa sannan ya dauka. Bayan mun gaisa sai muka danyi shiru kowa ya na tunani irin nasa.+ Can dabara ta fado min. “Albishirinka!” Na fada ina fadada murmushin fuska ta kamar wadda yake gani. “Goro, meye?” Ya fada a daqile. Gaba daya sai naji gwiwata ta sage. The little courage I gathered within me flew into nothing. Na neme shi na rasa. “Haba dan Allah. Ai ba haka ake yi ba. This your response just killed my vibe. Na fasa fadan abun da nayi niyya ma.” Kit na kashe wayar na mirgina daya barin gadon. A hankali naji wasu hawaye sun taho amma ko kadan ban san dalilin zuwansu ba. Na sani Sheikh ya tsani mutum ya kashe masa waya ko da kuwa kai ka kira shi, shiyasa na kashe saboda yaji haushi na. Ina kwance abun duniya ya ishe ni sai ga kiransa ya shigo. Hannu na yana rawar murna na dauka ina kallon wayar. Zuciyata ta rada min kar na dauka. Wani bangaren kuwa tunzura ni yake na dauka. Ban san ya akayi ba sai ki nayi na dauki kiran na kara a kunne na. “Kiyi hakuri.” Murmushi nayi na tabe baki. Sai da na sosa kaina sannan na shagwabe fuska. “Ni ban hakura.” “Haba Matar sheikh, so kike a ji kanmu ne? Yauwa gaya mun meye albishir din? Nasan babban goro ne. Um? Yauwa yan mata.” Qarshen maganar ne ya ban dariya. “To yan maza.” Dariya yayi mai qaramin sauti kafin naji yayi shiru. Da dukkan alamu ni yake jira. Hadiye yawun bakina nayi kafin nayi gyaran murya. “Dazu munyi magana da Umma akan ka.” “Bata amince ba ko?” Shiru nayi, ina nazari. “Nace bata yarda dani ba ko? Kamar yadda kowa baya so na ko?” Ban ce komai ba har yanzu. “Ki min magana mana.” A wannan gabar, dariya ta kufce mun. Sai da nayi mai isata sannan nayi shiru. Na san har cikin sa ya kada. “Ance ka zo gobe.” Ban jira amsarsa ba, na kashe ina murmushi. Pillow dina nayi hugging very tight feeling as if my chest wanted to burst open. Kamar zuciyata zata fito saboda yanayin da na tsinci kaina. ‘Karfe nawa zaka zo?’ Na tura masa saqo. Sai bayan kusan awa daya, sannan ma har barci ya fara fisgata sannan ya bani amsa wai zai zo bayan sallar isha’i. Ban ba shi amsa ba, na kifa wayar sai barci. **** Da sassafe na tashi na sanar da Umma da zuwan sheikh saboda ta fadawa Abba da wuri. Bayan na gaya mata ne an gama komai na aikace aikacen gida sai tace a hadawa Sheikh abinci. Ta tambayeni wani kalar abinci yake so na tsaya sosa qeya. “Ban fahimci shirun da kikayi ba. Kina nufin baki san me yafi so na ko me? Wannan wace irin soyayya kikeyi ne? I love you, I love you kawai kika sani ko? Ko ba shi kike son aura bane?” Ni dai yau Umma ta ritsa ni kuma ta saka ni a tarko. Na bude baki na yafi sau a kirga amma sam na rasa abun cewa. “Na sani daman despite your age, baki san meye soyayya ba kawai hauka kikeyi Jameelah. Baki da hankali.” A karo na farko na amince da bani da hankalin. Saboda da an kalle ni za’a ga alamun haka saboda duk nayi wani sororo a gaban Umma. Idona ya raina fatata. Na yarda bani da hankali amma haukar tawa ta son da nake ma Sheikh ne. STORY CONTINUES BELOW If I only I knew I was really crazy in the reality, things would’ve been easier in the future. Amma na makara! “Umma shi bai fiya son abinci ba fa. Ya fi son fruits, a gidan su ma fa fruits da veggies ake ci yawancin lokuta. Kuma baya cin naman kaza. In short, he’s a vegetarian.” Ban san ya akayi ba, kawai wannan qaryar ta fado min kuma na shararawa Umma ita. Bata kulani ba ita da Mrs Ruth suka cigaba da girke girken su. Juyawa nayi kawai na koma daki. Littafi na dauka na bude wai dan na dauke hankalina from the hassle of what just happened amma sam na kasa karanta komai. Kawai tuno yanda Umma tace mun bani da hankali nake yi. Shin da gaske ne? Waya ta na jawo na kira yaya. Yana dauka ko gaishe shi banyi ba. “Yaya is it true?” Sai da ya danyi jim kafin yayi magana. “What?” “That I’m crazy? Like Umma tace wai hauka nakeyi kuma bani da hankali. Yaya dama ni mahaukaciya ce ban sani ba? Yaya ta ya ake gane mutum mahaukaci ne? Wayyo Allah ashe duk inda nake zuwa kallon mahaukaciya ake min? I’m doomed yaya.” Tsaki kawai naji yayi. “Magana da yawa a lokaci daya, yawan surutu da tambayoyi duk alamar hauka ne.” Ya amsa min. “Wayyo Allah na shiga aljanna na makale. Yaya yanzu haukacewa zan yi?” Na sake tambaya. “Zama ki fito ne. Sakarya kawai.” Sai ya kashe wayar. Mahaukaciya, mara hankali, sakarya? Duk ni kadai a yau. Yau dai da alama ta hannun hagu na tashi. Ina cikin jujjuya maganganun a kai na sai Ilham ta shigo. Janyota nayi ta zauna kusa dani. “Ilham am I crazy? Wai bani da hankali?” Shiru tayi. “Gashi dai saura yan kwanki ki shiga shekara ashirin amma sis ba zan boye miki ba. Kin koma kamar yar shekara goma tun da kika hadu da mutumin nan. You used to be smart but now I can’t help but describe you as dullard.” Doluwa kuma? Oh ni Jameelah yau naga ta kaina. Yanzu ita kuma doluwa zata kira ni da shi. Da na hada sai naga yau nayi sabbin sunaye har hudu. Kallon da na watsa mata ne yasa tayi saurin barin dakin.1 “Ya Allah!” Na fada ina kwanciya akan gado. Ba zan ma kira big sis ba kafin ita ma ta fada mun nata sabon sunan da ta rada min. Wai ko hada baki suka yi ne? A haka dai na rufe idanuwa na. Na dade a kwance ina hutawa kafin barci ya dauke ni. Ban tashi ba sai wajen Maghrib. Nayi sallah na fara karatun qurani har zuwa lokacin isha. Da isha tayi, nayi sallah na watsa ruwa sannan na saka kaya. Falo na samu kowa yana zaune. Gefe kawai na zauna duk aka zuba min ido. Da alama dai so suke ince ko gashi a hanya ko kuma ya qaraso. Banyi ko daya daga ciki ba. **** Zaune Salim yake a cikin abokansa ana ta hira kamar ba shi ake jira a can gidansu Jamilah ba. “Sheikh wai ni kuwa yarinyar nan kana son ta kuwa? In baka so ka bamu hanya kawai.” Mudassir ya tambaya. Bai yi aune ba yaji Salim ya kai masa naushi. “Baka da hankali!” Salim din ya fada yana miqewa ya bar wajen yayinda sauran abokan suka riqe Mudassir kuma suka bi Salim da ido. Ko da ya qarasa cikin gida, bai tarar da kowa ba a haraba saboda haka daki ya wuce kai tsaye. Yana zuwa ya kunna wayar sa wadda ya kashe tun da rana. Saqonnin Jameelah ne tun daga barka da safiya har zuwa tambayarsa ko lafiya qalau yake. Ko zai iya zuwa ko ba zai iya zuwa ba. Shi kam kara kashe wayar yayi, zuciyar sa na masa zafi yayinda ya tuno kiran wayar da ya amsa na qarshe kafin ya kashe wayar. Kiran da gaba daya ya ruguza masa lissafi ya rasa kuma ta inda zai fara kama shi. Tsaki yayi kawai ya kwanta. **** Shiru shiru har tara tayi babu shi babu dalilinsa. Har tsakar gida na fita dubawa ko zan ganshi amma babu alamar sa. “Kinga irinta ko? Na gaya miki yaron bashi da mutunci. Kalli inda ya shanya mu kamar wasu sa’o’insa. Sai kije kiyiwa Abban bayani dan bani da lokacin jin haukar ki.” Jikina ba qaramin sanyi yayi ba. Da wanne zanji? Da rashin samun sa a waya ko da fadan Umma? A haka dai na lallaba naje na durqusa gaban Abba. Tun kafin nace komai naga ya daga mun hannu. Hannun nasa nabi da ido sannan kuma na kalli fuskarsa inda naga babu alamar wasa a tattare da ita. Idonsa yayi jaa. Abba baya son raini komai kankantarsa. “Kar kice mun komai. Ina so ki bude kunnenki da kyau ki saurare ni. Daga yau babu ke babu shi. Yaron banga alama yasan me ne girmama magabata ba.” “Amma Abba…” Hannun sa ne ya sake katseni. “Ki bace mun da gani. Jameelah I don’t want to see you here in the next minute!” Ya daka mun wata tsawa wanda na san qarar ta ne ya kada ni har dakina. Ina shiga na kullo kofa sai kuka. Wannan wace irin rayuwa ce? Wai meye laifinsa ne? Ni har yau ban ga ko daya ba! Wataqila yana can ma bashi da lafiya. Wataqila yana asibiti amma duk basu duba wannan ba. Allah sarki sheikh dina. ‘Ina tare da kai ko yaushe kuma zan cigaba da yi maka uzuri a kowanne hali!’ Na fada da qarfi ina sake fashewa da kuka. ******** Hannun ta ta saka ta toshe bakinta saboda dariya. Shi kuma kawai sai ya qura mata idanunsa masu kyaun gaske. Idanun da suka kasance suna rudar yan mata tun yana dan samari. “Salmah kenan.” Ya fada yana jinjina kai. Har zuwa lokacin bata dena dariya ba. Tun da yake da ita bai taba sanin tana da wannan bangaren a tattare da ita ba. Kullum fuskarta ba yabo ba fallasa kawai sai wataran ta danyi murmushi wanda a iya lebenta kawai yake tsayawa. “Dariyar ta isa haka nan Matar sheikh.” Dum! Kalmar ta doki kunnen Salmah wadda nan take ta dena dariyar. “Matar sheikh kuma?” Ta maimaita tana tuno wannan littafin. Gaba daya sai taji lissafin yaqi haduwa. “Eh mana ko sunan baiyi miki ba? Ni ba Sheikh bane? Kinga matata ta zama matar Sheikh ko kuwa?” Ya dage mata gira. “Hakane.” Ta fada tana sadda kanta kasa. “Yawancin matan abokanai na haka suke kiran kansu da shi. Amma ke fa?” Shiru tayi. “Toh ai kai malami na ne wanda nake neman shawarwari a wajen sa. Babu wata alaqa tsakaninmu.” Wannan karan Sheikh Salim ne ya sheqe da dariya. Lallai ma yarinyar nan. Duk irin kallon da take masa har cikin kwayar idonsa tana nufi bashi da wata ma’ana.+ “Toh shikenan ai. Zan yi kokari naga na nemi mata kwana kusa.” Zuciyar Salmah ce ta shiga rawa. Gaba daya taji wani irin yanayi mara dadin gaske ya mamaye ta. Meye hakan? Muryarta tun tana maqogaronta ta fara karyewa amma bata sani ba. “Toh Allah ya baku zaman lafiya idan ka samu.” Ta miqe tana tattara littafan ta, tana saka su a jakarta. Har wani yaji yaji idonta yake mata. Ji takeyi kamar kawai ta sa abu wanda zai ragewa idonshi kyau saoboda kar wata macen ta gani. “Ina zaki je kuma muna hira abun mu?” Qara saurin rufe zif din jakarta tayi ta dago ta kalle shi. Hadiya tayi amma duk da haka taji wani abu ya tokare mata wuya. “Class zanje.” Ta fada a takaice tana juyawa. Hade hannayensa yayi ya dora su akan kirjinsa yana jijjiga kansa. Har zai bita kuma sai ya fasa ya tsaya ya kare mata kallo har ta wuce. Murmushi kawai yayi. “Mata?” Ya sake girgiza kansa yayinda Jamilah ta fado masa a rai. Nan da nan sai yaji kwalla tazo idon sa. **** Jamilah. Page 6; leave me alone! Nayi kuka cikin wannan daren kuma cikin kukan nake ta gwada kiransa amma bata shiga. Ko kadan zuciyata bata saka min wani abu mara kyau ba. Ni dai fatana daya, Allah yasa lafiya qalau yake. Yanda naga rana haka naga dare. Fuska ta ta kumbura sosai. Ciwon da kai na yake kuwa har sai da na zata tarwatsewa yake shirin yi. Haka nayi ta jinya ni kadai ba wanda ya damu. Ina ta murna ai kwana biyar din da akace zanyi tayi. Sai na ga kawai an bude kofar daki na a sako min akwatuna na suka gangaro cikin dakin. Nan na fahimci dai kulle ake min. Abun duniya ya ishe ni. Babu wanda yake min magana. Iya kar a kawo min magani a ajiye shikenan. Amma ko sannu babu me ce min gashi kuma kwana hudu kenan rabona da shi. Ranar na shirya nace zanje gidan Maami aka hana ni. Nace zanje nayi rijista na NYSC shima aka ce sai wata shekarar. Qarshe ma dai wayar tawa karbeta akayi. Duk wadannan abubuwan basu saka naji na rage son shi ba. Idanun sa kawai nake gani cikin nawa duk sanda na rufe idanuwa na. Kullum a cikin duba kalanda nake ina kirga sauran kwanakin da suka rage su Umma da Abba su koma kasar waje. Da dan biro na nake yiwa kwankin alamu har ya zama saura sati daya. A sannan gaba daya damuwata ta ragu sosai tunda nasan na kusa samun yancin kai. STORY CONTINUES BELOW Ina ta planning yanda zan hadu da sheikh idan suka tafi. A yanzun komai ya sauko domin a tunanin su na manta da shi tunda har anyi wata biyu. Sai dai zuciyata ta kan yimin zafi idan naga ai ko yunkurin nema na Sheikh baiyi ba. “Tashi ki shirya!” Na tsinci muryar Abba. In shirya kuma? Naje ina? Allah yasa wajen Maami zai kai ni. “Wannan karan ba Brighton zamu je ba. Kin manta na gama? Shekara biyar ne dama. Amma na samu wani temporary aikin a Egypt. Zamu fara Umrah, in da hali zamu dubai sai mu wuce Egypt daga can.” Ban san sanda na daka tsalle ba ina ta murna. My dream was to visit the holy city and the ancient city of Egypt. Oh my Allah! Kai wannan abu yayi mun dadi. Ban ma ji ragowar abunda suke cewa ba kawai na tafi na sako hijab mukaje aka mun visa. Tun da muka dawo baki na ya bude ina ta surutu. “Ilham! Egypt for real?” Na tafa hannu na sannan nayi tagumi dreamily ina fluttering lashes dina. “Kin yi sa’a zaki. Abba ce baki je.” Tabe baki nayi ina kwaikwayonta. “Kinga karki fasa min kunne da wannan gurbatacciyar hausar taki. Tunda dai inajin turanci ai kawai ki min da yaren da zan gane abunda kike cewa.” Duk wannan abun da nayi bai hana ta sake gwada yi min bayani da Hausa ba. Da na gaji da jin ta kawai na bar mata wajen. ****** Muna ta shirye shirye. Ashe gaba daya family zamu tafi. Har big sis ma da mijinta da kuma babyn ta za’a je. Naji dadi sosai duk sai damuwata ta kwanta amma deep down, it’s embedded in my heart. “Finally!” Naji big sis ta fada daga baya na. Na juya na kalleta. “Finally what?” “Kin rabu da wannan yaron. Addu’a ta ta karbu.” “Ya Fiddy kenan. He might be miles a way from me. A thousand miles away yanda ko kwalla masa kira nayi na zai ji ba amma kuma har yanzu yana nan.” Na shafa gefen hagu na kirjina ina nuna mata saitin zuciyata. “Allah ya yaye miki. Amma ni kam kauyancin nan naki mamaki yake ban.” Ban ce komai ba, na miqa mata hannu na karbi baby Aayan da yake ta barci. Har muka kusa karasawa airport bamu sake cewa komai ba. A hanya kawai kallon sleeping figure din Aayan nake ina hasko yanda nawa dan zaiyi in akayi auren mu da sheikh. Sauran sai hirar su kawai sukeyi ni dai kam na tafi duniyar tunani. Motsin Aayan ne ya saka na daga ido naga an zo. Fitowa muka farayi aka yi abubuwan da za’a yi sai jirgi wanda bai sauka ko ina ba sai a Jiddah. **** Bayan munyi umra haka Abba yayi ta yawo da mu. Rannan yace zamuje wajen wani abokin sa a jami’atul madina. Yace mana tun suna yara abokin yake son zama malami. Kuma a yanzu hakan ma yana visiting lecturing a jami’ar madina. Sosai muka ji abun ya burge mu ni kuwa sai yashe haqori nake saboda Sheikh dina ma so burin sa kenan. Muna tafe muna hira har cikin makarantar. Tsayawa bayanin ginin ma wahala ce kawai dan ba zata kwatantu yanda ya kamata ba. Takalmi na ne ya tsinke na tsaya lallabawa su kuma duk basu lura ba suna ta hira. Ina ta kwada musu kira amma sam ba su ji ba. Hakan yasa kawai na cire takalman na rungume su na fara saurin kamo su. “Assalamu alaikum.” Naji an min sallama. Wani saurayi ne dogon gaske gashi fari tas amma duk da haka kana mishi kallo daya kasan ba balarabe bane. “Wa’alaikumus salam.” Na amsa ina kallon gaba na yayinda su Abba suka min nisa. “Nawfal Akhiy!” Naji muryar sa. Wallahi na zata gizo kawai take min shiyasa ko daga kaina banyi ba. “Na’am Muhammad Akhiy ha anaa, ra’aitu bintan Jameelah.” Ba wani larabci na iya sosai ba amma na gane abunda yace saboda mu’allim dinmu yana mana larabci jefi jefi. Yana karasowa ya kalle ni, nima sai na daga kai na kalle shi. Tsakanin ni da shi ban san waye yafi mamakin ganin wani ba. Wato ina can ina ta fama da kaina shi yana Madinah yana jin dadi. Bani da lokacin tambaya ko karatu yake ko akasin haka. Ni dai kawai na tsinci kaina da fushi dashi sosai. “Jameelah!” Ya fada yanda gaba daya naji sunan ya shige ni ta ko wacce kofar jikina. Amma sai na qudurtawa zuciyata ba zan nuna hakan ba. I truly missed him beyond my inscribing capability. Nasan zaiyi tunanin zanyi tafi nayi tsalle koma na rungume shi duk da ban taba yin hakan ba. Dauke kaina nayi. Shi kuma Nawfal kawai takalmin sa naga ya cire ya bani. Babu musu akan idon Sheikh na karba na saka. “Shukran Akhiy Nawfal.” Na juya zan tafi kamar ban ga Sheikh ba. Mamaki ma ya hana shi motsi. Ina juyawa naji Nawfal ya tambaye shi ko ya sanni ne. Yace masa eh. Bai qara da komai ba ya biyo ni. Yana ta kiran suna na naqi juyawa sam. Ya qara saurinsa yayin da Nawfal din kawai ya juya. Takalmin Nawfal yamin girma sosai shiyasa na kasa gudu saboda tsoron kar na fadi. “Jameelah listen!” Naji ya fisgo hannu na. Sai naji zuciyata tayi rauni. Fisgewa nayi. “No Sheikh!” Na cigaba da tafiya ta. Sake biyo ni yayi naga idan na biye masa mukayi yar tsere to ni zan sha wahala tunda ban taba zuwa makarantar ba. Hankali na take ta tashi da naga babu su Abba babu alamar su. Juyawa nayi naga bani da nisa da gate. Ajiyar zuciya nayi, ko ba komai sai na koma na jira su nasan dole zasu fito. “Meelaty, please. Dan Allah ki tsaya kiji,” daga masa hannu nayi irin kalar wanda Abba yayi min. Kai na a kasa yake. Bana jin zan iya kallon fuskarsa balle na saka ido na a cikin nasa. Ina da tabbacin zuciyata yaudara ta zatayi in har na hada ido dashi domin idon yana tafiya dani. “Bayani zan miki Meelaty.” Yayi kasa da muryar sa. Wannan karan ma ji nayi gaba daya jini na yana tsinkewa, zuciyata tana yunkurin yafe masa. “Ka kyale ni. Just leave me alone Salim. Leave me alone!” Ina fadan haka, kuka ya kwace mun. Da gudu na bace masa da gani. Ban juyo ba har na isa get. Nan na samu waje na durqushe na fara hawaye. Wannan soyayya tana wahalar dani. Gaskiya ne; na haukace. Babu tantama; na sakarce. Babu shakka; na dolence kuma na kauyence duk a sunan soyayya. **** Ganin security kawai yayi ya harde hannu yana kallonsa. Danshin da yaji a fuskarsa ya gane hawaye ne suke tsiyaya. Shi kuwa dan tsohon da yake sanye da uniform rasa abunyi yayi. “Malam kafi minti goma anan kana ta zubar hawaye. Me yake faruwa?” Firgigit ya dawo daga tunanin da yake sannan ya runtse idonsa. Ji yake kamar yanzu abun yake faruwa. Sai kawai yaji kamar abunda ya faru tsakaninsa da Jameelah ne zai maimaita kansa tunda gashi Salmah ma tayi tafiyarta ta bar shi a tsaye. Yasan cewa security officer ya gane shi saboda haka, bai ba shi amsa ba ya shiga mota kawai ya kunna AC. Ya jima kafin ya tayar da motar yaje har bakin faculty din su Salmah. Faculty of earth and environmental science. Jiranta zaiyi har su tashi. Ba zai bari tarihi ya maimaita kansa ba. Ba zai bari ya yi sakaci irin na da ba. Ba zai bari abunda Sheikh Salim na bogi yayi ya shafi real Sheikh Salim ba. Da haka ya kifa kansa akan sitiyari yana jira su tashi. **** *** Kusan minti talatin yayi yana jira, kuma a cikin mintuna talatin dinnan zai iya cewa ko da minti daya zuciyarsa bata huta daga dokawar da take yi ba. Idanunsa na kan daliban da suke ta wucewa. Shi dai yasan kallon masu wucewa yake amma kwata kwata hankalinsa ba a nan yake ba. Hankalin sa ya tafi rayuwarsa ta baya. Mutuwar Jameelah har yau tana daga masa hankali. Gashi kuma kafin ta rasu ta bashi wish daya. Tace yaje ya shirya tsakaninsa da mahaifiyarsa. Yana iya qoqarin sa, kuma mahaifiyar tasa tace ta yafe masa amma bai ga alamar haka ba. Tun bayan Jameelah, lokacin nutsuwa ta saukar masa, bai qara jin yana so yayi aure ba sai da ya hadu da Salmah. Shi yanzu ta ina zai fara? Shiru dai bai ga alama ba sai kawai ya kashe mota ya fito. Sanye yake da wata shadda kalar toka mai cizawa. Tayi mishi kyau sosai ba kadan ba. Haka ya fara takawa kanshi a qasa had cikin department din. Addu’ar sa daya, kar wata ta tsaya dashi. Mutane da yawa sun san shi, musamman ma mata tunda gashi yana ji da gayu ga ilimi kuma. Daga idonsa yayi yana dan kalle kalle. Can ya hango wata kujera ya taka inda take ya zauna. Bai jima da zama ba wasu mata suka zo suka yi masa sallama. Da ‘dan murmushin sa ya amsa musu yana mai kawar da ganin sa zuwa gefe. Wani murmushin takaici ne ya zo masa da ya tuna akwai wani lokaci a da, wanda ba abunda yake masa dadi irin yaga mata suna tururuwa a kan sa. Wannan lokacin da bashi da buri da ya wuce ya zama sananne a ko ina. Sai gashi Allah ya kawo shi lokacin amma ko kadan baya jin dadin hakan. Oh, rayuwa! “Malam naji rannan kana cewa zaka wallafa littafi. Ya sunansa?” Wata a cikinsu ta fada, tana kallon sa. Da alama tana so ya tattara hankalinsa akan ta ne. “Ban sa suna ba tukunna kuma har yanzu ban kammala shi ba. Saboda kashi kashi nake so nayi shi. Na yan mata daban, na samari daban, na iyaye daban.” Ya fada yana kallon agogonsa. Ya sani a iya hirar da sukeyi ta minti biyar a waya, ta na gaya masa lokacin da suke tashi. Kuma yanzun lokacin yayi amma bai ganta ba. Gara ya tashi ya duba. “Allah ya taimaka.” Amin kawai ya ce yana miqewa. “Sai anjimanku.” Bai jira amsar su ba, ya bar wajen. “Amma akwai girman kai.” Dayar ta dubi qawarta. “Ke kika jawowa kanki ai. Zo mu tafi dan Allah. Ai ya ma yi kokari, at least ya bamu amsa kuma ya mana sallama da zai tafi.” Tabe baki dayar ta yi sannan suka wuce. STORY CONTINUES BELOW ***** Salmah da maman Amirah ne ke tafiya suna hira sama sama. Duk da kuwa maman Amirah matar aure ce, hakan bai hana ta kula Salmah ba kuma bata nuna mata wani bambanci. Cikin yan kwanakin nan tare suke yin komai. Gaba daya sun ware daga cikin qawayen nasu. “Kinga mutumin naki,” daga ido Salmah ta yi ta hango shi sai waige waige yake. Da sauri ta dauke idonta da taga kamar zai ganta. “Kinyi sa’a fa Salmah. Saboda kin ga gashi malami mai tarin ilimi ga kyau ga gayu, ga kudi.” Maman Amirahn ta fada. “Bafa so na yake ba.” Salmah ta fada tana yarfa hannu. Yayinda take jin dacin abunda ta fada a saman harshenta. “Kai haba. Kinji ki? Da gani ma ke yake nema.” “Maman Amirah. Ki bari kawai duk fa mazan nan irinsu daya. Na san halinsu.” Maman Amirah dai mamaki ne ya kamata. Dama Salmah na kula mutane? Duk wannan shiru shirun nata? “Ko ni nan da nake shan wahala Salmah, na yarda ba duk aka taru aka zamo daya ba. Dan Allah kar ki sake yi musu jam’u. Akwai na kirki a cikin su.” Maman Amirahn ta dafa kafadar Salmah kamar wadda take shirin yi mata nasiha. “Haka kike gani maman Amirah. Amma ni din yanda kike tunani ba haka nake ba. Kuma abunda kika ji na fada ba wai saboda jin dadin bakina nake fada ba. A kaina ya faru. I’m a living witness that men are dogs!” Sauri maman Amirah tayi ta rufewa Salmah baki saboda mutane har sun tsaya suna kallonsu. “Wataqila ni kuma sai na baki labari na zaki fahimci nawa zancen. Wataqila ki gane cewa kowa da irin halinsa. Bari kiji…” Sallamar Sheikh ce ta tsayar da maman Amirah. “Wa’alaikumus salam Sheikh. Ina wuni,” ta dan sauke kanta qasa tana bashi girma. “Maman Amirah ya iyali? Da su Amirah?” Salmah da maman Amirah zaro ido sukayi. “Wa yace ma hakane sunan ta?” Salmah ta harare shi. “Ina jin dai aljanu na ne suka fada mun. Em yan mata har yanzu fushi ake dani tun dazu? Wai laifin me nayi ne?” Dariya maman Amirah tayi sannan ta kalli Salmah. “Bari na je can na zauna.” “A’a ba gida zaku ba? Sai na rage muku hanya ai. Kun ga hadari ya hado. Ruwa zai iya saukowa ko yaushe.” Inji shi. “Ba zamu shiga motar ka ba!” Maman Amirah ce ta mintsini Salmah alamun bai dace tace masa haka ba. Mutum ne babba gashi kuma malami. Gashi kuma gaskiya ya fada. Zai iya yuiwa kafin suje gate din makaranta an tsuge da ruwa. Kwace hannunta Salmah tayi sannan ta juya gefe. Murmushin gefen baki kawai yayi yayinda Maman Amirah ta matsa gefe kamar yadda ta fada dazu. “Toh tunda dai fushi kike dani ayi haquri.” Ya fada yana kama kunnuwansa. A hankali Salmah ta dora idonta akan sa. Gaba daya sai taji ya bata kunya. “Ka bari mana.” Ta fada a shagwabe tana rufe fuskarta. Shima murmushi yayi. “Toh kice kin haqura.” Har yanzu bai sauke hannun sa ba ita kuma gaba daya sai ta ke jin wani iri. Ya za’a yi qaton sa da shi ya riqe kunne kuma gashi mutane suna wucewa. Gashi kuma an san fuskar sa an san waye shi. “Toh sauke hannun.” “Toh na sauke.” Ya kwaikwayi muryarta yana mai sauke hannun sannan ya kafeta da ido. “Ni ka dena kallo na bayan kana can kana neman matar da zaka aura?” Salmah bata fahimci abunda tace ba sai da taji ya sheqe da dariya. A hankali abunda tace ya dawo mata. Nan ma kunya ta lullube ta. STORY CONTINUES BELOW “Ni fa bakomai nake nufi ba.” She grunted. Tana neman boye borin kunyarta. “Eh baki ce komai ba. Toh ya karatun yau din?” “Lafiya qalau.” Ta amsa tana kalle kalle. “Dafatan dai ban cika miki tunani ba.” Kai, ya fiya tsokana da yawa. “Kamar ya?” Ta dage girarta. “Bakiyi ta tunani ba?” Turo baki tayi bata bashi amsa ba. “Allah ya baki haquri kar kiyi kuka kinji?” Shiru ta sake yi. “Toh tunda na ganki bari na tafi. I may not be able to see you again. Ba lallai mu sake gamuwa ba.” Kamar ya? Ba zai sake ganin ta ba? Saboda me? “Me yasa?” Salmah tana kallon sa ya dan rufe idonsa. Kwayar idonsa mai kalar ruwan qasa mara haske, tayi kyalli. Sannan yayi murmushi wanda ya qawata fuskarsa. “Saboda aure zanyi. Duk shekarun nan da nake raye, ji nake kamar a mafarki nake yinta. Kamar a kan gajimarai nake yawo. Lokacin yin rayuwa ta gaske cike da kwanciyar hankali yayi. I have been in a dream Salmah. It’s time for reality.” Kamar dazu, idon ta ya kawo ruwa. Ba shiri kuwa sai hawaye wanda tayi saurin goge su ba tare da ya gani ba. A hankali ya matso kusa da ita. Ya dan rage tsawonsa saboda ya fita tsawo sosai. Rufe ido kawai tayi, wanda yake cike da hawaye. “You’re my reality Salmah. Ina son sake gina rayuwa da ke. Ke nake so ki zama matar Sheikh. Shin zaki zama matar Sheikh?” A hankali yayi maganar wadda ita kadai zata ji mai yace. Ba shiri hawayen ta suka zubo. “Ki bani amsa mana. Ke nake so. Kece matar da nake fada dazu. Ki gaya mun. Kina son Sheikh?” Girgiza kanta ta shiga yi alamun a’a. Gaba daya zuciyar Sheikh ta shiga rawa amma duk da hakan a tunanin sa Salmah gwada shi take. A nata bangaren kuwa girgiza kanta kawai takeyi babu tsayawa. Kwata kwata sheikh bai cacanci mata irinta ba. Mace kamila, hafizar quran, yar gidan mutunci ce ta cancanci zama matar sa ba ita ba. Ba zai yiuwa ba. Da me take tunani? Gaba daya yazo ya sauya mata tunani? Yazo yasa ta manta da ita din wacece? Mai zaiyi da irinta? Mai zaiyi da yar shaye shaye? Mai zaiyi da wawiya irinta? Yayyafi aka fara, gashi lokaci daya garin yayi duhu. Hakan yasa maman Amirah ta taso. Abunda ta gani yasa ta tsaya. Salmah ce take kuka. Domin yanzu ya wuce hawaye kadai. Sosai kukanta yake fitowa. Wata rumfa ta tafi ta tsaya dan tana ganin ba huruminta bane tayi magana. “Menene hakan Salmah? Na fadi miki magana mai ciwo ne? Dan Allah kiyi haquri idan na bata miki rai. Bana son hawayen nan naki.” Ya fara rarrashinta. “Ka tafi kawai. Sheikh ka tafi. Ka tafi!!!” Ta fada da qarfi yayinda ruwan sama ya tsuge. Ko kadan bai motsa daga inda yake ba. “Salmah please. Ki nutsu ki min bayani. Meye na kuka? Wallahi I really mean it. I do love you because I alone can see through your eyes. I can see something reserve for me. Your love is reserved for me. Kar ki min haka. Ki saurareni…” “You can see through my eyes alright. But not my soul! Sheikh ka tafi na gaya maka. Ni ba irin matar da zaka aura bace. Nayi maka kazanta da yawa. I’m too dirty for a silky pure fellow like you!” Ta qarasa maganar, tana fara tafiya da sauri sauri. Wata adaidaita ce tazo wucewa. Duk da cewa adaidaita sahu basu fiya shigowa cikin makarantar ba. Tsayar da ita Salmah tayi ta shige. A gaban idonsu ta tafi. Sheikh ya juya ya kalli maman Amirah sannan ya cire lema ya kai inda take tunda ita bata jiqe ba. Haka ta karba bata ce komai ba. Ita ma tayi sa’a ta samu mota ta tafi. Motar sa ya qarasa. Kafin ya shiga, ya dade ruwa na dukan sa. Gaba daya ya rasa me yake masa dadi. Meye matsalar ne? Me ya fada ba daidai ba? ***** Sanda Salmah ta qarasa unguwarsu, ruwa ya tsaya har gari ya dan yi dadi. Ji take yi kamar ta fasa ihu. Wai ya akayi ta manta da wace ita, har ta shagala tana kula shiekh wanda a hankali har son sa ya fara shiga zuciyarta. Ta chemist ta biya ta siya wani maganin tari sannan ta shiga gida. Tana zuwa tayi sa’a babu kowa a falo. Da sauri ta shige daki ta kullo kofar ta na jin zuciyarta na bugu. Hankalinta ya tashi, gaba daya duniyar ta jagule mata. Kallo daya tayi wa kwalbar hannunta, ta bude. Yau ko dan tunanin kar ta sha bata yi ba. Haka ta daga ta shanye. In ma mutuwa zatayi gara tayi. Tasan ta sha da yawa kuma bata sirka ba. Shirkif ta kwanta akan gado. A hankali take tuno rayuwarta… Wata mata ce zaune akan turmi tana ta kirga kudin hannunta. Cikin kudaden akwai yan biyar biyar, yan goma goma, haka dai har kan dubu dubu. Sanye take da wata bakar atamfa mai ratsin ja-ja wadda ta haska fatarta. Kallo daya zaka mata kasan tana jin jiki amma hakan bai rage mata haske ba. Kalba ce manya manya akanta wadda jelar ke rito bisa kafadarta. Tsakar gidan dan mitsitsi ne. Sai dakuna biyu da bandaki. Karime mai adashi aka fi sanin matar da shi. In dai kazo unguwar kana cewa haka za’a kawoka. Mata ce bafulatana wadda ba sai ta fada ba ake ganewa. Rana daya ta zo unguwar lokacin da goyon Salmah. Babu wanda yasan daga inda take amma da yake ana ganin yan uwa na zuwa wajen ta sai ake kyautata mata zaton kawai miji ya mutu ya barta ne da sabuwar haihuwa. Bayan an raba gado kuma ta chanja wajen zama. Wannan shine labarin da yake yawo a matsayin tarihin Karime mai adashi. Bata dade da tarewa ba ta fara sana’o’in hannu.+ Daga baya ta fara adashi. Mata ce mai fada idan aka tsokanota. Gashi bata ragawa kowa. Musamman ma idan kaci bashinta. Bayan nan, ba laifi ana zaman lafiya da ita. Abunda kowa ya sani shine, ta tsani yarinyar ta wato Salmah. Wannan abu na matukar daurewa mutane kai. Babu irin zancen da ba’a yi akan Salmahn. Wasu ma har cewa suke ko dai ba ita ta haife ta ba. Sai dai ita tayi fur tace ita ta haifi diyarta. “Salmah?” Ta kwala kira tana hangen kofar dakinta inda take tsammanin Salmahn zata fito. “Salame!” Ta sake kwalawa Salmah kira. Salmah da ke kwance a dakin tana barci ne taji kamar ana kiranta a mafarki. Zumbur ta tashi ta fito da gudu. “Gani Uwale.” Ta durkusa. Sai da Uwalen ta kalleta sama da qasa tayi tsaki sannan ta kirga wasu kudi ta bata. “Ki kaiwa Iya Abdulganiyu. Ki dade kinji? Kar ki dawo sai dare.” Lokacin Salmah shekarata bakwai kuma ta san halin uwarta. Ta san me hakan yake nufi. Saboda haka, dan kwalinta ta janyo akan igiyar tsakar gidan ta daura ta fita a guje.1 “Oh jibeta kamar tsinke, wannan yarinya?” Uwale ta fada amma Salmah bata ji ta ba tunda ta dade da fita. Tana fita ta tarar da su Jummai da Yahanasu suna yar gala gala. Ranta ya biya sosai don tana son wasa sosai. “Laa Jummai nazo muyi?” Ta tambaya tana cusa kudin a qasan zaninta. Nan ta fara tsalle tsalle akayi ta wasa da ita. Gaba daya ta manta an aike ta. Sai can dai Yahanasu ta tuna. “Salmah ba aiken ki aka yi ba?” Dafe kirji Salmah tayi ta fara salati. Shikenan yau ta shiga uku. Hankali ta bai gama tashi ba sai da ta shafa kasan zaninta, kudi suka ce dauke mu inda kike ajiye mu. Tun kafin tayi magana, yaran suka fara rantse rantse ba su suka dauki kudinta ba. A hankali duk suka zame suka bar ta tana ta kuka. Da taga dai babu wanda zai taimaketa, sai ta tashi ta kade kasar da ta kwasa a zaninta ta tafi gidan Iya Abdulganiyu. Tana ta tafe hawaye na zuba a fuskarta tana gogewa da bayan hannunta. Ko da take daidai langa langar da zata sada ta da gidan Iya Abdulganiyu, sai kukan ya sake tahowa. Haka ta tura kofar ta shiga. Gidan haya ne, kashi uku. Kuma dukka mazauna gidan yarabawa ne amma kiristoci. Iya Abdulganiyu ce kadai musulma kuma tana yawan zuwa gidan su Salmah. Salmah ma ta saba da ita sosai. “Ekaaro ma.” Ta dan russuna ta gaishe ta. “Ah Salamatu, kin dage sai kin koyi yaren mu ko? Wa ya taba min ke?” Iya Abdulganiyu ta kama hannun Salmah ta jawo ta gefe. Idan mutum yaji Iya Abdulganiyu na yin Hausa ba zai bambance ko bahaushiya ce ba ko bayerabiya saboda ta iya Hausa sosai. Cikin sheshekar kuka Salmah ta fara qiqina. “Kudi Uwale ta bani na kawo miki shine…” Sai ta sake fashewa da kuka. Ita kam Allah yayi ta da shirita. Ba yau ne ranar farko da aka aiketa ta tsaya a hanya wasa ba. Tana da son wasa, in dai taga anayi sai ta yi. Duk dukan da Uwale take mata idan ta fita mantawa take sai ta aikata ba daidai ba sannan take auno irin dukan da za’a yi mata. Iya Abdulganiyu na jin haka ta gane kudin adashi ne. Naira hamsin suke bayarwa wadda yawanci canjin cefane ne. Su ashirin suke zubin dashin inda ake dauka duk qarshen sati. Mazajensu ba masu karfi bane, hasalima wataran ko abinci ba’a samu. Wataran kuwa in kasuwa tayi kyau har kifi da kpomo suke siya suyi miyar agushi mai lafiya aci da sakwara. Wasu a cikin matan ma, mazajen sun rasu sun barsu da yara. Su suke fita su nemo. Iya Abdulganiyu tana da dan shagonta a kofar gida. Anan take saida busasshen kifi, ganda, agushi, ganye, gari da dai sauran abubuwa irin nasu na yare wanda take sarowa a garin su. Toh yar ribar da take samu, ita take yin adashi har kala uku. Adashin da takeyi na wajen maman Salmah kuwa hannu biyu take yi. Toh dubu biyu take dauka. Gashi kuma Salmah ta zubar dasu. “Salmah mi, daina kuka.” Duk da bata ji dadin batan kudin ba, sai ta yi iya kokarinta taga Salmah ta kwantar da hankalinta. Ta sani sarai Uwale dukan tsiya zata yi wa Salmah in dai taji labarin ta zubar da kudin. “Zata dake ni.” Salmah ta fada. “Kinci abinci?” Girgiza kai Salmah tayi wanda yayi daidai da shigowar Abdulganiyu. Abdulganiyu yaro ne da ba zai wuce shekara sha shida ba. Da yake ya taso a irin gidansu, dole yake fita yayi buga bugar sa ya samu kudi domin babansa yace ba zai biya masa kudin jarabawar gama sakandire ba tunda bai ci jarabawar gwaji da akayi makon da ya wuce ba. A ka’ida, in ka ci jarabawar gwajin, gwamnati zata biya ma kudin jarabawar kammala sakandire. Abunda baban bai sani ba shine, zamani ya kawo mu lokacin da sai mutum yana da hanya da kudi abubuwa zasu tafi daidai. Yanzu ko mutum yaci, za’a iya fadar dashi, a bawa wani saboda wata cuwacuwa da mutumin yayi. Abdulganiyu yasan yayi karatu iya karatu amma duk da haka ya fadi. Haka mahaifiyarsa tayi ta bashi baki yayi haquri. Zama yayi a gefe sannan ya bude ledar kosan da ya siyo. Ya tashi ya dauko faranti ya juye sannan ya miqawa maman tashi. “Maami, jeun akara.” Maami ci kosai ya fada yana dora mata farantin akan cinyarta. Ita dai Salmah Allah Allah take taji ance ta dauka. “Oladipo mi, ma belle full oo.” Shafa kanshi tayi tana murmushi. Oladipo shine sunan yarabancin sa wanda yake nufin arziqi mai yawa. Sai da ta haifi mata biyar kafin shi lokacin ma har ta cire rai. Kallon Salmah yayi wadda ta kure shi da ido kamar zata cinye shi. Bai kula ta ba, yaja farantin sa ya koma gefe. Can yana cikin ci sai yaga ta taso ta zauna a gefensa. Lokacin kuwa Iya ta shiga ciki ta dibo mata ragowar garri da gyada. Yi yayi kamar bai ganta ba. “Zaka cinye? Baiyi ma yawa ba?” Ta fara lashe lebenta. Shi dai bai ce mata komai ba.1 “Cikinka zai fashe fa.” Ta sake fada da taga alamar bashi da niyyar sanmata. Shi dai cigaba da cusawa yayi sannan ya fasa ledar kunun da ya siyo ya fara sha. Rungume siraran hannayenta Salmah tayi tana kallon sa yawun ta nata tsinkewa. “Toh dan Allah sammin ko rabi ne,” ta nuna rabin karamin yatsanta. Sannan ne Abdulganiyu yayi dariya har sai da ya kware. “Gashi.” Ya bata guda daya. Duk ta lunqoma ta tauna ta hadiye sannan ta kalle shi ta gefen idonta. Shima kallon ta yake yi. “Na kara?” Ta rausayar da murya gami da lanqwasar da kanta gwanin tausayi. Farantin ya tura gefen ta. “Ki cinye duk kinji sarkin wayo.” Ya fada yana miqewa. Ruwa ya sha daga randa sannan ya dibo ya ajiye a gefen Salmah. “Nagode Yaya. Dan Allah zaka zama yayana? Kaga in Uwale zata dake ni sai ka tare min. Kuma in su Halimatu zasu dake ni sai ka tare min.” Ta fada tana kafe shi da ido. Rufe idonsa yayi sannan ya bude. “Sai kin zama yarinyar kirki amma. Sai kin dena tsayawa wasa a kan hanya in Uwale ta aike ki. Kuma ki dena roqo.” Ya fada yana riqe kunnenta alamun kashedi. “Toh na dena.” Murmushi yayi. Iya Abdulganiyu tazo fitowa ta gansu. Sai ta tsaya tana jinsu tana dan murmushi. “Yauwa good girl.” “Toh mu kulla.” Ta nuna masa karamin dan yatsan ta sannan ta nuna masa yadda ake kullawa. “Yayy nima nayi Yaya!” Ta fara tafi. Tafawa sukayi sannan ya fice ba tare da ya gane mamansa na kallansu ba. “Ki gama ci muje ma raka ki gida.” Iya Abdulganiyu bata rufe bakinta ba sai ga sallamar Uwale da doguwar bulalarta. Da alama a hanya ta saka aka karyo mata a bishiyar darbejiya. *** Salmah na hangota, ta fita a guje zuwa dakin Iya Abdulganiyu ta buya. Shikenan yau kashin ta ya bushe. Ita kam dama ta zama kuda ko ta bace da komai yafi sauki. “Mama Salmah, shigo mana.” Iya Abdulganiyu ta dan saki fuskarta tana murmushi kamar bata san mai ya kawo Karimen ba. Kujerar tsakar gida ta nuna mata. Ita dai Karime sai huci take tana leqe leqe ko idonta zai hango mata Salmah. “Ina wannan marar mutuncin? Bata zo nan ba ko? Tuntuni nake ta yawo gida gida ina nemanta. Tsabar wulaqanci irin nata har yanzu bata dawo daga aiken da nayi mata ba. Nace ta kawo maki kudin ki kuwa?” Iya Abdulganiyu ce ta kalli kofar dakinta, ta kalli windo, sai ta ga Salmah tana leqowa idonta taf da hawaye. Numfashi taja. “Eh, ta kawo min.” Kwafa Karime tayi sannan ta miqe amma duk da haka jikinta na bata cewa Salmah na cikin gidan iya Abdulganiyu. “Bari inje na nemo ta amma yau sai na farfasa mata jiki da wannan.” Ta fada tana karkada bulalar. Salmah kuwa zaro ido tayi sai ga tanan ta fito a guje ta fadi a gaban Uwale. “Uwale dan Allah kiyi haquri kar ki fasa min jiki. Wallahi ban sani ba sanda kudin suka fadi. Kuma Iya Abdulganiyu ma bata yi fada ba.” Duk yanda Iya Abdulganiyu ta so ace Salmah tayi shiru, Salmah bata yi ba saboda rudewar da tayi. Gashi garin shirme ta je ta fallasa kan ta.+ “Au zubar da kudin kikayi? Nace zubar da kudin kikayi?” Sai kawai ta hauta da duka. Iya Abdulganiyu tazo janye Salmah ita ma aka kwada mata sandar. Ja baya tayi tana sosa baya. Su Deborah da Chiamaka ne suka gaji da jin ihun Salmah suka fito. Gani sukayi Salmah na kwance sai jibgarta ake yi. Da saurin su suka zo ta baya suka janye Karime. Ita kuma Iya ta janye Salmah wadda da kyar ma ta ke motsi. Kamar yanda Karime ta fada, sai da taji wa Salmah ciwo a baya. “Why you dey beat your pikin lai dis?” Deborah ta tambaya. Karime bata tsaya bayar da amsa ba ta matsa wajen Salmah. “Zaki dawo ki same ni. Ai nan ba gidan ku bane!” Da haka ta wullar da bulalar wadda duk ta kakkarye. Deborah ce ta kalli inda Karime ta fice sannan ta yi tafi. “The woman no get sense oo. Se kii se omobinrin re?” Ta tambayi Iya Abdulganiyu. Matar nan bata da hankali. Ba yar ta bace ba? “Omobinrin re ni oo!” Yar ta ce mana. Iya Abdulganiyu ta bata amsa tana daga Salmah sannan ta shige da ita daki tana mamakin halin Karime. Dukan da tayi ya wuce hankali. “Taa! Omo iyawere.” Kai! Allah ya sawwaqe. Chiamaka ta fada sannan duk suka koma bangarensu suna juya abun a ransu. **** “Uwale kinga kinga!” Salmah ta fito a guje hannun ta a tsakiyar kanta. “Bana son sakarci,” Uwale ta fada gami da juyawa ta cigaba da dama koko. “Kin gani, kullum idan na tashi daga barci sai na gwada. Yau hannu na ya tabo kunne na. Toh in munje makarantar su Jummai za’a dauke mu!” Ta sake yin bayani da murnarta. Tunda taga su Jummai na zuwa makaranta, ita ma abun yake burgeta. Rannan ta lallaba ta bi su Jummai. Da suka je sai shugaban malamai yace mata sai anyi mata rijista kuma sai hannun ta yana taba kunnenta. Tun daga ranar Salmah ta samu abun yi duk safiya. Kusan shekara guda kenan bata manta ba kuma ba tayi fashin ko rana daya wajen gwadawa ba. “Uwale ai zaki kaini makaranta ko?” Salmah ta durqushe a gabanta tana kallon ta. “Zaki matsa ko kuwa?” ” Uwale dan Allah in kina so ki shiga aljanna.” Ta sake roqonta. “Salmah ko kina so ba ko ba kya so, sai na shiga aljanna. Kin ga matsa min daga nan. Kuma saura naji kinje kin fadawa mutane naqi saka ki a makaranta. Sai na yanke bakin nan.” Rau rau idon Salmah yayi. Ta miqe tana ta kallon Uwale wai ko zata chanza ra’ayinta. STORY CONTINUES BELOW “Ki dauki kofin kokon ki, ki bace min da gani.” Dauka tayi ta wuce can bakin kofar daki tana sha tana hawaye. “Sai fari kamar mayya, ga siranta uwa tsinken sakace. Mtsww.” Uwale ta miqe da biredinta a hannu ta shige daki. Salmah na gama shan kokon, ta fice waje. Bata tsaya ko ina ba sai shagon Iya Abdulganiyu. Tana zuwa ta samu waje ta zauna tayi tagumi. Ko gaisheta ma ba tayi ba. “Salmah mi, me yake damunki?” Daga kai tayi ta kalle ta sai kuma ta kalli gefe. “Yunwa kike ji?” Girgiza kai tayi nan ma. Haka dai Iya Abdul tayi ta tambayarta tayi shiru. Cigaba da zama kawai tayi a wajen. In anzo siyan abu, ta karbi kudin ta miqawa Iya Abdul, in canji ne ma ta miqa mata. Ana haka har rana ta bullo, Abdul ya biyo ta shagon. Duk yanda yaso Salmah tayi magana, qi tayi. Shima ya gaji ya tafi cikin kasuwa. Awa biyu a wajen tayi shi ba tare da Uwale ta neme ta ba. Sai da taji yunwa kuma ta tuna anyi mata kashe din cin abincin gidan mutane sannan ta koma gida. Sanda ta koma Uwale bata nan. Ta duba babu alamar abinci. Kawai sai ta kwanta tana kuka. “Yauwa, maza maza dauki tsintsiya ki min shara. In kin gama ki zo yau nayi suyar awara ki kaimin cikin kasuwa.” Shigowar Uwale kenan ta tarar da Salmah kwance akan tabarma duk ta takure waje daya. “Uwale yunwa.” Ta fada har jikinta ya soma rawa. “Zaki tashi ko,” da jifar takalmin kafarta ta qarasa zancen nata. Jiri na kwasar Salmah haka ta tashi tayi sharar tsakar gidan. Ta saka dan qaramin hijabinta ta dauki bokitin awarar. “Kar ki dawo min gida sai kin sayar da duk. In kin dawo kya ci abincin.” Salmah durqushewa kawai tayi. Uwale tayi fadan har ta gaji. “Ungo nan. Kici kije ki siyar min kinji Salmah, sai na saka ki a makarantar.” Jin zancen makaranta ya sa Salmah ta karbi biredin da aka bata ta fara ci. “Da gaske Uwale? Zaki saka ni a makaranta idan na siyar?” Idonta har wani qyallin murna yake. Idan ka kalli fuskarta har gani zakayi kamar ta qara haske. “Eh mana. Maza maza kije ki siyar.” Da tsallenta, Salmah ta fice. Uwale ce ta kalli hanyar da Salmah tabi sannan ta tabe baki. “Wauta kamar ubanta.” Ta yi tsaki tana gyara daurin zaninta. ****** Duk wanda Salmah ta gani a hanya sai ta tsaya bashi labarin za’a saka ta a makaranta ba zata jira amsar mutum ba sai ta fara gudu duk dan ta yi saurin zuwa bakin kasuwa. Bakin kasuwar cike yake danqam da mutane wanda duk yawancin su mata ne. Daga yara kanana, sa’o’in Salmah da ba zasu wuce shekara bakwai ba, zuwa yan mata yan shekara sha shida sai manyan mata wanda su kuma zawarawa ne har kan tsofi masu saida abinci. Wasu na siyar da waina, wasu shinkafa da wake, wasu na suyar dankalin Hausa. A gefe guda kuwa maza ne cike a wajen, wasu na taya masu sana’ar hira, wasu na busheshen taba da cin bashi. Wasu kuma wajen yan matan su suka zo. Yara maza kanana kuma su kan yi aike ko su taya nemo canji. Haka dai kowa da abunda ya kai shi wajen. Ita dai Salmah tsaye take da bokitin awararta har ta dari uku tana kallo. Can ta hango inda wasu mata suke sanye da hijabinsu a zaune gaban bokitansu. Da saurinta ta qarasa wajen ta zauna. “A makaranta za’a saka ni fa.” Ta zunguri ta kusa da ita da taga alamar ba wadda take da niyyar yi mata magana a cikinsu. Ita kuma in dai ba ranta aka bata mata ba, da wuya ta zauna bata yi magana ba. “Babanki ne zai saka ki?” Wata mai koren hijabi ta tambayeta. Salmah ce ta qare mata kallo domin ta haddace fuskarta. Yarinya ce wadda na zata girme ta ba. Baqa ce mai doguwar fuska. Idonta yan madaidaita ne, hancin ta ma haka, sai girarta mai kauri, cike da gashi. Hijabinta duk ya yayyage haka ma rigar jikinta ta kode. “A’a mamata ce.” Salmah ta bata amsa tana sake kallon sauran da ke zaune sun sha tagumi. Wasu kuma sun ja gefe suna yar carafke. “Ni kuwa mamata ta mutu. Kuma na dena zuwa makaranta.” Lanqawasar da kai Salmah ta yi. “Kar kiyi kuka kinji? Ni ma babana ya mutu. Ban taba ganin sa ba.” Haka dai suka cigaba da hirar yarinta dai har aka zo akayi ta siya. Bayan la’asar kusan kowa ya fara tafiya, Salmah sai tana zaune tana jira a siye ragowar ta hamsin. Har wajen shida bata qara samun mai siye ba. Can sai ta hango Abdul ya shigo zai tsaya a wajen wata mai Gurasar bandashe. Ai kuwa ta kwala masa kira. Tayi sa’a kuwa ya jiyota. Murmushi yayi ya qara sa inda take. “Arabinrin mi,” qanwata. Jawo hannun sa Salmah ta yi ya zauna kusa da inda bokitin ta yake. “Uwale zata sakani a makaranta. Zan zama mai tuqa jirgi yuuuu yuuuu.” Ta nuna masa yanda jirgin zai tashi a sama. “Da gaske? Iyye ashe qanwartawa ta girma. Me kike yi anan?” “Cewa tayi kar na dawo sai na siyar, idan na siyar zata saka ni a makaranta.” “Toh shikenan. Ki kula da kanki kinji? Kar ki dinga yiwa kowa magana. Kin ga mazan can, in kika musu magana zasu yanka ki.” Qwalalo idanuwa tayi sannan ta gyada kai. “Yauwa toh tashi mu tafi.” Ya fada yana jin tausayin Salmah. Shi kam ba zai taba yarda ace diyarsa tayi talla ba komai talaucin da zai same shi. Yawanci a yawon talla yara suke lalacewa su gagari iyayensu. Yawanci a yawon talla suke sanin abunda yafi karfin su, daga nan sai zuciyarsu ta bushe su daina jin maganar kowa su kuma tafiyar da rayuwarsu yanda suke so. Abdul ya kanyi mamaki mai yasa hausawa suke saka rayuwar yaransu a hatsari sai daga baya su zo suna cizon yatsa. Shi ya sani cewa saboda shi namiji ne kuma ya fara tasawa shiyasa ma baban ya yarda ya fara sana’a. Baban bai dora masa talla ba saboda yara maza ma suna baci. Yara maza ma ana lalata su. Su ma sun cancanci a killace su kamar yadda za’a killace mata. “Ai ban siyar da dukka ba. Kuma tace kar na dawo sai na siyar.” Ta bude bokitin tana nuna masa. Nan ma sai Abdulganiyu ya shiga tunani. Wannan wani irin abu ne? Yaya Uwale zata yi wa Salmah haka? Salmah yarinya ce mara wayo, wadda kwata kwata bata san mai rayuwa ba. Ita dai kawai tana harkarta. In taji dadi tayi dariya idan taji rashin dadi kuma tayi kuka. Gashi kuma tana da surutu, yanzu idan tsautsayi yasa ta fada hannun mara imaani fa, ta bashi labarin cewa an ce kar ta dawo in bata siyar ba shi kuma ya samu hanyar yin mugunta. Yawancin yara da wannan barazanar da iyaye suke musu, suke lalacewa su fara juye. Anan ake cutar su. Haka dai yayi ta tunani. Hamsin din ya ciro ya bata. “Juye mana mu cinye koh? Nasan kina jin yunwa. Amma kar ki gaya wa Uwale ni na baki kudin. Kinga sai ta zata kin siyar da dukka koh?” Juyewa tayi suka cinye, suka sha ruwa suka qoshi. Abdulganiyu yasa Salmah ta wanke bakinta kamar bata ci komai ba sannan suka kama hanyar gida. Salmah ce zaune a tsakar gida tana dinke gefen rigar makarantar ta da ta yage daga gefe. Kayan sun fara yi mata kadan gashi duk sun kode. Dama Jummai ce ta bata, sanda aka siya mata sabon kaya. Lokacin da sauran kyaun su. “Uwale dan Allah a dinka min sabon kaya. Kinga wannan duk sun tsufa kuma tun ina aji uku nake sakawa. Gashi hijabin ko gwiwa ta baya rufewa.” Duk da dai Salmah ta san wacce irin amsa ce zata biyo baya, hakan bai hana ta roqon Uwale ba. Saboda tasan Uwale ta na da kudin siya mata sabo sai dai kawai tace ba zata dinka ba. Sa’ar da Salmah tayi shine ba’a biyan kudin makaranta sai dai a siya littafai. Da ana biya, ita kam ta tabbatar da tuni ta dena zuwa makarantar. Ta sani sarai Uwale bata son kashe kudi musamman ma in akan Salmah ne. Lokaci da dama ta kan rasa mai Uwale take yi da kudin. Gashi dai ita bata ga tana siyan sabbin kaya ba ko wani abu. Iya kaci duk safiya Uwale ta kirga kudinta, ta mayar ma’ajiyarsu. “Yo mai za’a gani a jikin naki? Iyi? Yarinya banda tsawo kamar sandan ba’are babu abunda kika ajiye. Su Jummai har sun fara yar kiba ke kam gaki nan kamar tsinken tsintsiya. Loqai loqai kamar lagwani.” Bayan Uwale ta gama fadin haka, sai Salmah ta runtse idonta tana jin wani irin yanayi marar dadi na gwaraye jikinta. Yana harbowa ne tun daga zuciyar ta zuwa sassan jikinta. Ita ya zata yi ne? Ita tayi kanta siririya ne ko yaya? Babu abunda tafi tsana irin maganar sirantar da ake mata. Ayi mata a waje, in ta dawo gida ma Uwale tayi tayi. Bata gajiya in dai ta wannan fannin ne.+ Cigaba da dinkin kawai tayi amma hankalin ta yayi nisa. Sai da taji ta soki kanta da allura sannan ta kalla. Ajiyewa tayi ta tashi yayinda ita ma Uwale ta shiga madafi ta fara suyar awara kamar yadda ta saba. “Ki zo ki yanka albasa da tumatir.” Gyada kai kawai tayi sannan ta rataye rigartata a kan igiya. Sanda ta gama yankan, Uwale ta sauke kaskon farko. Saboda haka, ita ta karba ta karasa suyar. “Uwale wallahi duk wanda muke siyar da awara tare sun dena zuwa bakin kasuwa.” Idonta har da kwalla domin yanzu ta fara ganewa zuwa talla ba abun kirki bane kuma wannan mazan sai suyi ta mata magana ita kuma bata so. “Su ai girma sukayi. Ke fa? Har yanzu kina nan kamar bango.” “Uwale me ake ci ayi qiba?” “Au tambaya ta ma kike? Toh bari kiji, ba zakiyi qiba ba. Kar ma ki sa rai.” “Toh in dai hakane sai ki dena zagi na.” Salmah ta turo baki. Uwale ce ta karkace sannan ta gyara daurin dan kwalinta. “An qi a dena din. Dauki nan ki fice. Bana son ganin qeyarki sai kin sayar da duk.” “Uwale in yamma tayi na dawo?” “Baki ji me nace bane? Ko iyayen naki sun maida ki bayerabiya irinsu? Nace kar ki sa min qafa a gida sai kin siyar kin kawo min dari biyar cas. In ba haka ba kuma makarantar kin dena zuwa. Na biyu sai kinyi sati ba ci babu sha babu kuma fita. Sannan…” Salmah bata jira jin ragowar zancen ba ta fice da saurinta tana hawaye. Addu’arta shine kar ta hadu da yan makarantarsu suyi mata dariya. Yawancinsu ma basa kiranta da sunan ta sai dai su ce mai awara. Wasu kuma su kirata da Salmah mai awara. Abun yana mata ciwo amma babu yanda zata yi. Dole ta jure saboda cikin biyu dole ta zabi daya. Ko dai ta dena zuwa tallan awara ta dena makaranta ko kuma ta cigaba da tallan awara, ta cigaba da makaranta. Haka dai ta cigaba da tafiya. Yau ko ta hanyar shagon Iya Abdulganiyu bata bi ba. Shima Abdulganiyun kwana biyu ran shi babu dadi balle ya rarrashe ta. Ya samu ya tara kudi, ya zana jarabawar kammala sakandire. Matsalar itace jarabawar da ake yi a shiga jami’a ce har yanzu bai ci ba. Gashi sai kudi tafiya suke. Da yaga yayi har sau biyu Sai kawai yace bari ya haqura ya zage dantse wajen neman kudi yanda idan bokon ma ba ta samu ba, ba zai samu matsala ba sosai. STORY CONTINUES BELOW Mahaifinsa kwanaki yayi hatsari. Shikenan ya kama jinya babu abunda yake iyayi saboda ya ji ciwo sosai har sai da aka yanke kafar sa ta hagu. Sai ya zama daga Iya Abdulganiyu sai Abdulganiyu sune masu jigilar gidan. Su suke nemowa su ciyar da gidan. Rayuwa tayi musu zafi. Yanzu haka Abdulganiyu ya tafi Legas. Gaba daya Salmah sai taji duniyar bata yi mata dadi. Sai taji tamakar komai nata ya tsaya mata domin kuwa kamar yanda Salmah ta buqata shekarun baya, Abdulganiyu ya dauke ta kamar kanwarsa. Shi yake share mata hawaye. Shi yake koya mata karatun makaranta idan bata gane ba. Kuma da yake tana son turanci, shi yake koya mata turanci saboda ba sosai ake yi a makarantar su ba. Idan Uwale ta dake ta, wajen sa take zuwa ya bata haquri. Watarana idan yana nan shi yake mata karatun Islamiyya don kuwa shi ya haddace quranin. A wajen sa ma ta koyi yanda ake sallah tunda bata zuwa makarantar allo balle islamiyya. “Salamatu almajira, salamatu mai awara!” Habiba ta fada da qarfi tana gwalo. Har da janyo hijabin Salmah sannan ta ruga a guje tana kyalkyala dariya. Kwafa kawai Salmah tayi ta cigaba da tafiya. Su Jummai ta gani sunyi shirin tafiya Islamiyya ita da qannanta. Nan ma sai taji dama itace Jummai. “Baba ina wuni.” Ta tsaya gaishe da babansu Jummai wanda kullum shi yake kai su makaranta akan mashin dinsa. Idan islamiyya ce kuma ya raka su a qafa har sai ya tabbatar sun shiga cikin makarantar sannan ya juyo. Wataran idan qanin Jummai ba za shi makaranta ba, sai a dauki Salmah akan mashin din itama a kai su tare da Jummai. Wataran kuma sai dai ta daga musu hannu ta cigaba da tafiya a qasa. “A’a malama Salmah, ina zuwa haka?” Baban ya tambaya yana dafa kanta. Nuna masa bokitin tayi, tana sosa kanta. “Ni ai bana zuwa islamiyya. Awara nake kaiwa bakin kasuwa. Kuma tace kar na dawo. Kuma ni inason Islamiyya. Da babana yana nan ai da nima ya saka ni.” “Ayya ai islamiyyar babu tsada banda abun Karime.” “Ai Uwale tana da kudi. Uwale ta tsane ni kuma nima na tsaneta. Ni guduwa ma zanyi kawai irin wanda na gani a talabijin din gidansu Hafsatu.” Salmah ta fada gami da yarfa hannun ta. Da mutum yaji yanda tayi maganar zai tabbatar da, da zuciya daya ta fadi hakan kuma da gaske takeyi. Babansu Jummai watau Malam Muhammadu ne ya yi saurin dakatar sa ita. “Kar na sake jin haka daga bakin ki. Ai idan mutum ya gudu yan yankan kai ne suke kama shi. Ko mota ma ta kade shi. Babu kyau kinji? Kiyi haquri.” Jin kiran sallar la’asar yasa ya fasa yin doguwar maganar da zaiyi. Sake kama hannun Jummai da na qaninta yayi sannan ya juya zasu tafi sai yaji Salmah na magana. “Ai a fim din da muka kalla yan yankan kai basu kamata ba. Ita ma kullum fada ake mata shine ta gudu kuma wasu masu kudi suka dauke ta. Nima haka zanyi. Nima masu kudi su dauke ni.” Salmah ta bashi amsa. Sai kawai yaji jikinsa yayi sanyi. Toh taya zai fara yiwa Salmah bayani? Uwale na can gida bata kula da tarbiyyar yarinyarta kwata kwata bata san mai yake faruwa da ita ba. Ina amfanin hakan? Yanzu yana da tabbas Uwale bata san sanda Salmah ta fita har taje tayi kallo ba kuma har ta haddace abunda ya faru a fim din har tana neman kwatantawa a kanta. Shi yasa shi baya barin yaransa su suka TV a gaba suyi ta kallo. In ma zai barsu toh ko shi ko matarsa na zaune a gefe da remote a hannunsu. Akwai finafinan da ko da kuwa na al’adar bahaushe ne, yaro karami bai kamata ya kalla ba. Wani abun ba zai fahimce shi daidai ba. Wanin abun kwakwalwarsa bata qarasa gun ba kuma amma in dai ya gani ba zai manta ba. Wani abun idan ya ji, shikenan ya riqe kenan ko da kuwa bai san ma’anar ba.1 Take note. “Ai ita ta fim din bata da hankali. Kuma masu kudin da suka dauke ta masu yankan kai ne bata sani ba.” Kamar yadda Salmah ta saba, zaro idanuwa tayi. “Eh, kar ki sake ki gwada kinji? Ki zauna da Uwale. Maza wuce ki tafi.” Sai ya juya ya cigaba da tafiya. Abun yana ta masa wani iri. Shi bai san wace irin mata bace Karime. Yanzu idan ma yace zaiyi mata magana yanzu zata ci masa mutunci ta zagan masa iyaye. ***** Waje guda ta samu ta zaune ta hade gwiwoyinta ta kifa kanta. Tafi awa daya amma kwata kwata cinikin naira hamsin akayi. Hakan na nufin sai ta kai magariba a wajen. Gashi Abdulganiyu baya nan balle ya taimaketa ko ya taya ta zama ko kuma ya rakota hanya. “Ke ji mana,” sai ta dago kanta taga wani yana busa taba. So take ta toshe hancinta amma tana tsoro saboda rannan da ta toshe cewa yayi sai ya dake ta. Wata yagaggiyar dari ya bata. Hannu na rawa ta karba ta zuba masa. Ya karba ya tafi. Da Salmah taji kiran sallah kuma gashi mutane duk sun fara tafiya sai kawai ta haqura. Malamin makarantar su yace su daina kaiwa dare a waje. Kuma yace duk wanda aka sa ya kai dare yaje ya gaya masa. Zai zo har gidansu. Kuma in ya zo baza’a daki mutum ba. Tuno hakan ne yasa ta tashi ta dauki bokitin. Duk da haka dai tana wasiwasin zuwa gida. Tana tsoron abunda Uwale zata yi mata kafin gari ya waye taje makarantar. Sai kawai ta fara hawaye. “A’a mai awara meye kike kuka?” Taga wasu maza su uku. Ba zasu wuce Abdulganiyu ba. “Zaku siya awara? Uwale tace kar na dawo sai da dari biyar.” Ta fada musu. Kallon junansu sukayi sannan sukayi murmushi wanda su kadai suka san ma’anar sa. “Dari biyar kike so?” Girgiza kanta tayi alamun eh. “Toh ki biyo mu.” Kallonsu ta shiga yi daya bayan daya. “Babu abunda zamuyi miki. Awara zaki zuba mana kawai sai mu baki kudin.” Inji daya daga cikinsu. Kallon inda shagon Iya Abdulganiyu tayi taga har ta rufe tunda gari ya fara duhu. Ji takeyi kamar kawai ta haqura taje ta zauna a gidan su Abdulganiyun. Sai kuma ta tuno kashedin da akayi mata akan hakan. Zaro kudin daya a cikinsu yayi. “Kin gani ko? Muje can, kinga ai can akwai wajen zama.” Ya nuna mata wani lungu. “Ko ba kya so?” Inji dayan wanda kan sa yasha aski. “Ina so.” Sai kawai ta bisu. Nan ma sake murmushi sukayi suna jin dadi sun samu yarinya mara wayo. Ko da suka isa wajen durgusawa tayi tana zuba musu a leda. Su kuwa kallon juna suke. Salmah bata ankara ba suka far mata. Zatayi ihu suka toshe mata baki da wani yadi. Haka suka wullata a qasa dayan ya sake rufe mata baki. Daya ya riqe hannayenta. Sannan su biyun suka hau layi suna jiran layi ya zagayo kansu. **** Ranar Abdulganiyu tafiyar dare yayi. Har ya wuce ta gefen kangon yaji kamar yaji kuka. Zuciyarsa ta saka shi ya matsa baya har lungun. Nan kuwa yaji sautin kukan na qaruwa. Ciro wayarsa yayi ya haska fuskar Salmah wadda daidai lokacin ta suma. “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.” Daga nan ya fara jero salati. Bai gama rudewa ba sai da ya ankara siket din Salmah ya yage ga jini ko ina. “La haula wala quwata illa billah.” Gumi ne yake zuba ta ko ina kawai a jikinsa. Can ya hango bokitin awarar ta. Haka ya dauke ta a hannu ko numfashinta baya ji. Bai tsaya ko ina ba sai asibiti. Cikin murna Uwale ta amshi kudin tana ta guda. Ranar dai Salmah ba’a yi mata fada ba ko sau daya. Haka wahse gari aka sakata a makaranta. Amma bayan ta dawo daga makarantar, tana zuwa tallan kuma ta siyar da dukka. Haka rayuwa ta cigaba da tafiye, abubuwa suka danyi sauki har Salmah ta shiga shekara goma. A sannan kuma wani fejin rikicin ya bude. Fejin da ko da wasa, Salmah bata shirya da zuwansa ba. Lokacin tayi tunanin tayi bankwana da baqin ciki ashe akwai saura a gaba “Ya Salam.” Da sauri nurses suka karbi Salmah daga hannun Abdulganiyu. Dama akwai kudi a hannun sa, haka ya ciro ya bayar saboda sun ce sai anyi mata dinki. Ko da ya biya komai ya nemi gefe ya zauna, sai hawaye suka fara sauka akan kumatunsa. Abunda yake ta hangowa kenan kuma yake ta kokari yaga ya kare Salmah daga fadawa cikinsa. Sai gashi kash, ya makara. Ina ma yayi zaman sa a Kaduna, don ya baya Salmah duk wata kulawa da ta rasa daga wajen mahaifiyarta. Ina ma Uwalen zata yarda ta bar musu ita tunda ita ta gaza kula da yar ta.+ Haka kawai an zo an lalata ma yarinya rayuwa. Ita bata san hawa ba bata san sauka ba. Yanzu idan Salmah ta qara wayo ta fahimci ma’anar abunda aka yi mata, da wani ido zata kalli Uwale? Tayaya zata so Uwale? Shi kam Abdulganiyu yana tantama. Anya Uwale ce ta haifi Salmah? Domin kuwa uwa dai mai hankali ba zatayi irin abunda Uwale take yiwa Salmah ba. Kanshi na jingine da bango yaji an dafa kafadarsa. Bude idonsa yayi ya sauke su akan wani dogon mutum yasha koren kayan tiyata. Da saurinsa ya tashi yana neman sanin yanayin da ake ciki. “Likita ya ake ciki?” Sai da likitan ya dan yi jim ya girgiza kansa sannan ya kalli Abdulganiyu. “Dan Allah likita kar ka gaya min abu mara dadi. In ma kudin basu isa bane zan kawo biko don’t allow her to die.” Likitan ne ya dan yi murmushi ganin yanda Abdulganiyu ya rude. “Anyi mata dinki lafiya. Everything has been done accordingly. Abunda yasa na zo nan shine ina so muyi wata magana da kai. Are you by any chance her brother?” “Eh, ni yayanta ne.” Abdulganiyu yayi saurin bayar da amsa ba tare da ya tsaya tunani ba. “You’re dark, ita kuma fara how comes? Anyway ina mahaifiyar ku?” Sai a lokacin ne Abdulganiyu ya tuna ashe ko gida bai qarasa ba. Ashe ma bai fadawa kowa ba. “Nayi tafiya ne, a hanya na ganta a kwance. Saboda I was shocked, I couldn’t even get the chance to tell anyone. Salmah was actually not breathing so I had to rush to save her life. Amma dai bari na tafi gidan na gaya musu. Kuma gidan da dan nisa.” Likitan ne ya jijjiga kansa. Tabbas yaga alamar hakan a tattare da Abdul. Tabbas Abdul din a rude yake don har izuwa yanzu gumi yake kawai. Har Abdulganiyu ya juya zai tafi sai kuma ya dawo. “Likita dan Allah amana na baka, zanje na dawo.” “You’re safe. In ka dawo sai muyi magana a ajiye report je ka dawo din.” Likitan ya bashi amsa tare da dan polite murmushi. Hannu ya miqawa Abdul sukayi musabaha sannan Abdulganiyu din ya kama hanyar gida. **** Uwale ce a tsakar gidan Iya Abdulganiyu zaune a qasa hankali ta duk ya tashi. Lokacin har anyi sallahr isha’i Salmah bata dawowa ba. “Mama Salmah kiyi haquri bari Abdulganiyu ya dawo sai muje police station. Baba Abdul ba lafiya ba zan iya fita ba.” Inji Iya Abdulganiyu. Ita ma hankali ta a tashe yake domin kuwa sanda Uwale ta shigo gidan, ta zuba abinci zata ci kenan sai ga shi yanzu har abincin yayi sanyi ta kasa ko loma biyun kirki. Kawai daurewa takeyi tana bawa Uwale haquri in ba don haka ba da tuni tana kuka. “Naje kasuwar ma ance ta dade da tafiya.” Uwale ta fada tana sake yin tagumi. Ita dai qarfin hali ya hana ta kuka kuma ta dage da sai ta nuna rashin damuwarta amma kuma kana kallon ta kasan hankalin ta a tashe yake nesa ba kusa ba. “Mama Salmah lefin ka ne. Na your fault oo.” Chiamaka ta yi magana bayan duk sunyi jugum jugum ana jiran dawowar Abdulganiyu. “Abi oo. Kai da zaka kama yaro ka, ka kulle a gida, ka sake shi banza banza yana yawo a geri.” Deborah ta qarasa da Hausar ta tana nuna dan yatsan ta a dai dai fuskar Uwale. STORY CONTINUES BELOW “Assalamu alaikum.” Sallamar Abdul ta doki kunnuwansu. Gaba daya suka miqe suka yi kansa. “Abdul mi, Salmah ta bata.” Girgiza kansa kawai yayi lokacin da ya kalli Uwale. Toh ta faru ta qare dai. Sai kawai ya rasa mai zaice ko mai zaiyi. Idan ya ja mamansa gefe ya fada mata abunda ya faru toh su Chiamaka yan tsurku zasui ta bincike har sai sun nemo meye asalin abunda ya faru. “Na kai ta asibiti.” Haka kawai yace yana mai kallon gefen inda yake tsaye. Buta yake nema yayi alwala yayi sallah. Matan kawai bin shi sukayi. “Abdul me ya sameta?” Uwale ta dafe qirjinta. “Mota ta buge ta.” Sai kawai ya fice ba tare da yace komai ba. Ita kuwa mamansa tana jin yanayin da yayi magana sai kawai taji bata yarda dashi ba. Ta san qarya yake yi. Musamman ma in yana magana bai kalli mutum ba, toh tabbas karya ce. “Mu jira yayi sallah. Mu ma bamu yi ba fah.” Butoci suka cika da ruwa sannan sukayi magariba da isha. Sanda suka gama yayi dai dai da shigowar Abdulganiyu. “Mu je.” Kawai yace. Iya Abdulganiyu ta dauko hijabinta ta dora kawai suka fice. Nan suka tari mota suka wuce asibitin cikin zulumi. ***** Salmah ce kwance ana mata qarin ruwa. A hankali ta bude idonta tana kalle kalle. Tunda take bata taba yin rashin lafiyar da aka taba kaita asibiti ba. Tura kofar akayi Uwale da Iya Abdulganiyu suka shigo. Tana ganin Uwale sai kawai ta kawar da kanta gefe. “Salmah mi, me ya faru?” Iya Abdulganiyu ce ta fara magana tare da kamo hannun Salmah. “Ce min sukayi awara zasu siya. Kuma basu bani kudin ba. Kuma nan dina zafi.” Uwale ce ta kalli Iya Abdulganiyu. “Ban gane ba. Ke mai kike nufi? Me suka miki, su waye?” “Nima ban san su ba. Kuka suka ga inayi. Nace Uwale zata dakeni in ban siyar ba. Shine sukace zasu siya. Muka je shine suka riqe min hannu…” Uwale ce ta katse ta. “Suka miki me?” “Nima ban sani ba. Amma da zafi. Har yanzu zafi. Iya bana son Uwale. Na tsane ta.” Uwale ce ta saki salati. Ita kuwa Iya hawaye kawai takeyi. Shikenan. “Ni fa ban gane ba.” Uwalen ta sake kallon Iya Abdulganiyu. “Kamar yanda ta fada din haka zancen yake. An lalata ta.” Muryar liktan ta doki kunnensu daga baya. Uwale ce ta kama qarfen gadon ta juya ta kalli likitan. Da gani a rude take kuma tana qoqarin tara nutsuwarta waje daya kafin tayi magana. “Na ajiye takardunta da duk wasu rubuce rubuce da muke kira da hospital report. Saboda idan zaku shigo da yan sanda cikin lamarin domin binciko wanda suka yi aika aikan nan sannan ku kaisu kotu saboda a gaskiya yarinyar nan na buqatar tayi hakan. An ci mata mutunci. Cikin ku wace mahaifiyar?” Tsalle Uwale tayi ta kamo rigar likita. “Likita idan kana son Allah ka bar zancen yan sanda. Mai zai kawo su? Salon kawai a tallata yarinya a bata min suna. Gara a kyaleta ta qarasa jinya nikam.” Likitan ma rasa abun cewa yayi. “Ayi yanda take so.” A haka dai aka binne zancen a cikin asibitin. Bayan sun kadai babu wanda yasan abunda ya faru. Mutane sun zo dubiya amma ko da suka zo cewa akayi ai zazzabi ne ya kamata. Masu kawo abun arziqi sun kawo, masu bayar da kudi ma sun bayar. Har wasu daga cikin malaman su Salmah sun zo dubiya. ***** Present. Sheikh Salim. Tun da ya dawo gida yaji gabadaya yaji duniyar ta tsaya masa. Ko jiqaqqen kayan sa bai cire ba haka ya zauna a tsakar gida kamar wani maraya marar gata. STORY CONTINUES BELOW Abu daya ne ya tsaya masa a rai. Meye dalilin da zai saka Salmah tace tayi masa datti da yawa. Mai yasa lokaci daya ta fara kuka? Ya sani cewa duk hasken dake cikin idaniyarta, duk kyaun da murmushin ke dauke dashi akwai wani abu a bayan su. Kamar kawai ta sanya mayafi ne tsakanin ainahin abunda yake faruwa a cikin ranta ne da kuma abunda yake a bayyane. Sai dai meye wannan din? Shi gaba daya sai yaji gabobin jikinsa sun sage. Jikin sa yayi kamar ya shekara da mutuwa. Zuciyar sa tayi lamo kamar batayin aikin da ta saba. Da kyar ya iya tashi ya saka makulli ya bude gidan ya shiga. Shiru ne ya masa sannu da zuwa, har qasan ran sa yaji babu dadi. Ajiye makullin yayi ya shiga daki. Ya ciro wayarsa ya ajiye sannan ya watsa ruwan zafi ya sanya jallabiya. Sai kawai ya zo ya zauna gaban mudubi kamar wani yaro qarami. Ya dade yana kallon mudubin, a hankali ya hango gidansu dake Katsina. Gidansu shi da Jamilah. Idonsa har inuwarta yake gani a cikin madubin. “Nayi kyau?” Jamilah ta tambaye shi tana gyara zaman daurin dankwalinta. Sanye take da riga da siket na wata shudiyar atamfa. Dinkin ya yi mata kyau sosai. Ko kallon ta baiyi ba yayinda yake kwance a kan gado. Har cikin ransa yasan tayi kyau. Amma akan mai yasa zai yabeta? Haka kawai ta dinga jin itan wata gangariya ce? “Habiby banyi kyau ba?” Ta taka bakin gadon ta zauna. Juyawa daya gefen yayi. Ita kuma sai kawai tayi murmushi ta kamo hannun sa. “Waye ya taba min Masoyina? What’s wrong honey?” Ta tambaya da siririyar murya. “Babu. Barci nake ji dan Allah ki tafi ki kyale ni.” Sai ya sake juyawa yana tsaki. Idonta ne ya cika da hawaye amma duk da haka sai ta danne zuciyar ta, ta rarrashi kwakwalwarta da kar ta bari hawayen su zubo a gabansa. Tashi tayi kawai. “Na saka ma ruwan wanka sannan na gama abinci. Kuma ina so na fada maka wani abu.” Ta dawo da dan murmushinta. Hmm kawai yace ita kuma ta fice. Karan wayarsa ne ya dawo dashi daga tunani. Dubawa yayi yaga baquwar namba. Ba shiri ya kara a kunnensa. Bayan sun gaisa da mutumin da ya kira shi, sai ya tsaya yana jira mai mutumin zai ce. “Abba ne, mahaifin Salmah. An sameta a sume a daki kuma wayarta ta nuna cewa da kai tayi magana a qarshe. Ina so kazo ka same ni a asibitin Nasarawa.” Gyada kanshi kawai yake yi yana bada amsa. Yana ajiye wayar ya saka manyan kaya ya fice. Tuqi yake a hankali saboda cikowar da ke garin Kano a ranar. Mutane nata shirye shiryen azumi. Nan ma sai ya tuna da Jamilah. “Ai da ka sani kace zaka shigo min da yan shan ruwa honey. I would’ve cooked abinci da yawa and they will mistaken the iftaar for buffet. Amma dai bari na kawo muku wanda na dafa mana ni da kai. In ya so kafin ku dawo daga tarawih ko dankali ne na fare.” Hararta kawai yake yayinda take magana. Sai da ta gama tsaf ya tsinke ta da mari. “Tsabar wulaqanci kina sane yau azumin farko amma kice baki dafa abinci da yawa ba? Dole ne sai na bude baki nace miki ki dafa abinci da abokanai na? Kin raina ni ko? Ko?” Hawaye ke tsiyaya a fuskarta kawai. Har ya gama fadan shi ya gama bata ce komai ba. Sai bayan ya fice daga kitchen din ta nufi bakin sink ta wanke fuskarta tana maimaita abu daya a qasan zuciyar ta. Laifi na ne! Da wannan tunanin take rarrashin kanta. Tabbas da ta dafa abinci da yawa ai da bazai mare ta ba. Saboda haka laifinta ne. Dabino ta wanke da kuma abincinta ita da sheikh ta kama hanyar falo. A gefen kujerar corridor ta ajiye tray ta tsaya gyara hijabinta tana kallon mudubin console. Sai da ta gama gyarawan ta yi ajiyar zuciya sannan ta dauki tray ta nufi falo. Tana jiyo hanyaniyarsu da qarfi. Sallamah tayi ta ajiye. “Amaryar mu mungode.” Daya a cikinsu ya fada. Satar kallon Salim tayi kafin ga amsa. “I..ina wuninka. Sannunku. Dafatan an kai azumi lafiya. Ku ci, you’re highly welcome. Please be my guests.” Ta danyi murmushi ta juya. Jin sautin takunsa a bayanta yasa gaban ta ya fadi mai kuma tayi? Sauri take ta qarasa kitchen din don ta rufo kofa. Tana juyawa rufewa din sai ya shigo ya rufo qofar. Da mamakinta sai taji ya rungume ta ta baya. “Dazu nayi miki fada na mareki. Kiyi haquri kinji queen tawa?” Zatayi magana yayi pecking side of her lip sannan yace, “I’m sorry once again.” Juyawa tayi ta rungumo shi. Tana ayyanawa a ranta daman ta san laifinta ne. Ta san ba zaiyi nata haka ba a son ranshi. Haka taji son shi na qara shiga ko wacce gaba ta jikinta. Sakin shi tayi. “Bari na qarasa abincin.” Murmushi kawai takeyi kanta a qasa. “Toh amaryata. Ina sonki sosai Jamilah ta.” “Nima haka.” Sai ta tura shi wajen kitchen din ta cire hijabinta, ta cigaba da aiki. ‘Dama ta san laifinta ne.’ Motar bayan sa ce ta danna masa horn. Hakan yasa yayi sauri ya cigaba da tuqi zuwa asibitin Nasarawa. Tunda likita ya kira Abba oficce dinsa ya masa bayani, hankalinsa ya tashi gaba daya ya rasa inda zai saka kansa. Dama dai tun da aka ce masa an ga Salmah kwance a daki kamar matacciya ga wata kwalba a gefen ta toh sai kawai ya rasa abunyi. Hirar su da likitan ya tuno. “Meye damuwarta?” Abunda likitan ya fara tambayarsa lokacin da ya zauna a gabansa. “Ba ta da wata damuwa. Kuma ita din ba ma’abociyar magana bace.” Abban ya bayar da amsa yana sake hasko yanda Salmah take yin abubuwa. “Toh a gaskiya ba zan boye maka ba. Cikin biyu ko dai yarinyar ku tana shaye shaye ko kuma tasha ne domin ta mutu. Saboda ta sha abunda yafi karfin jikinta. Ba iyakar kwalbar da kuka gani bace ta sha. Har da wasu abubuwan ma. Toh ina ganin yakamata ku zauna da ita sannan kuma muna da qwararrun liktoci da zasu iya dubata su kwantar mata da hankali. Idan zaka iya covering bills en toh I will talk to Dr Guri.” Abba dai gumi kawai yake sharewa. Har likitan ya gama bayanan sa, Abba hankalinsa bai kwanta ba.+ “Abba…” Muhammad ya furta, sannan ya qaraso in da Abban yake. “Abba baqon yazo. Kasan wa ka kira kuwa Abba? Sheikh Muhammad Salim fa. Wannan babban malamin kuma shugaban Hisbah. Anya kuwa shine?” Kallo daya zaka yiwa Abba kasan bama ya jin mai Muhammad din yake cewa. Tunda yaji ance baqon yazo bai qara jin komai ba. “Muhammad mu je. Mu je ka nuna min inda yake.” **** Kwance take, Ummah na gefenta sai faman addu’a take tana shafa mata. Kusan awanni uku kenan da zuwansu amma Salmah bata tashi ba. Motsi ta fara kafin taji tana numfashi. “Ya Allah!” Ta fada yayinda Ummah tayi saurin kamo hannun ta. “Salmah kin tashi? Alhamdulillah!” “Ummah ban mutu ba? Ummah mai yasa ban mutu ba?” Har yanzun bata bude idonta ba. Wasu siraran hawaye ne suke fitowa ta wutsiyar idonta. “Alhamdulillah!” Abba yayi tahmeed sannan suka taho wajen gadon shi da Salim. “Salmah kiyi haquri kinji? Ki zauna mana.” Ummah tayi kokarin gyara mata zama. Sanin cewa Ummahn ba zata haqura ba yasa kawai ta zauna amma bata bude idon ba. “Yaya jikin naki?” Inji Abba. Bayan ya danyi tunani sai yake ganin zaifi idan ya bari sai an sallame su sannan yayi duk wata magana da zaiyi. “Sannu Salmah.” A wannan karon, sheikh ne yayi magana. Abu biyu ne a ranta. Tana son jin muryarsa kuma bata son ji. Tana son ji saboda jin muryarsa kadai na saukar mata da nutsuwa. Jin muryarsa kadai na sakawa ta manta da duk wata damuwa da take damunta. Muryarsa na dauke ta daga duniyar mutane ta jefa ta wata duniyar da bata da masaniyar sunan ta. A daya bangaren kuma, muryarsa na bijiro mata da abubuwan da ta dade da binnesu a qasan ranta. Tana saqa mata da cewa ita din bata da wata daraja. In short, his voice crumbles every wall and barrier she built within the space of her heart. Kafin ya sake magana sai yaga su Abba sun bashi waje. Kujera yaja ya zauna sannan ya numfasa. “Assalamu alaiki.” Ya ce a fili. A zuciyar sa kuma addua yayi irin wadda annabi Musa yayi. Addua irin wadda annabi Ibrahim yayi. Duk dan ya samu dacewa, don Salmah ta gamsu da duk abunda zaice. “Da farko ina mai baki haquri akan duk wani abu da na fada miki a dazu har ya kai ga zuwanki asibiti. Allah ya saukar miki da salama da nutsuwa a zuciyar ki.” Kallonta yake yana adduar Allah yasa ta bude ido ta kalle shi ko da kuwa sau daya ne. “Ban san me nayi miki ba. Ban sani ba ko nine sanadiyyar hawayen ki.” Sai kuma kawai yayi shiru abubuwa da dama suna yawo a kansa. A hankali ta bude idonta ta kalle shi. STORY CONTINUES BELOW “Babu laifinka a ciki. Babu abunda kayi. Amma ka sani ni ban cancanceka ba. Rayuwa ta ta kasance wata iriyar rayuwa. Rayuwa mara alqibla ko saiti. Shiyasa nake fada maka, ni ba kowan…” Tsayar da ita yayi. “Ina son ki ara min kunnenki amma kuma idan zaki ban aron, ki taho da hankalinki saboda ina so ki fahimci abunda zan ce miki.” Gyada kai tayi kafin ya cigaba. “Salmah, Gaba da baya ba zasu taba tafiya a layi daya ba. In dai kana son yin gaba toh tabbas sai ka ajiye baya. Baya ta riga ta gabata, amfanin tuna ta kuma shine daukan darasi daga abubuwan da suka faru a cikin ta. Yayinda ka san baya zata rinjaye ka, mafi kyau shine ka wullar da igiyar ta, ka kama ta gaba. Idan kuma ka kama, ka zamto mai kyautata zaton cewa gaba za tayi kyau. Kuma sai ta yi kyau din!” Shiru ya danyi yana kallon idanunta. So yake ya gani ko tana fahimtar abunda yake cewa. Ganin ya gamsu da yanayin da fuskarta ta nuna yasa yayi murmushi. “Toh haka nake so dake. Bana son jin abunda ya faru dake because I am not part of your past. Gaya min abunda ya faru nasan tabbas zai saka ni damuwa amma mai? Ba zan iya komai ba a kai. Ke ma kuma hankakinki ba zai kwanta ba. Idan kuma hankalin zaifi kwanciya din idan kin gaya min, toh ko yaushe a shirye nake da sauraron ki. Ina tare da ke duk runtsi. Komai munin labarinki.” Salmah ce ta fara girgiza kai tana magana a ranta. Haka kake gani Sheikh. Gani kake kamar zaka iya dauka amma kam banajin zaka iya din. Labarina ba yadda kake zato bane. “Salmah duk wani abu da ya faru is either the consequence of your heart, or body. Wataqila zuciyarki ce ta aikata ko ma meye. Wataqila jikinki ne ko harshenki amma ni ba kowanne nake so a cikinsu ba. Saboda ko wannen su baya aiki shi kadai. Ko wannan su yana samun external influence. Idan shaidan ya samu waje, ya kan zuga zuciyar mutum. Zuciya ta zuga duk gabobin jikinki. So I’m in love with none.” “Instead, ruhinki nake so. Saboda ina da tabbacin ruhinki mai kyau ne. I mean I know your soul is squeaky clean. Zuciyar ma ina so sai dai zan qara sonta ne idan kika taimaka min kika wanke ta, kika tsarkaketa. Allah yana cewa haqiqa wanda yake tsarkake zuciyarsa yayi nasara. Toh ki manta da baya, ki wanke zuciyar ki daga jirwayen da shaidan ya disa miki. Ko jirwayen da yanayin rayuwa ya goga miki. Ni kuma ina mai tabbatar miki da cewa babu abinda zan so kamar zuciyarki domin aslan ta kasance mai kyau din.” “Haka kake gani.” Tace. Sheikh ya dafe kanshi. Da alama dai Salmah wasn’t ready to give in. “Shikenan na san yanda zanyi dake. Bari a sallame mu. Kafin nan ina so kisa a ranki idan babu ke, babu sheikh. Saboda haka in kika ji an ce Salim, Salmah ake nufi. Duba kiga sunan mu ma ai kusan ma’anar su daya saboda ni din naki ne. Kuma ke din tawa ce. Ko a hanya ma aka ganmu ai zata za’a yi yan biyu ne mu.” Salmah ce ta danyi dariya. Tab, wannan qaton mutumin ne za’a ce dan biyunta ne. “Tab ka rufa min asiri. Tsoho da kai ka hada kanka dani?” Harararta yayi cike da tsokana. “Shekarata ashirin da biyu fa kawai.” Ya bata amsa yana tabe baki. “Kaiii!” Sai ta jefe shi da pillown gefenta tana murmushi. “Ouch zaki ji min ciwo. Baki san ba’a dukan bafulatani ba? Yanzu zanyi jawur.” “Kayi ja kamar tumatir ma.” Ta fada ranta yana qara saki. “Toh shikenan ai. Mai zaki ci na kawo miki?” Yana fadan hakan sai ta tuno lokacin da ta kwanta a asibiti da lokacin da Abdulganiyu yazo duba ta. Da lokacin da yazo mata rakiya zuwa makaranta. ***** SALMAH’S STORY. * Bayan wata daya da sallamarsu, Salmah ta ware sarai amma sai ta koyi wani shiru shiru, duk wannan kazar kazar din ta rage shi. STORY CONTINUES BELOW Duk da kuwa safiya ce, Karime ce zaune abun duniya ya isheta. Ita yanzu an saka mata ido an hana ta samun kudi da Salmah. Iya Abdul tace duk sanda ta qara saka Salmah talla to tabbas zata je ta kira likitan nan shi kuma likitan ya kira yan sanda daga nan sai a sada su da hukumar kiyaye haqqin yara in yaso jami’an hukumar su zo su kama Karime su tafi da ita saboda cin zarafi da tauye haqqi da tayi wa Salmah. Hakan yasa Karime take ji kamar an daure ta ne an hana ta sakewa. Ita gaba daya wannan ai takura rayuwa ce a wajen ta. Bata da sanin cewa ko musulunce yara na da haqqi akan iyayensu kamar yanda iyaye ke da haqqi akan yayansu. “Uwale sai na dawo,” Salmah ta fada tana gyara hijabin makarantarta. Yanzun ta warke sarai kuma tana jin zata iya zuwa makaranta. Karime bata ce mata komai ba. Yi tayi kamar bata ji mai tace ba. “Uwale ina kwana, zan tafi makaranta.” Ta gyara maganarta ta. Ko karyawa batayi ba saboda ba taga an ajiye mata abun karin ba. Cikin wata gudan nan rana dai daya ne suke magana da Uwale shima baya wuce aiki. “Ba sai ki tafi ba? Dama nasan ke mayya ce mai farar kafa tunda na haifeki rashin sa’a ke samu na. Yanzu kin jawo min bala’i nace ki tafi din. Yanzu in nace kar kije ma wani bala’in zaki janyo min. Kaico, dama barinki nayi na huta wannan yarinya.” Abubuwa da yawa da Uwale ta fada Salmah bata fahimce su ba amma dai ta san duk zagi ne. Hakan yasa kawai ta koma gefe ta zauna. “Zaki tashi ki fice ko kuwa?” “Uwale kin ce kar naje.” “Ni nace kar kije? Salmah yanzu sharri zaki min? Ina magana ma kina musa min koh? Oh ni Karime.” Dafe kanta tayi zata fara kuka sai Salmah tayi saurin tashi. “Yi haquri Uwale kar kiyi kuka.” Daga nan, sai ta fice. Tana fita taga Abdulganiyu a tsaye kamar ya san zata fito din. Suna hada ido sai ta fara kuka. “Yaya ni bana son Uwale. Uwale ta tsane ni. Ni ban san me nayi mata ba. Kuma na bata haquri fa.” “Ki daina cewa haka. Uwale bata tsane ki ba kinji?” Kallonsa tayi kawai irin bata yarda dashi ba sam. Shima yaga hakan a idonta amma bai san mai zaice ba. “In tana miki fada ki daina mayar mata da amsa kinji? Allah ya hana hakan.” Tabe baki tayi. “Toh ai ni babu abunda nayi.” “Duk da hakan. Allah yasani ai. Ko meye ta miki shiru zakiyi saboda haka Allah yace ko da kuwa kaine da gaskiya.” Salmah bata qara cewa komai ba har suka je bakin makarantar. “Mai zaki ci na kawo miki da break?” Girgiza kanta tayi. “Ki fada mana. Ko meye.” Bata bashi amsa ba ta shige tana jin cikinta na qugin yunwa. Haka malamai suka yi ta tambayar ya jikin ta. Qawayenta ma haka. Duk ta ce musu ta ji sauqi sannan ta tafi aji. Tararwa tayi anyi mata nisa sosai. Hakan yasa ta nutsu a aji ba tare da tayi wa kowa magana ba. Da break yayi sai ga Abdul nan ya kawo mata daffafiyar indomie da lemon Caprison. Kallonsa tayi tana hade rai. “Iya ce tace na kawo miki.” Yayi saurin fada don kar tace ba zata karba ba. “Ba da gaske kake ba.” “Da gaske nake mana. Me yasa kika ce haka?” Zama yayi a kasan wata bishiya dake tsakiyar makarantar. Yara sai guje guje suke yi wasu kuma suna zaune suna cin abinci su. Dage gira Salmah tayi sannan ita ma ta zauna. “Ai idan ba da gaske kake ba baka kallon mutum.” Mamaki ne ya kama shi. “Wa yace miki?” Dariya ya dan yi sannan ya bude mata flask din ya bata. Straw din lemon ya ciro ya bude lemon ya bata. “Ki ci.” Babu musu ta ja flask din ta fara ci. Sai da taci rabi sannan ta tsaya. “Kaci abinci kai ma?” “Naci.” “Baka ci ba. Toh kaci wannan.” Ta miqa masa. “Ai ni bana cin wannan. Abincin yara ne.” Ya bata amsa. “Toh ko loma daya ne. Da dadi fa.” Sai ta dibo da cokalin ta miqa masa cokalin. Karba yayi ya hadiye da kyar. “In kaje gida kaci abinci. Ka cewa Iya nagode. Kaga an kada qararrawa zamu koma aji.” Tashi suka yi a tare suna karkade jikinsu. “Yaushe zaka fara makaranta?” “Kudin nake hadawa. Ki min addua naci jarabawa wannan karan.” Toh kawai tace. Ya juya ya tafi ita kuma ta koma aji. Haka dai suka cigaba. Yau da dadi gobe babu dadi. Har Salmah sukayi jarabawar shiga makarantar gaba da firamare. Taci jarabawar ta fara har ma yanzu tana aji uku (Jss 3) a lokacin tana shekara sha hudu. Abdul ma ya samu gurbin karatu a jami’ar dake Legas in da yake karantar Electrical Engineering. Duk sanda yazo hutu suna tare da Salmah. Lokacin ta qara tsaho amma jikin na nan jiya I yau. Watarana an tashi daga makaranta sai taqi tahowa ta zauna tana ta kuka a gefe. Wani abu ya tsayar da Abdul ya saka bai zo da wuri ba. Sanda ya tabbatar bata dawo din ba yasa ya je makarantar. A zaune take ta takure waje daya hakan yasa hankalin Abdul ya tashi sosai. “Me aka miki?” Yayi saurin qarasawa. “Babu.” Ta bashi amsa. “Toh tashi mu tafi.” Ko motsi bata yi ba. “Ki tashi mu tafi nace. Meye hakan? Ko an miki wani abu ne?” Kamar wasa yayi kusan minti sha biyu yana yi da ita taqi tashi karshe tayi magana. “Ni dai ka kira min Iya.” Shiru yayi yana tunani. “Kin san Allah zan tafi na barki anan kuma ba zan kira ta ba.” “Ni idan na tashi mutane zasu kalle ni.” Tsaki yayi ya dafe kansa. “Bana son shirme fa. Biko stand up.” Yayi taqi tashi haka dai ya haqura ya tafi da yaga da alama ko mai zaiyi ba zata tashi ba. Gida yaje ya kira Iya ya fada mata abunda yake faruwa. Ba shiri tace masa ya zauna a gidan tana zuwa. Ba a jima ba taje ta taho da Salmah bayan ta bata dogon hijabi ta saka. “Idan kinje gida ki gaya wa Uwale.” Iya ta gaya mata bayan ta gama yi mata duk wani bayani. “Iya ki gaya mata.” “Ke zaki gaya mata. Babu abunda zata miki.” Toh tace ta fito. Tana fita suka hadu dashi. “Meye ya same ki?” Ya tambaye ta. “Babu komai fa.” Ta qara saurin tafiyarta. “In baki fada min ba ba ruwana dake.” “To ai malamarmu tace ba’a fadawa maza.” Bata qara cewa komai ba ta juya ta cigaba da tafiya tana tunanin abunda zata gaya wa Uwale. “Toh muga meye a ledar?” Bata ma ji ba saboda tayi masa nisa. Murmushi kawai yayi, yana juyawa yaga Iya tana harararsa. Sadaf sadaf yayi ya shige shagon kofar gidan. **** Tana zuwa Uwale ta tsayar da ita. “Meye kika dade?” “Naje gidan Iya ta bani wannan.” Sai ta miqa mata ledar hannun ta. Budewa Uwale tayi sannan ta kalli Salmah. “Meye wannan din?” Sarai so take ta ji ta bakin Salmahn. “Ni ban sani ba. Ni dai ta bani. Kuma dama a makaranta ma an nuna mana irin shi. Jummai ma tace tana amfani dashi.” “Toh shige daki. Kuma bana son na qara ganinki da wannan dan iskan yaron.” “Waye?” “Abdulganiyu ko wa?” “Uwale me yayi?” “Ke baki san ba’a yiwa maza magana ba idan an fara? Toh kiyi magana ki gani, wuta zaki shiga.” Salmah dai bata ce komai ba ta shige dakin. ***** Salmah tayi kamar kwana biyu a asibiti aka sallame ta. Kuma duk a kwanakin babu ranar da Sheikh Muhammad Salim baya zuwa duba ta. Duk da kuwa tana jin duniyar tayi mata wani iri lokaci guda, amma in ta ganshi, ta kanji sanyi a ranta. Gashi kuma tana tunanin daga lokacin ya nemi izinin Abba na zuwa wajenta. Babu wanda ya fada mata hakan, a jikinta take jin alamu. Har yau Abba ko Ummah basu ce mata komai ba. Gaba daya tsoro take ji kar taje sun gane halin da take ciki. Wata iriyar kunya da nauyinsu take ji yanzu. Domin ta san su Abba suna qoqarinsu a kanta. Kuma ba zasu so a ce tana abunda take yi ba din. Ko ba sa qoqari ma ai basu cancanci ta watsa musu qasa a fuska ba tunda a qalla sun dauki nauyin ciyar da ita, sun sama mata wajen kwana kuma mafi girma, sun dauke ta daga gaban Uwale. Ajiyar zuciya ta sauke tana jijjiga kanta. Allah ya sani sanda ta fara shan abun bata taba tunanin zai kai ta zuwa yanzu ba. Abun takaici ma shine a halin yanzu kawai ji take tana kwadayinsa. Gashi dai ranta ba a bace yake ba ko wani abu. Haka kawai take jin wani abu yana dallarta yana ingiza ta. Wani abu yana ce mata ta kira qawarta ta kawo mata. Wani bangare na zuciyar ta ne ya shiga yi mata fada. Yanzu idan ta kuma sha wani abu ya faru kuma fa? Idan har tayi nasarar tsallake wannan tarkon da ta fada shin zata tsallake na gaba ne? Fadan da zuciyarta ke yi mata ne lokaci zuwa lokaci ke sakawa ta dan ji dadi. Ko babu komai zuciyarta bata gama mutuwa ba. Da sauran ran ta.+ “Assalamu alaikum.” Muryar Ummah ta katse ta. Daga yanda Ummah tayi mata murumushi ta sani cewa ba su da masaniya akan duk abunda yake faruwa. Ko mai likitan ya ce musu oho. “Wa’alaikumus salam. Ummah,” tashi tayi daga inda take zaune tana qarasawa inda Ummah take shigowa. Zata rantse da kyar qafarta take dagawa daga kasa, in an qura mata ido za’a lura da hakan. “Koma ki zauna. Magana zamu yi.” Zatayi qarya idan tace ba taji zuciyar ta ta buga ba. Ba bugawar kadai tayi ba har tsalle zuwa cikinta take tunanin tayi. Ba shiri taji wani zazzabi yana shirin kamata. Zazzabin da lokacin da yayi mata kamu na qarshe ya wujijjiga ta, ya saka duk tayi wata iriyar muguwar rama lokaci daya. Ko a mafarki bata sake fatan irinsa. Bata fatan wani abu da zai saka ta sake irinsa kuma ba ta jin ma akwai wani abu da zai saka ta yin sa. “Ki kwantar da hankalin Salmah. Ki min bayani dalla dalla…” Ta tsinci muryar Ummah. Gaba daya ta ji kamar an shafe wani bangare na cikin qwaqwalwarta, wato bangaren da yake bada izinin magana. Bude bakinta tayi amma ba’a aiko da komai ba daga qwaqwalwarta saboda haka bata iya cewa komai ba. Ji takeyi kamar an saka zare mai kaurin gaske an daure mata harshe yayinda kuma aka saka wani qatoton kwado a ka kulle bakinta. Ummah ce ta lura da yanayin da Salmah ta shiga ciki. Ita ma shigen yanayin ta fada lokacin da Abba yace mata ai Salmah tayi yunkurin kashe kanta ne. “Kar ki damu. Fada min zakiyi mai yake damunki har kika dauki wannan matakin? Salmah ina quntata miki ne? Ko kina son komawa gida ne?” Ummah ta tambaya. Mamaki kadai ya saka ta dauki kwanakin da ta dauka bata yi wa Salmah magana ba. Hawaye ne suka fara zubowa daga idon Salmah Tabbas bata yiwa Abba da Ummah adalci ba. “Ummah… Baku min komai ba… Abubuwa ne suka min yawa suke ta hautsina a cikin qwaqwalwata shiyasa na zata idan na mutu komai zai zo da sauqi… Amma…” Bata samu damar qarasawa ba kukan ya kwace mata. Tamkar zubar ruwa haka take kukan babu qaqqautawa. Yi take kamar zata shide. Ummah kuwa sai tausayinta ya kama ta. Janyo ta jikinta tayi ta rungume ta. Har cikin ranta take jin kukan Salmah na sosa mata rai. “Ki bude kunnuwanki da kyau ki saurareni. Kinyi yunkurin kashe kanki saboda ki samu sauqi ko Salmah. Suicide? Kin yi tunani sau biyu kuwa? Na tabbatar ba kiyi tunani biyu ba lokacin da kika yanke shawarar daukar ranki. Toh bari in gaya miki tunani na biyu da bakiyi ba.” Hannun Ummah taji a fuskarta yana goge mata hawaye. STORY CONTINUES BELOW Haka kawai taji tamkar hakan yana nufin ba zata sake kuka ba. Kamar Ummah na bata haquri da tabbacin cewa ba zata sake zubda ko da qwalla ba a rayuwarta. A karo na farko taji wani irin dadi wanda da wahala ta iya yin bayaninsa. Sai dai ta taba karantawa akwai irin dadin da ake ji idan mutum yana tare da mahaifiyar sa. Gashi dai ta girma a gaban mahaifiyar ta amma bata san wannan dadin da ake ji ba. Yau sai taji dama a tare take da Ummah duk tsawon shekarun nan maimakon Uwale. “Tunani na biyu da bakiyi ba shine, idan kika mutu ta wannan hanyar meye zai biyo baya? Wani irin daci zaki sanya a zukatan wanda zasu ji labarin yin hakan da kika yi? Shin kina da tabbacin abunda zaki tarar idan kin mutu?” Girgiza kai ta shiga yi. Bata da wani tabbas na rayuwar nan. Nan ta shiga wani fagen tunanin ta auna ta gani, me ma ta aikata wanda take ganin kamar zai tserar da ita? Sakanni haka suka wuce ba tare da ta samu qwaqqwarar abu ba. Lallai kam ta kusa tafka babban kuskure. Ga lefin kisan kai wanda Allah ya haramta kuma yayi wa wanda ya aikata hakan da albishir na wuta. Bayan wannan kuma sai me? Sallah ma ta tabbatar ba yanda ya dace takeyi ba. Karatun Qur’an fa? Sai tayi wata bata dube shi ba. Dama izu goma kadai ta iya. “Ko sahabbai wanda Allah yace ya yarda dasu, su ma suna tsoron haduwa da Allah duk da kuwa sun kasance salihan bayi Salmah. Ke kuma fa? Ba ina cewa wani abun bane, na sani Allah mai yawan rahama da gafara ne amma dan Allah kar ki sake irin wannan ko da wasa. Kar ki sake tunanin yin haka. Yanzun shekarar ki kusan ta uku a gidan nan kuma ban taba samun matsala da ke ba sai yanzu? Haba Salmah.” Ummah ce ta kawar da kanta gefe tana tunawa da irin zaman da Salmah tayi da mahaifiyar ta. Wataqila shine dalilin damuwarta amma ko ma meye kisan kai ba mafita bace… “Ummah kiyi haquri. Ba zan sake ba in sha Allah.” A yanzun ta goge hawayenta tana daukarwa kanta alkawari cewa ba zata sake zubda hawaye dangane da abunda ya faru a baya ba. “Ko ke fa… Ki riqe istighfari, da tasbihi da karatun qur’ani domin shi waraka ne ga dan Adam. Istighfari yana da matukar falala, ki riqe shi Salmah.” Kai kawai ta daga mata. “Bari na kawo miki abinci.” Dan murmushi ta yi. “Na qoshi Ummah.” Ta bayar da amsa tana daga kanta daga jikin Ummahn. “Ai kuwa sai kin ci.” Dariya tayi sannan ta fice. ***** Kusan mintinsa goma yana zaune yana tunane tunane. Kwanakin nan gaba daya ya rasa mai yake masa dadi. Tashi yayi ya watsa ruwa sannan ya fito yana goge jikinsa. Sai da ya shafa mai ya saka kaya sannan ya shiga kicin. Taliya ya dora, ya soya manja sannan ya jira taliyar ta dahu. Ita kadai ya iya dafawa sai indomie. Amma ko shinkafa ya dafa sai yaga batayi yanda yake so ba. Sanda ya juye ya dawo falo ya zauna wuta a ka kawo. Kunna talabijin yayi yana kai tashar da ake haska finafinan indiya. Jameelah ta kasance tana son fim dinsu sosai. In tana kallonta ko ta kanta baya bi amma kuma ya san sunayen wanda take kalla. Yanzun ma daya daga cikin su ne. Shi ko sunayen yan wasan ma ba ya riqewa. Jamilah kuwa har Indiyanci take ji shi kam babu abunda ya sani sai abu daya. Shi ma ita ce take kiransa da shi wasu lokutan. Meri pyar… In da ake haskawa ne yasa ya fara tunanin ta domin ya taba ganin tana kuka a wajen. Wata a cikin yan wasan ce ta taho a guje wajen wani namiji, bai san sunan sa ba. Tana qarasowa yace mata ‘I love you’ sannan kuma ya cigaba da surutai a yaren Indiyan wanda shi bai gane ba. Yana kallon fuskar matar tana murmushi kafin kuma ta dena. Daga baya kuma ta koma daki tana kuka ta hada kayanta ta bar garin. Sanda ta shiga jirgin qasa ma, Jameelah tana ta hawaye. Shi kam bai fahimta ba, sai yanzun kawai yake qoqarin gane meye abunda ya faru a daidai wajen. Wayarsa ya zaro ya nemo fim din ya sauke shi a wayarsa. So yake ya gane me ya faru duk da kuwa yasan yanzu ba amfani zai yi masa ba. STORY CONTINUES BELOW Sanda ya fara kalla sai ya burge shi musamman alaqar yan wasan biyu wanda yanzun ya gane sunayen su… Anjali da Rahul.2 Tunawa yayi ashe Jamilah ta taba gaya masa… Daga nan kuma ya fara tuno abunda ya faru a ranar… *** Kamar kullum idan ta gama aikinta na cikin gida, ta kan kalli fim ko wanne iri Musamman ma na indiya saboda sun fi burge ta. Yanzun ma qarfe biyar na yamma amma har girkin dare ta kammala, tayi wanka ta sanya riga da siket yan kanti sai qamshi take bazawa. Gashinta ta saki ya sauka kan kafadarta sannan ta fito falo ta kunna talabijin inda ake haska wani fim. Bata taba kallan sa ba kuma taga alamar zai yi mata dadi. Tana cikin kallo ne taji shigowar Sheikh. Duk yanda take son kallon, haka ta haqura ta tashi zuwa yi masa sannu da zuwa. “Sannu da zuwa Jaan.” Ta fada tana karban jakarsa sannan tayi murmushi. Kallonta yake yi yana ganin yanda tayi kyau. Ranar anyi rana saboda haka ya gaji sosai amma da ya ganta sai yaji gajiyar na watsewa cikin iska. Ajiyar zuciya yayi ba tare da ya tanka kwalliyar tata ba. “Yauwa sannu Meelaty.” Shiga yayi yayinda yake jin nutsuwa na saukar masa kasancewar ganin ko ina da yayi tsaf tsaf. Toh amma me? Ba sai ya yaba ba. Raini kawai zai jawo masa. Haka ya shiga ya yi wanka ya fito sanye da qananan kaya. Abinci ta kawo masa, ta zuba. “Na baka a baki?” Ta tambaya tana yar dariya. “Saboda kin maida ni sa’anki?” Girgiza kanta tayi. “Allah ya baka haquri.” Tace, sannan ta ajiye cokalin tana komawa kan kujera ta cigaba da kallonta. Ita dai taga Ummanta tana bawa Abbanta abinci a baki kuma babu wani raini a tsakanin su. Amma tunda shi Sheikh haka yake so, hakan zata bi da shi. Tana mishi son da ko mai zaiyi ba ya damunta. Ita kawai farincikin sa take so, shikenan. “Mai kike kalla ne?” “Wani fim ne. Zo mu kalla.” Matsawa tayi ya zauna a gefenta kanshi yana jingine da kafadarta ta. Hannu tasa ta shafa fuskarsa. “Wai nikam yaushe zamu je gida ne?” Ta tambaya lokacin da aka tafi talla. “Wani gidan?” Wani abu ta hadiya. “Gidan ku mana?” Tana iya tunawa rabonta da gidan tun ranar da aka kawo ta. Kuma yanzun ta kusa shekara a gidansa. “Ni ai ina zuwa ba sai kinje ba.” Yanayin da ya bata amsa ne ya saka taji ba sai tace komai ba. Ita kam tana mamaki ace babu wani dan uwansa da yake zuwan mata. Ai kuwa duk randa taje gida zata biya ta gidansu ta gaishe su. Ba satar hanya zatayi ba, a’a zata fada masa ta baibai. Cigaba da kallon tayi ba tare da ta ce komai ba. “Wannan fim din da kike kalla su suke sakawa kina kwatanta abubuwa a kaina ko? Kin manta ko ke wacece ko? Kin manta su indiyawa ne ke kuma bahaushiya? Ko nace bafulatana? Ba ki san matar bahaushe na da bambanci da matar wani daga wata qabilar ba?” Ita kam ta sani. Ita ta sani matar bahaushe ce mata tamkar baiwa. Matar da bata da yancin kanta. Matar da ake tsammani ta sadaukar da duk wani farin cikinta zuwa ga oganta wato mijinta. Matar da wasu sarqoqi ke rataye a wuyanta suna hanata sakewa, da wasu tagullai soke a huhunta domin su sanya ta numfashi da kyar. Matar da kawai rayuwarta da komai yana karkashin mijinta ne. Amma ita ba matar bahaushe take son zama ba. Ba kalar rayuwar bahaushe take so ba. Kalar matar musulmi mai bin abunda Allah yace da sunnar manzon Allah sallallahu alaihi wassalam. Hakan yasa ta auri Sheikh amma zai ta ga ba haka ba. Ta zata duk wasu abubuwan da yake yi sanda suna soyayya yana yin su ne saboda ba su zama daya ba. Yanzun kuma sai ta fuskanci ba haka bane. Shi kawai tsarin rayuwar sa ce a haka. Shima din mijin bahaushiya ne. STORY CONTINUES BELOW Duk mafarkinta bai wuce ta auri mutumin da zata sake da shi ba. Mutumin da zata yi rayuwa a cikin gidansa tare da yanci irin wanda addinin musulunci ya tanadar. “Ni ba matar bahaushe bace. Matar musulmi ce. Musulmin ma kuma Sheikh wanda zai zama Sheikh din gaske a gaba.” Ta bashi amsa. Tana ji ya gyara zama. Ba tace da shi komai ba ta cigaba da kallonta. Ko da yake idanunta nakan kallon amma hankalin ta yayi nesa. “Wace matar musulmi? Meye marabarta da matar bahaushe?” Ya fada bayan yayi wani nazari. Gyara zaman ta tayi itama tana juyowa ta kalle shi. Ba ta fara magana kai tsaye ba saboda ta san mai zai biyo baya. A cikin kwakwalwarta ta fara jero siffofin da ta kira da siffofin matar musulmi. Ita ce matar da; ita da mijinta suke tamkar abokai, suke bayyanawa junansu damuwarsu su samu maslaha tare. Idan suna cikin farin ciki, sukan taya junansu murna, suyi kuma adduar dorewar haka. Tsakanin matar da mijinta kuma wata shaquwa ce da ta wuce qawance, da wani sakewa da suke ji da junansu. A tsakanin su akwai girmama juna da kyautatawa juna, da kuma yabawa juna. Akwai rufin asiri, da tausayi, da taimako, da qauna, da yafiya, da bayar da lokaci, da tsokana da sauran su. Matar musulmi ita ce matar da mijinta yasan darajarta, mutuncinta da kimar ta kuma yake girmamata. Itace wadda in tayi ba daidai ba zai gyara mata cikin nutsuwa ya mata wa’azi, idan tayi daidai ko ta yi abu dan faranta masa ya yaba mata ya sa mata albarka ya mata addu’a Allah ya saka ta a aljanna. Ita kuma ta kasance mai girmama shi da qoqarin kyautata masa da yin duk abunda yake so. Wannan sune wanda suka bi ayar da tace ma’aurata kamar libas- sutura ne ga junansu. Amfanin sutura kuma yana da yawa. Bayanan da Jamilah take dashi akan wannan suna da yawa amma bata san ta inda zata fara yiwa Sheikh bayani ba kuma ma tana da yaqinin ya sani. Toh me yasa zai dauki abun al’ada ya daura akan sa. Al’ada tafi addini ne? “Ina jin ki…” Ya katse mata tunani. Ita ta manta ma jiranta yake ta kora masa bayani. Runtse idonta tayi sannan ta fara. “Manzon Allah S.A.W ya kasance ya na taya matan sa aiki, yana wasa dasu, yana girmama su, baya daga musu murya, yana kuma yaba musu, yana musu addu’a. Yana tafiyar dasu kamar abokan sa domin kuwa matar mutum abokiyar zaman sa ce ba baiwa ba. Har yar tseren doki suke yi da Nana Aisha. Ya kan rakata wajen kallon wasa ta hau bayan sa tana kallo kuma ba zai ce komai ba har sai ta gama. Misalai suna da yawa my Sheikh. Fiyayyen halitta wato annabin mu S.A.W shine ya kamata ya zamo role model din mu, someone who we are supposed to copy from ba mu zauna cikin jahilci da wasu al’adunmu suke dauke da shi ba. Idan ance Sunnah, ana nufin duk wani abunda annabi yayi shi ko?” Ta tambaya. Da kyar Sheikh ya daga kai yana jin wani abu a wuyansa. Wai wannan matar tasa a ina ta san wannan? Ita fa ta cika surutu da yawa kuma surutun nata yakan bata masa rai. “Toh me yasa ku maza ba zaku yi koyi da wannan ba? Mai yasa Sunnahr da kuka sani ta dingile wando ce da kuma yin mata hudu?” Ta tambaya kuma har cikin ranta amsa take fatan samu. A fusace ya miqe yana huci. Har gabanta sai da ya fadi tana tunanin ko tayi wani sabo ne. “Rashin kunya zaki min? Jameelah rashin kunya ko?” “Ni ban ga lefin abunda nace ba. Me nace ba daidai ba? Tambaya nayi kuma amsa nake son ji wataqila na samu qarin ilimi akai. Nikam ka bani amsa…” Daga hannun sa yayi sannan ya dungule shi. “Idan kika qara magana wallahi zaki kwashi haqoranki a qasa.” Bata ce komai ba, ya fice daga falon. Sauke ajiyar zuciya tayi. Ko babu komai ranta fes take ji saboda ta tabbatar yaji duk abunda tace. Ya rage nasa ya dauka ko kar ya dauka. Kuma amsa ce sai ta ji ta ko ba yau ba. Kuma daga bakinsa take son ji. Ita fa a tsarinta in dai magana tazo sai ta fade ta tun tana qarama haka takeyi. Bambancin da aka samu shine yanzun ta kan dan tauna maganar kafin tayi ta. A dole ta koyi hakan, saboda gujewa fushin mijinta, Sheikh. Tana jin sanda ya banko kofar waje. *** Assalamu alaikum. Fatan na same ku lafiya. I’m sorry for being away for so long… Ba ni da wani dalili da ya wuce rashin son rubutun. Wataqila idan kuna voting, commenting da sharing wa abokai da yan uwa na dinga typing kullum. I’m serious… Yeah. To those that checked on me, lafiya qalau kuma nagode da kulawarku. ***Bai dawo gidan ba sai bayan sallar Isha’i. Tare da abokansa uku suka shigo. Tun kafin yayi magana ta shiga kicin ta duba abincin ko zai isa ta basu. Ba zai isa ba kuwa, dama shinkafa ce da miyar kayan ganye, vegetable soup. Sheikh baya son cin tuwo da daddare shiyasa dole ta nemi abincin da zatayi musu da daddare kuma wanda ya bambanta da na rana. Fridge ta bude ta dauko wata jar miya da tayi ta ajiye musamman saboda abokan sa masu zuwan ba zata. Macaroni fara ta dafa nan da nan. Miyar kuma ta dan hade ta da ta kayan ganyen dan tayi yawa. Yawancin lokuta da abokan sa biyu yake shigowa duk da bai fada mata ba har sunayen su ta riqe. In bata gansu ba kwana biyu, ba ta yin magana. Rannan da ta tambaya cewa yayi wato har kallan abokan sa takeyi shine har sunan su ta sani. Tun ranar bata zancen su. “Abinci fa?” Ya sameta a falonta. “Yana kitchen.” Ta bashi amsa. Wucewa yayi ya dauko ya tafi da shi falonsa inda abokan suke. Tana jin hirarsu da dariyarsu har qarfe goma. Sannan taji suna shirin tafiya. A motarsa ya mayar dasu. Bayan ya dawo rabe rabe kawai suke yi shi da Jamilah. Bata yi yunkurin sake yi masa magana ba, bayan sannu da zuwa da tace masa. Ita dai in ta yarda tana da laifi to tana bada haquri ko ba’a buqaci hakan ba, idan kuwa bata yarda ba to ba zata bayar da haquri ba ko mai za’a yi kuwa. In dai ta wannan fannin ne mutumin zai zata wata yarinya ce daga mutanen annabi Nuhu; tsabar taurin kai. Ko thamud ko aad.+ A kan idonta qarfe goma da rabi tayi. A sannan ta gaji da zaman kallon ma. Kashe talabijin din tayi da fitilun falon. Kicin ta shiga ta sha ruwa sannan ta wuce dakinta. Dama tana idar da sallah taci abinci. Ba ta bari tara tayi bata ci abinci ba. Hakan kuma na da nasaba da shawarwari da masu kula kiyon lafiya suka bayar. Tana zuwa ta watsa ruwa ta saka kayan barci. Riga da wando ce. Sai da ta taje kanta ta daure shi a tsakiya sannan ta fesa turarurruka masu qamshi. Bata saka hula ba ta wuce dakin Sheikh. Tana zuwa ta qwanqwasa. Ehem yace sai ta zata ko yana bandaki ne. Tura qofar tayi ta shiga bakinta dauke da sallama. Zaune ta gan shi gefe guda da laptop dinsa. Tana kallo ya daga kai ya kalle ta. Da zasu hada ido, sai ya dauke kai. Tabe baki tayi ta shiga dube duben babu. Tafi minti koma tana bude wannan drawer ta rufe wancen. Bai ce mata komai ba sai da tazo fita. “Me kike min a daki?” Ya tambaya muryarsa kamar a gajiye yake. “Abu nazo nema.” Ta bashi amsa tana yarfa hannu. Tana sane da duk abunda take yi. Ta san irin abunda yake daukar hankalinsa duk da kuwa ko sau daya bai taba fada mata ba. “Mai zai kawo abunki daki na?” Ya sake tambaya. “Ba abu na bane. Dama wani turare zan dauka na fesa kuma ban gan shi ba. In ban fesa ba bana iya barci.” Kafe ta yayi da ido. Lallai… Yaushe aka fara hakan bai sani ba? Wanne a cikin turaren nasa? Haka kawai yaji abun ya burge shi har ma yana so a cigaba da zancen. Rufe laptop din yayi ya taso. “Nuna min shi.” Idonta ne ya fada kan mudubin nasa sannan ta kalle shi. Har ya qarasa inda take bata ce komai ba. Hannayenta ya kama ya hadesu waje daya kamar zai zaneta. “Sunan zaki fada min in har hakane.” Mutsu mutsu ta fara tana son qwace hannun. “Ni ban san sunan ba.” Ta fada tana tura baki. Yar dariya yayi da ta saka taji sanyi a ranta. “Cewa kika yi fa ba kya iya barci in babu shi, dole kin san sunan.” Kanta ta sunkuyar qasa tana motsi da yatsun qafarta. Daga kafarta daya tayi ta dora a kan tashi. Tana kallo ya kalla bai ce komai ba. “Jiran ki nake fa… Ya sunan turaren?” Ba shiri tace, “Sheikh Salim.” Bata ankara ba taji ya bushe da dariya. Kana ji kasan da gaske yake yi kuma daga bangaren nishadi na zuciyar sa yake fitowa. STORY CONTINUES BELOW Yana darawa ya kalle ta. “Ni ne turaren?” Gira daya ta daga mi shi alamun eh. “Taya kuwa na zama turare?” Yanzun ya saki hannun ta. Ganin haka yasa ta kama hannun sa. “Ana cewa turare shine signature din mutum. Turare yana da shiga rai, yana da wata lamba ta musamman shiyasa nace kai ne turare na.” Idan wani yaji abunda tace ba lallai ya dauke shi da wani muhimmanci ba shi kuwa ji yayi ko wata qofa ta jikinsa ta amsa abunda tace kuma ta sanya mishi wani irin farin ciki da bashi da kalmar misalta shi.2 Dakewa yayi ya bata rai. “Ke wato ba zaki bada haquri ba koh? Sai wayon tsiya.” Ya lakace mata hanci irin wanda ake wa yara. Bata ce komai ba, bai ankara ba ta rungume shi tana saka shi mantawa da cewar fushi yake da ita. Murmushi ta yi jin yanda zuciyar sa take bugawa. Ko bai fada ba ta san ya haqura. Ya haqura ba tare da tayi amfani da kalmar yi haquri ba. Kalmar ce dama bata son fada. ***** A daren jiya ta gaya masa tana son zuwa gida saboda duk yan uwanta sun zo daga nan kuma tana son taje kasuwa tayi siyayya. Bata fiye tambayarsa kudi ba saboda yawancin abubuwan gidan ita take siya da kudin da babansu ya kan turawa kowa duk wata. A da, ya daina bata daga baya aka bashi haquri yake bata. In Sheikh ya bayar da kudin cefane, ta kanyi amfani dashi, in bai bayar ba kuma da kudin ta take amfani. Bata taba fadawa kowa hakan ba kuma ko kadan bai dame ta ba. Sheikh bai tsaya yaji ragowar inda tace zata je ba. Cewa yayi kawai duk inda zata je kar ta bari ya riga ta dawowa. Taji dadin haka, dama tace tana son zuwa gidansu Sheikh din. Ba zai yi mata wahalar zuwa ba tunda ba boyayyen gida bane a garin Katsina. Yanzun ta tashi da wuri ne tana soya plantain din da zaici kafin ya tafi aiki. Tana gama soyawa ta juye, ta daka dafaffen nama wanda yaji albasa, tafarnuwa da attaruhu. Tare da kwai ta soya naman sama sama. A kwano daya ta saka da plantain din. Bata san sunan hadin abincin ba. Ita dai kawai tana da dabara ta fannin sarrafa abinci. Abun korawa kuma Sheikh ya fi son abu mai zafi. Satin farkon da ta fara girki yace mata ya koshi da shan tea. Shiyasa jefi jefi take bashi shi. Shima abun da zatayi na korawar bata san sunan sa ba. Ya daiyi kama da kunu. Dabino, aya, gyada da kwakwa ta saka aka mata garinsu ta ajiye. Sai garin tsamiya da citta wanda shima tana yawan amfani dashi. Da garin kwalba hade da dorawa. Yar dariya tayi, ta san da Sheikh zaiji hade haden da take masa cewa zaiyi ba zai sake sha ba. Yau din na dabinon da sauransu zatayi, hakan yasa ta dora ruwa ya tafasa sannan ta fara zuba garin. Sai da yayi kauri sannan ta sauke ta juye a kofi. Ko ba’a fada ba ta sani cewa kunun nata yana da amfani kala kala tunda ya tara yayan itatuwa masu sinadarai kala kala. A dining ta same shi yana kokarin zama. Ajiyewa tayi sannan ta zuba masa siga da madara ta juya. Ta dandana sannan ta miqa masa. Kewayawa tayi ta zauna suka fara ci. Cinyewa yayi tas sannan ya miqe yana goge bakinsa da tissue da ke kan table din. “Sai na dawo.” Ya fada, yana saba jakar laptop dinsa. “A dawo lafiya. Allah yasa yau dalibai su gane karatun sosai.” Dariya yayi. “Ameen.” Da haka ta matsa tayi masa sumba a kumatu. Shima yi mata yayi kafin ya fita, ya shiga mota. Bude masa gate tayi ya fita. Har ta rufe bata matsa daga wajen ba. Har I zuwa yau bata daina mamakin sa ba. Watarana sai ta zata Romeo din Juliet ne ya dawo a jikin Sheikh. Wata rana kuwa a wata siffa daban yake. STORY CONTINUES BELOW If only she knows why! Tana son ta san dalili amma ba ta san ta inda zata fara ba. Amma dai zata tambaya in dai da ranta. Ko da kuwa bayan shekaru ne. Duk da haka ba zata fasa masa addua ba. Da sharar tsakar gida ta fara kafin ta shiga ciki tayi share share. Har zata yi girki kuma sai ta ga yayi wuri. A gida zata ci na rana, ta taho masa dashi. Da daddare faten dankali zasu ci da lemon kankana, shiyasa ta fere dankalin ta ajiye, ta markada kankanar ta saka a fridge. Wajen qarfe takwas da rabi har ta gama komai. Barci ta danyi zuwa karfe goma sannan ta fita. **** Bata sha wahalar samun abun hawa ba. Duk yan gidansu suna da motarsu. Babban yayansu ma yace zai bata daya a cikin tasa. Ta fadawa sheikh yace babu komai. Ranar da za’a karbo Sheikh yace ya fasa barin ta, ta karbi motar. Har babanta sai da ya saka baki amma yace shi sam matar sa ba zata hau motar ba. Idan yayi ra’ayi nan gaba zai siya mata. Ran Jamilah ya baci sosai lokacin. Dalili kuwa, ya saka mata rai. Ta so jin me yasa ya canja shawara amma yace mata babu komai. A haka maganar mota ta mutu. Minti goma kadai aka yi ta ganta a kofar gidansu. Wani irin farin ciki ne ya lullubeta. Da sauri mai gadi ya bude mata. Ta kofar kicin ta shiga gidan inda ta tarar da Mr’s Ruth tana girki. “Matar Sheikh o!” Sai ta rungume ta. Dariya Jamilah tayi. Tayi kewar gidan gaba dayansa da cin abincin Mrs Ruth. Bayan sun dan gaisa ne ta shiga kofar da zata sada ta da falon Ummahn ta. Sallama tayi ba’a ansa ba. “Hey someone, I am home.” Ta fada qarfi tana haurawa sama inda dakin Ilham yake. Tana hawa taga Ya Nasir yana shirin saukowa. “Matar Sheikh!” Shima ya fada da sigar tsokana. Ko da yake dama haka suke kiranta dukkansu bayan bikinta da aka sha fama kafin a yi.2 “Say it again bro! Ka fada ka sake saboda hakan take.” Naushinsa tayi duk da kuwa ya girmeta sosai sosai. Tare suka koma dakin da ya fito. Nan ta ga kowa yana dakin. Ta rasa wajen wa zata je a cikinsu ko jikin wa zata fada. Sallama ta sake yi duk ka suka amsa idanunsu a kanta. Kallon mamaki suke mata saboda wani annuri da fuskarta take dauke dashi. Babu rama ko alamar damuwa a tartare da ita. Ba qaramin mamaki sukayi ba saboda a zaton su bata jin dadin zama da sheikh duba da irin yanda suka fahimce shi. Amma akasin haka suke gani. Aka ce soyayya ruwan zuma. “Ummah, Abba, ina wuni.” Ta fada a nutse tana jin wani iri. A tare suka amsa suna jin sanyi a ransu. A haka dai suka dan gaisa sama sama saboda alaqarsu da ta samu matsala tun lokacin aurenta. Da suka gama, tare suka fice. Ta sani cewa Ummah da Abba maganarta zasuyi yayinda suka kebe. Kawar da wannan tunanin tayi ta cire hijabinta ta watsar a gadon Ilham. “Ya Fiddy ina wuni. Ya naki gidan?” Ta fada tana kwanciya. “Lafiya qalau cray cray…” Jamilah ce ta bata rai. “Wai har yau ba zaki dena kirana cray cray ba? Ni gara ma kice min crazy din nasan kin fada. Kamar fa kice min mahau mahau ne fah. Me kenan? In zakice mahaukaciya gaba daya ki fada.” Ilham ce ta bushe da dariya. “Au kin yarda ace miki mahaukaciya?” Ta tambaya. “Ya zanyi toh?” Ana cikin haka, babyn yayar tasu Fiddausi, ta shigo. Tana ganin Jamilah ta taho da sauri har tana faduwa saboda bata gama iya tafiya ba. “Anty kiye kiye…” Ta fada. Jamilah ce ta kalli Fiddy da Ilham alamar kun gani ko. Alawa ta ciro a jakarta ta bawa babyn. Tana fita suka kwashe da dariya. “Kinga kin saka yar ki ta zata suna na kenan.” Ta bata rai. Da haka dai sukayi ta yar tsokana rana ta qarasa yi sannan suka ci abinci. Duk inda babyn tayi sai Jamilah ta dauka. Tana ta sha’awar ta. “Ke ma dai zaki iya haifowa.” Inji Fiddy. Dariya Jamilah tayi tana gyada kai ba tare da ta tanka ba. Amma dai ta saka a ranta ita ma ya kamata ace ta kusa haifar tata. Wajen qarfe biyu suna zaune Ya Nasir yayi magana. “Dama abunda yasa nace mu hadu shine saboda ina so mu bude sabon business. To expand the horizon and you know? Ya kamata ace mu ma mun tsaya da qafar mu.” Duk kan su sukayi na’am. Har Ilham da yake dama tana yar sana’ar abinci wanda Mrs Ruth ce mai girka mata. Ga kuma kudin da ake tura musu. “Yanzu dai kowa zai kawo dubu biyar kawai. Jiya jiya dai Abba ya turo kudi balle mutum yace ya cinye. Besides you all have your savings. Right?” Nan Jamilah ta hadiyi yawu. Ita babu wani kudi da take tarawa. A hidimar cikin gidanta take cinyesu. Da sallah ma har dinki tayi wa Sheikh a cikin su. Kuma ta kan bayar da sadaka. “Ni bana ajiyewa. I give alms and so on.” Tayi saurin fada. Kallonta sukayi. Sadda kanta kasa tayi kar a ga rashin gaskiya a fuskarta. “Toh tunda kince haka, wata na gaba sai ki bayar da duk biyun.” Toh kawai tace. Bayan mintuna kadan ta musu sallama. Direban gidan ta bawa yayi mata siyayyar kafin su gama hirar. Da zata tafi yace ai Abba yace ya kai ta gida. Har komawa ciki tayi, tayi godiya. Zuwa gida ranar ya mata dadi don har wayar hannun Ya Nasir ta karbe da wasu abubuwan da ga wajen Ilham. Ummah ma ta bata turarurruka da abubuwa. Taji wani irin dadin da ta dade bata ji ba. Da suka fita, kamar yanda tayi niyya gidansu Sheikh ya fara kaita. Bata wani jima ba ta fito. Ko direban sai da ya lura da yanayinta ya canja. Gaba daya farin cikin nan ya musanya da wani irin yanayi. A sanyaye ta shiga gida tana jin wani ciwon kai yana zuwar mata. A haka ta sarrafa abubuwan da ta siyo din tayi girkin dare. Har ta gama bata dena jin wani abu yana danne mata zuciya ba. Da ta sani bata je ba. Da ma tayi zamanta… Gashi yanzu ta jiyo wani abu da ya bata mata rai matuqa. Ta tsani wulakanci, ta tsani karya. Amma Sheikh ya hada duk biyun ya dama ya ajiye. Sai yau abun ya zube a fuskarta. Ji takeyi kamar yana shigowa ta mare shi. Abu daya ne ya daidaita mata nutsuwarta. Bata aiki da abunda wani ya fada mata. Sai ta binciko gaskiya…! ***** Da yawa daga yan level dinsu Salmah sun gane ta da rashin zuwa makaranta wasu lokutan duk sanda suka bincika sai a gaya musu ai rashin lafiya tayi. Hakan yasa suke kiranta da raguwa wasu kuma su ce mata langeru, watarana ta kanyi dariya wataran kuma sai dai ta kawar da kanta tana cewa a ranta ba zasu gane bane. Wannan karan wayarta a kashe take na tsawon kwanaki babu wanda ya same ta a waya, sannan basu yi tunanin zuwa gidansu ba sai bayan kwana uku suka yanke shawara zasu je daga makaranta. A na wayar gari kuma sai ga Salmah ta zo makaranta. “Muna ta tunaninki fa. Me ya same ki?” Sa’adah ta tambaye ta tana Jan kumatun ta. “Ouch,” Salmah tace sannan ta kai mata duka. “Zazzabin maleriya dai da ba’a rasawa kuma kinga dan jikin nawa, nan da nan yake kwantar dani.” Ta amsa yayinda maman Ameerah kawai take kallonta. Ita tasan ba haka bane ba, tana tare da Salmah ai lokacin da Sheikh yazo har Salmahn ta tafi tana kuka. Sai dai kawai ba zata tona mata asiri a cikin qawayen nasu ba wanda tasan dama ba da zuciya daya suke zaune ba.+ “In kin gama gaisawa da mutanen sai kizo mu tafi mu siyo abinci ai.” Maman Ameera ta fadi, ita Allah Allah take taga Salmah ta bar wajen su Sa’adah da Raudah. “Just a minute!” Ta fada sanda Raudah taja ta gefe. Idon maman Ameerah na kansu har suka gama maganarsu Salmah ta taho. “Sai kiyi min bayani ai.” “Maman Ameerah ki manta kawai. Amma dai muje zan baki wani labari,” gyada kai tayi suka qarasa Albarka restaurant suka siyo gurasa. A daya daga cikin sug chairs suka zauna daidai qasan wata bishiya. “Ina jinki…” “Labari na ne. Tunda muna da sauran lokaci kafin next lecture, shi zan yi ta baki har sai na gama.” “Toh gama cin abinci.” A tsanake suka cinye suka yi hamdala. Nan Salmah ta fara bata labarin ta. ***** PAST. Kwanaki suna wucewa kamar walqiya, shaquwa na qara shiga tsakanin Salmah da Abdulganiyu har ta kai ta kawo kowa na unguwar ya sani. Da yawa suna cewa so ne a tsakanin su amma su biyun suka ce su sam ba so bane ai yan uwantaka ce tsakanin su wadda suka gina tun shekarun baya. Kamar wasa dai suka cigaba da abokantaka. Ranar da Salmah suka gama makaranta, ranar Abdulganiyu yazo gidansu da daddare. Uwale na gyangyadi ta lallaba ta fita. Wani kati ya bata da abu a leda. Bata tsaya ganin menene a ciki ba ta shige gida. Da sanda ta shiga. Tana zuwa daki ta nemo yar qaramar fitilarta ta kunna. Kati ne babba da zanen zuciya a jiki. Wato heart. Haka kawai zuciyar ta ta fara bugu da sauri. Tana budewa ta ci karo da rubutunsa Wanda yayi da jan biro. Hannu tasa ta rufe rubutun yayinda ta rufe fuskarta fa dayan. Haka kawai takejin zuciyar ta bata shirya karban koma meye ba. Bata shirya karantawa ba. Rufewa tayi ta mayar ta ajiye. Ta bude ledar. Qaramar waya ta gani. Mamaki ya kamata, hade da wani tsoro da bata san dalilin zuwan sa ba. Sauri tayi ta mayar da wayar ta boye ta. Katin kuma ta saka shi a tsakanin kayanta sannan ta fito tsakar gidan, in da Uwale take zaune tana cin tuwo. “Kin san dai sa’o’inki sun fara aure ko?” Uwale ta gaya mata. Bata ce komai ba saboda ba ta san mai zata ce ba din. Ita ba wani saurayi take dashi ba, qarewarta ma bata jin ta san me ne so. Kuma ba zata iya shi ba. “Ki shirya zamu je Kano gobe.” Tunda take bata taba zuwa wani garin da Uwale ba. Yawanci idan Uwale zata yi tafiya, ita kadai take zuwa ta dawo. Sai Salmah ta kwana a gidan Iya Abdulganiyu. STORY CONTINUES BELOW “Uwale Kano? Wayyo Allah. Wajen wa zamu je a Kano?” Uwala ba ta bata amsa ba. Haka washe gari sukaje wani gida a Kano wanda daga baya ta fahimci cewa gidan kanin babanta ne wato Abba.h Tayi tayi a fada mata wani abu game da baban amma duk sukayi mata shiru. Haka ta haqura. Kwana daya sukayi a gidan suka dawo. Sanda suka dawo ne ta tuna da katin da takardar Abdul ya bata. Bata tsaya komai ba ta dauka ta shige bayan gida dasu. Bude takardar ta fara. Rubutun Abdul ne dara dara. ‘When I close my eyes I see you alone, Salmah mi.’ Tana karanta hakan sai itama ta rufe idonta. Hotonsa ne ya bayyana a ciki, fuskarsa dauke da annuri da murmushin da yake kwantar mata da hankali a ko da yaushe. ‘Nima in na rufe idona kai nake gani Yaya’ ta fada a hankali sannan ta kalli layin gaba. ‘Zuciya ta, ta kan kara sauri wajen bugun da takeyi yayinda nayi tunanin ki. Salmah mi, you’re special.’ Hannun ta ta sanya a saitin zuciyar ta, taji tana dokawa da kyau, da sauri. Mamaki ya kamata. Ya akayi duk abunda ya rubuta ita ma haka take ji? ‘Nima tawa zuciyar tana dokawa, kai din daban ni Yayana.’ Ta sake fada. Salmah ban san sunan yanayin nan ba. Amma ana cewa shine alamun so. In dai hakan ne, ina matuqar sonki Salmah. Kar kar, jikinta ya fara rawa. So kuma? Ashe da gaske yan ajinsu suke da suka ce mata Abdul son ta yake? To me yasa da ta tambaye shi ko hakane dariya kawai yayi. Tabe baki tayi. Sannan tace: ‘Toh kenan nima son ka nakeyi?’ Muryar Uwale da ta jiyo ya saka ta boye takardun a hijabinta ta bar wajen da tunani barkatai a kanta kamar suyi tsalle su fito waje. Zata rantse bata taba jin yanayi irin wannan ba. Duk sai ta ke ji kamar ba ita din ba ce. **** Tunda suka gama makaranta, tana yin kwana da kwanaki bata fita ba. Gashi kuma Uwale dama ta hana Abdul shigo mata gida. Abun duniya ya dami Salmah. Gaba daya ta manta ashe ya bata waya. Tana zaune tana tunani abun ya fado mata. Nan da nan ta tashi ta dauko wayar, ta kunna ta. Da sim kuwa a ciki kuma da kudi a cikin sa. Dama ta iya dubawa kuma a wayar Abdul din ta koya. Text ta rubuta masa na sallama. Ba a jima ba ya bata amsa. Kamar ta tashi sama dan murna. ‘Baki karanta abun da na rubuto miki ba?’ ‘Na karanta.’ ‘Baki ce komai ba.’ ‘Zan fito anjima. Mu hadu a qasan bishiyar bayan gidanmu.’ Ta rubuta masa saboda taji motsi a bakin kofarta. Wayar ta kashe ta mayar da ita cikin kaya ta kulle. “Uwale dan Allah zanje gidan su Hafsatu.” Ta roqa. Da taga babu alamar barinta a fuskar Uwale, sai tayi dabara. “Toh in bana fita taya zan yi auren?” Uwale ce ta kalle ta sannan tayi dariya. “Yauwa er gari ai na dauka ke kike korar samarin. Maza jeki ciki ki shafa jan baki na, ki saka mayafi na wannan koren yanda zaki haske. Kullum kina lullubi kamar wata gawa.” Bata ji ragowar ba ta shige ciki. Ko hoda bata shafa ba, kwalli ta saka wanda ya qara fito da manyan idanuwanta. Jan bakin kuma ya qara mata wani haske sosai. Shima koren mayafin ya karbeta. “Allah ya bada sa’a. In an baki kudi, ki karbo fa.” “Toh.” Sai ta fice. Bata kama hanyar ko ina ba sai ta wajen bishiyar bayan gidansu. Can ta hange shi a cikin kananan kaya tsaye jingine da bishiyar. Hannun sa harde yake akan kirjinsa yana ta kalle kalle. STORY CONTINUES BELOW Murmushi tayi tana rage saurin tafiyarta saboda ta qare masa kallo kafin ta qarasa. Kamar ance ya kalle inda take, ya juya suka hada ido. Ba shiri ta sauke kallonta zuwa qasa tana jin zuciyar ta na wani irin tsalle. Shima tahowa ya fara yi yazo har inda take yana sauke idonsa a kanta. Tayi mishi wani irin kyau da bai taba ganinta da shi ba. Ya sani tana da kyau amma yau din sai yaga ta chanza. Hasken fatarta har wani yellow yaga yana masa. Ga green din hijabinta da yasa kalar tata ta daidaita da hasken da idon sa zai iya dauka. Jin shiru yasa ta kalle shi wanda ya saka shi saurin dauke idonsa a kanta. Tare suka qarasa wajen bishiyar. A tare suka sauke numfashi kamar sun yi wani aiki mai wahala. Zagayawa Salmah tayi ta dayan gefen bishiyar in da bata iya ganin sa. Shima ya tsaya ta dayan gefen. “Arakunrin… Ka a ale…” Yana ta gefen idonsa ya zaro. Yaushe har Salmah ta iya yarabanci har hakan. Har ma ta iya gaisuwa doguwa… “Iya mi, wa ya koya miki yarabanci har haka?” Leqowa tayi ta gefen bishiyar tana murmushi. “Taya kuwa ba zan iya ba? Ba yaren mu bane ni da kai?” “Kina da gaskiya.” Bayan haka ba wanda ya sake magana. Tun jiya yake ta maimaita abunda zaice mata amma yanzun sai yaji ya kasa ce mata komai. “Kinga saqo na?” Ya fadi. “Na gani.” Ta bayar da amsa kai tsaye tunda ba ganinta yake ba. “I mean every letter of it.” Ya fada yana jin gudun zuciyar sa a qoqonta yana qaruwa. “I…” Sai kuma ta rasa mai zata ce. “You can’t love me. Me yasa zaka so ni? I mean you know everything about me.” Ta tambaya saboda a subutar baki rannan Uwale tace ba wanda zai so Salmah in dai ya san labarinta saboda haka kar ta sake ta bawa kowa labari. Abun ya mata zafi sai dai ita a lokacin ta riga ta saka a ranta duk abunda Uwale zata ce ba zai bata mata rai ba. Amma dai ta sani a qasan ranta ita din is a mess of bola. Bata da wani abun taqama da shi. “Gaskiya ina alfahari dake. Wannan turanci haka? Har kina so ki fini iyawa?” Yar dariya tayi ta na rufe fuskarta. “Kin san kuwa mene so?” Leqowa tayi ta kafe shi da ido ta na jiran jin duk abunda zai ce. “Nima ban san shi ba. Amma kuma na fada miki, duk sanda na rufe ido ke nake gani, na fada miki ina jin a jikina duk abunda kika buqata zan miki, ina ji in dai ke kike son abu toh kin riga kin samu, idan kika ce kai Abdulganiyu daga yau sunan ka Binta, to zan amsa…” Bai qarasa ba Salmah ta fashe da dariya. “Toh Binta..” Ta fada a sigar tsokana. “Na’am.” Ya ansa yana murmushi. “Toh duk wannan ai yan uwantaka tana kawo su.” Ta fada. “Naji… Amma abunda nake ji din ya wuce hakan.” “Kenan da gaske kai saurayina ne kamar yanda ake fada?” Wannan karan shi yayi dariya. Gaskiya wani halin mutum din baya chanzawa. Wata rana sai yaga kamar ta girma idan ta yi wani abun kuma sai ta dinga tuno masa da sanda ta na qarama. So free spirited. Ya karanta a waje da dama cewa wanda suka zama victim of rape su kan zama depressed for so long. Wasu har qoqarin kashe Kansu suke yi. Shiyasa yayi duk iya qoqarin sa na ganin ya zame mata majingina a rayuwarta ta yanda zai rage mata radadin abun. Zai iya cewa yayi nasara domin kuwa Salmah is still jovial and free. Ranaku kadan ne zaka ganta tana shiru shiru alamun ranta babu dadi. Ko babu komai bata taba yinkurin kashe kanta ba. He tried his best to make sure she feels worthy. “Eh mana ni mijinki ne ba saurayi ba.” Zagoyowa tayi tana kallonsa. Sai da yaji gabansa ya fadi da irin kallan da ta masa. “Miji?” “Ba zaki aure ni ba?” Ya tambaya. “Aure?” “Eh.” Sai kawai ta fara hawaye tana komawa inda ta jingina. Hawayen qaruwa sukayi tana jin wani irin nauyi da kanta yayi. A hakan zai aure ta? Ita bata hango auren sa. Eh, ta amince tana son shi amma kam tana ganin kamar idan igiyar aure ta hau kansu komai zai chanja. Daga hannun sa yayi saitin fuskarta kamar zai goge mata hawaye sai ya fasa. Ba zai taba ta ba saboda ba matarsa bace. “Kiyi haquri ki dena kuka. Ni babu ruwana da duk wani abu da ya faru. Babu ruwana Salmah. I just want you and no matter how you’re I will accept you that way. A hakan…” Bata bashi amsa ba har ya gama fadan abunda zai ce. A hankali ta fara takawa zata bar wajen. “Kar ki tafi baki bani amsa ba, Salmah.” Ai kuwa dai tafiyar tayi bata ce komai ba. Lokacin take jin kamar kawai ta zama babu. Idonta na kan wata bishiya da take kadawa sai kawai taji dama itace bishiyar. Abdulganiyu ya dade a tsaye yana jin wani iri. Bai san da wace kalma zai kwatanta yanayin ba, bai kuma san taya zai fara ba. Tunani ne bila adad a kansa amma idan an qure shi ya fadi daya, ba zai iya cewa gashi ba ko da kuwa mai za’a masa. Haka dai ya bar wajen bishiyar jikinsa babu qwari. Gidansu ya nufa domin yana jin kamar zazzabi zai kama shi musamman idan ya hasaso cewa Salmah zata iya rejecting love dinsa. Shi ba zai iya dauka ba. Bai zai iya ba, gara ma ta sani. In dai ba zata ce eh ba, toh kar tace a’a.+ Yana zuwa ya tarar da babansa a tsakar gidan zaune akan kujerar guragu wadda Abdul din ya siya masa sati guda da ya wuce bayan ya karbi albashinsa na farko. Yana da burrirka da yawa wanda yake son cimma wa yayinda kudi suka zauna masa. Yanzun kullum cikin godewa Allah yake da ya samu aiki da dan wuri akan sauran mutanen da suke harka tare. Ga aiki ga kuma dan kasuwancin sa da yake gudanarwa a Legas. Babu abunda zai yi sai hamdala. Kanshi yana sarawa ya karasa inda baban nasa yake zaune fuskar sa a daure. Jijjiga kansa Abdul yayi saboda yanayin baban nasa yana bashi tausayi. Baban sa ya kasance mai kazar kazar ne shi lokaci daya kuma qaddara ta hau shi aka yanke masa qafa shikenan ya zama wani iri. Kullum cikin fada yake da bacin rai kamar wanda bai yarda da qaddara ba. “Sannu da hutawa Baba.” Ya fada cikin yarabanci. Kai baban ya girgiza alamun amsawa sannan ya kalli Abdul din. “Akwai maganar da zamuyi da kai. Amma in ka shiga ciki mamanka zata maka bayani.” Toh yace masa. Sannan ya tambaya idan baban yana da buqatar wani abu. Jin babu komai ya saka shi ya miqe ya tafi dakin maman. So yake ko ma meye sai bayan sallar isha sa yi maganar. **** Sanda Salmah ta shiga gida idanunta sunyi ja sosai. Taga Uwale zaune tana qirken kudin adashi bata ce komai ba ta shige daki duk da kuwa tana jin idanun Uwale a kanta. Bata jima da shiga ba taji a turo kofar yayinda Uwale ta shigo. “Me kuma aka yi?” Ta tambaya. Salmah ce ta kalle ta wannan ne karo na farko da ta taba ganin damuwa a fuskarta. Sai da ta danyi Jim kafin ta bayar da amsa tana tunawa cewa Uwale ta hana ta harka da Abdul tun da dadewa. “Babu.” Kukan ne ya sake kwace mata saboda har cikin jikinta take jin ba zata iya rabuwa dashi ba. Shiyasa ta fiso su zauna a mazauninsu na yaya da qanwa. In har suka ce zasui soyayya toh mutane da dama zasu shiga tsakanin su. A ganinta kuma har Iya Abdulganiyu tunda tafi kowa sanin kalar tarbiyyarta. Wannan dalilin ya saka ta kuka, tana buqatar jin dadin rayuwa, tana buqatar hutu amma bata jin zata same su. “Kiyi shiru ki min magana.” Bata yi shirun ba kuwa amma dai ta kalli Uwale tana mamaki. “Ki cigaba ko bakomai zaki dandani abunda naji. Irin wannan kukan nayi ranar haihuwar ki…” Sai kawai Uwalen ta tashi ta fice. Abunda ta fada kuwa tamkar ana rura garwashi a zuciyar Salmah. Ji takeyi zuciyar ta tana tafarfasa. Gaba daya wani yanayi yabi ya addabe ta. Wayarta ta ciro ta kunna ta kira shi. Dole yaji kukan da take. Dole ya san tana kunci. Dole yasan bata da gata kuma shi kadai ne gatan ta. Tana so ya fahimci cewa ita din tana son shi amma bata da wani buri akan sa. So take kawai su zauna a matsayin da suke. Saboda tana da yaqinin cewa in har suka bari duniya ta san suna qaunar juna to hankula zasu tashi. Tabbas ta saba da tashin hankali amma bata so na Abdul ya tashi. Bugu na uku, wayar ta shiga. **** Yana kwance kiran Salmah ya shigo. Da sauri ya dauka yana murmushi. A tunanin sa ta kira ta bashi amsar sa ne. Jin sautin kukan ta ba qaramin tayar masa da hankali yayi ba. A hankali yake jin tsikar jikinsa yana tashi. “Salmah mi, me ya faru? Nazo?” Bata daina kukan ba. “Dan Allah kiyi haquri kiyi min magana.” Ya sake fadi. “Laifin me nayi? Me yasa ake hukunta ni da laifin da ban da masaniya akan sa? Me yasa??? Why me?” Sai ta sake fashewa da wani kukan mai tsuma zuciyar mai sauraro. Ta rasa dalilin da yasa abubuwa da yawa suke faruwa da ita. Ita ba fitinanniya ba balle tace hukuncin fitinarta ce. Sai da Abdul ya ja numfashi mai tsawo sannan ya fara magana. “Calm down okay? Ki kwantar da hankalin ki, kinji? Yi shiru ki saurare ni.” “Babu abunda zan saurara ni. Kullum baka da magana sai dai kace nayi haquri. Kullum sai ka ce duk kan tsanani yana tare da sauki. For all this years a ina sauqin ya maqale? Nikam na gaza…” “Shut up! Salmah kiyi min shiru kiji mana. Ya kike nema kiyi sabo ne?” Ya fada cikin zafin zuciya shima. “Ba zan daina fada miki ba… Mai haquri shi ke da riba. Ba zan fasa fada miki ba… Duk kan tsanani yana tare da sauqi saboda Allah da kan shi ya fadi hakan. Zan cigaba da tunatar da ke cewa duk wanda ya dogara da Allah, Allah zai kawo masa sauqi ta hanyar da baya zato, ita ma ayah ce. Ki tuna labarin da na baki. Labarin annabi Nuhu. Ko kin manta?” Shirun da tayi ne ya saka ya ciro wayar ya kalla, gani yayi kiran yana yi. “Kin manta? Shekarar dari tara da hamsin yayi yana kiran mutane zuwa ga Allah. Sun jefe shi, sun kira shi mahaukaci, in suka hango shi ma guduwa suke. Duk shekarun nan, qalilan din su ne sukayi imani da shi. Matar sa tana cikin kafirai, dan sa ma haka. Amma mai? Lokaci daya Allah ya kawo masa dauki kuma a hakan yayi tawakkali. Yes, nasan ke ba annabi bace. Imanin ku ba iri daya bane amma in kika duba ana bamu labarin su ne saboda mu kwatanta yin koyi dasu. Kin gane?” Ya tambaya. “Umm.” “Yauwa Salmah na. Kiyi haquri kin ji? Ko me ya faru ki dan qara haquri nan da dan lokaci kadan zan zo na dauke ki na kai ki dream land. In da ba zaki ji wani bakin ciki ba.” “Dream land?” Ta tambaya. “Duk abubuwan da nace abunda kunnen ki yaji kenan ko?” Dariya ya danyi. “Toh shine abunda ban saba ji ba ai.” “Toh ba sai ki jira ba. Toh ai zanyi miki bayani…” Ya kwaikwayi muryarta da salon maganarta. Dariyarta ce ta cika masa kunne yana jin wani kwanciyar hankali na ziyartarsa. Dadinsa da ita saurin mantuwa. He can’t believe wai har ya saka ta dariya a lokaci kadan kamar ba ita ce mai kuka ba mintuna kadan da suka wuce. “Zan zo na dauke ki mu gina sabuwar rayuwa wadda na kira da dreamland. Kar ki ce min a’a domin mace ce foundation din, kece ginkishin ginin.” Ya katse mata dariyar. Tsit tayi tana jin wani sabon yanayi yana maimaye zuciyar ta. Tabe baki tayi. “Wai gini… Zaka iya ginawa da wata ai.” Shagwabe fuska da murya yayi. “Ni da Salmah zanyi.” Murmushi tayi sannan ta dage girar. “Me yasa?” Ta tambaya cikin zumudi. Gyara kwanciyarsa yayi yana neman amsar da zai bata. “Saboda a karo na farko in the love world, Salmah na sani, da ita na fara soyayya. Kuma itace nake son ta saboda Allah. Akwai mata da yawa amma cikin su babu kamar Salmahna saboda Salmah na kamar yanda sunanta yake, haka ganinta yake saka min nutsuwa da farin ciki. Maganarta dabance, salonta daban ne a cikin mata, her heart and soul is different and created for me. Komai nata daban ne and specially for Abdul. Fatana tace dani tana so na…” Sai ya tsaya. “Ah…uhmmm…” Ta kasa cewa komai. “In kika ce a’a zanyi kuka…” “Kuka?” Dariya ta sakeyi. Shi kuwa sai ya bata fuska. “Da gaske nake. Zan saka kuka wallahi saboda shaquwar da mukayi ba zata tafi haka nan ba. I fit sacrifice my life for you Salmah na. I love you so much Salmah. Ina qaunarki, kinji ko?” Qit, yaji ta kashe masa waya. Ba jimawa yaji wayar tayi qara almaun text ya shigo. ‘Na kasa jurewa, wannan feeling din da yake zuciyata na rasa yanda zanyi dashi. Yana hana ni barci in na kwanta, yana hana ni nutsuwa idan idona biyu. Na bawa zuciyata haquri taqi ji saboda haka zan fada kowa ya huta. I love you so much too! Ina son ka sosai!’ Bai ankara ba, yana ta maimaita karanta text din har aka kira sallah sannan ya miqe ya tafi yana jin sa kamar a dream land din. Salmah ce tayi shiru hawaye yana zuba a idonta. Ta kalli maman Ameera amma sai ta kasa cigaba da labarin. Zuciyar ta ce tayi wani irin bugu da yasa ta dafe wajen. “Lafiya?” Maman Amirah ta tambaya. Girgiza kanta tayi ta goge hawayen fa ya sake zubowa. “Daga ranar ba sai na tsaya gaya miki irin soyayyar da muke yi ba saboda zai daukar mana lokaci.” Hawayen ta sake gogewa. “Abdul dina,” kasa cigaba tayi again tana goge fuskarta. “In ba zaki iya ba ki bar shi some other time kya gaya min.” Maman Ameera ta gaya ma Salmah hade da gogewa Salmahn hawaye. “A sannan ne Uwale ta gane, iya Abdul ta gane. Amma kin san me? Bata hana mu ba. Tayi farin ciki…” “Tayi farin cikin jin cewa ina tare da Abdul. Ban san wani irin so matar nan take min ba sai ma nace ta fi Uwale da ta haife ni. Saboda duk wani abu da zai saka ni farin ciki, Iya tana son shi. Lokaci zuwa lokaci tana aiko min da abubuwa. Uwale kam qi tayi sam tace ba zan auri bayerabe mara kudi ba. Zuciyata tayi min ciwo, na shiga wani irin yanayi saboda na kai matakin da ba zan iya rabuwa da shi ba. Ina ganin ko waye yace ba zan auri Abdul ba sai dai yayi ya gama domin kuwa sai na aure shi din. Ranar na shirya naje gidan qawata muka yi hira sai nace bari na biya ta gidansu Abdul na gaishe da Iya. Da sallama ta na shiga gidan tunda dama ba baqon wajena bane. Ina zuwa na tarar da baban Abdul din a tsakar gida. Na gaishe shi bai ce min komai ba illa gyada kai da yayi. Ban wani damu ba saboda nasan wataran suma yan gidan baya iya amsa musu. Munyi hira sosai da Iya Abdulganiyu kamar ba wanda zasu zama surukai ba kafin na tashi na tafi. Ranar ne karo na farko da raina ya baci. Saboda na hango Abdul da wata bayerabiya wato Favour. Gidansu gangare yake. Abun haushi abun takaici har dariya na gan shi yana yi. Kishi ya taso ya tsaya min a rai. A haka na lallaba na wuce bai gan ni ba. Da daddare ya kira ni ban dauka ba. Washe gari ma haka har dai rannan bayan kwana hudu ya haqura yazo gidanmu. Uwale tana ta masa fada amma yaqi ji a hakan ya shigo har cikin tsakar gidanmu. Lokacin ina shara. A gabana ya durqusa. “Salmah mi, ki mare ni ki huce haushi na da kike ji amma wani shirun ba zan iya dauka ba.” Ya fada. Ban kalle shi ba na cigaba da sharata kamar babu mutum a wajen. Ina kallo Uwale tayi murmushin jindadi. Ya dade yana magana ban ce masa komai ba. Sai naji kamar na bashi amsa sai kuma na tuno, kishi ya lullube ni. “Ka fice mana daga gida. Bana so na sake ganinka Abdul.” Na gaya masa cikin tsawa wanda na tabbatar ta ruguza masa lissafi. Da sanyin gwiwa ya fice ni kuma ina jin wani iri. Bana jin dadin shirun dake tsakanin mu. Haka na qarasa sharar sannan Uwale ta kira ni. “Naji dadin abunda kika yi Salmah. Me zakiyi da bayerabe?” A sannan ne na shiga tunani. Shi bayeraben ba mutum bane? Ko ba musulmi bane? Mai yasa ake wannan qabilancin? Abdul mutumin kirki ne, iyayen sa ma haka. Toh meye matsalar? Yaushe za’a daina nuna bambanci. Mutane ai al’umma daya ce, tushe daya ne. Babu wani bambanci a wajen Allah. A haka dai na danyi murmushi kadan sannan na tashi na watsa ruwa nace mata zanje makwobta. Bata hana ni ba saboda yanzu hankalin ta a kwance yake tasan ba zan hadu da Abdul ba. Ina fita naji an fisgo ni zuwa baya. Toshe min baki yayi ya jawo ni har zuwa bishiyar bayan gidan mu. Abdul ne. Kneel down yayi. “Ki min duk abunda kike so, amma bana son share ni da kike yi Salmahna.” “Hmm,” kawai nace. “Dan Allah kiyi haquri.” STORY CONTINUES BELOW “Ina Favour?” Na tambaye shi. “Favour?” Ya maimaita. Ban bashi amsa ba. Kallonsa kawai nayi ina isar masa da saqon da yake nuni da cewa kar ya min qarya. “Wallahi baba ne yace naje wajenta. Ina tsoran babana.” “Toh mu haqura mana? Dole ne?” Na fada cikin bacin rai. Da bacin ran shima ya kalle ni yana miqewa. “Kin san me kike cewa?” Gyada kai nayi. “Nasan me nake cewa. Da iyaye na, da naka basu bamu albarkar su ba. Mai yasa zamu cigaba?” “Saboda muna son junan mu. Kuma babu abunda zai raba mu. Zanje Lagos gobe idan na dawo komai zai daidaita.” Ya sanar dani. Har cikin Zuciyata nake fatan daidaitar abubuwan. Wani murmushi ya min wanda ya qara masa kyau. Nima murmushin nayi. “Akanka ne kawai zan zartar da sharadi, kar wadda ta kusanci inda kake. Kar wanda ya takura maka, har ya sa ka ja birki, saboda duk wanda yayi yunkunrin raba ni da kai zan dauki mataki mai tsauri.” Na fada mishi ba tare da wata damuwa ba. Da naje gidan qawata tace min wai ba’a nunawa namji so da yawa in ba haka ba zai raina ni. Ta dayan kunne na zancen ta ya wuce. Russunawa yayi sannan ya miqo. “An gama sarauniya.” Dariya nayi, na rufe fuskata da hannaye na. Shirun da yayi ne ya saka na bude na kalle shi. Hannuna yake kallo. “Baqin lallen nan yayi kyau, kamar na sace hannun.” Mayar da hannun nayi sannan na matsa daya bangaren bishiyar wanda nake ji kamar domin mu aka shuka ta. “Nayi kewarki a iya kwanakin nan. Kin wahalar dani.” Ban bashi amsa ba. “Amma saura kiris ai. Ina dawowa zan je wajen uncle dinki na Kano a fara magana.” “Kwana nawa zakayi?” Na tambaya ina qoqarin dodging wancen topic din. “Kwana biyar kawai.” Tura baki nayi na lanqwasar da kai “Bana so ka tafi.” “Ba zan dade ba. Wani abu ne ya taso dole naje kar a samu matsala. Kin san harkar kudi.” “Allah ya taimaka ya qara budi.” Na mishi addua duk da ban san ko tayi ba ko bata yi ba. “Ameen, Allah ya miki albarka Salmah na.” Kai na a qasa nace ameen. Ina kallo ya ciro biro a aljihunsa sannan ya tako inda nake tsaye. “Bani hannunki,” ba musu na ware tafin hannu na na dora bayan a jikin bishiyar. Da rubutun sa mai kyau ya zana min heart sannan ya rubuta ‘Abdul loves you so much, Abdul’s wife.’ Kallo na yai ni kuma na sauke kaina kasa. “Matar Abdulganiyu!” Ya fada wanda yasa dole na kalle shi. “Ki kula min da kanki kafin na dawo.” Ya fadi, yau gaba daya idonsa yana kaina. “Ina son ki…” Da wannan ya juya ya tafi. Nima na juya. Sai muka sake juyowa a tare. Wani irin nauyi zuciyata tayi min. “Nima ina son ka.” Na furta mishi, ban sani ba ko yaji ko bai ji ba haka na koma gida ba tare da naje inda zanje ba. Da safe kafin ya wuce sai da ya kuma zuwa. Wayata ta lalace shiyasa bamuyi magana ba. Nima da Biro na na fito. Hannun sa nayi mishi alama da ya bude. Da kyar na rubuta masa rubutu gajere saboda biron yana tsayawa. ‘I can’t wait to be your Mrs. Yes, matar Abdulganiyu.’ Sannan na juya na yi mishi bye. Shima dago min hannu yayi sannan na shige gida. **** Bayan kwana biyu ina zaune da safe kwance a tsakar gida jikina duk babu dadi naji hayaniya da ihu na tashi daga waje. A guje na fita ina ganin taron jama’a a lungun gidansu Abdul. Ko takalmi ban saka ba na qarasa har cikin gidan. Idona kan Iya Abdulganiyu ya fada tana ta rusa ihu. Na dauka baban Abdul ne ya rasu sai kuma na hango shi shima yana kuka. Kamar wadda aka dasa haka na kasa motsi ko tambaya. Ina nan tsaye wata mota ta faka a qofar gidan. Nan da nan aka shigo da mutum. A nan ne na kusa zarewa. Abdul ne da harbin bindiga a goshinsa.” Salmah ce ta tsaya tana kuka sosai. Sannan ta kalli maman Ameera. “Bai ce mun zai mutu ya bar ni ba, Bai yi mun bankwana na har abada ba. Bankwanan kwana biyar mukayi. Ban shirya ba kawai ya tafi ya barni, Munyi shaquwar da bana hango mutuwarsa ko tawa. Mun kasance tamkar ba zamu rabu ba, da farko na zata ko mun rabu zamu dinga haduwa. Amma sai mutuwa tazo ta raba mu, irin rabuwar da ba zamu sake ganawa ba.” Maman Ameera ce ta shiga rarrashin Salmah. “Ashe yan fashi ne suka taresu a hanya. Bai fada min hanyar Lagos tana da hatsari ba. Maman Ameera bai gaya min ba…” “Bana cikin hayyacina aka fita dashi aka masa sallah aka kai shi makwancinsa na har abada. Nayi kukan, nayi zazzabin, nayi ramar kamar zan bi shi. A nan ne Iya ta sake daukar dawainiyar rarrashi na amma na kasa jurewa, idan na kwanta mafarkinsa nake a ido biyu tunanin sa nake. A hankali kamar zan zauce sai kuma nayi mafarkinsa yana bani haquri. Tun ranar na yi iya qoqarin da zanyi na daure. Abu daya na sani, mutuwarsa taji mun ciwo a zuciya. Ciwon har yau bai warke ba. In ya dauko hanyar warkewa sai a fame min shi. Uwale…” A nan ta sake fashewa da wani kukan. Gaba daya jikin maman Ameera yayi sanyi.+ “Kwatsam sai ga Mansur yaro dan gayu, dan gata… Shima haka ya shigo rayuwata bayan mutuwar Abdul da shekara biyu…” Wani daci Salmah ta hadiye Wannan update din na mekyau ne da duk wani mai son book dinnan. Nagode. Ya dade a kofar gidan mahaifiyarsa yana tunani kafin ya shiga. Ko da ya shiga yayi sallama sai yaji tana bandaki hakan yasa ya nemi wajen zama yana jiranta. Ta jima bata fito ba, shiyasa bai ankara ba ya fara tunanin wani lokaci. Irin wannan lokacin da ya faru a baya, lokacin da iyayen Jamilah suka nemi su ganshi kuma ya watsa musu qasa a ido. Wata iriyar kunya yaji ta lullube shi hade da dana sani marar misaltuwa. Baya son baya ta sake maimaita kanta a kan Salmah shiyasa ya taho ya fara magana da mahaifiyar sa yaji ra’ayinta. Yana so ya auri Salmah da izinin ta, yana so ta sanya mishi albarka ya samu kwanciyar hankali har zuwa qarshen rayuwarsa. Wancen lokacin kam… Abubuwan da suka faru suna da yawa. **** Salim’s past. Jamilah tayi jiran dawowarsa tamkar akan kaya take zaune saboda yanda ta matsu yazo ya mata bayani dalla dalla yanda zata fahimta. Tana zaune taji alamar shigowarsa bayan sallar magariba. Sannu da zuwa tayi masa hade da komawa ta zaune inda take. Kallonta yayi na dan sakanni ya fahimci ranta babu dadi. Bai ce komai ba ya shige daki yayi alwala ya tafi masallaci. Fitarsa ke da wuya ta tashi ta jera mishi abinci sannan itama ta tafi dakinta tayi sallar. Kamar yanda tayi tsammani sai bayan isha’i zai shigo, sai sannan din ya shigo amma tayi mamakin rashin ganinsa da abokansa wanda suka dauki gidanta kamar gidan cin abincin su. Wataqila bai jawo su ba saboda ya fuskanci halin da matarsa take ciki ko kuma wani dalilin daban. Bata damu ba, in ma sun shigo tana da yanda zatayi da su. Ita burinta yanzu shine yazo ya gaya mata abunda taji qarya ne ko zata samu sanyi a zuciyar ta. “Matar sheikh.” Kallonsa tayi tare da yin qaramin murmushi wanda bai kai zuci ba. A hankali ya tako wajen da take zaune. Zama yayi kusa da ita, bata ce masa komai ba sai kallon da ta cigaba da yi wanda gana daya ma hankalin ta ba a kai yake ba. “Me ya faru ne?” Ya tambaya da ya gaji da zama kuma yaga alama ba zata mishi wata magana ba. “Me kuwa ya faru?” Ta bashi amsa tana bude haqoranta. “Sai wani sim sim kike yi. Fatan kowa qalau a gidan?” “Lafiya lau.” Tace. “Toh me ya faru?” Numfashi ta sauke. “Naje gidanku na gaida su Mama.” A zabure ya tashi. “Me suka ce miki?” Kallonsa tayi sai taji wata dariyar takaici tazo mata musamman da taga yanda ya kadu lokaci daya. Ko dai tace masa babu komai ta cigaba da sanin a sannu a hankali? Ko da yake ta riga ta yi kuskuren gaya masa taje gidansu. “Me kuwa suka ce min?” Sai ta dage kafadarta irin nuna rashin damuwa ko kulawa sannan ta daga girarta daya sama. “Wataqila ni ba yar gidan Abba bace, wataqila gidan mu yana qauye, wataqila bana zuwa gaida mahaifiyata, wata qila ni yar karya ce. Wataqila…” “Enough Jamilah!” Ya daka mata tsawa. Dariya tayi. “Tsawar ta meye? Labarina nake baka fa? Haba sheikh dina ka zauna na qarasa baka labarin mana.” Wani tsaki ya buga yana neman ya fice. “Na rantse da Allah idan ka fita bamu qarasa maganar nan ba ba zaka sake ganina a gidanka ba. I really mean it, try it and see.” Jin haka yasa ya dawo ya zauna gumi yana zuba daga jikinsa, hannunsa ya dungule sannan ya ware yana shafa fuskarsa ko zaiji sanyi. Bai ji sanyin ba sai dai jin da yayi gaba daya duniyar ta hade masa waje daya. STORY CONTINUES BELOW “Jamilah…” Ya fada yana gyara zaman sa, a cikin zuciyar sa kuma yana tunanin abun da zai ce mata. Ita kuwa hankalinta yayi nisa, kwakwalwarta ta tafi yawo tana tuno mata da wasu abubuwa. “Ba binciken da zan qara yi tunda ta dage sai shi ai gashi nan sai ta aure shi.” Ta tuna sanda Abba ya fada ran shi a bace sosai. “Jamilah,” Sheikh ya sake maimaitawa. Kallon sa tayi tana jin wasu hawaye suna kokarin zubowa daga idonta. Daurewa tayi ta mayar da su saboda in dai suka zuba toh taji kunya saboda komai lefin ta ne. “Kiyi hakuri. Na miki karya…” Ya sake furtawa yana ganin indai yace ba zai gaya mata gaskiya ba toh bata lokaci zaiyi kuma babu amfanin hakan. Na biyu kuma in yayi qarya daya, sai ya sake yin wata qaryar domin ya gaskata dayar. Hakan yasa kawai ya zabi da ya gaya mata ko ma meye. “Gidan mu yana Dan ja a garin Katsina. Nan mahaifiyata take, babana ya rasu ina qarami. Gidan Alhaji AbdulHamid gidan wan babana ne…” Bata san bakinta a bude yake ba sai da ta ga ya kalle ta. Rufewa tayi tana mamakin yanda Sheikh din yake yi kamar shi din dan asalin gidan ne. Kallonta yayi, ya hadiye wani abu sannan ya cigaba da magana. “Ranar da kika ce ana nema na a gidanku, ranar mahaifiyata ta kira ni tana nema na, fada tayi min sosai saboda rabon da na kai mata ziyara nafi shekara biyu shiyasa rai na ya baci na kasa zuwa gidan ku. Banyi niyyar zuwa ba amma Abba Abdulhamid ya tilasta ni haka na shirya naje washegari saboda gudun kar ta min baki…” Sake dafe kan shi yayi kafin ya kalli Jamilah yana tunanin yanda zata dauki zancen nasa. “Da naje ta aika ni makwabta tace naje naga Binta mu sasanta. Ban je ba, nayi tahowata kawai. Jamilah kiyi haquri, amma Hajiyata bata sanya albarkarta a auren mu ba. Abba ne ya tsaya min a kai… Kum…” Da wani irin ihu ta katse shi tana jin zuciyarta tana tarwatsewa. Duk da kuwa itama ta sha wahala da iyayenta amma ko babu komai sun amince. Wani kallo ta bi shi dashi kafin ta miqe da kyar tana bar masa falon. Dakinta ta shiga ta rufo shi sannan ta nemi gefen gado ta zauna. Wani irin abu take ji saboda ita ta tsani a yi mata qarya. A hankali take tunowa, tabbas da ta nutsu a wancen lokacin da ta fahimci komai… Jamilah’s POV. RECAP (cigaba daga feji na sha daya).+ “Ka kyale ni. Just leave me alone Salim. Leave me alone!” Ina fadan haka, kuka ya kwace mun. Da gudu na bace masa da gani. Ban juyo ba har na isa get. Nan na samu waje na durqushe na fara hawaye. Wannan soyayya tana wahalar dani. Gaskiya ne; na haukace. Babu tantama; na sakarce. Babu shakka; na dolence kuma na kauyence duk a sunan soyayya. Ina durqushe na goge hawaye na ina tambayar kaina meye amfanin zubar da su din. In dai sheikh ne to daga yau in Allah ya yarda na daina tunaninsa. Ba zai yuiyu ace ina wahala ba a banza. Na gama wannan tunanin kenan naji takun mutum a kusa dani. Daga kai nayi na kalle shi, Sheikh ne. Kamar ko yaushe sai na saka a raina na haqura dashi sai out of nowhere na gan shi a kusa dani. Duk sanda nayi yunkurin nesanta dashi, shi kuma sai ya qara kusanto ni. Juya masa baya nayi, ina sakawa a raina wannan karan ba zan sassauta masa ba. “Jameelah I can explain. Wallahi umra nazo shine na biya mu gaisa da Nawfal. And nayi tafiya ne, abubuwa ne da yawa suka faru wanda suka fi qarfina. Kiyi haquri, kin sani cewa ke ce priority dina, komai nawa bayanki yake bi. In har wani abu a yanzu yaso ya raba ni da ke toh na dan lokaci ne. Ke kuma you’re mine forever and I am yours to keep for eternity. Kiyi haquri dan Allah ki bani dama ta qarshe. Sannan zan zo na bawa su Abba haquri akan abunda ya faru, kinji?” Naso a ce duk abunda ya fada, ya bi ta da yan kunne na ya fice amma sai duk kalaman sa suka samu waje na dindin suka yiwa kansu masauki a zuciyata. STORY CONTINUES BELOW Duk da haka ban bashi amsa ba. Har yanzu ban kalle shi ba kuma. In har ni na yafe masa, su Abba ba zasu haqura ba. Abba baya son raini ko kadan. “Kai da Abba…” Na fada a gajarce sannan na bar mishi wajen. Bai biyo ni ba. Cikin makarantar na koma inda naci karo da ya Fiddy. Kallo daya ta min bata ce komai ba taja hannu na mukayi ciki. Ban gwada yi mata magana ba nima. **** Bayan munyi umrah aka ce zamu Dubai kafin mu wuce Egypt. Munga abubuwa masu kyau sosai, munje malls kala kala na siya abaya iri iri a Daga nan muka je muka ga Burj Khalifah. Dubai was fun in short. Daga nan da muka je Egypt, mun je Naama Bay Sharm El sheikh, wajen ya hadu babu qarya, munje museum da wuraren tourism da yawa. Da aka gama yawace yawacen sai ya Fiddy tace zata koma Nigeria wajen mijinta wanda shi da wuri ya koma. Nima haka na lallaba na biyota. A gidan kakar mu na sauka ita kuma ta wuce gidanta. A kwana a tashi wata rana a kace ana sallama da ni. Sheikh ne da abokinsa. Haka suka zo suka gaida kakata cikin ladabi da biyyaya. A sannan dai ya fara zuwa a kai a kai. Tun bana sauraron sa har na fara kuma suka fara shiri da kakata. In short, da taimakonta, da saka bakinta aka daura mana aure amma duk da haka Abba sai da ya bani sharadai kala kala. Na farko, ko me sheikh ya min ba zan kawo qara ba. Na biyu, kar na zo masa da matsalar kudi. Kuma kudin da yake bayarwa duk wata ya zare ni daga ciki. Duk na amince sannan akayin bikin. Ina tunawa da na fadawa sheikh sharadodin bai ji dadi ba. Haka muka fara zaman tare duk da kuwa yana da halayen da bana so haka nake haquri dashi saboda ni na zabi zama dashi. ***** Tana cikin tunani taji bugu a kofar dakin. Tashi tayi ta bude masa saboda tana so ya amsa mata wasu tambayoyi. Sai da ya kalle ta sannan ya samu gefen gadonta ya zauna. “Ba haquri zaka ban ba. Dama sai an cuci mutum a dame shi da kalmar haquri.” “Shin kana so na kuwa? Gaskiya zaka fada min? Ko ni kadai nake ta hauka ta? Me yasa ka aure ni in har baka so na. Ba zan kira abubuwan da ka min da sunan so ba. Ba so bane duk, ba so bane na gaskiya. Sheikh Muhammad Salim ka bani amsar tambayoyi na…” Kallonta yayi. Abunda yake cikin idanuwanta yana masa da nuni cewa ba zata aminta da qarya ba. Sai da ya shafa fuskarsa ya juya gefe. “Da farko da wasa nake yi…” A wannan karan taji zuciyar ta tayi wani irin bugu. Wasa fa yace? Ba kalle ta ba har yanzu. “Sai kuma abokai na suka nuna min cewa idan na aureki zan amfana saboda kina so na sosai kuma ba zaki wahalar juyawa ba.” Runtse idonta tayi. “Sai kuma na aure ki saboda kar na auri Binta. In gani na babu mata shi ne baya yiwa mahaifiyata dadi, to ga ki nan na aure ki. Sannan ko a cikin abokai, zasu dinga gani na da daraja tunda nayi aure…” “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.” Ta furta… “Amma wallahi yanzu ina…” “Kar ka kuskura…” Ta dakatar dashi hade da miqewa ta fara Jan shi har wajen dakinta sannan ta rufo dakin. Bata taba shan mamaki ba irin na yau… Ashe abun wasa ya dauke ta. Ashe da gaske ta haukace… Ashe sheikh bai dauke ta a matsayin mata ba. Sai dai ita din ba komai bace illa toy or an object. Ya Allah. Nan da nan taji zazzabi yana rufeta. Abu daya ne bata sani ba, a cikin duk amsoshin da ya mata, ya sake kara mata da wata qaryar. Ita bata ji alama ba, bata sani ba. Shi kam zama yayi a falo yana jin duniyar ta jagule masa waje daya. Amma babu komai, zai kira abokin sa. Zai fada masa mafita, sannan kuma Jamilahr sa zata yafe masa cikin ruwan sanyi. Yasan halin matarsa fiya da kowa a duniyar nan. Sannan wannan qaryar da ya mata, ko tafi quda naci, ko ita ce manjagara ba zata tono ta ba!!! ****** Present. Ya jima yana tunani kafin Hajiyar ta fito daga bandaki. Sai da ta shirya cikin kayanta tsaf tsaf sannan suka gaisa sama sama yanda suka saba na tsawon shekaru. “Dama Hajiya nazo miki da albishir. Ina so nayi aure kuma in sha Allah duk matar da kika zaba min ita zan aura…” Sai da Hajiyar ta dan yi jim tana kallonsa kafin tayi murmushi. “Yaro man kaza… A’a Muhammadu, ka zabi matarka da kanka. Ni ban iya zabi ba…” “Hajiya kiyi haquri ki sanya min albarka kafin na fara neman auren…” Ya fadi yana kawar da kanshi. “Allah sarki Jamilah diyar arziki…” Sai Hajiyan ta fashe da kuka tana tuno kirkin da Jamilah tayi mata har ya sanya taji tana son yarinyar sosai. Sai da tayi kukan ta koshi sannan ta kalle shi. “Je ka, Allah ya sanya albarka. Allah kawo ta gari.” Yayi mata godiya sosai sannan ya shigo mata da kayan abincin da ya siyo ya ajiye mata kudi kafin ya tafi. Zai je yayi wa Salmah siyayyar kayan azumi sannan yaje gidansu. Goben za’a fara azumin. ***** Yau ma ba su da wani lokaci isasshe da zasuyi ta hira da maman Ameerah. Tunda Salmah ta tsaya a wajen da zata fara labarin Mansur aka kirasu cewa malamin yazo. Tun sannan basu samu damar kebewa ba suyi hira. Fitowarsu kenan daga aji Salmah tace kanta yana ciwo zata tafi gida ta huta saboda gobe za’a fara azumi in ba haka ba, ba zata iya kai azumin lafiya ba. “Rike min jaka ta maman Ameerah, zan karbo aron littafin Khady.” Salmah ta fada tana ajiye jakar tata. Sanda ta dawo kuma sallama suka yi da maman Ameerah wadda tace ita zata zauna tayi karartu. Hakan yasa Salmah ta tafi ita kadai. Tana zuwa bakin get din makaranta tayi sa’ar samun abun hawa. Sai da ta hau suka gamu da go slow. Garin ya cika fam, ko ina motoci. Qisshirwa ta ishe ta sannan ta tuna ta ajiye ragowar lemon da tasha da safe a jaka. Babu sauran sanyi taji saboda ana rana sosai, tayi tsaki sannan ta daga ta shanye. Dai dai sanda mai adaidaita ya sauke ta a qofar gida, sannan motar sheikh ta faka, a sannan kuma taji wani abu na fusgarta, nan da nan ta fara tangadi. Da kyar ta sallami mai adaidaitar tana tunakarar kofar gidansu. Sannan sheikh ya fito ya same ta. Kallonsa tayi, jikinta yana ta lilo, ta kasa tsayawa waje daya. “Wannan kaamaaar sheeeeikhhh diiiinaaaa…” Ta fada cikin maye tana kallonsa. Hannun ta gaba daya rawa yake yi. Kana mata kallo daya kasan ta bugu sosai da sosai. “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…” Sheikh ya furta. Ganin kamar mutane zasu fahimci abunda yake faruwa yasa kawai ya dauke ta caraf yayi cikin gidansu da ita yayinda ta fara barci a take. Shi kuma wani irin ciwon kai ne ya kama shi…. **** Da kyar yake takawa, ba don nauyin Salmah ba, asali ma bata da nauyi kwata kwata tunda siririya ce. Bai kalli fuskarta ba, idonsa kawai yana gabansa ne yana karasawa cikin gidan. Jakarta ce take lilo a jikinta. Bai kula da ya cire mata ba saboda hijabi ne a jikinta. Bai san mai zai ce wa iyayenta ba, bai san taya zasu dauki labarin ba, gaba daya ya rasa inda zai kai tunaninsa ya samu mafita. A hankali yake tuno haduwarsu ta farko, ranar da ta saka niqabi ya ganta a bakin kemis. Ya tuna ya kira ta da sunan khair wanda a sannu a hankali ta hana shi kiranta da wannan sunan, lokacin tace masa sunan ta Salmah saboda haka ya daina ce mata Khair ita ba sunan ta bane. Daga nan ya tuno sanda zata kira shi tana kuka tace ya mata nasiha saboda ranta babu dadi… Zuwa ranar da suka hadu a makaranta ya bayyana mata niyyarsa na auren ta. Yana tunawa da abunda tace, yana tunawa da abunda ya faru a ranar, tabbas babu shakka abunda yake zargi hakane. Ko da yake ga zahiri, Salmah a hannun sa, a yanayin buguwa sakamakon wani abu da ta sha. Neman abunda zai kare ta yake amma da ya bincika cikin kansa sai ya hango komai kara bayyana masa da gaskata masa cewa tana shaye shaye yake. Kaico! Gumi yake ta ko ina, duk da haka yana kokarin kawar da tunanin cewa MATAR SHEIKH ce a hannun sa a daya bangaren kuma, YAR SHAYE SHAYE ce a hannun sa. Taya biyun zasu hadu waje daya? Ya za’ayi ace matar sheikh ta kasance yar shaye shaye? Sai dai daya a ciki. Ko wanne mazauninsa daban yake…+ Sallama yayi a cikin gidan, idansa ya kada yayi jawur saboda zulumin da ya tsinci kansa a ciki. Umma da Abba suna zaune a tsakar gidan, suka jiyo Sallama. Umma tashi tayi ta shiga cikin daki shi kuma Abban ya amsa sallamar yana cewa a dakata zai fito ya yiwa ko waye iso. Sarai ya san muryar sheikh din amma a yau bai dauki muryar ba saboda a raunane ta fito. Yana zuwa inda sheikh yake tsaye da Salmah kamar matacciya a hannun sa, sai yayi turus. Ya rasa ma qarfin da zai daga kafarsa ya tako ya tabbatar abunda yake gani haka ne. Ganin Abban ya kasa motsi yasa Sheikh din yayi kokarin yin magana. “Abba, salam alaikum.” Yace. Sannan Abban ya dan kalle shi. “Wa..wa’alai…wa’alaikumus salam. Bismillah.” Ya furta da kyar suna qarasawa cikin gidan. A tsakar gida suka tsaya. Tabarmar da Abban yake zaune dazu, nan yayi nuni da Sheikh ya ajiye Salmah. Shiru ne ya ziyarce su duk su biyun, can kuma sai ga kiran sallahr la’asar. Haka ba tare da musanyen ko wace irin kalma ba duk su biyun suka tafi masallaci. Salmah kuwa kwance take kamar babu abunda yake damunta duk fadin duniyar nan, barcinta take kamar jaririya. Umma ta fito yin alwala kenan taga Salmah kwance. Salati ta saka, tana mamaki. Ganin barci Salmah take yi, ya saka ta yi alwala. Bata tashi Salmah ba, saboda in da Abba yana so a tashe ta, da ba zai fita ba tare da yayi wa Ummahn bayani ba. Ta jima a tsaye tana kallon Salmahn kafin ta saka hijabi ta tada sallah. A masallaci kuwa bayan sun idar da sallah sun fito, Abba kallon sheikh yayi sannan yayi murmushi. “Kaje gida, idan ta tashi kuma naga da buqatar yi ma magana, zan neme ka.” Da haka sukayi sallama sheikh ya koma motar sa. Ya kai minti ashirin yana tunani kafin ya bar unguwar. ***** Bata farka ba sai bayan sallar Isha, ko da ta farka dinma, bata fahimci a inda take ba, bata fahimci a wani hali take ba sai dai ta shafa gefenta taji ta taba filo. Firgigit ta tashi zaune, zuciyar ta na dukan uku uku ko ma talatin talatin a lokaci guda. A hankali ta tuno abunda ya faru, sannan ta tuna fuskar wa ta gani a qarshe kafin taji ta bace daga duniyar gaba daya. STORY CONTINUES BELOW Sauko wa tayi daga kan gadon, ta rasa mai zata fara yi. Sai kawai ta fara kuka. Shi kenan mutuncinta ya zube, a idon Umma da Abba, a idon Sheikh, a idon yan unguwa. Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Wannan wace irin rana ce. Can kuma sai ta tuna wani abu, lemon da ta sha. Shi ya saka ta a halin da ta shiga. Zata iya rantsewa da Allah ba ita ta saka abu a ciki ba. Hasalima rabonta da wani abun maye tun kwanciyar ta a asibiti duk da kuwa lokaci zuwa lokaci tana ji wani bangare a kwakwalwarta yana ingiza ta da ta sha. ‘Innalillahi wa inna ilaihi raji’un’ ta sake furtawa. Tana tsaye kamar bishiyar da aka dasa, taji an turo kofar dakin. Abba ta gani da Umma a gabanta. Sauke ganinta tayi zuwa qasa, basu ce da ita komai ba kawai suka fice. Can anjima kuma sai gashi an turo mata abinci, bata ci ba. Zama tayi kawai tana tunanin waye ya zuba mata a cikin lemo, sannan kuma ya akayi bata lura ba, mai kuma aka zuba mata wanda kwata kwata bai canjawa lemon dandano ba. Tana da tabbas din ba maman Ameerah bace, toh waye? Ta tuna cewa ta tarar da zif din jakarta a bude amma batayi tunanin komai ba. Yanzu itawa zata zarga? Ta san idan ta tunkari wata a cikinsu toh tabbas fada ne zai barke a tsakanin su kuma a halin yanzu bata da wani bakin yin fada. Tana zaune, idonta ya fada kan jakarta. Da sauri ta sauka daga kan gadon taje ta dauko wayarta a ciki. Toh wa zata kira? Maman Ameerah? Tace mata me? Haka kawai fada ya shiga tsakanin su? Sai kawai ta fasa. Ajiye wayarta ke da wuya taji saqo ya shigo. Wata baquwar number ta gani, hakan yasa ta bude. ‘Nasan I zuwa yanzu kowa na unguwarku yasan wacece ke, yar maye, yar shaye shaye? Duk wanda suka zaba yayi. Nasan iyayenki ma yau zasu kore ki saboda sun gano ko ke wacece. Shi kuma Sheikh din da kika same shi a tafin hannunki, bayan ko wacce salihar mace da mara tarbiyyar neman soyayyar sa take ruwa a jallo. A yau dai ina da tabbas din ya sullube daga hannunki. Domin kuwa idan yazo bincike, zai tarar ashe miskilar yarinyar, yar maye ce. Ki huta lafiya. Ops na manta ban gabatar miki da kaina ba. Haha. Nice wadda zata riqe tambarin MATAR SHEIKH ko kin so ko baki so ba.” Salmah gaba daya hannun ta rawa yake yi. Amma can kuma sai wani sauqi yazo mata. Ko babu komai ta samu abunda zata nunawa Umma da Abba. Hakan yasa ta kwalawa Umma kira da qarfin gaske hade da fashewa da wani irin kuka mai nuna firgici… Da sauri Umma ta shigo, a take Salmah ta miqa mata wayarta, tana kuka. Karba tayi ta fice. Tare suka karanta da Abba. Sai gashi sun shigo suna rarrashinta. A fahimtar su, sharri aka mata, tsoro ne ya dar su a zukatan su. Ita kuwa Salmah da taga sun rarrashe ta sai taji ai saqon ma gaba ya kai ta tun da ya wanke ta. Da haka dai suka yi mata sallama, ita kuma tayi alwala tayi ta sallolin da ta rasa. Sannan ta samu taci abinci. Bayan ta hau kan gado ne ta turawa Sheikh saqon da aka turo mata. Amsar da ya bata ce ta sanya taji zuciyar ta na tarwatsewa. ‘Duk da haka, duk da an so a bata miki suna, a bata sunan gidanku ta hanyar baki abun maye. Gaskiya daya ce Salmah, kuma na san da ita. Salmahn da na sani, wato ke. Kina shaye shaye. Kuma kar ki yi min musu. Na sani…’ Kashe wayar tayi ta fara kuka. Tana kukan barci ya dauke ta, bata tashi ba sai da Umma ta tashe ta Sahur. Da ta tashi sahur dinma bata iya cin komai ba. Ruwa kawai ta kora, bakinta yana mata daci. Ranar bata fita makaranta ba, wayarta ma kashe ta tayi. A daki ta yi ta zama tun safe har azahar. Bayan sallar la’asar ne ta fito domin taya Umma hada abun shan ruwa, taci karo da Abba. “Yauwa dama ina neman ki.” Ya fada yana mata nuni da ta bi shi falonsa. Bin shi tayi ta zauna a kasa yayinda ya zauna a kan kujera. “Duk abunda zan tambaye ki gaskiya zaki fada min.” Jikinta gaba daya yayi sanyi, ga yunwa da take ji, ga yanayin da ta shiga tsakanin jiya da yau. Bata taba hango kanta a cikin wannan yanayin ba. “Kina son sheikh?” Shiru tayi. “Kina son shi? Eh ko a’a?” “Eh Abba.” Ta amsa tana jin kunya. “Alhamdulillah.” Abba ya fada sannan ya zura hannun sa a aljihunsa ya ciro wata baqar leda. “Wannan sadakin kine. An daura aurenki da Sheikh dazu.” Sai ya ajiye mata a gabanta ya tashi ya fita. Shima kunyarta yake ji. Ita kuwa ta zata bata ji daidai ba har sai da ta dauki ledar taga kudi a ciki sannan ta shiga har dakinta ta janyo wayarta ta kunna. Saqon sheikh ta fara tararwa. “Ina miki murna, a yau kin zama MATAR SHEIKH. Congratulations.” Bata san sanda ta saki wayar ba ta fadi a qasa ta tarwatse. ***** Tunda ya koma gida, kansa yake wani irin sarawa wanda ko barci bai runtsa ba, da sahur ma ruwa kawai yasha yana jin wani iri, ya dade yana tunani da safe kafin yaje ya sami Abba yace idan babu matsala yana so a daura musu aure a ranar, bai san dalilin yin hakan ba, kawai yana ji a ranshi kamar hakan ne dai dai. Bayan ya turawa Salmah saqo, bincike ya shiga yi a wayarsa. Mene yake saka mata shaye shaye? Ya karance duk abunda aka rubuta a matsayin amsa sannan yayi sake rubuta wata tambayar. Mene yake hana shaye shaye? Mene maganin sa? Mene… Mene… Mene… Haka yayi ta rubuta tambayoyi har sai da yaji sauqi sannan ya ajiye wayarsa. Zuciyar sa duk da haka, zafi take masa. Tana radadi, duk a lokaci daya. Haka ya daure yasa a ransa zai je yaga Salmah idan an sha ruwa. Bai ankara ba yaji ya fara tunani, ashe dama irin wannan ciwon Jamilah take ji? Wata rana ce da ba zai manta ba, ranar da yaga yanda Jamilah tayi rauni sosai a gaban idonsa. Rana ta farko da yaji ba shi da abun cewa. Ranar da, da bakinta tace ya sake ta…+ **** Past. Wata rana ne yayi tafiya bikin abokin sa a qauyen su, bayan an gama bikin ya leqa gidansu inda mahaifiyarsa tace ya tafi da Gaaji gidansa dake birni. Sai da ta yi masa duk wani bayani sannan ya taho ranshi a bace sosai da sosai. Shi baya son takura sam sam. Haka kawai anzo an maqala masa wata yar qanwar mahaifiyarsa wai ita Gaaji. Saboda kawai na zai iya cewa a’a ya gamu da fushin mahaifiyarsa ba shiyasa ya haqura ya ce su tafi. Ko tawagar abokan na shi bai bi ba tsabar takaici. Haka ya tattara ya taho da ita gidansa, gidansu, shi da Jamilah. “Ke Gaaji, bana son surutu, in ta ja ki da surutu, eh ko a’a ne amsar ki.” Ya mata kashedi kafin su shiga cikin gidan. Sallama sukayi a tare, Jamilah ta amsa sannan ta fito sanye da riga da wando wanda suka kamata tsam. Matar ta fara hangowa kafin sheikh amma duk da haka sai tayi murmushi ta taka a hankali inda yake ta rungume shi ba tare da ta ji kunyar farar matar ba. Tayi kewarsa, kwanansa uku baya nan. “I missed you.” Ta fadi masa a kunne sannan ta sake shi. Murmushi yayi. “Ina tare da baquwa. Mu je ciki.” Sannan suka shiga cikin gidan. Sanda Jamilah ta kawo musu ruwa ne sannan matar ta gaishe ta. Da fara’a ta amsa tana tambayarta lafiyarta da na mutanen gida. Bayan sun gama cin abincin ne, Sheikh ya kalli Jamilah ya mata alama da yana so ya yi mata magana ita kadai. Tashi tayi ta tafi daki. “Kin ji dai abunda na gaya miki ai.” Ya qara gargadan Gaajin kafin ya tafi dakin inda Jamilahr ke jiransa. “Baquwa ce, sunan ta Gaaji. Tun muna yara aka barwa Hajiyar mu ita raino, ina jin ma kamar ita ta yaye ta. Shine wai yau aka ce nazo da ita birni ta kile ta samu mijin aure saboda kyaun ta ba na mazan kauye bane. Ki kula da ita.” Haka kawai yace wa Jamilah sannan ya fice ba tare da tace komai ba. Shi ma yayi kewar matarsa amma yanzun ran shi a bace yake, ya baro abokansa a can suna ta shagali ban da shi. A kwana a tashi, Jamilah da Gaaji suka saba sosai kasancewar ita Jamilah bata da wata matsala. Asali ma dadi taji saboda a qalla yanzu Sheikh yana kula da yan uwansa tunda gashi har ya je ya dauko wata. Ta hanyar Gaajin take so ta san komai game da gidansu, saboda ta je ta gaida mahaifiyarsa. Gaaji fara ce sosai, yar siririya. Bata da gashi mai tsawo, amma yana da tsantsi irin na Fulani. A fusge, tana yanayi da Sheikh kadan. STORY CONTINUES BELOW Zaune suke suna kallo, Jamilah ta tashi ta hado musu lemon kankana. Dawowa tayi suka zauna suna sha tare. “Ni kam anti irin kayan nan da kike sakawa ne suke burge ni.” Yar dariya Jamilah tayi sannan ta kalli kanta. Riga da siket ne a jikinta. Rigar kuma mai hannu daya ce shi kuma siket din iya gwiwarta. A qalla kaya uku take sakawa a rana, saboda tana da kaya birjik. Da safe in tayi wanka sai ta saka atamfa. Zuwa yamma kuma bayan ta gama aikace aikacen ta har abincin dare, sai ta saka irin wannan na jikin ta bayan ta yi wanka. Da daddare kuma in tayi wankan dare tana sauyawa zuwa maras nauyi, in da baqi a gidan, sai ta daura after dress a kai. “Gaaji kenan, sai na baki wasu amma fa sai zakiy aure.” Jamilahn ta bata amsa. Gaajin bata ce mata komai ba. “Haushi kika ji? Toh shikenan yi haquri, muje ki zabi guda uku. Ai sun ishe ki yanzu koh?” Murmushi tayi, tare suka je durowar Jamilah. Ran Gaaji fal da baqin ciki da kishin cewa dan uwanta yana kashewa matar sa duk wannan kudi akan kayan sakawa. Haka ma tana kishin irin abincin da ake ci a gidan, su suna can qauye suna cin garau garau. Bata da masaniyar cewa rabin abubuwan gidan da kudin Jamilah aka yi shi. Kuma ko da Jamilah zata fada mata, ba zata yarda ba. Dama yawanci haka abun yake, a zahiri idan an ga gidan mace sai a fara mata hassada ana kwadayin mijinta. Ba’a san mai take jurewa ba, ba’a san mai da mai tayi da kanta ba. Abubuwa da dama idan zata fada, ba za’a yarda ba. Cewa za’ayi makaryaciya ce ko bata da godiyar Allah. Duk da haka Jamilah bata damu ba, rufin asirin mijinta shine rufin asirinta. Ba ruwanta da wanda zaiyi tunanin komai Sheikh ne yake mata, bayan ba shi din yake yi ba. Kuma babu wanda zata nunawa cewa ita take yin wasu abubuwan da kanta. “Nagode Allah ya saka da alkhairi anti, Allah ya qara budi.” Gaajin tayi godiya sosai. Jamilah bata ce komai ba sai murmushi da tayi sannan ta tafi kicin domin dora abinci. Matsalarta daya, Gaaji bata taya ta aiki ko kadan. Ko da ta nuna mata ya kamata ta dinga shiga kicin tare da ita, nuna mata tayi ai hutu tazo. Shiyasa Jamilah ta rabu da ita. Tunda suna zaman lafiya, alhamdulillah ba sai taje tayi abunda zai sa su fara fada ba. Kafin dare ta gama komai tsaf. Ta shiga dakinta tayi sallar magariba sannan ta zauna chatting a Facebook ita da yan gidansu. Jin bata ji alamar Gaaji a falo ba yasa tace bari taje dakinta. Tana zuwa bakin dakin taji hayaniya. “Na rantse da Allah idan kika sake kika gaya mata ke mata ta ce sai na karya ki. Gaaji, kina wasa dani…” Ta ji muryar mijinta “Har yau baka taba ko kallo na da kirki ba, da mai ta fini? Wannan kayan mutanen banzan da take sakawa ne? Toh nima na karba zan saka. Kuma wallahi sai na gaya mata, yau shekarar mu biyu da aure…” Jamilah bata qara jin komai ba sai faduwar da tayi a qasa wanda yasa jikinta ya taba kofar. Ba suma tayi ba, kwakwalwarta ce ta dauke na dan sakanni saboda bata taba tsammanin jin zance irin haka ba. Ba lallai irin wannan ya girgiza wasu matan ba, amma ita ya taba ta sosai saboda a ganinta wannan cin amana ne ace mijinta yana da aure bai sanar da ita ba. Da bata fadi ba, babu abunda zai hana ta wanke shi da mari. Da sauri Sheikh ya fito ya tarar da ita, a qasa. Sauri yayi ya riqo ta, idanta na neman ya rufe amma cikin qarfin hali ta bude bakinta zatai magana. “Ka rabu dani sheikh…” Ta riqe cikinta wanda yake mata zafi sosai. Jini da ke bin qafarta ya saka ya dauke ta sai asibiti… Gumi yake yi. Wannan ita ce karyar da ya boye mata, qaryar cewa bayan yaqi Binta, an daura masa aure da Gaaji. Qaryar da yace ba zata tono ba, gashi ya tono mata da kansa. STORY CONTINUES BELOW Sanda ta farfado a asibiti, tana ganinsa cewa tayi ya sake ta. A maimakon hakan, komawa gida yayi ya saki Gaaji cikin bacin rai yana bata laifin komai… Wai ita ta jawo matar sa tayi barin dan da bai san dashi bama. Da aka sallami Jamilah, bata koma gidansa ba, gidan kakarta ta koma. Duk zuwan da yake yi ba ta saurare shi ba. ***** Present. Yana tunani, alarm din sa ya kada, lokacin da zai gabatar da wata lakca ya turawa kafafen yada labarai kafin a sha ruwa, yayi. Audio recorder ya kunna a wayarsa sannan ya fara, sai da ya gama sannan ya tura inda ya kama ta. Da safe ma wajen sha biyu yaje wani babban masallaci a Kano, inda shi da alarammansa suka gabatar da wa’azi da tafsiri a matsayin yau na ranar farkon azumi. Kwana biyar din farko a garin Kano zasui kafin su tafi Kaduna. Waya ya dauka, ya kira Sheikh Usama wanda shine wanda yake shugaban committee din tsare tsaren yanda Sheikh din yake tafiyar da lakcocinsa. Bayan nan akwai kungiyarsu ta malamai, inda suke tattauna matsaloli kala kala sannan su gabatar da wa’azi akan abubuwan. Sai da ya fada masa duk wani bayanai da komai da komai sannan ya kashe wayar. Ya kira alaramma Sabir Sulaiman ya fada masa abubuwa sannan ya ajiye wayar sa wadda chaji ma ya kusa qarewa saboda saqonnin da suke shigowa babu qaqqautawa. Mutane suna ta turo saqonni da tambayoyi, ta message, email da kuma website dinsu wanda ba shi kadai yake bada amsa ta website din ba. Daya wayar tasa ya dauko, wadda daga Hajiyarsa sai Salmah su kadai suke da lambar. Sai sheikh Usama. Sai da ya tabbatar babu matsala a komai sannan ya watsa ruwa, ya fara tasbihi da azkar din yamma. Har zuwa sanda aka sha ruwa, yayi buda baki da dabino sannan ya fita gidan abinci ya siyo. Sai da yaci, yayi sallahr isha’i da tarawih a masallacin da yake limanci sannan ya dawo gida. Lokacin har tara saura tayi. Yasan in yace bari ya haqura da zuwa, gobe ma ba lallai ya samu lokacin ba. Haka ya daure babu wannan fara’ar da annurin a fuskarsa ya nufi gidansu Salmah. ***** Bata kira Sheikh ba, bata bashi amsar saqonsa ba. Sannan bata tura masa barka da shan ruwa ba. Gaba daya kanta a kulle yake, Salmah bata san mai zata yi ba. Bata sani ba, fushi zatayi ko farin cikin zama matar Sheikh. Mai yasa zai yi mata haka? A karo na babu adadi taji wani irin zafi a zuciyar ta, zafin rashin Abdul. Yau gashi wai ita ce matar wani. Matar sheikh. Allah yaji qan Abdul dinta, da yana nan shi zata aura. A karo na farko taji tana so taga Uwale, tayi mata magana. Ta gaya mata yau burinta ya cika, Salmah tayi aure. Wani ciwon ne ya sake famewa, saboda tun da ta bar gidan, Uwale bata sake nemanta. Wannan wace irin tsana Uwale tayi mata? Duk wannan abubuwan sumka hade mata waje daya ta kasa cin abinci. Tana zaune, hawaye na zuba a idonta Umma ta shigo. “Amarya…” Ta fadi. Tun da zancen daurin auren ya iske kunnen Umma, Umma bata ce komai ba sai yanzu da ta zo tsokana sannan ta gaya ma Salmah angonta yana jiranta a kofar gida saboda anyi anyi dashi yaqi shigowa. Sauri tayi ta goge hawayen ta, hawayen da ya zame mata abokin rayuwa. Ji take ita kadai take rayuwa a duniyar nan, bata da kowa. Tunda gashi shima Sheikh din bai nemi shawararta ba kawai ya saka aka daura musu aure. “Umma…” Muryarta a dashe ta yi magana. Umman bata kula ba tayi murmushin tsokana. “Maza maza ki watsa ruwa kije mijinki na jiranki.” “Umma…” “Babu abunda zanji ba zaki fita haka nan ba kamar wata marar gata.” Salmah runtse idonta tayi sannan taje ta watsa ruwan, Hijabi ta saka a saman rigarta ta fita zuciyarta kamar zata fito waje. Ba don Umma ta takura mata ba, wallahi babu inda zata je. STORY CONTINUES BELOW Haka ta fita tana fushi, ga tsoro fal cikin ranta. Umma kuwa girgiza kanta tayi bayan Salmah ta fita. Har cikin ranta taji dadin auren saboda ba taga damuwa tare da Salmah ba. Daga baya za’a yi ko yar walimah ce sannan su tare. Babu wata bidi’a da zasu bi, da so samu ne ma, Umma so take walimar ma ta zama iya mata kawai. Shi ma sheikh yayi iya shi da abokansa. Irin yanda ake yi da, lokacin zamanin annabi s.aw. Umma bata gane hikimar da Abba ko Sheikh ya hango ba har suka daura musu aure lokaci daya ba tare da wani shiri ba. Haka ma tayi mamakin amincewar Abban saboda tun kwanaki yayi binciken sa akan Sheikh din. Ya sani, ya taba aure amma bai samu labarin irin zaman da yayi da matarsa ba. Ya samu labarin zaman sa a Katsina gidan Alhaji AbdulHamid, da dadewar da yake bai je gida ba. Wani abokinsa da yake aiki a Katsina ya saka ya samo masa duk bayanan. Abun ya tsaya masa a rai, amma sai Ummah ta nuna masa cewa da da yanzu ba iri daya bace. A da, za’a iya yiwa Sheikh din uzurin kuruciya da zugar abokai. Sannan bai yi nisa ba a karatu wancen lokacin. ‘A koyaushe mutum ya kan canja daga mummunar dabi’arsa domin hali tamkar riga yake, ka yadda da sauyawar tasa kada ka taba kallonsa a matsayinsa na jiya wannan shi zai bashi damar dorewa akan sabuwar dabi’ar da ya dauka wato halayyar kwarai. Lissafashi ko kallomsa da tsohuwar dabi’arsa shi zai sanya masu irin halin nasa su gaza wajen canjawa.’ Haka ma abokin Abban yace shiyasa Abba ya haqura ya bar Sheikh din ya cigaba da zuwa wajen Salmah. Sanda Salmah ta qarasa kofar gidan, kamshin turaren sa ne ya fara dokar hancinta. “Salam alaikum.” Ta fada bayan ta gama kare masa kallo taga tunaninsa yayi nesa. “Wa’alaikumus salam. Muje.” Ya mata nuni da motarsa. Bata matsa ba sai da ya sake kallonta. A karo na farko yana ware mata manyan idanunsa a kan fuskarta. Wani kwarjini ya mata shiyasa ta bi shi. Gidan direba ya zauna ita kuma ta zauna wajen fasinja. “Ina wuni.” Tace, a taqaice. “Toooh ku ji min ikon Allah,” da sauri ta kalle shi. Mai tayi? “Ji yanda kike gaishe ni kamar kina gaida makiyinki. Mijinki ne fa.” Ya fada yana murmushi wanda ya saka ta ta sake tsarguwa. “Toh me zance?” Kada kai yayi ya gyara murya. “Cewa zakiyi assalamu alaikum wa rahmatullah ya zawji, mijina, sanyin idaniyata, barka da dare. Da fatan an sha ruwa lafiya. Haqiqa ina cikin yanayin kewar ka sai gashi ka zo…” Salmah kallonsa tayi ta jinjina kai. “Tabdi!” Ta fada a fili. “Ba zaki iya ba?” “Ni ka dai na duk wannan. Muyi maganar me yasa ka min haka? Auren mu cikin gaggawa? Bayan ka sani, na gaya maka, I’m too dirty for you. Na gaya maka ba irin matar aurenka bace ni… Ni…” Sai kukan da take riqewa tun jiya ya subuce mata. Kukan ta ba qaramin taba masa zuciya yake ba. Hannu ya miqa ya goge mata hawayen sannan ya riqe hannayenta biyu. “Ki bude ido ki kalle ni.” Bude idon tayi, fuskarta jawur. Sauke nashi idon yayi cikin nata, yayi zaton zata dauke nata amma bata dauke ba din. Ya san akwai abunda take karanta a cikin su. “Na fahimta, kina cikin wani yanayi, zuciyar ki tasha karaya, ina iya karantar haka ta cikin idaniyarki. Na sani, abubuwa da yawa sunyi miki nauyi akanki, kin rasa inda zaki saka su, na sani, kina iya kokarinki. Naji labarin rayuwarki tsakaninki da Uwale, na ji rasuwar dan uwa Abdul. Duk wannan abubuwa ne da suke da karfin gaske, abubuwan da suka so su tarwatsa miki zuciya lokaci guda. Amma ban san yanda kika yi ba, duk ke kadai, all by yourself, you fought through them. You almost won, kin kusan cin galaba sai wani ko wata suka gaya miki shaye shaye yana yaye matsala ko?” Tsayawa yayi yana son jin amsarta. Abba ya bashi labarin komai da ya sani, amma banda wajen shaye shayen. Abba bai yarda Salmah tana shaye shaye ba. Amma shi Sheikh tunaninsa ya bashi, bayan yaji abubuwan da suka faru da ita. Shiyasa ma ya turo mata da wannan saqon. “Ban san haka yake ba. Wallahi ban sani ba, ban san da shi ake maye ba… Cuta ta sukayi kuma na kasa denawa.” Hawayen ne suke zuba sosai. Sheikh, ya gyada kai. “Na sani. Wannan shine dalilin da yasa na ke so ki zo mu gina sabuwar rayuwa, ni da ke. Na sani, kullum ciwon da yake zuciyar ki, yana shan famu, shiyasa nake so ki zo mu warkar dashi. Salmah ba zan guje ki saboda komai da ya faru da ke ba. Ki sani, ina tare da ke a ko da yaushe. I will help you heal. Zaki warke, zakiy raha kamar kowa. Zaki murumushi, wanda zai haska duk inda kika shiga. Ki sani ke tauraruwa ce. Tauraruwa mai haska rayuwa ta. You’re my star. Kar ki sake cewa baki cancan ce ni ba, kin cancanci zama matar sheikh da duk wani abu da yafi wannan ma. Kina ji na ko?” Da sauri ta gyada kai. Bata san ya akayi ba, amma sai gashi tayi murmushi. Sanyin motar na shiga jikinta… Kanta ya riqe wanda yasa ta rufe idonta, shi kuma ya mata sumba a goshi. “Sai da safe, matar sheikh.” Ba tace komai ba, idonta a rufe ta fice daga motar tana jin kunyarsa. Hawaye take har yanzun amma wannan karan ba masu zafi bane. Ji take kamar an yi mata musanyen zuciya. Murmushin fuskarta bai bace ba har ta shige cikin gida. Shima haka yayi ta murmushi, yana jin sabon yanayi a tare dashi. Haka ya tuqa motar ya bar unguwar duk da yana ji kamar ya kira ta ya qarasa gaya mata komai da ke ranshi a kanta. Ta tarar da Umma a tsakar gida, shiyasa tayi sum sum ta wuce cikin dakin ta, da ta shiga ma, rufowa tayi da niyyar ba zata fito ba sai safiya. Ranta take ji fes, kamar jaririya. Haka ta kwanta tana ta tunani kala kala, tayi wannan tayi wancen har sai da ta kiyasta yanzu ya je gida sannan tayi murmushi. Wayarta ta dauko domin ta tura masa saqo amma sai ta rasa mai zata rubuta. Batir din ta saka ta kunna. Nan taga sakon kawayenta suna tambayarta mai yasa bata zo ba yau. Ba wanda ta bawa amsa a cikinsu. Yanzu ba su bane a gabanta kuma in Allah ya yarda, ba zata kara karban abinci daga hannunsu ba balle ma wani abu ya faru. Duk da kuwa sun nuna damuwarsu qarara a rubutun saqon da suka aiko mata, sai kawai take ji ba wanda ta aminta dashi a cikin su yanzu. Nagode. Kawai ta rubuta ta tura masa, sannan ta kwanta. Ba’a jima ba ya rubuto mata amsa. ‘Matar Sheikh kenan.’ Kifa wayar tayi sannan ta kwanta, tayi wani irin barci mai cike da nutsuwa da kwanciyar hankali. Karfe uku da rabi ya kira ta yace ta tashi tayi sallah sannan da safe in zata tafi makaranta ta kira shi. Da safe da zumudinta ta, tashi saboda tana so ta qara ganinsa. Yau kam har shara tayi, ta gyare dakinta. Lokacin ta tuna da wannan koren littafin da ta tsinta, littafin rubutun Jamilah. Tayi ta dubawa, ta daga nan, ta daga can bata gani ba. Qarshe ta haqura tace zata tambayi Umma ko ta gan shi.+ Haka kawai takeso ta qarasa karanta littafin saboda ta ji rayuwar da Jameelah tayi a matsayin matar sheikh. Gashi bata yi nisa ba kwata kwata dan ko sunan sheikh din Jamilah bata sani ba. A fejin farko ta tsaya, sai kuma wani feji da ta bude ta fara karantawa kafin ta ajiye. Shiga dakin Umma tayi tace mata zata tafi makaranta. “Yauwa Umma wani littafi kore mai kwalliya a jiki, ko kin ganshi?” Jim Umma tayi. “Ko wani littafi cike da rubutu kike nufi?” Ta tambaya. “Shine Umma.” Umman ce ta dafe kanta. “Kash ai na qona shi rannan da na ke so ba kunna wuta a itace, randa na suya masar bauci. Allah sa ba na amfani bane?” Salmah taji babu dadi amma sai ta haqura saboda kar ta saka Umman damuwa. “Kawai ina neman sa ne.” Sai tayiwa Umma sallama ta fita. Bayan fitar Salmah Abba ya nemi Umma da ta shigo falo yana so suyi doguwar magana. Sai da ta qarasa wanke wanke sannan ta shiga falon nasa dauke da sallama a bakinta. Ta dade a zaune kafin Abban ya dan juya kansa. “Nasan bakin ki yana dauke da tambayoyi da dama amma duk da haka kika dake baki tambaye ni ba. A yau kafin nace komai, zan yaba miki na kuma roqi Allah ya sanya albarka a rayuwarki, ya hada mu dake a aljanna. Hassana, kin kasance mace ta gari, mata ta gari a gare ni, kin min abubuwan da ba zan iya gode miki ba cikin su harda riqe yar dan uwana, Salmah kamar yadda kika riqe Muhammad da yayansa. Ina matuqar alfahari dake kuma ina fatan mala’iku suce ameen ga duk adduar da zan miki. Kina mamakin auren Salmah da akayi lokaci daya, ba tare da na tambayi shawararki ba. Na sani, ba abu ne mai sauqi ba ace kin riqeta amma ban nemi ta bakinki ba. Gaggawa daga shaidan take amma ina tabbatar miki da cewa wannan ba gaggawar bace. Da yazo min da zancen, sai kawai tunani yazo min na halin da aka sameta, kuma duk da hakan ya nuna yana so. Wataqila za’a ce nayi son kai amma gani nayi gara kawai a daura din kafin ya canja ra’ayinsa. Kin ga dai babban mutum ne shi ba iya garin nan ba, zan iya cewa a fadin kasarnan. Yana daga cikin manyan malamai da ake alfaharin samun irinsu a Najeriya kuma ko wanne uba zai so ace yar sa ta samu irin sa.” STORY CONTINUES BELOW “Hakane.” “Yauwa. Duk abunda na binciko kuma, kafin ma na tambaye shi sai da ya fada min da bakin sa wanda yasa na qara aminta dashi. Ya gaya min bai fadawa Salmah ya taba aure ba. Kar ki gaya mata, zai gaya mata da kansa.” “Toh shikenan Abba. Allah ya sanya alkhairi.” “Ameen Allah miki albarka Hassana.” “Ameen. Amma ba ka ganin ya kamata a sanar da yaya Karime?” Abba shiru yayi yana wani nazari. “Jiya ma naje mun gaisa. Rabu da ita, sai za’a yi walima zan gaya mata. Har yau ban nuna mata cewar Salmah na tare dani ba. Karime bata da tunani…” Sai Abban ya girgiza kansa kafin yayi tsaki. “Amma kamar bamu yi mata adalci ba. Ko babu komai ita ta haifi Salmah.” “Kina sane da irin wulaqancin da takewa yarinyar ai. Ba za’a gaya mata ba. Na sani Bello ba shi da mutunci amma Karime ma sai a hankali.” “Amma dai,” “Hassana, ya isa haka.” Umma dai shiru tayi bata qara cewa komai ba. Ita a ganinta boye boyen ya isa haka. Wataqila mahaifiyar Salmah ta yi nadama amma ba lallai Abban ya gane ba. Yanzu an kusa shekara uku kenan rabon Salmah da Uwale. Ko sau daya kuma Salmahn bata taba nuna tana son komawa ba. Ita kuwa Umma zata yi iya kokarinta na ganin cewa ta shirya tsakanin uwa da yarta. Ko Sheikh ne zata gaya wa domin yayi kokarin sasanta su. Ta sani da wahala Salmah ta haqura, saboda Uwale ta chanja ta sosai ba kadan ba. Tana iya tuno sanda suka zo, Salmah ba ruwanta, faran faran ga surutu amma tun ranar da ta saka kafarta ta bar gidansu ta dawo wajen su Ummah, Ummahn ba zata iya cewa ga ranar da taji Salmah na surutu dogo ba ko kuma dariya wadda take ba yaqe ba. Oh Allah. Wannan wani irin abu ne? **** “Ke shikenan in baki ga dama ba, ba zaki fadawa mutum me yake faruwa dake ba?” Shiru Salmah tayi amma murmushin da ke fuskarta bai ragu ba. “Ji wani murmushi da kike yi. Me yake faruwa? Kar dai yunwa ta fara taba miki hankali.” Maman Ameerah ta fada tana dafe kirjinta. Zama Salmah tayi sannan ta ajiye jakarta a gefenta kafin ta kalli maman Ameerah. “Qalau nake fa.” Maman Ameerah shiru kawai tayi saboda taga alamar hakan a tartare da Salmahn. Sai dai jiya da ta kira ta a waya ai bata same ta ba kuma Salmahn bata biyo kiran nata ba sannan ba tazo makaranta ba. Har malami ya shigo ajin basu sake yin magana ba. Sanda lakcar sa tayi nisa, sannan ne Salmah ta ciro wayarta ta aikawa da Sheikh saqo kafin ta kashe wayar don kar ma ya kira ta ya katse mata karatu. Jarabawa zasu fara nan bada jimawa ba. Bayan wasu mintuna malamin ya fice saboda ya gama dukka darasin da zai musu a wannan zangon. “Ina zuwa.” Salmah tace hade da tashi ta fice. Kunna wayarta tayi sannan taga saqonsa. ‘Ina lakca, kin manta? Ki kunna talabijin ki kalla yayinda muke yi. In kina makaranta, kya kalli maimaicin da daddare.” Hakan da ta karanta ne ya saka kawai bata bashi amsa ba. Tana qoqarin kashe wayar ne wani saqo ya shigo. Naga kinzo makaranta yau yar shaye shaye. Ya ciwon zuciya? Sheikh ya rabu dake. Haha. Naga ma kina da qoqarin boye damuwa. Ta dade a tsaye a wajen tana sake maimaita tes din. Wannan wacece haka take bibiyar ta kamar tana bin ta bashi. Numfashi ta sauke sannan ta goge tes din. ***** Sanda Salmah ta koma gida, sosai ta dage suka hada abincin shan ruwa tare da Ummah. Tunda take bata taba yin koko ba sai ranar duk da kuwa in taje gidan Iya Abdul tana ganin sanda ake hada kamun da yake har da shi Iya take siyarwa. Ko kosai bata san yanda ake yi ba duk da yana cikin abubuwan da ta fiso. STORY CONTINUES BELOW Uwale bata bata yin girki, sai dai ta barta tayi qarshe ko wani aikin gidan kamar shara da wanke wanke wanda bashi da yawa ko kadan. Zuwanta Kano, Ummah bata takura mata ko kadan. A karo na farko taji rashin hakan da tayi. Ta rasa dalili, amma daga jiya zuwa yau abubuwa da dama suke mata yawo a kai. “Ummah.” Ta fadi, tana daukar butar alwala inda ita ma Ummah ta dauki butar. “Ina son ki Ummah, Allah ya saka da alkhairi.” Ummahn ce ta sake kallonta. Ko kadan bata taba saka komai a ranta ba duk tsawon lokacin nan. Bata da takura, amma tana son kyakkyawar tarbiyya. Bata taba saka Salmah abu mai yawa ba saboda ita da kanta take ganin bakin ciki a idon Salmah. Bata so a ce ta zama sanadiyyar qarin baqin cikin mutum shiyasa kawai tayi haquri. “Salmah kiyi alwala kin ji ma ana kiran Sallahr.” Ta katse mata tunani. “Ummah wallahi ba zan taba iya gode miki ba. A rayuwa bani da kamar ke a yanzu.” Salmah ta share wata yar kwalla. Ita kuwa Ummah murmushi tayi kadan kafin ta fara alwala. Mamaki ne kawai ya hana ta iya bayar da amsa. ***** Sai wajen tara sannan Salmah ta zauna bayan sun wanke duk wasu kwanuka da suka bata kasancewar kowa yana nan sannan ana fita da abincin sadaka. Abba ba mai kudi bane, amma yana iya kokarinsa na ganin ya taimakawa na kusa dashi, dan uwa ko bare. Mutum ne wanda zai iya haqura da yi wa kanshi abu yayi wa wani tunda Allah ya rufa masa asiri. In Ummah tayi magana akan yanda yake yi sai ya ce mata ai ba sai mutum yana da makudan kudi ba sannan zai taimakawa mutane. In har mutum yace sai ya tara da yawa sannan zaiyi, toh watakila har ya mutu ba zai yi ba. Daga baya Salmah ta tuna da yakamata ta kunna ta kalli lakcar Sheikh. Amma sanda ta kunna, an kusa gamawa domin kuwa amsoshi yake amsawa. Idonta ta kafe shi dashi tana murmushi. Sanye yake da yaluwar shadda mai haske. Kalar ta sake haska shi. Idansa kyalli kawai yake mata. Haka taji wani irin abu ya mamaye zuciyarta. Wai duk shi dinnan, nata ne. Ita ce mamallakiyarsa. Matar Sheikh. Tabbas, yaf’alul lahu ma yashaa. “Malam ana cewa akwai hurul in a aljanna, shin yaya suke?” Alramma ya karanto tambaya. Sai da Sheikh yayi dariya sannan ya amsa. “Ni dai ban taba ganinsu ba,” dariya mutanen wurin sukayi. “Hoor daya kawai na sani. Mata ta, ta duniya, Salmah.” Zare ido Salmah tayi kamar tayi ihu. Sheikh yasan mai yake cewa kuwa? A bainar jama’a? Lallai ma, har da kama sunan ta. Allah yaso ba tare da su Ummah suke kallo ba, da bata san ya zatayi ba. Alramma ne ya gyara zama. “A’a ko dai sheikh ya shiga daga ciki ne bamu da labari?” Sheikh murmushi yayi. Baya so a yayata a duniya tukunna. Shiyasa kawai yace, “Zai shiga dai in sha Allah. Mu dawo kan tambayar mutumin nan. Qurani dai ya siffanta mana su da cewa suna da manyan idanuwa…” Salmah bata ji ragowar ba saboda tashin da tayi ta nemo tishun da zata goge fuskarta saboda hawayen da bata san dalilin zubowarsu ba. Sanda ta dawo ta zauna, anje tambaya ta gaba. “Malam meye matsayin shafa turare ko sanya kwallin bita zai zai saboda aka hankalin namiji ko a mallake miji da su sarqa ko jigida da ake sakawa na mallaka…” Sheikh din ne ya kalli alaramma sannan yace, “Haramun ne kuma shirka ce. Domin kuwa duk macen da ta sanya kwalli a idanunta, ko turare, ko sarka, ko duk wani abu da nufin cewa anyi masa wani lakani na musamman tayi shirka saboda ta yarda cewa wadannan abubuwan zasuyi mata abubuwan da ta saka a rai. A fakaice dai ta zama mai bauta musu. Adduar nan dai da muke rainawa wadda Allah ne kadai ke amsawa, itace mafita. Amma matan mu a yanzu suna cikin bala’i. Duk wasu yan kudaden su wasu ke kwashewa da sunan siyan maganin mallaka. Shi kuma shaidan ya samu abunyi domin yayi alkwarin batar da mutane shiyasa zai yi ta tona wa mutane rami suna fadawa. Manzon Allah sallalahu alaihi wassalam da yaje isra’i da mi’iraji yace yaga mata sun fi yawa a wuta. Kuna mamaki? Bayan gashi nan kiri kiri mata suna aikata shirka, wasun su basu sani ba. Wasun su, sun sani. Wasu zasu ce ba suje wurin boka ba ko malami, amma ita shirka, harshe ma yana yinta. Allah yasa mu dace.” Wurin ya dauka da, “Amin.” “Yakamata mata su dawo hankalin su, su kama addua domin ana cewa addua makamin mumuni. Kar wata ko wani ya kawo miki abu yace in kinyi kaza zaki mallake wani saboda yin hakan yana yiwa imaninki rauni. Aure ibada ce, ita dama ibada sai anyi haquri, sai an jajirce ake yinta. Toh saboda haka, ki yi saurin tuba yar uwa, ki dage da yiwa mijinki biyayya. Ki kuma hada da addua sai komai ya zo da sauki. Domin kuwa dukkan wahala yana…” Alaramma ne ya yi bismillah zai kawo ayar. “Inna ma’al usri yusra.” Sheikh ya kara cewa. “Duk wanda yake tsoran Allah, Allah zai kawo masa mafita… Alaramma karanto mana…” Sai alaramma ya cigaba da ayar gaba. “Wa yarzuquhu min haithu la yahtasibu, wa man yatawakkal alal lahi fahuwa hasbuhu, innallaha baligu amrihi, qad ja’alal lahu li kulli shai’in qadaraan.” Sai ya azurta shi ta hanyar da baya zato, duk wanda ya dogara da Allah, Allah ya ishe shi. Allah zai aiwatar da manufarSa. Allah ya riga ya saka wa komai qaddararasa. “Saboda haka ina jan kunnenku yan uwa, amma committee ya shirya za’a yi wa mata fadakarwa ta musamman bayan sallah. Zan yi karin bayani in Allah ya kaimu lokacin. Yanzu lokaci yana hararata.” Sannan aka rufe shirin da addua. Salmah kuwa shiru tayi. Tana tunowa ranar farko da Mansur yazo bayan ta koma gida, washe gari sun je gidan Marka mai magani an karbo mata wani kwalli wanda aka ce ta dinga sakawa in zata wajen Mansur saboda kar ya gudu ko ya fasa. Gashi nan dai, ba’a yi auren ba. Rufe idonta tayi, tana tuna komai. ****** A kwance take a kan tabarma abun duniya ya isheta. Babu abun da yake mata dadi, shekara uku cif kenan tana zaune ita kadai in dai ba makwabta ne suka shigo mata ba. Tun ranar da ta nemi Salmah ta rasa, hankalin ta ya tashi. Amma sai take fadawa kanta ai batan Salmah sauqi ne a gareta. Ko babu komai ta daina ganinta sannan baqin cikin da take ji a kullum sai ragu. Zata iya cewa tayi wa kanta karya domin kuwa gashi ji takeyi kamar ta kurma ihu ta fadawa duniya cewa yar ta ta bata kuma tana kewarta toh amma duk wanda yaji zai qaryata ta ne saboda kowa yasan irin yanayin zaman ta da Salmah. Sai dai kuma ba’a shiga tsakanin da da mahaifiya. Rufe idonta Karime tayi, yayin da kwalkwalwarta ta wana zuwa baya, ranar da Salmah ta tafi. Da kanta ta ce ta fice mata daga gida saboda ta gaya mata Mansur ya fasa aurenta. Ta zata Salmah ba nisa tayi ba, ta zata gidan Iya zata je da taga ta hada kayanta. Sai kuma bayan kwana biyu da taji shiru ta haqura ta tashi taje gidan Iya din amma bata tarar da Salmah ba. Hankalin ta ya tashi har ya sa bata iya jira ba ta shirya ta tafi Kano. Zuwanta gidan kuma Abba yace mata ai sam bai ga Salmah ba. Kwanan ta biyu kafin ta koma, ko kadan bata ga alamarta ba. Yanzun ma Kanon zata koma saboda ta samu Abba ya taimaka mata ko gidan rediyo ne a bayar da cigiya saboda tana jin idan har ta mutu bata saka Salmah a idonta ba toh ba zata taba yafewa kanta ba. Da wannan tunanin ta yanke shawarar zuwa nan da kwana biyu saboda saura kwana uku Sallah. Wannan shekarar azumin yayi sauri sosai.+ **** “Gaya min wani annabi ne wannan, kina ji na?” Salmah gyada kai tayi duk da kuwa ba ganinta Sheikh yake yi ba tunda waya suke. Rarraba ido kawai take Allah yasa kar ya mata tambayar da ba zata iya amsawa ba. Tana tunawa da wani littafi da Abdul ya bata na tarihin annabawa. Tare suke karantawa amma bata sani ba ko ta manta wasu abubuwan, shiyasa yanzun take ji kamar ta kashe wayar ta ce chaji ne ya qare. Ko da yake dama ai ta fadawa Sheikh ita ba irinsa ba ce. “Wani annabi ne. Sai da yayi shekara sha uku ba shi da lafiya. Ya sunan sa?” Nan taji cikin ta ta kada, ya murda. Ga yunwa daman tana ji. “Annabi…” Sai tayi shiru kamar tana kokarin tuno sunansa. Daga yanda ta fada Sheikh yaji yanda muryarta ke rawa amma tana kokarin boye hakan. Shiru yayi da yaji ita ma tayi shirun. “Annabi Ayyub. Mantawa kika yi?” Salmah dai bata ce komai ba. Tunani kawai take yi. “Ni ban sani ba. Daman na gaya maka ai… Ni ba irinka bace…” Sai tayi shiru tana kokarin danne zuciyar ta akan cewa kar tayi kuka. Sheikh kuwa daman yana sane ya mata hakan. So yake ya auna yaga iya iliminta akan addinin. “Toh shikenan zamu yi wannan zuwa wani lokacin. Na baki assignment, zan bayar a kawo miki wani littafi sai ki karanta bayan sati biyu zan miki tambayoyi akai. Yayi?” “Unm.” “Baki kalli lakcar yau ba koh? Wai abun mamaki aka min tambaya na kasa amsawa. Farillan alwala fa.” Duk sa dai ya nuna kamar ba tambayarta yake ba, Salmah ta gane so yake ta bayar da amsa. Numfashi taja sosai kamar ta kashe wayar. “Farillan alwala ba guda bakwai bane? Munyi da yaya Abdul.” Ta bashi amsa. “Allah sarki dan uwa. Allah ya kyauta ta makwancinsa Amin. Bayan dan uwa Abdul sai waye ne?” Ya tambaya. Salmah bata fahimci tambayar tasa ba. “Kamar yaya?” Murmushi yayi mai sauti. “Yayyin naki mana wanda suke so su kai ki gidansu basu san matar sheikh bace.” “Mansur.” Ta fada a takaice. “Allahu Akbar, bani labarinsa muji ko zamu je mu gaishe shi. Ai babban wa uba, ko ya kika ce?” STORY CONTINUES BELOW “Ni bansan labarin sa ba.” Haka kawai tace saboda bata san yin maganar sa kwata kwata. “Toh shikenan ga wata tambayar?” Daga girarta tayi. “Jarida zaka buga?” “Wataqila Salmah Trust.” Dariya sukayi a tare sosai kafin duk su biyun suyi shiru sannan Sheikh ya fado tambayar tasa. “Wace rana ce tafi miki dadi a rayuwarki?” Ranaku hudu ne suka zo kanta. Ranar farko ita ce ranar da aka saka ta a makaranta, duk da tana karama ne, taji dadi sosai kuma ba zata tana mantawa da ranar ba. Bata da niyyar boyewa Sheikh komai shiyasa ta fara bashi amsa kai tsaye. “Ranaku hudu. Ran da aka sani a makaranta, ran da yaya Abdul yace yana sona. Ranar da naci jarabawar shiga jami’a da kuma ranar da na…” Sai ta danyi shiru tana jin nauyin abunda zata ce. “Ran da aka ce min na zama matar aure.” “Um Khairi kenan.” “Ni ba sunana ba kenan.” “Toh mayar da wuqar, Selmah.” “Ba Selmah bane Salmah ne.” “Toh anji amma ni Selmah zan dinga cewa. Aha, wace rana ce wadda ba kya alfahari da ita?” Ranaku biyu ne wanda da za’a bata zabi toh tabbas zata goge su daga rayuwarta. Ranar da abun nan ya faru lokacin da tana dawowa daga talla sai ranar mutuwar Abdul. Zata so ta jera ranar da Mansur ya wulakanta ta a cikin su amma sai take ganin ai kamar tsintar dami a kala ne tunda gashi abunda ya biyo baya yafi mata alkhairi. Shiyasa bata lissafa ranar a cikin wanda bata so. “Rana mafi muni ba zan iya fada maka ba a waya. Ta biyu ita ce ran da Abdul ya tafi. Ka san radadin mutuwa kuwa?” “Na sani mana Selmah.” “Nima nayi rashi shekaraun baya da suka wuce. Na rasa matata, Jamilah.” Anan ya fada mata abunda bata shirya ji ba. Tayi zaton bata ji daidai ba shiyasa tayi shiru amma sai taji ya gyara murya. “Na shiga wani kuncin rayuwa lokacin amma Alhamdulillah yanayin da na tsinci kaina a wancen lokacin shi ya saka na zama abunda nake a yanzu. A duk wani abu da zai faru a rayuwa, akwai boyayyiyar hikima a ciki wadda ko me zamu yi ba lallai mu ganta ba sai daga baya. “Kana nufin ka taba aure?” Ta sake tambaya saboda ta tabbatar da abunda kunnenta yaji daidai ne. Shafa fuskarsa yayi. Dama ya san ba wannan ce hanya da tafi da cewa ya sanar da ita amma ya juya ya juya ya rasa ta ina zai kamo zancen shiyasa yace bari ya gaya mata a hakan. Shi dama mutum ne wanda rayuwarsa ba a tsare take ba. Bai cika tsare tsaren abunda zai yi a gaba ba sai dai kawai in lokacin yayi kawai yayi. Baya son dabi’ar sa ta hakan amma yayi yayi ya gyara ya kasa. Dama kowa da irin halayyarsa da dabi’arsa a ka hallice shi. Wani yana samun nasarar gyara abubuwa da dama, shi ma din ya samu yayi gyaran sai dai fatan sa Allah yasa gyaran ya dore. “Na’am Selmah amma kamar yanda na gaya miki ai ta rasu. Bamu wani dade tare ba ta rasu a wajen haihuwa. Tare da abunda ta haifa suka koma ga mahallicinsu.” Salmah taji babu dadi da taji hakan. Ko kadan bata taba tunanin hakan ba. “Babu abunda ta bari sai littafin ta shima kuma ranar da nayi lakca a Kano na rasa shi.” “Wait, Kore ne?” Ta katse shi. “Taya kika sani?” “Na tsince shi… No, tsaya… Kai ne wanda ka bani complimentary card naku kace na tuntube ka?” “Selmah?” Ya maimaita yana tunowa da komai. Ya tuna tabbas ya bawa wata bayan ya gama lecture din. Yana tunawa ya tambayi sunan ta amma kwata kwata bai kalli fuskarta ba. STORY CONTINUES BELOW “Na tsinci littafin amma Ummah ta kona shi.” Ta fadi masa. “Eyya wataqila wannan yana nuni da cewa shafin Jamilah ya wuce yanzun lokacin mulkin Selmah ne.” “Allah ya ji qanta.” Salmah ta fada. “Amin.” Bayan yace amin ne sannan wani abu ya fado masa a rai, yana tunawa da saqonnin da ya amsa ta website dinsu amma ba zai gane wanne na Salmah ba a ciki. Amma yana tuno guda day da ya tsaya mishi a rai… “Kin taba bayar da labarinki wa wani malamin?” “Eh lokacin ina jin kamar na kashe kaina. Amma nasan ba kai bane ka amsa…” “Na taba amsa makamancinsa. Ke na bawa number?” “Eh. Nima an bani number. Na kira ina kuka na kasa fadan komai amma na tura saqo inda na fadi duk wani abu da yake saka ni tunanin kashe kaina amma ban rubuta cewa ina shan abu ba, ban fadi sunan Abdul ko Mansur ba. Bayan nan anyi ta kira na naqi dauka, sannan ne aka turon da saqo mai ratsa zuciya. Har yau ba zan fasa godewa malamin nan ba. He played a part in my life wanda yasa ma ya ciro ni daga fadawa halaka amma bayan nan kawai na karya sim din na zubar.” “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.” Sheikh ya fada bayan nan ya fara jero tahleel. Salmah tana jin haka ta san shi ta gaya wa komai. Haka kawai taji duk wani tsoro da fargaba nata ya tafi. “In dai kai na turawa then, In kana tuna komai, that’s Salmah for you. Kowa yana da labari a rayuwarsa, wasu na da tabo a rayuwa. Wataqila kana da tabo, nima ina dashi sai dai nawa ya taka kara ya karya naka. Wannan shine rayuwar matar da ka zaba ka aura. Yes, uwata ta tsane ni, ban san ko waye babana ba, nayi talla, I was raped and the worst of all, da sani na, ba tare da amin dole ba, nayi abunda Allah baya alfahari dashi tare da Mansur, saboda ina tsoran kar ya fasa aurena Uwale ta tsine mun. Amma duk da hakan gashi nan, Mansur din dumped me, yace ba zai aure ni ba. Ya dauke ni mu fita wai shopping ashe wulaqanta ni yake son yi. Ya ci mun mutunci a gaban abokansa ko da yake laifi na ne da na yarda yayi amfani dani. Yace ba zai auri second hand ba, yace ba zai auri siririya ba. Ya ce kudinsa nake kwadayi, ya zagar min mahaifiya. Ya gaya min maganganu marasa dadi sannan shi da abokansa suka sani a gaba sukayi ta dariya kamar sun kunna talabajin ne. Sannan kuma ya fada min ba zai aureni ba bayan ya min wayo ya bayar da wasu kudi yace ai in an kawo kudi kamar anyi aure ne. Ko mayar dani gida baiyi ba ya tafi ya bar ni. Haka na koma gida ina kuka. Na gaya wa Uwale yace ba zai aure ni ba nan tace tunda ni buri na na kunyata a rayuwa toh na tashi na bar mata gida. Na zata wasa take, amma da gaske take, ta kore ni. Shine na taho nan, gidan dan uwan babana. A hanya, a cikin mota na gamu da wata ta biya min kudin mota da taga ina kuka. Ta gaya min karatu zata taho nan Kano. Anan ta bani abu tace yana maganin damuwa, wannan shine mafarin komai. Ba course daya muke yi da ita ba amma ita ta hada ni da su Sa’adah sanda na samu gurbin karatu a jami’ar. Ban san illar sa ba, ban san mene mene ba amma sai na tsinci kaina a yanayin da bana iya barci in ban sha ba. Daga baya na fuskanci shi ake cewa shaye shaye. Shine abunda wasu yan daban unguwarmu suke sha. Nayi kuka nace na daina amma sai nayi ta komawa ruwa. Ban san ya ya akayi ba amma Mansur ya same ni har gidan da nake ya zo. Ban kula shi ba. Sai dai kuma haduwata da kai ta mantar dani dashi. Wannan shine labarina dama na gaya maka duk yanda kake tunani ba hakan bane. Gashi nan, na gaya maka gaskiyar komai.” Da hawaye taf a idonta ta gama bashi labari. Dama ta fada mi shi tayi mishi datti da yawa kuma abunda tayi da Mansur ne take nufi da hakan. Gashi nan ta fadi komai ya rage na Sheikh ya yanke shawara. Wataqila ya cigaba da zama da ita a hakan. Wataqila ya sake ta in yaji ba zai iya ba. Duk wanda yayi, falillahil hamd. “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.” Ya sake maimaitawa kafin ya kashe wayar, ba zai iya daukar duk abunda yake ji ba. Ya zata ya gama jin duk wani mummunan labari daga gareta amma gashi Salmah ta gaya masa abunda bai taba hasasowa ba. Bai taba tunanin jona irin wannan labarin da Salmah ba. Tsantsar nutsuwa da sanyin dake cikin idonta yake hangowa yayinda zuciyar sa take neman duk wata hanya da zata bi na gaya mishi cewa ba dai dai bane. Sai dai kuwa hakan gagara yayi. Yaji komai daidai daga bakin Salmah ba daga bakin kowa ba. Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Yanda taji karaya a muryarsa ne ya tsinka mata hanji, ta sani da wahala mutum yaji wannan bai kadu ba. Wataqila farkon labarin nata akwai ban tausayi amma cikinsa akwai laifinta. Shikenan. Qarshen ta yazo. Ko babu komai dai, na yan kwanaki ta amsa sunan. Matar Sheikh. ***** **** Salmah ba ta sake jin muryar Sheikh ba bayan ya kashe wayar tunda bai sake kiranta ba. Gashi yau ana gobe Sallah ne, cikin kwanki biyun da suka wuce, idan qarfe ukun dare tayi, tana kiran Sheikh su tashi suyi sallah kamar yanda ya nuna mata. Idan ya dauki kiran babu abunda yake cewa sai dai ta gaji ta kashe. In an sha ruwa ma, tana tura masa barka da shan ruwa. Littafin da ya fada, an aiko mata da su wajen kala goma ko wanne da fassara a cikinsa. Salmah ta yi godiya ta tura masa amma bai ce komai ba. Gaba daya taji ta takura ta daina jin dadin komai a duniyar nan. Dama Sheikh ne mai dauke mata duk wata damuwa yau gashi nan ya juya mata baya. Ko da taje makaranta ta dawo kwanciya kawai tayi. Tana kwance ne aka ce mata ana sallama da ita. Ba shiri ta miqe duk da yunwar da take ji. Tana zuwa ta tarar da motar Sheikh. Kamar ta fita a guje taje inda yake take ji. Can sai ga wani ya fito, turus tayi ganin ba shi bane. Bata motsa daga kofar gidan ba har ya tako inda yake ya mata sallama. “Ina wuni.” Ta fada a takaice. “Lafiya qalau. Sheikh Muhammad Salim ne ya aiko ni da saqo. Ko akwai yaron da zai shiga dasu?”+ “Masha Allah, ba mu da yara a gidan namu kuma amma nan yace ka zo?” “Ko ba kece Salmah ba? Hoor din aljanna.” Salmah kawar da kanta gefe tayi, tana jin kunya. Shikenan tasan duk wani wanda yaji in ya ganta sai ya tsokane ta. “Bismillah.” Kawai tace masa kafin ta shiga gida ta fadawa Umma za’a shigo da saqo. Nan Umma ta saka hijabinta suka gaisa da dan aiken. Haka ya samo wani a waje ya taya shi shiga da kayan abinci birjik. Sai da suka gama sannan ya dauko wata qatuwar leda ya miqawa Salmah. “Wannan yace a baki.” “Nagode Allah ya saka da alkhairi.” Daga hannu yayi. “A’a ni dan aike ni.” Yar dariya sukayi kafin yayiwa Ummah sallama ya fita. Ba’a dade ba sai ga Muhammad nan ya shigo. “Salamatu,” ya kira yana shiga dakin Salmahn. “Na’am.” Ta amsa yayinda ya mata nuni da su je falo akwai abunda zai gaya mata. Sanda suka zauna har Ummah zata shiga sai kawai tace bari ta kyale su su biyu tunda yau shiri suke ji. “Gaskiya kin yi sa’ar miji. Tun kafin na karaso fa ake gaya min duk kayan da ake shigowa dasu gidan shiyasa nace bari na zo na gani.” “Ni duk bai dame ni ba. Kudin ba su bane a gaba na.” Ta bashi amsa tana kifta idanunta saboda kar hawaye ya zubo. Yanzu damuwarta shine kar Sheikh ya fasa zama da ita. Duk da dai gashi ya aiko mata da abubuwa amma bata ji sanyi ba. Muhammad ne ya kalle ta na dan sakanni. Har ga Allah tun ranar da tazo gidansu yaji yana sonta a matsayin ta na yar uwarsa. Sai dai tsirar da ke tsakanin su ba mai yawa bace ya saka ya cire rai. Asali ma basa shiri saboda ta fiya bata rai. Amma tunda azumi ya kama, zai iya cewa kullum a daidai yake ganinta sai yau da yake ganin makamancin yanayin da tazo dashi gidan, shimfide a fuskarta. “Nasan ban taba yin hakan ba. Amma dai naga alama wani abun yana damunki. Care to share?” Girgiza kanta tayi alamun eh amma sai wani siririn hawaye ya zubo. Muhammad ne yake kallonta yana mamakin yanda take da saurin kuka. “Ke idonki kamar famfo wanda magudanar ruwan sa ke jone da teku. Ko yaushe hawaye?” Ya tambaya yana dage girarsa sama. Shi wannan kukan ma shi yake sake hada shi da ita. “Ba zaka gane bane.” Ta fadi tana miqewa. “Ko ma meye, kiyi haquri. Nasan bai wuce tsakanin ke da mijin naki ba. Maimakon wannan kukan da kin sani zama kikayi ki ka tsara mishi sako mai dadin karantawa wataqila ya sauko koma meye. Shawara ce.” Har ta daga labule zata fice sai ta juyo ta kalli Muhammad din wanda hankalinsa ke kanta. STORY CONTINUES BELOW “Nagode.” Da hakan ta fice. **** “Oh ni Hassana! Duk wannan ke kadai? Ai rabin kasuwa ya kwaso mana shi kam.” Ummah ta fadi tana bude kayan da aka bawa Salmah bayan ta kama kawar da kayan abincin da aka shigo dashi gefe tana jira in Abba ya dawo ya gani sai ya fadi abun yi. “Ummah nima haka na gani, sun yi yawa.” Salmahn ta fada tana kawar da kanta daga kallon kayan. Abayoyi ne har guda goma, baqaqe guda biyar sauran kuma kaloli daban daban. Sai atamfofi guda uku da mayafen su. Agogguna guda hudu da takalma. Ciki, har da kudin dinki. “Ko dai yana nufin kayan lefenki kenan?” Ummah ta tambaya. “Anya.” Salmah tace a takaice. “Allah ya baku zaman lafiya dai. Allah ya kade fitina. Ince dai kin kira kinyi godiya? Nima saka min lambar na kira shi kafin Abba yazo. Bari na dawo.” Salmah ta san Ummah tana sane ta tashi ta bar mata wajen saboda ta kira shi. Ita kuwa ba yanzu take da niyyar kiransa ba. Sallar la’asar tayi ta watsa ruwa sai taji tana son gwada daya a cikin kayan. Dauka tayi ta saka sannan taje ta dauko babbar wayarta wadda bata wani amfani da ita ta kunna tayi hotuna ta ajiye. Sai da ta cire ta kawar da kayan gefe sannan ta dauko wayar ta hau kan gado. WhatsApp ta shiga wanda da ace gida ne a gaske, da tuna yana ta bata shi saboda rashin kulawa. Profile dinsa ta bude sannan ta fara rubuta mishi saqo. ‘Salam alaikum Saahib, barka da yamma. Ina fatan kana lafiya. Kwana biyu sam ka manta da matar ka ko?’ Sai ta goge da taji baiyi mata ba. Ta sake rubuta wani. A cikin littafan da ya aiko mata harda wani mai kalmomin larabci da ma’anar su. A ciki taga kalmar Saahib din kuma taji dashi zata dinga kiran Sheikh. ‘Salam alaikum Saahib, barka da yamma. Ya aiki da fama da mutane? Allah ya bada lada, amin. Mun ga saqo, Allah ya saka da alkhairi. Allah ya ji qan mahaifa, Allah ya bada lada.’ Sai ta tura. Ba a jima ba taga alamar ya karanta. Ameen kawai yace mata. Ganin yana kusa kawai sai ta ji bari ta tura mishi hoton ta. A tare da hoton ta rubuta. ‘Saahib ka san wannan? Wai tace tana gaishe ka kwana biyu tayi kewar ka sosai. Tace ace maka tayi kuskure dan Allah ka yafe mata ba zata sake ba. Tace ba zata iya rayuwa ba in babu kai, saboda kaine saahibinta, abokin rayuwar ta.’ Bata qara da komai ba ta tura hade da yin numfashi mai sauti. Tana kallo a take ya bude. Minti biyu yayi kafin ya bayar da amsa. ‘Wannan ai sai ta jawowa mutum matsala da yamman nan.’ Sake karantawa tayi bata gane komai ba. Tana sake karantawa ne sai wani saqon ya shigo. ‘Kice zan zo na ganta in an sha ruwa.’ Salmah ta kusa tayi ihu tsabar murna. Zata bashi amsa amma sai ta rasa mai zata ce. ‘Toh zata ji.’ Kawai ta rubuta. ‘Um kice mata ta jawo wa kanta.’ Hade girarta tayi waje daya. ‘Me?’ ‘In mun hadu zata gani.’ Sai ya sauka ta daina ganinsa online. Murmushi tayi tana ji kamar ta tashi tayi rawa. Duk da dai baice ya haqura ba amma tunda zai zo sai ta ke ganin kamar komai ma ya wuce. Da wannan tunanin tayi ta jiran lokacin shan ruwa yayi. *** Ba’a ga wata ba shiyasa za’a tashi da azumi washe gari. Salmah da Ummah na shan koko Abba ya shigo. “Hassana!” Ya kwala mata kira tun daga waje. Sai da ta kalli Salmah su ka danyi dariya kafin ta tashi da saurin ta. “Gani Abba. Sannu da zuwa.” STORY CONTINUES BELOW “Wannan fah?” “Sirikinka ne ya kawo dazu.” “Duk wannan din?” “Eh fah, aikowa ma yayi saboda aiki ya masa yawa.” Jijina kai Abba yayi kafin ya fita daga gidan saboda ya kira shi yaji. Shi baya son irin wannan, baya son mutum ya daurawa kansa dawainiya mai yawa kamar haka. Shiyasa ya kira shi amma daga yanda Sheikh din yayi magana, Abban yaji ba zai iya mayar masa ba. Hakan yasa yayi masa godiya a sakayance sannan ya sanya mishi albarka. Ba a jima da shan ruwa ba yazo. Wannan karan cikin gida ya shigo saboda ya tarar da Abba a waje kuma Abban yace masa ya shiga daga ciki. Bayan sun gaisa da sauran mutanen gidan ne aka fita aka basu wuri a falon Abban. “Ina wuni. Hope ka sha ruwa lafiya?” Salmah ta fada. “Lafiya qalau alhamdulillah.” Ya bata amsa yana kallon ta har cikin idonta, kallon da yake mata sai da yasa ta jin tsoro. Kar dai bai haqura ba. “Masha Allah. Allah ya bada lada.” “Ameen.” Duk su biyun shiru sukayi. Ba wanda yayi magana har sakanni hamsin suka shude. Gyaran murya sheikh yayi sannan ya kalli Salmah. “Haqiqa labarin ki ya taba min zuciya, a lokacin ban san mai zai iya fitowa daga baki na ba shiyasa na kashe wayar. Sai yanzu na tabbatar ina cikin hankali na shiyasa nazo. Alhamdulillah. Duk abunda ya faru da dan Adam yana cikin littafinsa ne. Naji duk abunda kika ce kuma kamar yanda na taba gaya miki, baya da gaba basu haduwa waje daya. Har in dai bawa yayi laifi kuma yasan ya nemi gafarar ubangiji bayan aikata laifin, toh lallai yana da sa’a saboda da yawa daga cikin mutane basa neman gafara bayan sun aikata laifi. A yau ina so ki bude kunnenki kiji nasihar da zan miki. Na farko zan fara da kan mahaifiyarki. Lallai ita mutum ce kuma kowa yasan mutum ajizi ne. Baki san dalilin da yasa ta ke miki abunda take miki ba. Nasan zai yi wahala ace baki riqe ta a rai ba. Selmah, so nake ki cireta a ranki. Ya’ani, ki yafe mata.” Numfashi Salmah ta ajiye bata ce komai ba. “Ba abu bane mai sauqi amma ki saka a ranki na cewa zaki yafe mata din, sai ki ga komai yazo da sauqi. Domin kuwa mahaifiya ba abun wasa bace ko da kuwa mai tayi miki. Kina ji ai koh?” “Unm.” “Masha Allah, Allah ya miki albarka.” “Ameen.” “Kice wa fika barakallah. Nima Allah ya min albarka mana.” Ya tabe baki cikin shagwaba. “Hmm,” sannan tayi dariya. “Wa fika barakallah.” “Ameen Selmah.” “Na biyu shine, bani da wani ikon yanke miki hukuncin cewa kina cikin fushin Allah akan abunda ya faru, ki dage da istighfari da kuma taubatan nasuha da sakawa a ranki ba zaki sake aikata abun da kikayi ba, domin Allah yana son masu tuba. Aljanna da wuta duk masu laifi na shiganta. Sai dai ita aljanna masu laifin da suke tuba ne, suka gyara ayyukan su, suke neman afuwa da rahamar Allah, suke adduar samun gafara da dacewa da aljannah, suke jajircewa a ibadah ne suke shigarta. Masu shiga wuta kuma sune masu laifi wanda basa neman afuwa, basa damuwa da nunawa mutane cewa su masu laifin ne, ba su kuma damu ba, ba su tuba ba har su mutu, sune suke shiga wuta.” Sai da yayi shiru ya kalle ta yaga hawayen da suke zuba a idonta sannan yaji tausayinta ya lullube shi. “Idan kika yi hakan, toh kinyi kyan kai. Wannan labarin ya saka dole na sake fadakarwa da nunawa matasa illar abunda suke aikawatawa din. Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yace da ka taba matar da ba taka ba, gara a buga maka kusa a tsakiyar kai. Taba hannu kenan ma balle a kai ga zina wadda take cikin manyan laifuka a musulunci. Da yawa mun shagalta komai in anyi magana mu ce wayewace ko zamani ne ya kawo hakan. Allah ya sa mu dace amin.” STORY CONTINUES BELOW “Da wannan nake cewa Allah ya yafe mana gaba daya. Kuma ki sani, har yanzu Sheikh yana tafin hannunki sai yanda kika yi dashi. Naki ne, duk.” Salmah dagowa tayi ta kalle shi. Shima kallonta yayi sannan yayi murmushi har sai da ta dauke kai. Kwana biyun da ya dauka ba haka kawai yayi su ba. Ya dade yana tunani. A ganinsa gujewa Salmah ba shi bane mafita, da yawa mutane ma maza ko mata in suka tsinci kansu a hali irin nata, sai mutane su guje su. Wasun su wanda zasuyi magana da shawara dashi suke nema, wasu kulawa suke buqata kafin a hankali su daina. All they need is for someone to tell them everything will be fine and they could scale through their situation. Ba abu bane mai sauqi, amma zai so ace mutane su fahimci cewa kyara da tsangwama basa gyara mutum. Shiyasa ya zabi ya cigaba da rayuwa da Salmah, ya gina ta a kan hanya mai kyau. Wataqila hakan ya zama silar samun babban rabo a wajen Allah. Sannan in ya rabu da ita bai san mai zai faru ba. Bai san wace irin mace zai samu ba kuma. Shiyasa ya dage da salloli da addua da neman zabin Allah a yan kwanakin. Kuma sai yaji kawai son Salmah na qaruwa a zuciyar sa shiyasa ya yanke shawarar zuwa wajenta. “Um, ina take ne? Wadda take gaishe ni dazu?” Ya fada cikin raha. “Wa?” “Wadda kika turo min a waya mana. Wata yar gayu, ta sha jam baki.” Salmah dai bata ce komai ba. “Ko Selmah na ce? Naga dai Selmah na kullum hijabi take saka min. Yanzu ma haka.” “Saahib!” Ta fada tana katse shi. “Kul! Wannan sunan da yan matan nan ta kira ni dashi ne. Kar ki sake mata amfani da lafazi.” “Ka bari mana.” Salmah ta fada a shagwabe. “Toh toh shikenan. In dai kece ita sai ki maimaita min abunda ta rubuto min naji. Saboda nasan ke baki iya ba.” Kallonsa tayi. Shi kuma sai ya gyada mata kai. Yasan halinta, ba sai ya matsa da yawa ba zata fada. “Cewa nayi fa, I was missing my Saahib. Na ban ce kai ba ai. Saahibina nace ba Sheikh ba.” “Um… Interesting. Bari mu gani.” Sai ya ciro wayarsa daga aljihunsa ya duba. “Toh shikenan tunda dai bani kike nufi ba.” Tana gani kalar yanayin fuskarsa ya chanja. “Anyi hutun school ko?” “Unm. Jarabawa zamu fara da zaran mun koma nan da sati biyu.” “Toh masha Allah. Sai mu tare nan da sati daya kenan?” Da sauri ta kalle shi. Mai yake nufi da hakan? “Na’am?” “Sai a kawo ki nan da sati daya. Akwai wani shiri da zaki yi ne? Har na fadawa Abba fa.” “A’a. Gani nayi ai baka tambayi shawarata ba kawai ka yanke hukunci ka gaya min. Bayan gashi ni Saahib nake ce maka saboda abokin rayuwa na dauke ka.” “Allah ya baki haquri Hajiya ta.” “Ai gaskiya nake fada maka.” Nan Sheikh ya girgiza kan shi. “Za’a duba a gani.” Abunda ya fada kenan yana sakawa a ranshi zai gyara. Da alama wannan karan za’a samu chanji saboda dukkan alamu sun nuna masa cewa Salmah ba irin zaman da suka yi Jamilah zata yi dashi ba. Fatan sa dai Allah ya hada kansu ya kade fitina. “Yauwa yafi.” “Allah ya miki albarka. Muje ki rakani na tafi koh?” “Baka ci komai ba ni na dafa fah.” “In ana so naci a min packaging.” “An gama.” Salmah ta miqe ta fita domin taje ta masa fakejin din. Shi kuma sai yayi sallama da su Abba da Ummah ya fito. Sanda ta dawo bata ce komai ba suka je motar ya bude mata ta ajiye mishi. Yana tsaye a gefen fasinja yana jira ta gama jerawa sannan ya rufe. Da ya rufe sai ya kamo hannun ta suka zagaya daya bangaren direba. “Hoton yayi kyau sosai.” Ya fada, yan yatsunta cikin nashi. “Haka kawai mutum yana azumi kika turo mishi.” Ita dai bata ce komai ba saboda bata ma gane mai yake nufi ba. “Toh ai ba komai.” “Koh?” Ya tambaya yana dariya. “Eh mana.” “Sannunki kinji. Lallai ma yarinyar nan.” Turo baki tayi wai ita yace mata yarinya. “Da nine ke da na daina turo baki.” “Ai ni nice ba kai ba tunda gashi nan ma kawai kaje ka yanke shawara ba tare da ka tambaye ni ba. Kuma daman sanda aka yi daurin auren ai ko gaya min baka yi ba. Ni ka tafi ma bana son ganinka.” Shi dai Sheikh tsayawa yayi yana kallon ikon Allah. Kullum mamaki take bashi. “Kince na tafi kuma hannunki riqe da nawa har yanzu.” Kallon hannun tayi amma duk da haka bata saki ba. Ba zata iya kwatanta mai take ji ba. “Sai dai ka tafi babu shi, ni ina son hannun.” Sheikh murmushi yayi. “Na yanke shi kenan? Ba zan rasa abun yankewa ba a cikin motar. Bari mu duba.” “A’a bari mana,” sai ta sakin masa hannu ba a son ranta ba. “Ki cigaba da riqe abunki mana.” “A’a sai da safe.” Bata da niyyar dawowa shiyasa ma bai bita. Dariya kawai yayi sannan ya tafi. Akwai aiki a gabansa kuma zai fara shi ne daga sanda suka fara zaman tare. Zai qara mata nasihohi masu shiga jiki. Zai fadakar da ita akan abubuwa da dama. Duk babu sauqi, amma da yardar Allah zai yi komai ba tare da gajiyawa ba. Ita kuwa Salmah har yanzu tana jin kamar hannun sa yana cikin tafinta. Allah sarki Sheikh dinta, tayi zaton ya barta ashe yana nan daram. Ko dan wannan, zata yi iya qoqarinta taga ba ta bashi kunya ba. Zata dage wannan karan. Zata yi duk abunda zai ce in sha Allah duk dai ba a kan komai ne ta fiya yin shiru ba. Allah ya taimake su ya basu zaman lafiya. Da fara’a ta shiga gidan, wata murya taji daga falon Ummah hakan yasa tayi saurin karasawa. Tana bude labule taga fuskar da bata taba tsammanin gani ba. A take wani yanayi na daban ya ziyarce ta. “Uwale?” Ta tambaya tana so ta tabbatar ita din ta gani. **** “Salmah?” Uwalen ta fadi, tana miqewa daga inda take zaune. Mamaki gaba daya ya hana ta qarasa da komai. Bata cika da mamaki ba sai da taji hawaye na zubowa daga idonta ba tare da ta san dalilin ba. Ko da wasa bata taba tunanin zata ga Salmah ba cikin sauqi. Bata taba zaton kewar Salmah da tayi ya kai hakan ba. “Ke ce a nan?” Salmah ta tambaya bayan ta rasa mai zata ce. Ita ma kallonta takeyi, tana jin zuciyar ta a bushe. Ko na minti daya bata ji wani abu da ya darsu a zuciyar ta. She just felt numb, like nothing was moving in her heart. Da kyar dai ta kalli Ummah wadda take gefe tana kallonsu. Kallon da Ummah ta mayar mata ne ya saka ta gane ba Ummahn bace ta kira Uwale. Qaramin murmushi Salmah tayi. “Ummah yace a gaishe ki.” Hakan kawai tace sannan ta kalli Uwale, a wannan karan taji zuciyar ta ta yamutse waje daya. “Uwale albishirinki. Salmah ta fidda ki kunya. Zaki huta da bakin cikin da kike ji a dalilin Salmah. Domin kuwa Salmah tayi aure.” Tana kallo Uwalen ta hadiye wani abu. Tana kallon yanda gabadaya Uwalen ta ta rikide ta koma wata daban amma ko kadan hakan bai taba mata zuciya ba.+ A hankali Salmah ta qarasa inda Uwalen take. Ta dafa kafadarta sannan tayi murmushi mai sauti wanda bashi da alaqa da jin dadi. “Mabrook. Ki zuba ruwa a qasa ki sha Uwale.” Salmah tana ji Ummah ta taba ta ta baya amma duk da haka bata fasa fadan abun da tayi niyya ba. Sake kallon mahaifiyarta ta tayi. “Amma kash!” Sai ta dafe kanta. “Na samu farincikin da ba kya son gani na dashi. A kan wannan kam sai dai nace ki dau wuka ki…” Bata qarasa ba taji saukar duka a bayan ta. Tayi tsammanin hakan daga wajen Ummah. A yanzu kam Uwale ce tayi magana. “Kyaleta Hassanah ta zage ni iya son ranta tunda bata da mutunci, wallahi idan kika bari…” Daga nan Salmah ta fice bata qarasa jin mai zata ce din ba. Sanda ta shiga dakinta, rufe kofar tayi sannan ta fara kuka. Tace ba zata sake kukan ba akan wannan dalilin amma gashi tana yi. A hakan tayi ta kukan kamar ranta zai fita. Kukan dukkan kuncin da ya sameta a baya. Kukan yanda take kwadayin soyyayar mahaifiya. Kukan maganganun da ta fadawa Uwale. Kukan cewa har yanzun tana son komai ya zamto daidai tsakaninta da Uwale. **** Daga Salmah zuwa Karime babu wanda ya runtsa cikin dare. Haka suka yi ta juye juye har sanda suka tashi yin sahur. Salmah zuwa da ta duba taga ta bar robar ruwa a dakin, sai kawai tasha. Saboda bata so ta fita tsakar gida ta hadu da kowa. Har safiya bata fita ba, har yamma tana daki sai dai Ummah tayi haquri kam yau. Uwalen ta taya ta aiki amma ita ba zata fito su sake haduwa ba. Ko da taji bugu a kofar ma, bata yi yunkurin dubawa ba, kawai luf tayi akan gado kamar barci take. Sai da taji mai bugun ya bar bakin kofar sannan tayi numfashi a hankali. “Kinsan surukin naki kuwa?” Ummah ta tambayi Uwalen. “Taya zan sani kuwa Hassana? Bayan an hada baki da ke an munafurce ni. Ko da yake ma babu wanda ya damu da abunda nake ji nikam.” Uwalen ta fada, kana jin dacin muryarta daga yanda tayi maganar. Ummah kuwa ta san halin Uwalen shiyasa bata qara cewa komai ba. Qarar bugun kosai kadai yake tashi a tsakar gidan, inda Karime take kwance a kan tabarma. “Nikam ban sani ba. Ban sani ba, ko me nayi oho!” Ummah tana jin hakan tasan zancen zuci ne ya fito waje. Amma duk da haka zai ta dan yi murmushi. “Baki san me ba Karime?” “Ban san me yasa bani da sa’a ba. Kowa bai damu da abun da nake ji ba. Jibi yar da na haifa ma ba ta bar ni haka nan ba. “Shiru dai Ummah tayi domin zancen ba kadan bane. Ba kuma hurumin yin maganar ta bane, magana ce Karime ta yi a dunqule, wadda da kaji kasan akwai abubuwa da dama a binne a zuciyar ta. Shiyasa kawai ta danyi shiru sannan tace, “Duk sanda kika ji damuwa ki yawaita ambaton Allah Karime.” Yanda Karimen ta kalle ta ne kamar qaramar yarinya ya saka kawai bata qara cewa komai ba. Cikinsu ba wanda ya sake magana dai har aka sha ruwa. Bayan Isha’i ne Abba ya ce yana neman Ummah. Tana jin hakan ta san me yake tunani a ransa. Duk da hakan dai bata ce komai ba har ta samu waje ta zauna. “Wato kiran ta kika yi dai din ko?” Da taji bai qara da komai ba ta san amsa yake so. Yawanci in yana fada baya so a dinga saka masa baki sai ya gama tsaf. Yanzun ma ta zata hakan ne, saboda ita tun da ta gama gane halinsa komai nata yayi sauki. Da ne sanda su Muhammad suna yara kusan kullum sai tayi kukan bakin ciki. Amma yanzu sai hamdala, dama dai haquri a inda ya dace, riba ce dashi mai yawa. Da wahala haqurin, Ummah zata gaya wa ko wacece hakan amma dai in aka daure komai me wucewa ne. “Kamar walkiya na ganta a gidan nan. Nayi zaton ma ko kunyi waya ne.” Ta bashi amsa kai tsaye. Sai da ya jinjina kai sannan yace ta kira masa Karime. Nan ya gaya mata duk abunda zai gaya mata din, ya fada mata auren Salmahn da akayi sannan da kuma dalilinsa nayin haka. A duniya, Karime bata da kamar sa sannan kuma tana tsoransa. Shiyasa duk abunda yace din kawai tayi na’am dashi duk da kuwa ranta baiyi dadi ba sam. ****** Qamshin abinci da muryoyin mata kadai ke tashi. Komai lokaci ne, domin kuwa yau ne ake shirin kai Salmah gidan aurenta a matsayin matar Sheikh. Zaune take da qawayenta duk sun gewaye ta suna ta mamakin boye musu da tayi akan maganar bikin. Duk a tunanin su a ranar ne aka daura aure. An yi Salmah duk wata nasiha da za’a yi sai aka bar ta da Uwale. “Uwale ki yafe min duk abunda nayi miki.” Ta fada tana wasa da yatsun ta. “Uwale wallahi lokacin rai na ne a bace.” Sai da Karimen ta bata fuska sannan ta juya. “Allah bada zaman lafiya.” Sai da jikin Salmah yayi sanyi kafin ta amsa da amiin. Nan dai Uwale tace ita zata kaita har gidan. Ita wasu qawaye ba zasu kai yar ta ba. Su Ummah ne suka fara gaya mata cewa a matsayin ta na uwar amaryar bai kamata taje ba a al’adance. Budar bakinta sai tace, “Ai kowa yasan Hassana ce take kamar uwa a wajen Salmah. A bar ni a matsayin kanwar uwarta kawai. Ni dai ku bar ni.” “Ki bari in an kwana biyu kya je kiga gidan.” A nan dai wasu yan uwan Abba da baban Salmahn suka yi ta mita akan cewa bata da kaara bare kunya. Ba ta ji duk abunda sukace ba, ta saka Salmah a gaba suka shiga motar Abban aka tafi gidan. Da Abba, da wasu mata biyu sai Muhammad sai ita Karimen. Muhammad ne yake jan motar dama yaje ya gano gidan saboda su san irin gado da kujerar da zasu saka amma sai suka tarar Sheikh yayi komai. Da suka yi magana sai ce musu yayi su manta da wata al’ada. Haqqinsa ne ya qawata gidan dai zai saka matarsa. Gida kam yayi kyau, Masha Allah. Ya sha kayan ado na zamani, kujerun kirar yan turkiya ne. Gadon ma haka. Ga kayen kyalekyale birjik. Toh Uwale sai labari taji shiyasa aka yi tunanin ko da idonta take son gani. Ko da suka je, Yan uwan Sheikh mata hudu da suke aure a garuruwa daban daban suna can tare da mahaifiyar Sheikh din. Ita dai Uwale kada kai take tunda suka shiga tana mamakin wannan wani irin tsarin aure ne wanda sam bai bi al’ada ba. Kwalliyar gidan ta burge ta matuqa amma bata san ko daga ina wani abu yazo ya tsaya mata a wuya ba. Salmah dai na tsakiyar matan kanta a rufe. Bayan an zazzauna ne aka ce bari a kira mahaifiyar Sheikh. Nan dai Salmah taji kamar tayi tsuntsu. Bata san ya zata yi ba. Sanda Hajiya Hauwa’u, wato mahaifiyar Sheikh ta fito, gaban ta sai da ya fadi saboda tana gano ta ta kasan mayafi. Hankalin ta bai gama tashi ba sai da taji Uwale tayi magana a razane. “Kulu! Me kike yi a nan?” Salmah daga mayafinta tayi tana kallon Hajiya Hauwa’u wadda mahaifiyar ta ta kira da Kulu. Sun san juna ne? Me ye hadinsu? Wannan shine tambayoyin da suka fara zuwa kan Salmah. *** “Reemimi!” Ita ma ta fada. Juyawan da sukayi suka ga mutane a zaune ya saka duk suka fuske kuma kamar basu san juna ba. Salmah tana ganin yanda duk yanayin fuskokinsu ya chanja zuwa wani irin yanayi. Sauke mayafinta tayi tana tunanin abunda ya wakana. Anyi duk wani abunda za’a yi aka kai Salmah sashenta. Abunda Salmah ta fahimta shine, gida daya zasu zauna da mahaifiyar sheikh. Bai gaya mata ba. Haka dai ta zauna jiransa har ta tashi tayi sallar magariba bayan an watse kafin shi ma din ya shigo daga baya ya mata bangajiya duk da bawani gajiya tayi ba sannan ya fita. Ajiyar zuciya ta sauke sannan tayi wanka ta kwanta, abunda ya faru dazu yana mata yawo a kai har barci ya dauke ta.+ **** Ko da ta tashi da safe, bangaren nata tsit yake babu alamar kowa. Hakan yasa tayi sauri ta yi wanka sannan ta nufi bangaren Hajiyar Sheikh domin ta gaishe ta. Ta dade a tsaye tana tunanin yanda Hajiyar zata tarbeta saboda irin kallon da taga sun musanya tsakanin Hajiyar da Uwale ya kada ta sosai. Kallon kiyayya suka yiwa junansu kafin su waske. A hankali ta kwankwasa kofar kafin ta soma wasa da jelar mayafinta tana jira a bude. “A’a amaryarmu har kin tashi?” Taji an fada, daga kanta tayi. Suka hada ido da daya a cikin kanwar sheikh din wadda ba zata wani girmi Salmah da yawa ba. In ma yayi yawa shekara uku. Kallon ta ta tsaya yi kamar ta santa a wani wajen. “Salam alaikum. Har na tashi fa nace bari na zo mu gaisa da kyau.” Itama dayar kallon Salmah tayi har sai da girarta ta kusa hadewa da goshinta. Gyaran murya Salmah tayi sannan ta bar kallonta. “Bismillah.” Tare suka shiga cikin falon. Qaton falo ne, da kujeru irin royal chairs dinnan. Bangon falon yasha takardun kwalliya na bango wato walfefa. Ga wani qaton kafet mai laushin gaske a malale a falon. Gefe guda kuma Salmah ta hango Samiru da Kumbo. Ta na gani ta san Hajiya ce tace a taho mata da abunta nan din. “Matar Sheikh ni sunana Hadiza. Ina aure a Yola ne.” Wadda suka shigo tare ta fada mata. “Masha Allah. Dafatan kin zo lafiya qalau.” “Lafiya qalau alhamdulillah. Kinsan da kyar fa Abban Basma ya bar ni. Da cewa yayi ba zan zo ba fa. Nikam na qi fir nayi ta magiya. Auren babban wa fa?” Salmah yar dariya tayi dai sannan ta kada kanta. “Ya kyauta dai da ya bar ki kika zo din.” “Ke dai barshi da rigimarsa. Sai yafi shekara ban zo ba fa. Yanzu kuwa ban komawa sai nayi sati uku tunda na samu na fito daga gidan nan.” Ta fada tana fari da ido, ita a lallai ta samu yanci. Salmah dai ba haduwa ta taba yi da ita ba balle ta bude baki tayi ta surutu. Suna zaune sai ga wata ma ta fito. Itama Salmah ta ganta jiyan. Ranta a bace ta fito kamar zata yi duka. Salmah na lura da hakan tayi saurin rissinawa. “Ina kwana…” Ta gaisheta a takaice. Bata amsa ba ta samu kujera ta kame. Hadiza ce ta dan matso kusa da Salmah sannan tace “wannan ce Adda Gaaji. Kinsan bayan Anty Jamilah ita ma yaya ya taba aurenta amma basu wani yi zaman tare ba suka rabu. Anty Jamilah ce kadai ta iya zama da shi har rasuwar ta. Ita kam Adda duk da tayi aure naga alama kishi take dake. Ni dai ina miki kallo daya naji ina son ki shiyasa ma nake gaya miki wannan.” Salmah bata iya cewa komai ba illa gumin da ta fara yi kamar me. Nan taji cikinta ya kulle. Dama har mata biyu yayi? Ai bai gaya mata ba? Sannan wani hali ne Jamilah ta jure? Me ta kawo kanta ciki ne? Zata iya kuwa? Ko da yake ta san zama matar sheikh ba lallai ya zo da sauqi ba. “Sannu.” Taji Adda Gaajin ta fadi. “Yauwa, ya yara. Ya gajiyar ku?” Salmah ta tambaya. Sai da tayi shiru, ta kunna talabijin sannan ta kalli Salmah. “Lafiya.” Daga nan bata kara cewa komai ba. Hadiza ce ta kama hannun Salmah ta shiga da ita wani daki inda Salmahn take tsammanin nan ne dakin Hajiyar. “Hajiyar mu ta na son Anty Jamilah, ki yi kokari kema ta so ki.” Daga nan sai ta zame ta bar Salmahn a bakin kofar dakin. Sallama Salmah tayi tana jiran a amsa. Kofar bandaki taji an bude sannan aka amsa mata. Da bismillah ta tashiga zuciyarta na kara gudu yayinda take tuno jiya. STORY CONTINUES BELOW “Maraba amarya!” Saukar da ganinta tayi zuwa qasa har ta zauna a qasa daidai gefen gado. “Ina kwana Hajiya, dafatan an tashi lafiya?” “Lafiya qalau, miyetti Allah. Ya zaki zauna a kasa? Dan Allah ga dadduma nan ki zauna.” Salmah dai bata motsa ba sai murmushi tayi. “Bari nayi walaha, ki jira ni.” Haka tayi ta zama har Hajiyar ta idar da sallahr. “Yauwa akwai abunda nake so na dan gaya miki duk da kuwa na san a gida sun miki. Kinga shi auren nan ba abun wasa bane. Duk da ba baqon abu bane a wajen maigidan naki, ke yakamata ki san wasu abubuwan. Na san a gaya miki kalmar haquri tafi sau a kirga amma ni zan fada miki wani abu.” Gyada kai Salmahn tayi. “Ba zan bari wata mace ta sake cutuwa ba a gaba na bayan ina da ikon hana wa. Saboda haka, kiyi haqurin dai, ki kawar da kai akan abubuwa da dama amma idan abu yafi karfinki toh kar ki yi qasa a gwiwa. Ki garzayo wajena domin ni mai share miki hawaye ce. Kinji? Ban ce kizo a kan abu kadan ba, a’a sai abu yafi qarfin ki. Kar ki kashe kanki da ciwon zuciya ko wani abun. Kar kiyi zurfin cikin da zai cuce ki. Ki yi masa biyyaya daidai gwargwadon iyarki amma ban amince ba sam da ki zauna kiyi gum in ya cuce ki. Kin ji? Kar ki ji komai wai dan ni na haife shi. Allah sarki ita Jamilahr da tayi haqurin a inda bai dace ba, ba ga yanda haqurin ya kai ta kabarinta ba.” Salmah dai hawaye take amma da taji an ambaci kabari sai da hawayen nata ya daskare. Me? Me ake boye mata ne hakan? Anya kuwa zata iya? “Nagode Allah saka da alkahiri Hajiya. Nagode. Kuma in sha Allah ba zamu baki kunya ba.” Ta fada da kyar, tana jin kanta ya mata nauyi da yawa. To shi haka ake yi? Ta kwashe duk wani sirrin rayuwarta ta fada masa amma shi bai bari ta san komai ba? Ko da yake laifinta ne da ta fada masa har abubuwan da yakamata tayi shiru. Ai shikenan. Daga nan Hajiya ta dauko wata yar jaka ta bawa Salmahn kyauta. Sannan Salmah tayi godiya ta tafi. Tana zuwa bangarenta aka kawo mata abinci. Nan ta zauna ta tuttura tana jin babu dadi ranta. Akwai aiki a gaban ta da dukkan alamu. **** Salmah na hira da Hadiza Sheikh ya shigo. Daman hankalin ta gaba daya ba akan hirar yake ba. Ta tafi tunanin yanda zata samu kwanciyar hankali a cikin gidan ta. Ummah ta gaya mata ta saka a ranta cewa duk abunda zata yi domin Allah zata yi shi sai komai ya zo mata da sauqi. Ta fada mata zaman tare yafi qarfin wasa saboda haka watarana rai zai baci wata rana za a yi farin ciki. Amma tace mata ta yi iya kokarinta taga komai ya tafi daidai, ta bi mijinta tayi duk abunda yake so in dai bai sabawa addini ba. Sannan tayi haquri domin aljannarta take nema ta hanyar sa tunda Allah ya riga ya sanya shi a sama da ita. Haka dai Salmah tayi ajiyar zuciya. “Bari na gudu,” inji Hadizah. Kafin Salmah tace wani abu, ta tashi ta fice. Sheikh dai dariya yayi sannan ya nemi waje ya zauna. “Sannu da zuwa.” “Amarya amarya… Na dan fita exercise ne. Dafatan kin kwana lafiya?” Salmah dai bata ce komai ba. Gaba daya ji take kamar bata san shi. Kamar wani baqo ne shi. “Lafiya qalau. Ban dade da shigowa ba nima mun gaisa da Hajiya. Ta bani tsaraba,” “Ah lallai yar Hajiya. Har kun saba kenan.” “Unm.” “Masha Allah. Kawo min abinci na dan wallahi gudun nan da nayi kamar an cinye min kayan ciki.” Salmah ta kusa yin dariya saboda yanda yayi maganar kamar karamin yaro. Da alama dai baya wasa da abinci. Haka dai da wancen tunanin ta tashi ta hado masa sannan suka zauna a table suna ci tare duk da kuwa ta dan taba dazu. “So, jiya kin kwaso gajiya ko gani na ma ba kya son yi. How’s everything?” “Nifa ban ce haka ba.” Ta fadi. “Amsa min dai naji lafiyar amaryata tukunna.” “Komai alhamdulillah.” “Masha Allah. Ni ko oho ko?” Kallan sa tayi ta girgiza kanta. “Eh mana, ba ruwanki da lafiya nake ko akasin haka. Shikenan ai.” Salmah zata bude baki tayi magana kenan karar wayarta ya katsar da ita. Bata so dauka ba amma ganin Uwale ce ya saka ta dauka ta saka a sifika. Gaisawa suka fara yi faran faran sannan ta kalli Sheikh. Murmushi ya mata sannan ta mayar da wayar kunnenta dan taji abunda zata ce ita kadai. Dama ta saka a speaker ne saboda ta nuna masa yanzun abubuwa sun fara daidaita tsakaninsu. “Nace ba, wannan matar da nayi wa magana jiya ya take da shi malam din naki?” Salmah bata fuska tayi. “Wace mata? Kuma Uwale Sheikh ake cewa ba Malam ba fa.” Sheikh da yake gefe dariya yayi inda Salmah ta harare shi daga nesa kafin ta bar wajen ma gaba daya. “Nasan kinji ni sarai. Oho ke kika san wani Shehu. Matar Shehu naji ana ce miki ko me?” Maimakon bata rai sai ta fashe da dariya. Ita ba matar Shehu bace. “Sarai ma so kike na mance da zancen da na kira zan miki. Ki ban amsa.” “Maman Sheikh ce Uwale.” “Me? Kulun? Toh bari kiji maza maza ki tattara naki ya naki ki yiyo gida. Ba zan hada jini da ita ba na rantse da Allah.” “Uwale…” “Salmah kinji ni.” “Uwale…” Wannan karan hawaye har ya fara sauka kan kumatun ta. Ta dawo gida fa? Washegarin bikinta? Tabdi. “Sai ki zaba. Ko ni da na haife ki ko kuma su. Sannan gani nan zuwa gidan.” Salmah bata san sanda taji ta zauna akan gadonta ta fara kuka ba. Wannan wani irin abune? Ya Allah. **** Rike kanta tayi da hannuwanta biyu tana ji kamar ya rabe gida biyu. Yanzu ita shikenan haka rayuwarta zata kasance? Babu wani farinciki mai daurewa? Wani kukan ta fashe dashi. Gaskiya ita ta gaji. Gara kawai Uwalen ta zo ta warware mata komai, in ma ba ita ta haife ta ba gara ta sani akan ta cigaba da rayuwa a hakan. Da hakan ta miqe ta shiga bandaki ta wanke fuskarta sannan ta fito. Sheikh ta gani a dakin hakan yasa tayi saurin goge guntun hawayen da yake shirin zubowa fuskarta. Ba sai ta fada masa ba. In Uwalen tazo ya ji ko ma meye. Ganin yanayinta da kuma tsayawar da ta yi a waje daya ya saka ya tako har inda take. “Me ake mata?” Ya fadi yana riqo hannun ta. Tambayar da ya mata ya saka kukan ya fito. A hankali ya ja ta jikinsa ya rungume yayinda take kara kukanta. “Na gaji. Har cikin kashi na a gajiye yake. Just today… Komai sai a han..ka…” Bata qarasa ba ta cigaba. Tana jin hannunsa yana yawo a hannun ta alamun rarrashi. Abunda take ji a zuciyar ta bai hana ta jin yanda hannun nasa ke tafiya a bayan nata ba. “Tell me, menene?” Bata bashi amsar da yayi tsammani ba sai dai shirun da tayi ta riqe shi tsam kamar zai gudun mata. Babu inda zata je gaskiya. Bata so ace suna ta samun sabani tsakaninta da Uwalen amma abubuwan sunyi mata yawa. Tunda ta bude ido a duniya bata taba yin wata guda cif ba tare da wani abu ya saka ta kuka ba. Sai gashi ta samu Sheikh mai qarfafa mata gwiwa a ko yaushe. Yau daya kuma, kwana daya tal da yin bikinsu ace ta dawo. Ita kam wannan umarni yayi mata yawa.+ Bata san iya dadewan da tayi a jikinsa ba, a tsaye har sai da suka ji alamar ana magana ta waje. A hankali ta zame zata fita ta gani. “Zauna a nan bari na dubo.” Ba musu ta gyada kanta dan dama ba son fita take yi ba. Bata son ganin fuskar Uwale a yanzun. Ta dan jima a zaune Sheikh bai dawo ba. Amma jin hayaniya da tayi ta gefen windon dakinta ne ya tayar mata da hankali. A nan sashen Hajiyar Sheikh yake. Miqewa tayi ta saka hijab, tana bude kofar ta ganshi a tsaye. “Bai kamata ki fito ba yanzu. Ki zauna har sai na ce miki ki fito kinji?” Jiki babu kwari ta gyada masa kai. Hannunta ya sumbata sannan yace, “everything will be fine.” Haka kawai taji a ranta komai zaiyi sauqi din. Shiyasa tayi masa dan murmushi kadan kafin ya fice. Zama tayi a kan gado tana jingina jikinta da kan gadon. Tana jiyo muryar Uwalen ta a saman na kowa. Ita shikenan ko kunyar surukan nata bata ji ma. Wani lokacin takan rasa mai yasa Uwale take wasu abubuwan kamar ba babba ba. To amma mahaifiyar ta ce. Shiyasa take shiru sau da dama. Jin muryar Uwalen na kara kusanto ta ya saka ta miqe, ai kuwa nan take kofar dakinta ta bude. “Ki cewa mijinki ya sake ki. Dauko takarda da biro.” Ba musu Salmah ta dan duba ta dauko tana kallon Uwalen. Fisgo hannun ta Uwale tayi suka yi sashen Hajiyar Sheikh. Suna isa ta gansu duk hankalin su ya tashi. A hankali Salmah ta qarasa inda yake tana kallonsa. “Gashi. Zaka sake ni in har labarin da Uwale zata bayar yanzu ya gamsar da ni.” Bai karbi littafin ba. Kama hannunsa tayi sannan ta saka masa littafin a ciki. “Uwale ina son jin labarin da kike boyewa. Ina son jin labarin da ya sa ba kya so na. Ina son jin labarin rayuwarki kafin ki haife ni. Na miki alkwari in dai ya gamsar dani ba zan kara ko sakan daya a matsayin matar Sheikh ba.” “Salmah ranki zai yi mummunar baci a nan wajen. Zaki wuce mu tafi ko kuwa?” Sai da Salmah ta kalli Sheikh taga bai yi mata alama da kar tayi magana ba sannan ta yi numfashi. STORY CONTINUES BELOW “Uwale wannan shine sharadin. Kiyi haquri ki gaya min.” Hararar da ta watso wa Salmah bai hana Salmahn ci gaba da magana ba. Ba yau ta fara ganin harararba, amma har yau bata saba ba. “Uwale duk tsawon shekarun nan baki taba tunanin ya zan ji ba in kin zartar da hukunci. Kullum kan ki kike tunani. Duk wani abu kina yin sa ne domin farin cikinki. Ban sani ba ko tozarcin da kike min shi yake baki farinciki. Ban sani ba ko duk wahalar da nake sha a rayuwa shi yake dadada miki rai, ban sani ba ko so kike sai kin kai ni makura. Uwale duk shekarun nan ni kadai nake bawa kaina hakuri, ni kadai nake faduwa na tashi da kyar. A wannan gabar ina tsoran idan kika kayar dani ba zan sake iya tashi ba. Uwale ba zan yafe miki ba in kika bari hakan ta faru…” Babu wanda ya yana Salmah yin magana har I zuwa yanzu da ta fashe da kuka mai zafin gaske. Gaba dayan su sai da suka nemi wajen zama. Karime ma ta zauna sai rarraba idanu take yi. Salmah kuwa tana gefe sai da tayi mai isarta ba tare da kowa ya kusance ta ba sannan ta rarrafa inda Uwalen take. Riqo hannun ta tayi hawaye na zuba a idonta. “Na roqe ki da Allah Uwale ki gaya min komai. Na gaji, wallahi Uwale zan mutu. Mutuwa zanyi ki huta…” “Ba zaki mutu ba. Salmah am.” Hajiyar Sheikh ta taso ta riqe Salmahn dake durkushe tana kuka. “Ni zan baku labarin tunda ita Karimahn ba zata fadi komai ba. Zan gaya miki…” Kowa ya zuba mata ido kuwa suna jiran jin labarin. Sheikh kuwa gaba daya kan sa ya kulle yana mamakin abunda yake wakana kamar ba gaske ba. “Kulu ba ruwanki. Kin kwace min komai…” Duk kansu tsit suka yi. “Kowa ke yake gani.” “Karimah…” “Kar ki ce min komai Jiddah. ” Hajiyar Sheikh murmushi tayi. Ba zata iya tuna wani lokaci ne na qarshe da wani ya kira ta da Jiddah ba. Kulu shine sunan da bata so kuma tunda suka samu sabani shine sunan da ke shiga tsakaninta da Karimah. “Ku saurareni. Jiddah yayata tace.” Ba Salmah kadai ba, ba Sheikh kawai ba, qannensa gaba daya sai da suka firgita da wannan kalaman. “Uwa daya, uba daya.” Karime ta qara da hakan. Kamar wanda aka caka da allura haka suka zabura suna kallon iyayen nasu. Sannan ne Salmah ta kalle su. Sannan ne ta hango yanda kwayar idanunsa bata da wani bambanci. Da yanda jelar gashinsu da ta bullo ta kasan dan kwalinsu tayi kama da juna. Sannan ta lura da kamar fatarsu da take shigen iri daya. Hancin su ne ba iri daya ba sam. Hajiyar Sheikh tafi Uwalenta dogon hanci da kyau. Hajiyar Sheikh siririya ce sosai kamar yanda jikin Salmahn yake. “Kusancin da ke tsakanin mu ba zaku taba ganewa ba duk yanda zan muku bayani. Kullum muna tare da Addah Jiddah am. Tsiranmu bashi da yawa shiyasa kusan kan mu daya. Da kadan na fita kiba. Tare muke wasa, muci abinci tare, muyi karatu tare, muyi dariya muyi kuka tare. Toh da hakan dake tsakanin mu ban taba tunanin akwai abunda zai shiga tsakanin mu ba…” Tsayawa tayi ta kalli Hajiyar Sheikh wadda idonta yake kanta. Budar bakinta zata cigaba, Hajiyar Sheikh din ta karbe labarin. “Ban so hakan ba amma a ganin Karimah iyayen mu suna nuna bambanci a tsakanin mu. Sun fi so na saboda ita din akwai rashin ji. Duk yanda naso na nuna mata ba haka bane Karimah qin ganewa tayi fur. Wannan shine mafarin komai.” Sai ta kalli Karime, sannan ta sauke idonta. Shi kuwa Sheikh yana jin yanayin da Hajiyarsa tayi magana yasan cewa kaara take son yi irin nasu na Fulani. Daga ji an san iyayen nasu sun nuna fifici akanta. Ita kuma Uwalen Salmah ta dauki abun ta saka a rai. Hakan ya tuno masa da qissar annabi Yusuf inda yan uwansa suka shirya makirci har suka jefa shi a rijiya duk dan suna ganin mahaifin ya fi son sa. Ya sani cewa in dai mutum yana da yara, dole za’a samu wanda yafi ko wanne nagarta da nutsuwa. Sannan za’a samu wannan din da son yin duk abunda aka ce yayi. STORY CONTINUES BELOW Ita kuma zuciya bata da qashi sannan tana son mai kyautata mata. Nan da nan iyayen zasu ji zuciyarsu tafi karkata gare shi. Ba laifi bane amma kamata yayi ace iyayen sunyi kokarin boye wannan a zuciyarsu. Domin shi shaitan kadan yake jira ya shiga tsakanin mutane. Tun ba’a cigaba da labarin ba, Sheikh ya gano kan zaren. Saboda shi yaro in dai yana karami yanda aka rene shi haka yake tashi. Yanda aka tarbiyartar da shi hakan yake tashi. Gyarar murya Hajiyar Sheikh tayi sannan ta sake cewa, “ranar ne aka min sabon kaya ita ba ayi mata ba shikenan ta daina kula ni sosai. Da na sanarwa da mahaifiyar mu sai kawai ta basar da abun. Dama ita ba mai zama da yara bace ba kuma mai jin zancen yara bane. Duk abunda ya faru sai Karimah tace an fi so na. Haka dai muka cigaba, alaqar mu ta ja baya sosai har sanda aka daura mana aure. Bamu san su waye mazajen ba sai bayan an daura. Aka yi rashin sa’a kuwa Karimah ta fi son mijina. Nan ma qiyayya ta shiga tsakanin mu. Haka dai ko wacce ta tafi gidan mijinta. Ban sake haduwa da ita ba sai da ta haifi Ummu wadda ta rasu washegarin sunanta. Bayan sati daya na haifi Muhammad Salim wato Sheikh. Nan tayi ta kuka tana cewa ai saboda Allah ya fi so na ya sa na haifi namiji.” Hawaye ta goge sannan ta yi shiru. “Gaskiya ne ai. Da kin gaya min adduar da kike yi ai ba haka ba. Na haifi Ummu ta rasu, na haifi Khadijah ta rasu sai bayan shekaru masu yawa sannan na sake haihuwar, namijin da na haifa ya zauna har sai randa na haifi Salmah ya koma saboda ita Salmahn mai baqin jini ce. Bata tare da alkhairi saboda tunda na haife ta ai komai tabarbarewa yayi.” Salmah bata san sanda wani kuka ya kwace mata ba da ta hada ido da Uwale. “Yo kukan me zakiyi? Randa kika shiga wata daya Malam Bello yace zai qara aure. Yace shi banyi komai ba. Toh taya zai ce nayi abu bayan idonsa ya rufe namiji yake so a haifa? Nikam dama ai gani nan ne. Da ya auro Safara’un ba ta haifa masa namijin ba kuma ya rasu yace laifi nane? Ni kuwa nasan Salmah ce annobar. Qarshe dai ba saki na yayi ba? Duk dan saboda ni ba’a so na? Nikam ban ga laifi na anan ba. Duk ita ta jawo min gashi tana yanayin mahaifin nata.” Bayan tayi shiru wajen ne yayi shiru kamar makabarta. Gaba daya iskan falon ta jagule waje daya. Ko sautin kukan Salmah ba a ji. Shi kuwa Sheikh tunda ya hada hannuwansa biyu ya riqe kansa bai qara dagowa ba. Tunanin sa daya wai dan wannan Salmahn shi take wahala. Abu da bayani daya tak ya isa ya sauya shi amma haka aka dauki shekara har shekara ashirin da biyu ana abu daya. Wannan wani irin abu ne. Wai meye ya saka mutane suke da wannan akidar son da namiji a zuciyarsu. Su da Allah ya bawa kiwo? Burin na meye? Ba Allah bane mai bayar da abunda ya so din? “Uwale…” Ya furta yana kallonta. Ya sani ba ta yi wani karatu mai zurfi ba. Ko Hajiyarsa ma shi yake dora mata karatu kwanan nan da suka shirya. Yana da tabbacin cewa daina karatu sukayi bayan sunyi aure. Bayan shi karatu baya karewa. Yayinda aka yi aurenma shine lokacin da aka fi buqatar ilimin domin shi gidan aure tamkar makaranta ce, in akwai ilimi wadatacce sai zaman lafiya yafi dorewa. Kowa ya san haqqin da yake kansa. Gashi kuma yara zasu samu tarbiya ta kwarai har su zama abun alfahari wa iyayen da duniya baki daya. Toh ina amfanin mace ko namiji su ce tunda sunyi aure ai sun daina neman ilimi. Kuma ilimi duk biyun yake nufi, boko da arabi. Duk suna da muhimmancin gaske. Jijjiga kansa yayi yana duba yanda rayuwarsu take. Da Alhaji AbdulHamid bai dauki nauyin karatunsa ba da bai san mai zai faru ba. Amma alhamdulillah gashi nan da taimakon Allah yazo inda yake kuma duk yan uwansa mata hafizai ne a dalilin tilasta musu da yake yi. “Uwale gaskiya kam bil haqq ba’a kyauta miki ba. Na so ina nan ma na tsayawa mahaifiyata Karimah. Naji ba dadi da jin wannan labarin. Komai dai muqaddari ne daga Allah. In da Allah yana son bawa da alkhairi ya kan jarabce shi da abubuwa da dama. Duk wani abu da zai samu mutum an riga an rubuta shi babu wani abu wai shi in abu ya same ka kace ai laifin wane ne, wannan ba daidai bane. Selmah bata da wani laifi. Babu wani kwakkaran abu da za’a nuna ace laifinta ce. Kawai dai duk abunda ya faru wanda yayi daidai da haifuwarta haka Allah ya tsara. Al’amurra a wajen Allah jira suke kawai ace musu ‘kun’ sai su kasance. Irin wannan yardar na cewa wani ne yayi sanadiyar faruwar wani abu a rayuwarka na nuni da rashin yarda da qaddara da kuma da yarda da Allahn shi kanSa. Irin wannan abun ke kai mutum ya aikata shirka ba tare da ya sani ba. Allah yasa mu mutu a tafarkin musulunci, ameen. STORY CONTINUES BELOW Uwale baki da labarin nan ne? Ba ki ji hadisin ba? Wanda annabi sallal lahu alaihi wassalam yace duk macen da ta rasa yara biyu, zasu yi mata ceto? Kai kai kai amma Uwale ya akayi kika manta?” Salmah kuwa wani haushi yake taso mata. Mai yasa za’a a hukunta ta akan abunda bata da ikon chanja shi? Kuma ji Sheikh ma yanda yakewa Uwalen magana kamar wata yarinya. “Ina na sani? Gaya min.” “An rawaito hadisai masu yawa wanda suke nuna muhimmacin haqqin dake tsakanin iyaye da yaran su. Sannan kuma inaso in tuna mana cewa da mace da namiji Allah ne mai bayarwa. Allah madaukakin sarki yana cewa a suratul shura, aya ta arba’in da tara da ta hamsin: Lallai mulkin sammai da qassai na Allah ne. Ya kan hallici abunda yaso, ya kan bawa wanda yaso ‘ya’ya mata, ya kuma bawa wanda yaso ‘ya’ya maza. Ko kuma ya bayar da duk biyun macen da namiji, Kuma ya sanya wanda yaso baya haihuwa.” لله ملك السموات والارض يخلق ما يشاء يهب لمن يشاء انثا و يهب لمن يشاء الذكور(٤٩) اويزوجهم ذكرانا وانثا ويجعل من يشاء عقيم انه عليم قدير(٥٠). “Uwale, Allah ke azurtar da mutum yara. Jinsin ba shi bane abun dubawa. Abun dubawa shine yanda abunda aka haifa din zai girma ya zama wani abun. Ko kadan mazan basu fi matan daraja ba a wajen Allah. Idan kika ga mutum yana son ya samu namiji toh saboda wani amfanin duniya ne. Lallai wanda yafi karamci a wajen Allah shine wanda yafi tsoransa. Akwai lokacin da mata sahabbai suka taba kokantawa akan cewa kullum idan ayah zata sauka da jinsin maza ake ambata. Sai Allah ya saukar da ayar da ta musu bayanin cewa Allah ba zai yankewa wani mutum mace ko namiji wani aikin sa na alkhairi ba. Menene matsalar ne da ya kai ake tayar da jijiyar wuya? Mai ‘yaya mata ma yafi samun sauqin shiga aljannah ta dalilinsu. Suna da rahama sosai.” Kallon sa kowa yake yi kawai. “Akwai wani hadisin Nana Aisha radiyallahu anha. Tace, watarana wata mata tazo min da yaranta mata guda biyu tana neman sadaqa a wajena. Bata samu komai ba daga gare ni sai dabino guda daya, sai na bata. Ta karba ta raba shi biyu ta bawa yaran nata ba tare da ta ci ko gutsire ba. Sai ta tashi ta tafi. Da annabi sallallahu alaihi wassalam ya shiga sai na bashi labarin abunda ya faru. Sai yace, duk wanda yake dawainiyar tarbiyar yaransa mata kuma ya kasance mai tausaya musu ko kyautata musu, zasu kare shi daga wuta ranar qiyama. Bukhari da Muslim ne suka rawaito wannan hadisin. Uwale…” Kafin Sheikh ya cigaba da magana sai kawai ji suka yi da Hajiyarsa da Uwale sun fashe da kuka. Sheikh kuwa yasan halin mahaifiyar sa in ta fara kuka sai abunda hali yayi saboda haka cigaba yayi. “Afwan.” Ya fara cewa sannan suka danyi shiru. “Mahaifiyar Nana Maryam taso ta haifi namiji amma Allah ya azurta ta da mace. Kuma macen ya ta kasance? Ita ce macen da Allah ya tsarkake ta ya zabe ta sama da duk matan duniya.” “Misalai da yawa Uwale. Amma albishir daya shine ko yanzu kika yi nadama Allah mai karban tuban ki ne. Ko yanzu kika nemi gafarar Salmah, Selmahna mai yafe miki ce saboda tana son ki sosai duk da wannan abubuwan. Allah yasa mu dace amin.” Sai ya miqe ya zagaya inda Uwalen take zaune. Yana zama ya zagaya hannunsa a jikinta. “Haba meye kuma na kuka tsohuwa? af af, ashe surukata ce?” Duk yanda Uwale taso ta share shi sai da ta sa hannu ta kwade shi sannan ta yi murmushi. A lokacin ta kura masa ido taji wani son shi yana shiganta. Dama tun sanda aka haife shi take son shi amma gaba daya rashin sani, rudin shaidan da son zuciya ya rufe mata ido. Sheikh kuwa da yaga haka sai yayi wa yan uwansa alama da su tashi su fita. Shi kuma ya kama hannun Salmah suka fice su bawa iyayen nasu waje. Suna fita ya daga Salmah sama cak a hannun sa. Tana dukan hannunsa amma bai sauke ta ba har sai da suka shiga bangaren su. Yana sauke ta kuwa ta rungume shi ta fara kuka. Kukan da ba zata iya cewa takamaimai ga abunda ya kawo shi. Bata sani ba, ko kukan cewa komai ya zo karshe, ko kukan cewa Sheikh dan uwanta ne na jini, ko kuwa na samun sulhu. Shima rungume ta yayi kamar wadda zata bar shi. Karan hancinsa na taba wuyanta ya rada mata. “Babu inda zaki Selmah, babu inda zani. Ni dake tamkar taurari ne da basa barin sararin samaniya.” Sun dade a hakan kowa yayi shiru yana sauraron bugun zuciyar dan uwansa. “Sunan nawa ne, taken nawa, ni kadai, sheikh din nawa ne, Matar Sheikh.” Sai ta kara rike shi tana mantawa da duk wata kunyarsa da take ji dazu dazun nan. Amma sake tunawa yau washe garin aurensu yasaka tayi saurin sakinsa. “Menene kuma Matar Sheikh?” Girgiza kanta tayi, kanta a kasa. “Kunya ce?” Nan ma ta girgiza kanta. “Toh mene ne?” “Babu komai.” A hankali ta zame ta fice daga bangaren nasu zuwa na Hajiyar. A tunanin ta sun gama. Yanzu lokacin da zata gana da Uwale ne. Akwai maganganun da ta ke so su musanya. In sun hade sun zama tamkar ko wacce uwa da ya to alhamdulillah in kuma Uwalen bata amsa ba shikenan. Da bismillah ta shiga sashen tana gyara hijabinta. ***** “Salam alaikum.” Ko da tayi sallamar sai taji dama bata zo inda Uwalen take ba saboda ji tayi ta rasa mai zata ce idan ta zauna. Amma tunda tazo din, zata fara bawa Uwale haquri akan duk wani mayar mata magana da ta taba yi. Uwale tafi qarfin hakan a wajenta, bai dace ace ta daga murya sama da na mahaifiyarta ba. “Wa’alaikumus salam.” Uwalen ta amsa. A hankali Salmah ta qarasa ta zauna a gefe. Sun danyi shiru na mintuna kadan kafin Salmahn ta dan kalle ta. “Uwale ki yafe min duk abunda nayi miki ina sane ko bana sane. Yaya Abdul ya sha gaya min akan kar na yarda na daga murya ko na miki rashin kunya. A wasu lokutan nabi son zuciyata ba tare da na duba girman da kike dashi ba a wajena. Uwale ki yafe ni.” Tana wasa da yatsunta tana jiran amsa kuma daga wajen Uwalen. “Shikenan bakomai.” “Komai fa Uwale?” “Komai. Allah ya yafe mana.” Salmah bata yi tunanin komai zai zo da sauki haka ba. Bata san sanda tayi tsalle ta riqo Uwalen ba. Wannan ne karo na farko da ta taba riqe maihaifiyarta da fatan jin nutsuwa da dumin uwa. Gaskiya zata tambayi Sheikh sirrin. Ace rana daya lokaci guda ya sauya mata Uwale? Mai yasa tuntuni hakan bata faru ba?+ “Salmah am,” jin hakan ba qaramin faranta mata yayi ba. “Kiyi haquri.” Rufe idonta tayi. Allah ya saka mata son Uwale sosai a ranta. Ba zata iya riqe ta ba. “Uwale ban taba riqe ki a raina ba. Na haqura akan komai. Oh ya Allah.” Kan ka ce me, gaba dayan su hawaye suke yi. Amma cike yake da farinciki da annashuwa. Wani irin farinciki da ko wannen su zai iya cewa bai taba jin irinsa ba. Daban ne wannan. ***** Bayan sati biyu ne Salmah da Sheikh na zaune suna hira ta so ta tambaye shi a kan Jamilah amma sai ta rasa yadda zata yi. Da tayi wani tunanin kuma sai taga yin hakan bashi da wani amfanin da zai yi mata. Sati biyun da suka wuce a tsaitsaye suka yi su saboda su Salmah sun koma makaranta gashi jarabawa zasu fara. Cikin sati biyun ne aka kira Malam Bello mahaifin Salmah mai kama da ita sosai duk da akwai kamannin Uwale a tartare da ita. A lokacin Salmah ji tayi kamar mafarki takeyi saboda ko sau daya bata taba tunanin babanta yana da rai ba. Wai ashe yana Legas. Dadi bai gama cikata ba sai da aka nuna mata yan uwanta a waya. Daya shekararta Sha takwas wadda ake kira da Juwairiyya daya kuma sunan sa Mu’az. Abun ya mata dadi sosai wai ace itama tana da mahaifi yana da rai ga kuma yan uwa. Bata sani ba ashe Uwale ta san dasu. A zaman da aka yi dai da farko sam Uwalenta cewa tayi ba zata kuma zama da shi ba matukar yana da wata matar. Da kuma aka qara yi mata bayani sannan aka kara mata da cewa ya rage nata ta zabi zama hakanan ko ta koma gidan mijinta da suka yi shekara ashirin da biyu da rabuwa. Qarshe saboda akwai sauran rabo na zaman su, haka ta koma. Da yawan yan uwan Malam Bello haka sukayi ta juya abun. Duk ya musu bambarakwai. Malam Bello kuwa ko a jikinsa, yana sonta sosai daman. Ko a wancen lokacin babban abunda ya jawo rabuwarsu shine ganowa da yayi ta na shiga malamai ita a lallai sai ta hana shi qara aure. Da ya tuhume ta tace ai ba shirka tayi ba. Qarshe dai suka barke da musu da fadace fadace har yayi auren. Da sukayi fada kuma cikin fushi tace ai ita ce ta saka wa dan magani. Ya sani ba zata aikata hakan ba amma da yake a fushi yake haka ya sallame ta. Da kyar ya samu ta zauna idda kafin tayi tafiyarta kuma. Shima dai da laifuffukan da yayi, cikin su harda rashin adalci da ya mata kala kala. Ya nuna yafi son amaryarsa bayan har kasan ransa ya san Karimahnsa ma yana ji da ita. Sau uku yana haduwa da ita a gidan yayansa amma nuna masa tayi ai Salmahn ma kamar sauran yaran da ta haifa itama ta rasu. Yanzu dai duk sun watsar da duk wani abu da ya faru a baya kuma har an daura musu aure inda ya nemi gida dan daidai ya siya mata. Dama yana da niyyar dawowa Kano gaba daya saboda yanzu kasuwancin ya zauna alhamdulillah. STORY CONTINUES BELOW “Taya ya ka zama Sheikh?” Shine tambayar da ta fara masa. Shi kuwa jin haka Jamilah ce ta fado masa a rai. Yana tuna lokacin da yake fada mata cewa Sheikh din sunan da mutane suke kiransa ne. Lokacin kuwa lecturing yake a Islamic studies department. Daga baya ne bayan rasuwarta ya karanci Qur’an science a jami’atul Madinah. “Kamar wasa ya fara fa. Na karanci Islamic law. Toh uncle dina da yaji ana ce min Sheikh sai yace in na so da gaske zai tallafa min. Shine fa ya biya min na tafi jamiatul madina na karanci Quran science. Daga nan kuma nayi diploma a fiqh. Sanda na dawo shine nayi joining Hisbah anan Kano har Allah yasa na zama shugaban Hisbah din. Kinji dai yadda aka yi. Ba sauqi abun. Burin Jamilah taga na zama Sheikh din saboda shine buri na nima.” “Masha Allah. Allah ya kara daukaka.” “Unm unm ba daukakar jama’a nake nema ba Selmah. Allah ya qara mana imani dai. Kin san a wancen lokacin bani da wani buri da ya wuce na wataya duniya. Amma yanzu alhamdulillahil lazi hadani. Na shiryu. Shekara arba’in ba wasa ba.” Salmah zaro ido tayi tana kallonsa. “Arba’in?” “Kina mamaki? Ko kin zata Sheikh din yaro ne?” Sai yayi dariya ita kuwa Salmah mamaki ma ya hana ta yin dariyar. Wallahi in an barta ba zata taba cewa ya kai hakan ba. Sam baya nuna alamun hakan. “Kin san wani sirri? In kana son mace ta so ka sai ka sauko da shekarunta daidai nata. Nasan abunda kike tunani kenan, ina yin wasa da yawa ko?” “Ni ban ce ba.” “Hakane ma. Jamilah tana yawan cewa ita ba matar bahaushe bace. Matar Sheikh ce, saboda tana so na dauke ta tamkar abokiyata in da kuma ya dace na nuna cewa nine gaba a cikin gidana. Kinsan abunda ake cewa nadama? Nayi ta sosai. Amma tarihi ba zai maimaita kansa ba akan Selmah na.” Shiru Salmah tayi musamman da taji yanda muryar sa ta raunana daga yanda yake magana. Yanda take a kishingide haka ta matso dashi jikinta kamar yanda ya nuna mata yana son hakan a yan kwankin nan. Shi kuwa Sheikh da ya rufe idonsa hango Jamilah yake. Ya tuna bayan tayi bari abubuwa suka fara chanjawa amma sai ya zauna da ita ya bata haquri kuma ta haqura din. Hajiyarsa tayi fushi akan sakin Gaaji da yayi. Da kyar dai ta haqura. Bayan nan kuma ba zai manta ba duk sanda suka zauna hira da abokai ko wanne yana nunawa babu gwarzo kamarsa saboda yanda suke tafiyar da gidansu. Shima hakan yake basu labarin, a nan ne suke zuge shi suke gaya masa ba a wasa da mata. Shiyasa lokuta da dama Jamilah take ganin ya rikide mata. Bata sani ba, sharrin abokan sa ne da ya dauka kamar iyayensa. Duk abunda suka ce shi yake yi. Wannan ma yana cikin abubuwan da yake Allah wadai dasu. Mutum ya kan bi addinin abokinsa ne. Hausawa suka ce abokin barawo a barawo ne. Sau da dama sai mutum yaga babu wanda ya isa ya chanja shi. Ana mantawa shi chanji ba rana daya yake faruwa ba. Abune wanda yake daukar lokaci kuma kafin mutum ya ankara sai yaga ya chanja din. A wancen lokacin da wani zai ce masa ya chanja abokai domin suna tasiri sosai a rayuwarsa, da sai ya ji haushin mutumin. Yanzu kuwa shine wanda zai budi baki ya nuna wa mutane muhimmancin taka tsantsan da irin abokan da mutum yake hulda dasu. Ya tuna Jamilah ta sake samun ciki, a farko yace shi baya so saboda abokan sa sun zuga shi akan cewa yayi qanqanta ya zama uba. In kuwa ya zama tsufa zai yi. Haka ya hau ya zauna akan hakan. Ita kuwa sam taqi ya taba mata ciki. Haka nan har ta kai watan haihuwa ba wani shiga sabgarta yake ba. Ya fita waje, nakuda yazo mata. Sai can bayan ta wahala ya shiga gidan ya tarar da ita. Nan hankalinsa ya tashi ya tafi asibiti da ita. A nan ne ta haihu dan babu rai. Yaji babu dadi matuka amma da ya fadi hakan wa Jamilah sai tayi murmushi tace ai hakan yake so daman. Haka ya dake ya haqura. Ranar haka ya kwana bai yi barci ba. Past. Ranar uku da haihuwarta a asibiti, tana zaune a kan gado tana tunanin ranar za’a sallame ta tace masa, “dan Allah in na taba yi maka abu ka yafe min. Ina son ka sosai kuma ina son na kasance a aljanna tare da kai.” STORY CONTINUES BELOW Girgiza kan shi yayi. “Babu abunda kika min. Kullum ma nine mai laifin. Nagode.” Iya abunda yace kenan wanda ya faranta mata rai. Kullum burinta shine ta gan shi yana farun ciki. Ba don halinsa ba sai dan aljannar ta take nema ta hanyarsa. Allah ya sanya farincikin sa a tare da mijin da mace take aure. Ma’ana, sai har mijin ya kasance yana farin ciki da matarsa sannan Allah zai yi farinciki da ita. Haqqi ne wanda Allah ya dora a kanta kuma take son saukewa. Da yawa zasu ce Sheikh baya kyauta mata, ita bata damu da hakan ba. Don baya kyauta mata ba yana nufin ita ma ta daina ba. Haka take cigaba saboda Allah. “Yoghurt nake shaawar sha haka kawai.” Ta fada masa, tana kallonsa yayinda wani hawaye ya zubo mata. Da sauri ta goge. Qoqari kawai take tana danne zuciyar ta akan abunda ya faru a gefe guda kuma gaba daya jikinta yayi sanyi. Bata san me yake faruwa ba amma bata jin dadin jikinta. Wataqila hakan yana da nasaba da rashin dan da ta haifa. “Bari na fita na siyo miki.” Haka ya fita. Daidai fitarsa Hajiyarsa ta shigo. Sosai suka gaisa saboda sabo da sukayi tun wani lokaci da Jamilah taje har Danja ta duba Hajiyar. Daga baya yan gidansu suka zo dukkan su kamar yanda ta buqata. Tana zaune akan gado suna hira kamar babu abunda yake damunta. “Abba, dan Allah in akwai sauran fushi a zuciyarka sanadiya ta, ka yafe min. Ummah, please.” Sai ta fashe da kuka. Haka Abba ya rungumota yana jin tausayinta. Wataqila mutuwar dan ta ta taba mata zuciya sosai. “Na yafe miki fid dunya wal akhira. Allah ya miki albarka Jamilah.” Hakan Abban ya fadi lokacin da ya koma wajen zamansa. Ummahnta kuwa kallon cikin idonta tayi taga lallai wannan Jamilahr dake gabanta ta chanja. Matsawa kusa da ita tayi, “Allah ya baki ladan haqurin da kike. Ki daure komai me wucewa ne. Allah yasa mai ceto ne. Allah miki albarka.” “Ameen Ummahna.” Bayan nan ta kira Ya Fidy da yaya Nasir a waya suka ce mata zasu zo yau da yamma. Ilham ta tafi islamiyya saboda haka basu samu damar haduwa ba. A wannan lokacin tace tana jin barci. Littafinta ta dauko a qasan filo tayi rubutu a ciki. Wannan koren littafin. Ta kwanta barci, barcin da bata tashi ba kenan. Da ya dawo kasa yarda yayi, kamar zai zauce haka yaji. Dama ya gaya mata yayi appreciating efforts dinta. Dama ya gaya mata yana sonta sosai, dama ya gaya mata… Haka yayi ta jero su bayan bashi da damar yin ko daya daga cikinsu. Mutuwa haka take. Bata sallama, bata neman izini. Bata duba shekaru, bata barin wani dan wani. Ranar ya tabbatar da hakan. Normal ya fita ya bar Jamilah amma daga dawowarsa aka ce fa cika. Shiyasa ake so kullum mutum ya zama yana aikata mai kyau, yana neman yafiyar mutane. Bai san yaushe ne lokacinsa ba. Wataqila yanzu ne, wataqila anjima, wataqila gobe. Ko jibi ko gata. Ajalin musamma. Allah yaji qan Jamilahrsa, Allah yaji kan musulmi baki daya. Present. Da wannan ya dawo daga tunanin da yake yi sannan ya bude idonsa. “Me yasa ka aure ni bayan ka san ina da tabo da yawa?” Murmushi yayi. “Saboda kin cancanci na aure ki din.” Haka yace ma Salmah a fili. A ransa kuwa cewa yayi, saboda bani da tabbas din wa zan gamu da ita ko na rabu da ke. Ba wai ina kare ki ba ne, a’a laifi ne babba ace mace ko ma namijin suna shaye shaye. Ba dabi’a bace ta mutanen qwarai. Amma idan aka samu akasi ko kuma abun yazo da qaddara ba yanda za’a yi toh sai a duba a gani. Wani irin hali ne ya jefa mutum cikin wannan tagayyarar. Hakan yayi ya duba sannan yaga idan ya tsamo Salmah da ga cikin halin da take ciki ba qaramin abu bane. Bayan wannan kuma ita din ba tambadaddiya bace. Shiyasa ya danne zuciyar sa yayi hakan. Kuma yana sonta. Shi aiki saboda Allah riba ce dashi ba qarama ba. Ko mutum bai gani a duniya ba zai gani a lahira. Yanzu da ya rabu da Salmah haka nan ta fada wani mugun hannun fa? Da tuni yana nan cike da nadama musamman tunda ya gane tamkar qanwa take a wajen shi. Alhamdulillah. Hakan Sheikh yace a ransa saboda abubuwan da suka faru. “Naji dadin haduwa da kai, ka canja ni zuwa mutum daban.” “Unm unm, da kan ki kika chanja kanki. Saboda ni kadai ban isa nayi hakan ba. Ke ma kin sa a ranki zaki chanja din. Nagode da hakan da kika yi Selmah. Shiyasa nake gaya miki your heart is clean, your soul is beam.” “Jazakallah khair ya Saahibi.” “Wa anti Selmahna.” “Barci nake ji fa.” “Yau ko a baya za’a goya ki maza muje mu kwanta. Ko na dauko zani?” Tana dariya ta kau da kai. “Da gaske. Muga idon barcin?” Maimakon budewa sai ta sake rufewa gam. “Shikenan ai. Muje.” Bata ankara ba ya dauke ta cak. Ba zata yi gardama ba saboda taga alama ko kadan hakan baya bashi wahala kuma bini bini ya daga ta dan ma anyi sa’a bata da nauyi. Sunyi shirin barci sun kwanta ya gyara murya. “Ki shirya bana da ke za’a yi hajj. In muka dawo sai a san yanda za’a yi a fara karatun addini ko kuwa.” “Hajj? Ya Rabbi! Oh ya Allah…” Gaba daya ta rude. Ko da wasa bata taba hangowa ba wai zata je Makkah. A kalla a kwana kusa. Sai gashi wai Sheikh yana gaya nata zata je kamar kawai gaya mata zata kasuwar rimi. Oh Allah. “Na rasa abun cewa. Allah ya saka da alkhairi Saahibi, Allah ya qara budi. Allah ya…” Yatsan sa ya dora a lebenta. “Shhh.” “Ba wannan kalar godiyar nake so ba. Action speaks louder. Aywah?” Bata ce komai ba amma a shirun nata ya karanci amsar ta. Hakan ya sanya shi murmushi kafin ya musanya yatsansa dake kan lebenta da nashi. ***** Bayan wata daya. Tun sassafe Salmah ta tashi yau, zasu je qauyensu Uwale a gaida yan uwan da aka dade ba’a hadu ba. Duk da kuwa Uwale ta fadawa Salmah cewa ai tana zuwa gaishe su lokaci lokaci, ta kuma ce zumuncinsu ya ja baya tun rasuwar iyayensu. A hankali Salmah take gane mutanen da ko sau daya bata taba ganinsu ba a rayuwar ta musamman yan uwan Abbanta wanda duk a nesa suke. Uwalen asalin yar Katsina ce. Abban ta ma haka. “Tunanin me kike ne? Maza ki rufe jakar.” Uwale ta yiwa Salmahn magana tana dawo da ita daga tunanin da take. Dukkan su zasu tafi har Sheikh din. Kuma da sun dawo ba dadewa zasuyi ba zasu tafi Hajj. Su uku. Hajiyar Sheikh, Salmah da Uwalenta. Bata san harda su ba sai randa suka je yin fasfot wanda duk cikinsu babu wanda yake da shi. A kwanakin kuwa Sheikh ne yake musu bitar yanda ake yin aikin hajjin. Salmah ba zata iya kwatanta farin cikin da take ciki ba sai dai tace Alhamdulillahil lazi bi ni’imatihi tatimmus saalihat. Sai yanzu take gane abunda Abdul ya ce mata. Duk kan tsanani na tare da sauqi. Amma a wancen lokacin gani take kamar yana fada ne saboda taji dadi. Yanzun taga gaskiyar al’amarin. Duk wata addua da mutum zai yi, ana karbanta ne daidai lokacin da yayi. Sakamakon ne wani lokacin mutum baya ganinsa. Wani ma har ya mutu haka zaiyi ta ganin kamar ba’a amsa masa adduar sa ba. Allah ya san mene mafi alkhairi a wajen mutum kuma yake zaba masa hakan. Sheikh ya gaya mata cewa tarihi ya nuna cewa lokacin da annabi Musa yayi adduar a hallakar da Fir’auna, Allah a take Yace Ya amsa. Amma sai bayan shekara arba’in aka hallakar da Fir’aunan. Malamai sun ce abunda ya faru shine mahaifiyar Fir’auna tana nan da rai kuma kullum adduarta shine Allah kar ya nuna mata mutuwar dan ta. Sai bayan ta rasu bayan shekara arba’in sannan aka hallakar da Fir’aunan. Nan Sheikh ya dinga nuna mata qarfin adduar uwa ga danta. Da yawa in sun girma mantawa suke da wadda ta musu komai wato mahaifiyarsu. Jin hakan ya saka duk wani abu da zai farantawa Hajiyar Sheikh ko Uwale rai, shi suke yi. Har rigerige suke yi saboda su samu rahamar Allah.+ “Uwale nikam kwana biyar din da zamuji a Dan ja nake jinjinawa.” Salmahn ta fada tana cusa kayanta cikin wata haka hade da rufe zif din. “Iyi ba dole ba. Kin ji dadin gida mai na’urar sanyaya daki ko? Ga mai aiki an dauko miki dole ki guji qauyen mu.” Uwalen ta fada ta sigar tsokana. Dariya Salmah tayi. “Kai Uwale! Ni na isa? Ba mai aiki bace ba fa. Da yake dan naki ya fiya ci, shine ya dauko wadda zata koyan girki kala kala. Tana gamawa za’a sallame ta fa.” “Ah lallai. Soyyaya dadi ko Salmah?” “Ah to Uwale kema fa kina da mijin babu wanda ya…” Salmah bata qarasa ba Uwale ta jefe ta da dan kwalin kanta. “Ke kam baki da kunya.” Tare sukayi dariya sannan suka fita inda ake jiransu domin a dauki hanyar Katsinan. **** Gidan da suka sauka ba mutane da yawa a cikinsa, gida ne ginin zamani sosai. A nan Salmah ta samu labarin Sheikh ne ya sake ginin gidan. Sanda suka gama sauke kayansu suka zauna cin abinci dare, sannan ne Sheikh ya miqe. Da ido kowa ya bi shi amma sai yayi murmushi yace musu zai fita ne ya dawo. Salmah dai bata tanka ba sai da ya fita taji qarar wayarta ta duba. ‘Zan je wajen abokai na da muka dade bamu hadu ba ne. A saki fuskar.’ Da kyar ta boye murmushinta suka gama kowa ya watse. Uwale da Hajiyar kullum cikin hira suke kamar ba zasu daina ba. Yanzun ma tsakar gida suka fita suka fara hira da matan gidan da suka rage. Salmah ita kadai aka bari. Haka ta kwashe tarkacen abincin ta wanke sannan ta tafi daki ta zauna. Wayarta ta dauka ta kira maman Ameerah wadda suka yi kwana da kwanaki basu yi magana ba. Sauran kuwa dama sun jima basa mata magana tun ranar da suka yi fada. Sun gaisa sosai da maman Ameerah. Duk yanda maman Ameerah taso Salmah ta bata labarin chanjin rayuwar ta Salmah qi tayi sam. Haka kawai abun bai yi mata ba, bata ga amfanin gayawa qawa yanda rayuwar ta take kasancewa ba. “Amaryar Sheikh kenan. Sai mun hadu a makaranta. Kamar wasa wai level three. Daga nan saura shekara daya mu gama.” “Eh wallahi. Amma ni kuwa naga dadewar shekarun. Allah sa dai result din mu yayi kyau.” “Ameen.” “Yauwa a gaida Ameerah. Sai da safe.” Sai wajen tara da rabi duk sun kwanta sannan Sheikh din ya dawo. Lokacin Salmah tayi barci dama ga gajiya ta kwaso. Bude kofar da yayi ne ya tashe ta. “An sha hira.” “Yauwa sannu da gida. Bari na watsa ruwa na dawo.” Ya harareta. “Oh sannu da zuwa.” “Kya ji dashi.” “Toh kai baka san missing dinka nayi da yawa ba?” Har ya miqe sai ya dawo ya zauna. Hannun ta ya kama ya sumbata. “Na sani an yi kewa ta da yawa. Bari na watsa ruwan sai na dawo a bani labari?” Gyada kai tayi. Sanda ya tafi ne taga wayarsa dake ajiye a gefenta tana haske. Kamar ba zata kalla ba sai ta ga kiransa ake. Kallon sikirin din wayar tayi. ‘Ummu Khalil’. Ita ce take kiransa. Bata kula ba kawai ta dauke kanta har kiran ya tsinke. To in ta dauka ma me zata ce? In ya zo zai ga waye ya kira shi ai. Ita babu ruwanta. Kuma ko kadan ba ta ji komai ba a ranta. Tana gyangyadi taji gefen gadon ya lotsa. Ko kula wayarsa bai yi ba kuma Salmah bata gaya mishi an kira shi ba. Luf din da tayi ya zata tayi barci ya saka bai tashe ta ba. Sai dai hannun sa da ya sa ya matso da ita kusa dashi kafin ya tofa mata adduar barci sannan shima yayi ya kwanta barcin. **** A na gobe zasu tafi ne Sheikh yace wa Salmah wajen goma ta shirya zai kai ta taga gari. Ya gaya mata zasu yi zagaye da yawa domin har cikin garin Daura zasu je taga ababen tarihi. Da shirin ta ta kwana amma sanda ta tashi karfe takwas na safe ta ganshi ya tashi. “Zan fita na dawo kafin goman.” Haka ya gaya mata. Ba ta ce komai ba ganin yanzu ya fito daga wanka. Kayan sa ta dauko ta ajiye masa sannan ta dauko zanin wankanta da ta taho da shi tana goge masa jiki. Nan da nan ya shirya. Tana saka masa maballin riga ne wayarsa dake gefen gado tayi qara. Zuwa tayi ta miqo masa. Ganin sunan Ummu Khalil a karo na biyu ne ya saka taji wani irin abu ya so ki zuciyar ta. Haka ta danne ta miqa masa. Ba a speaker wayar take ba amma ta jiyo muryar mace tace, “Abu Khalil, dan Allah ka zo wani abu ne mai muhimmanci…” “Gani nan. Ina hanya…” Bai qara cewa komai ba ya fice. Wasa wasa Sheikh bai dawo ba har goma ta wuce. Sannan hankalin Salmah yayi mugun tashi. Wacece wannan har ta fita muhimmanci hakan? Tana yi tana kyautata masa zato amma duk da haka zuciyarta dokawa take, yayinda take jin kamar jinin jikinta yana tafarfasa. Qarfe hudu da rabi sai ga Sheikh a gidan. Amma yana kallon cikin fuskar Salmah ya san ya tafka laifi babba. Salmah kam sai dai tayi haquri saboda Ummu Khalil da Khalil suna da matuqar muhimmanci a gare shi. Musamman dan sa, Khalil. “Matar Sheikh!” Ko kallansa bata yi ba har ya qaraso inda take zaune ya zauna. Shi kuwa yana ganin yanayin fuskarta a karo na biyu sai hanjin sa ya tsinke. Bai san ya zata dauki labarin ba. “Oh ashe ka dawo. Sannu da zuwa, a kawo abinci ne?” Ganin yanda ta washe haqori yasan ba lafiya ba, ko da yake laifi yayi ai.+ “Na koshi.” “Oh ai ban sani ba. Bari nima na je na ci…” Miqewa tayi zata fice daga dakin ya kamo hannun ta. Kallonsa ta shiga yi babu wani yanayi takamaimai a fuskarta. Sai da tayi murmushi mai sauti sannan ta zare hannun ta. “Wai da sallahr la’asar zanyi.” “Selmah,” bata bashi amsa ba ta fice daga dakin. Tun da ta fita kuwa dama bata da niyyar qara kallon inda yake har sai dare. Nan ta shiga harkokinta da matan gidan, har makwabta ta raka Uwale suka gaisa. Sai can yamma suka dawo. Duk da haka bata kula shi ba duk da kuwa ta tabbatar yana nan. Sai kai kawo yake mata amma bata kula shi ba. Abun ma yado ya bata dariya. Da daddare ta shiga daki daukar abu sai gashi. Da sauri ya rufe dakin. “Da ka bude min da yafi? Akan kayi ta sintirin nan da zama kayi kana istighfari akan laifin da kayi wataqila da ya fiye maka amfani.” “Selmah!” Ya fadi sunanta da qarfi. “Na’am. Na dauko ma carbin ne?” Sheikh bai san sanda ya dafe kansa ba. Wannan wace irin yarinya ce ko tsoro ma bata ji. “Alaiki bil kamala Selmah!” “Ban iya larabci ba ka sani ai.” “Selmah! Wai meye hakan?” Ganin yanda ran shi ya baci ne ya saka ta yin murmushi. Ko babu komai yaji abunda taji itama. Shikenan ya wuce. “Ou, ina ta jiranka fa.” Ta bata fuska zata yi mishi kuka. “To ba sai ki fada min ba amma sai kin min tsinin baki?” “To ba kaine kake yin kamar baka yi laifi ba?” “To ba sai ki jira ki gani ba?” “To ba na jira ba?” “To ai jiran bai isaba gashi kuma ni an bata min rai.” Ya fadi yana lankwasar da kansa. “To ai sai kayi haquri ai.” Salmahn ta fada. “To na haqura ba dan halinki ba. Zo ki ji.” Sanda ta matso inda yake ne yayi murmushi yana jin dama dama. Yanzu inda ya biyewa zuciyar sa da tuni sunyi baram baram. “Wani abu ne ya taso dole naje.” “Fatan dai tana lafiya ita da Khalil din?” Hakan da Salmah tace ne ya saka shi yin shiru. Tunda ta fadi haka yasan inda zancen zai kama kuma bai shirya masa ba. Shiru yayi, a cikin shirun yake tuna komai. Komai dake littafin Jamilah. Lokacin da ya fara duban littafin ya na karanta duk fejin da ya ga dama. A nan yabi duk wani buri nata yana cikawa. Ba zai taba manta yanda rubutunta yake a cikin littafin ba. Yanzu haka ma yana gano shi a karkace a cikin littafin. Jamilah’s POV Page 20. Talata, karfe biyar na yamma. Salam alaikum qawata, littafina. Daga yau sunanka Yusrah. Saboda duk sanda nayi rubutu ina jin dama dama. Kwana biyu na buya ko? Abubuwa ne suka faru ya saka ko rubutun ma bana iya wa. Amma yanzu alhamdulillah, ina ta karanta istighfari. Ina ta yawan ambaton ‘Ya hayyu ya qayyum, bi rahmatika astigisu, aslih li sha’ani kullahu wa la takilni ila nafsi d’arfata ainin. Sai na samu sauqi sosai. STORY CONTINUES BELOW Yusrah wallahi Sheikh a rashin saninsa zai kashe ni. Ina da wata iriyar zuciya da bata daukan abubuwa kawai yawan ambaton Allah da neman tsari daga sharrinta ne ya saka nake jin dadi. Kishi na ba ka dan bane. Wai kinsan me Yusrah? Aure fa yayi bai gaya min. I mean he get married just few months away from our marriage. Mai yasa bai gaya min ba? Da ya gaya min wataqila na yarda. Amma haka kawai ya saka duk wani yarda da na yi da shi yanzun ya ragu. Lokacin da na ji suna magana na zata ba zan tashi ba saboda irin bugun da zuciya ta tayi. Amma me? Na rasa dan dake cikina. Haqiqa hakan ya kuntata min rai. A hankali, ban san wani irin so nake masa ba. Ya zaunar da ni ya ban haquri. Ya rungume ni, yin hakan yasa naji na haqura. Ban fadawa kowa ba na cigaba da zama da shi. Sai dai fatan Allah ya sa ya gyara din. Zan cigaba da karanta ‘Rabbana la tuzig qulubana ba’ada iz hadaitana wa hab Lana min ladunka rahma, innaka antal wahhab.’ Ba zan daina ba saboda kar zuciyata ta kitsa min abunda zai jayo min da na sani. Yusrah, ina yin qiyamul layli kuma ina da yaqinin cewa Allah zai amsa min. Wataran Sheikh dina zai dena duk abunda yake yi. In ma wani ne yake saka shi, Allah ya raba su. Ameen. Duk da haka, ina son abuna. Matar Sheikh sunana. Page 21. Laraba, qarfe goma. Yau kam ko sallamar ban iya rubutawa ba saboda farin cikin da nake ciki. Amma assalamu alaikum Yusrah. Yau Sheikh dina da bakinsa ya ban haquri kafin ya fita. Ya qara ce min yana sona. Naji dadi sosai. Sai anjima. Page 40. Asabar. Abubuwa da dama suna faruwa amma sai dai nayi hamdala. Na gaji wallahi amma saboda Allah nake yin komai tunda Sheikh ya riga ya zama miji na, shiyasa nake samun qwarin gwiwa. Wai kin san me? Akan abokinsa yazo ban bari ya shigo ba ya a mare ni? Dama ya taba mari na amma lokacin saboda ban da hankali kamar yanda su Ilham suka ce, ban dauka da zafi ba. Amma yanzu abun ya ban mamaki wai an mare ni saboda aboki! Wai shi Sheikh dinnan wani irin mutum ne? Qarshe ma dai dan a saka min baqin ciki abokin tarewa yayi a gidan mu. Yau satinsa guda kuma duk abunda yace na dafa masa sai na dafa. Saboda miji na ya saka ni. Yusrah ba abunda zan ce sai dai Allah ya saka min. Sai anjima. Page 45. Alhamis. Qarfe bakwai na safe. Tun da na yi sallah ta asuba nake jin babu dadin jikina. Ban bata lokaci ba na kira ya Fiddy a waya. Nan tace na gwada yin test. Ban jira komai ba na dauko pregnancy test strips na gwada. Na jima zuciyata tana bugawa kafin na duba. Holla! Alhamdulillah! Ciki ne da ni amma duk da haka sai da na bi Sheikh muka je asibiti aka gwada. Nan suka tabbatar ina dauke da juna. Na kusa yin tsalle saboda babu abunda nake kwadayi a yanzun sai ganin dan da zan haifa da kaina. Sabanin farin cikin da nake, Sheikh wasn’t happy. He just looked at me as though I were a dummy. Ban ji dadi ba kwata kwata. Sai bayan ya dawo yake gaya min yana so a cire. Fada mukayi sosai. Har yanzu rai na a bace yake. Bye. Page 46. Guess what? Qauyen su Sheikh zanje bayan na tambaye shi yace naje shi yana da abunyi. A gidan Alhaji AbdulHamid aka hadani da dan rakiya. Nayi siyesiye na tafi dashi saboda yanzu alhamdulillah business din da muka fara da su ya Nasir ya bunkasa. Muna yin nomar shinkafa. Sannan mun bude shago. Sanda muka shiga kauyen nayi mamakin layinka da mukayi kurdawa kafin mu isa gidan. Da kuma muka tsaya a kofar gidan ban aminta da cewa nan ne gidan ba har sai da muka shiga cikin gidan. Tsakar gida ne mai bishiya a tsakiya, gefe kuma bangare biyu ne daban daban. Da alama gidan mata biyu ne. Amma ko ina babu alamar mutane. Can na hango wata mata tana fitowa daga bandaki tana raben bangon da rabinsa ginin kasa ne rabi na bulo. Da alama wani waje ne ya ruguje aka gine da bulon. Yar rakiyar tawa ta juya ta dauko tarkacen motar. STORY CONTINUES BELOW Da sauri na qarasa na taimaka mata ta zauna a inda tayi shimfidar tabarma. Jikinta yayi zafi sosai da alama zazzabi take. “Ina wuni Mama.” Na gaishe ta. Bata bani amsa ba sai gyada kai da tayi. Da gani tana jin jiki. So I helped her, na kama ta na sa ta a mota sai asibiti. Asibitin was so poor, the system was pathetic amma sauri nake. Qarin ruwa aka yi mata sannan bayan ta huta ta kalle ni. “Nagode Allah saka miki da alkhairi yar nan.” Murmushi nayi. “Suna na Jamilah. Matar Muhammad Salim.” Ban san mai taji ko ta fahimta ba amma sai ta fashe da kuka. Nan ta rungomi tana bani haqurin da ban san dalilinsa ba. A lokacin na fahimci ita mutum ce mai sauqin kai. Da zan tafi cewa nayi da ita zamu tafi amma sam taqi yarda tace tana da yan mata kuma duk sun tafi makaranta ne. Ban so ba amma haka na tafi na barta bayan na barta da kayan amfani tunda nasan ba zata karbi kudina ba. Banyi mamakin godiyar da tayi ta min ba. Naji dadi sosai. A qalla na wanke kaina. Amma sanda na shiga mota sai hawaye suka fara zubo min. Gaskiya Sheikh dina ba shi da hankali. A yanzun na yarda da duk abunda su Abba suke fadi. Ya za’ayi yayi wasa da aljannarsa haka? Bai sani bane? Aljannarsa na qasan tafin mahaifiharsa? Taya zai barta a wulakance saboda yana tunanin ta tsufa? Toh ina tsufan anan? Kamar Ummahna na ganta. Tunda su auren wuri suke yi. Ni kuwa yau sai na mishi magana. Bai san wata kissa bane a zamanin annabi Musa? Haba mana. Yusrah, uwa fa! Wata rana annabi Musa yana ta roqan Allah ya nuna masa makwabcinsa a aljanna. Sai yayi mafarki Allah yace masa ya fito waje, duk wanda ya fara wucewa shine makwabcin nasa. Yana zaune wani mutum ya wuce. Bai tsayar da mutumin ba, bin sa yayi tayi har yaje inda zashi. Nan yaga ya tsaya a bakin wani gida. Ya fito da wata tsohuwa ya zaunar da ita ya bata abinci ya bata ruwa sannan ya mayar da ita ya fito. Annabi Musa ya tsayar dashi ya tambaye shi. Mutumin yace masa ai mahaifiyar sa ce kuma watarana sai yayi dako yake samo abincin da zai bata. Yace kullum kuma idan na gama ciyar da ita, ta kan daga hannu ta roqa min Allah. Tace: ya Allah ka sa da na a aljanna. Ya Allah ka sa shi makwabtaka da annabi Musa a aljanna. Annabi Musa sai ya fashe da kuka ya gaya wa mutumin abunda ya faru. Wani mutum ma ya taba daukar mahaifiyar sa yana dawafi da ita. Da aka tambaye shi yace zai biyata ne duk goyon da tayi masa amma sai wani sahabi yace ko mai zaiyi ba zai taba iya biyanta ba. Wai shi wannan Sheikh din bai san wannan bane? Haba dan Allah. Ai kuwa zan masa fada. Ni ba ruwana dole yaji. Ya dauko mahaifiyar sa yazo mu kyautata mata a gidan mu ko kuma ya gyara gidan nan ya zama gida mai kyau. Ya inganta rayuwar gidansu gaba daya. Ai aljanna yake nema. Kai yau rai ba dadi sam! Amma nasan ba lallai na iya fada masa ba. Bye. Page 60. Saura kwana bakwai fa EDD dina. Har yanzu kamar yanda na rubuta in previous pages we’re not that cool ni da Sheikh. Kawai dai muna zama ne shi a lallai haushi yake ji. Ban bi ta wannan ba saboda yanzun zumudin na haifi abun ciki na nake. Haka nayi ta zama. Babu yanda ba’ayi ba na tafi gida yaqi. Ni kuma nace a bar ni tunda haka yake so. Zuwa yanzu ina da nambar Hajiyarsa. Na kira na gaya mata halin da ake ciki. Tayi masa magana amma duk da ya amsa sai yake ta kumburi. Ni kuma gudun fushi kawai na haqura na zauna. Ban fadawa kowa dalilin ba. Nuna musu nayi cewa ni nake son zaman. Ita kuwa Hajiya da taji labarin ina nan sai ta min addua kawai. Page 61. With heavy heart nake rubuta wannan. Na rasa dan da na haifa. Yusrah this is too heavy for me to carry. Wallahi da kyar nake kifta idona saboda halin da nake ciki. Ina ta maimaita innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Sabanin kwana bakwai din da nake lissafin zan haihu, rana ta biyar nakuda tazo min. Babu irin kiran da banyi wa sheikh ba yaqi dauka. Sanda tunanin na kira yan gidan mu yazo ko wayar kasa dagawa nayi. Sai can ya dawo bayan na gama galabaita. Nan ya dauke ni muka je asibitin. Da kyar na zata zan mutu amma haka na haifo da namiji. Mummunan labari shine zuwan da yayi babu rai. No, an ce da ransa amma wahalar da muka sha ya saka he couldn’t make it. I want to remain sane, bana so na kurma ihu amma wallahi this pain is beyond me. Yanzu haka na nemi gafarar kowa. Kowa yana min murmushi da nuna min cewa komai zai wuce. Allah sa ya wuce din. Wani barci nake ji yana fusgata. Da alama zai yi min dadi. So zan kwanta yanzu na dan ji dadi. Na so Ilham zata zo kafin na kwanta. Ita kawai nake son gani yanzun. Ina son Ilham, sosai. Bari na kwanta. Har wani sanyi nake ji a raina yanzu. Sai na tashi! A wannan gabar, Sheikh na haqura da trying. Na haqura da kokarin hada kan mu. Amma ba zan dena sonka ba. Na yafe ma komai amma kuma na gaji. Na sare, I surrender. Yusrah ki gaya masa. Bye. **** Wannan shine fejin qarshen cikin littafin da Jamilah ta rubuta. Sosai yake kokarin danne zuciyar sa. Salmah jin shirun da Sheikh yayi yasa ta kalle shi. “Ina jinka.” “Khalil da na ne.” A razane ta kalle shi. Sai da ya bari ta gama kaduwa sannan yayi dariya. “Kwantar da hankalinki gimbiyata. Sunan maman sa Ilham. Kanwar marigayiya Jamilah. Jamilah tana sonta sosai shiyasa nake kokarin faranta mata. Na dauki danta kamar nawa.” “Allah yaji qanta. Ina babansa?” “Yana nan.” “Toh ka bar shi yayi aikinsa.” “Ba sa tare ai.” “It doesn’t matter. Ko sun rabu, shine ubansa ba kai ba. Ji min daura wa kai wahala. Jamilah ta riga ta tafi. Akwai hanyoyin yin abubuwa dominta. Zaka iya gina massallaci ko islamiyya dominta amma ba sai ka kula qanwarta ba.” Salmahn ta fada ranta a bace. Shi kuwa Sheikh mamakin yanda take masa magana yake. Babu tsoro sam. “I’m sorry, aurenta zan yi ai sai komai yafi sauqi.” Da gaske aurenta yake son yi saboda ya inganta rayuwarta. Addini bai haramta masa yin hakan ba. Da farko bai taba tunanin ya aureta ba din amma da yaga alamun ita Ilham din tana nuna masa cewa babu laifi a hakan sai yaga ai babu laifin in ya aureta din. Ba ta haka ya kamata ya gayawa Salmah ba amma bata shi da zabi da wuce wannan tunda ta nemi ta sani. Yanzun Hajiyarsa kawai zai kaiwa zancen, da ta amsa shikenan. Kamar anyi an gama ne. Ba son kai yayi ba, burin marigayiya yake son cikawa. Tunda qarshen kulawa da zai nunawa Ilham shine ya kawo ta qarqashinsa. Jiki a sanyaye Salmah ta zuba masa ido sannan ta sheqe da dariya. In da wasa yake to ga amsa nan. In ma da gaske yake ga amsa nan, zata gane ko wanne daga ciki. “Allah ya baku zaman lafiya toh. Ha’an ka ga angon Ilham.” Yanda Sheikh ya kafeta da ido bai sa ta daina abunda take yi ba. Sai da yaga ba dainawa zata yi ba sannan ya fisgota ta fada kanshi. “Wai ke baki da control a bakin kine?” Ya dage mata kira. “Daga taya ka murna?” Matse lebenta yayi da hannunsa yana harararta.+ “Ba kya kishi na?” Bai san me ya sa ya fadi hakan ba. Kamar ba babba ba, gaba daya yau dinnan yanda take masa baya jin dadinsa sam. “Ba na yi nikam. Ban iya ba.” Toh me yake so tayi? Ihu yake so ta masa ko kuma ta daga hannu ta mare shi? Gani tayi ko wanne tayi daga ciki ba zai canza komai ba. Ina amfanin ta mayar da kanta kamar mahaukaciya akan wannan. Sarai ba qaramin kaduwa tayi ba amma ya za ta yi? Bata da wani zabi da ya wuce ta danne duk wani kishi da yake taso mata. Tsoranta daya shine in har tayi nasarar danne zuciyar ta, bakin ta zai iya cin amanarta dan wani lokacin haka maganganu suke fitowa ba tare da ta shirya musu ba. “Ya Allah.” Ya shafo fuskarsa tare da tura ta gefe yana miqewa zai fita daga dakin. Shi bai san me yasa dan wani abun ya bata mishi rai ba. Jamilahrsa ba haka take ba. Ita wannan Salmahn bata san me ya dace bane? Ha an. Sai da ya kai bakin kofar sannan yaji hannu ya zagaye shi. Tsayawa yayi bai motsa ba yana auna abunda zaiyi mata a ransa. “Saahibi zo na baka labari. Mijina yayi fushi dani fa saboda yana tunanin bana kishinsa. Toh ni ya zanyi? Dole na mishi haka ai tunda shi ma ya min haka. Amma har cikin raina nake jin babu dadi. Dan Allah ka gaya mishi ina son shi sosai kuma ina kishinsa sosai. Saahibi, tell him. Matar Sheikh tana son shi sosai, dan Allah ya haqura da wata Ilham. Ba lallai sai ya aureta ba. Duba min fa, kwata kwata yaushe mukayi aure? Nikam dama na sani alfarma kawai ya min ya aure ni.” Yana jin yanda ta kwantar da kanta a bayan sa. Her problem is she’s too straight a komai. Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya juya yana kama habarta. Hawaye take kamar gaske. Taya zata ce alfarma ya mata? Da wani ne ya fadi hakan da tuni ya zubar masa da haqoransa a qasan saboda irin dukan da zai masa. Duk da hakan dai sai yayi shiru. Babban yatsan sa yasa yana goge mata hawayen sannan ya shiga shafa kumatun ta a hankali. “Ki gaya mata ta rage tsinin bakinta ko na rage shi da kaina. Ta cika surutu da fadan abu farat. Amma dai ya haqura.” “Ni ai komai nake so nake fada.” “Ai hakan bashi da kyau kuma. Ke mace ce, yana da kyau ki dinga yiwa kalaman ki ado. Wananyn baki naki ko, dadinta ma ya iya dadin magana.” “Toh shikenan.” “Amma dai ko yaya ne inaso a dan koya min nima. Ina nufin zakin maganan.” “Ban san yanda ake koyawa ba.” “Ni na sani ai.” Ya bata amsa. Daga yanda ya kalle ta ga san sauran shiyasa tayi saurin sadda kanta kasa amma bai fasa ba. Sai da ya isar da duk saqonsa gareta sannan ya kalle ta yace, “Ko da wasa bana so na sake ji kince alfarma nayi miki na aure ki. Na gaya miki cancantar ki ce ta saka na aure ki. Ba dan kar ace nayi butulci ba ma sai nace kin cancanci wanda yafi ni. Don haka ba na son na sake jin makamancin wannan ko da kuwa a mafarki ne. Ke kinsan kuwa martabarki kike raina kanki? Ko hurul in sai sun sara miki amma kike ragewa kanki daraja. Na tabbatar mata da dama suna kishi dake saboda basu da abunda kike dashi. Matsalar daya ce tak wadda basu sani ba. Selmah akwai dogon baki, haka.” Ya kwatanta a bakin sa yanda zai nuna tsawon bakin. Hannu ta sa ta dan ture shi kafin kuma ta kwantar da kanta a kafadarsa. STORY CONTINUES BELOW ****** A kan wata Ilham haka har suka koma Kano Salmah tana jin haushi. A zahiri kamar abun ya wuce ne, a ranta kuwa ji take kamar ta kurma ihu. Ta riga ta saka ran zuwa ganin gari amma kawai hakan ta faru. Duk sanda ta zauna ita kadai sai abun ya dawo mata. Bayan sati uku ne suka fara shirin tafiya Saudi. Gaba daya bata samu zama ba saboda shirye shirye. Da kuma ta tuna idan sun tafi Sheikh zai iya daukar kafa ya tafi wajen Ilham sai taji kamar ta fasa zuwan. Haka tayi ta dannewa amma hakan bai hana da ana jibi zasu tafi tace masa, “A hisbah kake. Kayi amfani da damar ka kaga ka sulhunta Ilham da mijinta. Idan kuma sulhun ba mai yiwu wa bane ai sai ta sayi form din zawarawa, in tayi sa’a tayi dace da miji na kwarai.” Ba kadan ta bawa Sheikh dariya ba daga yanda ta bata rai. Da kyar ya danne dariyar saboda kar ya ballowa kan sa aiki. Daga baya ya zauna ya sake tunani. Babu wata Ilham da zai aura, dama bai gaya wa Ilham din ba. Toh komai ya zo da sauqi. Ya sani iyayenta ma zai yi wahala su bashi ita duba da irin zaman da yayi da yayarta. Yanzu kuwa abunda Salmah tace, shi zaiyi. Sulhu alkhairi ne. “Banda abun Selmah ai ba sai kin tayar da hankalinki har haka ba. Ita ma kam hajjin zata ai. Jirginsu anjima zai tashi.” Kallonsa tayi na dan sakanni amma bata ce komai ba. A haka ta lallaba dai har suka tafi. Zaman Saudiyya yayi mata dadi, a wani bangaren kuwa ya gajiyar da ita nesa ba kusa ba saboda sai suna cikin tafiya sai kawai Hajiya da Uwale su nemi wajen zama wai su sun gaji. A wasu wuraren kuma sai sun gama kwaso kayayyaki su barta da dako. Bata wani damu ba amma dai ta gaji. In sun koma masauki kuma warin abubuwa duk ya ishe ta. Tsofin da suke wuri daya da su suyi ta shanya abinci. Wasu suyi amfani da bandaki su bar shi haka. A haka dai aka yi aikin Hajjin ana fatan karbabbiya ce. Dawowarsu ya qara kusanta ta da mutane da dama na dangi. Kullum a cikin godewa Allah Salmah take da ya kawo mata canji a rayuwarta. Tsakaninta da Sheikh kuwa sai hamdala. Kusan kullum sai sun samu sabani, har ya zame musu jiki. Maganar Ilham kuwa an shafeta tun ranar da bincikensu ya nuna ita ce take turawa Salmah saqonni kala kala domin ta tsoratar da ita. Ganin haka Sheikh yace ba zai daukowa kansa abunda ba zai iya ba. Haka kawai yazo ya kunnowa kansa matsalar da zai yi masa wahala ya magance ta. A haka dai yayi kokarin sasanta ta da mijin amma fir mijin yace bai yadda ba. Qarshe ma dai mijin ya karbe dan sa. Haka rayuwar shi take da Salmah. Ayi fada, ayi wasa, ayi karatu, a yi musu. Ya dauke ta kamar yar shi ce in yana wasa da ita. Abubuwa da yawa kuma in tayi yarintar ta yake gani akan shekarunsa. Wataran in sun gama musun nasu sai su kwashe da dariya. Duk abun su basa iya barci suna fushi da dayansu. Shi kuwa ranaku kadan ne suke wucewa bai tuna da Jamilah ba. Irin wannan rayuwar tayi burin samu tare dashi. ****** “Na gaji da abu daya ni fa. Yau ba haka Jamilah take wannan, gobe ba haka Jamilah take wancen ba. Salmah ce wannan, in Jamilah kake nema kana iya zuwa ka haqo ta a kaba…” “Selmah!” Yanda ya daka mata tsawa sai da ta girgiza. Bata san sanda hawaye suka zubo mata kan kumatunta. Shekararsu guda da rabi kenan da aure amma duk wani abu da zata yi sai ya bude baki ya ambaci Jamilah a cikinsa. Da farko tayi masa uzuri amma sai abun nasa ya zama wani iri. Yanzu zata kawo masa abinci, yana gama ci zai ce ai Jamilah tana saka citta a nata kuma sai hakan yafi dadi. In gyarawa yake so tayi zai iya gaya mata ta wata hanyar amma yawan ambaton Jamilahn yana kona mata rai. Duk da haka, muryarta a makale tace, “Allah ya huci zuciyarka.” Bai kula ta ba, sai huci yake yi. Dama ta riga ta sani in zama ya yi zama dole zata fuskanci canji shiyasa bata yi mamakin shareta da yayi ba. “Kayi haquri rai na ne ya baci na gaya maka abunda bai kamata ba.” Tana fadin haka da hawaye a idonta ta fice daga dakin zuwa nata. Barin hawayen tayi yayi ta zuba har sai da taji dadi sannan ta dauki Qur’ani ta karanta kamar yanda ya koya mata har sai da dan ji sauki. In da ta biye ta son ranta, ba zata bashi haqurin ba saboda ita yayiwa laifi amma ibada take yi. Kullum tana kara tunawa kanta hakan kuma Ummah tana yawan tunatar da ita duk sanda suka yi waya. Har dare bai kalli inda take ba, bai kuma taba abincin da ta ajiye masa ba. Gaba daya hankalin ta ya tashi. Da kyar tayi wanka ta saka kayan barci sannan ta tsaya a bakin kofar dakinsa. “Salam alaikum.” Tana ji ya amsa ciki ciki. Ta tura kofar ta shiga. A kan gado ga gan shi ya zauna har yanzu ran shi a bace. Sai da ta jima a gefe sannan ta ja numfashi. “Da dukkan alamu anty Jamilah mace ce ta gari. Ko wacce mace zata so tayi koyi da ita, har nima ina kwadayin hakan. Mutuwar ta ta shafe ni saboda da zata tafi ta tafi da wani bangare na zuciyar miji ta. Allah ya mata rahama ya kyauta ta makwancinta. Zan so na bata haquri akan abunda ya faru yau. Na bata wa mijinta rai yakai ko gani na baya son yi. Ya Allah, ka yafe min.” Tana gama fadan hakan ta tashi, tayi tsammanin jin hannun sa ya dawo da ita. Amma bai dawo da itan ba. Komawa tayi ta zauna. “Kayi haquri kai ma.” Ko kifta ido bai yi ba. Da ta gaji sai kawai ta kade gefen gadon ta kwanta abunta. Bata taba kwana babu shi ba kuma don yau yana fushi da ita ba zata fasa ba. Jarabawa zasu fara gata amma bata jin zata iya karanta komai. Suna first semester a level four. **** Da safe ya amsa gaisuwarta sama sama. Haka ta fita makaranta ranta duk babu dadi. “Kalau kike kuwa?” Wata cikin qawayen nata ta tambaye ta. Salmah sai da kalleta sau biyu. Rabon da suyi magana tun suna level three. Yanzun meye kuma damuwarta da ita. “Lafiya ta kalau.” Ta bata amsa da wata irin murya. Murmushi Raudah tayi sannan ta zaro yar kwalba a jakarta ta dauki jakar Salmah ta saka. “Na san kin manta da wannan. Ki manta wannan kalar relief din.” Sai ta juya tayi tafiyarta. Zuwan maman Ameerah ya saka hankalin ta ya dauke. Sai da taje gida tana zazzage jakarta ta tuna da kwalbar. Sanda ta kalla, runtse idonta tayi sannan ta bude taje sink zata zubar. Bata san me aka yi ba, ko ya aka yi. Kawai taji wani abu yana tura ta da ta sha din. Sauqin da take nema zai zo. Duk yanda ta gwada yaqi da zuciyarta, sai da tafi qarfinta ta bude ta fara sha. A sannan Sheikh yayi sallama kuma ya hangota a kicin. Tuni, ta fara fita daga hayyacinta. **** Sai yamma lis ta farka, a sannan komai ya dawo mata musamman da ta bude ido ta ganta a kan gadonta bayan ta san ba a nan take ba da. Hankalin ta ya tashi sosai saboda ko abinci bata saka wa Hajiya ba. Da kuma ta tuna yanda taga fuskar Sheikh da irin maganganun da tayi kafin barci ya kwashe ta, sai taji kamar ta yi ihu. Ji take kamar an kwarara mata kankara a jikinta tsabar daskarewar da tayi. Tana wannan tunanin ne ya tura kofar dakinta ya shigo. “Wooo oga Salmah sannu.” Wani abu ta hadiye, tana sauke kanta kasa. Fata take ta bace bat kawai duk da ta san ba mai yuwuwa bane. A gefe guda kuma ga wani ciwon kai da ya saukar mata. Jikinta kuwa sai karkarwa yake. Sheikh ne yayi murmushi. “Oga Salmah ne ko gaye Salmah? Ko kuwa Ale ko Baaba Salmah?” Juya kansa yayi ya sake murmushi mai sauti wanda ba abunda yake nunawa sai bacin rai da gatsen da yake mata.+ “Ko ma dai wanne ne zaki iya zuwa kiyi wa surukar ki bayanin barin ta da yunwa da kika yi.” Bata motsa ba amma yanzu hawaye take sosai sannan jikinta bai bar rawa ba. Ina amfanin irin wannan rayuwa? Ina amfanin aikata irin wannan abun? Ace mace da ita, wadda ake mata kallon miskila, nutsatsiya amma tana irin wannan rayuwar. Ta kusa shekara rabon ta da shan wani abu. Ba zata ce bata jin sha’awar shan abun na taso mata ba lokaci lokaci amma tayi iya kokarinta ta danne. Sai yau kawai ta sake, a cikin gidan ta. Gidan Sheikh. Duk wani hukunci da ya dauka a kanta yayi daidai saboda ba tilasta mata akayi ba, ba danneta akayi ba, son zuciyar ta tabi. Lallai annabi sallallahu alaihi wassalam yayi gaskiya da yace idan zuciya ta lalace dukkan jiki ya lalace. Gashi nan ta biye ta ra’ayin zuciyar ta da rudin shedan. Shedan kuwa kamar jini yake yawo a jikin mutane. Duk wata hanya da shedan ya san zai bi yaga ya saka mutum fadawa ga halaka bin ta yake qarshe ya kai ka ya baro ka. Sau da dama son zuciya ma haka yake, ya kai mutum ya baro shi. Salmah qanqame jikinta tayi tana kuka da dukkan karfinta. Taci amanar Uwale, Hajiya, Ummah, Sheikh. Gaba dayan su suna mata kallon kamilar mutum kuma ko yaya ba zasu taba aminta zata yi hakan ba. Sheikh ma tana sane yayi mata uzurririka a baya saboda abubuwan da tayi cikin rashin sani. Yanzu kuwa bayan zaman su na shekara daya da rabi, ta koyi abubuwa da yawa. Abunda ta sha bashi da maraba da giya, saboda ai shima bugarwa yake. Giya ana kiranta da sunan uwar laifuffuka da sharri saboda ba ta da wani alkhairi a tare da ita. Giya haramun ce, duk wani abun maye masu kama da giyan, haramun ne. Ta san wannan. Amma ta take ta sha. Yanzu wani sauqi taji? Face qarin damuwa da ta tsinci kanta a ciki. Wayyo! In Allah ya yarda ba zata sake ba. Har cikin zuciyar ta take jin nadamar abunda tayi yau. Da wani ido yanzu zata kalli Sheikh ta bashi haquri? Bayan ta gama zubar da mutuncinta tunda ta kawo abun maye cikin gidansa. Ya Allahu. Sau nawa ne tana sha tana tuba? Sai yaushe zata watsar? A hakan ne take fatan samun yara? Wacce irin tarbiyya uwa mai shaye shaye zata iya bayarwa? Kash. Ko wacce irin kwafsawa tayi ta. Har ta mutu ba zata manta da wannan rana ba. “Sheikh…” Tayi kokarin fada. Kallonta yayi, idanunsa cike da hawayen da ta saka shi dole. Bacin ran da yake ciki ya fi karfinsa. “Salmah… Kin bata… Kin ruguza yardar da nayi miki…” Bata taba jin wani abu da ya ruguza mata lissafi irin wannan ba. Yau ina zata saka kanta ne? “Sheikh…” “Ki huta.” Da haka ya fita ya bata wuri. Toshe bakinta tayi domin kar qarar kukanta ya fito. Zata lura da wannan. Komai yarda da tayi da yaranta zata binciki duk wani al’amari da yake tare da su. Da yardar Allah zata musu tarbiyya mai kyau, yau ta gama shan duk wani abu in sha Allah. Yau ta kudurta cewa zata ja yaranta a jiki, zata nuna musu so, ba makahon so ba, a’a, zata kwabe su in sunyi ba daidai ba. Zata bincika irin abokan da zasu yi mu’amala dasu. Domin babbar matsalar da ta samu shine rashin abokai na gari. Matsalar ba shine tarbiyartar da yaran kawai ba, mutanen da suke harka dasu sune abun tsoro. Da wannan ta tashi tayi sallah. Ta juye duk damuwarta a sujjada, tayi roqi gafarar Allah saboda ta yadda Allah zai yafe mata. Haka ranar ta wuce a daddafe sai washegari bayan Isha’i sanda ta tabbatar nutsuwarta ta daidaita ta je wajen Sheikh. A zaune yake kuwa, idonsa yayi ja. Gwiwarta ta saka a qasa. “Saahibi, lallai yau na maka laifi babba kuma nazo da kokon bara ta ina neman afuwarka. Na amsa laifi nayi, na amsa na ci amanar yardar da kayi da ni. Amma ina so na tabbatar maka da cewa wannan ne na qarshe. Ba nayi hakan bane domin na bata maka rai, ba zan maqalawa shedan ba. Na amsa laifi nane. Dan Allah dan annabi, ba don ni ba ba kuma dan na cancanci ka yafe min ba, ka yafe min. Zuciyarka cike take da alkhairi, duk inda kaje, kana yada shi. Ka yafe min Sheikh…” Kuka ne ya kwace mata. Gwiwarta tuni ta sage. Bata ankara ba taji ya riqo ta. “Hasbuki, ya isa…” “Ki sani nadamar da na gani karara ya saka zan haqura. Za kuma ki daukar min alkwari ba zaki sake ba. Kullum ina gaya miki ki dinga takatsantsan da mutanen dake gewaye dake. Ba kowa ne yake son ki da alkhairi ba. Gaya min wace tazo gidan nan?” Duk yanda ya so ya shareta na tsawon lokaci mai yawa sai ta bashi tausayi. Gaba daya ta chanja yanayi duk da kuwa bata fasa yin kwalliya mai daukar hankali ba. Ba abun yayi magana ba tunda fushi yake. Wannan biyu ya saka ya ga gara ya haqura komai yayi masa sauqi shima. “Ba zuwa tayi ba. A makaranta ta saka min a jaka. Na dauka zan yar amma na sha…” Babu amfanin tayi masa qarya a wannan gabar. Gara yaji komai daga bakinta ya dauki matakin da zai dauka. “Kin ga irinta ba? Ranar kiyama akwai mutanen da za’a tashe su suna kuka suna kaico. Suna cewa dama basu yi abota da wane ba. Na gaya miki ki kula da qawayen ki amma ba kya ji. Yau zan datse alaqarku. Daga yau kin daina zuwa makarantar.” Halin da take ciki bai hana ta kalle shi da sauri ba. Yana nufin ta daina makaranta? Kai, wannan yayi taauri da yawa. Bayan saura yan watanni su kammala. “Eh. Sauqi shine a magance matsala tun daga bakin zaren. In ba daina zuwa kika yi ba, ba zasu daina neman su dawo dake cikinsu ba. Lallai duk wani tsanani da zan miki yanzu zaki kalle shi a matsayin takura da rashin son ki. Bayan kuma rashin hakan ne ya kawo ki in da kike. Ina nufin yardar da Umma da Abba suka yi dake ne ya qara cutar dake. Sai basu gano matsalar ba balle su magance ta. Yau na miki iyaka da duk wata qawa. In shawara kike nema gani nan ko Hajiya amma sam ban yarda naji kin dau waya wai kina magana da qawa ba. Dauko min wayar.” Da sauri ta tashi ta kawo ba tare da ta duba komai ba. A gabanta ya cire sim din. Qarshe ma wayar karbeta yayi. Sannan ya shimfido dokoki. Ko da ya gama, fashewa da kuka tayi. Yanzu da gaske ta daina makaranta bayan tana gabar gamawa? Shi hakan ne ya masa daidai? Ai shikenan. “Zan koma karo karatu kwanan nan, tare zamu tafi sai ki zabi duk abunda ya miki ki fara daga farko. Sam ban yarda ba bar Selmah na ba wani ya bata min ita.” “Ba zan yi wani abu dan na muzguna miki ba, duk abunda zanyi miki a gani na shine daidai. Ba zan cutar dake ba Selmah ko a mafarki na.” Wannan furucin nasa ya wanke mata duk damuwarta na wannan lokacin. Wasu dokokin da ya saka mata sunyi tsauri, wasu kamar tayi ihu amma babu yadda ta iya. Yadda yake so hakan za’a yi. Ta san babu abunda zai cutar da ita daga cikin su. Allah sa hakan ne alkhairi a gareta. Amma duk da haka bakin ta qaiqayin magana yake. Haka ta daure bata yi ba. Ance baki shi ke yanka wuya. Kar taje ta fadi abunda zai bata sulhun su. Bata samu yin barci ba saboda tana ta tunanin gobe za’a shiga jarabawa babu ita. Ta saka karatun a kanta dan kuwa tunda Abba ya nema mata admission ta sa a ranta zata yi karatun. I zuwa yanzu bata da carryover ko daya duk da kuwa sauran qawayen nata akwai masu su ratata. Yanzu da ance mata zata daina tana gab da gamawa, da ba ma zata fara ba. Allah kenan, ya riga ya tsara mata hakan. Ajiyar zuciya tayi kawai sannan tayi hamdala hawaye taf a idonta. Daga baya ta tashi tayi alwala, tayi raka’a biyu ne Sheikh yaji motsinta ya tashi.+ Haka suka yi tayi har a kayi asuba. “Shine baki tashe ni ba don nayi nauyin barci yau ko?” Hannun ta ta daga masa tana nuna masa cewa tasbihi take kuma ba zata iya magana ba yanzun. Murmushi yayi shima ya cigaba da yi. Basa amfani da carbi lokuta da dama. Da hannun su suke yi. Tana cikin yi Sheikh ya matso kusa ya kama hannun ta ya fara istighfari yana taba layikan yatsunta domin kirge. Ganin haka ita kuma sai ta koma yi a ranta. Haka sukayi tayi har rana ta fito. “So nake mu samu ladan tare.” Murmushi tayi tana jin dama dama. Daga nan suka yi wanka sannan aka fara aikace aikacen gida. Wannan shine tsarinsu, bai taba ce mata ga taarin ba. Shi dama sai dai ya nuna maka abu kuma in dai ya nuna hakan yake so a yi. Tare suka shiga kicin. Har ta saba yana shigowa, wataran ya isheta da hira wataran ya taya ta abunda ba a rasa ba. Bayan ta je ta gaida Hajiya ta kai mata abinci ne ta tarar dashi yana jiran shigowarta bai tafi aiki ba. “Sa Hijabi akwai inda zamu je.” Tunanin farko da tayi shine makaranta zai kai ta wataqil ya jira ta fito sannan su tafi. Amma da ta ga sun shiga mota an dauki wata hanya daban sai ta mayar da kanta ta kallon hanya ta windo. Bata tambaye shi ba sai da suka yi tafiyar kusan minti arba’in. “Psychiatric hospital? Asibitin mahaukata fa Sheikh???” Ta tambaya tana zaro ido. Dariya yayi sannan ya kashe motar. “Fito,” ba musu ta fito din. Bai qara cewa komai ba sai dai riqe hannun ta da yayi suka fara shiga asibitin. Sosai hankalin ta ya tashi. Mai yake nufi da hakan. “Tsaya anan bari na dawo.” Bai jira amsarta ba ya wuce. Ita dai zama tayi ta rakube waje daya, numfashinta sama sama saboda tsoro da take yi. Ya kai kusan minti talatin a yanda ta kwatanta domin ko agogon da ke hannun ta bata gwada dubawa ba. Kar wani a cikin mahaukatan ya fito ya same ta ya mata duka. Kar wani abu ya same ta shine tsoranta. Can sai gashi ya dawo tare da wani mutumin. “Selma, wannan shine Dr Gambo zai zagaya da mu.” “Ina wuni.” “Seems like she’s scared Sheikh. Are you sure she can do it?” “Ni ba tsoro nake ji ba.” “Toh kaji amaryata ba tsoro take ji ba likita. Mu je ko?” Dariya Dr Gambo yayi sannan ya kalli Sheikh. “Har yanzu amarya ce?” Salmah bata san sanda ta harare shi ba. “Har yanzu.” Iya abunda Sheikh din yace kenan sannan suka fara tafiya can cikin asibitin. Tun ba a fada ba Salmah ta fara jiyo hayaniya. Bata san sanda ta damqe hannun Sheikh ba. Ta kusa yin ihu amma ganin wannan Dr a kusa ya hana ta. Da alama saka ta a gaba zai yi yayi ta tsokana. “Saboda protecting privacy, daga nan zamu tsaya ba sai kun ga fuskar wancan mutumin ba ba kuma sai kun ji sunan sa ba. Shekarar sa biyar a nan. Yan unguwa ne suka tsinto shi yana hauka a titi. Background check ya nuna mana cewa ba ko mai ya saka shi hauka ba sai son kudinsa.” Salmah da Sheikh ne suka kalli wajen suka ga yanda yake ta tsalle tsalle a cikin dakin da aka adana shi. Sannan Dr Gambo ya cigaba. STORY CONTINUES BELOW “Ance ya saka kudi a ransa kuma dan kasuwa ne, yana da qaton shago a kasuwar Kwari. Ba a san ya aka yi ba amma sai tashi akayi aka tarar shagon sa na ci da wuta. Daga nan fa labari ya chanja game da mutumin nan. Ya kasa daurewa har sai da ya samu matsala da kwakwalwarsa. Yanzu da zaku matsa kusa ji zakuyi yana ambaton sunayen qasashen da yake saro kaya da manyan kudin da yake dasu. Allah ya bashi lafiya ameen.” Ameen suka amsa da ita kafin su matsa gaba. Kamar na wannan din baya ya saka suka ja sannan ya fara. “Ita kuma wannan matar da ku ke ganinta, in zaku kalla zaku ga ita dakinta a suturce yake. Haka muka tanadar mata saboda a kwana biyu zuwa uku zaka ganta kamar mai hankali har ma ta baka shawara daga baya zaka fuskanci cewa akwai motsi akanta. Ance tun ranar da mijinta yace zai yi mata kishiya abubuwa suka fara canzawa. Babu wanda ya kula ta, haka take zaman kadaici a daki ta yi ta kuka. Ko tana zaune a ji tana ta surutai. Wasa wasa da yake shi ba adili bane sai ya watsar da ita, wani ya bashi shawarar ya kawo ta asibiti amma sai yace shi ita kalau take. Har dai abun ya munana. Yar uwarta ce ta kawo ta nan bayan tayi yunkurin kashe kanta. Ana ta mata therapy dai ana fatan ta samu sauki. Shiyasa muke bayar da shawarar mutum ya dinga ziyartar likitoci yayinda yaji baya jin dadi. Yawanci abu yafi sauqin warkewa in an gano shi da wuri.” “Allah ya bata lafiya.” Salmah ta fada. “Ameen. There’s light at the end of the tunnel because naga magungunan suna mata aiki. Zata warke in sha Allah.” “Ameen.” Sun danyi tafiya kafin suzo wani daki. Ba su ga fuskar mutumin ba amma gashi nan suna hango shi an daure shi da igiyoyi. “Wannan kuwa ya taso cikin gata amma sai ya fada shaye shaye. Baya qaqqautawa sam a wannan harkar har ta kai abun ya taba masa kwakwalwa. Gashi nan shekararsa takwas anan amma bamu alamar warkewa a tare dashi ba. Muna cigaba da aiki dai.” “Kuma iyayen nasa suna nan?” “Su suka kawo shi nan. Suna biyan kudin asibiti amma ko zuwa basa yi. Sun ce an masa rehabilitation yakai sau hudu amma da an kwana biyu yayi kamar ya daina sai ya sake haduwa da abokan harkar tasa ya cigaba.” Salmah gaba daya sai taji kamar da ita yake. Yana nuna mata cewa zata haukace ita ma. Da kyar ta riqe kukan ta tana rarraba ido. Kallon Sheikh yayi. “Sheikh ka tuna kun kawo wasu rehabilitation centre din asibitin nan wata uku da suka wuce. Alhamdulillah duk ana samun cigaba akan yanayin nasu. Sai dai nace ma Allah ya saka da alkhairi da ka dauki nauyin biyan komai nasu. Ga shi kuma harda wata dawainiya ta daban.” “Dr ka bari mana kar kuma kasa ladan nawa ya zube.” Dariya sukayi. Sheikh kuma yana sane da yanayin Salmah. Yau da safe Alaramma Usama ya kira shi yace ai yaran da suka kamo a titi suka kaisu asibiti suna samun cigaba ga kuma lakcar da Sheikh din ya saka a dinga musu itama tana tasiri. Shine ya yanke hukuncin ya dauki Salmah su je su gansu. Ko kadan ba zai yi kuskuren sakata a cikinsu ba. Sai dai ya dauki duk wata hanya da ake bi da su ya na dora ta a kai. Dadewar da yayi ma dazun, yana ta yiwa likitan tambayoyi ne akan yanda suke saka mutum ya dena harka da miyagun kwayoyi ne. Sai da ya masa bayani tsaf sannan ne suka fito tare. “Allah ya bawa kowa lafiya. Zan je aiki ne yanzu text ya shigo min an kawo wani case. Bari mu wuce.” Da haka suka yi sallama ba tare da sun qarasa sauran dakunan ba da kuma shi kan shi rehabilitation centre din. Sanda suka shiga mota ya tayar, Salmah ta fara kuka. Sai da ya bari tayi ta koshi sannan ya faka motar a gefe. Wajen yayi shiri sosai. “Selmah,” sai da ta kalle shi sannan ya nisa. “Banyi hakan dan na tozartar da ke ba, ba kuma dan na saka ki kuka ba. So nake ki gane ni’imar da Allah ya miki. So nake ki gane akwai hope a rayuwa, ki gane cewa ko yaushe kofa a bude take na mutum ya gyara kansa kafin lokaci ya kure masa. Har gobe ba zan taba gaya wa wani halin da kike ciki ba a baya. Asirin ki nawa ne. Saboda haka ki kwantar da hankalinki. In har ina tare da ke, da yardar Allah babu abunda zai qara saka ki damuwa. Fahimti?” Gyada kai tayi. Sai da ya matsa ya mata sumba a goshi sannan ya kalle ta. “Allah ya miki albarka.” Sannan ne murmushi ya kwace mata. “Ameen. Saahibi. I love you.” Sai da ya sake kallonta sosai jin hakan ba tare da yayi tsammani ba. Bai yi magana ba ya tayar da motar su ka cigaba da tafiya gida. Sai can yace, “Ba ko yaushe nake son farin nan da ake min da ido ba.” “Toh ai shikenan.” Sai ta sake yi. “In ya tashi, izu ashirin yake gogemin daga kaina a lokaci guda.” Sai da tayi dariya sosai tana me gane inda zancen nasa yake. “So nake na goge duk sai mu fara daukar sabuwar hadda tare.” Kallonta yayi suka hado ido ta saki murmushi, tayi fari hade da lumshe idonta. Shima murmushin yayi. Sannan yace, “Saufa ta’arifi…” Yana dariya. Itama dariyar ta dan yi, har yanzu tana jin ta a yanayi na daban. Hakan na faruwa da ita duk sanda suka hada ido ko duk sanda hannunsa ya taba nata. A hankali take fahimtar larabci saboda yi mata da yake yi jefi jefi. Itama dai zata koya yanda zata dinga masa magana a cikin mutane ba tare da kowa ya fuskanci mai take cewa ba. Da ta iya, da ta kwatanta masa abunda take ji yanzun a ranta, a zuciyar ta, a kuma jikinta game dashi. Amma yanzu a Hausa abun nauyi yake mata. Allah ya kawo lokacin koyar larabcinta, zai yi bayani. **** Salmah na zaune da Hajiya suna hira a bangarenta Hajiyar ta gyara muryarta. “Kwana biyu baki fita makaranta ba. Qalau kuwa ko har kun gama jarabawar ne?” Sai da Salmah ta dan yi jim bata san mai zata ce ba sannan itama ta gyara muryar. “Matsala na samu da wasu a makarantar shine yace kar na sake zuwa. Zai nema min wata.” Yanda take hira da ita, a matsayin yayar mamanta take mata magana kuma mai bata shawara. Ba don hakan ba ba zata iya gaya mata Sheikh ne ya hana ta zuwa ba.+ “Ayya, ke kuma hakan ya miki?” Murmushi tayi. “Hajiya duk abunda ya zaba min yayi.” Hajiya ta dan yi shiru na daqiqa sannan ta kama hannun Salmah. “Ba hakan ba. Ke ya miki? In bai yi miki ba ki fada sai a mi shi magana.” Saukar da kanta Salmah tayi qasa bata bayar da amsa ba. Ita ta gamsu da matakin da ya dauka. Bai yi hakan dan ya cutar da ita ba. Sai dan ya gyara mata lamuranta. Suna zaune kiran wayar Uwale ya shigo. “Ya salam! Tun yaushe? Toh gamu nan.” Taji Hajiyar ta fada. Tana kashe wayar ta dube ta. Sai dai tayi ajiyar zuciya sannan ta kalli Salmah. “Malam Bello bai ji dadi ba. War haka ma yana asibiti.” Ba shiri suka tashi zasu nufi asibiti. Sheikh ba ya gida lokacin gashi basu da direba. Haka Salmah ta mishi waya ta fada masa zasu fita yace yana aiki kam yanzun sai dai suyi haquri su hau motar haya. Ba su ji komai ba suka fita. In dai yana da sarari ba zai kasa zuwan ba. Asibitin Nasarawa suka nufa. ***** Sheikh na zaune a ofis dinsa yana bin wasu takardu aka yi masa sallama. “Ya sheikh bakuwa ce muka samu.” “Yi mata iso.” Ya fada yana cigaba da dube duben. Ba a jima ba wata mata da ba zata wuce shekara talatin ba ta shigo. Daga kan da yayi dan ya amsa sallamar ne yaga duk bandeji a fuskarta ga hannun ta da alamar karaya a tare dashi. Wani takaici yaji ya taso masa tun kafin ta fadi matsalar da ta kawo ta. Sai da ya saka aka kawo mata ruwa ta sha, da alama ta debo rana sannan ta soma bayani. “Miji na ne ya min duka saboda yaro yayi laifi na dake shi.” Ta fada da raunanniyar murya. Sai da yayi ajiyar zuciya sannan ya ajiye takardun. Yanzu ya tabbatar idan aka wayi gari yaron ya tashi a wani iri, da mijin da mutanen gari, mahaifiyar sa zasu bawa lefi. Ita zasu ce bata bashi tarbiyya mai kyau ba. Da yawa basu gane cewa ita tarbiyya tafi kyau idan iyayen biyu suka hada kai suna bayar da ita. Amma maza da yawa sai suke ganin ba aikin su bane. Aikin mata ne. Sheikh dai ya danyi shiru yana jin kukanta. Sai ta bashi tausayi. Kuka take yi sosai. “Malama ko zaki bayar da adireshinki ko nambar mijin naki?” “Dan Allah nikam ba sai yazo ba. Kawai ya sake ni na huta Sheikh. Ko kotu zamu je na shirya zuwa.” Sannan ta sake fashewa da kuka. Ita kam ta gaji. Ya zata yi da namiji mai duka akan karamin abu. Yanzu akan ta manta tayi wani abu da ya saka ta sai ya mata dukan tsiya. Jiya jiyan nan yaron ta, tayi baqi ya hau kan cinyar bakuwar yana ta mata sukuwa. Tayi tayi ya sauka ya kiji. Da baquwar tayi magana sai yaron ya mata daquwa da hannu ya zageta. Hakan ya bata mata rai har ya sa ta saka hannu ta dake shi. Can ya tafi dakin baban nasa yana kuka. Bayan bakuwar ta tafi, mijin nata ya fito yana tuhumarta akan me yasa zata dakan masa dan shi. Bayani ta soma yi amma bai qarasa ji ba ya tunkude ta ta bugi dining table dinta har gefe ya fashe ya yanke ta a gefen kai. Sannan ta fadi akan hannun ta ya karye. Nan kuma ya rude ya wuce da ita asibiti aka bata taimakon da za’a bata. Da aka fara zancen a kawo police shine bai sake zuwa asibitin ba ya mata waya yace ta taho gida. Ba wannan ne karan farko da ya dake ta ba sai dai wannan ne na qarshe da zata iya dauka. Shi yasa ta wuce can Hisbah dan ta samu sauki. Tana zaune Sheikh ya kira shi ya gabatar da kansa yace yana son ganinsa a lokacin. Bayan minti ashirin sai gashi yazo yana budawa. Wajen zama aka bashi kafin a fara mishi tambaya. “Matar ka tace kai ne sanadin wannan rauni da take dauke da shi.” Kallon matar tasa yayi sannan ya kalli Sheikh. “A’a bani bane.” Ya fada. “To waye?” “Kaddararta ce haka. Daga dan tureta taje ta buge. Ai bani bane. Ba laifi na bane.” Sheikh dariya yayi. Ya kalli matar ya kalli mijinta. “Allah shi gafarta malam ba wajen wasa bane nan dukkan mu kuma ba yara bane. Gaskiya ne kana dukan ta ko kuwa sharri ta maka?” Sai da ya danyi shiru. “Gaskiya ne.” “A kan wani dalili? Idan karfi kake son nuna wa, ba mace zaka daka ba. Zaka iya tattaki har barikin sojoji ka samu daya ka wanke shi da mari. Daga nan sai ku kara kowa ya nuna iya qarfinsa.” Sun danyi dariya kafin sannan Sheikh ya bashi shawarwari sannan yace ya bawa matarsa haquri. Ya miqe kenan a ka dakatar dashi. “A’a ka tsaya akwai hukuncin bulala hamsin da na yanke maka. Zaka tsaya ka karbi kayanka. Ko da yake sarkin tauri ne kai ai.” Nan ya shiga zare ido. Bulala ana zaune qalau? Rabonsa da a dake shi tun yana qarami yana zuwa makarantar allo. “Masoyiyita Samira ba kince kin yafe ba?” Ya kalli matarsa. “Eh na yafe.” Nan ya gyada kai sannan ya kalli Sheikh. “Tace ta yafe.” Sheikh dai murmushi yayi. “Toh yayi kyau. Ta yafe nata saura nawa. Muje ka karbo guda talatin ba yawa.” Kamar wasa amma haka aka kama shi aka tafi dashi inda ake dukan. Wata dorina ce muradaddiya kamar za’a yi dukan doki da ita. “A riqe ka ko zaka iya?” Wani ya tambaye shi. Shi dai mutumin bai san sanda jikinsa ya fara rawa ba. Muryarsa ma tana rawa ya kalli wanda yake riqe da bulalar. “A…a…a… Ri..riqeee ni..” Ya fadi yana runtse idonsa. Matar sa kuwa yana gefe tausayinsa ya kama ta. Kamar taje ta karbe shi take ji. Ai da mutumin ya dake ya zabga masa daya a baya bai san sanda ya tsala ihu ba kamar yaro. Duk da tausayinsa haka dariya ta kubce mata. Ta juya inda ba zai ganta ba tayi ta dariya. Da kyar aka masa talatin. Sannan ya taho ko miqe wa baya iya wa. “Baka yi godiya ba Malam. Ko a qaro wasu talatin din?” Sheikh ya tambaye shi da sigar tsokana. Shi dai mutumin bai ko iya bude bakinsa ba. “Toh shikenan. Kama hannun matar ka ku tafi. Allah ya baku zaman lafiya.” Ba shiri ya kama hannun nata suka yi waje. Ita dai har suka isa gida tana riqe dariyarta. Wannan hukunci yayi mata. Gobe ma ya qara sake kawo qarar sa zata yi. Ta san dai ba zai sake ta ba. Ko da Sheikh ya koma ofis, jijjiga kansa yayi ya cigaba da aiki. **** Malam Bello dai jikinsa yayi zafi sosai. Nan take a ka bashi gado. Hankalin Uwale duk ya tashi daga sanda ta lura. Nan dai likita yazo ya bada sunayen magungunan da za’a siyo. Salmah aka bawa ta siyo a kemis din asibitin. Bayan ta fito ne taji ana kiran sunanta. “Mansur?” Ta fada cike da mamakin ganinsa. Shi kuwa da ya qaraso bai tunkareta da maganar da tayi tsammani ba. “Salmah ki yafe min. Na dauki alhakin ki. Ki yafe min.” Tayi mamaki sosai amma ta boye. Mamakinta a fili na ganin yanda duk yan canja kamannni ne. “Salmah HIV gare ni. Shekara biyu kenan da na gane ina dauke da ita. Damuwa ta saka ni ramewa…” Abu daya taji. HIV. Itama tana da ita innalillahi wa inna ilaihi raji’un “Baki da ita Salmah. Kin tuna abunda ya shiga tsakanin mu ai ba…” “Mansur!” Nan hawaye suka fara bin kumatun ta. “A ina ake dubawa. Zanje. Innalillahi.” A take ta manta da duk wani abu. Abu daya ne a ranta. Yanzu in tana dashi kenan Sheikh ma hakan? Haka tayi ta salati tajea gwada. Jikinta babu qwari ta qarasa ranar. Washe gari ta karbi sakamako. Sannan aka tabbatar ba ta da ita. Sai da tayi sujjudar godiyar Allah. Hankalin ta sosai ya tashi kuma bata gaya wa kowa ba. A take ta yaga takardar ta zubar. An rufe wannan shafin. Da alama komai nata a daidaice yake yanzu. Alhamdulillah. ***** Wasa wasa shekararsu uku da aure babu alamar ciki a tare da ita. Nan ta shiga damuwa sosai. Sheikh kullum yana gaya mata cewa komai lokaci ne. Duk yanda ta kai ga sauri in lokaci bai yi ba, abunda take so ba zai faru ba. Watarana ta dame shi ne ya dauke ta suka je asibiti. Sakamakon gwaje gwajen da suka yi ne ya caja musu kwakwalwa. Sheikh ya sani bai taba bata wani maganin hana daukar juna ba. Itama kuma bata taba sha ba. A bincike kuma ance sai ya shekara uku zai bar jikinta.+ Nan suka yi ta ta tunani har dai suka tuno da wannan abun da tasha. Wataqila a ciki aka saka mata. Allah masani. Basu dai sani ba amma ganin hakan yasa Sheikh ya fara musu rijista na makarantun da zasu karanta a Malaysia. Sosai Salmah taji dadin hakan. Watarana tana zaune tana game a sabuwar wayarta Sheikh ya shigo da yarinya biye a bayan sa. Da akwatin kayan ta kuwa. Taci kwalliya sosai tayi kyau. Da ganinta ma ka san daga gidan masu hali take. “Sunana Zubaidah.” Bayan nan bata qara komai ba. Ita Salmah ma bata ce komai ba. Har ta kwana biyar bai ce mata komai ba akan yarinyar. Bata saba yin shiru ba akan abubuwa amma akan wannan dai yin shiru tayi. Shirun ta koya tunda ya nuna yafi son haka. A rana ta bakwai bayan sun ci abincin dare ya kalle ta ya fashe da dariya. Gaba daya duk jikinta yayi sanyi. Tunani take ko aure yayi. “Gaskiya dole na bawa bakin nan nawa tukwuici. Irin wannan kokari haka?” Ita dai bata kula shi ba. Hmm kawai tace. “Toh mana ki dan yi murmushi mana Selmah.” Qarshe ma miqewa tayi zata rabu dashi. Sannan ya kamo hannun ta ya dawo da ita ta zauna. “Guduwa tayi daga gidansu. Akan babanta zai yi mata auren dole. A wannan kwanakin ina ta qoqarin nayi magana dashi ne yace baya nan. Toh yanzu dai gobe zan je mu gana. Sannan na nuna masa cewa yar sa tana gidana.” “Toh yayi. Allah ya bada lada.” Sam ba taji ta yarda ba. So take kawai taga yarinyar ta bar gidan. Shi shikenan sai a mayar masa da gida otel? Gidan tarar mutane barkatai? Wannan kam ba zata dauka ba. Ba zata iya ba. Hankalin ta bai kwanta da hakan ba. **** Sun tafi Malay da wata shida suka samu mummunar labari. Malam Bello ya rasu. Gaba dayan su suka zama sai a hankali. Walwalarsu ta bace bat. Musamman ma Salmah da take ganin yanzu ne lokacin da zata kasance tare dashi na tsawon lokaci sosai. Ba kadan mutuwar ta taba su ba. Sannan suka tabbatar mutuwa aba ce da take tunatar da mutane a hankali and in silence. Ba kowa yake daukan darasi ba daga mutuwa. Da an kwana biyu sai a cigaba da harka ba tare da an yiwa kai jarabawa ba an duba mai ya kamata a sake kimtsawa dan samun rayuwa mai kyau da zata amfani mutum a lahira. Sosai suka kara yawan ibadarsu domin samun rahamar Allah da kusanci zuwa shi. Ko wacce rana na qara kusanta mutum zuwa ga kabarinsa. Dama shi baqo ne a duniya. Yana da gidansa na gaskiya. Sai dai kuma shi wannan gidan hanyar sa dauke take da duhu. Kabari hanya ce ko gida ne ma’abocin duhu. A tare dashi akwai kunamu, akwai micizai, akwai tsutsotsi. Qasa ce birjik cikinsa. Sai dai kuma mutum zaya iya masa sabon gini tun yana duniya ta hanyar aikata aikin alkhairi. Kabari, gidane mai duhun gaske amma mutum zai iya haskaka shi da yawan alkhairinsa. Yin sallah akan lokaci, karanta suratul mulk na kare mutum daga azabar kabari. Kabari ba ruwansa, ko waye kai sai ya matse ka. Dauke yake da azaba iri iri. Shiyasa ake son mutum ya yawaita karanta. ‘Allahumma ajirni min azabil qabar.’ Allah ka min tsari daga azabar kabari. Irin wannan darasin Salmah da Sheikh suke yi da dare. Su qare da cewa, Allah yasa mu cika da imani. Da safe kuma, Salmah ta kan je sashen Hajiyarsa ta biya mata duk darasin da suka yi. Sosai take dawainiya da ita take yawan tunawa Sheikh da kula da ita sosai. In ya tambaye ta sai kawai tayi murmushi. “Kaine aljannata, Hajiya ce aljannarka. In ban taya ka kula da aljannarka ba dame zan taya ka? Bayan ni ka saukaka min komai? Da Abba ma yana raye hakan zanyi.” Tabbas tayi gaskiya. Hadisi sahih da aka karbo daga abu darda yana cewa lallai annabi sallallahu alaihi aassalam yace, maihaifi tsakanin kofofin aljanna. In ka ga dama ka yi wasa da kofar ko ka kiyayeta. عَنْ أَبِي الدَّرْدَاءِ قَالَ قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الْوَالِدُ أَوْسَطُ أَبْوَابِ الْجَنَّةِ فَإِنْ شِئْتَ فَأَضِعْ ذَلِكَ الْبَابَ أَوْ احْفَظْهُ سنن الترمذي كتاب البر والصلة باب ما جاء من الفضل في رضا الوالدين المحدث الألباني خلاصة حكم المحدث صحيح في صحيح الترمذي. Wani hadisin da aka karbo daga Mu’awiyah bin Jahimata alsalamiy cewa Jahimata yaje wajen annabi sallallahu alaihi wassalam sai yace ya rasulillah ina so naje yaqi shine nazo neman shawararka. Sai annabi sallallahu alaihi wassalam yace, kana da mahaifiya? Sai yace eh. Sai annabi yace ka zauna da ita saboda lallai aljanna na kasan kafarta. عَنْ مُعَاوِيَةَ بْنِ جَاهِمَةَ السَّلَمِيِّ أَنَّ جَاهِمَةَ جَاءَ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ يَا رَسُولَ اللَّهِ أَرَدْتُ أَنْ أَغْزُوَ وَقَدْ جِئْتُ أَسْتَشِيرُكَ فَقَالَ هَلْ لَكَ مِنْ أُمٍّ قَالَ نَعَمْ قَالَ فَالْزَمْهَا فَإِنَّ الْجَنَّةَ تَحْتَ رِجْلَيْهَا Sheikh bai san sanda ya riqe ta gam a jikinsa ba yayinda kwalla tazo idansa. Tabbas Salmah tayi kurakurai da yawa amma gashi yau itace mai tunatar da shi. Hakan yake so mutane su fahimta. Zai yi lakca akai. Duk sanda mutum ya qudurta nutsuwa da tuba a ransa, Allah zai taimaka mishi ya gyaru. Allah yana son masu tuba, masu tsarkakakiyar niyya. Sheikh zai gaya ma mutune, laifi komai girman sa Allah yana yafe shi. Allah madaukacin sarki da kansa yace kar da mutane da suka zalinci kan su (masu laifi) su cire rai daga rahamar Allah. Allah mai yafe dukkan zunubai ne. Ko yaushe shaidan zai cigaba da sakawa mutane a rai kamar ba za’a yafe musu ba. Duk sanda suka yarda da hakan kuma shaidan yayi nasara akan su. Allah ya kan shiryar da wanda yaso. Lallai Sheikh shaida ne. Shi ma Allah ya shiryar dashi, Allah ya shiryar da Selmahn shi. Ajiyar zuciya yayi yana cewa. Ya Allah ka yafe min da iyayena, ya Allah ya yafe wa muminai ranar da za’a yi hisabi. Rabbigfir li wal walidayya walil mu’umina yauma yaqumul hisaab. Ya Allah inni as’ulikal katmul hasanah. Rabbana atina fid dunya hasanah wa fil akhirati hasanah wa qina azaban naar. Ya Allah ina rokan ka, cikawa mai kyau. Ya ubangijinmu ka bamu mai kyau a duniya, ka bamu mai kyau a lahira, ka kubutar damu daga azabar wuta. Bayan shekara goma sha biyar. “Mama, wani satin zan kammala haddar izu sittin dina. Mama za’a kaini makka ko?” Huzaifah, ya tambaye ta. Yaron shekararsa sha biyu. Kuma shine yaronta na farko. “Mama nima ai za’a kaini har da Madina ko?” Inji Isma’il. Salmah shiru tayi tana kallon su, suna musu. Ita kuwa zai aikin karance karance take yi kafin su suzo su ishe ta. Sun gina Islamiyya kuma ita ma tayi karatu mai yawa a tsawon shekarun shiyasa ma da kanta take yi wa yan mata da iyaye karatu. Duk yaranta a islamiyyar suke. Kuma a tsarin makarantar tasu mai suna Darul Ilm, in dai aka kawo yaro hana shekara biyar. A shekara shida da shiga makarantar zai kammala haddar qurani hade da sanin fassarar. In yayi nisa, yaro yana shekara sha biyar ya gama haddarasa, wasu har a sha daya suna gamawa. Ba sa daukan dalibai da yawa. Amma duk sanda suka yaye dalibai suna kai su makka tare da tallafin iyayen. Kadan daga cikin kudin iyayen suke bayarwa su kuma su dauki nauyin ragowar.+ “Huzaifah, Isma’il. Hasbukum. Kowa idan ya gama, za’a kai shi. Tamam.” “Shukran Mama!” Duk su biyun suka fada suna tafiya falonsu. Ajiyar zuciya tayi sannan ta miqe kafarta. Ta kusa haifar dan ko yarta na uku. Rufe littafan gabanta tayi ta dan rufe idonta domin ta danyi gyan gyadi sai taji hannu a bayan ta. “Huzaifah barci zanyi. Kuje wajen Abiy ya muku tadrib ko kuje wajen kakar ku.” Murmushi Sheikh yayi sannan ya matsa kafadarta hade da yi mata sumba a kumatu. “Sheikh ne Mama.” Sannan ya zagayo ya zauna a gefenta. “Toh a kyale ni nayi barci kadan. Kai ma kan ka wani yaron ne.” Ta fadi tana bata fuska. Murmushi yayi sannan ya shafa fuskarta. “Ki sha barcin ki lafiya Mama.” Bai biye mata ba saboda tun farkon wannan cikin tabi ta canja masa kamar ma haushinsa take ji. Yasan ba ko mai ya jawo hakan ba sai hormones dinta. Can wajen kafarta ya koma, ya kama kafar yana mata tausa har ta fara barcin. Murmushi yayi sannan ya zauna a kusa da ita yana kureta da ido. Yana zaune Isma’il ya shigo. “Mama! Huzaifah ya tsinkan miki fulawa.” Ganin Sheikh ya saka ya nutsu. “Abiy ba san kana nan ba. Ka sani ai ko? Ana asif. Kayi haquri. Salama alaikum?” Ya lanqwasar da kai. Sun tarbiyartar dasu akan kar su taba shiga waje ba tare da sallama ba kuma kar su shigo sai an basu izini. Amma wataran in dai kawo kara ne da gudu suke zuwa. Sheikh fada yake sosai amma Salmah tace masa yara ne kuma zasu daina. Isma’il, sosai yake kama da Sheikh har yanda yake abubuwa shigen na babansa yake yi. Salmah wataran har haushi take ji akan hakan. “Wa’alaikumus salam Isma’il. Shish. My queen is sleeping.” “Nima idan na girma, Zahara zata zama queen dina?” Ya tambaya. “Man hiya Zahara?” Duk da ana larabci a islmaiyyar, ba sosai ya zauna kan harshen yaran ba shiyasa suke sirka musu dashi a gida. Duk su biyun sun yi kwas din koyan larabci shekarun baya. “Fi fasli. Hiya Jameelah wa humairah misli Mama.” A ajinmu take. Tana da kyau da haske kamar Mama. “Ba ruwanka da ita. Sai ka girma zamu daukota ta dawo nan ko?” Gyada kai yayi sannan ya fice a guje. “Ni duk kun dame ni.” “Sarkin mita sai ki tashi sallar la’asar ai. Bari na taimaka miki.” Da hakan ya dauke ta cak har inda zata yi alwalan. **** Salmah ta haifi mace an saka mata sunan Hajiyar Sheikh. Hauwa. Suna kiranta da Mimi. Haka rayuwa ta cigabar musu. Ayi wasa da dariya. Ayi fada a shirya. Rannan Salmah an gayyace ta wani biki taje ta dawo take ta kumbura. Gaba daya Sheikh ya rasa kanta. STORY CONTINUES BELOW “Wai me ya faru ne? Ni wannan kumburin yana taba min zuciya. Laifin me nayi?” Sai da ta sake dadewa a hakan har zuwa dare bayan sun kwanta sannan ya sake tambayarta ko yayi abu bai sani ba. “Ba a wajen bikin bane.” Ta tura baki. Shi dai yau yana ganin ikon Allah. “A kayi me?” “Wata take ta yabonka take gayawa kawarta wai kullum sai tayi addua akan ka. Har qiyamul layli take yi. In aka amsa mata kuma fa?” Sai da yayi dariya sosai sannan yaja hancinta. “Toh wai ita wannan din da tabi ta tayar mana da hankali balarabiya ce ko me?” Harara kawai yasha. “Zan so na ganta. Wataqila mu daidaita.” “Sai kuyi tayi ai.” “Matar Sheikh kenan. Ban yi miki alkwarin ba zan qara aure ba saboda bani nake riqe da kaddarata ba. Amma ina son na gaya miki ko mata dubu zan aura babu wadda zata kaiki a wajena. Kinji?” Juyawa tayi. “Bai min dadin ji ba.” “Wataqila sai na chanja salon…” “A’a ni ban ce ba.” “Ala ayyi waqat, ayyi sa’ah wa ayyi dakika, anta fil qalbi. Uhibbuk jiddan wa katheer. A kowanne lokaci, ko wanne awa, ko wanni minti, kana zuciyata. Ina son ka sosai, da yawa.” Bayan wannan kalaman nata, ta san qarshen zancen nasu musamman da taji bai bata amsa ba da bakinsa. Da safe kuwa gaba daya ta manta da cewa zaiyi tafiya. Sai da taga yana shiri ta tuna. A sati baya wuce kwana uku take samun lokacinsa. Kullum yana ta zirga zirgar da’awa da abubuwa makamantan su. Babu sauqi sam zama matar Sheikh amma kuma it’s worth it. Bata taba nadamar kasancewa matar Sheikh ba. Ta san har a gobe ba za’a rasa masu son zama matan mijinta ba. Sai dai abu daya da take da tabbas shine ba zasu iya ba. Ba zasu jure ba ko da kuwa zata karantar dasu yanda zasu bi dashi. Ba wanda yasan sirrikan da ta boye. Ba wanda yasan abubuwan da ya mata. Sai dai kawai tayi godiya wa Allah. Komai ya wuce. Alhamdulillah. Bayan tafiyar Sheikh kafin ta fita makaranta ta bude shafinta na Instagram ta rubuta. Zuwa ga wanda aka yiwa fyade, Zuwa ga wanda rayuwa ta matse musu, Zuwa ga wanda suke neman soyyayar iyaye, Zuwa ga masu burririka. Kuyi haquri ku dage da addua. Ku dogara ga Allah. Komai mai wucewa ne. Watarana sai labari. Sauyi zai dauki lokaci, ganin sakamako zai dauki lokaci, haquri da wahala, juriya da wahala amma a qarshe sakamakon sai wanke duk wani hawaye. Da hawayen ta qarasa rubutun. Bata yi posting ba tukunna. A draft ta ajiye shi. Ajiyar zuciya tayi, sannan ta sake hamdala. Qawayenta Sheikh bai qara bari taje inda suke ba amma shi din yace mata ya saka su a makaranta. Labari mara dadi shine Raudah ta sha abu taje tayi hatsari. Nan take ta rasu. Abun yayi wa Salmah ciwo da ta samu labarin. Da ita ma bata daina ba, da hakan ya faru? Ya Rabbi. Allah yaji kan Raudah. Bata mantawa ta bayar da sadaqa dominta. Komai mamaki yake bata. Wai ita ce nan. A matsayin da bata taba hangowa ba ko mafarki. Tayi karatun da bata taba zaton zata yi ba. Gata nan mutane da dama suna fatan zama irinta. Ba su sani ba, abun babu sauki. Ta sha wahala kafin tazo gabar da take. Amma zata bawa ko waye shawarar canzawa zuwa mutum nagari. Ba abune mai sauqi ba tabbas, amma qarshe mutum zai godewa kansa. Ance komai lokaci ne. Bata taba yarda ba sai yanzun. Fatan ta daya, yaranta su girma cikin imani da aminci. Ta yadda bazasu taba mantawa da ita a rayuwa ba. Tashi tayi ta dauko wayarta ta kira Uwale wadda anyi anyi da ita ta dawo gidan su Salmah taqi. Wai kunyar surukai. “Uwale na, Allah ya saka miki da aljanna.” Haka tace yayinda Uwalen ta dauki wayar. Sai da Uwale ta share wata kwalla. “Salmah, Allah ya miki albarka. Nagode, ko yau na koma wajen mahallicci na, ba ni da nadama. Allah ya miki albarka.” Da Salmah ta amsa da amin ta kashe wayar, sai ta lanqashe a waje daya tana kuka. She couldn’t believe it. The reality was making her emotional. It was too overwhelming to be true but there was it, the reality and the truth. She’s there, all sleek and fine. And mafi muhimmin abu shine, Matar Sheikh ce ita. Allah ya mishi albarka. Ta godewa Allah da ya sako shi cikin rayuwarta. Ta godewa Allah da ya shiryar da ita. Tana fatan duk wani mai laifi irin nata ko makamancinsa zai shiryu wataran. Alhamdulillah. **** Salam alaikum. Fatan kuna lafiya. Alhamdulillah! Finally! Kurakuren dake cikin littafin nan wanda nayi a bisa rashin sani ko ajizanci na dan Adam, Allah ya yafe min. Alkhairan da suke cike Allah yasa su amfane mu.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE