MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 11
MEYE ILLAR YAYA MATA
CHAPTER 11
Tana karasawa taga ko motsi baya yi gajini yana zuba ajikinshi tako Ina ihu ta saki tare da kuka, driver din da suka zo tare yazo Ya fara kokarin daukanshi Dan suje asibiti amma Ya kasa, ya kalli mutanan dake wajan yace dan Allah ku taimaka mu sashi a mota kowa dake wajan yaki tare da fadin babu ruwan mu wannan case din police nejin haka yasa zainab da tayi zaman durshan a kasa take ta kuka yasa ta tashi suka kamashi ita da driver suka wuce dashi asibiti suna zuwa akai emergency dashi inda aka fara dubashi ganin bai mutu ba yasa aka sa mishi oxygen domin numfashin shi ya dai daita, driver ne ya kira gidan amma basu dauka ba dan suna can suna ta hidiman birthday, lokacin da za‘a yanka cake duk yan uwanshi mata suka tsaya kusa dashi Alh Ibrahim yace Ina zainab, sai a sannan kowa Ya fara dube dube, khairat tace, ta flta tace mun zata ta dawo, alh Ibrahim yace zuwa ina? Khairat tace Wlh nima ban sani ba, daukan wayanshi yayi da nufin kiranta yaga miss call din driver, yazo zai kira zainab din kiran driver din ya kara shigowa, dauka yayi tare da fadin hello, driver yace ranka ya dade gamu a asibiti da zainab mijinta babban mota ta bigeshi rai a hannun Allah Alh Ibrahim sakin wayarshi yayi tare dayin salati, mama tace lafiya kuwa? Yace zainab na asibiti yazeed yayi hatsari babban mota ta bigeshi, kowa salati ya fara ita kam Amina tsoro ne ya kamata Kar dai ace saleh ne ya aikata hakan, fita sukai su duka suka nufi asibitin inda suka ganta zaune a kasa kusa da d’akin da yake ,dukansu sun tausaya mata, ummi ta nufeta tare da tabata rungume ummi tayi tana kuka tare da fadin ummi shikenan yazeed, ummi bana son ya mutu ummi ku fad’a mishi ya tashi da wuri, alh Ibrahim dake tsaye cikin tausayin y’ar tashi ya matso kusa da ita yana share mata hawaye tare da rungumota jikinshi wannan ne Karo na farko da mahaifinta ya taba yi mata irin haka, yace kiyi hakuri zainab zai tashi insha Allah Kinji, nan Alh Ibrahim yaita bata baki tare da rarrashinta suna nan zaune har dare domin suna son ganin farkawanshi, wasu daka ciki har sun Fara d’an gyangyadi, saleh dake asibitin tun dazu a boye Ya samu ya shige d’akin dai dai lokacin yazeed din ya fara kokarin d’aga hannu saleh ya girgiza kai yace Allah sarki yazeed banyi niyyan kashe ka ba, bude ido yazeed yayi yana kallon sale, yaci gaba da fadin amma babu yanda na iya dole ka mutu tunda kaji komai eyya kayi hakuri yazeed harda matso kwalla lokaci daya kuma ya share tare da cirema yazeed oxygen din, nan ya fara zuba tare da zare ido ko minti uku baiyi ba da cirewa ba yazeed ya rasu. yana ganin haka yayi saurin mayar mishi yabar d’akin, yana fita Abun ya fara kara farkawa sukai tare da shiga d’akin da gudu Dr shima yazo amma ina rai yayi halinsa Amina najin haka ta fita Tana kuka tana fita suka had’u da saleh da hannu ta nunashi alaman kai ne? Yace Nina kashe shi kuma duk saboda asirinki yaci gaba da rufuwa dan haka Kinga taflya ta, Amina zama tayi a wajan Tana kuka mai cin rai tare dayin dana sanin da saleh ya zamo d’an uwanta, ita kam zainab tunda Dr ya fad‘a Ya rasu gaba d’aya ta kasa kuka sai kallonsu take da ido tana musu kallon kaman basu da lafiya, Maman yazeed taci kuka d’anta kwaya d’aya yabar duniya, haka aka dauki gawarshi zuwa gidan Alh Ibrahim ruwan da akeyi gashi yamma tayi yasa dole sai gobe aka bari a birneshi gidan Alh Ibrahim aka Kai gawar nashi, Kafin gari ya Waye har Labarin mutuwar yazeed ya baza ko Ina, zainab kam tun jiya ta kasa kuka hankalin Alh Ibrahim ya tashi Sosai domin yasan rashin kukan nata hatsari ne, yan uwanta mata babu abunda suke sai kuka tare da tausayin y’ar Uwar tasu, lokacin da akayi ma yazeed sutura mahaifiyarshi ta mishi addu‘a tanayi tana kuka ita kam zainab koda tazo kallon gawan tayi da mutanan wajan tace miye haka zaman miye kukeyi mai yasa kuke kuka maiya sami
yazeed bashi da lafiya ne, kowa dake wajan mamaki yake tare da tausaya mata ummi ce ta
ru’ko mata hannu tare da fadin zainab yazeed ya mutu, kwace hannunta tayi tare da fadin a’a ummi ba mutuwa yayi ba, mutuwa in anyi ba’a dawowa yazeed bazai mutu yabar niba ban yarda ba, ummi tace zainab yazeed ya mutu bazai taba dawowa ba ya tafi kenan har abada wani irin ihu ta saki Wanda ya razana mutanan wajan tare da fadin shikenan yazeed lokaci d’aya ta Fara kuka ganin haka aka dauki gawar aka wuce dashi zainab kuka take mai shiga rai tare da fadin shikenan Ya taf’l ya tafi kace bazaka taba bari naba mai yasa ka tafi ka
barni, duk Wanda yake wajan saida yaji tausayinta Sosai …….
Haka aka Kai yazeed gidanshi na gaskiya, mutane nata zuwa musu gaisuwa, zainab ta koma Abun tausayi lokaci kad’an, Dr din data amshi haiyuwar faruk da saleh ya kama wasu yara suna buga kwallo sukajefa gidan saman wani yaro yaje daukowa yaga tsohuwar daga shiganshi ta kirashi tare da bashi takarda tace yakai mata gidan su yazeed tare da kwatantamai, yaron Ya tafi a lokacin su zainab duk sun koma gidan mum din yazeed ana amsar gaisuwa, koda yaron yaje gidan ya rasa wa zaiba takardan can ya hango ummi ya bata yace gashi Wai a bama yazeed, ummi ta amsa Tana hawaye zama tayi zata bude dai dai lokacin Alh Ibrahim ya kirata ajiye takardan tayi ta tafi wajan mijin nata koda taje yace zainab ta samu taci wani abu kuwa? Tace a‘a babu yanda Banyi ba amma taki ci, alh Ibrahim cikin jin tausayin y’ar tashi yace ki kara gwadawa Kar a barta da yunwa ummi tace
toh Bari inje in sameta.
Koda saleh ya koma gidan da yake yaje da nufln kashe tsohuwar shake mata wuya yayi ta Fara fadin ka kashe ni babu komai domin ko yanzu na mutu zanyi farin ciki domin nasan yazeed zai fad’a Dan na tura mishi message akan kana son kashe shi dan haka babu damuwa kuma yaji komai zai fadama Alh Ibrahim, saleh najin haka Ya saketa tare da wanka mata Mari yace bazan kasheki ba sai na nemo letter din zan kashe ki Shegiyar tsohuwa Yana fadin haka Ya flta, kiran Amina yayi ta tashi ta fita da sauri ta dauka yace amina wannan Shegiyar Dr din ta rubuta letter tasa a kawo ma yazeed bata san Ya mutu ba, dan haka kisan inda letter din yake Kar wani ya gani domin ta rubuta komai a ciki, amina tace ka gani koh saleh yanzu miye Abun yi? Yace ki nutsu ki duba abunda nace kawai tace toh, koda su alh Ibrahim zasu tafi ummi tace zata zauna da mum din yazeed da zainab a gidan, Amina tayi caraf tace a’a ita zata zauna dasu ummi ta koma Gida, ummi taji dadin karan da amina tayi dan haka suka tafi, cikin dare Bayan kowa Ya kwanta, amina ta fito falo tana haskawa da waya ko zata ga letter din, kunna wutan falon akayi cikin tsoro ta waiga ‘taga zainab ce, amina ta Fara in ina tare da fadin nazo insha ruwa ne, muje nama sha, komawa sukai ciki, Amina kasa bacci tayi sai juyi take tayi, kwanan su uku a gidan amina na neman letter din amma bata gani ba, zainab na zaune rungume da hotan
yazeed tana kallo tare da kuka, mum din yazeed ta shigo cikin tausayin zainab din ta zauna kusa da ita tare da janyota jikinta tana fadin kiyi hakuri zainab addu’a za muyi ta mishi domin shi yafi bukata sannan addu’a itace babban gata da zamu nuna masa kiyi hakuri Kinji? Kai ta d’aga alaman eh cikin kuka tace mum Kafin yazeed ya rasu akwai abunda yake son fad‘a min, mum dinshi tayi caraf tace Nima ya kirani ranan da yayi hatsari yake fadamin akwai matsala a gidanku muna cikin maganan wayan ya yanke naita nemanshi ban samu ba kuma yanda naji yana maganan a tsorace yake, toh ban dai San miye matsalan ba na Fad’a miki hakan ne dan nasan Kema kiran da yake ta miki kenan, yana son fad’a miki,mum ta canza maganan da fadin ki shirya kayanki yau zaki koma gidanku, da sauri zainab ta kalli mum din tare da fadin mum bazan koma ba tare zamu zauna ni dake ….. Maganan ummi sukaji wacce take fadin zainab hakuri za kiyi kizo mu tafi zainab tace ummi bazan iya tafiya inbar mum ta zauna ita d’aya ba a wannan gidan, mum tace zainab Nima yau zan tafi kano wajan yan uwana bazan Zauna ba dama saboda yazeed nake zaman kaduna yanzu baya nan zaman mai zanyi? Zainab Kuka take akan Kar mum ta tafi amma mum tace bazata iya zaman gidan ba domin zai dinga tuna mata yazeed Sosai, haka suka shirya gaba daya suka tafi, Amina taji dadin hakan domin tasan babu Mai ganin letter din yanzu tunda an rufe gidan, saleh ta doka ma kira yana dauka yace Anga letter din? Tace a’a amma rufe gidan kowa yabar gidan, ajiyan zuciya yayi tare da fadin yanzu hankali na ya kwanta yau zan koma in kashe wannan tsohuwar likitan, yana fadin haka ya kashe wayan, gidan ya nufa direct Wanda rabon shi da gidan kwana biyu kenan, yana shiga yaga baiga tsohuwar ba duba wajan yayi duka bai ganta ba, fita yayi yaje gidanta Wanda Ya satota shekara ishirin da wani abu, koda yaje ya Tarar da gidan a kulle wata mata ya gani kusa da gidan tana wanki yace dan Allah mai wannan gidan fah? Tace an saceta jiya ta dawo kuma a jiyan Allah yayi mata rasuwa, yace Innalillahi’wa inna’ilaihira jun, tare da goge hawaye yace Kai rayuwa kenan Allah yaji qanta matar ta amsa da Ameen sannan ta tashi tayi ciki, matar na barin wajan yayi wata Shegiyar murmushi tare da fadin kin hutar sheni daukan zunubi ban kashe kiba kin mutu da kanki, yanzu babu wani mai tauna asiri kuma tunda wanda suka San
Abun sun mutu yanzu daga ni sai Amina.
Koda zainab ta koma Gida tunanin
maganan da mum din yazeed ta mata take tayi, itama in bata manta ba sanda suke waya taji kaman a tsorace yake yanda yake magana ‘kasa ‘kasa, khairat ce ta kirata akan tazo police din da suke bincike akan mutuwar yazeed sunzo domin suna son sanin Wanda ya bigeshi mai yasa ya gudu, koda tazo police din yana fadama Alh Ibrahim sun gano number din motar amma basu San inda zasu ga mai motar ba suna dai kan bincike ne sannan hatsarin daya faru bigeshi akayi da gangan, zainab ta girgiza Sosai, dan haka ta shige d’aki ta dauko hotan yazeed, d’akin zarah ta nufa akan suzo su rakata wajan da yazeed yayi hatsari zarah bata musa ba dan a halin yanzu suna matukar tausayinta fita sukayi su duka matan, harda Abubakar mijin zarah shine yake tuka su, koda suka je wajan nuna ma mutane hotan yazeed zainab take tayi wai ko sun sanshi amma kowa sai yace a’a har zasu wuce taje wajan yaran da suke buga kwallo ta kamo hannun wani yaro tace ka taba ganin wannan? Yace a’a yaron yace Anty yana da kyau Ya sunanshi koda na ganshi d’an murmushin takaici tayi tace yazeed tare da barin wajan yaron shuru yayi yana tunani yazeed kaman na tabajin Sunan har zata shiga mota yaron yace Anty zainab ta waigo yazo wajanta da gudu yace kwana uku da suka wuce wata tsohuwa ta bani letter in Kai ma yazeed naje gidansu nakai naga mutane da yawa, zainab tace letter? Ina tsohuwar data baka? Yaron yace ta rasu, zainab tace ngd, mota ta shiga tace zarah muje gidan su yazeed mu duba letter din Abubakar yace kina tunanin zamu gani? Tace eh zamu iya gani, zarah tace toh amma gidan ai a rufe yake, zainab tace zamu iya shiga ta windown baya muje kawai ….. Hmm toh muje zuwa muga ko za suga letter din sannan miye tsohuwar nan ta rubuta a ciki duk ku biyo ni ……