MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 12

MEYE ILLAR YAYA MATA 
CHAPTER 12
Koda suka isa gidan, kowa yana ta dubawa amma basu gani ba sai bude bude suke amma shuru, dukwani inda takarda take sun duba amma shuru babu shi, zarah tace Kai Wlh na gaji wannan takardan bata gidan nan, zainab dai bata ce komai ba sai dubawa take, komawa falo tayi inda ta Fara duba kujeru Tana d’aga 3seater saiga wata takarda ta fad’o d’auka tayi ta bude ta Fara karantawa kuka ta saki mai karfi wanda yasa yan uwan nata fitowa da sauri Abubakar ne ya amshi takardan ya fara karantawa kaman haka ‘yazeed rayuwanka Tana cikin hatsari domin naji saleh yana waya zai kashe ka Dan haka ka kula sannan ka tabbatar ka fad’ama Alh Ibrahim abunda suka boye mishi tsawon shekaru masu yawa dan Allah kayi kokari ka fad’a ko na sami salama’ khairat tace saleh shine ya kashe yazeed kenan? Sannan mai ake son a fad’ama Abba? Zainab tunanin wayan da sukai da yazeed ta farayi Kafln ya rasu, lallai gaskiyan police ne kashe yazeed akayi kuma saleh shine ya kashe mata miji fita tayi tare da fadin kuzo muje Gida, binta sukai a baya zarah saida ta rufe 
window din sannan suka nufi Gida. 
Koda suka karasa gida motar police suka gani, alamun police sun zo, da sauri suka karasa, dai dai lokacin da police din yake fadin saleh shine ya bige yazeed mun kama mai motar ya shaida mana ya bama saleh hayar motar ne inda ya bige yazeed din sannan yaba mai motar kudi mai yawa, kowa dake wajan Ya girgiza musamman amina domin ita zufa yake ta keto mata, police din yace muna bukatar matarka ta kirashi inda zaifi mana saukin kamashi, tunda y’ar Uwar shice, kallon Amina yayi da idonta ya ciko da kwalla ga kuma tsoro yace Amina kirashi, bata musa ba dan Kar Ayi zargin wani abu kiranshi tayi tasa speaker tace kana Ina inzo? Fad’a mata inda yake yayi tace gani nan tare da fad’in kizo min da kudi dan banda kudi a wajena Sosai tace toh tare da kashe wayan. 
Bayan Amina sun had’u da saleh police dasu Alh Ibrahim dake binta a baya suka fito, nan aka kama saleh, kallon Amina yayi yace ni kika cuta kika ci amana ta duk rufa miki asiri da nayi, Nayi kisan Kai saboda in boyema duniya da mijinka cewa faruk ba d’anki bane d’a nane ke mace kika haifa Amina tana ta girgiza mai kai alaman yayi shuru amma shi ina fad’a yake kin cuceni tare da fad’in mace kika haifa faruk d’ana ne, alh Ibrahim da gaba d’aya wutar lantarkin dake kanshi ya dauke duk watajijiya dakejikinsa ya tsaya dan tsabagen kaduwa, police sukai gaba da saleh,,,,
 Abubakar ya kama Alh Ibrahim suka koma Gida wanda inda za’a gwada jininsa zai Kai d’ari biyar dan Tashin hankali, suna shiga ya zauna a kujeran falo yana fad’ama mama abunda Amina da saleh sukayi faruk kam babu abunda yake sai kuka da ba’kin cikin abunda saleh ya aikata tare da takaicin shine ubanshi Wanda yayi sanadin mutuwar mijin yayarshi, Amina ce ta shigo falon Alh Ibrahim ya tashi cikin zafin nama tare da fad’in Amina kin cuceni Allah ya isa tsakani na dake, dan haka ki flta ki bar min gidana yanzu bana bukatar in sake ganinki sannan ki kawo min y’ata duk inda take, ummi tace babu inda Amina zata kowa waigowa yayi yana kallon ummi cikin mamaki taci gaba da fadin Amina bata da laifi kaine mai laifi kaida mama da kuka nuna 
kuna son d’a namiji kowa yasan da wannan burin naka, bako wace mace bace zata iya jure ba’kin cikin dani na kunsa ba wajan shekaru ishirin da wani abu ba, saboda na haifi y’ay‘a mata, ganin yanda ake min a gidan nan da nuna min dani da babu duk d’aya ne dole yasa Amina ta boye abunda ta haifa tunda inka gani ba zaka amshi kaddara ba , shin MIYE ILLAR Y’AY’A MATA da yasa baka son su? Yanzu gashi Allah ya nuna maka baka isa ba gaba d’aya yaranka mata ne bai baka namiji ko guda d’aya ba, alh Ibrahim yace hakane Allah ya nuna min iyakata lallai na aikata babban laifi kubra ko hakkin ki dana danne na matsayin matata Allah bazai barni ba, ina miki hukunci akan abunda bake kike bama kanki ba sannan ina nuna butulci akan abunda Allah Ya bani, mai makon in gode mishi sai na tsaya zaba, wanda wasu suna nan basu taba haiyuwa ba amma ni Allah ya bani Ina butulci, kubra dan Allah ki yafe min duk da Nasan ba abu bane mai sauki ki yafe min amma ….. Tace ban taba ri’keka ba duk abunda kamin na yafe maka duniya da lahira, godiya yaita mata tare da kallon Amina yace zaki zauna ne saboda kubra yana fadin haka ya haura sama, Amina ta matsa kusa da zainab dan tayi mata magana zainab na ganin ta matso tabar wajan domin babu komai cikin ran zainab sai tsananta, kowa Ya watse a falon, Aneesa da magajiya suna zaune suna tattaunawa akan maganan Aneesa tace yanzu amina itama zata zama Abun tausayi, gidan zai koma hannun ummi, magajiya tace nidai burina mu zauna a nan har abada, aneesa tace uhm karki damu gidan zai zama nawa bada dadewa ba, magajiya tace taya Bayan faruk ba d’ansa bane, aneesa tace zaki gani Kedai kawai ki zuba min ido tunda yanzu Ya gano ba d’ansa bane zai dinga jin tausayin shi Sosai…. Koda yake Kedai magajiya kisa ido kiyi kallo. 
Ummi tana d’aki tana taba Alh Ibrahim baki akan yayi hakuri, yace bazai taba samun nutsuwa ba har sai yaga y‘arsa, Amina ta shigo hannunta dauke da hoto, yana ganinta yace maiya kawo ta d’akin shi? Tace kayi hakuri na kawo maka hotan yarinyarka ne, da sauri ya amsa tare da fadin tana Ina yanzu Nima ban sani ba amma saleh yace min Tana tafa wajan wata mata yace ana kula da ita Sosai ummi tace yanzu abunda ya kamata sai kaje prison ka sami saleh ya fad’a maka yace hakane yanzu kam zani ma ….. Hmm
Koda alh Ibrahim yaje wajan saleh, Bayan anyi mishi lso, saleh da yaga alh Ibrahim ya fara dariya tare da fadin Nasan zaka zo dama Nasan zaka zo, gashi kuma kazo, alh Ibrahim yace saleh ina son ka fad’amin inda yarinya ta take, saleh ya bushe da dariya tare da fad’in in kana son Kaga inda y’arka take Toh kasa a sakeni, alh Ibrahim yace Kai yanzu har kana tunanin a sakeka? Saleh yace kwarai kuwa domin bada manufa Nayi laifin ba, alh Ibrahim yace kama daina wannan tunanin ina son ka fad‘amin inda zanga y’ata, saleh yace koda zaka mutu bazan taba fad‘a maka inda take ba, sai kaje kaita nemanta, babu yanda Alh Ibrahim baiyi ba amma sam saleh yaki fad’a mishi inda zai ga y‘arsa, haka ya dawo gida rai bace, kowa Ya shigo gidan ya Tarar da ummi na zaune a falo daga gani Tanajiran dawowan shine, tashi tayi ta nufeshi tare da fadin an dace kuwa? Kai ya girgiza mata sannan yace yaki fad’amin, amma tunda ina da hotan ta zamu tafi muje muga ko Allah zai sa mu ganta, alh Ibrahim yaci gaba da fad’in ban taba ganin mace mara imani ba kaman Amina ka dauki d’anka na cikinka, ka bada shi a kaishi wajan da baka san ko Ina bane wannan rashin imanin yayi yawa sai kace ba mace ba, Amina dake sama tana jinsu ta sauko Tana kuka tare da fad‘in Wlh kullum da tunanin yarinyata nake kwana nake tashi abunda yasa hankalina yake kwance saboda saleh yace min Tana lafiya, lumshe ido yayi sannan ya bude cikin takaici yayi sama, ummi itama binshi tayi Amina kam zama tayi a nan tana kuka. 
Washe gari alh Ibrahim shida Abubakar suka shirya dan zuwa tofa nemo yarshi, kowa ya musu fatan alkhairi sannan suka tafi, koda suka isa tofa hanyar abuja, hotel suka kama dan su huta amma shi alh Ibrahim kasa zama yayi daukan hotan yarinyar yayi ya fita Abubakar dake d’aki yana kallon window ya hangoshi da sauri ya nufeshi yace abba Ina zaka? Yace zani dubo tane, Abubakar yace Toh muje tare, fita sukai a kafa ba tare da driver ba, duk Wanda suka gani sai sun nuna Mai hotan ko ya Santa amma sai suce a‘a haka sukai ta yawo duk sun gaji, wani mai dafa indomie suka hango suka nufeshi tare da nuna Mai hotan kallon hotan yayi sannan yace nawa zaku biya in kaiku? Alh Ibrahim zaro kudi yayi masu yawa ya bashi, amsa yayi yana Washe baki yace muje in kaiku inda take, alh Ibrahim cikin jin dad’i suka bishi, tafiya suke suna shiga wani lungu lungu koda suka je kofar wani Gida da mata ne da maza birjit wasu na shaye shaye wasu na manne dajuna, alh Ibrahim yace ma mutumin Mai mukeyi a nan? Mutumin yace zan kaika wajan yarinyar ne, alh Ibrahim ya kalli Abubakar cikin damuwa, dakyar dai alh Ibrahim ya shiga gidan inda bakajin karan komai saina kid’a, suna shiga gidan yaga ana ta rawa mata da maza, idanshi ya sauka akan yarinyar shi wacce itace shugaban rawar ga wani namiji yana ta mammanneta ido ya bude cikin tsoro shiko Mai indomie wajanta ya nufa ya mata magana akan Tana da ba’ki , biyoshi tayi ya nuna mata alh Ibrahim, murmushi tayi irin na karuwai tare dasa hannu a baki tana tsotsa, tace kwana za muyi ko yanzu za kayi? Alh Ibrahim shuru yayi yana kallonta, tace Mlm yi magana mana, yace ni mahaifinki ne,ta daka Mai tsawa tare da fadin karka kuma cewa haka bani da iyaye sun mutu bani da dangi sun mutu bani da kowa sun mutu, alh Ibrahim yace injiwa ni …… Tace inji Wanda yasa na Fara wannan rayuwar tun ina yarinya, yace Waye? Tace saleh shine ya bata min rayuwa ina ji ina gani sannan duk abunda na Samu na kudi shike amsa tun banjin dadin rayuwan da nakeyi harna Faraji, dan haka Mlm 
karka bata min lokaci muje kayi abunda za kayi ka sallameni, yace dagaske nine mahaifinki, lumshe ido tayi tare da kiran wasu akan suzo su fitar mata da wannan tsohon, jan alh Ibrahim da Abubakar akayi aka watsar dasu waje, dariya tayi tare da fadin ldan ka shirya ina jira dan daka ganinka zakai dad’i, lumshe ido alh Ibrahim yayi yana hawaye, dai dai lokacin police suka zo kame aka kama harda alh Ibrahim da Abubakar da wanda ke shaye shaye a wajan, tana ganin an sasu a mota ta Fara dariya tare da d’aga musu hannu sannan ta koma ciki, koda aka Kai su alh Ibrahim station yan sanda suna ta fad’in tir tsohon banza har kasan gidan ta Goma Kai baka ji kunya ba, Abubakar yace ku daina fadin kalaman batanci akan mahaifina domin ba haka yake ba, wani police yace Kai tsoho zinan ma in zaka harda d’anka kake zuwa? Lallai naka Abun babba ne Toh mace d’aya kuke ci k0 kowa …… Abubakar ne ya daka ma police din tsawa tare da fadin karka kuskura ka kara fad’in haka inko ba haka ba ……. Police din yace Mai zai faru iye Mai zai faru Karya akayi muku fad’a min ba a gidan karuwai aka kama ku ba, alh Ibrahim ya kalli Abubakar yace karka kara magana kayi shuru kaji bai kuma cewa komai ba police din nata fad’a musu magana haka suka kwana a station ga sauro, Washe gari da safe aka sakesu akan karsu kara komawa wannan wajan, koda suka fito hotel din da suka sauka suka nufa, suna zuwa alh Ibrahim yace ma Abubakar ya shirya yazo su koma, Bayan sun gama shiri inda suka fito ya kalli Abubakar yace yana son ko sun koma Gida karya fad’a abunda ya faru karya fad’a ma kowa halin daya ga y’arsa, yace Abba Toh Mai za’ayi? Alh Ibrahim yace ta mutu ita ba y’ata bace, alh Ibrahim hawaye ke Zuba a fuskanshi tare da fadin duk ni naja ma kaina yau y’ata ce gidan karuwai Allah bazai barni ba duk nine sila da nake kyamatar y‘ay‘a mata, saboda wani dalili na wanda bai Kai ya kawo ba, dakyar Abubakar ya rarrasheshi suka shiga mota sukai gida, koda suka je, gaba d’aya kowa yana ta murnan dawowan nasu Amina tace Kun ganta Tana ina? Alh Ibrahim yace ta mutu ……. 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE