MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 15

MEYE ILLAR YAYA MATA
CHAPTER 15
Sun gama had’a kayansu tsaf suka fita, Allah yasa wannan karan Aneesa Nada d’an kudi dan haka basu sha wahalan neman wajan kwana ba, kuma sunci Sa’a sun sami d‘aki a wani Gida wanda mutanan gidan sun Kai su ishirin kuma bayi biyu ne a gidan, na wanka d’ana bahaya, d’akin ciki da falo ne, sannan kana hango masu wucewa ta waje haka kaima da kake wucewa kana hangosu dan katangar gidan ya zube, magajiya kallon d’akin tayi da yayi uban kura ga bangon d’akin dukya tsage saman silin din duk shaidan ruwa alaman in ana ruwan sama yana zuba shine ya lalata silin din, tace amma dai Banan zamu zauna ba koh? Wani irin kallo Aneesa ta watsa mata tare da fad‘in in kina da inda zamu ai sai ki kaimu ni dan Allah jeki samo tsintsiya a share d’akin, magajiya fita tayi tana surutu taya mutum Mai rai zai kwana cikin wannan d’aki, haka harta samo tsintsiya da mofa tana Shara tana surutai ganin kura na tashi Aneesa ita da d’anta sukai waje, haka magajiya ta share d’akin tas tare da gogewa bayanta sai ciwo yake mata, Bayan ta gama ta fita ta kira Aneesa, Aneesa tace Kai d’akin yayi kyau yanzu, muje mu nemi katifa mu siya, magajiya tace kije ke d’aya wlh kafana da bayana yanda kika san ana min daka dan gajiya, Aneesa tace ke Wlh kin cika raki d’an wannan aikin da kikayi dan Allah tashi muje, haka magajiya ta bita badan son ranta ba, sun siyo katifa dasu stock da tukunya seti biyu dasu cup plate da d’an sauran tarkacen kitchen sai d’an kayan abinci, gidan suka koma yan gidan sai gulma suke kun san gidan yawa. 
Wani yazo neman auren khairat lokacin da suka zo aka kirata suka ce ba ita suke nufi ba d’ayan macen wato rahma, ranan khairat taci kuka tare da tsanar ciwon idon daya kamata domin tasan duk saboda shine ake nuna ba’a Sonta, rahma tace itama kam bata son yaron haka aka hakura har Alh Ibrahim Ya samo mata wani shima dai hakan ya faru yaron yace bazai auri Mai sa glass ba, alh Ibrahim ya damu Sosai domin khairat itace yayar rahma kuma yafi son tayi aure Kafin Ayi na rahma, ganin ya damu yasa khairat ta sameshi akan ya zabama rahma miji ita hala lokacinta ne baiyi ba aure lokaci ne, sannan akwai matan da Allah yasa bazasu taba aure ba a duniya tayu ina cikinsu saboda ni Abba Kar a batama rahma lokaci domin rayuwar mace kalilan ne, alh Ibrahim yana tasa mata albarka hakan koh akayi, 
Rahma alh Ibrahim ya samo mata miji, hakan yayi ma kowa dad’i amma ita rahma ta nuna bata so, har ran amina ya baci, amma duk da haka ta nuna ita sam, yau suna zaune a falo Su duka suna fira alh Ibrahim yayi gyaran murya tare da fad’in rahma mai yasa baki son auren wanda na baki Bayan baki taba haduwa dashi ba? Tace Abba bawai bana so bane a’a, ina tsoran ldan yaji rayuwar da nayi na baya na tabbata duk wani namiji bazai yarda ya aureni ba, alh Ibrahim shuru yayi ummi tace rahma ki daina tunanin haka lndai yana sonki zaiyi accepting naki koda Mai kika aikata baya tunda yanzu kin tuba, amina tayi caraf tace ma Alh Ibrahim ya turo yaron ita zata mishi bayani da kanta, hakan yayi ma rahma dad’i domin tace gwara a fad’a mishi yasan ko ita wacece Kafin Ayi auren, kowa dake wajan yaji dad’i data yarda, Washe garin ranan yaron yazo inda Amina ce tayi mishi bayani, babu laifi guy din yana da kyau sannan Suma suna da kudi, sunanshi usman yace baya son bikin yayi nisa hakan ko aka fara hidiman biki, yau za’ayi dinner kasancewan sai an fara dinner 
Kafin Ayi daurin aure. wannan dinner din ya had’u an tara manyan mutane su khairat dasu aysha da zainab zarah sunyi kyau Sosai, ana ta bidiri tare dacin abinci Kala Kala, wani ne yazo kusa da amarya da ango ya basu takarda tace zasu fito su karanta jokes ne, rahma ta kalli usman tace miye haka amma kasan ban iya karatu ba? Yace wannan wani irin wasa ne, tace kaman ya wasa Bayan kaima ka sani, yace tashi muje yanzu za’a kiramu tace bazanje ba dan ban iya karatu ba, yace rahma degree fah gareki plz tashi, tace degree injiwa? Yace inji mum dinki, gabanta ne ya fad’i kenan mamanta bata fad’a musu cewa ita jahila bace bata fad’a masu labarinta na baya ba, wani hawaye ne ya fara zubo mata gashi Anata kiran amarya da ango akan su fito, y’an uwanta mata suna zaune suna ta fargaba mai yasa take hawaye, khairat ce ta tashi da nufin zuwa amma usman ya d’agota suka tashi, ri’ke mata hannu yayi da nufin su karasa amma ta kwaci hannunta cikin kuka take fad‘in na fad’a maka ban iya karatu ba, gashi an kashe kid’a wajan yayi Tsit kowa hankalinshi na gunsu, usman yace dagaske kike yi? Kai ta d’aga mishi alaman eh, yace no no it can’t be bazan auri illiterate I can’t never ………. 
Kowa kallonsu yake harda Iyayensu dake zaune a wajan, Amina kam babu abunda take saI kuka dan batayi zaton haka ba, shiko usman fad’i yake bazan auri macen da batai karatu ba…. D‘an shuru yayi yana kallonta sannan ya daura hannunshi akan kafad‘anta yace rahma stop dis kind of joking mum dinki tace kina da degree plz ki daina wannan maganan muje,jan jikinta tayi tare da barin hall din da gudu y’an uwanta mata na ganin haka suka bita, flta tayi daka hall din Tana ma ta samu Mai taxi ta tsayar ta fad’a mishi inda zai kaita, koda su khairat suka karaso motarta wuce, mutane kam sai surutu ake tayi, alh Ibrahim wani irin kallon tsana yake ma Amina, wajan mahaifin usman yaje Wanda usman din shima yana wajan, alh Ibrahim yace dan Allah alh kayi hakuri wannan abunda ya faru banga laifin usman ba domin a wannan zamanin ilimi yana da matukar amfani tun Farko yarinyar taki yarda tace sai an fad’ama usman batai karatu ba, mahaifiyarta tace zata fad’a mishi ashe bata fad’a ba, dan Allah Ina Mai baku hakuri yana fad’in haka ya flta ummi itama ta Mara mishi baya. 
Gida aka Kai rahma Wanda bata dad’e da shiga ba y’an uwan nata suka shigo, dakinta data rufe shi suke ta Buga mata alaman ta bud’e amma taki, kuka take Sosai a cikin d’aki tare dayin dana sanin rayuwarta ta baya wanda itama tsintar kanta tayi a ciki, kuma dole tayi tunda inda ta taso abunda taga anayi kenan, ido ta lumshe dake ta zubar da hawaye tare da fad’in duk mahaifiyata ita taja mata wannan Abun kunyan tare da kaskanci a gaban dubunnan mutane, jin muryan mahaifinta yana kiran sunanta tare da buga mata kofa yasa ta tashi ta bude tare da fad’awa jikinsa tana kuka, tausayinta duk ya kara kamashi, Amina ce ta shigo d’akin cikin sanyin jiki, alh Ibrahim cikin zafln rai yace maiya kawo ki? Mai kika zo kiyi mata? Anya Amina kina da tausayi da imani kuwa? Rahma y’arki ce ta cikin ki, mai yasa kika mata haka? Gashi yanzu kin rusa mata komai ki fita daka nan, Amina cikin kuka take fad’in Wlh Nayi hakan bada wani manufa bane, ina tsoran su San rayuwarta ta baya ya fasa aurenta domin Indai aka fad’a musu batai karatu ba za suso su San miye dalili tunda duk y’an uwanta sunyi Kaga dole a fad’a musu inda ta taso, matsayina na uwa bazan iya juran hakan ba shi yasa Nayi musu karya akan tayi karatu ban taba sanin hakan zai faru ba, alh Ibrahim yace tunda an fad’a miki aure wasa ne koh? Yau za’ayi gobe a daina, Amina kin Masan miye aure kuwa? Bari kiji in fad’a miki aure anayi ne har abada ba’a tunanin rabuwa sai mutuwa, yau kwana biyu kayi da mutum sai ka gane halinsa balle rayuwar aure da za’ayishi na har abada, maganan aure ba’ayin aure inko akayi karya cikin sa Toh babu inda zashi, ki kalli yanda kika wulakanta y’arki da kanki kin nuna ma duniya ko ke wacece tunda ke kikai karya akan tayi karatu, Amina cikin kuka take bama rahma hakuri akan ta yafe mata, rahma da idonta yayi ja ya kad’a tace mum haryau na kasa yarda koni y’arki ce, in kuma ni y’arki ce dagaske Toh bakya so na, ranan da nazo duniya kika kyamace ni kika nesanta ni dake Wanda duk burin uwa yau Idan ta haihu taba d’anta Nono, amma ni baki min haka ba, wannan Abun da kika min banyi mamaki ba dan nasan zaki iyamin Wanda Ya fishi Wlh Ina dana sanin d …… Ummi ta daka mata tsawa tare da fad’in rahma kina cikin hayyacinki kuwa? Karki manta da wacce kike magana mahaiflyarki ce, ki daidaita harshenki akanta, tace ummi Ina ma ina d’aya daka cikin yaran da kika haifa da cikin ki, ta 
kalli su zarah da suke hawaye tace kunyi sa’ar samun uwa ta gari Mai kaunarku ina ma Nima itace mahaifiyata ummi rikota tayi tare da rungumeta tace rahma Kema y’ata ce dake dasu zarah duk d’aya kuke a wajena, sannan ina son itama Amina ki dauketa matsayin uwa sannan duk abunda ya faru ki manta dashi ki d’auka a matsayin kaddaran rayuwanki, itama uwa ce ta gari, sannan wannan abunda tayi son da take miki yasa tayi, kiyi hakuri Kinji Kai ta d’aga alaman Toh, fita iyayen sukayi Bayan Amina ta kara bata hakuri, y’an uwanta mata suka zauna suna ta bata baki tare da kokarin mantar da ita komai duk da ba Abu bane mai sauki. 
Faruk ne cikin gidansu Aneesa yana zaune kan y’ar katifar d’akin, fuskan Aneesa a murtuke faruk sai hakuri yake bata, tace yanzu a cikin wannan gidan d’anka zaiyi rayuwa? Zai taso cikin wahala abunda nake fad’a maka kenan wannan alh Ibrahim din baya kaunarka Wlh gwara kasan abunda kakeyi inda Kai d’ansa ne na cikinshi bazai koreni ba kodan saboda jikansa amma da yake kaiba d’ansa bane aiya koreni, yanzu jiba gidan da d’anka yake rayuwa, faruk shuru yayi yana tunani lallai abunda Aneesa ta fad’a gaskiya ne, ya kamata yasan abun yi, kud’i ya dauka yaba ta amma taki amsa babu yanda Baiyi ba amma taki karba, magajiya dake falo tana jiyo su ji tayi kaman taje ta Mari Aneesa tasan basu da kud’i amma ana bata taki amsa, haka ya tafi bata amsa ba, yana fita magajiya ta fito tana fad’in miye haka? Kinfa san bamu da kud’i kika ki amsa, Aneesa tace magajiya karki damu ni Nasan Mai na shirya kuma zaki gani, murmushi magajiya tayi tare da fad’in Allah yasa shirin komawa gidan Alh Ibrahim kike mana, Aneesa tace koma miye zaki gani bada dadewa ba. 
Faruk koda ya fita tuki yake amma yana tunanin abunda Aneesa ta fad’a mishi wanda yasan gaskiya ta fad’a yau Idan alh Ibrahim ya kwanta ya mutu wannan motar da yake hawa ajiyeta zaiyi dan ya zama na magada lallai ya kamata insan abunyi kodan in inganta rayuwan yaro na Nima, direct office ya nufa yana zuwa yaga Abubakar da wani akwati daka gani kudi ne zai Kai banki, wani mutumi ne ya tsayar da Abubakar yana mishi magana faruk ya karaso wajan, dai dai lokacin Abubakar yake cema mutumin banki zani ka Bari in dawo, mutumin yace yanzu ake son Abun, faruk yace kawo in kaima banki, Abubakar ya bashi tare da fad’in kasa a acct din Abba kudin da zaiba ma wanda zai kawo kaya nejibi Idan suka kawo, yace 0K, direct banki ya nufa ya Tarar da layi yana cikin bin layi Aneesa ta kirashi tace d’anta yana ta amai fita yayi direct ya nufi gidan koda yaje bata nan kofarta rufe da kwado Ma yayi waje yana kiranta bata dauka ba hangosu yayi suna dawowa da sauri ya nufeta yana tambaya yajikin yaron tace da sauki amma fa akwai damuwa Dr yace canjin waje ne, tare da ruwan da yake sha, yace Indai muna son laflyan danmu Toh mu canza waje tare da ruwan da yake sha, inko muna son rasa shi Toh shikenan, hankalin faruk ya tashi yace ku shiga ciki yanzu zan dawo, baiyi ko awa biyu ba sai gashi ya dawo, yace su zo suje, aneesa tace ina zamu, yace magajiya dauko muku kayanku magajiya da sauri ta dauko 
musu kaya tana murna zasu koma gidan Alh Ibrahim, koda suka shiga sai suka ga ya shiga wani Gida Mai kyau fakawa yayi yace su flto, shiga ciki sukai wani falo Mai kyau suka shiga wanda aka tsarashi da kayan more rayuwa yace na siya gidan nan saboda d’ana saiku zauna a ciki hatta kayan abinci akwai kud’i ya ajiye mata masu yawa sannan ya tafi, gidan 3bed room ne sannan duk d’aki ukun ansa gado a ciki, yana flta magajiya ta saki ihun murna tare da fad’in Allah ya rabamu da wannan gidan mai bayi d’aya rannan saura kad’an inyi kashi a wando dan bala’i bayi sai anyi layi, dariya Aneesa tayi tace Kinga kad’an daka plan dina koh? Magajiya tace toh a ina ya sami kud’i Bayan yanzu alh Ibrahim baya Bari ya cira kud’i? Aneesa tace oho duk inda ya samu ma wannan ba damuwa na bane nidai burina in huta dariya suka saki mai sauti ……. 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE