MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 18

MEYE ILLAR YAYA MATA
CHAPTER 18
Magajiya da Aneesa ne zaune a falo suna f’Ira, saiga Abubakar nan yazo wucewa, Aneesa ta bishi da ido tare da fad’in oh magajiya namiji har namiji amma bashi dako sisi, ya kasa tsinana ma matarshi komai, Abubakar yasan dashi take dan haka ya girgiza kai tare da d’an murmushi ya fita ba tare daya ko ya  kalleta ba, Aneesa cikin ranta tace shi wannan wato ya maidani mahaukaciya kenan zanyi maganinsa. Abubakar yana zaune a office saiga police nan sun shigo cikin office dinshi Wai zasu bincike an sace kud’i har naira million biyar a company din, Abubakar Yace 0K Toh ku duba, Aneesa ce tazo itama cikin office din nan gabanshi ya fad’i tare da tsoran Kar ace ta kulla mishi wani Abun aiko yana cikin tunanin yaji ana fad’in ga kud’in nan, da sauri ya dawo cikin hayyacinshi tare da rudewa yana fad’in Wlh ban d’auka ba, Aneesa tace in baka d’auka ba Mai yasa ba’a gani office din kowa ba sai naka? Shuru Abubakar yayi dan yasan bamai fItar dashi sai Allah kuma wannan shairin aneesa ne, dan Haka yasa yayi shuru ta kalli police din tace ku tafl dashi, haka aka tafi da Abubakar tana ta murmushi yana kallonta, koda labari yakai masu zarah cikin tashin hankali suka nufi station din, amma police sunce bazasu ganshi ba dakyar suka yarda suka basu minti uku su ganshi, Bayan zarah ta isa inda yake tace maiya faru Abubakar Nasan wannan shairin Aneesa ne amma karka damu za muyi billing dinka, yace Aneesa makira ce amma babu komai abunta zai koma kanta insha Allah, wani police ne yazo yace ma zarah ta fito lokaci yayi, haka ta flta Tana kuka, inda sukai ma police magana akan belling suka ce Indai zasu belling dinshi sai sun bada dubu d’ari uku, zarah ta zaro ido domin basu da dubu d’ari uku duk wasu kud’in su a acct din Abba suke sawa gashi kuma yanzu komai na wajan Aneesa, haka suka flto jiki a sanyaye suka koma Gida, suna shiga Aneesa ta Fara bala’i wai ina suka je basu gama Mata aiki ba, zarah ta nufeta tana kuka tare da fad’in Aneesa dan Allah kisa a saki Abubakar Nasan bai d’auki kud’in ba, Aneesa ko kallonta batayi ba saima kiran Sunan magajiya da tayi tana tambayanta akan sarkan data siyo koh tayi kyau, rahma da ranta ya baci ta matsa kusa da Aneesa tace Aneesa tunda na taso ban taba ro’kan wani abu wajan kowa ba dan Allah kiyi hakuri ki saka a sako shi, Aneesa ta daka mata tsawa tare da fadin kar in karajin wani ya furta min wata magana maza kuje kuyi min aiki khairat kawo min coffee, zarah cikin kuka take kara bata hakuri akan tasa a sakar mata miji, rahma tace zarah kibar ro’kanta domin rashin imaninta bazai sa tasa a sa’ko shiba, kin San bata san miye so be tunda a titi ta taso Aneesa ta d’aga hannu zata Mari rahma da sauri rahma ta ri’ke hannun tare da fadin karki sake ki fara duk wannan Abun da kike bazan kara dauka ba, Aneesa tace sake min hannu karki manta nan gida nane komai nace shi za’ayi in kuma kina son zama cikin sa dole kiyi, rahma ta sakar mata hannu tare da fad’in baki isa ba babu wani abunda zaki kara Sani inyi domin yau zanbar gidan nan bazan ci gaba da zama a karkashin wacce bata san abunda take ba mara imani Mai zuciyar kafirai tana gama fad’in haka ta haura Sama inda suke kwana ta kwaso kayanta Amina tace rahma Ina kike kokarin zuwa? Y’an uwanta mata suka tareta tace dukanku bazanji maganan kowa ba yau zan bar gidan nan tana fad’in hakan ta fita cikin fushi Aneesa tace duk Wanda bazai yi abunda nake so ba ya bita tana fadin haka suka haura ita da magajiya, Amina cikin damuwa itama tayi d’akinta domin ita har yanzu a d’akinta take kwana, su khairat da sukai jigum suna jimami yanzu Ina rahma zata tafl? Ina zata wata sani? Wannan tunanin suke tayi, ita kam zarah abubuwa sun taru sun mata yawa 
tama rasa abunyi na farko ga mijinta a station babu kud’in billing ga rahma tabar gida wanda basu San inda zata ba, gaba d’aya komai ya had’u ya jagule mata wani irin hawaye ne ya silalo mata Mai zafin gaske, zainab da cikinta yake ta girma ta karaso dakyar tana fad’in zarah kiyi hakuri insha Allah zai fito, zarah tace zainab rahma ta tafi ko Ina zata oho, yanzu itama ta gujemu kenan Wlh Ina takaicin abunda tayi, khairat dake gefe tace zarah kiyi mata hakuri hala akwai manufar yin haka ne, zarah bata kara cewa komai ba ta tashi ta had’a kayan wanke wanke ta nufl waje danta wanke. 
Zarah duk ta rame tayi duhu ba komai yasa Mata haka ba sai damuwa, Ummi ce ta shigo ta sameta tana Shara a kitchen ummi cikin tausayin y’ar tata ta kira sunanta, tare da fad’in zarah, d’agowa tayi ta kalli ummi tare da fad’in na’am ummi, Ummi ta ciro kud’i a Leda tare da mi’ka ma zarah tace gashi kije kiyi billing din mijinki, cikin jin dad’i tace ummi Ina kika sami kud’i haka? Ummi tace Abun hannun da mahaifinku ya sai min Kafin ya rasu Shina saida, zarah cikin kuka tace ummi Mai yasa kika saida Bayan Abba ne ya siya miki? Tace zarah bazan iya kallonki haka ba ina shiga damuwa Sosai zarah ta rungume ummi tana fad’in nagode ummi Allah ya biyaki, suna cikin haka saiga Aneesa ta shigo ta fisge kud‘in a hannun zarah da sauri suka waiga suna kallonta dan basu ga shigowanta ba sai dai ganin kwace kud’in da tayi, zarah tace Aneesa miye haka bani kud‘in, zarah tace komai dake cikin gidan nan ba naku bane nawa ne harta kayan da kuke sawa dan haka bazan bada kud’in ba Tana fad’in haka ta fita tabar kitchen din ….. 
Zainab ce ta shigo ta samesu cikin tashin hankali ganin irin halinda suka shiga yasa ta Fara tambaya Ummi lafiya maiya faru kuma? Ummi ce ta fad’ama zainab abunda ya faru, cikin zafin nama ta fita falon ta sami Aneesa ita da magajiya zaune ga kud‘in tasa akan cinyanta Tana girgiza kafa, zainab tace Aneesa ki bani kud’in da kika amsa a hannun zarah, aneesa bata ko kalleta ba balle tasan da ita take magana Abun ya batama Zainab rai ta nufeta da nufln d’aukan kud’in dai dai lokacin su Ummi suka karaso wajan Aneesa dauke kud’in tayi tare da dauke Zainab da wani gigitaccen Mari Wanda yasa saida taga stars ga ciki, khairat da sauri ta karasa ta riko Zainab dake kokarin fad’i, Aneesa tace naga kuna kokarin wuce gonarku amma Bari in tuna sharku, mama mama Aneesa ta Fara kiran mama cikin tashin hankali suke kallonta Zainab da takejikin khairat tace Aneesa dan Allah karki fad’ama mama abunda ke faruwa dan Allah kiyi hakuri, amma Aneesa ko kallonta batayi ba sai faman kwadama mama kira take, mama ce ta fito gaba d’aya cikin tashin hankali suka nufeta, mama ta kalli ummi tace Ibrahim har yanzu bai dawo ba? Ummi tace eh bai dawo ba mama muje in kaiki d’aki ki huta, mai makon mama taje d‘aki kaman yanda Ummi tace saita kara jefo mata wata tambayar da fad’in baiyi waya ba? Ummi kodai kuna boyemin wani abu ne? Yau kwana nawa haryanzu bai dawo ba, ya kuma san banda lafiya, Ummi tace Mama doctor yace ki daina sama kanki damuwa yace kina bukatar hutu muje ki kwanta ki huta, ummi ta kamata sukai ciki, Bayan sun shiga Aneesa ta kallesu tare da fad’in wannan ya zama na farko dana karshe da zan kara fad’a wani ya fad’a ko kuma inyi Abu wani yayi gigin tambaya na, Tana gama fad’in haka ta haura Sama ita da magajiya, zarah kasa tayi tana kuka yayinda y’an uwanta suke ta rarrashinta akan tayi hakuri komai zai wuce, tace taya zai wuce? Zainab mijina yana station na kasa fito dashi babu hanyar da zan sami kud’i taya komai zai wuce, ummi ce ta karaso inda suke tace zarah kiyi imani da Allah 
komai zai wuce Allah baya daura ma bawa abunda yafi karfinsa kiyi hakuri. 
Lokacin da rahma tabar gida rasa wajan zuwa tayi, gashi dare yayi cikin damuwa take tafiya gashi ta gaji, wani kango ta gani wanda an fara gini ba’a gama ba shiga tayi ta ajiye akwatin ta, tare da budewa ta d‘auko wani zani ta shimfid’a tayi pillow da akwatin ta, jin kaman mutane a kanta yasa ta d’aga kanta wasu maza ta gani su hudu k0 wanne da sigari a hannunsa, d’aya daka cikinsu yace Yadai y’an mata tare da d’aga mata gira, wani ya cabe da fad’in yarinya mai zafi irinki bai kamata ki kwanta a titi ba kizo mu baki masauki saimu kwana tare, d’aukan akwatinta tayi tare da zaninta da nufin tafiya janyota sukai suna shafa mata fuska wani kuma ya ri’ke mata hannu tare da fad‘in ina zaki kuma y’an mata?fisge hannunta tayi da karfi tare da fita daka wajan amma ganin suna kokarin binta yasa ta jefar da akwatin ta Fara gudu tazo wajan titi suka kamata da yake dare ne babu kowa suna kokarin cire mata kaya sukaji jiniyan y’an sanda da gudu suka bar wajan, Allah tayi ma godiya tare da komawa ta d’auki akwatin ta tabarwajan, kusa da wani Gida taje akwai masallaci a wajan ta ra’be a barandar gidan ta kwanta, Washe gari tunda asuba tabar wajan dan zuwa neman aiki domin ta samu ta tsira da kanta, tafiya take tana hawaye domin tunawa da tayi batai karatu ba, bazata samu irin aikin da take buri ba danta taimaki y’an uwanta, haka taita yawo wajan masu saida abinci amma bata sami aiki ba dan wasu cewa ma sukai suna tsoran irinsu, wasu kuma sun ganta jikinta fresh ga kyau sai suce bazasu iya biyanta ba, haka dai ta gaji da yawo ga yamma tayi ga akwati Tana ta fama dashi 
ga yunwa, wani wajan gida ta nufa ta zauna, wani tsoho ne ya fito yaje masallaci harya dawo ya ganta a wajan yace yarinya laflya kuwa? Bata kikayi ne? Cikin kuka tace eh dan Allah baba ka taimaka min, mutumin yayi shuru can yace tashi muje, cikin gidan tsohon suka shiga babu laifi yana da kyau da d’an girma, kiran matarshi yayi Mai suna Hajara yace ga Bakuwa nan a bata abinci da masauki Hajara ta amsa da Toh, rahma tace dan Allah Bari in farayin sallah tukunna bayi Hajara ta nuna mata ta shiga Bayan ta fito ta kaita d’aki ta Fara sallah, Hajara ma tayi Bayan ta kaita d’akin wajan mijinta taje inda ta sameshi tace wannan bakuwar daka ina kuma? Yace Wlh ganinta Nayi a waje a zaune ban San daka inda tazo ba koma dai daka ina take bari ta huta sai muji dan Ina zargin ta bace ne ko bata gane inda zata ba Hajara tace Allah ya kyauta ya amsa da Ameen. 
Su Ummi suna kitchen suna aikin abincin dare, zarah ta kalli aysha tace aysha Wai yaushe zaki koma gidanki ne? Ummi tace Nima abunda ke raina kenan, aysha kuka tasa dukanku sukai kanta cikin tashin hankali, zarah tace aysha maiya faru lafiya kuwa? Cikin kuka tace ummi na sami matsala da Sirika ta wata y’ar uwarta tazo taita zugata suka sakani a gaba gab da Abba zai rasu suka koroni tare dayima d’anta kashedi Idan ya nemeni bata yafe Mai ba, ummi shuru tayi tare da jimami su zarah ne sukai ta rarrashinta, ummi Kam ta fad’a duniyar tunani lallai dama Idan kana da y’ay‘a mata ka dinga ganin irin abubuwan nan kenan Allah yasa hakan shine alkhairi, haka sukai ta aikinsu har suka gama sukajera a dinning sukai sama inda suke kwanciya dan su huta, ummi tunani tai tayi Kala Kala akan abubuwan dake faruwa, na farko ga matsalan zarah na biyu ga zainab haiyuwa yau k0 gobe, na uku ga aysha ta sami matsala da mijinta ga rahma tabar gida, wani hawaye Ummi ta matse Mai zafl lallai Allah baya barin wani dan wani yau inda mijinta yana Raye da abubuwa basu cabe haka ba, gashi y’ay’anta suna cikin matsala amma ta kasa magance musu, ta gefen zarah itama tunani ne fal cikinta taya zata fitar da mijinta daka prison, duk tayi ba’ki ta rame, jin Aneesa sukai tana fad’in kuna ina? Tashi sukai suka sauka kasa dan bata abinci. 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE