MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 19

MEYE ILLAR YAYA MATA
CHAPTER 19
Bayan rahma tayi sallah taci abinci, Hajara matar Malam ta shiga inda take tare da fad’in baiwar Allah daka ina haka? Rahma cikin hawaye ta fad’a mata komai ba tare data boye mata ba sai dai ta boye mata Sunan iyayenta, Mlm dake waje yana jinsu ya tausaya mata Sosai, shima shigowa d’akin yayi tare da fad’in rahma Toh yanzu miye fa’idar barinki gida? Tace nabar gida ne dan in nema Sana’a in tallafa ma y’an uwana, Mlm yace shikenan zaki 
zauna damu Kafln ki sami abunyi godiya taita musu cikin girmamawa. 
Zarah Tana ta sauri ta gama aiki dan taje ta duba mijinta dan yau ne ake ganin wanda suke prison din, tana ta sauri dan Kar lokacin ganinsu ya wuce, Aneesa duk ta Lura da hakan, saida ta gama aiki saiga Aneesa da kaya niki niki, ta watsa mata tare da fad’in gashi ki goge min, kallon kayan zarah tayi sannan tace Aneesa ki bari Idan na dawo saina gage zani ganin miji nane, Aneesa tace wannan ba matsalata bane naki ne, nidai matsalata ki tabbatar kinyi min wannan gugan Kafin kibar gidan nan, tana fad’in haka ta wuce, zarah diban kayan tayi masu uban yawa ta Fara gogewa da sauri, khairat ne da aysha suka shigo d’akin, aysha tace zarah lokaci fah yana kurewa har yanzu baki fitoba, zarah tace Wlh aneesa ce taban Guga tace kuma inyi Kafin in fita, aysha tace Kinga tashi kije ni kiban gugan inyi Mata, da sauri zarah ta tashi tanayi ma y’ar Uwar tata godiya, d’aukan jakarta tayi ta fita a falo taga Aneesa da magajiya, Aneesa tace zarah kin gama gugan ne? Tace aysha namin tana bata amsan ne tana taflya, tashi Aneesa tayi ta nufi dakin kofa da sauri ta tare da hannunta tare da fad’in ban yarda kije ko Ina ba, zarah kallonta tayi sama da kasa sannan tace Aneesa bani hanya Ina sauri, Aneesa tace na fad’a miki babu inda zaki maza ki koma, zarah sa hannu tayi ta bangaje hannun Aneesa ta fita, Aneesa da mamaki ya hanata k0 matsawa saida magajiya tazo ta ri’kota, Aneesa tace magajiya kina gani kuwa? Magajiya tace na gani aike kike sake musu shi yasa suke kokarin raina ki, Aneesa cikin fushi tace yau saina koya Mata hankali sai tayi dana sani. Rahma da Hajara na zaune suna aiki, saiga wata kawar Hajara nan tazo rahma gaidata tayi matar ta amsa tare da tambayar Hajara Ina ta samo yarinya kyakyawa haka ko y’ar uwarta ce? Hajara tace eh y’ar uwata ce, matar tace Allah sarki, rahma ta kawo ma matar abinci tana ta santi, Hajara tace ai rahma ta iya girki, har matar ta gama, nan suka zauna suna ta flra matar Mai suna Haulat tace, Hajara da zaki taimaka ki bani Aron wannan yarinyar zuwa abuja wajan gasar dafa abinci da naji dad’i, Hajara tace Mai zai hana Indai za’a biyata Toh amma ina yaranki? Haulat tace Kin San yanzu ba kowa yake da yarda ba wannan ne karo na farko da za’ayi a abuja, mutane sunki yarda su bada y’ay’ansu zuwa wani gari, Hajara tace gaskiya yanzu duniya abun tsoro ne, Hajara tace toh wannan wani irin gasa ne na dafa abinci? Haulat tace company din Maggi ne suke gasar sun ware mutum Goma duk Wanda girkinshi yayi dad’i Toh za’a bashi million d’aya, nima wajan saida abinci na yana d’aya daka cikin wanda akaba damar, gashi yarinyar naji ta iya girki, Hajara tace babu damuwa yaushe ne tafiyar? Matar tacejibi ne insha Allah, Hajara tace babu damuwa sai kizo kuje zan fad’ama Mlm inya shigo suna cikin firan Mlm ya shigo Bayan sun gaisa da Haulat Hajara Take fad’a mishi abunda Haulat tace yayi na’am da Abun inda ya kira rahma itama tace Tana so zata, Haulat tayi musu sallama akan jibi Tana nan tafe, rahma kam ranan sai murna take cikin jin dad’i zata sami kud’i danta taimaki y’an uwanta. 
Gaba d’aya su Ummi ne da yaranta a tsaye wajan dinning aneesa na zaune ita da magajiya suna cin abincin dare, dama sai sun gama suke ci, zarah ce tazo cikin damuwa take da fad’in aneesa dan Allah zan diba abinci lnba ma afra y’ar zarah kenan, sai kuka takeyi Tana jin yunwa, Aneesa ko kallonta batayi ba balle tasan da ita takeyi, zarah ta kara matsawa kusa da ita Tana ro’kanta akan dan Allah tayi hakuri taba yarta abinci taci murmushi Aneesa tayi tare da fad’in magajiya Kinga kuwa rigan dana siyo a kasuwa dazu? Magajiya tace eh na ganta gaskiya ta had’u Sosai, duk wannan abunda suke faruk na sama yana jinsu 
amma yarinyar sai kuka takeyi, zarah ta tsugunna har kasa tace Aneesa nasan nayi miki laifi kin hanani fita amma saida na fita dan Allah kiyi hakuri Kar laiflna ya shafi yarinya ta dan Allah, aneesa watsa mata shinkafa tayi a kasa tare da fad’in gashi kwashe kije ki bata, zarah shuru tayi tana kuka akan Aneesa ta taimaka ta bata wani tunda wannan a kasa ta zuba, suna cikin haka saiga mama ta flto da sauri zarah ta tashi mama tace Mai akama afra take kuka haka? Zarah tace yunwa takeji mama, mama tace diba abinci ki bata mana, da sauri zarah ta Fara zuba abinci a plate Aneesa kam fuska ta d’aure cikin takaici, zarah kam tana gamawa tabar wajan dan taba yarta abinci, mama ta kalIi ummi tace nifa na gaji yau sai kun kiramin Ibrahim. 
Ummi ta matsa kusa da ita cikin damuwa tace mama ya kusa dawowa inda yake babu service ne ba’a samun shi sai dai Idan shiya kira, mama shuru tayi dai dai lokacin hindu ta shigo falon mama kallonta tayi tace hindu Ibrahim baya son magana dani Ina fushi dashi Sosai, hindu da tunda d’an uwan nata ya rasu itama ta zama wani iri kullum tana d’aki a zaune duk da itama Aneesa ta korota waje amma a wani dan karamin d’aki take zama, tace mama yace ya kusa dawowa, kama hannun mama tayi tace muje ki huta kin San doctor ya hanaki yawan tunani binta mama tayi sukai d’aki. 
Washe gari da safe farida na goge step Tana yi jiri na dibanta sai tayi kaman zata fad’i sai ta ri’ke Abun step din, faruk dake ta kallonta yazo inda take yace farida kibar wannan aikin, bata ko kalleshi ba balle tasan yana yi, kamo mata hannu yayi da nufin ya kaita wajan da zata zauna ta fusge hannunta da karfl tare da fad’in karka kara, domin banda halaka dakai yanzu, yace inke baki dashi Toh ni inada shi domin jini nane a jikin ki, ido ta lumshe tare da cije lebe domin kalaman nashi sunyi Mata zafl, ido ta bude cikin takaici tace kwana biyu da baka kulani yasa na manta Waye uban d’ana amma yanzu ka tuna min wanda Indai na haifi abunda ke ciki na zanyi ba’kin cikin Waye ubansa Wlh da in haifi d’an dake ciki na gara in zubar in Huta saboda ina takaicin yasan kaine ubansa, faruk idonshi ne ya kad’a yace farida komai zaki fad’a ki fad’a amma karki zubar min da ciki na inko kikai haka zan Manta koke wacece saina hukunta ki, yana fad’in haka yabar gidan cikin sauri, kuka tasa Sosai cikin tausayi khairat ce ta sameta tana kuka da sauri ta nufeta tana fad’in farida lafiya maike damunki? Farida cikin kuka tace khairat ina takaicin wannan cikin nawa daya kasance na faruk ne, khairat ina son faruk amma abunda yayi yasa na tsaneshi bana ko son ganinshi khairat Idan na haifi d’an ciki na wani labari zan bashi akan ubansa? Khairat faruk ya biyo halin ubansa Ina tsoran abunda zan haifa karya biyo halinsu khai…. Khairat ce ta toshe mata baki alaman tayi shuru Khairat tace farida nasan faruk Nasan Waye shi, faruk ba halinsa d’aya da mahaifinsa ba, duk abunda faruk yakeyi haduwa da Aneesa ne, sannan Idan kikace kina takaicin wannan cikin kin San wa zaki haifa? Baki Sani ba wannan maganan da kikeyi bata dama kyau, ki kwantar da hankalinki ki daina d’aga ma kanki hankali a wannan step din da kike domin zai cutardake da abunda ke cikin ki, inaso ki nutsu kiyi takai ma Allah kukanki akan ya zaba miki mafl alkhairi, yasa abunda zaki haifa ya zama mai tausayinki dajin “kanki, farida rungume khairat tayi tana kuka tare da fad’in nagode khairat. 
Aneesa ce ta fito taga gidan duk datti falon duk ya yamutse, kira ta Fara kwad’a musu akan suzo, futowa sukai da sauri, tace uban wa zai gyara gidan? Kalla yanda kuka bar gida duk datti, na baku nan da awa d‘aya ku gyara Kafin in dawo dan yanzu zan flta, suka amsa da Toh sannan sukai waje ita da magajiya, Fara gyaran gidan sukai Zainab ta dauko ruwa da 
tsumma dan tayi goge gogen kujeru aiko ta saki ruwan ya zube tare da sakin ihu mai karfl da gudu sukai kanta, daukanta sukai dan zuwa asibiti domin na’kuda takeyi, suna zuwa akai labour room da ita, dukansu sun shiga cikin damuwa domin halinda ta shiga, Dr ne ya flto yace sai anyi mata cs domin tayi weak bazata iya haiyuwa da kanta ba, yace suje su biya kud’i sannan a Fara mata aiki yana fad’in haka ya wuce, sun shiga cikin mugun damuwa gashi basu da kud’i, ummi ce taja aysha tace zo muje, zarah tace ummi lna zaki? Ummi tace zani wajan Aneesa in tambayeta zarah tace ummi am…. Ummi tace karki damu aysha muje flta sukai. 
Aneesa Sun dawo ita da magajiya a gajiye, magajiya tace muyi sauri mu shiga, khairat ta had’amin tea insha yarinyarta iya hada tea na rasa mai take zubawa, suna bud‘e kofar falon Aneesa tace kutumar uba, haka suka bar gidan basu gyara ba, Fara kiransu tayi cikin fushi amma taji shuru, kallon magajiya tayi tace ina sukaje? Magajiya tace taya zan sani nima, amma gaskiya wuyansu ya fara kauri, Aneesa zama tayi tana girgiza kafa cikin fushi domin ranta a bace yake Sosai suna cikin haka saiga ummi da aysha Sun shigo da sauri Aneesa ta tashi tare da fad‘in daka gidan uban wa kuke? Ummi ce tace Aneesa Zainab ce take asibiti zata haiyu doctor yace sai anyi mata cs gashi sai mun biya za’ayi dan Allah ki taimaka ki bamu aje Ayi Mata, wani irin murmushi Aneesa tayi, tare da kallon ummi tace zan baku amma sai kin Tsugunna kin rokeni Kafin in baku, aysha tace Aneesa miye haka? D’aga mata hannu Aneesa tayi tare da fad’in babu dole ai, ummi tace Aneesa ki taimaka dan Allah Kema fah uwa ce y’ata tana can tana jin jiki a matsayinki na uwa ki taimaka min dan Allah, aneesa tace na fad’a miki sai kin tsugunna jakarta ta dauko ta ciro bandirdin dubu d’aya d’aya guda biyu dubu d’ari biyu kenan, tace ga kud’i nan kina tsugunnawa zan baki, aysha tace Aneesa ni bari in tsugunna, tace sam uwarki nake so tayi bake ba, ummi cikin kuka ta farayin ‘kasa saiga khairat nan tashigo da gudu tana fad’in ummi kizo mu koma anbiya kud‘in aikin da sauri Ummi ta d’ago Wanda idonta ya dame da hawaye haka itama aysha flta sukai suka bar aneesa cikin takaici, aneesa buga hannu tayi tace toh Waye ya biya musu? D’an shuru tayi can tace kodai faruk ne? Tana yin maganan tana kallon magajiya wacce itama din ita take kallo ……… 
Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE