MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 2

MEYE ILLAR YAYA MATA
CHAPTER 2
Dr ya girgiza kai tare da fadin mace aka samu, wani irin shock Alh Ibrahim yaji Lokaci daya duk wani jini dake gudana a jikinsa Ya tsaya dan bakin ciki da takaici, saida Dr ya tabashi sannan yayi firgit Dr yace zaku iya shiga, Dr na fadin haka yayi gaba abunsa, Alh Ibrahim kam juyawa yayi da nufin barin asibitin ba tare da yaje yaga matar tashi ba da kuma yar da aka haifar mishi ba, mama ce ta kira sunanshi wanda yasa ya tsaya cak, karasowa tayi kusa dashi tare da daura hannunta akan fuskanshi tana shafawa tace Ibrahim kaje Kaga matarka, cikin bacin rai yace mama mai zan mata mai zan mata bana bukatar ganinta ita da abunda ta haifa, mama na tabbata tunda kika haifeni Nasan Nima zan haifi d’a namiji, ya mace ba komai bace bata da amfani a wajena Ina bukatar da namiji wlh inda zan sami namiji guda daya da bazan so kara haiyuwa ba domin shi kadai Ya isheni Ina bukatar wanda zai gajeni mai kula da duka harkokina, mai mace zata iyamin, mama kuka takeyi tare da fadin kayi hakuri wasu matan suna haka sai su haifi mata biyu sannan su ya kalli mama da sauri alaman dagaske? Kai ta daga mishi alaman eh tace muje kagansu bai musa ba yace muje. 
Ummi dake window duk taji abunda suke fada jin zasu shigo yasa ta koma da sauri ta kwanta, koda suka shigo Alh Ibrahim baiko Kalli inda yarinyar take ba, sai ummi da yayi ma ya jiki, ta amsa da laflya bai kara cewa komai ba, sai mama ce ta katse shurun da fadin baka dauki babyn ba gata kaman Kai, baiso tashi ba amma haka Ya daure ya tashi ya nufi yarinyar yana ganinta yaga sak shi kaman anyi 
kaki, daukanta yayi yarinyar ta saki murmushi wanda ya kara mata kyau, baiyi k0 minti daya da daukanta ba Ya ajiyeta, tare da fadin zashi Gida anjima zai dawo, aka bar ummi daka ita sai baby da mama, Bayan fitanshi kukan da ummi take boyewa 
ya fito amma bamai sauti takeyi ba dan Kar mama taji, 
*MIYE ILLAR Y’AY’A MATA* da mijinta yasa yake kyamarsu koya manta da mace dana miji Allah ne ke badawa, wasu na nan na neman haiyuwa k0 wani Kala ne amma Allah bai basu ba, shi gashi Allah Ya bashi amma yana fushi da kyautar Allah lallai da yasan irin tausayin da yay‘a mata suke dashi da k0 kadan da baiyi burin samun d’a namiji ba, kallon yarinyar tayi cikin tausayi wacce take bacci abunta, lallai tana tausayawa yaranta musamman zarah data fara girma bata samun wani gata na uba k0 sakewa data samu cikin nan nema ya fara Dan sakema zarah dan a zatonshi namiji zata haifa 
gashi mace ta haifa haka taita tunani tare dajin tausayin rayuwan y’ay’an nata. Kwananta daya aka sallamesu tunda Alh Ibrahim Ya tafi bai dawo ba sai dai ganinsu da yayi a gida, zarah na ganin ummi ta nufeta da gudu tayi hugging dinta tana dariya, Alh Ibrahim kam k0 kallonsu baiyi ba, mama ta taimaka mata suka haura sama zuwa dakinta, Alh Ibrahim fushi yake Sosai wanda ya kasa boyuwa saida Ya fio fili, duk yanda mama taso ta mishi dan ya sauko amma Abun ya faskara Dan haka ta kyaleshi, ummi yanda taga baya kulata Abun ya dameta Sosai gashi 
ita ba dangi ba balle ta kirasu su dibe mata kewa tun tana karama iyayenta suka rasu gashi ita daya suka haifa, bata san inda zata ga dangin mamanta k0 babanta ba dan ance daka nijar suka zo, riqonta ya dawo wajan liman din anguwansu a wajanshi ta taso har Alh Ibrahim Ya ganta yace yana Sonta ya aureta gashi bata son fadama limam matsalanta dama inna adama na nan ne matar limam din wacce ta dade da rasuwa tunda ta rasu bai kara aure ba wannan kenan shine labarin ummi bari muji na Alhaji Ibrahim shima. 
WAYE ALHAJI IBRAHIM? 
Alh Ibrahim Dane ga mlm ayuba,mlm ayuba manomi ne yana da kudi Sosai yana da mata fatima suna zaman lafiya, yan asalin garin kaduna ne zazzagawa kenan amma suna zaune a u/kanawa, suna da yara biyu Ibrahim sai kanwarsa hindatu wacce suke kira da hindu, tana aure a garin adamawa, Ibrahim yayi karatu akan fannin business Dan haka yaba mahaifinshi shawara akan su bude company na sana’an hannu mahaifinshi Ya yarda inda aka fara ginin katon company din mai gefe daban daban, akwai inda ake hada atamfofi da shadda, akwai gefen da ake hada kayan kwalliya akwai gefen da ake hada kayan hannu na yara wato wanda ake saqawa, Bayan an gama komai mahaifinshi yace ya mallaka mishi company din halak malak, tunda ya mallaki company din yake samun mahaukanta kudade inda Ya fara gini a anguwan rimi ya Gina wani mahaukacin Gida, suka koma tare da iyayenshi yace ya Gina gidan shida yaranshi dazai Haifa ne koda sunyi aure bai yarda suje k0 Ina ba, basu dade da tarewa ba Ya auri ummi, shekaranta daya ta haifa zarah, tun a lokacin yake nuna mata ra’ayinshi akan son haiyuwan d’a namiji, shekaran zarah uku mlm ayuba ya rasu, sunji mutuwarshi Sosai Dan abunda Ya bari aka raba musu gado haka rayuwa taci gaba da kasancewa, tun zarah na karama bata wani samun kulawa wajan babanta Dan shi bashi da burin haiyuwan ya mace Dan yace wahala ce ya mace wannan kennan,,,,,,,,, 
Haka rayuwa yaci gaba a gidan Alh Ibrahim cikin rashin jin dadi har ran suna tazo ummi batai taron suna ba amma Ya yanka mata rago guda daya duk da ba wani mai girma bane, hakan bai dami ummi ba dan bata sa ran zai mata ragon bama, yarinya taci suna aysha, wasa wasa har sunyi arba‘in duk da bawai yana kulata bane ummi rashin kulata din da ba yayi Ya dameta Sosai Dan haka yau tace gwara suyi ta ta Kare dan ta gaji, ita ba ita bace taba kanta haiyuwan ba Allah ne Ya bata dan mai yasa zai dinga fushi babu gaira babu dalili. 
Ummi Bayan ta dai daici lokacin dawowarsa ta kuma San zuwa yanzu komai yake Ya gama yana kwance ne, dan haka ta nufi dakinshi kaman ta Sani kam a kwancen ta sameshi amma ba bacci yakeyi ba, jarida ne a hannunsa yana karantawa, zama tayi kusa dashi tana hawaye tare da fadin haba mijina Mai yasa kake hukunta ni akan lailin da bani na aikata ba? Wlh inda ta nice Nima zanso wannan karan in haifi d’a namiji kodan farin cikin ka amma da yake bani nake badawa ba sai Allah ya bamu mace, inaso ka duba dakyau kaifa musulmi ne yaka mata ka amshi duk abunda Allah Ya baka da hannu bibbiyu Dan nuna farin ciki gareshi, wasu …… Ya dakatar da ita tare da fadin ya isa haka, miye Abun farin ciki ga y’a mace bari kiji ita rayuwan mace gaba daya a bauta zai Kare ita kanta bazata iya tsinana ma kanta komai ba balle mu iyayenta, tun daka yanzu muke dawainiya dasu har zuwa sanda zasu girma suyi aure wani yaci gaba dayin hidima dasu, komai sai anyi mata kullum tana fama da bani bani tana karkashin wani tana mishi bauta a haka rayuwanta zai Kare, amma shiko d’a namiji koda aure yayi muna da iko dashi sai abunda mukace sannan shine zai taimaka mana wajan harkokin mu nayau da kullum koda kuwa karfinmu Ya Kare amma ita mace tana gidan mijinta ki
Kalle ni ki gani girma kamani yake ba yaro nake dawowa ba kullum dad’a tsufa nake ina bukatar d’a namiji wanda zai dibe mini kewa tare da daukan duk wani aiki na, ummi a yanzu kam tama bar hawayen babu komai a fuskanta sai mamakin kalaman mijinta wanda ya manta  da Allah shine mai bayarwa mai kuma hanawa kuma ya manta da duk abunda Allah yaba mutum akwai dalili, dakewa tayi dan a zauna laflya tace kayi hakuri na fahimci duk damuwanka haihuwa dai yanzu muka fara saimu kara hakuri tayi ciki na gaba in mun samu haka mu haifi namiji, bai san lokacin daya saki dariya ba tare da rungumota yana mata 
magana a kunne dariya naji ta saki itama daka nan naji dif wutar dakin ta mutu ina ganin haka nayi waje. Yanzu Alhaji Ibrahim Ya sake dan a yanzu yana ganin tana samun ciki namiji zata haifo mishi, ummi taji dadin yanda Ya sake sai dai abunda ke damunta yanda yake nunama yaranta halin k0 in kula, shi bai damu dasu ba baya shiga harkan gabansu baya wasa da Yaran duk da Yaran suna son wasa dashi, amma baya basu fuska, kwanci tashi babu wuya yau shekaran aysha uku zarah kuma tana shekara tara inda ummi take dauke da cikinta wanda yayi girma Sosai gaba 
daya cikin da tayi baya babu wanda yakai girman wannan ganin irin girman cikin yasa Alh Ibrahim tunanin k0 yan biyu zata haifa inko ba yan biyu baneToh d’a namiji ne tunda wannan cikin ya ban banta da sauran, Alh Ibrahim Da mama suna bama ummi kulawa Sosai da Sosai dan itama mama tana da burin samun jika namiji, wata ranan talata cikin dare ummi ta tashi dana kuda wanda ita daya ce a daki, Abun tun tana daurewa har takai ta Fara kuka tare da salati Allah cikin ikonsa yasa ta saki wani nishi mai karli saiga baby Ya fito tare 
da kuka, daukan baby din tayi tana kallo …….. Toh masu karatu ku biyo ni dan jin mai aka samu ….. 
Hmmmm 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE