MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 20

MEYE ILLAR YAYA MATA
CHAPTER 20
Koda su Ummi suka karasa asibitin har an fara yima Zainab aiki basu wani dad’e ba, doctor ya fito yana fad’in na tayaku murna Allah ya sauketa lafiya ta sami y’a mace, zo kuga murna wajansu, sannan Dr ya kara da fad’in ldan aka gama gyarasu za’a kaisu d’akin hutu sai ku gansu, ummi ta kalli zarah tace waya biya kud‘in? Zarah tace baku kuka biya ba? Ummi tace kaman ya? Waigawa tayi ta kalli khairat wacce take zaune kusa da Farida, tace khairat waya biya kud’in? Shuru tayi can ta tashi tare da fad‘in ummi Ina zuwa, bata dad’e ba sai gata ita da rahma, kallon mamaki duka suke ma rahma, zarah ce tayi karfln halin fad’in maiya kawo ki? Kinzo ganin ko Aneesa ta kashe mune da bauta? Kitafl Ina matukar jin haushinki har zaki iya tafiya ki barmu cikin wannan halin? Rahma hawaye takeyi ta kasa furta koda kalma d’aya, khairat tace zarah baki fahimci Rahma ba, zarah tace wani fahimta zan Mata? Eyeh fad’amin? Bayan abunda tayi shine zan fahimceta? Khairat tace zarah ranan da rahma tabar gida na bita d’an in bata hakuri akan ta dawo Gida, Bayan na flta inata nemanta ban ganta ba ina shirin dawowa gida saina hangota a zaune a wani waje, da sauri na nufeta na rungumeta Ina kuka akan tayi hakuri tazo mu koma Gida, tace min bazata koma ba tunda ta fito akwai dalilin da yasa tabar gida, Wanda dalilin da yasa tabar gidan shine tana son ta sami aiki duk da batai karatu ba dan ta sami kud’in da zata sa ayi belling din Abubakar sannan ta sami kud’in da zamu ri’ke dan rayuwar yau da kullum, zarah wani hawaye ne ya silalo mata lokaci d’aya kuma ta rungume rahma tana fad‘in kiyi hakuri ban fahimce kiba, rahma cikin kuka tace Nima ku yafemin zarah na rashin bayanin da ban muku ba kuma na hana khairat ta muku bayani, ciro kud’i tayi cikin jakarta taba ma zarah tace gashi kije ki fito da mijinki, zarah ‘kin amsan kud’in tayi tare da girgiza kai tace a’a rahma kinyi kokari kin biya kud‘in aikin Zainab haka ya isa, rahma tace zarah ni wacece a Wajanki? Tace kanwata, rahma tace toh amsa lndai badai kina kallona a matsayin y’ar kishiyar ummi ba, da sauri zarah ta amsa tare da toshe ma rahma baki tace rahma ban taba kallonki a yarinyar aunty Amina ba Wlh Ina miki kallon wacce ummi ta haifa a cikin, cikin ta ne, karki kara fad’in haka, suna cikin haka wata nurse tace zasu iya shiga kuga baby din, da sauri sukai d’akin sukai tama Zainab sannu tare da daukar baby din wannan yaba wannan haka sukai tayi, khairat tace ma zarah taje ta fito da Abubakar tafiya tayi station direct dan yin belling mijinta, bata dad’e ba sai gasu tare ita da Abubakar haka sukai ta murna, ummi ta kalli rahma tace amma rahma wani aiki kika samu haka? Zamu dawo baya kad’an In baku manta ba rahma anyi zasu tafi abuja jibi dan yin gasan da zasuyi na dafa abinci, kaman yanda Haulat tace jibin Nayi tazo suka kama hanyar abuja suna tafiya sunzo wani kauye tayar motarsu ta fashe Wanda yasa dole suka tsaya dan su canza wata, duka y’an motan suka fito, Haulat tace ma rahma kishi takeji Sosai, rahma tace bari inje in samo miki ruwan, Haulat tace Kar kuma ki tafi mota ta tashi, rahma ta kalli driver din tace gyaran zai dad’e ne? Yace eh zamu canza taya ne, muna canzawa zamu tafi, tace 0K ta kalli Haulat tare da fad’in bari inje samo miki, Haulat tace kiyi sauri, shiga cikin garin tayi tana ta tafiya wani shago ta hango ta siya ruwa amma babu canji wata mata dake wajan tace ta barshi zata bashi, godiya rahma ta mata sannan tai gaba itama matar ta biyota tare da fad’in amma dai ke bakuwa ceko? Rahma tace eh muna tafiya ne tayar mota ta fita shine ake saka wani 
matar tace eyya suna cikin taflya wani mai mota yazo da gudu ya bangaje matar ta fad’i duk kayanta ya baci rahma kallon motar tayi da bashi da niyan tsayawa da gudu tabi motar taga tayi mata Nisa tsayawa tayi ta d’auki dutse tajefa ma motar glass din motar ya fashe ta baya cak motar ta tsaya, da sauri ta nufi motartare da shiga gaban motar ta tsaya, bud’e murfin motar akayi wani Guy hadadde ya fito daka cikin motar, kallonshi tayi cikin tsana tace tir da hali irin naka, maika d’auki mutane? Ka buge mata kana kallo amma kaki tsayawa, kud’i yana rudank …… Ya d’aga mata hannu alaman tayi shuru yace Mai kike bukata? Kud’i right? Basai kin fake dana buge wata ba kice kina son ki ro’keni kud‘i, nawa kike 50? Check book ya dauko da biro yace dubu d’ari kike so? D’ari biyu? D’ari biyar? Million d’aya ko nawa kike so? In baki karki ‘batamin lokaci fad’i abunda kike bukata? Rahma da takaici ya gama cikata yama maida ni y’ar maula shi baima d’auki abunda yayi a komai ba, kallonshi tayi cikin zafin rai tace baka da kud’in da zaka bani sannan ina son ka sani kud’i baya siyan rayuwa, kana takama kana da kud’i inda ka kashe matar daka bige kana tunanin zaka iya biya danka dawo Mata da ranta? Ku masu kud’i kuna d’aukan Talaka ba komai ba kuna wulakanta Talaka, kasan Mai gobe zata haifar? Yau kana ganinka Mai kud’i kana taka Wanda kaso Allah zai iya jarabtanka ya kwace komai daya baka sai yaga yanda za kayi, murmushi yayi tare da fad’in kin gama? Yana Mata tambayar ne a gadarance, tace koda ban gama ba bana tunanin zan iya kara bata lokaci na da baki na wajan magana da wanda bai son abunda yakeyi ba mara tunani kuma, tana fad’in haka ta wuce, magananta sun mishi zafi Sosai shine mara tunani ido ya lumshe tare da buga motarshi   cikin zafin rai da takaici, rahma itama ranta a bace ta nufi inda motarsu yake tana ko zuwa taga ana shiga Haulat tace yauwa hankalina ya tashi najiki shuru zomu shiga, motar suka shiga, suka karasa garin abuja direct masauki suka nema dan gobe ne gasar da safe. Washe gari muka shirya muka je wajan gasar, naga manyan mata Wanda naji na karaya, domin nasan sun fini iya girki, mu Goma aka bamu girki ko wacce ta fad’i abunda za tayi, nidai dambu na d’auka, abincin gargajiya, an bamu lokaci awa d’aya cikin ikon Allah Kafin lokacin na gama, aka saka girkin kowa a plate don aji nawa yafi dad’i, koda za‘a fad’i sakamako daka na uku aka fara tunda naji ba’a kira sunana a na uku ba Nasan na fad’i, aka kira ta biyu, ana fad‘in ta Farko naji sunana, bakaramin mamaki nayi ba, nan take aka ban check din million d’aya da wasu kyautuka, Bayan na amso kud’in naba Haulat akan ta cira abunda zata d’auka tace a’a in ri’ke kudin ta d‘auki sauran kyautar da akamin, Nayi ta mata godiya, D’an shuru rahma tayi sannan ta kalli ummi tace toh Kinji yanda na sami kud’i 
Ummi tace Allah ya miki albarka rahma su kuma Su Haulat Allah ya biyasu, duka yaran suka amsa da Ameen, zarah tace amma dai yanzu kin dawo Gida koh? Babu inda zaki koma, rahma tace zarah dole zan koma in taimaki Haulat Tana cikin damuwa, zarah tace name kuma? Tace Akwai gidansu na gado dake garin Jigawa, sai suka maida gidan boko yara suna zuwa amma ba Sosai ba, Toh shine aka sami wani mai kud’i yace gwamnati ta saida Mai domin, Wai fllin gwamnati ne, shine hankalin Haulat ya tashi Sosai, yanzu haka zan bita mu tafl Jigawa tare, ummi tace kai Allah ya kyauta tabbas ya kamata ki taimaka mata Kema kije ki tayata neman hakkinta sannan in Kinje ki tabbata kin kiramu muji halinda kuke ciki, rahma tace insha Allah, ta dad’e a asibitin sannan ta wuce. Kwanan Zainab uku aka sallamesu, gida suka nufa direct, Bayan sun shiga Gida suka ga babu kowa wajan da suke kwanciya suka nufa dan su huta, ummi tace ma zarah da khairat da aysha ya kamata kuje ku daura abinci, suka amsa da Toh sannan suka nufl kitchen dan d’aura abinci, sirikar Zainab tazo taga y’arjikan tata, Tana ta murna tare da godewa Allah da yasa taga jinin d’anta, sai kallon yarinyar take tana hawaye tare da fad’in yarinyar na kama da yazeed Sosai, ta bu‘kaci Zainab ta koma gidanta Wanda suka rufe har Ayi suna, ummi ta amince, Zainab suka koma gidan ita da yarinyar ta, harda aysha da khairat suka koma dan tayasu zama dan gidan babba ne, koda Aneesa ta lura basa gidan ba karamin haushi taji ba dan taso ta wulakanta su da suna, amma sai taji Sun tafi gidan yazeed a can za’ayi hakan ya mata zafi Sosai, gashi yanzu basa zama a gidan harta ummi ummun yazeed ta roketa akan ta dinga zuwa kullum tunda tace bazata zauna a gidan ta kwana ba, sai dare suke dawowa su tawo ma mama da abincinta,
Aneesa yanzu su suke dafa abincin da zasu ci, wanda magajiya ce ke girkin, magajiya Tana aiki Tana bata fuska ta kalli Aneesa dake zaune akan kujeran kitchen din tace Aneesa gaskiya fah na gaji Wlh, Aneesa tace kiyi hakuri magajiya dan Allah, bari su gama Sunan su dawo zan nuna musu matsayinsu, magajiya tayi tsaki tare da fad’in ni tea din da khairat take had’a mana nake kewa wlh gashi ban San yanda y’ar banzan take had’awa ba, Aneesa dariya tayi tare da fad’in saiki kira ki tambayeta ai, magajiya turo baki tayi irin na goggun y’an duniya tace Aida zan iya da nayi, yanzu naga wuyansu ya fara kauri, Aneesa tace zan seta musu zama. Su rahma sunje Jigawa cikin kauyen ‘Babura wajan kauye ne Sosai, dan makarantu guda biyu he a kauyen kuma duk na yara wato primary babu secondary a kauyen sai mutum ya shiga cikin gari, a gidansu Haulat na kauyen suka sauka wanda yakejikin makarantar kuma in Haulat tazo a nan take sauka, gidan yayi kura Sosai, haka suka fara gyarashi lokaci kad’an gidan ya koma kaman bashi ba, yayi ‘kal, saboda Sun gaji Tea da bread kawai suka ci suka kwanta, Washe gari da safe suka shirya suka nufi gidan mai anguwa, Bayan sun isa suka ga mutane da dama masu Kai koke wajansa tunda shine kaman Sarkin su, Haulat 
gaisawa sukayi inda ta Fara mishi magana akan yasa baki akan makarantarta da ake kokarin kwacewa, yace Haulat yanzu filin bana gwamnati bane an saida ma wani, shine kawai zai iyajanyewa Wanda bana tunanin zai janye domin naji ance zai bud‘e hotel ne da Plaza Kinga lndai ya bud’e Muma zamu sami ci gaba kauyenmu zai zama gari, babu yanda Haulat batayi ba amma Mai anguwa daka karshe hakuri ya bata, rahma ce tayi karfin halin tambayan Waye ya siya wajan fad’a mata yayi yace alh Mahmud karaye, nanata Sunan tayi dan kaman tana jin Sunan, tace a ina yake? fada mata office dinshi yayi tare da fad’in a cikin Kano yake, taflya sukai gida, rahma ta kalli Haulat tace gobe zani Kano inje inga mutumin in Mai magana, Haulat tace kina ganin zai yarda kuwa? Rahma tace insha Allah zanje in gani. Anyi Sunan Zainab yarinya taci Suna Fatima suna kiranta ummul khairi, Zainab inta kalla yarinyar takanci kuka tare da fatan Inama ace yazeed yana Raye, Bayan suna suka koma Gida inda sukaci gaba daka inda suka tsaya, Aneesa da magajiya na zaune a falo ummi ta kawo ma Aneesa juice, kallonta Aneesa tayi tare da fad’in ni kike so In zuba, d’aukan jug din tayi ta Fara zuba ma aneesa tazo zata bata ya zube ajikin Aneesa, tashi Aneesa tayi ta d’aga hannu zata Mari ummi da sauri khairat ta ri’ke hannun ummi kam ta rufe ido tana jiran saukan Mari,jin shuru yasa ta bud’e ido taga khairat ta ri’ke hannun Aneesa, khairat tace karki kara gigin aikata wannan abun Aneesa tace khairat sakemin hannu, khairat kin sakin hannun tayi,jin muryan zarah zukayi tana fad’in khairat sake mata hannu kina da hankali kuwa? Maza sake mata hannu Kafin in mareki, khairat sakin hannun Aneesa tayi, zarah ta kalli khairat tace karki kara aikata abunda kikayi Aneesa sirikar nan gidance dole ku girmamata domin kuma a girmama ku I’n kunyi aure, Aneesa mamakin maganan zarah takeyi, khairat tace zarah ummi fah tazo zata mara, zarah tace toh sai Mai? Duka y’an uwanta kallon mamaki suke ma zarah, zarah taci gaba da fad’in ke baki ga abunda ummi tayi mata bane? Aneesa ta kalli khairat tace Kinji abunda yayarki tace koh? Toh dan haka saiku koya daka gareta, zarah tayi murmushi tace Aneesa Mai kike bukata yanzu? Aneesa cikin jin dad’i da gadara tace babu komai sama suka haura ita da magajiya, suna shiga d’aki Aneesa tace magajiya Kinga abunda ya faru kuwa? Zarah ta dawo wajena tabar y’an uwanta, magajiya tace na gani amma bakya tunanin makirci take kullawa? Aneesa tace Kai Anya kuwa ban tunanin haka, magajiya tace koma miye zamu saka mata ido mu gani,inko dagaske ta dawo wajanmu dole ta koma d’akinta, dariya suka saki cikin jin dad’i, su zainab da khairat da aysha, suma barin falon sukayi cikin takaicin abunda zarah tayi, ummi ta kalli su zainab dake ta zirya tace lafiya kuwa? Aysha tace ummi Ina mamakin abunda zarah tayi, Zainab tace ummi daka yau zarah ba yayata bace tunda harta zabi aneesa akanmu, haka sukai ta fad’in magana cikin fushi, ummi shuru tayi dan itama Abun ya dameta, zarah na kitchen ummi ta sameta tace zarah, waigowa tayi ta kalli ummi, ummi tace zarah nasan abunda kikayi akwai manufa, ni mahaifiyarki ce nafi kowa sanin halinki ki fad’amin Mai kike shiryawa, cikin kuka tace ummi nice babba a gidan nan, bazan iya zama ina ganinmu cikin wannan halin ba, Aneesa tana son girma tana son taga ana binta sau da kafa, Nayi 
tunani in bita domin in sami daman kwato mana dukiyarmu ne, amma ummi dan Allah karki fad‘ama su zainab abunda nake shiryawa, ummi ta rungume y’ar tata tace bazan fad’a musu ba Allah yayi miki albarka, zarah ta amsa da Ameen. 
Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE