MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 22

MEYE ILLAR YAYA MATA
 CHAPTER 22
Aneesa na d’aki saiga kira an kirata, d’auka tayi tasa a kunnenta, ban San ma’l aka fad’a mata ba naga ta tashi zumbur tayi waje d’akin magajiya ta shiga, Tana shiga ta rufe kofarda karfi tare da fad’in magajiya ina kud’in da nake baki duk wata ki tura yau ya kirani yace wata uku kenan baki tura mishi ba, magajiya tace heeey ya isa haka ki daina min ihu Inba so kike wani yaji abunda ke faruwa ba,inko wani yaji kin shiga uku domin sai an kamaki rayuwar prison za kiyi ko kuma a kashe ki  Aneesa tace magajiya ni kike fad’a ma haka? Toh Bari kiji Indai aka kamani dole Kema a kamaki domin komai tare mukeyi dan haka maza ki fito min da kud‘in da nake baki tana fad‘in haka tabar d’akin, zarah dake labe duk taji abunda suka fad’a, Aneesa d’akinta ta koma tana shiga taga wayarta na kara, d’auka tayi mutumin yace ki flto waje ina wajan gidanku, aneesa tace maiya Kawo K ….. Bata gama magana ba ya kashe wayan, flta tayi tana dubawa k0 akwai wanda yake ganinta, aiko tana Flta taga mutumin hannu ya mi’ka ma Aneesa alaman ta bashi kud’i, duk wannan abunda suke zarah na sama na kallonsu, kallo d’aya zakama Aneesa ka gane a tsorace take, Aneesa tace ka tafl zan aiko maka dashi yanzu banda cash, yace Ina babu inda zani sai kin ban kud’i kona tona miki asiri, Aneesa ganin in bata sallameshi ba zai iya aikata komai yasa ta cire awarwaran hannunta ta bashi tare da fad’in gashi zinari ne saika saida, yana amsa yabar wajan aneesa ta dawo ciki, zarah data labe ta fita tabi bayan mutumin tana cikin tafiya taga mijinta Abubakar dake fushi da ita akan abunda takeyi ma Aneesa, yace zarah lafiya na ganki a haka? Tace Abubakar zo muje dan Allah zan maka bayani daka baya nuna Mai mutumin tayi tace dan Allah mu kamashi akwai abunda nake son sani muje binshi suka farayi ganin kaman shi suke bi yasa ya fara gudu, Abubakar shima gudun ya fara har Allah ya bashi Sa’a ya kamashi, mutumin cikin tsoro ya fara fad‘in dan Allah ka sakeni in tafi, zarah tace Mai kuke boyewa kaida Aneesa fad’a min inji? K0 in kira police mutumin yace zan fad’a ba komai nake boyewa ba sai kisan alh Ibrahim mahaifinku da Aneesa sukayi, zarah da Abubakar cikin firgici sukace me? Mutumin samu yayi ya ture Abubakar ya gudu, zarah tsayawa tayi kaman an dasa gunki,ashe dama dagaske kashe mahaifinsu akayi, wani irin kuka takeyi Mai ban tausayi, Abubakar yaita rarrashinta akan tayi hakuri, yace Toh yanzu sai ki daina biye mata ai, tace Abubakar inada dalili Labarin abunda take shiryawa ta bashi, koda suka koma Gida tama ummi bayani ummi tace yanzu abunda za tayi shine ta samu dukiyar su ta dawo hannunsu Kafin a hukunta Aneesa,zarah tace hakane, Aneesa must pay for what she did. Aneesa ce zaune cikin d‘aki ita d’aya saiga zarah ta shigo ta zauna kusa da Aneesa tace lafiya kuwa Aneesa? Aneesa tace zarah faruk dazu yamin magana akan yana son yaba farida wani abu a cikin kud’in nan, zarah tace Ahap abunda nake fad’a miki kenan tun kwanaki akan ki bashi ya dawo da kud’in na d’anki ko naki signing kawai zai miki shikenan komai ya zama naki, aneesa tace hakane zarah sai yanzu nake ganin lokaci yayi daya kamata inyi haka, toh yanzu taya zan had’a komai? Ina nufin takardan yarjejeni, Amina ce ta shigo d’akin Tana fad’in gashi nan na had’a miki komai kawai kisa faruk yayi signing komai zai zama na d’anki, Aneesa cikin jin dad’i ta amsa tare da fad’in nagode nagode Bari in Kai mai yanzu kuwa, fita tayi ta nufi d’akin faruk, samunshi tayi a wajan window yana 
tsaye, sunanshi ta kira da faruk, waigowa yayi tace faruk gashi yace Mai nene tare da amsa, tace signing nake so kamin yanzu akai, yace takardan menene wannan? Tace so nake duka dukiyar nan ya dawo Sunan baby na ya tashi daka kan ka, yace what? Tace ina jira kamin yanzu kaban, yace mai yasa Aneesa, tace kasan Dai ina tare da sirrinka koh dan haka maza kayi min signing Kafln raina ya baci kowa yaji, d’aukan biro yayi badan ranshi yaso ba yayi mata signing ya bata cikin murna ta flta Tana shiga d’akinta ta fad’a gado tana dariya, zarah da Amina suka shigo suna fad’in Aneesa, aneesa tashi tayi ta mi’ka musu tana murna tare da fad’in da badan kuba da duka dukiyar nan yana wajan faruk daga karshe harda farida da abunda zata haifa za’aci yau gashi komai ya dawo wajena, Amina sauri tayi ta boye flle din da Aneesa ta basu ta canza wani, aneesa tana ta murna, Zainab da tazo wucewa taji komai cikin rashin hankali Ta nuf’I ummi tana fad’a mata abunda sukayi, khairat tace zarah mai take nufi, lallai zarah daka yau mun cireta daka cikin y‘ar Uwar mu, daidai lokacin zarah tazo, aysha tace zarah tafi ki bamu waje daka yau duk wani girmamaki da muke ya zube keba yar ……. Ummi tace ya isa haka ya isa, kuna zarginta akan abunda baku sani ba labari ummi ta basu, kuka suka fara tare da ro’kan zarah gafara Zainab tace Mai yasa kika boye mana kikayi komai ke d’aya,? Zarah tace zainab mubar wannan maganan yanzu tunda mun dawo da dukiyar mu sai mu dau fansa akan kashe mana mahaifi, khairat tace hakane yanzu saimu kira rahma tazo itama mu d’auki fansa tare, aysha tace toh mama Amina 
itama tare kukeyin aikin da ita? Zarah tace eh itama tasan komai. 
Rahma tana zaune tana had’a kaya dan tafiya kaduna wajan y’an uwanta domin d’aukan fansan mahaifinsu, Haulat tace rahma kiyi sauri Kar kiyi zuwan dare rahma tace toh, jin karan mota sukayi ya tsaya kofar gidan, fita rahma tayi taga mutanan Mahmud ne mutum d’aya ne yazo inda rahma take, yace Kin tunani koh? Bata kulashi ba ta kira yaran dake karatu tace su korashi yara suka fara mishi ihu tare da tureshi har yana faduwa, koda suka kaishi waje ranshi a bace rahma ta kwashe da dariya tace karka kara zuwa nan har sai lokacin ku ya cika, tana fad’in haka ta koma, rahma ta dawo kaduna, koda alh Mahmud ya sami Labarin tabar kauyen da kanshi yaje ya sami Haulat tace rahma ta karaya ne tabar garin? Tace ko d’aya rahma bata da tsoro a kullum bata sama ranta faduwa sai nasara dan haka zata dawo, kuma tun yanzu ka Fara sawa ka fad’i, murmushi yyi tare da barin wajan. 
Aneesa tana kwance taji karan Abu ya fad’i kaman glass tashi tayi, Tana bude ido taga hotan alh Ibrahim ga jini a jiki, wani irin ihu ta saki tare da flta daga d’akin da gudu tayi kasa tana ihu, dukansu dake gidan suka fito, zarah tace Aneesa mai nene? Cikin kuka tace naga alh I ……. Shuru kuma tayi tana sauke ajiyan zuciya zarah tace wa kika gani? Tace zarah bani ruwa insha, zarah kitchen ta nufa ta d’auko mata ruwa tare da fad’in muje in rakaki d’akin ki, binta tayi cikin tsoro har suka shiga d’akin bata ga komai ba, zarah tace ki kwanta aneesa babu abunda zai faru Nasan mafarki kikayi, Flta zarah tayi tare da rufe ma Aneesa kofa, ranan dai kasa komawa bacci tayi dan idonta biyu har gari Ya Waye, bayan ta shiga toilet tayi wanka ta nufi mirror taga anyi rubutu da jini ‘Aneesa Kun kashe ni Kema saina kashe ki saina dau fansa‘ ihu ta saki tare da fita daka d’akin da gudu, tana ihu, da magajiya sukaci karo Aneesa tace magajiya alh Ibrahim yace zai kasheni zai d’auki fansa a ka ….. Da sauri magajiya ta toshe mata baki ganin su zainab sunzo wajan suna tambaya lafiya, aneesa cikin kuka take fad’in Wlh naga rubutu a mirror dina da jini, zarah tace muje mu duba Aneesa kin binsu tayi koda suka shiga d’akin babu komai a mirror dariya sukayi tare da fad’in u wil pay for what u did Aneesa, wayar magajiya ne yayi kara ta d’auka ban San mai aka fad’a mata ba naga taja hannun Aneesa zuwa d’akinta, magajiya tace Aneesa muna cikin tashin hankali yanzu aka kirani Wai akwai shedar da aka Bari akan kisan alh Ibrahim a wajan da muka kashe shi Kinga ya kamata muje mu gani, aneesa tace yanzu kuwa, fita sukayi harda faruk suka nufl gadar da suka kashe alh Ibrahim sai dube dube suke a wajan, suna cikin duba Abu saiga zarah da y’an uwanta sunzo Aneesa cikin tsoro tace Mai kukeyi a nan? Zarah tace munzo wajanki ne keda kika kashe mana mahaifi Munzo d’aukan fansa, baya Aneesa ta farayi aiko tana cikin yin baya ta fad’a daka gadar Allah ya taimaketa ta ri’ke karfan gadar da hannu d’aya, ihu ta Fara saki magajiya ta Fara kiran faruk dake mota jin ihunsu yasa faruk yazo da gudu ko Lura da Suwa suke wajan baiyi ba Ya fara kokarin kamo Aneesa yace Aneesah bani hannunki bazan bari ki mutu ba kaman yanda Abba ya mutu Nayi takaici dana kasa ceton Abba bani hannunki, magajiya dake tsaye jin faruk ya tona asiri yasa ta d’aura hannu a Kai cikin ikon Allah faruk ya ciro Aneesa sai a sannan yaga y’an uwanshi dasu ummi da mama Amina, yace zara…. Kafln ya karasa zarah ta wankeshi da Mari zai kara magana ta kara sakar Mai wani Marin tace faruk mai Abba yayi maka da ya Fuskanki wannan sakayyan da kayi mishi faruk ka cucemu ka nuna ma duniya kai d’an sale ne ka d’auko halin ubanka dai dai lokacin police suka zo harda mutumin dasu aneesa suke bama kud’i, mutumin yace zarah faruk bashi bane ya kashe mahaifinku Bari in fad‘a muku yanda Abun ya faru ….
Mutumin ya fara magana kaman haka ranan da Abun ya faru Ina wajan wancan dutsen a kwance duk ina kallonsu amma su basa ganina lokacin da faruk da alh Ibrahim suke magana akwai wata igiya dake kusa da kafarshi yana danja baya kafarshi ta shiga cikin igiyarAneesa taja igiyar Wanda shine silar fadawanshi duk da bai fad’a kai tsaye ba ya ri’ke Abun gadar faruk ya mi’ka Mai hannu yana son ciro shi amma ya kasa wanda dole yasa Alh Ibrahim ya fad’a duk ina wajan ina kallonsu, Aneesa tace faruk ka kashe mahaifinka faruk ya rud’e matuka Aneesa ganin haka ta d’aura Mai hukuncin kisa din wanda bashi ya aikata ba, bayan sun bar wajan, na sami number din Aneesa na kirata akan nasan komai ta tsorata Sosai tace Tana son mu had’u, bayan mun had’u na nuna mata video din abun daya faru wanda a lokacin na d’auka da y’ar wayata, ta tsorata Sosai tace in rufa Mata asiri zata dinga bani kud’i duk watajin haka na amince Toh kunji yanda Abun ya faru amma faruk baida laifi Aneesa ce da wannan matar ya nuna magajiya, faruk shago wuyan Aneesa yayi tare da fad’in kin cuceni kinyi amfani da tsoran da nakeji kikasa na musguna ma y’an uwana, dakyar aka kwace Aneesa daka shakar da yayi mata police sukai gaba da Aneesa da magajiya, zarah ta tsayarda police din tare da fad’in shima faruk a kama shi domin shima Mai laifi ne, tunda ya rufa ma masu laifi asiri, haka aka tasa keyar faruk aka wuce dashi, su kuma suka koma Gida cikin farin ciki, a falo suka suka zauna suna fad’in Allah yaji qan Abba Allah sarki Abba yanzu sun kashe ka, ihun mama suka ji Tana fad’in wani Abba din cikin Tashin hankali faduwa tayi kasa sumamma, cikin Tashin hankali suka nufeta kiran Dr akayi Don ya dubata, Dr yace ta tsorata ne hala in anyi Sa’a inta tashi zata iya tuna komai, sallama yayi musu Bayan yace a bishi a amso mata magani, suna nan zaune har mama ta farka tare da salati, binsu tayi da ido sai kuma tasa kuka tare da fad‘in rayuwa kenan Idan Ina kallonku sai inji inama Ibrahim na nan, dukansu hamdala sukai domin sun gane ta tuna komai ganin suna hamdala yasa tace maiya faru? Ina faruk naga ban ganshi ba a nan, zarah tace mama faruk ……. Labarin abunda ya faru suka bata basu boye mata komai ba, mama cikin kuka take tasa musu albarka tare da fad’in yanzu duk saboda ni kuka shiga wannan halin kuka zama bayi, Allah ya muku albarka suka amsa da Ameen. 
Yanzu rayuwar gidan Alh Ibrahim ya canza komai ya dawo kaman da, yanzu sunajin dadinsu, gaba daya suna zaune a falo rahma tace gobe zata koma Jigawa dan karasa abunda ta Fara, zarah tace rahma tare dukanmu zamu dan bazamu Bari ki tafi ke d’aya ba dole mu tayaki, rahma taji dad’i Sosai, Washe gari da safe suka shirya su biyar a motar Haya suka tafi Bayan iyayensu sunyi musu addu’an nasara da kuma fatan sauka lafia, Sun sauka Jigawa wajan karfe hudu duk sun gaji, Haulat tayi farin cikin ganinsu Sosai, Bayan sunci abinci sun koshi, suna d’an flra Haulat tace rahma Anya zamuyi nasara kuwa gashi saura kwana shida, rahma tace karki damu Haulat Kafin muzo nan saida muka shiga kauyen kusa kusa muka wayar musu dakai akan ilimi kuma sunyi alkawarin ranan Monday zasu turo yaransu Kinga ranan shine lokacin daya bamu, Haulat cikin jin dad’i tace Kai Alhmdlh Allah ya tabbatar mana da alkhairi, suka amsa da Ameen. 
Alh Mahmud yana office wasu mutane biyu suna ta mishl bayani akan Irin ginin da zasu tsara Idan sukai nasara, shi gaba d’aya hankalinshi baya wajan tunani yakeyi ba tunanin komai yake ba saina Rahma ranan da suka fara haduwa harta fasa Mai glass din mota da zuwan da tayi ta sameshi suna meeting ta gaya Mai maganganu, murmushi yayi tare da lumshe ido,jin kaman ana kiran sunanshi sir sir yasa yayi firgit, tare da kallonsu suka ce sir mun gama, yace OK, suna fita saiga wani ya shigo office din, yace sir yarinyar ta dawo, yace 
what? Mutumin yace jiya ta dawo garin, alh Mahmud yace ok, tare da sakin wani murmushi. Kaman dai yanda ya fad’a hakan ta kasance, yau dai dai wata d’ayan daya basu kuma ya kasance ranan Monday , rahma dasu zarah suna tajira suga yara sunzo amma shuru gashi Lokaci nata kurewa gaba d’aya hankalin rahma dana Haulat ya tashi Sosai, suna cikin haka saiga wata yarinya tazo da gudu ta nufi rahma tana fad’in Anty ban San maita fad’a mata ba naga ran rama ya baci Sosai domin fuskanta kawai zaka kalla kasan Tana fushi , dai dai lokacin Alh Mahmud yazo inda suke kallon rahma yayi yace time off, lokaci ya Kare kin fad’i nayi nasara, karasawa tayi inda yake ta wanka Mai Mari ji kake tas, kowa dake wajan ya tsorata musamman security dinshi dake wajan, rahma tace kayi nasara kake cewa? Nasaran cuta tun Farko inda kasan haka za kayi Mai yasa kasa wannan Wasan ka bata mana lokaci, kana kiran kanka mutum Mai kirki Ashe karya ne, dama na fad’a kai d’an kasuwa ne, baka san Asara ba sai cin riba nasan duk yanda za kayi sai kayi dan kayi nasara, yace rahma mai kike fad’a haka? Tace abunda ka aikata aika fi kowa Sani, zarah tace haba rahma miye haka? Tace zarah bari kiji abunda yayi yara Sun shiga babbar mota za’a kawo su nan yaje ya dakatarda motar dan Kar suzo shi yayi nasara, yace ni Mai kike fad’i haka? Tace ya isa haka zamu bar maka nan wajan gobe kayi duk yanda Kaga dama Tana fad’in haka tayi ciki, suma y’an uwanta da Haulat sukai ciki, alh Mahmud kam tunani yaita yi akan Mai take fad’i haka, rahma cikin kuka ta rungume Haulat Tana fad’in kiyi hakuri Haulat ban San haka Abun zai kasance ba Haulat tace ya isa rahma nayi hakuri babu komai a raina domin haka Allah ya tsara, had’a kaya suka farayi domin motar asuba za subi, koda alh Mahmud ya koma office sawa yayi Ayi bincike domin ance matarshi ce taje kauyen ta tare yaran, bayan anyi bincike ya gano cikin ma’aikatanshi ne sukai hakan, fita yayi cikin fushi danya samu wanda yayi Abun sai yaga mutumin yana fad’ama wani saboda ni oga ya sami filin inda badan niba daya fad’i, alh Mahmud kiranshi yayi yace ya shiga mota Jigawa suka koma inda yagansu a waje su duka da alama Haulat Tana fita da manyan kayan dake cikin gidan ne, ganin alh Mahmud yasa duka suka tsaya suna kallonshi, kusa da rahma yaje yace nazo na baki hakuri domin bani naci gasar ba Kece kika ci ,kiran mutumin yayi yace ya fito yace fad’a mata abunda kayi, mutumin ya fara bama rahma hakuri yace nine na tare yaran dan Kar suzo domin abunda kika saka yara sukamin rannan, amma dan Allah kiyi hakuri, alh Mahmud yace Toh Kinji abunda ya faru ki daina zargina yanzu filin ya zama naku yana fad’in haka ya wuce, Haulat kam wani ihun murna Ta saki, saboda murna suka ce gobe zasu had’a party, bayan sun shiga ciki su zarah sukace ta kira Mahmud ta gayyaceshi party din, rahma tace Wlh kunya nake ji, ni bani ma da number dinsa, zarah tace naga card dinsa daukowa tayi tace ga number dinsa nan daukan wayan rahma tayi ta kira number din tare da mi’ka mata wayar to muje zuwa shin Alhj mahmud zai amshi gayyatar rahma kuwa

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE