MIJIN DARE CHAPTER 2 BY R.HUSSAIN(Zinariya)
MIJIN DARE CHAPTER 2 BY R.HUSSAIN(Zinariya)
*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
_BANYI DON CIN ZARAFIN WANI KO WATA BA,IDAN KINGA WANI ABU WANDA YA DANGANCE KI, TO ARASHINE🙏_
*SADAUKARWA GA ƳAN ƘUNGIYAR ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION,☀️🌟*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
______Tunda Baba ya kasa kayan miyansa ya zauna ya na tunanin yanda zai yi da Inteesar abun ka da Fulanin Daji ba wani ilimin muhammadiyya bare ya yi tawakkali, “Baba tsoho a ba ni kabewa” wata Mata ta faɗa wacce ba ta fi sa’ar Firdausi ba, ɗaure da goyonta, ga kuma wani a hannunta.
“to ta nawa” Baba Ayuba ya faɗa
” zu ba min ta hamsin”
Zuba mata ya yi ya miƙa mata,kuɗinsa ta ba shi ta ce” shige mu je” ta riƙo Yaron su ka tafi.
“yanzu ga wannan Matar da gani bata fi sa’ar Firdausi ba,amma ga Yaronta ya girma, mtswww wannan baƙin jini na Inteesar ya yi yawa,wallahi duk wanda ya zo, ko mara hankali ne ba shi zanyi na huta”
Hangota ya yi kamar ko da yaushe ta sha make-up ɗinta, ta na taku one by one.
baƙinciki ne ya cika masa zuciya, ya ɗauke kansa.
Rumfar Mahaifin nata ta nufa, sannu da kasuwa Baba” ta faɗa ta na marairaicewa, “to meye kuma ke ni banyi ko sisi ba bare ki ce, Inna ta aiko a ba da kuɗin cefa ne, ruɓaɓɓun kayan miya ya fara haɗa mata attaruhu,albasa,tumatir da yayin salad.
“Baba ba kayan miya zan karɓa ba, daman Hafsat ce ta haihu yau ne suna, shine Inna tace” ka ba ni kuɗin mota in wakilceta, tunda ba ta da lafiya, idan ba ta je ba, ba daɗi tunda maƙota ne Baba Hadiza ba za taji daɗi ba”
“to radio uwar zuba, ni ba ni da ko sisi,ai ba dole ba ne ki haƙura da zuwan mana mtswww ji be ki, ko kare bai taɓa zuwa ba,bare ɗan mutum”
Cuno baki tayi ta na ƙananun maganganu.
Halinta ne rashin kunya, juyawa ta yi ta koma gida dan sanarwa Innarta Laure(Umma), ” Wallahi ko da bashi sai naje” ji tayi kamar wani Saurayi na bayanta da sauri ta juya taga wayam ba kowa, mtswww ta ja tsaki.
Duk abinda taka MIJIN DARE na tare da ita, duk wani fitsara da rashin son ibada da taimakonsa take duk wannan abun.
Har ta isa gida tana jin haushin hanata kuɗin da Baba ya yi.
“Assalamu alaikum, to ya ce ko sisi baiyi ba” ta faɗa a lokaci ɗaya. “wa’alekummussalamu, to ai shikenan, Babanku ba ya kyauta min ni ban je ba ke baki je ba ai ba daɗi, duk rabin hidimar bikin Hafsat a gidansu aka yi, katangarsu ɗaya da gidansu Hafsan.
Irfan ne ya shigo, hannunsa riƙe da file na credential ɗinsa, Yaron ya na da son karatu da kansa ya ke ta ƙoƙarin inganta rayuwarsa da ta ƙannensa masu tasowa.
“Umma lafiya naganku haka?”
“ni da Babanku ne yau sunan Hafsat ya ce baza ni ba, na tura Yayarku ya ba ta kuɗin abun hawa, ya ce ba shi da ko sisi”wanda ake kira da Irfan yace” to dole ne a haƙura mana, ba ance gida za’a tawo da ita wanka ba idan ta zo kwaje mata barkan”
“to ɗan rainin hankali ba za’a haƙuran ba, ka na tafiya wuya uwa mariƙar lema mtswww” Inteesar ta faɗa ta na jin haushin ƙanin nata.
Kuɗi ya ɗauko a aljihunsa ƴan ɗari da hansim-hamsin har da su biyar-biyar yace”kinga ni wallahi ba zan bayar ba”
Umma ce ta hau lallaɓashi, da ƙyar ya ba da ɗari biyu, ya wuce ɗakinsa wanda yake mai ƙofar langa-langa, sai ya durƙusa ya ke shiga ɗakin.
Da murna Umma ta bawa Inteesar tace” ma za ki shiga, Allah ya sa ba’a tafi ba” to ta amsa ta na shiga ɗakinta ta ƙara shafa powder ta kuma jujjuya jiki ta fito, “na tafi”
” to ki mata barka, kafin ta iso, na shiga” (gare ku iyaye a duk lokacin da yaranku za su fita, ku dinga yi musu addu’a tare da tunasar da su addu’ar fita daga gida, idan ba su iya ba, ki na faɗa, su na faɗa har su iya da kansu).
Gidan kuwa cike yake da ɗan zuwa gidan suna, a yangace Inteesar ta shiga gidan, Yaya Haidar babban ɗa a gidan ya na ciki, ya kawo Matar Uban gidansa, ganin Inteesar ta shigo fuskarta kamar kullum two colour da Maza su ke ganinta, dan duk kyanta ba sa gani, muninta su ke gani, gaishe shi tayi, ya amsa ya na basarwa, ya fice.
“a’a Inteesar ke ce, ai kuwa Hafsa za ta ji daɗi Yayarta ta zo mata suna”
Hajiya Kursum Uwar mai jego ta faɗa da fara’a.
Haka aka tattara a ka samo mota aka tafi gidan suna.
Tun kafin su isa, kiɗa ke tashi a layin,Mai jego da jaririyarta na tsakiyar fili ana ta rawa, jikin Inteesar har ɓari yake ta shiga fili, ai kuwa ta na sauka daga mota ta shige filin rawa,Mai jego na ganinta ta hau murna dan ta na sonta, a bikinta ma ita ta fidda ta kunya, yanda ta zage ta na rawa a filin wajen ba kunya ga Maza cike da kango, sosai ta burge shaiɗanun wajen.Gaisawa su ka yi aka fito da Maijego dan tarar maƙotansu.
Inteesar tace a sauwa mata waƙa, aka sa mata, waƙar Zee baby ai kuwa ta fara rawar ta samu wasu daga cikin ƴan mata da samarin wajen su ka tayata, yanda su ke komai a tare shi ya ƙawatar da wajen, sai girgiza nonuwa da ɗuwaiwai take ta yi sharkaf da gumi, ko abincin sunan ba ta samu ta ci ba.
D.J kuwa kira yake “Allah dai ya biya Hajiya Inteesar mai zamani, godiya muke da wannan abun arziki” la’asar aka kira, wasu manya su ka ce a kashe a je ayi sallah, kamar Inteesar ta dake su haka ta ji haushinsu.
Sannan ta shiga gidan sunan, tuwan shinkafa, da dambu da alale aka kawo mata, da pure water a raini ta kalli abinci ta ci dambun da alalen wai a lalura ta ɗauka za ta ga kaji da lemo, kowa ya na ƙoƙarin sallah amma banda Inteesar hakan ya sa aka ɗauka ko ta na fashin sallah ne, nan kuwa ba haka ba ne, duk lokacin da aka kira sallah, sai ta ji kasala ta rufeta ba ta iya tashi ta yi, har sai an idar sannan ta ke jin daɗi kuma ba za ta yi ba, sai ta, ta ra watarana ta rama duk ka wata rana kuma tayi optional.
“Ina mai gayya mai aiki, Maijego da babbar Yayarta Hajiya Inteesar a fito a yi mana kara a filin nan yauwa, a buɗe bakin purse a zazzaga mana eh,da eh ,ana yi muna jin daɗi” M.C ke ta faman banbaɗanci, Inteesar ta buɗe jakarta ganin kuɗi ta yi tasan saura ɗari kuɗin mota, amma yanzu ta ga sabbin ƴan hamsin-hamsin rafa guda.
“kai waye ya ba ni, ko Hafsat ce ta zuba min dan ta fidda ni kunya” murna ta hau yi da fara’a ai kuwa tuni ta koma fili da ƙarfinta, jakar ta zuge ta fara yi wa Maijego liƙi, tafi ake ta yi mata da kirari kamar wata shegiya a ƙasar, sai da ta ƙarar da kuɗin tas, sannan ta ɗora da cashewarta, har ƴan unguwarsu su ka fito za’a koma, Inteesar ba ta so ba, sai da aka fara kiran Magriba D.J ya tashi sannan ta shiga gidan, ta yi wa maijego sallama ta fito, wasu Matan su ka ce, sai sunyi sallah sai su tafi, wasu su ka ce in sunje gida sa yi, Inteesar na jerin waɗan da ba za suyi ba, tsabar rawa jikinta a mace ya ke, a haka su ka koma gida, ita kuma mai jego sai bayan suna da kwana biyu za ta tawo gida wanka.
Tun daga soro ta ke jiyo faɗan Baba, ” mtswww wannan anyi jarababban tsoho wallahi” kamar yanda ta fita ba addu’a haka ta shigo gidan ba addu’a, sallama ta yi,
Inna ta amsa, kun dawo?”
Inteesar tace” eh ta na gaishe ki, sannu da hutawa Baba”
Kamar yanda ta sani, ba amsawa zai yi ba hakance ta faru. Wanka ta shiga ga ba wuta banɗakin ya yi duhu ba ɗankwali take shiga bayi haka ta ke yin wankan cikin duhu, ji tayi kamar ana kallonta, duhu ya sa ba ta ga kowa ba, sharewa ta yi ta ƙarasa wankanta, Aljanin na ta kallonta ya na lashe baki sa bo da tsananin so da buƙatar da ya ke mata.
Zani ta ɗauro ta yi alwalarta ta rashin nutsuwa ta nufi ɗakinta ta yi sallar isha’i kaɗai ta fito taga yau shinkafa da wake Ummaa tayi, ci tayi sannan ta zauna a tsakar gidan dan rage dare, Ni’ima da Salma su ka zo kusa da ita za su bata labarin abinda ya faru a school ɗinsu, ta hantare su ” ku dalla ku tashi anan za ku dawo nan ku ishe ni da surutu mtswww” ta miƙe ta koma ɗakinta, dan tafi son zaman kaɗaici akan zama cikin mutane Kallo ta kunnan a ƴar keypad ɗinta ta na yi, bacci ne ya kwasheta.
MIJIN DARE da yake cikin ɗakin tun da su ka dawo su ke tare da shi, bayyana ya yi a zahiri, cikin mummunar siffarsa , girgiza ya yi ya zama Mutum sosai, ya nufi katifar Inteesar, nuni ya yi da hannunsa take komai na jikinta ya buɗe ta koma tsirara, shafata ya farayi, yana lasarta, tsotsar mata nono ya shiga yi, ya na jindaɗi, tamkar wani Mutum na gaske ya ke sarrafata, biye masa take yi, tana ba shi haɗin kai, gabanta ya nufa ya fara wasa da shi, gaba ɗaya ya gama burkita ta, sannan ya sami damar shiga jikinta, ƙara rikiɗa ya yi ya zama baƙin Aljani MIJIN DARE sannan ya fara haƙarta yi yake da zafi-zafi ya na jin daɗi, wani surutai take yi na zautuwa sosai ta ke zuba Aljani na shanye ni’imar da ke zuba, sai da ya gamsar da ita a matsayinta na wacce ya aura, sannan ya ɓace.
Yau ko bugun Inna ba ta ji ba, ganin rana tayi ta hasko mata ɗaki,yanda ta kwanta da kayanta haka ta ta shi, sai dai jin yanayin da ta sa ba ji aduk sanda ta yi mafarkin ana kusantar ta, miƙa ta yi gami da hamma ” hahhhhyyyyy mtswwww kai nagaji.
(ba hailala bare salatin annabi) ta fito tsakar gidan ganin ƙannenta a tsakar gidan, tace “ku ina Umma?”
Gaisheta su ka hau yi, “na ce muku ina Umma kun wani hau yi min shirme”
Imran wanda yake bai fi 14yrs ba yace” ta fita, ta tashe ki tace ki dafa mana shayi, Yaya ma ya tafi makaranta,Baba kuma ya tafi siyo kayan miya”
Da murna tace ” yau shayi tace za mu sha,ke Na’ima dan kutmar ubanki ba ki iya hura wutar ba da ba za ɗora ba, sai ni ki ke jira”
Jikin Na’ima na rawa ta nufi wajen murhun ta fara haɗa icce.
Imran yace” Umma fa ta hana ta tunda ta ƙone Aunty”
“zan tsinka maka mari, kai to ba za ka ɗora ba, ni ba bacci nake ba, sai ku jira nayi salla na gama abinda zanyi”
Imran da Na’ima dai su suka dafa shayin, sannan ta fito bayan ta yi sallarta ta farilla wato sallar safiya…………
WANE NE SHAMSUDEEN AL-HASSAN?
Alasawa family, family ne babba wanda su ke ji da dukiya, Alhassan Nuhu ɗaya daga cikin masu faɗa a ƙasar nan, ya na da Mata ɗaya Aliya(Mami) ta haifi Yara biyu Shams da Iftihal tunda ta haife shi, ba ta ƙara haihuwa ba sai da ya shekara goma sha biyu, Alhaji Al-Hassan ya dinga aure-aure amma duk matar da ta ga ta shekara shiru sai ta ce ta gaji, da alama ba shi da yawan ƴaƴa, wasu kuma su zauna sa bo da dukiya , idan ya mutu su ci gado, Alhaji Alhassan mutum ne mai imani da hangen nesa, hakan ya sa a hankali ya gane cikin matansa, babu wacce ta ke zaune da shi dan Allah sai Mami.
Duk da haka bai rabu da sauran Matan ba, ya na zaune da su a hakan, shekarun baya tun kafin haihuwar Iftihal, ya dawo daga Dubai da ya ke bai sanarwa Matan na shi zai dawo ba, ya sauka gidan Amaryarsa Munubiya, abin da ya ji shi ya yi sanadiyyar sakin su.
Ita da abokiyar zamanta Hajiya Umma, su na tattaunawa a kan hanyar da za’a yi a kashe Alhaji, hakan da ya ji ne yasa ya sake su, bayan ya haɗasu da hukuma, sai da su ka sha wahala su ka yi danasani mara amfani, tun daga lokacin ya haƙura da ƙarin aure ya zauna da Mami da ɗansa, Sham, bayan tsawon lokaci sai ta sami cikin Iftihal, murna a wannan family kamar me, haka ya dinga rabon saudiya a family domin nuna godiyarsa ga Allah (swt) da ya ba shi haihuwa, a karo na biyu.
Bayan haihuwa Iftihal kuma shikenan ba’a ƙara samun wani cikin ba yanzu Iftihal ta na shekara goma da bakwai, sun ta so cikin tarbiyya ta addini duk da dukiyarsa hakan bai sa an sangar ta su ba.
Shams Ustaz ne, dan majority ɗin dressing ɗin da ya ke ma, indai ba wai fita zaiyi taro ko wani abun ba, jallabiyya ce da hular nan ta taɓani kaji hadisi.Baya rabo da azumin Alhamis da Litinin duk ranakun satin nan to kuwa da azuminsa a baki, tunda ya fara girma ya faralantawa kansa wannan azumin.Shams Architect ne ya na zana gidaje, industries, companies dasauransu……….
DOMIN SAMUN CI GABAN LITTAFAN DUBA👇
https://arewabooks.com/u/rhussain