MIJIN DARE CHAPTER 5 BY R.HUSSAIN

MIJIN DARE CHAPTER 5 BY R.HUSSAIN

 

*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟

*بسم الله الرحمن الحيم*

PAID BOOK

 

__________A salin Alaramma Malam Kabiru mai almajiran haifaffan garin Sokoto ne, karatun allo ya kai shi Maiduguri inda ya samu ilimin addini a can, ci rana ya maida shi garin Yola inda anan ya yi aure ya ta da tsangayansa wacce ta ke cike da almajirai Alaramma ya na da Mata biyu, Baba Safiya da Baba Maimuna , ƴaƴa guda tara Baba Safiya ita ce uwargida ta na da Ƴaƴa biyar Aliyu (Assadullah) shi ne babba sai Khalid sai Rukayya sai Anisa sai auta a ɗakinsu shi ne Ibrahim, Baba Maimuna ta na da ƴaƴa guda huɗu, Zulaihat ita ce babba, sai Umar(ɗan Malam) sai Umma aimana sai Abdullahi, gidan addini ne dan Alaramma ya tsaya sosai akan iyalinsa, amma Baba Maimuna amaryar Malam Kabiru ta na kishi sosai da Baba Safiya sa bo da gani ta ke tunda ƴaƴanta ne manya a gidan kuma ta fita da Namiji guda ɗaya shi ne take kishi da Safiya, Baba Safiya ta kasance Mace ce mai matuƙar haƙura da kamun kai, dan ko lokacin da Malam zai auri Maimuna ba ta tada hankalinta ba, lokacin ƴaƴanta biyu Asadullah da Khalid, aka auro Maimuna a tare su ka sami cikin su Ruƙayya da Zulaihat, haka Malam Kabiru ya yi wa Maimuna hidima sosai wai sa bo da ita haihuwar fari ce, Baba Safiya ta kauda kanta akan komai har Allah ya sa yaransu su ka girma, yawan nuna wa ƴaƴanta so da Maimuna ta ke yi ne ya je fa Umar(ɗan Malam) harkar shaye-shaye, asalin sunan ɗan Malam kuwa ya samo asali ne wajen Babarsa Maimuna ta na haifan Namiji ta sa masu suna ɗan Malam,a gaban Baba Safiya ta ke masa rawa ta na saɓa shi, ta na yarwa da Baba Safiya magana, sai dai Baba Safiya tayi murmushi dan ita ba ta da ga abun magana akan ɗa Namiji ba, ita da ta ke da guda biyu ma (a lokacin) da Baba Safiya ta haifi Ruƙayya murna wajen Maimuna har ta kasa ɓuya kowa sai ta ce masa ai Mace ta haifa haka tai ta nuna murna, ita ma sai Allah ya kuma bata Mace ta haifi Umma aimana, ranar har kuka Maimuna tayi sa bo da baƙinciki Namiji ta so haifa,Baba Safiya ta kuma haifar Mace, Anisa nan ma Maimuna tayi murna, ita kuma ta haifi Abdullahi, kar kaga murna wajen Maimuna ta kamo Safiya ba ta fita ba, anan ne sai mahaifarta ta samu matsala sa bo da yawan shan kayan mata da ta ke, aka juyar da mahaifarta, ta yi kuka sosai haka ta haƙura sai Baba Safiya ta samu ciki babu abinda Maimuna ba ta yi ba dan ganin cikin nan ya zube amma Allah ya ƙaddara dole sai Ibrahim mu’azzam ya zo duniya, ranar da aka haife shi kuwa sai da Maimuna ta nuna baƙin cikinta a fili, yau da gobe ya sa take yiwa ƴaƴanta huɗubar banza akan Baba Safiya, kowa ya na tsoron Yaya Asad a gidan dan ba ya wasa da kowa, ga tarin Ilimi da Allah ya ba shi, duk kan ƴaƴan Malam su na karatun boko, a yanzu haka Asad ya na karantar engineering, Haidar kuma ya na karanta mass.com Zulaihat ta yi aure, ansa ranar Ruƙayya da babban almajirin Malam Yunus, Maimuna sai murna ta ke za’a aurar da Ruƙayya ga Almajiri, Baba Safiya da su Asad sunyi murna da hakan dan Yunus mutumin kirki ne, asalinsa ba ɗan ƙasar nan ba ne kawo shi karatu wasu su ka yi tun ya na ƙarami bai san kowa na sa ba sai Malaminsa malam Kabiru, duk gidan Alhamdulillah ƴaƴan Malam a nutse su ke sai dai Umar(ɗan malam) wanda ya fita zakka a gidan Malam Kabiru…….

 

* * *
Alhaji Alhassan ne zaune a garden ɗin gidansa ya na karanta jarida idanusa sanye da medical glass, Iftihal ƴarsa ce ta fito hannunta ɗauke da ƙumdatul-ahkam sanye ta ke da hijab har ƙasa onion colour da carpet ƙarami a hannunta, ” sannu da hutawa Daddy” ta faɗa bayan ta yi sallama, cikin kulawa Alhaji Alhasan ya amsa ya na rufe jaridar hannusa ya ce” Faɗimatu kin fito, ina Malam ɗin kuma?” Iftihal ta ce” yau bai sami daman zuwa ba kuma ba na son zama ba’a ƙara min ba, shi ne na zo ka biya min dan Allah” ta faɗa ta na marairaicewa,Murmushi Alhaji Alhasan ya yi ya ce” to yau kenan ba Malam, babu Yayanki shi ne aka tawo wajena ko” dariya Yarinyar ta yi wanda ya bayyanar da asalin kyanta ta na rufe fuska, tambayarta ya yi ina ne ƙarin faɗa masa ta yi ya juya baki ya koma larabci ba tare da ya kalla ba ya fara biya mata hadisin, tare da bayani duk cikin harshen larabci, sai da ya gama sannan ya tambayeta ta gane, ta amsa da eh ta biya tare da bayani iya fahimtarta.
Sannan ta yi masa godiya ta koma ciki.
Mami ce ke waya da SHAMS wanda ya je meeting garin Yola, sanar da ita ya yi komai ya kammala na buɗe company’nsa na zane-zane amma garin ya yi masa kyau ba kaɗan ba, shiyasa zai kwana biyu kafin ya dawo gida.
Fatan alkhairi tayi masa sannan su ka yi sallama.

 

Tunda SHAMS ya wuce a mota ya ga yanda wani matashin saurayi ya ke tafiya a ƙasa a wahale da gani daga makaranta ya ke ya tausaya masa, har binsa da kallon da ya yi ya gani ta mirro’n motarsa, zuciyarsa ce ta cika da tausayin Yaron, sai da ya yi nisa ya dawo dan ganin ko zai ganshi amma bai ganshi ba haka ya juya ya nufi masaukinsa, tunanin yanda Unguwar da ya bi yake, duk takalawa ne a area shima goslow ne ya sa ya yanke hanya ya ɓillo ta nan, sai da ya yi waya da Mami sannan tunanin ya sake shi, ya tashi ya yi wanka ya yi sallar isha’i ya fara duba ayyukan da ke wakana game da sabon company’nsa da zai buɗe.

 

* * *
Ana ta shi daga meeting Ibrahim ya zo gurin Baba Ayuba mai kayan miya, daga cikin motar su ka gaisa, Baba Ayuba sai washe baki ya ke dan yasan wanda ya ke masa alkhairi ne ya zo, ya ce” Alhaji mai za’a sa?”
Ibrahim ya ce” ba komai Baba daman a ma’aikatarmu ne aka ne neman massenger wanda zai dinga yiwa staffs ɗan aike-aike shi ne na ce ko kana da sha’awa na kai ka, dan sabon waje ne, za ka samu alkhairi a wajen”
Baba Ayuba ya yi shiru na seconds sannan ya ce” to Alhaji gaskiya yanzu duniya abun tsoro ce, sai nayi shawara” Ibrahim ya ce” gaskiya ne Baba amma wallahi ba ni da niyyar cutar da kai, na zo maka ne da alkhairi amma shawara abu ne mai kyau, duk abinda ka yanke ina sauraron ka,nagode” ya ciro 2k ya ba shi ya ce ” ga wannan” jiki na rawa Baba Ayuba ya karɓa ya na ta godiya. Ibrahim ya nufi gidansa.

Khaleesat ta sga wankant ta yi girkinta ita kaɗai ta ci tana kwance ta na chatting ta ji dawowar Abban Ansar, haushi ta ji dan ta tsani ya dawo gidanma, parking ya yi ya shige ciki ya na sallama “assalamu alaikum” a daƙile Khaleesat ta amsa” waalekumussalam, sannu da zuwa” ta ɗauke kanta ko kallo bai ishe ta ba,Ibrahim ya amsa da “yauwa ya gidan?” banza ta yi masa ta ci gaba da chatting ɗinta.
Ansar ya duba ya na kwance ya na bacci akan kujerar falon cikin katifansa na Yara, wucewa ciki ya yi ya watsa ruwa, ya fito ya nufi masallaci, sai da ya yi sallah ya dawo ya nufi dinning dan cin abinci, ko ta yi masa yau.

Wayam ya gani babu komai, juyawa ya yi ya ce” dear ina abincina?” Khalesat ta ce “banyi ba” Ibrahim da ransa ya fara ɓaci ya ce” ko me ya sa?” Khaleesat ta ce “banyi ra’ayi ba” ta tashi ta barshi tsaye a wajen……..

 

DOMIN KARANTA CI GABA DUBA 👇

https://arewabooks.com/u/rhussain

*Zinariya ce✍🏻*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE