MIJIN YARINYA COMPLETE
MIJIN YARINYA COMPLETE
Dedicated to*******
*TUKWICI*
_Wannan littafin tukwici ne gareki mahaifiyata..innasanki sosai Allah ya qara miki tsawanrai mai albarka..💋_
*GARGADI*
🎀🎈Zaune mumy take a palo Irfan yayi sallama ya shigo palon fuskarsa cike da fara’a..haka zalika mumy ma dake zaune ta amsa tana murmushi..
Irfan(Abdulrahman kabir) saurayine fari daidai kuma kyakyawa meji da kansa.. Mahaifansa dikka fulani ne Dan hk dikkansu daga shi har kanwar tasa kyawawane…
Zama yayi kusa da ita tare da fuzar da iskan dake bakinsa yana fadin
“Am so tired mum”
Murmushi tayi tana
“Nace kayi aure kaqi ai by kafiso kayita zama hk ynxu hk ita khaleesat din tayi auren ta ma ta manta dakai kaima sekayi hkn kawai start afresh son”
Bata rai yayi yana fadin
“Mum plxx Wallahi banason zancen ni bazanyi auren ba”
Hade rai ita ma tayi tana fadin
“Aikuwa za kasha mamaki na indai bazaka kawomin wacce zaka aura ba toh zannemo acikin yan uwana”
Da sauri ya juyo ya kalleta yana fadin
“Wat!!! Haba mum a village fa kenan”
Da mamaki take kallonsa tana fadin
“Lallai Irfan toh uban naka ma daga qauye yake kan yayi kudin kajimin yaro”
Miqewa yayi ya nufi hanyar stairs Dan zuwa dakinsa yana fadin
“Nidai bazan zauna da yar qauye ba wallahi sedai kizauna da ita”
“Iye I can see kai badaga qauyen kake ba kenan”
Shigewarsa yayi daki ita ko kanwarsa suhaima dake dakinta dik tana jinsu ta fitoh tana fadin
“Kema dai mum kiga yanda bross yake ji da kansa dangaye kice zaki basa yarqauye”
“Toh ai nima yar qauyence kan ubanku ya auren”
Dariya suhaima tayi tana fadin
“Ai dane wannan mum buh for nw ba’a haka ya Irfan fa cewa yayi shi ko zeyi aure baze aure YARINYA ba ba wacce take da degree ze aura”
Tsaki mum tayi tana fadin
“Yuh guys are not serious bazai auromin Mara kunya ba Wallahi tayi degree din agidan sa yanda kema agidanki zakiyi”
Turo baki suhaima tayi ta miqe ta nufi hanyar qofa..
Tsaki mum tayi tana fadin
*ASALINSU*
Alhaji kabir Dan garin gombe ne kamar yadda matarsa haj.maryam itama yar cen ce.. Yaransu Uku Hamra wacce Allah yayi mata rasuwa sai Irfan da kuma qanwarsa suhaima wacce 2016 ta kammala ss3 dinta shikuwa Irfan SOJA ne me ji dakansa budurwarsa daya khaleesat ya sota sosai amma daga baya iyayenta suka rabashi da ita suka bama wani Alhaji ita..
Bakadan hakan ya batama ibrahim rai ba amma ba yanda ya iya dole ya hakura amma acewar sa ba zeyi aure…
“Maryam ya gidan inna Abdulrahman din yake?”
Acewar innah
Murmushi mum tayi tana fadin
“Yau yana da aiki ne shiyasa be biyomu ba”
Kallon suhaima inna tayi tana fadin
Tabe baki innah tayi tana fadin
“Suhaima?”
Dariya dik sukayi..
“Kaji yar tsohuwarnan zata batan suna”
“Ke dallah ni ban iya fada ba khadija nasanki dashi”
Hira suke sosai nan mum take bama innah labarin auren suhaima suna cikin hk ne wata yarinya yar shekara goma ta shigo gidan tana kuka tana Jan majina sai Sosa kai takeyi…
“Innah innah kinga abbati yacimin awarata yaqi ban gudin ko?”
Sake baki sukayi suna kallonta..
Jawota innah tayi ta dorata kan qafarta tana fadin
“Haba umimi ta nawane kudin bar kuka hakan”
Tana Jan majina tana kuka tana sosai kai tasoma fadin
“Gomace wallahi se an biyani”
Gomar innah ta Ciro ta bata kafin ta miqe zata fice sai inna ta dakatar da ita tana fadin
“Ummi bakiga uwartaki bane kigaidata ga kuma yarki nan”
Inna wuni kawai tace musu tayi ficewarta..
“Ohh Ashe baki ganeta ba…yar marigayiya zulaice..Aisha ce fa”
Da mamaki mum ta soma fadin
“Wai Aishar yaya zulai ce?amma tayi saurin girma”
“Murmushi inna tayi tana fadin nan shekarar ta goma..”
( *Yaya zulai itama yar innah ce watoh yayar mum*)
“Amma innah aikin bata Ummi dayawa wallahi”
“Toh maryama ba dole ba itakadai zulai ta rasu tabar mana dole amata dik abinda take so”
Itako suhaima agarinan ba Wanda ke bata dariya irin umimi hakanan zata tsokaneta Dan tayi dariya…
Aikuwa suna isa kano suka iske Irfan agida nan fa suhaima ta kama basa labarin umimi shi kansa sanda yayi dariya yana kallon mum yana fadin
“Kinga halin yan qauye ko ..”
Toilet ya fada yayi wanka ya fitoh..can Palo kuwa tam bayar mum suke inna Irfan
“Kunnan zaune zaku gansa ai”
Shine amsar da mum take basu..aikuwa ya bata lkci yana shiryadaga bisani ya fitoh cikin taqama yana tafiyarsa…
Yana fitowa yana qoqarin rufe qofar dakinsa yaji an taka masa qafa da sauri ya juya yana kallon wacece?
Umimi ce kasancewar shi bama saninta yayi ba..
“Ke baki da hankali ne”
“Akasuwa ake siyarwa meka siya ka kawomin”
Tana fadan haka taja hanci tare da Sosa kai ta masa gatsine tayi gaba abinta shiko binta da kallo yayi daga bisani yayi tsaki aransa yana fadin
“Inbanda qaddara ma me akeyi da yan kauye mstw..so childish”
Washe baki innah tayi tana fadin
“Ahhh wannan miji nawa dakyau yake lallai yar leleta tayi sa’ar miji”
Guda aka kumayi ya miqe mum na kiransa amma ina ya fice yana kawai qofa yana banmami aiko sukai cinkaro shida umimi wannan karon ya ganeta fusata yayi ya dauketa da mari ya kayi wucewarsa itako kuka tasa tazo tana fadama innah..
“Innah kinga wancen mutumin ya dakeni ko haka kurin”
“Tohh wanne mutumi?”
Haka akayi ta shagalin biki
Kwanansu hudu agidan kafin suka fara tatattare yanasu yanasu suka koma gida bayan ankai Amarya .
“Kiyi hkr innah insha Allahu baza akuma ba”
Daqyar aka shawo kan innah tayarda umimi ta zauna gun mum..itako umimi ko a kwalar rigarta Dan taga gidan babbane Dan hk tana murna aka tafi aka barta anan…
*Night*
Zaune mum take umimi na gefenta suna kallo se dariya umimi takeyi..motar Irfan ce ta shigo harabar gidan sanye Irfan yake cikin kakinsa na sojoji ya fitoh daga motar tasa ciki ya nufa da sallamarsa..
Cike da fara’a mum ta amsa..da mamaki yaga umimi azaune
“Mum dama basu tafi bane?”
“No sun tafi she will be leaving wit us for now”
Umimi dake kallonsa tasha jinin jikinta dan aynxu kam tsoransa takeji sosai…
“Ke Ummi baki ga yayan ki bane ko gaidasa”
Kallonsa Ummi tayi da gefen ido tana fadin
“Inna kwana”
Tsaki yayi ya wuce dakinsa….
“Ke kidinga yin abu da hankali mana da daddare nan zaki wani ce inna kwana?”
Gyada kai kawai takeyi ta cigaba da dariyarta tana kallo…
Daddare misalin karfe 9 Kwance Irfan yake yana chatting awayarsa daga bisani ya fita cikin gallary din wayarsa ya shiga kan hoton khaleesat yajima yahaka yana tunanin irin soyyar da suka sha..
Ihu yaji yayi firgigit ya miqe zaune..Can ya kuma jin wani ihun fita yayi da gudu daga daki lokaci daya suka iso palo shida mum wani ihun suka kuma ji acikin nan suka hanzarta ..
“Ashanane yaqonana”
Cikin shesheqar kuka yasoma ba mum ansa tana Jan hanci..
“Yooohhh ni nagaji da cin irin abincinku tuwo nakeso Wallahi”😫
Tana fadan haka ta fashe da kuka…takaicine ya cika irfan
” village girl kawai”
🎀🎈Har Irfan ya shiga daki yana jiyo saurin kukan Ummi sai tsaki yakeyi har barci yadaukesa..
“Mum plxx stop dis girl let her eat slowly nd mature”
Murmushi mum tayi
“Son kanasa ma ‘yata idofa kindly eat yuhr own”
Harara kawai ya ke watsawa Ummi..itama tana kallonsa..
“Wannan yarinyar jikinta be gaya mata bane shiyasa take rainani amma zatayi bayani”
Yafada aransa muryar mum ya jiyo tana fadin
“Yauwa Abban siyama..plxx why not amaida Ummi school”
“Cab aikuwa asarar kudinku zakuyi”
Acewar irfan Wanda yana kaiwanan ya miqe ya fice abunsa…
Mum ko tadage sai an maida Ummi skul Dan haka dad yace akaita makarantar da suhaima tayi su mata interview..
Dadi ya kama mum sosai tayima dad godiya…Akan washe gari zata kaita…
Misalin karfe 8 irfan ya shigo gida ya paka motarsa tinda ga waje yake jiyo wari yarasa na meye ..
Yana bude kofar palon su warin ya gumosa sosai …mum ya gani zaune itama toshe da hanci..
“Mum wats dis smell all about?”
“Sory Ummi ce take tuwo shine tasa daddawa guda goma acikin miya”
“Wat!!!! Mum its as if its burning”
Da sauri mum ta miqe tayi kitchen shima yabi bayan mum riiii…
Ummi suka tarar tana Tari tana kwashe tuwon a kwana…tuwon masara ne amma dik ya canja kamaninsa haka zalika miyar ma sai qauri kawai ke tashi..
“Haba Ummi ke bakya jin magana Wallahi nace ki bari merry(yar aikin gidan) ta miki amma kinqi ji ynxu yanda kika bata ko inna..kizubar dashi amiki wani”
Acewar mum…da sauri ta kalli mum tana fadin
“Cab bazata sabuba nidai kayana zanci”
Murmushin mugun Irfan yayi ya kalli merry yana fadin
“Heyyy clear dis mess plxxx”
OK merry ta amsa dashi ta shiga gyara wurin…
Palo suka tafi yasa Ummi ta zauna Dan haka shima yasamu gu ya zauna..
Mum turaren wuta da room freshner ta shiga sama palon ba arziki kamar annan akwai da huwar…
“Se kincinye shi tass Wallahi koki daku ynxu”
gatsina tayi masa tana fadin
“Toh da ca nayi bazancinye ba?badan tayi nake nema ba”
Tsaki yayi ..
“Dallah mallama rufe bakinki kici”
Shiru tayi tana ci dik Dan karya raina ta amma ita kanta tagane abincinan beyi ba ko kadan…ga yaji gashi ya qone ga magi yayi yawa ga daddawa ma haka…
Watoh yajin dake ciki ne yafara displilata idanun sun kasa sunyi jaaaa..ajiye kwanon tayi tana kallonsa da idanunta da sukai jaaa kamar zatayi kuka…
Sannan ta soma duban ta inna zata ga mum ta ceceta…
“Dau kwanon maza kici kojikinki yayi tsaki”
“Ruuuwwwwaaaa”
Tafada muryar na rawa tana niyar kuka..harara ya galla mata ya kira merry ta kawo mata..
Abincin nan cinsa kwai take tafara hawaye daga bisani tafashe da kuka..fitowa mum tayi daga daki ta bama Irfan hakuri daqyar Irfan ya hakura ya qyaleta ta kuka ta bar gun sanda suka kai qofar dakin mum ta juyo tana fadin
“Allah ya isa”
Da sauri mum ta janyeta tana huge mata baki..nanfa mum ta shiga mata fada..kuma ta sanar mata washe gari ta shirya zasu makaranta…
Irfan ko daki ya shiga ransa bace ace *YARINYA* kamar Ummi tace masa Allah ya isa …
Washe gari gari da safe Ummi ta shirya cikin farinciki da zumudi tana fitowa tayi cinkaro da Irfan kallon da yamata ne yasa tayi qoqarin juyawa tsawa ya daka mata
“Keee zonan”
Jikinta na rawa ta nufisa riqe kunenta yayi
“Sauran inkinje kiyi qauyanci kiba mum kunya zaki gane kurenki”
Tsaki yayi ya wuce..itama tsaki tayi tana fadin
“Yaaaa yaaa yaaa wahalallale”
Tafiyarta tayi gun mum..
Suna zuwa skul din mum ta roqesu akan su dauketa a jss3 saboda tayi girma da jss1 daqyar suka yarda amma da yarjejeniyar mum zata sama mata lesson teacher a gida..
Aranar mum ta biya kudin komai ta bari Ummi a mkrntar…
Anna tashinsu mum ta aika driver ya daukota..tana shigo taga motar ya irfan tsaki tayi ta nufi gun motar ta hau leqawa tana murmushi
“Ashe dai motar tasa Nada kyau”
Ta jima tana kallo se daga bisani ta miqe har tayi kana sena dawo ta Ciro rezar dake Jakarta da mun ta saimata sabuwa aikuwa tahau kartar motar..
🎀🎈Irfan tagani a tsaye ya hade rai gaba daya tasha jinin jikinta Dan haka ta shiga qoqarin bata masa rai..
Riqota yayi suka shige ciki kanta ankare ta saukar belt ajikinta..dukanta ya shiga yi ta ko inna tana ihu tana neman agaji kamar daga sama mum dake bacci tajiyo ihunta aikuwa ta miqe tare day in addu’a kafin ta sauko da gado ta fitoh..
“Subhannallah mezan gani haka ka qara dukanta ranka saiya baci”
*Night*
Karfe 9 Saura irfan ya shigo gida mum na zaune a Palo da fara’arsa ya shiga ya gaidata amma shiru bata ansa ba…
“Irfan ka fita daga idona me Ummi ta maka zaka mata wannan dukan?”
“Kiyi hkr mum motatafa taje tana karta da rexa a sorry”
“Wat Eva it takes bekata ka mata wannan dukan ba”..
Shiru yayi bece komai ba..
” kaii Irfan in fadama tun wuri kusasanta kanku kaifa ita saboda ita zan aura ma”
Da sauri ya dago ya kalli mum
“Mum aure ko..mum wannan ai yarinyace “
“Toh meye laifin yarinyar?”.
Miqewa yayi yana bubuni
” no mum I can’t kawai salon ta rainani adinga cemin *MIJIN YARINYA*🤣”
“Oho kaikajiyo koma mijin tsohuwa ne ni bata damen ba ka gaggauta zuwa bata hakuri”
Dakinsa ya shige ransa a bace..hanunsa gaba daya rawa yake idanunsa sunyi jawur ya Ciro tabar dake cikin kwalli yasa lighter ya kunna ya hau zuqa yanayi yana rufe idanunsa saboda wani iri yakeyi gaba daya jijiyoyin wayarsa sun tashi…
“Why mum!!!! Whyyyyyy!!!!!”
Khaleesat ce ta fada masa arai Dan haka ya fara hawaye masu cin rai murmushin ta kawai yake gani da irin gwabar da takeyi in yanuna masa ranta ya baci….
Yannan zaune a haka har qarfe goma yaji shigowar dad Dan hk bayan 20min da shigowar dad ya miqe yaje ya watsa ruwa kafin ya sauya kaya ya nufi gun dad…
Da sallamarsa ya shiga dakin dad ya amsa.. Cikin sa’a yayi katari da mum batannan taba dakin Ummi..
“SOn ya akayi ne any problem?
Gyada kai irfan yayi yashiga korowa dad lbrn yanda sukai da mum…da mamaki se ganin dad yayi yana murmushi…
” Son kayi Addua Allah yasa hakanne mafi alheri tinda kaqi yin aure bamu da choice din da ya wuce haka… Kawai kaje kusasanta is d best solution”
Cikin sanyin jiki irfan ya bar dakin ranar haka ya kwana ransa abace sosai…
Mum ko can data shiga dakin Ummi ta sameta a kwance…
“Ummi ki shiga hankalinki da girmanki amma kiyi ta abubuwa kamar YARINYA yaza kayi kije ki kartar masa Mota da reza ..inya shigo ki gaggauta basa hakuri kinji ko?”
*2days later*
Dakin irfan mum ta kwankwasa kafin ya bude mata..
“Son kayi sauri ka shirya kar Ummi tayi latti”..
Zaro ido yayi yana fadin
” mum wat did u mean”
“Kai zaka kaita makaranta koma ince zaka dinga kaita ataqaice”
. ba yanda ya iya dole ya kai Ummi kafin ya wuce skul din…
Yafito kenan Palo ya hango Ummi ta fitoh hijab dinta a hannu tana gyara Dan kwalki uniform din ya mata kyau taba hangosa ta hararesa tare da juyawa tana gyara dankwalli sanda tasa hijab kafin ta juyo …
Tsaki yaji aransa yana fadin
“Foolish girl kome zan gani da zata boyemin..mtsw”
Sallama yama su mum kafin ya nufi motarsa gidan bata ta nufa zata bude
Ba musu ta shiga gaba…bakin gate din skul ya sauketa ta shige skul din…
Kawayen da tayi washe garin fara zuwanta skul ne ta iske su a assembly sufa fara hira Iklas da hanan…
Bayan sungama assembly dinsu ne suka nufi class
“Ke wai waye wannan sojan me kaki dinan da yake saukeki a Mota?”
A cewar hanan…shiru tayi Dan ta gano wasuke nufi..
Caraf hanan ta soma fadin
Gajiya tayi da surutunsu da yadda suke zuzuta irfan din
🎀🎈Irfan ka saurareni kaji mezan fada ma..dik shirya shiryen da zakayi kaje kayisa Ummi nakammalla Ss3 za ai aurenku kamar yadda nama suhaima tinda ynxu Ummi ta shiga Ss1″
“Mum Dan Allah kibari Wallahi ni banason Ummi me zanyi da yarinyarnan?”
“Ni ba dogon surutu nake buqata ba..ummice dai seka aure ta Dan hk ka tashi ka bani wuri”
Qoqarin mgn yasoma yi ta daga masa hannu..shiru yayi ya miqe ya nufi gate daidai nan Ummi ta shigo tana tafe tana cin awara..takaici ne yacikasa kamar ya fasa ihu ynxu wannan yarinyar akeso ya aura ji ta batada ko kamun kai…
Tsaki tazo ta wucesa ko kallon banza be isheta ba balle ta gaishesa…Tafiyar da takeyi ne yasa ya sake baki yana kallonta da mamaki…
Taku take kamar bazata taka qasa ba tana ran gwada…harya wucesa
“Ke zonan”
Tsaya wa tayi ta juyo cikin shagwaba tana fadin
“Nifa yau nagaji ko kulaka banyi ba ka kyaleni”
Da mamaki yake kallonta ya mata allama da ahannu ta tafi wani salon tafiyar ta canja kawai yayi tsaki aransa yana fadin ko ubanwama zatama rangwada ta birgesa…tsaki yayi ya fice zuwa masallaci kasancewar kiran sallahr la’asar dayakeji..
Zaune Irfan yake adakinsa yarasa meke masa dadi dabara ce ta fado masa akan yaje yasamu Ummi ya mata mgn tacema mum bakason auren..
Miqewa yayi ya tafi jikin corridor din da zata sadasa da dakin Ummi ya soma kiranta..
Miqewa tayi ta fitoh kanta bako dan kwalli tana turo baki..
“Gani”.
” ke dallah ki nutsu ki saurareni abinda zan fada miki”
“Innaji”
Mamaki mgnrsa ce ta cikasa sosai
“Dallah rufamin baki stupid kawai ko a kafa aka dauramin ke kunceki zanyi jibeki fa”..
Washe gari
Yau kamar kullun Ummi tagama shiryawa zuwa mkrnta fitowa yatayi tana tafiya cikin qasaita sallama tama mum kafin ta nufi motar Irfan…
Tana zuwa ta bude kofar gidan gaba kamar kullun inda take zama gani tayi ya murtuke fuska aranta tana fadin
“Toh masifaffe yau kadanyi kyau”
Zama tayi ya yada motar sadda sukai Rabin tafiya seya Ciro tissue ya miqa mata…
“Goge Jan bakin da kinasa”
Turo baki tayi tana bunbuni
“Nidai bakason irin haka Wallahi”
Tsawa ya daka mata aikuwa ta shiga goge Jan bakin dake bakinta…
Suna isa qofar skul ta sauka fuuu ta shige ko turo qofar batayi ba sedai ya rufe da kansa…
. zaune suke lkcin break suna hira
Iklas ce tasoma fadin
“Yar uwa yau naga sojana naki yai kyau fa”
Murmushi tayi ta kasa idanu tana fadin
“Kunga kubar zugani dayawa batan rai yayi yauma kawai yasa na goge Jan bakina”..
Da sauri ta miqe tana juyi
“Nidin ba wasa bace”
(Ni afreen nace su Ummi anqaro iskanci)
ynxu kam Ummi na Ss2…Ya Irfan kuwa yau watansa 5 dayin tafiya kasancewar an posting dinsa abuja yana can da aiki..ba karamin haushi Ummi taji ba Dan ynxu kewarsa takeyi kullun setama su iklas da hanan Mota..
Bayan tafiyarsa mum ta siya mata tab numbern ya irfan ta dauka a wayar mum.. tasa iklas ta kawo mata layi banda Wanda mum ta bata watsap ta bude dashi tama Irfan sallama..
*Fatyafreen1*
afreennovelseries.blogspot.com
*Night*
🎀🎈Kwance take akan gado tana chatting message din Irfan tagani da sauri ta be gurin message din sallamar kawai ya amsa..
Nan suka fara chat suna gaisawa amma bata sanar mishi cewar ita bace har bacci ya dauketa suna abu daya..
*Morning*
“Ahhh toh Shknan Allah yakaimu goben Son’
ameen ya amsa dashi sukai sallama ta latse wayar…
Amsawa tayi da toh cikin murna ta nufi dakinta ta canjo..
Yanzukam Ummi yan Ss2 an waye sosai amma harynxu tsayinta na ayanda taje bata qaru ba mum na siyamata dik abinda take buqata wani lkcin ma kan ta tmby an mata…
Tan shiryowa suka fice zuwa wani boutique dake kusa Riga da wanduna da kuma skirt ta zauna ganin haka yasa mum taqara mata da doguwar riga guda daya suka zama shida..murna kawai takeyi har suka isa gida..
Tana zuwa tabayardasu wajan wanki aka wanke mata..
“Yauwa Ummi gobefa irfan ze dawo”
“Gobe!!wayyoh shikenan zedawo ya hanani sukuni”
Acewar Ummi wacce ko cikin ranta fal yake da farinciki
“Kefa bakida wayo wallahi wani lkcin senaga kamar ynxu kinyi hnkli inkikai wani shirmen kuma kamar na makeke”
Dariya Ummi tayi ta shige daki tana murna su iklas takira ta basu lbrn ai sojanta ze dawo nanfa suka ita hira suka rabu akan washe gari zasu hadu a skul.
Illai washe gari da safe ta shirya mum taso Ummi ta hkra da zuwa mkrntar amma taqi haka tayi wucewarta..
“Ke kibari murna nake nasan ynxu yaqaro kyau”
“Hhh kema seki qara daukan wanka kisace zuciyarsa”
Dariya sukai dikkansu
“Ni abinda yake nasani dashi akwai sa da fada da yawan mita wallahi”
Tana fadan haka malaminsu ya juyo Dan hk dik suka nutsu suka maida dubansu garesa…
” ya gajiya hanya son”
“Alhmdulh mum gsky nayi kewar girkinki”
“Hhh son kenan baka ce inna Ummi ba”..
Batarai yayi yana fadin
” toh innaga Ummi mum mezan mata ne?”
“Haba Irfan ykmt ka tsaya kufahimci junan ku kasan bazan canja zancena ba Dan seka auri ummi”
Shiru irfan yayi be kuma cewa komai ba mum ko ta miqe abunta.. Yana gama cin abincin sa ya shige daki watsa ruwa yayi ya kwanta abinsa..
Karfe 3 saura Ummi tashigo gidan dakin mum ta nufa ta isketa tana kallo ta gaidata ..
Toh kawai tace ta miqe ta nufi nata dakin wanka tayi tasa daya daga cikin Riga da wandon da mum ta sai mata fitowa tayi ta nufi kitchen Dan yinwa da takeji flask din abinci tagani a ajiye
“Mery abincin waye wannan?”
“Sauran wanda Oga irfan ya rage ne”
Murmushi tayi ta dauko kular da plate harta zauna sekuma tamiqe tadauko nutrimilk a fridge Palo ta nufa da kular ta zauna qasa dirshen ta zuba abincin remote ta dauka tasa mbc3 tama manta shaf da irfan yadawo da har mum tace taje ta masa sannu da zuwa…
Karar TV dince ta tashesa tsabar jin haushi ko kayan barcinsa be sauya ba ya fitoh fuuuu kadan kadan Dan yasan baze wuce Ummi ba yana isowa ya ganta zaune ko ajikinta tabama kallo himma da mamaki yake kallonta da irin shigar datayi dariya ma ta basa Dan har ynxu kallon yar qauye kuma karamar yarinya yake mata..
“Keeeeee”!!!.
Ya daka mata tsawa firgigi ta juyo ganinsa cikin kayan barci yasa tayi ihu ta miqe ts juya ta masa baya shiko sake baki yayi yana kallonta
🎀🎈”Toh wai me yarinyarnan take nufi tayi hankali kenan?”
Tsaki yayi yadauki rmt din yarage volume din ya juya abinsa sanda tajiyo karar rufe qofar dakinsa tukunna ta juyo tana tsaki .
“Kai kullun bakada aikinyi sai masifa mtsw”!!
Zama tayi kawai tayi saurin janyo wayarta ta kunna data..
Messages dik sun shigo amma bata ga na ya irfan ba..dubawa tayi ta gansa online saki tayi tsaki seta soma rubutu
” hmm bazaka kulani ba?”
Ba’afi minti 3 ba ya dawo mata da reply
“Sory nagajine nayi tafiya ne shiyasa kuma bacci nakeji..
Daga wannan reply din taga ya sauka hakan ya bata mata rai ta kwanta tana chatting dinta jin bacci yasoma dibanta yasa ta kwashe dikka abubuwan dake kawo tamaidasa mazauninsa ta nufi dakinta…
Washe gari tinda safe ta fitoh ta nufi dakin ya irfan kwankwasawa tayi tana fadin
“Ya irfan nagama kazo kakaini skul”
“Mum yau ya Irfan ne zekaini mkrnta ko?”
“Ehmana tinda yadawo inkinaso a shknan”
Murmushi tayi ta tana fadin kanaso miqewa mum tayi tabi bayan mum tana murmushi sai tafiyar rangwada takeyi..
Suna zuwa Palo mum ta soma kiransa fitowa yayi cikin shirinsa..kallonsa ta tsayayi saboda kyandaya mata sewani fari take da idanu
“Yauwa tinda kashirya sekazo ka kaita”
“Haba mum wai driver dinta na koma ne”
“In baka koma driver ba zaka koma mijinta”
Kallonsa ta dingayi tana gwalo tana dariya shiko ransa a bace yake..
Kashe murya tayi tana fadin
“Cab mum inna auresa aiseya kashe miki ni kuma yace ni yarinya ce”
“Kyalesa Ummi seya koma mijin yarinya ai”
“Allah yasauwake nazama mijin yarinya”
Yana fadan hk ya fice tama mum sallama tabi bayansa suna isa jikin motar se wani karairaya takeyi shiko yasake baki yana kallonta sanda takai jikin motar ya kalla mata harara yayi tsaki kafin ya shige itama shiga tayi ya kalleta yauma tissue ya miqo mata
“Goge Jan bakinan da baqin da kinada a ido”
“Haba ya irfan meyasa kkmin haka ne”
Karban tissue din tayi tana kuka tana gogewa har suka isa..fuuuuu tafice daga motar yayi tsaki yaja yayi gaba abinsa..
“Matar Soja ya akayi ne yau naganki haka?”
Nanfa sukaita bata shawarwarin abubuwan da zatayi…
Tana komawa gida ko ta caba kwalliyar ta..
Sanda ta dimanci sadda ze dawo daddare tukunna taci qanan kaya ta sawa kanta ribbom baki dankwali ta fitoh palo kusa da mum ta zauna..
“Ahhh yanmata irin wannan kwalliya haka”
Dariya kawai Ummi tayi
“Mum gsky ya irfan baya sona ahaka kike cewa za amana aure”
“A’a Ummi kezaki koya masa sonki kidinga yin dik abinda ki kasan zefaranta masa yar kwalliyar nan kyau take miki kidinga yinta SBD dik kallon yar qauye yake miki kuma kidinga jamasa aji kin gane ai”…
Gyada kai tayi rufe bakinta keda wuya suka juyo horn din motarsa..kallon juna sukai
” toh kinga ni zanshiga daki inya shigo ki karba jakar hanunsa ki basa ruwa ki kawo masa abinci daga baya ki basa hakurin laifin da kika masa kinji”.
Gyada kai tayi mum ta shige wa daki tasoma fadin
“Wallahi ba hakurin da zan basa aikuwa ze mole”
🎀🎈Bema lura da ita ba ta nufosa kamar daga sama yaji ankarba jakar dake hanunsa .
“Ya irfan sannu da zuwa”
Binta yayi da kallo riqe da jakar ta nufi qofar dakinsa tsaki yayi yabi bayanta yana isa ya karba jakar yana qoqarin bude qofar yana fadin
“Nifa banason iyayyi da rawan kai”
Wannan zance ya qona mata rai Dade agurin tsaye bace komai ba har ya gama bude qofa ze shiga kenan ya juyo da mamaki yaga tana hawaye
“Lafiya haka?”
Kamar jira take ta fashe da kuka ta nufi dakinta ta fada kan gado tana kuka sosai..bayanta yabi harya sa hannu ze bude se kuma ya fasa
“Kar naje tarainamin hankali”..
Har daganan yana jiyo sautin kukanta Dan hk ya shige daki abinsa….
Washe gari da safe idanunta diksun kumbura allamun tayi kuka qin kula kowa tayi sai gaisuwar da tama mum da dad kawai ta nufi jikin motar irfan ta tsaya harya gama shirin sa ya fitoh atunaninsa ma ta tafi seya gabta tsaye ta hadiye rai..
Budewa tayi ta shiga tazauna yau fuskarta ko allamar kwalliyarma bata samu ba…
Murmushi kawai yayi ganin har sunci Rabin tafiya bata tanka masa ba yasa yasoma fadin
” Saura shekara nawa kigama mkrnta”
Shiru bata ansa ba
“Bakya jinane?”
Shiru nan ma
“Ke badake nake mgn ba”
“Kaje ka tmbyi mum kuma ma inna ruwanka ni bansani ba”
Tinda tafada masa hk bece komai ba har suka isa skul din tayi ficewarta Jan motarsa yayi abinsa…
“Kai irfan ka shirya insha Allahu zakaje gurin su innah kaifa Ummi Ku gaidasu”..
Acewar dad
Toh kawai irfan yace dad ya cigaba da fadin
” kuma kome kake kafara shirye shirye akan bikinku”
“Dad biki fa kace”..
” eh kaida ummi kuma banason musu”.
Shiru irfan yayi daga bisani ya miqe ya fice yana fita sukayi cinkaro da ummi tafe take da wasu qanan kaya da ko qasa basu kaimata ba yi tayi kamar batasan yana gun ba…
“Ummi”..
Cik ta tsaya batare da ta juyo ba harya qarasa gareta..kanta yayi fuuuu har backyard din gidan yanda mum bazata jiyosu ba..
” innajinka” tafada tare da turo baki
“Kije kice wa mum bakya sona bazaki auren ba”..
” dama cewa nayi innasanka kai kai je ka fada musu mana”
“Dama ynxu gane kan naka nakeyi?kacigaba dayin dik abinda kaga yadace komai lokacine kuma ka ajiye wannan a kanka cewar wataran seka dawo gareni”..
Fizge hanunta tayi tana ragwada abunta ta shige cikin gida..
Akwana atashi ba wuya yau aka fara shagalin biki shagulgula iri iri akayi har masoyan Asali na hango *Ibrahim* da *fatymah* (Akan So) sun zo gurin bikin Amarya ummi tasha kyau mum ta gyara yadda yakamata…
“Kamarya anan?”
“Mum inna qarasa ginin semukoma plxx mum”..
” naji aidai anyi bikin shknan”
Haka akayi taron bikin har kowa ya watse akan sunan da wata za ayi sabon taro na komawarsu sabon gida…
Zaune take akan gadon dake dakinsa ahankali taji an murda qofar
“Ke meyasa kawoki dakina?”.
Dafe kai yayi yana tsaki shidai betaba ganin Amarya irin haka ba wallahi…
Tsaki yayi ya shige toilet yana fadin
“Kiyi gaggawar fita tinkafin na fitoh ko jiki yayi tsami”
Miqewa tayi tana fadin
“Uhmm mekuma ya kawo tsamin jiki inna amaryata”
Hartakai qofa taji ringing din wayarsa…
Ahankali ta nufi inda wayar take tadauka number ce Dan hk ta kara a kunenta batare da tace komai ba…
“Hello nasan zakayi mamakin ganin kirana..khaleesat ce inna maimaka albishir din nadawo gareka irfan kasan innasanka”.
” kan uba me harkin isa kikira mijina”
Jitayi an fuzge wayar tajuya tana kallon irfan se huci takeyi kallonta ya tsaya yi da mamaki..
Meyarinyar nan take nufi kishi takeyi inkishi ne itakuma nata salon kenan..
Kara wayar yayi akunensa
“Hello”
“Baby wacece tadaga wayar”.
Yayi mamaki jin muryar khaleesat
” khaleesat ya akayi kika kirani?”
“Idan kazo gidan mu zanma bayani”
“Toh shknan gobe insha Allahu zanzo”
Yana juyawa yaga ummi tsaye tana kallonsa idanunta sun ciko da da hawaye rufe baki tayi sbd kuksn dake qoqarin kufce mata seta juya ta bar dakin…
Yana samu wuri yazauna ya miqe yabi bayanta
Shima kansa yasan baya kyautawa Dan hk ya nufi dakin nata..
Murda qofar yayi yashiga yasameta kwance a qasa se kuka takeyi ..
“Ummi”
“Ummi meyasa kike kuka kishi kikeyi”
Da sauri tadago
“Allah yasauwaqe nayi kishinka”
🎀🎈Dariya ma ta basa kawai ya miqe ya koma daki qara kiran khaleesat yayi sukayi waya kafin ya kwanta yayi baccinsa…
Washe gari
Haka suka wuni ranar tsakanin shida ummi ba Wanda yace da Dan uwansa qala…ganin yazo ya zauna yauna ko kallonsa batayi ba yasa ya soma fadin
“Jeki ki hadamin ruwan wanka”
Batare da tace komai ba ta miqe fuuu ta shiga dakin tana zuwa ta sirka ruwan me zafi tana fitowa tasoma fadin
Shiko yana shiga beyi aune ba ya kwarawa jikinsa ruwan..salati kawai yafarayi dan haka ya ta miqe tadawo palo ta zauna…
Fitowa yayi ya zira jallabiyarsa ya fitoh cike da masifa kwance ya isketa ko ajikinta..
” ke wacce irin yarinyace da zaki samun ruwa da zafi”
Waqa tasoma yi kamar bata jisa ba
“Ummi bakyajinane”.
Miqewa tayi zaune ohh harka fitoh
Qoqarin kai mata duka ya farayi mum ta daka matsa tsawa wacce ta fitoh daga daki
” ko da gigin wasa karka fara kanajina ko”
“Mum wanna yarinyar harta isa tasamun ruwan zafi?”
“Kyalesa inke yarinya ce shi kuma *MIJIN YARINYA* ba”
“Kekuma nadawo gareki maza bisa ki basa hakr”..
Turo baki tayi tana qunquni ta shiga dakin tana zuwa ta iske ya shiga wannan taja ta zauna akan gadon…
Misalin karfe 8 na dare irfan ya fitoh cikin shirin sa yasha qananan kaya da suka masa kyau sosai zaune take suna kallo ita da mum..yafitoh
” mum bari inje indawo”
Toh mum tace ya juya ya harari ummi yayi gaba abunsa tasan gun khaleesat zashi sarai …mum ko ganin batada niyar tashi takalleta tana fadin
“Tashi kije kice masa seya dawo”
Miqewa tayi tana sharar hawaye Tana zuwa ta toge jikin motars wajan seat din xamansa
“Meye haka?”
Sharar hawaye kawai takeyi batace komai ba wayarsa ce tasoma ruri khaleesat ce ya amsa
“Hlo innaji”
“Yes am on my way”
Katse wayar yayi yana kallon ummi wacce tacika tayi Pam
“Kimatsamin in wuce”
Kuka ta fashe dashi taja gefe wajan kofar Palo ta zauna bece mata komai ba yayi tsaki ya shige motarsa ya nufi gidansu khaleesat…
Sosai sukayi farincikin ganin junansu..
“Khaleesat meyasa kika tafi kika barni”
“Kasan innasanka insha Allah I wil be wit yuh nw”
Hira suka cigaba dayi yayi mata alkawarin bada bata lkci ba ze turo gidansu…
Goma Saura ya isa gida atunaninsa ze tarar da ummi a Palo amma beganta ba dakinsa ya shiga nan na gatanan cure kaya ya shiga yi ya nufi toilet ya watsa ruwa harya kwanta wata zuciyar tace yaje yadubo ummi sekuma ya share har bacci yadaukesa..
Kwance ummi take tana chatting da su hannan da iklas taji anturo qofa mum ce miqewa tayi zaune tana fadin
“Mum kece”
“Eh ummi dama so nake infadamiki ki shirya nxtweek insha Allah zaku tare agidanku”
Kwata kwata ummi bataso hakan ba…amma ta ansa da toh kawai…
Hira sukadanyi kadan kafin mum ta nufi ma kwancinta..itama kwanciyar tayi SBD ynxu ko ganin irfan batason yi ma. Ji tayi anqara turo qofa ta miqe tana fadin
“Mum baki kwanta ba”
Tana juyawa sukayi do hudu da irfan komawa tayi ta kwanta
Yana ganin hk shima ya juya abinsa ya fice..
Acewar sa bayaao tarainashi..
*10*
🎀🎈 “Ummi inna kayana Dana ajiye akan gado?”
Cewar irfan dake tsaye cikin jallabiya alamun daga wanka ya fitoh shiru tayi kamar bata ji meyake cewa ba
“Ke Ummi bakya jinane?”
“Ohhh dani kake?”
Takaicine yacikasa lallai yarinyarnan ta rainasa kasa cewa komai yayi yana kallon kafin yace
“Kayana Dana fitoh dasu na ajiye akan gado suna inna?”
“Ni bangansu ba ai”..
” karki rainamin hankali mana daga ni se me agidanan zannemi kaya na rasa kice bakisan inda suke ba”
. sassauta muryar tayi ta juya tana fadin
“Aifadai kanka akeji”
“Mekikace???”
“Ni bance komai ba cewa nayi qila akwai aljanu agidan”
Ganin tama raina masa hankali yasa ya juya yashiga daki yana shiga tafara maimaita maganarsa rufe bakinta keda wuya ta gansa da zabgegiyar belt aikuwa ihu tasa ta miqe adari tayi daki taba wayyoh nashiga uku..
“Zaki dauko min kosenayi maganinki”
Itako tana shige wa daki kan ya qaraso fadama dakin key bugawa yashiga yi amma ta koma kan gado tana fadin
“Wallahi sedai kafada fitar haka kurin katafi can gurin wata kaita wa share baki nikuma kana dauremin fuska “
Baci ransa yayi sosai ya juya ba yadda ya iya sedai ya nemi wasu kayan yasa…itako sanda taji dirin motarsa allamun ya fita tukunna ta fitoh
Tana fitowa ta zauna tana fadin
“Zanyi maganinku kaida ita”
Zama tayi tadau wayarta tasoma kiran hanan
“Hello kawata ki naji”..
” eh Amarya ya har nagama cin amarcin ne”
“Kedallah can kekiasan wani amarci”
“Toh meyayi zafi kuma”
“Kingafa wai ya irfan bashida aikinyi sena kullun daddare yadau kwalliya ya fita kuma nasan gun wannan makirar khaleesat data kirasa kwanaki yake zuwa”
Tsaki Sosa hannan tayi..
“Aike kikayi sake bakya kula dashi ne shiyasa”
“Kibar fadan haka bakisan irin zaman da mukeyi bane baya sona kwata kwata”
“Hakuri zaki farayi yar uwa”
“Ni kinsan meyake damuna ace wai yadinga cemin yarinya”
Dariya hanan tayi tana fadin
“Seki yarda kawai kutafi a ke yarinyar ce”
Tsaki tayi ta latse wayarta dan ita taqi jinin ace mata yarinya…
“Dad aure nakeso nayi”
“Aure kuma son wani irin zancene wannan dikka dikka yaushe kayi auren”
“Dad kasan mum ce ta takuramin kuma ni khaleesat nakeso Dan Allah dad ka taimaka min”
“Amma kasan mum dinku bazataji dadi ba ko?”
“No dad shiyasa nafadama I knw za kafahimceni plxx”
“Bakomai jeka zamuyi mgn da ita”
Rufe bakin dad keda wuya mum ta shigo cike da fara’a suka gaisa tana tmbyrsa ummi yace tana lafiya miqewa yayi cikin rawar jiki yabar gidan…
“Zauna innason magana dake”
Cike da mamaki mum ta wangale baki tana kallon dad ya cigaba da fadin
“Kiyi hakuri kibarsa yayi aurensa tinda dai ummi ba muxguna mata yakeyi ba kings ykmt ke zaki qara hada Kansu”
“Yanaga kin sake baki kina kallo na”
Se ynxu mum tasoma fadin
“Haba ba dole in sake baki inna kallon ikon Allah ba…”
Ran dad ne yabaci yasoma fadin
“Tinda ke haka kike toh aure seyayishi”
“Haba Abban suhaima wannan aiyi bane”
Dad neyasoma fadin
“Yaronan biyayya yayi fa ya auri ummi indai kinasonsa aiyakmt shima ki basa farin cikinsa..”
Qin yarda mum tayi Sam da batun dan haka dad kuwa ya dage akan se irfan yayi auren…
Yau kwana uku kenan in irfan ya shigo mum bata sake masa sosai..
Ummi ko tanacan bama tasan da xancen auren ba kullun burin ta tasan yadda zata jawo hankalin irfan gareta…
Zaune yake bakin gado yana waya da khaleesat ta turo qofar dakin cikin shigar Riga da wando da suka mata kyau…
Tsaya wa tayi cik gane wa tayi da khaleesat yake waya Dan haka tayi wuf ta fuzgewayar
“Wallahi ynxu ni ykmt kabama lkcinka ba ita ba”
Shiru yayi yana kallonta ta latse wayar ta jefa kan gado kallonta ya tsaya yi..tayi masa kyau sosai amma ya dai daure fuska yana fadin
“Me kinrainani ko”
Damqota yayi tahau fadin nashiga uku
🎀🎈”Dallah rufamin baki Abinda kikeso zan baki innace lokacina kikeso”
Kuka ta somayi gmya saketa yana tsaki aikuwa batayi aune ba tafice daga dakin…
Shiko kwana iya yayi ya jingina jikin gado shiru kamar me tunani…
Shirye shiryen biki aka fara tsakanin dad da irfan mum kuwa tace bada sa hanunta ba…
“Irfan ka fadawa matarka Abinda ke faruwa kuwa?”
Acewar Abba..gyada kai irfan yakeyi yana fadin
“A’ah dad ban fada mata ba”
“Toh yau in kaje kasanar da ita kagane?”
Eh ya amsa dashi suka cigaba da zancensu…betashi komawa gida ba se daya biya gurin khaleesat su kasha hirarsu ya bata kudi domin siyayyar da take buqata…
Misalin qarfe 9:30pm ya shiga gida zaune ya iske ummi tana cin abinci tasa doguwar riga wacce bata qarasa qasa ba allamun ta barci ce takoyi mata kyau sosai…
Tana ganinsa ta washere baki ta miqe tana fadin
“Sannu da zuwa yau kayi dare”
Shiru yayi yana ta binta da kallo ta dauko kular abinci ta kawo masa…
Har ynxu bece komai illa binta da yakeyi da kallo tausayi ta basa se yaji kamar kar ya fada mata amma ba yadda ya iya dole tayi hkr…
“Kizauna innason magana dake”
“Toh kaci abincin tukunna ai ynxu kadawo”
Bece komai ba yasauka yanaci kallonta yakeyi ita ko hankalinta na kan TV tana kallo…
Matsowa tayi kusa dashi ta zauna saman kujerar dayake zaune..janyota yayi ta baya ya hadeta da jikinsa sosai hakan ya bama ummi mamaki irfan betaba mata haka ba..
Kuka tafarayi harda yan guntun hawayenta aranta tana fadin
“Allah yasa ynxu irfan sonta yakeyi”
Tadade ajikinsa yana tunanin ta inna ze fara..
“Ummi dama wani zance zan miki”
“Zancenme ya irfan”
“Ummi Dan Allah kiyi hkr da Abinda zakiji am so sory inna Santa ne sosai”
Shiru ummi tayi ynxu kam jikinta yariga ya mutu…
Ahankali ta soma janye jikinta daga nasa…
“Ummi kinga harynxu ke yarinya ce..bazan yarda na zama mijin yarinya ba..secondary kawai kika gama innada burin insama miki mkrnta kici gaba.. Khaleesat kuwa ta kammala aiki kawai take jira kings baza’ace ita yarinya ba..amma ynxu ke bazaki wuce shekara 18 ba”
“Nifa dik surutunka ba gane wa nakeyi ba”
“Ummi kiyi hakuri nan da wata daya insha Allah zanyi aure kuma ke amatsayin kan wata kike har ynxu”
Da sauri ummi ta miqe tana kallonsa batace komai ba ta juya ta nufi hanyar daki sokoko kamar Mara lafiya..
Ganin yasa ya soma kiran sunanta amm bata tsaya ba seda yashiga dakinta key tasa ta rufe ta koma ta kwanta shiko zuwa yayi ya qara ci bugun qofarsa ya gaji ya tafi dakinsa….
Hawayene kawai ke zuba afuskarta tajanyo wayarta tasoma kiran hanan…
“Hello kawata ya akayi ne?”
“Hanan ya irfan aure zeyi”
“Aure kumavwani irin zancene haka”
Magana suka shigayi Wanda banajin mesuke fada sosai..har suka gama wayar ta kwanta so take tayi kuka amma takarasayi ahaka bacci ya dauketa…
Yau bikin irfan Sauran sati daya
Mum ce ta shigo da sallamar ta ummi na kishingide gaba daya ta rame tayi fari kamar ba ita ba shiru mum ta tsaya kallonta…
Da sauri tadago ta kalli mum aikuwa kamar jira take tafashe da kuka..rungumota mum tayi ta shiga bata hkr…
“Jibi yadda kika rame kinutsu makaranta nasa Neman miki kar ki saki komai nasa yadameki kingane”
Tana cikin gyda kai irfan ya shigo isowa yayi ya gaida mum ummi kuwa dauke kai tayi batace komai ba..kallonta yakeyi dik tayi wani iri kamar ba ita ba Dan ynxu was an buya sukeyi seya fita take fitowa Palo..
“Ummi bakida lafiya ne?”
Tsaki mum tayi tana fadin
“Jibi yadda ka maida min ‘yata irfan toh bari ma kaji yau dinan gida zamu koma da ita”
Da sauri ummi ta kalli irfan Wanda shima ita yake kallo share hawayen fuskarta tayi baso bin mum ba SBD har ynxu tana sonshi….
*Barka da juma’@h*
🎀🎈Irfan na zaune a Palo mum da ummi suka fitoh da sauri ya nufi gun mum yana fadin
“Mum plxxx kiyi hakuri Dan Allah”
“Irfan ka matsamin karna bata ma rai”
Kallon Irfan kawai ummi takeyi itama yana kallonta ahaka mum ta jata suka fice driven da mum tazo dashi ne yasa kayan a mota ..suma suka shiga irfan na tsaye bakin qofa yana ji mum tana fadin
“Kazauna da wadda kakeso kucinye soyayyar ita kanta”
Jan motar driver din yayi
“Mum tafiya fa mu kayi muka barsa”
“Zaki samu damar rufe min baki ko ya akayi? Mara zuciya kawai se yarinya ta dake damunki”
Shiru Ummi tayi tana sharar hawaye ita dai tana son mijinta sosai..
Suna isa gida dad nan Dan hk mum tace dashi ummi banajin dadi ne zata kula da ita..ba musu da ya amsa da toh yana tmbyr ya jikin ummin…
Ummi kuwa kuka tadingayi a daki sosai wannan karon dakin irfan ta shiga wanda har ynxu akwai wasu abubuwan nasa aciki hotunan sa ta shiga kallo tana kuka se kuma zancen aurensa ya fado mata arai…
Wani sabon kuka ta somayi…Irfan kuwa yana juyawa yaji gidan ya masa shiru irin tsiwarta ya soma tunowa da rashin kunyar da take masa tunani ya shiga yi
*Flash back*🤣
“Ummi kin rainani ko? Ki bani key din qofar”
“Bazan bayar ba hk kurin se dare yayi ya dinga fita cabdijan”
Fusata yayi ya nufi daki..tsaki tayi tana fadin
“Nasan belt ce kullun da ita kacemin barazana ba iya dukana zakayi ba Wlhi ba inda zani”
Zama tayi can taga yafito ta miqe tsaye taja ta tsaya..
Yana zuwa ko ganin taqi guduwa yasa ya zuga mata daya ihu tasa tana fadin
“Wayyoh Allah ba yana qasan kujera fa”
*Back to current scn*🤝
Zama yayi shiru daga bisani ya nufi dakinta….
Dik a tunanin ummi irfan ze biyosu yabama mum hakuri amma shiru bashi ba dalilinsa koya shigo ma sedai taga ficewarsa…
Yau daurin auren Irfan da amaryarsa khaleesat… Hankalin ummi beqara tashi ba sedataga gidan ya cika da yan tafiya saurin aure dik tana kallonsu ta window.. Irfan se washere baki yakeyi yana dariya cikin abokansa…
Kuka sosai ta shiga yi abun ya bata mata rai sosai da sosai bata taba tsamanin hakan agunsa ba…Dan hk itama zata canja daga yadda yasanta…
Dad ne ya kirasa yana fadin yaje ya dubo ummi kafin su tafi daurin auren.. Ba musu ya nufi dakinta be ganta ba yama shiga dakinsa yaganta tsaye jikin window bama tasan yashigo ba ba Abinda takeyi banda kuka..
Ta bayanta ya rungumota yama fadin
“Yarinya dake har kin iya kishi./”
Mamaki zancenta yayi betaba tunanin hakan daga gareta ba gaba daya jikinsa yayi sanyi..
Ruqo hanuwanta yayi yana fadin
“Ummi baki babu kyau mace ta bude baki tace mijinta ya saketa ba..”
“Wallahi kai ba mijina bane”
“Ai dama ni ba’a matsayin matata kike ba nariga na fada miki mstsayin kanwa ta kike Dan haka ki qyaleni”
Har ya juya ze fita ta riqo rigarsa
“Bazan iya rayuwa da Wanda baya sona ba seka sakeni”
Fusata yayi yana fadin
“Na sakeki daya”
Mum ce ta shiga bata taimakon gaggawa har ta farfado..
“Me ya hadaki da irfan?”
Wayincewa tayi tana fadin
“Wane irfan din?wani abu kikaga ya faru?”
. jin hk yasa mum tace bakomai ta miqe ta fice bayan sun dawo daga daurin aure ne mum tasanar dad ai irfan ya saki ummi…
Suna zuwa part din khaleesat suka nufa suka tarar har an kawota..
Hira suka dingayi amma Sam hankalinsa baya jikin sa kokadan…har abokansa da kawayenta suka tafi bayan yadawo part din ummi ya fara isa abun duniya dik ya ishesa yarasa meke masa dadi…
🎀🎈 Daga bisani ya miqe ya nufi part din khaleesat
Murmushi take tayi har yashigo daqyar yasamu ya tattaro fara’arsa ya zauna suna hira…
Can kuwa gun Ummi waya takeyi da hanan suna hira…
“Ai irfan ya sakeni gwara na huta nacire son danake masa hakan abun nasa yayi yawa”
“Keko kawata kinyi wauwta Wallahi da baki bari ya sakeki ba”
Tsaki ummi tayi tana fadin
“Dallah nidai kizo gobe Dan Allah inna gida”🙊
Kwance ummi take tarasa meke mata dadi arayuwarnan..wata zuwarce ke cemata gwara ki koma can gombe gurin inna ki huta”
Murmushi kuwa tayi Dan hk ta miqe ta nufi dakin mumwacce ke gyara kayan sip dinta…
Dasallamar ta yashiga mum ta amsa
“Ummi ya akayi ne?”
“Mum dama cewa nayi innaso inje gurin inna se inyi iddah acan daga baya se ondawo incigaba da karatu”
Sam mum bata so ba amma dole ta amsa mata da toh…
“Kishirya toh zanma dad dinku bayani innaso zuwa jibi sekije”
Dadi sosai ummi taji Dan haka tasamu wuri kan gadon mum ta kwanta tana game awayarta..
Mum ko tsaya wa tayi tana kallon ummi dik ta bata tausayi…
_2days later_
Misalin qarfe 4pm ummi ta isa garin gombe napep ta samu wacce zata kaita har qofar gida murna sosai innah tadingayi har da wasu qawayenta na anguwa aka dinga zuwa ganinta..
Wata makwafciyarsuce ta shigo tana fadin
“Ummi innace batayi wata uku da bikinki ba ya naga kindawo nan”
Innace tayi caraf tana fadin
“Hutu tazo yi zata koma insha Allah”
Nanfa akaita hira ummi tasamu ta sake..
*Night*
“Ummi kodai ciki ne dake?naga kinyi fari”
cewar innah…tabe baki ummi tayi
“Cab ciki inna zaman lafiya barma zancenan innah”
Nanfa innah yashiga tmbyrta Abinda ya faru kaf ta bata lbr….tsaki innah tayi tana fadin
“Wannan yaro beyi halin uwarsa munan dake seya biyoki”
“Cabdijan ai wallahi banason ko ganinsa ynxu”
Dariya kawai innah tayi ta juya ta soma iza wutar iccen data hura…
*garin kano*
“Khaleesat meyasa kafarki bata zama a wuri daya kullun inna dawo bakya nan abinci sedai nasiyo”
Yatsine fuska khaleesat tayi tana fadin
“Aifa sekayi kanka akeji ninagaji”
Daki ta shige ta barshi tsaye agun sokoko kaya tashiga cirewa tasamu wuri tayi kwanciyarta shigowa dakin yayi yana fadin
“Ki tashi ki samu abinda zaki dafamin yinwa nakeji”
Sake baki yayi yana kallonta ya rasa mexece mata fita yayi daga dakin har yakai motarsa ya shiga part din ummi dakinta ya shiga ya tsaya kallon hotunan ummi dake dakin…
Daga bisani ya fita abinsa ya nufi gidan mum…
Da sallamarsa ya shiga ya iske Mery tana goge dinning
“Plxxx kawomun abinci am hungry”…
Owk tace masa tana shiga kitchen mum ta fitoh ya gaidata sama sama ta amsa ya zauna qofar dakinsa kawai yake kallo yaga ta inna ze ummi zata fitoh.. A iya saninsa dai iwar haka ummi tana Palo…
“Mekakeyi anan daddare”
“Mum yinwa nakejine kuma khaleesat taje anguwane bata dawo dawuri ba”
“Har qarfe nawa yadawo da bazata iya ma girki ba”
“Mum gurin biki tajene wajan 9 yadawo”
Tsaki mum tayi tana fadin
“Ynxu wacce matar kirkince kuma Amarya ko wata biyar batayi ba harta fara zuwa gidan biki tana kaiwa qarfe 9 na dare”
Shiru yayi bece komai ba Dan shi kansa yasan khaleesat din bata kyauta ba..sosai yake so yakawowa mum Ku kasan sa akan khaleesat din amma tsoro yake…
Abincin aka kawo masa yasoma ci miqewa mum tayi zata tafi daki da sauri yasoma fadin
“Mum ummi tayi bacci ne?”
Shiru mum tayi sai ta juyo ta qare masa kallo tana fadin
“Ya akayi meye hadinka da ita kake tmbyta?”
Shiru yayi
“Mum dama gani nayi ban ganta apalo ba”
Tsaki tayi tana fadin banda lokacin ka..ta shige daki abinta
Shiko harya gama cin abinci ummi bata fitoh ba Dan hk ya tmby merry inna ummi nan ta fada masa ai ummi ta tafi gombe.
Gabadaya jikinsa yayi sanyi ko mum bema sallama ba ya fice daga gidan…
Yana isa gida ya zauna akan kujera khaleesat ce ta fitoh tana hamma
“Ashe kadawo”
Eh kawai yace ya juya daga dubanta..
“Inna abincin yake ne yinwa nakeji innace siyowa kayi”
Kallon takaici ya mata ummi ta fado masa arai lokacin ko da bazeci ba setayi ta ajiye amma khaleesat din yakeso ita take masa wannan abubuwan…
“Kayi shiru inna yake”
🎀🎈Tsaki tayi itama ta shige kitchen tasoma dora indomie…
Washe gari da safe irfan yasa khaleesat ta shirya akan taje ta gaida mum ba musu ta shirya tadauko wani guntun gyale ta yada ta fitoh
“Khaleesat meye haka kuma bakida hijab ne”
“Haba baby nifa wannan nakeson sawa”
“Jeki canja kisa hijab”
“Nidai bazansaba wannan nafiso”
Ganin ya miqe fadan fadan tasan ze iya jibgarta yasa tayi daki da gudu can sai gata ta canxo hijab tsaki yai. yayi gaba tabi bayansa…
Har suka isa bawanda yace da wani ‘A’ suna isa suka shiga gidan Palo suka zaune kafin ya shiga daki ya sanar da mum ai yazo da khaleesat ta gaisheta…
Bawata fara’a a tattare da ita ta biyosa suka fitoh…
Sama sama khaleesat ta gaisheta ta amsa
Miqewa mum tayi ta nufi kitchen
“Gsky ka tashi tafi bazan iya zama anan ba”
“Kinada hankali kuwa khaleesat kiga yadda kiga gaida mahaifiyat”
“Toh dan mahaifiyar ka ce fa?”
Daga hannu yayi ze mareta yajiyo muryar mum tana fadin
“Kul karka kuskura ai dama dik Wanda yasani rariya yasan zatayi zuba”
Turo baki khaleesat tayi tayi gaba abinta ta fice…
“Wuce kaje ka maida ta”
Marairaice fuska yayi yana fadin
“Dan Allah mum kiyi hakuri”
“Ba’abinda kamin kawai dai naji dadi da Allah ya hadaka da daidai dakai”
*2weeks later*
“Ikon Allah idan nadawo da ummi nan mezatai maka ai ynxu ummi ba matarka bace”
Shiru yayi ya rasa mezecewa mum
“Mum wallahi ynxu innasan Ummi”
“Nooo ba wannan zancen Irfan ummi yarinya ce kuma kai kam bazaka zama *MIJIN YARINYA* ba ko?”
“Dan Allah mum kiyi hkr kitaimakeni”
“Bataimakon da zanma irfan kariga ka watsamin qasa a I do dan haka se ka kwashi jiqaqqun qafafuwanka ka tafi gombe nidai bazan sa baki na aciki ba”
Ganin mum taqi basa hadin kai yasa ya miqe ya fita shida khaleesat kuwa kullun fada se yawo da take dashi tin baya taba lafiyar jikinta harya fara amma bata denawa…
Bayan sati daya shirye shirye irfan yake na tafi ya gombe ya shirya akan ze je gurin aiki ya nemi permission SBD abarsa ya tafi yana tukunsa be akankare ba birkin motar ya kwace masa ya bigi wani gini kafin yaje ya bigi bishiya…
Mutanen dake gun ne suka hau salati aka taimaka aka kaisa asibiti… Wayarsa aka dauka kasancewar da pin sedai aka cire layinsa akasa awata wayar aka kira khaleesat aka sanar mata aka kira mum ma aka sanar musu..kan kace me harsun hallara asibitin ..
Dad ko sawa yayi aka maidasa babban asibiti yafi 2hours be farfado ba se daga bisani ya far fado mum ya fara gani sanan ya kalli dad khaleesat dake gefen sa ya kalla kafin ya qara kallon mum…
“Mum meya kawo khaleesat nan gurin bayan ta yaudareni tayi aure ta barni”
Kallon juna suka dingayi kamar muna fukai miqewa yayi zaune yana dafe kansa mum ta taimaka masa…
“Mum inna ummi ne ko batanan?”
Nan ma mum ta qara kallon dad
Khaleesat ce takai hannu tana ce masa sanu..
“Mum plxxx kuce tabar gurinan dik son dana nuna mata ta auri wani kuma ma tana matar wani meyasa kawota wuri na..ummi ce matata..plxx mum Ku kira mata ummi ta ga ummi..khaleesat kin yaudareni bana sonki”
Kallonsa suke tayi khaleesat ce ta soma fadin
“Baby nice fa khaleesat matarka”
Tsaki yana fadin
“Bazaki taba zama matata ba ki koma gun mijin naki plxxx leave”
🎀🎈likitan na shigowa ya kallesa yana fadin
“Sannu me sunanka ma?”
kallon yayi yana fadin
“Irfan “
Nuna masa mum da dad yayi yana fadin
“Suwaye wa’anan kuma ni bansan su ba”
Acewar likita..
“Iyayena ne mana”
Acewar irfan yana rufe baki suhaima ta shigo ita da mijinta..
Juyawa likitan yayi yace
” itace sis dita my 1 nd only sis”
Maida dubansa likitan yayi ga khaleesat yana fadin
“Tsohuwar budurwa tace wacce ta yaudareni ta auri wani”
Likitan nunfasawa yayi ya kalli mum and dad yace subiyosa office suhaima kuma ta kula dashi…
Suna shiga office din likitan ya musu iso…
“Alhaji a iya Sabina da Ku wanan itace yarinyar da irfan ya aura..kuma yayi lossing memory dinsa na watannin baya da suka wuce…Ku tmbysa idan akwai Abinda yakeso idankuka basa kuma kunayi kuna tuna masa dawasu abubuwan ze iya dawowa daidai insha Allah kuma zan Baku magungunan da zau dinga basa kuma kar kuyi Abinda ze qara birkita masa lissafi”
Shiru mum tayi daga bisani dad yama likitan godiya kafin suka miqe..
Daidai ta fara fadin
“Ai ummi tana gombe”..
Mum ce tayi karaf tana fadin
“Eh kamanta kai kace taje gida”
Zaro ido yayi yana fadin niii…
Harara dad ya gallama mum
“Meyasa kike hakane?”
“Ai gwara shima ya dandana wallahi”
Tsaki dad yayi yana fadin
“Irfan ka nutsu kaji ni zanje in taho da ita kaji”
Sannu mum tace ta koma ta zauna khaleesat ko jiki dik ya mutu dik da basu fada mata ba tariga ta gane abinda yasameshi miqewa tayi ta fice daga dakin tasamu wuri ta rabe gurin daya ta zauna ta tunanin yadda zatayi…
Dad ko kiran mum yayi sufa fita gefe
“Ki kira ko ki aika a taho da Ummi”
“Cab aiko kasan ummi ba matarsa bace dan yaci ace ma ta gama iddah”
Shiru dad yayi daga bisani ya soma fadin
“Base asake daura musu aure ba ko ya kika gani”
“Aiko nasani ba salon nan gaba in hankalinsa yadawo yazo yace ba matarsa bace”
“Haba hajiya ya kike hakane”
“A’a kawai yayi hakuri ya cigaba da zama da khaleesat din zama zakayi ka fahimtar dashi ynxu khaleesat ce matarsa”
Mum na fadan haka ta juya tayi shigewarta dakin..
*Bayan An sallamosu*
“Dad wai yaushe ummin zata dawo ne?”
Murmushi dad yayi ya kalli mum yana fadin
“Kar ka damu insha Allah zata dawo”
Khaleesat ce tashigo dauke da plate din. Abinci ..
“Ga abinci kaci”
Tsaki yayi yana fadin
“Cemiki nayi innajin yinwa…dad wai meyasa bazata tafi anan bane”
“Irfan matarka ce itama dole ta zauna anan”
Girgiza kai ya shiga yi allamun be yarda ba
“Mum kibar fadan haka kema fa kinsan innason khaleesat tayi aure ta barni dan hk ynxu banason ta mum”
Dad ne ya kallesa yana fadin
“Kaiii irfan ya isa hakanan”..
Karbar abincin mum tayi tana qoqarin basa khaleesat kuwa fita tayi ranta abace aranta tana fadin
” wannan ma ai rainin hankali..kuma Allah ya kawo Ummi’n lfy inga ko ita wacece “
*Night*
“Hajiya wannan karon umarni nake baki ba shawarar ki nake nema ba”
“Toh name kuma”
“Zuwa zakayi kidauko ummi koda bazaki yarda ya aureta ba ta zauna dashi har hankalinsa yadawo”
Shiru mum tayi daga bisani dad ya kuma fadin
“Kishirya gobe muje gombe tare”
🎀🎈Washe gari suka shirya zuwa gombe tinda sasassafe suka dau…
“Innah kiyi hakuri ki bamu Ummi “
“Dannan bawai naqi bane..yaronan naku bason ummi yake ba shi meyasa bezo biko ba?se Ku”
“Bashi da lafiya ne” acewar dad shiru inna tayi tana fadin ynxu ya kakeso ayi?
“Inna Aron ummi za’a bamu tazauna da irfan tadinga taimakawa ya tuno abubuwan sa na baya”
Tabe baki innah tayi daga bisani tace su bari ummi ta fitoh daga wanka…
Ba’afi yan mintina ba ta fitoh sadda ta gama shiryawa kafin ta fitoh ta same su gabadayansu kallonta sukayi dantadan rame cike sa fara’a ta gaisasu suka amsa..
“Watoh ummi kin taho kin barni ko dama guduwa kikayi”
Acewar mum dariya ummi tayi
“A’ah ai zan dawo mum kodan makaranta”
Murmushi mum tayi tana fadin aiseki shirya mu tafi”
Innah ce tasoma fadin
“Kunce yau zaku koma kumata bayanin abinda ke tafe daku”
Mum din ma kallon dad tayi kafin yayi gyaran murya yana fadin
“Ummi dan Alfarma mukazo nema agunki dik da mun San abinda irfan ya miki be kyauta ba”
Gaban ummi ne ya fadi kanta na qasa kunyar dad takeji amma bataso takoma
saboda irfan ba taso karatunta ne ze maidata…
“Ummi kiyi hakuri nasan ynxu bakyason irfan ba aurensa zakayi ba zama kawai zakiyi amatsayin matarsa ki taimaka hankalinsa ya dawo kuma maganar karatunki zaki cigaba dayinsa”
Jimmm ummi tayi tana jin nauyin dad sosai ba yadda ta iya saidai ta amsa da toh
Dadi sosai dad yaji..innah kuwa bata so hakan ba mum ma bataso ba..
“Jeki tayata hada kayan mu tafi”
Dad ya fada yana kallon mum..innah da mum ne suka miqe suka bita daki dad ko godiya ya dinga ma innah ya fice daga bisani…
“Idan kikaje so nake ki juyamin shi ba yana miki kallon yarinya ba..ki basa wahala kuma kisani ke ba matarsa bace ynxu”
Acewar mum..innah ma qarawa tayi da..
“Umimi ta ki qoda min shi yadda ze gane shayi ba ruwa bane”
Itadai ummi gyada musu kai kawai takeyi..suna gama hada kayan suka kama hanya…
Dad ko qin yarda yayi mum ta wuce da ummi gida sedai amaidata gun irfan din har seya warware tukun na…
Ba yadda mum ta iya saidai ta yarda..shiko dad burinsa kawai in ummi ta koma yasan yadda za’ati sa sake musu sabon daurin aure…
Suna isa gida da sallamarsu khaleesat na zaune tana ganin su ta washare haqora tana musu sannu da zuwa dad ne kawai ya amsa mata mum ko aranta tana fadin
“Yarinya daga baya kenan ai kin makaro”
Daki suka shiga gun irfan yana ganin ummi yayi murmushi yana fadin
“Ummi inna kikaje kika barni”
Harara ta watsa masa tasamu wuri bayan mum ta tsaya…
“Gatanan se ka qara korata ai in ka so”
“Haba mum metamin dazan korata”
Jan ummi mum tayi suka fice suna fita part din ummi suka nufa
“Kinutsu kiji bance ki sake jiki dashi ba..kuma karki sake masa fuska hakan ze gane yarinyar ma nada daraja…kuma waccan itace matar tasa..kar ki kuskura ki raga mata balle tarainaki..”
Toh ummi tace nan mum ta bata lbrn rashin mutuncin data mata da irfan ya kaita kuma ta bata labarin abinda ya samu irfan din…
“Amma kuma banda rashin kunya dan yaya ne agurinki kin gane ai”
“Eh mum bakomai insha Allah..amma mum innaso insiya abu banda kudi”
“Kawata kizo gidana gobe akwai magana…ki kawomin kaya masu kyau na zaman gida”
“Kewanne gidan naki?”
Hanan ta fada daga can…
“Gidan ya irfan mana”
“Inna zakaje”
“Inna ruwanki gun matata zani”
Takaicine ya cika khaleesat dan tasan gun ummi zashi
“Irfan nice fa matarka khaleesat”.
Tsakiysyi yabita gefentaya wuce…
Jingina yayi jikin jikin bango daga bisani ya matso yana fadin
“Zan iya tayaki?”
Bude baki tayi da niyar cewa a’ah sai ta hango khaleesat tana leqensu ta window murmushi ta qaqalo tana fadin eh…
Shiko dadi yaji sosai besan dan khaleesat ta masa hakan ba goge gogen da takeyi yatayata itako khaleesat kamar ta nutse kuka tafarayi ta nufi part dinta..
“Ya isa hakanan nagama ai”
Tana fada tana hautsine fuska..toh yace kamar wani soko yanufi kitchen tana kallonsa bata ce dashi komai ba ta dauko turare tahau sawa..
Leqawa tayi taga me yakeyi wanke wanke yakeyi tsaya wa tayi kallonsa ta tsinci kanta dayin murmushi dan har ynxu banajin Son irfan a zuciyarta amma ba yadda ta iya dole ta rama abinda ya mata…
Juyawa tayi tabar gurin ta nufi dakinta tahau gyara wa tasa turare ta wanke toilet haka ma nasa tasa turare ta wanke toilet… Irfan ko yana gamawa fita yayi ya nufi gun khaleesat
“Mekika dafane yinwa muke ji”
Kallonsa khaleesat tayi tsaf dik yabi ya wani rude
“Bandashi”
Fitowa yayi tahau motarsa yaje ya siyo musu abinci itadai khaleesat nata ido..
Bayan sun gama abincin ne ya miqe zeyi wanka kallonsa tayi tana fadin
“Kaje kawa khaleesat sallama”
Shiru yayi kamar bazece komai ba
“Daganan seka dauko maganinka”
Toh kawai yace ya nufi qofa tana ganin ya shiga part din khaleesat ta dan nawa qofar part din nata key..
Can ko yana shiga ya dauko maganin ze fita
“Irfan inna zakaje?”
“Inna ki kasan zani gun matata mana”
“Irfan nice fa matar ka waccan ba matarka bace bafa irfan”
“Inna ruwan ki dani?ummi matatace baki isa ki rabamu ba tunda ke kin manne min”
Wucewarsa yaya yana zuwa ya murda yaji qofa a rufe ..
“Ummi ki bude min”
“Inka shigo me zakayi ka tafi gurin Khaleesat kawa”
Shiru yayi ransa ya baci matuqa yarasa me zeyi tana kallonsa window ya juya kokadan nagaji dadin abinda tayi ba..haka ta koma ta kwanta…
*Washe gari*
“Yauwa kawata ai nayi tunanin bazakizo ba”
Dariya hanan tayi tana fadin
“Ai gani nazo kuma yarda kayan da kuka ce”
Fiddosu hanan ta farayi qanan kaya ne masu kyau sun hadu ba kadan ba Dariya ummi tayi tana fadin
“Shiyasa nake sonki qawata akwai ki da qwanya”
Dariya sukayi suka tafa..
“Inna matar tasa?”
“Tana can gefenta shi kuma ya tafi aiki”
Bayan tayi sallar magrib ta wanke kayan data zaba Tass ta shan yasu..
Wajan 11 irfan ya dawo su khaleesat anyi kwalliya harda girki…
Irfan na fitowa daga motarsa ya nufi part din ummi yauma kamar jiya ta kulle qofa tsaki yayi tare da buga qofar ya juya a fusace ya nufi part din khaleesat…..
Tana ji an turo qofar da sallama ta miqe ta nufi inda yake tana fadin
“Baby sannu da zuwa”
“Ya akayi bazaki ban wuri incire kaya ba koya akai?”
*Washe gari*
Irfan tinda safe ya shirya ko sallama be mata ba ya nufi part din ummi tavi kwalliya tasha qananun kaya..tana ganin shigowarsa amma seta make kamar bata gansa ba ta miqe ta nufi kitchen ya rakata da ido tana dawowa suka hade ido…
“Auhh Ashe tashigo”
“Eh nashigo..ummi yinwa nakeji”
“Kashh aiko banyi girki ba”
Khaleesat kuwa yana fita ta saba gyale ta nufi gidansu irfan cikin sa’a ta iske dad na shiru ze fita gaidasu dikka tayi suka amsa…
“Ya akayi naganki da safe kuma inna irfan din”
“Ya tafi gurin aikin”
“Toh toh madallah ya jikin nasa inji dai bakomai ko”
“Dasauqi amma dad dan Allah sonake kace ma irfan ya yacanja gida gwara ya hadamu agida daya kome akeyi inna kallo kullun fa seya kwashi qara ya tafi gunta baya kulani”
Shiru dad yayi daga bisani yasoma fadin
“Karkiji komai ki kara hakuri zan kirasa kinji”
Amsawa tayi da toh mum ko dake gefe aranta tasoma fadin
“Aikin ummi na kyau kenan zan ga karyar rashin kunya ai gwara a hadasun”
🎀🎈Tana zuwa tasawa ummanta kuka tana bata labarin kaf abinda ya faru..
“Toh hakuri zakiyi tinda ke kikace kinasonsa se ki iya takunki”..
Ba abinda khaleesat take se kuka…
Wajan karfe 2 ta nufi gida tana zewa ta iske ummi zaune a varender din part dinta taxi Riga da skrt masu kyau Wanda be kaima ta har qasa ba se chatting dinta takeyi…
Khaleesat ko kamar taje ta rufeta da duka haka takeji ..part dinta ta shige tarasa me zatayi ne ahaka har barci ya dauketa…
Bayan sallahr isha’i irfan ya nufi gidansu kasancewar dad ya kirasa…
Da sallamarsa ya shiga ya gaidasu suka masa ya jiki mum tana tamabayar ya ummi…
” irfan dama Sonake incanja muku gida zan baka daya daga cikin gidajena kamaidasu ciki SBD nafiso su hada Kansu”…
“Ahhh dad ai wannan ma yayi”..
” noo son kanta yayi kayi godiya ka karba “
Badayan so ma ya karba keys din gidan yamudu godiya dad yace washe gari yakeso su tare..shiko irfan babban tashin hankalinsa bayaso ya hada khaleesat da ummi aguri daya….
Sallama yana su mum ya nufi gida yana zuwa ya iske ummi a kitchen tana daga indomie murmushi yayi ya koma Palo ya zauna tasan sarai cewa zeyi zeci indomie din dan haka tayi greating din attarugu guda biyar tasa a cikin indomie din..
Tana jinsa apalo se zabga uerban attishawa yakeyi dariyar mugunta tayi tana gamawa ta zubo a plate harda guzirin nasa cokalin…
Murmushi umyayi ya sauko qasa ya zauna ta kunna TV..
Ahankali take cin indomie din dan kar yajin ya dameta sosai irfan ko yana cokali daya yaji yaji shiru yayi yana kallonta itakam ko ajikinta…
Ci ya cigaba dayi yana can majina gashi ko ruwa bata kawo ba..idanunsa sunyi jaaa..
Jin azabar yayi yawa ya miqe yana fadin “kaiiiiiiiiiiii” juyawa tayi ta kallesa kamar tayi Dariya taga ya nufi gurin fridge budewa yayi tahau daddakar ruwa Dariya ta dingayi yana juyowa seta make ta cigaba da kallonta..
Zuwa yayi ya zauna akan kujera
“Ahhh harka qoshi ne sauko mucinye”
“ahhh naqoshi”
Yafada tare da miqewa yayi hanyar waje ummi kuwa binsa take da ido tana Dariya ficewa yayi ya nufi gun khaleesat yana shiga ya isketa zaune tana game
“Ban yoghurt a fridge bakina yaji”
Zuwa tayi ta dauko masa ta basa tana fadin
“Mekaci ne haka meyaji”
“Abu naci”
*2days later*
Dad ko kiransa yayi yana masa fada
“Irfan ka kasance me adalci dik sadda khaleesat ts kawo min qararka toh gombe zan maida ummi dan haka ka shiga hankalinka dik da limits yace Kananta abubuwan baya toh anriga an fada ma khaleesat matarkace kayi hankali inba kanaso raina ya baci ba”
*Night*
Khaleesat ce sai girki takeyiwa irfan shinkaface da stew da coslow ta jera Akan dining Ummi dake zaune tasha Riga da wando jins ta dora qafa daya saman daya..
“Ke ummi wai meye haka kikeyi ne?”
Shiru ummi tayi kamar bagaji
“Inns miki magana mijina zeshigo ki koma ciki naga dai ba aurenki yake ba”
Miqewa tsaye ummi tayi tana fadin
“Kinga banda lokacin ki kiyi har karki inyi tawa kin gane ko”
“Lallai ke hsrkin isa ki gayamin magana ke qanwar bayana”
“Mstw wannan kuma keta shafa inkinji haushi kisa amaidani inda aka dauko”
“Lallai zan nuna miki baki da wayau”
Khaleesat na rufe baki irfan yashigo da sallamarsa miqewa ummi tayi ts hsrari khaleesat kafin ta soma tafiya ta gaban irfan taje ta ratsa ta wuce ta shiga kitchen…
🎀🎈”Sannu da zuwa cewar khaleesat “
Amsawa irfan yayi batare daya kalleta ba fuskarsa cike da fara’a ya shiga daki khaleesat tabi bayansa…
Kaya kawai ya cire suka fitoh Palo dinning suka nufa suka zauna khaleesat tasa masa abincin…
Yakai cokali daya kenan ummi ta fitoh daga kitchen dauke da plate din soyayyan dankali da juice a hanunta ..tafiya take tana canja salon tafiyar tata binta da kallo irfan yayi…
“Ummi ba magana ne?”
“Ohhh banmasan kadawo ba sannu da zuwa”
Yauwa yace yakaracin abincin harar juna kawai sukeyi ita da khaleesat..Zama ummi tayi tana cin abincin ta..
“Ummi ba tayi ne?”
Juyowa ummi tayi sanda ta tabbatar khaleesat na kallonsu tukun na tayi qasa da muryar tana fadin
“Kazo kaci ai har dakai na fada ma”
Murmushi yayi ya miqe
“Baby baka cinye abincin bafa”
Bece da khaleesat komai ba ya juya nufi gun ummi sanda ya zauna tukunna ummi ta kalli khaleesat da gefen ido tana murmushin mugunta..
“Ko na baka abaki ne?”
Eh ya cemata dan haka ta dibo ta basa abaki rufe ido yayi yana fadin
“Wow dadi”
Juya wa tayi tana kallon khaleesat…wacce ta buga tsaki ta miqe ta nufi daki irfan ma ya bata da kallo sanda ta shige tukun irfan ya juyo ya kalli ummi
“Ummi meyasa kike gudu na bakyason kulani?bakya kula dani?”
Dagowa ummi tayi ta kallesa gabadaya yasa jikinta yayi sanyi..miqewa tayi zata bar wurin ya riqo hanunta..
“Meyasa zaki tafi ki tsaya ki fadamin”
“Kasakeni”
Saketa yayi ta shige daki shiko ya dauki indomie din ya cigaba da ci yana murmushi shikadai…
Itako shiga tayi daki tadinga kuka..magana da irfan sa jikinta yake yayi sanyi ji take sabon son shi na shigarta ji take kamar bazata iya rama abinda yayi mata ba ga kishin khaleesat da kullun qaruwa yake dik da tasan cewar ynxu khaleesat itace matar irfan amma bazata iya jurewa ba…
*Washe gari*
Acewar irfan dake zaune kusa da dad shiru dad yaya daga bisani ya soma fadin..
“Kayi hakuri irfan kaje ka bata hakuri Ku shirya shine kawai”
“Toh dad ni zan wuce gida”
“Toh Agaidamin dasu Allah ya muku albarka ya qara hada kanku”
Amin irfan yace yaje yayiwa mum sallama ta bada kayan ciye ciye abawa ummi…
Karba yayi cikin fa’a ya nufi gida…yana zuwa ummi kadai ya iske a Palo tana ganin shigowarsa ta amsa sallamarsa tana juyawa taga khaleesat bata palon dan haka tayi saurin miqewa zata nufi daki…
Cikin sauri yasha gabanta
“Dan nashiga zaki tashi…meyasa kike guduna?ko baki son innason ki ba..gashi inji mum”
Batace dashi komai ba ta karba khaleesat dake tsaya tana kallonsu tasoma fadin
“Sannu da zuwa”
Amsawa yayi da yauwa …kasa ummi tayi da muryarsa tana fadin
“Nagode”
Karbar ledar tayi tasago hanunta ta baya da ledar saboda khaleesat tagani da kyau tayi tunanin shiyasiyo mata…illai kuwa khaleesat taji haushi…
Wucewa irfan yayi ya shige daki afusace khaleesat taji tabi bayansa suna shiga ta shige gabansa ta soma kuka
“Haba irfan Abinda kakeyi baka kyautawa yaza’ayi ace nice matarka kuma baka damu dani ba kadinga nunawa wannan yarinyar kanwata ta baya so fiye dani salon tarainani”
“Ni mijinta ne *Mijin yarinya* ynxu ummi nakeso kin yaudareni khaleesat bayan nasoki kuma idan ledar Dana bata ce ta tsone miki ido umma ce ta bata kije kasamu umman..”
🎀🎈kwance ta iske ummi da sauri ummi ta miqe ta zauna qoqarin tashi ummi ta soma yi kan ta ankare khaleesat ta kai mata daka…
Acewar khaleesat…
“Ni kike kira da karuwa?”
“Eh inba karuwa ba mecece ke?”
“Toh wallahi sena nuna miki irfan nawane kuma kece karuwar”
Hañnu khaleesat ta daga zata mari ummi taji daukar mari a kuncinta…
“Ke harkin isa kizo har dakinta ki mareta?ummi matatace”
Da sauri ummi ta dago ta kallesa..
“Wallahi bamatarka bace nice nan matarka ta sunnah”
“How dea yuh say DAT”
“Yes its d truth I am yuhr only wife irfan”
“Fita a dakinan fita nace”
Fita khaleesat tayi irfan ya zauna a kan gadon yana me dafe kansa…
Ummi ce tafara zancen xuci
“Ynxu kenan irfan ya manta dani ba matarsa bace”
Da sauri ya juyo har seda ya bata tsoro..
“Ummi ummi ke matatace karki damu da zancen khaleesat am sory”
Shiru tayi tana kallonsa hannu yakai ze tabota tayi saurin ja baya tana daga masa kai…miqewa yayi yana ja da baya cike da rashin fahimta…
Ficewa yayi ummi kuwa tasa kuka…taso ace yaya irfan nata ne ita kaidai amma segashi yau wata can tana kiranta da karuwar irfan..
Irfan ko dakinsa ya shige khaleesat na masa mgn beko cemata komai ba ya hau gado yayi kwanciyarsa
“Irfan yanaganka da safe haka aikin fa?”
“Dad zuwa nayi muyi mgn..”
“Innajinka irfan”
“Dad meyasa khaleesat take cewa ita kadaice matata?kuma ummi haka ta nunamin alamun”
Shiru dad yayi kamar karya masa bayani..sedaga bisani yace
“Kaga irfan matsala kuka samu da ummi kasaketa ka auri khaleesat indai kanason ummi kaje Ku sasanta se asake daura musu aure”
Toh irfan yafada cike da fara’arsa yayi wa dad sallama ya nufi gurin aiki..das yaji dadin hakan dan shima bayason zamansu hakanan…
Yana shigowa yaga ummi zaune a palo tana danna wayarta murmushi yayi yasamu wuri ya zauna…
“Ummi”
Da sauri ta dago ta na ganinsa ta miqe zatayi daki ya riqo hanunta…
“Zan sakeki amma ki fadamin meyasa kike guduna”
Kiniyar kwance kanta ta shiga yi yasaketa tayi daki..binta yayi yana shiga ya iske tana kuka zama yayi kusa da ita…
“Ummi kiyi hakuri..innasanki sosai baby..kidena guduna”
Da sauri ta dago ta kallesa bata taba tsammanin zefurta yana sonta ba. Jin tayi shiru yasa ya tsugunna gabanta
“Baby zaki aureni..plxxx”
Dagowa tayi ta tsiresa da ido…hawaye yafara bin kuncinsa…
“Ummi dan Allah kitaimakamin innasanki”
Kuka ta fashe dashi ya rungumota tana fadin
“Kai ka gujeni dik son danake maka”
“Baby am sory am sory baby wallahi nadena”
“Bayan kanada mata ynxu kuma kace kai ba mijin yarinya bane”
Shiii yafada yana dora hanunsa a baki
“Kibar fadan haka nayarda no *MIJIN YARINYA*”
Banko qofa khaleesat tayi tana fadin
“wallahi bazaka aureta salon kama ta rainani wannan yar karamar yarinyar kanwar bayana”
🎀🎈”Ai ba shawararki nake buqata ba ko neman yardarki.. Inkinga zaki iya ki zauna in bazaki iya ba kuma kofa a bude ne..fashewa da kuka khaleesat tayi ta fita daga dakin da gudu..
Juyawa ummi tayi ta basa baya
“Yi hakuri ummi”
“Ni gurin mum zan koma”
“Haba ummi inkika tafi bazanji dadi ba”
Daqyar ya shawo kanta..itako tausayi yake bata sbd memory dinsa da akace ya loose amma badan haka ba bazata yarda ta qara aurensa ba…
*washe gari*
Acewar kawar khaleesat zuby dake mgn daga cikin wayar khaleesat wacce ta kara a kunne..
“Hmm kedai kawats ai no ynxu takaina nakeyi babban matsalata shine irfan yayi loosing din memories dinsa ynxu baya sona aurena sa Alhj Ibrahim kawai yake tunawa sedai yace na yaudaresa seda abbansa ya masa mgn ma yake cin abinci na ynxu tsohuwar matarsa ummi yakeso ya aura na rasa yadda zanyi”
“Kina zaune kina me? Tintini baki fadamin ba?toh innan tafe anjima kadan insha Allah”
“Toh kawata Allah yakaimu sekinzo
Ahaka sukayi sallama..
Zaman jiran zuby khaleesat tayi har misalin karfe 3pm taji an buga qofa cikin sa’a tana fitowa taga ummi zaune a Palo tsaki tayi taje ta bude qofar…
Ganin zuby yasata sakin murmushi…
” my zuby welcome “
Dariya zuby tayi tana fadan
“Shegiyas dik kin rame”
Shigowa zuby tayi suka samu wuri suka zauna..
“Badole in rame ba an hanani sakat ba nida mijina”
“Ai ke kika bari da kin ci uwar mutun kin huta lafiya”
Ummi na zaune ko qalaquss batace dasu ba
gyara kwanciyarta ma tayi tasoma chatting zuby ce qara fadin
“Wai ita wannan idan kinyi baqi bata baki wuri ne?”
“Toh gadaitanan,Ummi ! Ummi!!”
“Wai ya akayi ne?kuncikani da surutunku inna zaman zamana kuma kina wani kwalamin kira kamar zaki karar min da sunana haba”
Acewar ummi,zuby ce ta miqe taho kanta tana fadin
“Iyehhh Allah me iko wannan yar ficiciyar yarinyar ce take mana rashin kunya”
Miqewa zaune tayi tana fadin
“Ahaka irfan din tagani yace yanaso kuma yan baqin ciki sedai su mutu”
Sake baki sukayi sunana kallonta wayartace ta fara ruri tadauka tana fadin
“Kunga irfan ne kusan bani iska hakanan”
Wuce wa tayi tana me amsa wayar takara akunne
“Hello swthrt”
Tana shiga daki tayi Dariya tana fadin
“Kaiii Allah yataimakeni Alarm ya ceceni Dana daku yau wannan kawar tata mekama da horo”
Kwanciyarta tayi akan gado can kuwa zuby tariga tagama fusata..
“Wallahi seda daki yarnan bazata rainani abanxa tasha ba wa’anda suka fita sunmin ban qyalesu ba se ita”
Tafiya zubytasomayi xuwa dakin Ummi da sauri khaleesat ta riqota tana fadin
“Kaiii rufamin asiri aikuwa da zama na ya qare agidanan rufamin asiri”
Tsaki zubytayi tana fadin
“Mstw dallah kings tafiyata dik kin koma matsoraciya *AKAN SO* kinga inna huce nadawo muyi mgn”
Hakuri khaleesat tadinga bata amma inna seda tayi taficewarta daga gidan
Khaleesat kuwa dakin ummi ta shiga
“Abun naki yaisheni ace kawayena ma baki barsu ba “
“Toh khaleesat ya kikeso inyi dakene?kunzauna kuna mgnku bansamuku baki ba inna ruwana daku?”
Tsawa kallonta kawai khaleesat tayi daga bisani ta fice daga dakin…
Akwana atashi ba wuya se shirye shiryen bikin ummi da irfan akeyi khaleesat ko bata da aiki kusan kullun addaikun rana ne batawa irfan kuka daddare
Yaukam Saura sati daya bikin irfan da ummi hankalin khaleesat ya qara tahi..ummi kuwa gun mum ta koma ynxu da zama syyrsu dairan kuwa kwanin ban sha’awa…. zuwa khaleesat tayi tasa mesa zaune yana danna waya
“Irfan dan Allah karka aure ummi”
“Meyasa wai ke bakya gajiya ne..in harkinason zaman lafiyabdole kiyi hkr kizaunabda ummi matsayin yar uwarki”
Kwanciya yayi itako tafashe da kuka mecin rai..tausayi take basa ynxu sosai…ya miqe zaune yana kallonta riqota yayi yasata ajikinsa…
“Khaleesat meyasa kullun kikesawa kanki damuwa ne?idan kika fahimci Ummi bata da matsala zaku zauna lfy idan kika kwantar da hankalinki namiki alkawarin kome kikeso xan miki kisauke girman kai plxx”
“Ke kike nuna hkn kikeso amma zangyara”
Nanfa daqyar ya rarrasheta yasata jikinsa suka kwanta…
Washe gari aka hado lepe mum ce da kawayensu sukaje shida na ummi uku na khaleesat… Aka kawo mata taji dadi khaleesat din sosai…
Haka akayi shagalin biki ganin birgewa khaleesat ta shiga cikin su annata shagali da ita…
Ranar da aka kawo Amarya kuwa sunana nasiha agun mum da dad…
“Anty yau meza’adafa ne?”
Acewar Ummi khaleesat cetayi murmushi tana fadin
“Adafa kouskous ko?”
“Eh anty bari na dafo inna zuwa”
“Toh jeki dora ki dawo mu cigaba da kallon”
“Kiyi hkr kawata wallahi tafiya nayi ne jiya nadawo”
Zama sukayi zuby tana fadin
“Inna makirar yarinyarnan?”
“Wace makira kuma?”
“Ummi mana”
“Habadai ai irfan ya aureta kuma ynxu muna zaman lfy wallahi ba wata matsala”
Bude baki zubytan fadin
“Amma gsky khaleesat kina batamin rai ynxu dik Abin data miki zaki shanye”
“Toh yazanyi ynxu innasamun kulawar irfan kuma ba matsala tsakanina da ummi”
“Dallah ki bar zancenan jibi kisamo kudi agurin irfan ki shirya nakaiki gurin wani malami ya miki aiki irfan yazama naki kekadai se abinda kika ga dama zema ummi ko tabar miki gidan”
Wahe baki khaleesat tayi tana fadin
“Allah kawata kinada wanan kikaqi sani ahanya”
🎀🎈gaida zuby tayi tasamu ta zauna kallon ummi ta kunna musu tsaki zuby tayi tace
“Nidai natafi sekinjini jibin”
“Toh shknan Inna samu zankiraki se inshirya”
Acewar khaleesat ta miqe zata mata rakiya…
“Ummi bari in rakata innazuwa”
Murmushi ummi tayi tare da fadin toh tasama film din false harse khaleesat tadawo..wayar ummi ce ta soma ruri irfan ne tayi murmushi ta dauka…
“Dftn gimbiyata tana lafiya”
“Lafiya kalau nake dftn kaima haka”
“Eh kindai ci abinci ko?”
“A’ah ynxu na dora mana ko zaka dawo ne?”
“A’ah gsky sedai anjima daddare ki fadamin jellof din rice nd beans”
murmushi ummi tayi tace
“Toh Allah yakaimu take care karka bari akallemin kai”..
Dariya sukayi dikkansu…kafin ta katse wayar
Ita kuwa khaleesat can ita da zuby
“Kiyi kokari kasamu kudinan so nake kishana ki wataya se abinda kikace za ayi”
“Allah kawata yau kinsani anishadi sosai wallahi”
Dariya sukayi sukai sallama zuby ta wuce…khaleesat ciki tadawo tazauna kafini tashigo ummi ta kawo musu kouskous din sunaci suna kallo…
*Night*
Zaune suke a Palo Irfan yashigo palon shida abokinsa jameel cike da fara’a suka gaidasa ya zauna daki khaleesat ta shige ummi kuwa kitchen ta nufa ta debo musu abinci ta nufi daki ta basu wuri itama…
Sun jima sunanki hira se wajan karfe 10 tukun na irfan ya tafi rana jameel shaff irfan ya manta da cewar wajan window din ummi suke tsaye itako jin muryarsu yasa ta leqo tana kallon mijin nata tana dariya
“Kaidai ai dabarar nan danayi tayi..badan na hada baki da likitan yace musu nayi losing memory na ba baza adawomin da ummi ba”
Dariya jamil yayi yana fadin
“Shegen kaya amma meyasa ita khaleesat din kace bakasan ka aureta ba”
“Iskanci naga zata kawomin ne shiyasa ai gwara nazama *MIJIN YARINYA* da ta mai dani bansan abinda nake ba ba gashi ynxu ta nutsu ta dena yawo ba”
Dariya sukayi sunata hirarsu dik subutan bakin da irfan yake ummi na jinsu ta window… Hawaye kawai tafarayi har suka gama hirarsu jameel ya tafi irfan ya shigo tana tsaye agurin…
Yana shigowa ya ganta jikin window se a lokacin ya Tina…
Gabadaya jikinsa yayi sanyi tunanin ta inna ze bullo yakeyi…ya matso
” Allah dai yasa ynxu dik kagama tuno abubuwan daka manta na baya?”
“Ummi ki tsaya kisaurareni”.
” Ba abinda zaka fadamin dik naji komai”
Tafada cikin muryar kuka…ruqo hannuwanta ya farayi tana fizgewa..
“Dama basona kakeyi ba ka au reni, saboda matarka bata kula dakai shiyasa ka aureni..meyasa dik San danake ma naka gani Ashe dik yaudarata kakeyi”
Zubewa tayi jikin bango tana kuka sosai zuwa yayi ya rungumota jikinsa
“Innasanki ummi karki min mumunsn fahimta sanda nake miki ne yasa nayi hakan dik dan saboda mum tasa adawomin dake plxx Ummi am sory”
Shige wa tayi jikinsa ta shiga rera masa kukan shagwaba kasa daure kukan nata yayi ya dauketa ya dorata kan gado yasa ajikinsa…
Khaleesat nacan zaune tana jiransa har barci ya dauketa…
Rungume ummi yayi ajikinsa tsam kamar Wanda za akwace masa ita…
Ganin abun nasu yawuce in kwaso lbr yasa na baro dakin…
Washe gari shida kansa yama Ummi wanka ya shirya ta kafini ta koma barci wani sabon shagwabar ta tsuro masa dashi ganin ya shirya ze tafi aiki yasa ta fara masa yan qanqanan kuka daqyar ya rarrasheta ya fice daga dakin..
Yaukam da wuri ya dawo dakin khaleesat yake tagama masa girki tare da taimakon ummi itako khaleesat yau take shirin tmbyr irfan kudu SBD zuwa inda Zuby ta bata labari….
Yau tun 9 irfan ya dawo yana cin abinci yacema khaleesat zeje gurin Ummi yadawo…
🎀🎈Bayan ya zaunane tasoma fadin
“Dama innaso nama mgn”
“Owk innajin ki”
“Dan Allah innadan bukatar kudi ne ko 6k ne innaso xandanje insiyo Abu gobe”
Shiru yayi yafara qoqarin kwanciya yana fadin
“Toh bakomai da safe Kitunamin”
Dadi khaleesat taji Sosai ta masa godiya…
Kwanciya yayi abinsa itama ta kwanta…
Washe gari yadauki 7k ya bata tayi ta masa godiya misalin karfe 2tagama abinda take ta shirya gidansu zuby ta nufa
“Kawata harkinzo”
“Ke tinda ninakeda buqata badole intaho ba..”
Dariya zuby tayi ta shirya suka fice daga…can kwana daki suka nifa da kukan tsintsaye kawai akejiyowa…
Khaleesat kuwa dik ta gama tsorata
“Dan Allah zuby mukoma gida wannan wanne irin wuri nehaka”
“Dallah kika bakin ki kiyi shiru muje inda zamu in aiki yayi kyau ai zakifi kowa bude bakin yin dariya”
Shiru khaleesat tayi sun kusan hour daya suna abu daya suna zuwa suka iskesa zaune se surutai yakeyi kamar wani sabon mahaukaci…
Zama sukayi bece musu komai ba Zuby ta gama zayyano masa komai se yasoma fadin
“Yakukeso ayi da ita?”
Mgnrsa amsawa takeyi agurin sosai..zuby ce ta zunguri khaleesat akan tayi mgn muryar khaleesat narawa tasoma fadin
“Sonake a korata tabar gidan”
Surutai yadinga yi yana yan bude budensa…Se cewa yayi
“Bazata koru ba kota tafi seta dawo gidan”
Kallon juna sukayi ita da zuby
“Toh tafara fadan wani abun”
Yafada..shiru sukayi sai khaleesat tasoma fadin
“Toh asa ya tsaneta nikadai yakeso se abinda na basa ze bata kar komai yazama nawa”
Wata iriyar muguwar dariya bokan yayi yayita bige bigensa yana wani irin ihu daga bisani ya dauko magani a leda ya baqa ya wurga mata harta tsorata..
“Kije zuba masa a abinci…kuma inda yake kwanciya a dakinta kizuba a gefen gadon…da sharadin dik Wanda yaganki abun zedawo kanki…ke ze tsanaaaaaaaa”
Jikin khaleesat ne ya mutu ynxu ya za ayi ta shiga dakin ummi har ta xubama irfan wannan maganin…
Zuby ce ta tabota taba mataalamu akan ta basa kudi…
4k khaleesat ta Ciro ta ajiye masa saman wata kwarya…
Sunata masa godiya suka bar wurin sanda sukayi nisa atafiya khaleesat tasoma fadin
“Ai wannan wahalace zuby ya za ayi ace dik uwar tafiyarnan da mukaci ace idan aka ganni ze dawo kaina”
“Toh kema banda shirita yaxa ayi ki bari aganki”
Sai misalin karfe 5 duka isa gidan su zuby
“Kinga nikam bazan shiga gidan ba wucewa zanyi”
“Toh shknan nikuma mezansamu?”
“Kaiii zuby bakya gajiya”
“Ke irin wannan aikin cemiki akai annayinsa kyau..qyala qawancanan agefe ki miqon kawai”
Dubu daya khaleesat ta miwo zuby ta nuna batasan da wannan zance ba dubu daya ta mata kadan
Daqyar khaleesat tararrashi zuby takarba dubu dayan..
Khaleesat bata isa gida ba se bayan magrib ta iske Ummi zaune…
“Sannu da dawowa anty”
“Yauwa tace ta shige dakinta”
Hakan yabama ummi mamaki amma seta mata uziri ko gajiya ce tasata hakan…
Bayan su yi sallah ne khaleesat ta shiga kitchen tana girgiki ummi kuwa tana daki tana karatu gabadaya jinta takeyi ba dadi..
Bayan khaleesat tagama girki ne tafara tunanin taya zata zuba maganin adakin ummi…
Dakinta nufa tayi sallama ta shiga ummi dakekaratun Qur’ani axaune ta ta amsa sallamar…
Juyawa Ummi tayi ta cigaba da karatun itako khaleesat ta daki icon ummi ta hau zuba wannan magani…
“Kiyi hkr dazu nadawo agajiyene shiyasa”
“Ahhh bakomai anty wallahi ya hanya”
“Lafiya lau dama cewa nayi bari nazo na baki haquri”
Murmushi ummi tayi tana fadin bakomai khaleesat ta miqe tafice daga dakin
Misalin karfe goma irfan ya dawo dakin ummi ya shiga ya yi wanka khaleesat ko kafin ya fitoh tariga ta zuba masa maganin a abinci tare da ummi suka fitoh suka zuba masa abincin khaleesat tayi…
*Morning*
Irfan ka tashi yau ko karatu bakayi ba ka kwanta da asbah gashi har 9 ya wuce tsaki yadingayi ya miqe zaune..
“Wai meyasa ke nakyaso kiga ba huta ne mtsw”!!
Yana fadan hakanya miqe ta shige toilet itako ta rakasa da ido cike da mamaki
Miqewa tayi ta je ta hada masa abun karyawa ta ajiye a dinning..
Bayan tagama shiryawa ya fitoh haka ma khaleesat.. Be kula ummi ba yanufi hanyar fita
“Ya irfan bakaci abincin ba”
“Cemiki akayi yinwa nakeji?khaleesat natafi”
“Toh adawo lfy” acewar khaleesat ummi ce ta miqe ta bisa waje
“Baby haka zaka tafi bakaci komai ba”
Cik ya tsaya kafin ya juyo…
“Idan kinamin mgn bata min rai kikeyi banason inbata mik kidinga nisa dani”
Yana fadan haka ya shige motarsa khaleesat kuwa tana leqensu ta window tana dariya daga bisani ta shige dakinta…ummi kuwa tajima agurin har sanda ya fita daga gidan tukun tadawo ciki..
Dakinta ta shige tana gyara wa.khaleesat kuwa zuby takira
“Hello kawata albishirinki aiki yafara kyau”
“Haba dai”
Acewar zuby daga can…khaleesat ta amsa da
“Wallahi kuwa kinga yau ko girkinta bazauna yaci ba”
Dariya suka dingayi ummidake daki tana jiyo dariyar khaleesat amma badai tajin me take fada…
Irfan da fara’arsa ya nufo gidaya but in yazo yaga ya ummi take daga waya yayi ze kirata se kuma yafasa..
Dadi taji ynxu yasauko danhk hankalinta ya kwanta…
Shigowa yayi da motarsa ya paka da sallamarsa ya shiga wajan khaleesat yafara shiga ya bata abinda yasiyo musu…a tunanin ta zama zeyi sejitayi yace
“Natafi gun ummi seda safe”
“Gun ummi kuma”
“Eh da wani abun ne?”
A atace masa dan haka yayi gaba abinda cike da farinciki ya tura qofar dakin amma se ya tsinci kansa da wani irin bacin rai zama yayi gefen gado daga qasa ta fitoh daga toilet
“Sannu da zuwa baby”
Ko A bece mata ba ta nufi inda ta ajiye kulolin abincin zuba masa tayi..
Yana son mata mgn amma sedai ransa dayakeji yana baci sosai…
“Harka qoshi?baka ci bafa”
Shiru yayi bece komai ba…
Ya miqe yaje ya watsa ruwa ya fitoh..qoqarin kwanciya ya soma yi
“Meyasa bakasan kulani innata mgn kamin shiru”
Kwanciyarsa yayi bece komai ba…
Gabansa ta nufa tana fadin
“Meyasa mekane?
🎀🎈 Washe gari da bayan yadawo daga Sallah ya yana shigowa ya iske ummi tana karatu kallonsa kawai tayi ta cigaba toilet ya shiga yay I wanka kan ya fitoh ta gama karatun..
“Inna kwana”
Lafiya kawai yace mata ya cigaba da sa kayan sa…
“Ya irfan yau innaso naje gurin mum”
Shiru yayi bece mata komai ba
Har ya gama shirin sa ya fitoh tana biye dashi abaya dakin khaleesat ta shiga ya mata sallama suka fitoh …
“Ya irfan baka cemin komai ba”
Ransa bace ya juyo yana fadin
“Kina damuna..na hanaki zuwa ne?”
Yana fadan hk jikinta yayi sanyi yana juyawa sukayi ido hudu da khaleesat wacce abin yai mata dadi seya juya ya kalli ummi ya sassauta murya yana fadin
“Kije cikin sip akwai kudi ki dauka Wanda ze isheki”
Yana fadan hk yayi juyawarsa ya fice…Ummi ma daki ta nufa tana share hawayen SBD taji zafin abinda yayi mata khaleesat ko daki ta koma ta kira zuby..
“Kedai bari qawata abin ai yamin dadi yau amma kinsan meya ban mamaki?”
“Ah ah saikin fada” zuby ta fada daga can
“Daya mata tsawar ya kalleni sekuma ya sassauta murya ya mata mgn”
“Toh SBD kina wurinne me yiyuwa bakaso kigani ne karki masa mgn akai shiyasa”
*1week later*
“Ya irfan kasan meye?kwana biyu ka canja Wallahi ko laifi na maka”
Nan ma be qara ce mata komai ba se runtse ido yake bayason ya bata mata Raine shiyasa yake qin kula ta..matsowa tayi kusa dashi
“Ya irfan kanajina fa”
Wuf yayi ya miqe har seda ita kan ta ta tsorata cafkota yayi ya jijigata tafara ihu khaleesat na Palo ta jiyo ihun taji dadin hakan sosai tanata murmushi can kuwa irfan kasa yayi da murya da kagansa kasan baya jindadi yanayin dayake ciki shikansa..
“Ummi meyasa bazaki gane bane? Banason bata miki shiyasa nake nesa dake meyasa ba zaki kyaleni ba”
Hawayen ta farayi ta bude baki zatayi magana taji amai ya taho mata miqewa tayi ta shige toilet nagudu tana amai…
Shiru yayi yabi bayanta da ido..hartagama ta fitoh yanan zaune inda tabar sa..
Tsawa yayi kallonsa harya bude baki ita kanta ta lura da hkn yanason mata mgn amma ya miqe ya fice…
“Khaleesat kishirya kije ki cewa ummi inna jiranku amota”
Yana fadan hakan ya fice murmushi tayi azatonta wani abun yayi mata ..
Gyalenta ta fara dauko wa kafin ta nufi dakin ummi
“Ummi ki fitoh irfan yace zamuje asibiti”
Toh ummi tace khaleesat ta fice suna fita khaleesat ta shiga gidan gaba ummi na baya…
Ta madubi yake kallonta data dago seya kaifa fuskarsa..
Suna isa irfan na gaba ummi kuwa tafiya kawai take suna kawowa tsakiyar asibitin ta zube qasa…
Irfan da sauri yayi kanta khaleesat kuwa setayi tsaye sororo taimakon gaggawa aka bata …
Bayan wasu mintina likita ya kira irfan ..khaleesat na biye dashi suka shiga office din likita ya sanar masa da ummi nadauke da juna biyu…
Firgigit khaleesat ta miqe hankalinta atashe kallo daya irfan ya mata ya maida hankalinsa ga likitan…
Fitowa tayi daga office din kamar Mara hankali tana fadin…
“Nashiga uku”
Fitowa tayi tasoma kiran zuby
🎀🎈 fitowa tayi tasoma kiran zuby
“Hello kawata na shiga uku yaukam kashina ya bushe..Ummi ta qwace gidan”
“Ke ki nutsu kimin bayani meke faruwa”
Acewar zuby
Kuka Khaleesat takeyi sosai
“Ummi cike ne da ita”
“Ciki kuma?maganin beyi bane”
“Zuby bansani ba bansani ba Wallahi ki taimaka min”
“Ki kwantar da hankalinki gobe zanzo gidan”
Toh kawai khaleesat tace ta fice ta nufi gida gabadaya tarasa meke mata dadi…
Shiko irfan gaba daya farin ciki ya rufesa amma koda ya shiga dakin da ummi takese kuma yadda yakeji da ya dawo masa…
Kuka ya farayi ya juya ya kira mum
“Mum muna asibiti kizo”
Kasa shiga dakin yayi ya zauna daga waje yana ganin mum yayi murmushi …
“Yana ganka anan?inna Ummi da khaleesat din”
“Ummi dai tana ciki”
“Toh ya akai naganka anan?”
“Mum idan naje kusa da Ummi innason mata magana amma se innajin haushinta..Mum innason ummi bansan meyasa hkn yake faruwa ba
Shiru mum tayi ita kanta abun ya daure mata kai…
“Inna zuwa wanne daki take?”
Nuna mata dakin da take yayi ta shiga kallo daya tama ummi ta gane ciki ne da ita sosai mum tayi murna tana fadin Alhmdulh
Bayan farfadowar Ummi ne aka sallamota daga asibitin amma ko A bata hada su mum dik tana ankare dasu ko ummi ta masa mgn baya amsawa..
Dan haka mum ta basa addu’o’i ya dingayi ba musu ya karba..
*Night*
Bayan sun koma gida ne mum tace kar aqara barin ummi tayi aikin komai acewar mum ma me aiki zata kawo mata…khaleesat kuwa ihu ne kawai bazata yi ba sedai qoqarin washe baki da takeyi
Yau irfan dakin khaleesat ze kwana..amma dakin ummi ya fara shiga ya isketa zaune se ciye ciye takeyi..kallonta ya tsaya yi daga bisani ya shiga da sallama murmushi tayi ta amsa ta gyra masa wuri ya zauna..
Kallon ta kawai yakeyi
“Ya irfan naga kadaure fuska kamar baka murna”
Cikinta kawai ya shafa tayi murmushi ta dora hanunta saman nasa a hankali ya janye hanunsa ya miqe ta bisa da ido har yakai qofa seya tsaya cik..yayi Jim kadan kamar bazece komai ba sekuma ya soma fadin
“Inna murna ummi nafiki murna”
Yana fadan haka ya fice daga dakin sebayan ya fita ne ya tsinci kansa day min murmushi..
Dakin khaleesat ya shiga ya isketa zaune ta zuba uban tagumi..sallamarsa biyu amma bata ansa ba zuwa yayi ya ta bata setayi firgigit ta dago kai..
“ohh harka shigo”
Qoqarin cire agogon hanunsa yakeyi yana fadin
“Tunanin me kikeyi?”
Bakomai tace ta miqe tanufi bayansa ta rungumosa..
“Baby meyasa baka damu dani ba se ummi kodan tanada ciki ni bani dashi”
Cirota yayi daga jikinsa ya juyo yana kallonta yana fadin
“Kishi kike dan ummi zata rigaki haihuwa?ai ummi ita ma fara aura”
“Toh ammafa ummi yarinya ce fa”
“Bkm in hakane nazama *MIJIN YARINYA*_kuma dazu meyasa kika bar asibitin?”
Janye jikinta tayi daga riqon da yayi mata tayi ta juya tana kame kame
“Kawai jinayi kaina yana ciwo lokacin shiyasa”
Murmushi kawai yayi ya shige toilet yana shige wa ta juyo ta share hawayen fuskarta tana fadin…
“Ummi bata taba rigana haihuwa ba”
Abincin sa taje tadauko masa kan tadawo ta tarar ya fitoh zaune ta iske sa yana danna wayarsa ajiye wa tayi tazauna…
“Khaleesat inna cikin farinciki yau sosai”
“Name fa baby”
“Ummi zata Haifa mana yaromana ykmt kema kiyi farinciki”
Hade rai tayi bata ce komai ba yayita surutunsa…ba abinda yakeyi banda kular da ita itakam…bayan ya gama ne yayi alwallah yayi sallah yai addu’ar da mum ta basa kafin ya kwanta
Gidan irfan ne cike da jama’ah yan uwan ummi ma gombe dik sun hallara annata murna sosai innah kuwa hard a guzirin kayan jarirai…sai bayan isha’i mum ta aiko da Mota su innah suka koma gidan ta kasancewar can xasu kwana khaleesat ko dik abinda ake tana daki…
Bayan watsewar baqin ne khaleesat ta kira zuby
“Kince zakizo najiki shiru abin yafara isata”
“Kiyi hkr yar uwa abubuwan suka riqeni amma xuwa jibi zanzo”
“Toh ykmt kizo saboda asan yanda za ayi da cikinan tinkafin ya girma”
Toh zuby tace sukayi sallama..khaleesat bakin shigowar irfan atunaninta gunta zefara shigowa senaga yayi dakin ummi …
Ummi kuwa cikin murna na gaidasa bayan ya butane ta soma dago kayan dasu inna suka kawo mata na jirirai dikkansu sunata dariya cikin nishadi…
🎀🎈khaleesat ko najiyosu sama sama kamar ta nurse..kuka kawai yasa hard a shesheqa tana fadin
“Ummi I wil surely make yuhr life miserable like a hell..irfan nawane nikadai”😫😫😫
Dakin khaleesat ya nufo ya iske tayi bacci toilet ya shiga yayi wanka yayi alwala kafin ya fitoh yayi sallah tare da yin addu’ar da mum ta basa…
Seda ya tabbatar ya gama tukun ya yada khaleesat daga bacin..
” kikawomin abincin”
Miqewa tayi I don’t a a kumbure ko sannu da zuwa batayi masa ba ta fice daga dakin shiko ko ajikinsa yayi zamansa tana shigowa ta dire masa agabansa ta koma kan gado..
Binta yayi da kallo daga bisani ya soma fadin
“Meyasameki?”
Kamar dama jira take ta miqe daga kwanciyar da take tana kuka..
“Irfan yaufa kwana na ne yakamata ace dakina kafara zuwa amma tin 9 ka shigo gidanan amma se ynxu 12 kake shigowa nan”
“Khaleesat kinsafa ummi tana buqatar kula wata ynxu ko ykmt nadinga bata lokacina”
Cikin muryar kuka take fadin
“Kai komai ummi komai ummi da anyi magana ummi ummi”
Hayewa tayi can kan gadon ta juya tana kuka tana yan qananan surutan da shikansa banajin me take cewa..murmushi kawai yayi cigaba din abincinsa…
Bayan ya gama ne ya dan huta na yan mintina dan abincin abu jikinsa kafin daga bisani ya hau kan gadon ya kwanta shima..bacci ne ya dauketa khaleesat ko miqewa tayi dan dik tsawon lokacin data dauka tana jira taji ya bata hakuri ne jin ya kwanta tajira shiru yasa ta miqe ta leqasa ganin yayi bacci yasata yin wani sabon kukan…
*Morning*
Da safe yana gama shiryawa ya fitoh dinning ya zauna ya karya khaleesat na zaune gefensa ya miqe yana fadin
“Innazuwa”
Ra kasa tayi da ido dan tasan karshen zancen dakin ummi zashi illai can ya shiga…
Tsaye ya iske Ummi jikin madubi taci kwalliya Riga da wando wandon iya gwiwa ya tsaya mata …cikinta kawai take kallo ajikin madubin jin anturo qofa yasa ta juyo tana ganin shine ta juya ta cigaba da kallon cikin nata tana shafa wa…
“Ya fara girma ne”
Yafada tare da qarasa wa inda take ya rungumota shima yana shafa cikin…
“Ehmana baka gani ba”
Dariya sukayi khaleesat dake jiyosu tayi tsaki..ummi ce ta kali agogo
“Laaa kayi latti muje inrakaka”
“Toh ki shirya anjima dayamma zamu fita”
“Toh ummi tace Allah yakaimu”
Yana gaba ummi na biye dashi har suka fita sallama kawai yama khaleesat yafice…ranta bace ta nufi daki ta kira zuby
“Zuby maganin ya karye”
“Kamanya ya karye”
Kuka tafashe dashi
“Zuby karki so kig wani ikon Allah kama daga jiya zuwa yau dasafe”
“To ki karba kudi yau agurinsa inyazo ki kirani inya karba kinaji ko?”
🎀🎈 Eh khaleesat tace sukayi sallama da zuby
Bayan fitar irfan ne su innah sukazo ma ummi sallama zasu koma gombe sekuma ta haihu…
Kuka sosai ummi take har tasa inna sharar hawaye itama…
Yau ummi ce da girki dan haka tun bayan magrib ta dora abinci…jellof din shinkafa da wake ne ta yana cabbage da carrot qanana tayilemon ginger drink…
Bayan ta gama ne taje tayi wanka tayi sallar isha’i kwanciya tayi jiran irfan bacci ya dauketa…
Misalin karfe goma da rabi ya shigo gidan da sallamarsa ya shigo dakin ummi ya fara shiga ganin tana barci yasa yayi murmushi ya nufi dakin khaleesat…
Dasallamarsa ya shiga ya isketa zaune tana karatun novel…
Murmushi tayi shima hakan yayi
“Sannu da zuwa”
Ta fada ta miqe ta kawo masa ruwan sha
“Yau ba rigima ne?”
Yafada yana kallonta..tabe baki tayi tana fadin
“Hmmm oho”
Dariya ta basa ya miqe tsaye yana fadin
“Bari naje zan kwanta bacci nakeji yau nagaji”
Miqewa yayi itama ta miqe
“Dan Allah innaso naje kasuwane akwai kayan Dana nakeso na siya”
Shiru yayi yana kallonta..
“Inna 7k din Dana baki kince zaki siya abu dasu kuma baki nunamin ba..ynxu kuma kina buqatar qari”
“Dan Allah kabani innaso xan siya abune dashi”
“Sekin nunamin abinda kika siya da 7k din tukunna sena baki wani”
Harya kai qofa seta soma fadin
“Amma ai da ummi ce jikinka na rawa zaka bata kamar Wanda aka asirce”
Juyo wa yayi ya kalleta..
“Ummi bata tmbyt kudi dik da tafi ki buqatar su a ynxu kuma zancen asircewa ai ita ba hk take ba qila ke kika tsargu da kanki”
Tunani take ta toh mexata nuna masa a zuwan shi ta siya da kudin…miqewa tayitafa duba dip dinta sabon less dinta dabata dinka ba ta fiddo murmushin mugunta tayi ta zauna tana kallon less din atanta tana fadin..
“Irfan tinda kuka sani kuka wallahi sena saka kuka”
Dariya tayi ta koma ta kwanta shi kuwa can yana shiga ya iske ta tashi kallonta yayi yana murmushi yasamu wuri ya zauna..
Sannu da zuwa ta fada ta miqe ta nufi toilet ta dauraye fuskarta shima wanka taje yayi kafin ya zauna ya ci abinci..
“Kiyi hkr nace zan dawo zamu fita aiki yamin yawa”.
” bakomai ya irfan”
“Toh gobe insha Allah zan muje”.
Murmushi tayi tana fadin Allah yakaimu..
Washe gari da safe irfan ya fitoh bayan sunyi sallama irfan taje dakin khaleesat.. Bayan sungaisa yace ze tafi..
” yauwa ga abinda na siya da kace in nuna ma”..
“Ki shirya anjima zan fita daku kome zaku siya seku siya”
“Bazan baki ba inkinga dama karki je”
Yana fadan haka ya fice ta biyosa tana fadin
“Wallahi ni seka bani”..
Ganin ummi yasa yasa tayi tsaki tayi juyawarta daki..
Tana shiga ta jiyo wayarta na ringing tana dubawa taga zuby…
“Hmm zuby kedai kibari narasa gane kan irfan yadda ki kasan maganinan da sukayi kaina yadawo haka naji”
“Ke kikayi sake qila bakiyisa da kyau yadda ya kamata ba”
“A’ah ni ynxu ma yaqi bani kudin”
“Toh ki daki yadda zakiji karki wuce yau da gobe dan tafiya zanyi”
Toh khaleesat tace ta katse wayar…
Misalin karfe 12 irfan ya shigo gidan dakin ummi ta shiga yace ta shirya kafin yake gun khaleesat zaune yasaneta
“Khaleesat ki shirya muje”
Miqewa tayi tana fadin
“Nifa bazani ba wallahi “
Shiru yayi ya tsaya kallonta daga bisani yaga bama shida lokacinta ya dauka 6k ya miqamata…
🎀🎈ficew yayi Daga dakin shikuma…
Yana fita ya tarar ummi tagama shiryawa fita sukayi shopping complex na yara suka nufa …
Itako suna fita takira zuby akan tana zuwa…ta fice itama Daga gidan..
Zuby ta fada tare da daukan gyalenta…fita sukayi daga gidan..
Gurin wani mallamin daban zuby takaisu wannan karon suna zuwa zasu fara magana ya dajatar dasu yana fadin
“Nasan meke tafe daku ya isa”
Shiru khaleesat tayi ta kalli zuby zuby kuwa murmushi kawai tayi
“Me kikeso ayi da cikin?”
“Azubar dashi kawai”
Yan bugs bugebugensa yayi Daga bisani ya soma fadin
“Ciki nan baze zubu ba”
Kallon juna sukayi ita da zuby khaleesat kuwa qara shiga tayi cikin wani tashin hankalin…
“Ynxu ya za ayi?”
Acewar khaleesat zuby ce ta soma fadin..
“Tinda so kike ki rigata haihuwa meze hana a bar cikin ya zauna acikinta shi be zube ba kuma ita bata haihu ba..kuma koda ance asibitin gab da haihuwarta se ace babu da acikinta har se kin rigata haihuwa”
Dadi sosai khaleesat taji tace da zuby ayi hakan..kamar yadda suka umarta mallamin ya musu…
“Gashi wannan zaki zuba mata a ruwan wanka…wannan kuma Ku samata a abinci wannan layar kuma ki birne ta a wajan dakinta ta baya”
Gaban khaleesat yafadi sosai ynxu ta inna zata fara wannan aikin dayasata?karba tayi suka basa 4k tare da yi musu sharadin muddin aka ganta to kanta ze dawo…
Sosai khaleesat ta tsorata wannan lamari ji take kamar ta hakura amma zuciyarta na mugunta na qara tunzirata…
Kanyarsu ta barin gurin bokan ne khaleesat tafara amai dariya zuby tayi tana fadin
“Toh ai shikenan abun nema yasamu semi wuce muje asibiti”
Ba musu sukaje suna zuwa aka dubata nan aka tabbatar mata da tana da juna biyu
Dadi taji sosai kamar ta Goya zuby ta mata alkawarin 5k muddin maganin yayi aiki..
Gida taje ko zuciyarta fes…su irfan kuwa Daga gurin shopping dinan gidan mum suka tafi..
Sewajan 9 suka dawo gida..suna dawowa ummi ta shige daki shiko dakin khaleesat ya shiga yana shiga ta taso ta rungumesa tana dariya mamaki yayi sosai
“Albishirin me aka miki yau kuma?
” baby innada ciki”
Ta fada kan drawer ta nufa tadauko takardar ta basa karba yayi ya bude ya karanta…
Dadi yaji sosai ya Daga hannu sama yana godewa Allah dayasa dikka matansa zasu Haifa masa yara…
Khaleesat ko bataaji dadi sosai ba sbd a tunanin ta farin cikin da ze nuna yafi hakan…
Shi kuwa zama yayi murna fall afuskarsa amma itako dik hakan be mata…
“Toh ni yaushe zaka kafini shopping din baby”
“Ba inda zan kaika ynxu senaga dama sbd ke kikace baza kije ba”
Hau shine ya cikata ta miqe ta haye kan gado ta kwanta…
“Tafi nono fari”
Ficewa yayi ta fashe da kuka sosai dakin ummi ya nufa .yana zuwa cikin murna yafada mata…
Murna itama tayi sosai tace sedai araba kayan data siyo biyu abama khaleesat rabi..
*2days later*
Tindaga ranar ummi bata yarda khaleesat tayi aikin komai sedai girki inkwanantane..amma khaleesat ko Idonta ya rufe burinta kawai tasamu tayi abinda bokan ya bata…
Girki ummi ta dora musu suna zaune a Palo…
“Anty bari kiga na sa ruwan kwanka”
. toh kawai khaleesat tace amma cikin ranta taji dadi…ummi na shiga daki khaleesat ma ta shige nata daki maganin ta dauko tana fitowa taji motsin ummi a kitchen allamun tana duba girkin..
🎀🎈Tana shiga ta nufi toilet tinda ruwan dake cikin bucket ta zuba ma maganin fitowa tayi har taso qofar dakin sukai cinkaro da ummi kame kame khaleesat tafarayi tana fadin
“Dama nazo in duba ko kinshiga wannan ne innaso na kwanta ne”
Kallonta ummi tayi allamun rashin gsky a tattare da ita seta sona fadin
“A a kijira Na fitoh ynxu ai abincin ya dahu”
“Toh khaleesat tace ta fitoh itakuma ummi ta shige”
Ajiyar zuciya khaleesat tayi tasamu wuri ta zauna ita kuwa ummi tana shiga ta taka garin maganin a qasan dakin daidai inda khaleesat ta tsaya tsugunnawa tayi ta diba maganin baqi dashi…
“Toh me hakan ke nufi khaleesat me tashigo yi dakina?”
Tattare gun ummi tayi ta Tara a wuri daya akan idan irfan ya dawo ta nuna masa…
Toilet ta shiga kallon ruwan wannan nata tayi dik da ba ta ga komai acikinsa ba amma ta kwarar ta dauraye bokatin ta qara dinan wani ruwan ..
Murmushin mugunta tayi tanan zaune tajiyo allamun ummi ta fitoh daga wanka dan haka ta miqe ta nufi kitchen abincin tasamu su a try amma setabi gefe daya na abincin ta barbada masa maganin da akace tasa ma ummi a abinci..
Murmushi tayi tazo ta ajiye abincin ganin ummi bata fitoh ba
Komawa tayi kitchen din dan ta dibo musu ruwa ita kuma ummi ta fitoh harta zauna taji gabadaya ynxu bata yarda da khaleesat ba dan haka seta juya gaban ya koma na khaleesat…
Itakuwa khaleesat batare da tayi tunani biyu ba tazauna suka fara cin abinci ummi kasa cin na kirki tayi amma khaleesat kuwa secemata take…
“Kici ummi kici”
Tinda ummi taga hakan jikinta yayi sanyi dan khaleesat bata taba suna cin abinci ba tadinga cemata taci taci ba…
Tashi ummi tayi tace ta qoshi ta shige daki akan zata kwanta…
Khaleesat kuwa dariyar mugunta ta dingayi har ummi nadan jiyo ta kadan kasan dan hk jikin ummi tahau rawa nan danan zazzabi ya rufeta dan tagama tsorata da lamarin khaleesat addu’o’i kawai takeyi har bacci ya dauketa…
Khaleesat kuwa tana shiga daki taji cikinta ya murda sosai kwanciya tayi tare da riqe cikin sanda ta danyi yan mintina ahaka kafin ya sake kuma kwata kwata zuciyarta bata bata wani abun ba…
Yau kwanan khaleesat ne dan haka ta dora masu abinci tuwo ne tayi ummi kuwa nacan kwance xaxxabin ya rufeta…
” innazuwa asibiti zan kaita acewar irfan”..
Sanda taji Qarar tada motar su tukunna tayi dariya me isarta hard a tafi ta kira zuby…
“Kedai yar uwa ta ki bari kawai aikinan yayi kyau ba kadan ba kinsan ynxu haka suntafi asibiti”
“Haba dan Allah”
Zuby ta fada daga can..kwashe wa khaleesat tayi da dariya tana fadin
Can kuwa irfan yana zuwa aka duba khaleesat zuka bata magani…
Gida suka dawo khaleesat ko cikin barci tayi firgigit ta miqe ta tuna da yakamata ta birne layarnan tinda nasan kamar daga sama tajiyo dariyar irfan da ummi tsaki tayi…
🎀🎈Tsaki tayi tare da jin haushin narcin daya dauketa
Kuma ynxu idan taje gurin zasuji qarar tona ramin da zatayi..
Can ko Ummi na kwance kan qafar irfan kallonsa tayi se wannan garin da khaleesat ta zubar bata sani ba…
Miqewa tayi ta nufi bakin qofar ya biyota diba yayi yace toh a inna kika same shi?
“Nima bansani ba”
“To waya shigo dakin naki yau?”
Shiru tayi tana tunanin kodai ta fada masa khaleesat ce muryarsa ta jiyo yana fadin
“Kinyi shiru ko akwai wanda shiga ne?”
“A’ah babu shiyasa abun yaban mamaki”
Shiru yayi shima daga bisani ya Daga ta ta koma kan gado paka ya dauko ya kwashe yakai ya zubar…
“Kidinga Addua kinji dear kar kidinga yin sake da Addua kinji”
*2days later*
Khaleesat ce ta rasa meke matadadi burinta ta birne layarnan kawai..bayan magrib ummi na kwance a daki ahankali khaleesat ta murda qofar dakin ummi kwance taga ummi allamun barci take murmushi khaleesat tayi ta nufi waje wajan window din ummi ta nufa tahau tona rami dik abinda take ummi najinta miqewa ummi tayi zata fita palo setaji motsi awajan window
Wajan window din ta nufa tana leqawa taga khaleesat mamaki tayi amma har khaleesat tagama abinda takeyi ummi na tsaye…
khaleesat na gamawa ta tattaka gurin ta nufi cikin gida ummi kuwa tunani ta farayi toh me khaleesat ta birne agurin…
Bayan ta tabbatar khaleesat ta shiga dakinta seta fita ta zakayi daidai gurin taje ta tone da mamaki taga kaya..Leda ta hango a gefe ta dauka ta qulle layar aciki megadin gidan takira tana fadin
“Gashi dan Allah gobe dasafe ka qona”.
Ciki ta koma khaleesat kuwa na daki tana murna….
Kamar yadda irfan ya saba kullun 10:30 irfan ya shigo dakin ummi ya nufa kamar kullun shigarsa keda wuya suka jiyo ihun khaleesat..
“Wayyoh na shiga uku Ku taimaka min cikina”.
Rikicewa sukayi gaba dayansu ummi ta taimaka ma irfan aka daga khaleesat suka kwana amma irfan gun mumy yakai Ummi..
Washe gari misalin qarfe 11 nasafe likita ya nemi irfan bayan su mum da dad da ummi sun hallara a asibitin suka nufi office din likita.
“Likita ya matata da Dana”
“Matarka tasamu sauqi sosai amma base on binciken da mukayi babu komai acikinta”…
“Toh gsky bansan dalili ba ashawarce amata maganin gida”
“Magunguna likita yabama irfan”
Godiya suka masa washe gari aka sallamesu daga asibiti…
🎀🎈Kwance khaleesat take irfan yazo ya riqe mata hannu tana magana sama sama
“Irfan meyasami dana”
“Kiyi hkr khaleesat ance ba komai acikinki”
“wayyoh Allah nashiga uku ni khaleesat najawa kaina”
Rarrashinta ya shiga yi yana bata hakuri…mum ma da ummi hakuri suka adinga bata…
Kwance take tana kuka bayan kowa yabar dakinta ta miqe zaune daqyar ta kira zuby tana kuka
“Zuby na shiga uku yadawo kaina ance bakomai acikina ynxu yazanyi zuby kitaimakeni”
“Khaleesat kema akwai wawanci to anjima zanje gurin mutumin muje yadda za ayi”
“Yauwa khaleesat kitaimakeni dan Allah”
“Bakomai kikwantar da hankalinki”
Toh khaleesat tace suka katse wayar…ummi ce tashigo dauke da abinci
“Ummi ke yakamata wannan abin yasama meyasa ze dawo kaina”
Kuka taqara fashewa dashi…
Irfan yauma da yadawo wani asibitin suka qara tafiya abu daya aka fada musu wannan karon likitan cewa yayi agwada maganin Hausa ko zeyi…
Kuka khaleesat takeyi kawai…abinci daqyar takeji tafiya ma daqyar take yinsa kullun batada aiki se kuka tun irfan na lallashinta har ya gaji shima…
Mum kuwa ynxu ta hana irfan kai khaleesat asibiti acewar ta asarar kudinsa kawai yakeyi itakadai tasan abinda yasameta…
*1 week later*
“Wai zuby najiki shiru har yau sati daya innarasa dan jikina shknan fa kitaimakeni”
“Khaleesat haushi kika bani ne tinda naje gurinsa yace wannan layar da kika birne anganki ne shiyasa kuma da alamar maganin ba daidai kikayi kamar yadda aka ce miki ba”
Cikin rawar murya tasoma fadin
“Zuby ynxu ya za ayi”
Jin anturo qofa yasa tayi saurin kashe wayar irfan ne…
“Keda wa kike waya baki da lfy kadena stressing kanki”
Alamun rashin gsky ne a tattare da ita dik tabi ta rikice
“Da zuby ce kawai muje gaisawa”
Hmm kawai yace yana fadin
“Nidai natafi aiki”
“Irfan ynxu kafiso inta zama ahaka”
“Khaleesat ya kikeso nayi karshe sedai inkaiki gurin malamai amiki sauka dan kina gani abun yafi qarfin asibiti”
“Wallahi ni inna zargin kardai matar kace takes on kama min Dana”
Tsaki yayi yana fadin..
“Watoh rashin lafiyar be barki hakanan ba seya hada miki da hauka ko?”
Kuka tafarayi tana fadin
“Dama dole kacemin hauka tinda abun ba ummi ya sama ba dole”
Ganin inya biye mata ma baya lokacinsa yake ya juya yayi ficewarsa yana fadin
“Allah dai ya shirye ki”
Sallama yama ummi ya fice ummi ko jin khaleesat na kuka ta shiga dakin
“Anty meyasameki ko akwai abinda kikeso ne?”
“Dallah fitamin adaki munafuka kawai muguwa kin kamamin da tsabar baqin ciki”
Tsaya wa kallonta ummi tayi daga bisani tace
“Anty lafiyarki lau kuwa so sena kira mum”
“Kece Mara lafiya…nace kece Mara lafiyar muguwa kawai kin kacemin irfan ynxu zaki kashe min da”
“Anty me kike nufi ne”
“Uwarki nake nufi kinji nace uwarki nake nufi”
Wannan karon ummi ta fusata da zagin da khaleesat ta mata tinda uwarta dai tana kabari batasan me ake ba…ummi hawayen tafarayi afusace tana fadin
“Wallahi badai uwata sedai taki…mutun bashida tafiya baze iya zama yayi Addua ya roqi Allah yabasa lafiya ba se zagi da masifa..mstw”
Ummi nafadan haka tafice tana fita khaleesat tafara daga murya tana fadin
“Wallahi senayi maganinki semi bargidanan kijira nasamu lafiya kigani makira kawai”
Zuby ta kuma kira tana fadin
“Ynxu zuby yaza ayi?”
“Kije ki tono wannan layar gobe zan zo na karba ze miki wani abun dashi semi warke”
💋💋
🎀🎈Misalin karfe Tara irfan ya dawo wannan karon gun khaleesat ya shiga kwanciya tayi tayi kamar barci takeyi..
Tsaya wa yayi yana kallonta na yan mintina kafin ya juya ya tafi dakin ummi sanda khaleesat ta tabbatar ya shiga dakin ummi kafin ta miqe daqyar take tafiya tasamu ta bude kofar palon…
Wajan data birne layar ta nufa daqyar ta duqa kasa..tana jiyo muryarsu irfan tona ramin khaleesat tafarayi kamar mahaukaciya tadinga tone tone amma babu allamar layar…
Nashiga uku ta fara fada acikin zuci…sanda ta totone gurin batagani har goma da rabi takai awaje tana abu daya…
Miqewa tayi tadawo ciki jikinta na rawa ta kira zuby
“Hello zuby nashiga uku banga layar ba”
“Cabdijan bari zankiraki gobe”
Kashe wayar zuby tayi khaleesat tabi wayar da kallo
“Yau naga ta kaina”
“Mtsw ni bazaki jamin abu yahada hardani ba…tincan kinsan bazaki iya ba kikace aje”
Kashe khaleesat aqallah tama zuby kira yakai 6 msd call amma bata dauka ba..
Kuka kawai khaleesat tafara tana fadin..
“Me zuby take nufi ne haka zata barni da wanan cikin nashugesu”
Kuka tadingayi..irfan yagama shirinsa ya fitoh yana fadin
“Khaleesat ki shirya anjima mallan zezo ya miki Addua”
Miqewa tayi da sauri tana fadin
“Banaso Wallahi”
“Bakyaso kuma?”
Eh ta fada sbd tsoro take kar aje asirinta ya Tonu kame kame ta farayi tana qoqarin kwanciya ta juya baya..
Ganin haka yasa ya table baki yayi juyawarsa…
Yaukam da irfan ya tashi daga aiki gurin mum ya nufa..
“Ya masu jiki”
Acewar mum..
“Lafiya suna samun sauqi..khaleesat ce nakeson nakawo mallami ya mata addu’a amma taqi yarda”
“Hmm ka qyaleta ciwon baya damuntane shiyasa take hakan in taji wahala dakanta zatai magana”
Toh kawai irfan yace badan yaso ba SBD lafiyar abinda ke cikinta sallama yama mum ya tafi gida…
Zaune ya iske khaleesat a Palo tayi jugum ..sallama yayi amma bata ansa ba ba abinda takeyi banda zubar hawaye.. Zuwa yayi ya ta bata firgigit ta juyo tana kallonsa..
Kadawo? Tafada tare da miqewa
“Eh tunanin me kike haka..”
Kamar dama jira take tafashe da kuka cikin daga murya tafara mgn..ummi kuwa fitowa tayi taga meke faruwa tsawa tayi bakin qofar dakin suka hada ido da irfan..
“Mezesani tinani in ba halin danake ciki ba SBD baka sona shiyasa baka damu da halin danake ciki ba…da wannan makirar matar takace da ynxu hankalinka ya tashi..”
Riqeta yayi yana fadin
“Banda mata makira sedai in ke kika koma makirar”
Qara fashewa tayi da kuka tana fadin..
“Akanwaccan karuwar matar taka kake cemin makira”
“Karki qara cewa matata karuwa”
Bata qarasa ba taji ya dauketa da mari…cikin sauri ummi tazo ta riqeta ta baya tana fadin
“Ya irfan bata da lafiya fa”
Fizgewa khaleesat tayi har sanda ummi ta tsorata tana fadin
“Muguwa kawai kece baki da lafiya badai ni ba”
Kallon ummi irfan yayi idonsa yayi jaaa yacema Ummi ta shige daki…
“Ke kuma kinci sa’ar abinda ke cikinki Wallahi da senayi maganinki”
Tafiya yasoma yi tafara tafi tana fadin tsawa abakinta tana fadin
“Wuuuuuuuuu andaiji kunya kazo ka kayi abinda zakayi mana”
Tsaki yayi ya shige dakin ummi…yana shige wa ta zauna dabas akan kura tana kuka tafa fadin
Cikin sauri irfan da ummi suka fitoh dakinta suka nufa suka isketa kwance se ihu take
“Lafiya khaleesat meyasameki?”
“Irfan cikina wayyoh na shiga uku”
Ummi ce tayi qoqarin qarasa wa kusa da ita…tsawa ta dakama ummi
“Karki kuskura kizo kusa dani..salon ki kashemin Dana..wayyoh irfan nashegesu”
Tsaki yayi ya nufi inda take yana rarrashinta ahankali taji ra dadin datakeji ya rage dan hk irfan ya fitoh ya nufi dakin ummi wacce tinda khaleesat ta mata ihu ta fitoh daga dakin…
Kwance ya iske ummi ya qarasa kusa da ita
“Babyna ya akayi ne?”
“Bakomai me ka gani?”
Ta fada tare da miqewa zaune rungumota yayi yana shafa cikinta yana fadin
“Ya babyna hope suna lafiya”
“Eh karka manta fa yakamata yau naje asibiti”..
” Owk toh kishirya se muje tare ko”
Asibitin suka tafi aka dubata scanning aka mata aka tabbatar musu da yan biyu ne acikinta..
Murna suka dingayi gidan mum tace ya ajiye ta inzeje gida seya dauketa…
Ba musu yakai ta can kafin ya wuce gurin aiki…khaleesat kuwa dake can kiran zuby tayi har 4msd cal na biyar dinne ta dauka…
“Hello khaleesat ya akayi ne”
“Kanbu ya qayine fa ki kacemin?”
“Toh mezancemiki kinriga kin kwafsa abu yadawo kanki toh nikuma naso yahau kai cab badani ba”
” zuby kije kice masa nafasa nafasa Wallahi na hakura”
Kwashewa da dariya zuby tayi tana fadin
“Cemiki akayi nijahilace irin ki?”
“Zuby dan girman Allah kitaimakeni zuby”
Katse wayar zuby tayi tana tsaki kuka khaleesat takeyi sosai hanunta na rawa tafara kiran zuby mad call uku ta mata sena hudu ta dauka
“Khaleesat kina damuna fa zaki qararmin da cajin waya fa”
Mamaki ne ya cika khaleesat da kallaman da zuby tayi..
“Zuby nikie fadawa haka iye zuby”
“Toh kindameni ne ko baki gane ba”
Kuka khaleesat takeyi sosai da sosai tana fada
“Amma zuby Allah ya isa tsakanina dake bazan taba yafemiki ba zuby kin cuceni sai Allah yasakamin”
Tsaki zuby tayi tana fadin
“Kanki akeji”
Kashe wayar tayi khaleesat ta qara kira wannan karon jin wayar tayi akashe..ihu tayi tana fadin
” Khaleesat meyafaru jikin ne?”
Acewar irfan..itako ba abinda take fada illah
“Wayyoh zuby ta kashe ni ta cuceni”
Shiru sukayi ummi ce tafara tunowa da qawartace zuby seta kalli irfan tana fadin
“Ya irfan zuby fa kawarta ce”
Shiru yaya ya tsaya yana kallon khaleesat din
“Mekike nufi da hakan”
“Irfan kayafemin Wallahi Sharrin zuby ne Dana shedan”
“Kamarya me kike nufi “
“Bakomai kawai kayafemin Wallahi nayi nadama irfan”
Tsaki yayi yadau wayarsa ya kira likita.. Itako se fadi take
“Zuby kin cuceni wayyoh nashiga uku irfan kayafemin”
Cikin yan mintina likitan ya ido idanun khaleesat sunyi manya tsabar kuka…
“Dan Allah ka mata allurar bacci”
Cewar irfan ga likitan..ba musu likitan ya dura allurar tana gani tafara ihu tana fadin
“Wayyyohhh zuby..irfan ze kashe wayyoh”
Tsaki irfan yayi har yafara gajiya da hau kanta dan haka ya nufi inda take ta ya rirriqeta ummi ma ta riqe qafafuwanta…
“Gsky kunema mata magani tin kafin abun yazaman mata matsala”
Acewar likita…amsawa da toh irfan yayi yama likitan godiya kafin ya rakasa ya fita…
Komawa yayi gurin ummi ya isketa zaune adaki…
“Baby ya akayi ne?”
“Ya irfan kawai akai anty khaleesat gida iyayenta zasufi nema mata magani fiye da mu anan”
Shiru yayi daga bisani yace
“Toh bari gobe insha Allah zanje in nemi shawarar mum muji yadda za ayi”
Amsawa tayi da toh…
Washe gari da safe irfan yau ba inda zeje dakin khaleesat suka shiga dubata..ga mamaki sukaga cikin ya qara kumbura gashi tayi baqi qafafuwanta da hanunta ma haka…
Riqesa ummi tayi gam tare da rufe ido gam juyawa yayi suka fitoh
“Jeki daki bari naje nadawo”
Kuka ummi tafara tana fadin
“Wallahi bazan zauna ba kaga ni gidan mum ba zani”
Dariya ta basa sosai ya tsaya kallonta…
“Zaki fara damuna kenanko”
Acewar zuby…kuka khaleesat tafarayi tana fadin
“Zuby jikina jikina zuby yayi baqi”
“Cab Ashe ke kikaci Wanda aka baki kisa a abinci kenan..dan ranar Dana koma yacemin idan har kinci na abincin toh jikin ki baqi zeyi”
“Zuby ki taimaka min zuby Wallahi inna cikin wani hali”
“Khaleesat gsky zan fada miki ba abinda zan iya miki sedai kawai dau wannan a matsayin qadararki”
Kuka khaleesat tafarayi tana fadin
“Zuby inna zaman zamana da mijina da matarsa kikazo kika huremin kunna ynxu kuma kin gujeni”
“Toh yazanyi dake daukarki zanyi na Goya haba “..
” Amma zuby Allah ya tsine miki”…
Dariya zuby tayi tana fadin
“Ya tsine mana dai tare”
Kuka khaleesat tafarayi taba fadin
“Allah ya isa zuby kin cuceni kin sani ga halaka”
Tsaki zuby tayi ta kashe wayar abunta ta kulle wayar ma..
Kuka khaleesat ta shiga yi tana warwargaza kayan dakinta shigowarsu irfan ne yasa ta tsaya da sauri ta nufosa tana fadin
“Irfan kayafemin kaji kayafemin”
Kaucewa yayi yana fadin
🎀🎈Kaucewa yayi yana fadin
“Kar ki tabani”
Dososo ta tsaya tana kallonsa da mamaki..
“Irfan guduna kakeyi?”
“Khaleesat me kikeso na miki nace miki zan kawo malami amiki addu’a kinqi to ya kikeso na amiki? Jiba yanda jikin ki yake dawowa”
Durqucewa tayi qasa tana kuka mum ce ta soma fadin
“Khaleesat tashi ki kwanta ki huta kibar kukan hknan Allah yabaki lfy”
Miqewa khaleesat tayi tana juyowa tana kallon irfan Wanda ya sadda kansa qasa gaba daya ransa ya baci…
Kwanciya tayi ba dadewa barci ya dauketa fitowa Palo sukayi mum tace yakira iyayenta ykmt Susan halin da take ciki..ba musu irfan ya dau wayarsa..
Mahaifiyar ta ya kira bugu biyu ta amsa
Sallama yayi ta amsa yagaishe tana fadin
“Ya iyalin naka inji dai lfy”
“Lafiya amma khaleesat kam bata da lafiya shiyasa nace bari na kiraki na fadamiki”
“Subhannallah toh insha Allah zamuzo ynxu nida Abban nata”
Toh ya amsa dashi yana fadin se kunzo..kallon mum yayi yana fadin
“Sunce wai sunanan zuwa”
Amsawa da toh mum tayi …ummi ce ta shigo palon dauke da juice ta bama mum da irfan zama tayi itama..
Khaleesat ko nacan kwance tana mafarki me cike da ban tsoro dai dai shigowar iyayenta cikin palon ne sukaji ta kuma ihu yayindata farka daga bacci tana kiran sunan irin tana fadin wayyoh nashiga uku..
*{Subhannallah ynxu kiduba inba gushewar imani ba amma ace mutun yayi mummunan amafarki amma ya tashi yana ihu yana fadin ya shiga uku..mtsw Allah yasa mufi qarfin zuciyoyinmu}*
Cikin sauri suka nufi inda take suna shiga suka isketa zauna…
“Wayyoh irfan kayafemin irfan”
Kusa da ita suka qarasa umma tana fadin
“Khaleesat meyasameki haka jibi yanda kika koma”
“Umma Wallahi balaifina bane zuby ce umma kicewa irfan ya yafemin”
“Me zubyn tayi?”
Acewar umma..mum ce ta soma fadin
“Ki nutsu kiyi magana”
Ido hudu sukai da ummi nama tasoma fadin
“Ummi ki gafarceni Wallahi Sharron zuby ne kayafemin Wallahi nayi nadama”
Acewar ummi..irfan ne yasoma fadin
“Khaleesat meke faruwa ne?”
Fashewa tayi da kuka ummanta tana fadin
“Khaleesat kiyi mgn mana meyafaru”
“Umma umma Wallahi zubyce “
“Toh me zubyn tayi ne wai?”
Acewar mum wacce iya ynxu khaleesat din ta fara qular da ita
“Umma zuby ce tazo bayan irfan ya auri Ummi zuby tazo tace muje wurin wani boka”
Salati kowa yafarayi irfan kuwa dafe kai yayi ummi ko jikin bango ta jingina gabadaya jikinta ya mutu tare da dafe cikinta..
Kuka sosai khaleesat take tana fadin
“Ummi kiyafemin Wallahi nayi nadama”
Kukan ta cigaba da yi daga baya tacigaba da fadin
“Da mukaje aka bani magani nazubama irfan a abinci da gurin kwanciyarsa a dakin ummi..”
Tana fadan haka ummi da irfan suka kalli junansu .. Khaleesat cikin muryar kuka ta cigaba da fadin
“Dana zuba maganin beyi aiki ba nafadama zuby shine da ummi tasamu ciki shine muka koma sani gurin nida zuby”
Salati umma tayi tana tafi tason girgiza khaleesat tana fadin
“Khaleesat mekika koma ne kashe mata dan kikayi ko ya akai?”
Shiru tayi tana kuka umma ta qara da
“Kiyi magana”
“Damu kaje yabani magani nasama ummi a ruwan ruwan wanka kuma nasa mata a abinci kuma na birne laya abayan dakinta SBD cikinta ya kumbura in naje asibiti ace bakomai acikinta Wanda abun yadawo kaina ynxu”
Qarashe magana tayi tana kuka..Salatin ummi da sukaji yasa suka juyo suka maida duban su ga ummi tana salati..da sauri suka qarasa gunta riqeta mum da irfan sukayi har sukai bakin qofa irfan ya juyo yana fadin
“Ki tabbatar ki tattara komai naki kibarmin gidana”
Kuka khaleesat ta qara fashewa dashi tana fadin
“Wayyoh irfan kayafemin Wallahi nayi nadama”
Umma ce tasoma fadin
“Khaleesat kin kin cuci kanki khaleesat ..Abban khaleesat bakace komai ba”
“Mezance toh?kin kazo auren ki na farko ynxu kinzo zaki kashe ma wani auren zaki kashe yayan mutane gashi kin kashe aurenki mekika koma?”
Kuka tafara yi tana fadin…
“Abba umma kayafemin kayafemin”
*🎀🎈MIJIN YARINYA*🎈🎀
🎀🎈”Abba Umma kuyafemin kuyafemin”
Taqarashe maganarcikin kuka..
“Ynxu yakikeso muyi khaleesat? Nida mahaifinki daqyar muke samun abinda zamu ci balle ynxu kikoma gida. Dawanne kudin zamu neman miki magani”
Kuka khaleesat takeyi..umma ko kallon Abba tayi tana fadin
Muryarsa na rawa yake fadin
“Kinban kunya khaleesat dik tarbiyyar Dana baki ace rana daya rana daya kawar banza ta ruguzamin komai kinban kunya”
“Wayyoh Abba Abba kayafemin”
Shiko ficewa yayi daga dakin umma tana fadin
“Inna zakaje kazo musan yadda zamuyi da ita”
Ficewarsa yayi ya tari napep zuwa babban asibiti dan yasan baze wuce can ne su irfan suka tafi kai ummi ba”
Daga nesa ya hango irfan naqarin shiga asibitin sauka yayi ya bada kudin kafin ya kalli asibitin ajiyar zuciya yayi yanufi ciki…
Yana zuwa wajan ward din mata ya nufa yatarar dasu irfan a tsaye allamun an shiga da ummi ciki…
Irfan naganinsa ya sunkiyar da kansa qasa..abba ko qarasa wa yayi inda irfan yake mum na tsaye tana kallonsu…hada hannu wa biyu abba yayi yana fadin
“Dannan kataimaka min karka saki khaleesat nasan bata ma adalci ba..Wallahi Wallahi ba halinta bane sharin kawayene…irfan kaduba halin danake ciki abinda zanci ma gagarar mu yakeyi balle muqaru da ita kuma kudin da za aneman mata magani bandashi dan Allah**”
Riqe hanunsa irfan yayi yana hawaye yana fadin
“Kayi hakuri Abba naso khaleesat amma tayi abinda ko wa alama baze iya yafewa ba…Abba khaleesat taso ta kashemin ‘yayana koda yake ma ta kashe guda daya na jikinta”
Ajiyar zuciya irfan yayi ya cigaba da fadin
“Bazan iya zama da wacce take shirka ba..Shirka fa tayi Abba..Khaleesat tafi karfi na..”
Yana fadan haka ya juya ya bar gurin mum qarasowa gun Abba tayi tana fadin
“Kayi hakuri kawai shi zefi kurungumi kaddara itama zatadau darasi kuma na gaba ma zasu dauka masuyi sudena..Allah kuma ya bata lafiya..”
Fiddo 3k mum tayi ta basa kafin itama ta juya…hawaye kawai Abba yakeyi ya juya ya koma gida zama yayi dabas yarasa meke masa dadi…
Yanan zaune yajiyo sallamar Umma
“Seki shigo ai kizo mu zauna”
Yajin haka yayi tsaki wani hawayen yasake zubo masa…
Can kuwa Irfan fitowa likitan yayi cike da fara
“Congrat matarka ta sauka lafiya”
Cikin sauri mum tasoma fadin
“Me aka samu?”
“Baby boy and girl”
Alhmdulh suka dinga fada suna murna irfan kuwa hawayene kawai kebin kuncinsa…
Bayan Asu lokuta irfan da mum suka shiga ganin ummi da jariranta Dad ma shigowa yayi aka dingamurna nanfa aka kira su innah aka fada musu kowa murna…
Kwananta daya a asibiti aka sallamesu gida suna zuwa suka iske baqi daga gombe se kuda ake Anna murna…innace ta karba macen tana fadin..
“kaiii Wannan kama take dani”
Wutace tafara cin labulen dakin kan kace me dakin Yakama da wuta..qaurin datajiyasa ta fitoh tanafa ihu tana Neman ta inna zata fita..
Daqyar ta fita amma ta qone a gefen fuskarta sanda aka balla qofar dakin ta tukunna aka samu aka fita da ita.
Ba abinda ta tsira dashi daga dakin nata karshe ma suma tayi mutanesukai ca akanta…
Khaleesat kuwa Abba zuwa yayi tadauko mallami aka mata addu’o’i daqyar aka samu cikin ya sauka.
Amma daga qarshe cikin nata zubewa yayi..kuka tadingayi.ba zagin da ba tasha agun su umma ba taci kuka ta godewa Allah…
Can kuwa irfan ranar suna anyi taro sosai yara sunci junansu *(taci sunan mahaifiyar ummi inda suke kiran ta da (mumy)* *shima yaci sunan dad amma suna kiransa da (dady)*
Kowa yayi murna sosai da sosai…
Zuby ce tafe ta lullube fuskarta inda ta qone tafe take kamar muna fuka tana zancen zuci
“Dole inje in roqi khaleesat ta yafemin nasan alhakinta ne ke bina”
“Haba aidama qawaye basuyi shiyasaidan zamuyi qawaye mudinga sanin dawa zamuyi”
Wucewa sukayi suna mgn zuby tashare hawaye tana fadin
“Nikaina nasan bankyautawa khaleesat ba”
Karasawa tayi ta iske khaleesat se qoqarin huta wutar itace takeyi
“Khaleesat nice zuby”
Da sauri khaleesat ta dago..zuby ta bude fuskarta gabadaya gefe daya ta qone..khaleesat kuwa dik tayi baqi tarame se dabbaran baqinan da har ynxu be bar jikinta ba
“Khaleesat da kayafemin nasan Alhakinki ne ke nuna”
Takalmi khaleesat ta cire ta jefi zuby
“Allah ya isa tsakanina daki..ki kalla yadda na koma dik ta dalilinki ..qosan nake siyarwa dashi nake ci da gidanmu wataran daqyar nake samu Anna siya wasu ma in sukacisedai su zagen sugudu kin cuceni kin rabi da mijina iyayena kuma ynxu suncanjamin mutane qyamata suke nayi danasanin sanin ki nida qawaye har a bada..”
Taqarasa maganarta tana kuka..
“Kibar nan gurin tin kafin na qara qonaki da man gyada”
Can kuwa irfan cikin nishadi yake wasa da yaran sa ummi na zaune tana kallonsa…juyawa yayi yace
“Albishirinki”
Goro tace tana murmushi..
“Kishirya inkika yaye su mumy zakuje aikin hajj da mum insha Allah”
Dikka dikka nan na kawo qarshen litafinan dftn kun nishadan tu kuma kun fadakantu..masu hali irin na khaleesat se akiyaye adena..Allah yasa mufi qarfin zuciyoyinmu ..