MISBAH BOOK 2 CHAPTER 10 BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH BOOK 2 CHAPTER 10 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Anan Deeni ya dinga taimaka mata da wasu ayyukan kasancewar sa likita, duk da kwarewar sa da karatun sa bai kai nata ba zama da ita yau da gobe yasa ya fara sabawa da koyon aiki sosai, daga dalibi ya bige da (practicing) da (trainning).
Bahijja takan yi mamakin kokari da nuna kwarewa na Deeni gashi da saurin fahimtar aiki, tabbas da ya jima yana aiki da karo karatu da ba karamin taimako zai yi ba.
A kwana a tashi Deeni ya warware shakuwa da sabo yana karuwa tsakanin sa da Bahijja, sukan wuni tare a asibiti suna aiki tare.

Sai dai har yanzu Deeni bai taba fada mata damuwar sa ba wanda ke cinsa, abinda iyayensa da Farida suka masa ya kasa mantawa da wannan cin amanar, haka kullum gudun haduwa da su yake, gudun mmaganar su yake ko jin labarin su. Wanda Bahijja kuma ta dage sai ya fuskanci abinya wuce ya huta, sai dai duk Kokarinta ya kauce.
Bai taba tambayar ta tarihinta ba, haka bai taba fada mata nasa ba, a haka suke zaune, haka nan har yanzu bai fasa binciko labarin MISBAH ba.
Wata safiya Bahijja da Deeni bayan sunyi aiki sun gama da marasa lafiya, suna zaune a (free time) dinsu, Bahijja ta kalle shi. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Deeni, me yasa ka ke gudun mahaifin ka? Me yasa ba zaka fuskanci gaskiya ba da abinda ya faru? Abinda ya faru ya wuce, kayi hakuri ka yafewa dan uwanka, wannan kaddara ce, bashi da laifi. Farida ta ci gaba a rayuwa, tana rayuwarta da mijinta da yaranta, me yasa zaka yi ta kuntatawa

kanka?”Idanunsa ne suka kada suka yi ja, ranshi ya mummunan baci, duk da haka bata fasa maganar ba.
“Deeni (you have to let go of your past) ba zai yiwu ka rike su a zuciya ba kana wahalar da kanka, (please) ka yafe musu”. Nan kuwa taga ya haukace mata yana zazzaga mata bala’i.
“Bazan yafe ba, saboda me zan yafe? In ma na yafe musu kina jin zan iya manta abinda suka min in zauna lafiya da su? Ko na yafe musu ba ni ba su, bana son jin maganar su a rayuwata,
na tsane su, zan iya kisa idan na gansu gabana”. Ta kalle shi cikin fuskar damuwa ta tsiyaya masa ruwa mai sanyi a (cup) ta mika masa, ta ce.
“(Please) Deeni, zauna”. Ya zauna amma bai karbi ruwan ba.
“Saurare ni Deeni, in har ka dauke wannan zafin a ranka ba zaka iya yafe musu ba, ko tsana ne ko so ne ka sake shi a ranka, ka fidda shi a zuciyar ka akansu. Ganin su ko maganar su dole ne, dan uwanka ne uwa daya uba daya, zumunci dole kayi, Allah Ne Ya ce kayi. Gaba ma ba zaka yi da Musulmi dan uwanka ba balle dan uwanka na jini. Www.bankinhausanovels.com.ng
Farida kuwa akwai lokacin da kyakkyawar
dangantaka ta hada ku, yanzu kuwa matar yayanka ce, dole ka yarda da wannan. Mahaifin ka kuwa in kayi fada da shi baka
da riba, duk kai zaka sha wuya kayi ta wahalar da kanka.
Kayi hakuri Deeni, Allah Zai baka ladan hakurin da kayi, Ya kuma baka sakamako mai
kyau duniya da lahira”. Tana maganar kamar zata zubar masa da hawaye.”Kamar kani kake a gareni, ba zan so
ganin kanina cikin wannan halin ba”. Tsura mata ido yayi yana kallonta, maganarta na ratsa shi, haka nan ya dinga jin maganganunta na masa tasiri a zuciyar sa, yaji zuciyar sa ta sauka, tayi sanyi.
Ya dauki ruwan sanyin yasha, ya kalleta ya mata murmushi tare da mika mata (tissue). “Gashi, share hawayen da ke shirin zubo
miki, kar su zubo in miki tsiya nan gaba”. Murmushi tayi ta amsa, “Deeni ba zaka canja ba, tashi yau kaine (best student) koyarwar da na maka ya shiga kwakwalwar ka da zuciyar ka, don haka yau da kai za muje (outing)”.
Ya yi dariya, “Yau ta ina rana ta fito Abokiyata Doctor Bahijja zata fita dani yawo?”. Murmushi tayi bata kula shi ba, taje ta
dauko mota ya shiga suka fita. Kai tsaye suka wuce asibitin gwamnati na garin suka dinga bi tana nuna masa marasa lafiya, wasu gasu nan kwance cikin azabar ciwo ba lafiyawasu ga ciwo ba kudin magani, wasu na son yin ibada da sauran ayyuka ba lafiya. Abin tausayi kala-kala da ya kara sa jikin Deeni mutuwa, daga nan suka wuce sauran asibiti na masu kudi su kuma ga kudin ga komai amma lafiya da saukin Allah Bai nufa ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Daga nan suka zarce gidan marayu, marasa galihu, masu neman taimako basu da kowa ba su da komai sai Allah, sai abinda gwamnati taga dama ta san musu, suna watse basu da mai tallafa musu, ba uwa, ba uba da za su lallashe su, basu da wanda suka damu da su da rayuwar su. Anan Deeni ya ga abin tausayi, sai da ya zubar da kwalla.
A mota duk jikinsa ya yi sanyi, Bahijja ta kalle shi ta ce
“Yaya bakin cikin ka da dacin ranka yake da na wadannan bayin Allah? Ba ka ganin ni’imar da Allah Ya maka, kana da lafiya da karfinka da gatanka da iyayen da suka damu da kai.
Anya baka ganin matsayin iyaye ya kai suyi mana yadda suke so ko da bata mana rai ne suna da hakki? Deeni rayuwar nan tayi kadan mu tsaya muna bata lokacin mu akan wani ɓacin rai ko tsana, gaba ko wata kiyayya.
Ka godewa Allah da ni’imomin da Ya maka, in Ya jarrabe ka sai kayi kokarin ka ci jarrabawar. Ka yarda da kaddara, ka saki rankakayi hakuri Allah Yana tare da masu hakuri”.
Ya yi murmushi idonsa jawur, hawaye ya gangaro masa, ya ce
“Na gode Bahijja, tabbas kin cika abokiya tagarí, likitan da tasan hakkin (patient) dinta, sannan ke mutuniyar kirki ce, Allah Ya miki  sakayya da abinda kika min. A yau kin sa naji wani kunci da nauyi ya bar zuciyata, duk wani fishi da kiyayya da nake ji a raina ya tafi.
Tabbas nayi nadamar bata lokacina da nayi, sai dai inshaa Allah zan gyara gaba, daga. yau, daga yanzun nan Deeni ya zama sabon mutum wanda ba ya rike da kowa a zuciyar sa, ba ya fushi da kowa. Ina jin zuciyata fara, zanyi kokarin gyara rayuwata da tsakanina da iyayena da ‘yan uwana. Www.bankinhausanovels.com.ng
Yau ce rana ta farko da nake ji da son fuskantar yaya Shamsu da Farida ba tare da wani bacin rai ko tsanar su ba, na yarda na amince haka Allah Ya hukunta min. Na gode Bahijja”.. Lumshe ido tayi hawaye na gangara
wanda bata san yaushe suka zo ba, tana fadin.
Alhamdulillah”. A ranta.
Ya tsura mata ido yana kallonta kamar wata bakuwa ko sabon halitta, kaunarta yaji ta shiga ransa, haka yana bata wani girma na musamman.
, “Yau ranar farin ciki ce a garemu da ni da kai, sai godiyar Allah. Yanzu saura guri guda zan kaika, ina fatan zaka ji dadin zuwa wurin”.Me zai hana?” Ya bata amsa.
“Musamman inda ke a wurin”. Murmushi tayi ta girgiza masa kai suka
tafi. Wani tafkeken (farm house) ta kaishi na (Lagos State Gobernment) ba abinda babu ciki, kaji ne, dabbobi ne, shuke-shuke ne, tsuntsaye ne kala-kala a a wurin.
Wani farin ciki da jin dadi ta gani ya bayyana a fuskar sa, ya dinga ratsa cikin gonar yana bin kan dabbobi da tsuntsayen yana ganin shuke-shuken dake wurin sun matukar burge shi, bai san lokacin da ya fara dariya shi daya ba. Irin abinda yake so yaga ya yi, ya kafa a rayuwar sa. Ga bishiyoyi, ga shuke-shuken ‘ya’yan ita ce kala daban-daban.
Lumshe ido yayi ya ware hannun yana. shakar iskar wurin yana jin yana ratsa shi, yana jin wani irin tsananin dadi a ransa irin wandaya jima bai ji ba.
Zuwa tayi gabansa ta harde hannu tana kallon sa tana murmushi, tana jin dadin yadda ta ga tayi sanadin kawo farin ciki a rayuwar sa. Nan ta dinga jin wani irin farin ciki a ranta, wannan dama shi ne burinta a rayuwa ta ga tana sanya dariya da farin ciki a rayuwar mutane, anan take samun nata farin cikin da nutsuwa da jin karfin gwiwar cigaba da rayuwa.
Kamshin turarenta yaji iska ta debo yana sauka kan fuskar sa yana shaka yana ratsa jiki da zuciyar sa, a take yaji wani bakon yanayi yana ziyartar zuciyar sa, yana shiga yana ratsa shi. Soyayyar ta ce mai zafi da sanyi tare da dadin gaske yaji yana shiga yana kama zuciyar sa da dukkan illahirin jikinsa yana ratsa shi tare da saukar masa da wani irin farin ciki da ni’ima mai dadin gaske. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Alhamdulillah, Allah na gode Maka”. Ya bude ido ya ci karo da fuskarta tana masa murmushi, shima ya hau mata murmushin. Suka kyal-kyale da dariya duka, ta ce.”Wow! In kayi dariya kana cikin farin ciki (you really look great)”.
Ya kalleta, “(Thanks to you) Bahijja”.
Ta girgiza kai, “Mun godewa Allah, don haka Mr. Deeni daga yau kasan inda ka kama, kasa gaba, (you belong here)…”. Ta nuna masa gonar
“Ba gidan magani da allura ba, duk da likita kake amma kafi kyau da dacewa da nan gidan gonar, inda farin cikin ka, jin dadinka da (passion) dinka yake, to me zaka jira? Ko ka nemi aiki anan ko kayi kokarin bude naka, duk wanda kake so zaka iya”.
Ya yi dairya, “Na gode da shawarar ki, tabbas a nan (passion) dina yake, (thank you so much) Bahijja. Daga yau din nan na miki alkawarin bude sabon rayuwa, kuma zan fara yin wani abu me ma’ana da rayuwata inshaa Allah.
Amma ina so ki min alkawarin ci gaba da zama (one and only) abokinki, ki zama abokiyata mai ban shawara, yayata kuma mai (guiding) dina”.Tayi murmushi, “Inshaa Allah, Allah Ya
yi mana jagora duka”. “Amin”. Ya amsa tare da fadin.
“Sannan za ki bani littafin nan na MISBAH, kuma za ki zama ABOKIYAR RAYUWATA”.
Ta dalla masa harara, “Abokiyar rayuwar ka kadai? Ka manta har ABOKIYAR MUTUWAR ka ma zan zama”.
Ya yi dariya, “Yauwa my Bahijja”. Wucewa tayi ta fita ta wuce wurin mota, har ta saba da halinsa na zolaya. Ya bita har ya shiga suka tafi yana zolayarta.
Har gida ta kaishi ta ajiye shi, ba yadda bai yi ba ta shiga ta ki, ta ce ya gaida Hajiya. Anan ya karbi number wayarta suka yi sallama. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kai tsaye ya wuce falon mahaifinsa, anan ya same su duka har da Lukman, yana dariya ya gaishe su. Kallo daya zaka masa kasan yana cike da tsantsar farin ciki.Ya zauna a kusa da mahaifinsa tare da kwantar da kansa a cinyar sa.Baba ka yafe min”.
Alhaji Umar ya dinga ji da ganin Deeni kamar mafarki, sai da hawayen farin ciki ya zubo masa bayan shekara takwas zuwa tara Deeni ya fito daga kejin da ya shiga.Mahaifinsa ya
kalle shi, “Deeni Alhamdulillah, tsantsar farin cikin da nake ciki yau ban san iyakarsa ba. Nima ka yafe min”.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE