MISBAH BOOK 2 CHAPTER 12 BY SA’ADATU WAZIRI
Www.bankinhausanovels.com.ng
Mun tsaya
wannan lokaci ba a magana, yayin da ya sako Bahijja gaba da nasa salon tsokanar wanda ya samo.Wata (number) ya samu yana tura mata (text message).
Tana zaune (office) dinta tana karance karancenta taji wayarta tayi kara alamar shigowar sako, ta dauka ta bude. Gabanta ne ya ba da ras!
“MISBAH” shi ne abinda taga an rubuta. Tayi bala’in rudewa saboda duk duniya
mutum daya ne yasan ita ce MISBAH, wanda yanzu ba ya duniyar. Kafin ta gama fita daga wannan rikicin ta
sake ganin an turo mata wani.
“(I know you are my MISBAH) wato nasan ke Misbah na ne”. Mikewa tayi tana sake maimaita sakon a ranta, mamaki ya bayyana karara a fuskarta, nan tayi saurin mai da amsa.
“Waye kai? (Wrong number)”.
Ya bata amsa, “In (wrong number) ne me yasa kika tambaye ni?”
Nan tayi saurin kiran layin amma sai taji a kashe, tayi shiru tana tunani duk wanda ya yi abin nan yasan yadda take tunani, yasan zata kira, to waye ne? Ko da wasa bata taba kawo Deeni a zuciyarta ba, asali ma ta kasa kawo kowa a ranta. Haka tayi aikin wunin da abin a ranta.
Tana sallama gidanta kuwa wani sakon ya shigo
“Allah ya huce gajiyar ki my Misbah”.
Yanzu abin ya fara taba mata rai,
wane dan rainin wayon ne? Tayi tsaki, zata wuce ciki taji muryar sa. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Haba Madam Bahijja, wucewa haka ba kya duba gabanki? Tun dazu na zo ina jiranki, awa na guda na samu Baba Andi itama har ta gaji ta tashi, amma ni ban gaji da jiranki ba. Haba abokiyata”.Bahijja ta harare shi, “Gama cin abinci ka sha ruwa maza kaje gida kayi wanka ka kwanta kayi bacci, kana da aiki gobe”.
Ya yi saurin mikewa ya sha gabanta, “Wa
kike cewa yaro? Wai an fada miki shekara talatin wasa ne?”
“Matsa ni kaban wuri, talatin din har wata kayan gabas ce? Akai na dai talatin ka ba komai bane”.
Har ta soma tafiya ya sake shan gabanta ya harde hannu tare da shan mur, ya kafa mata idanunsa.
“Waye yaro?”
Muryar sa da irin salon kallon da yake mata duk suka rikita ta, ta rasa me yasa take jin shakkar sa. Nan dai ta dake, murya na rawa ta ce
“Way… waye kake zarewa ido? Wa zaka
bawa tsoro? Ni da waye a wurin?” Cikin muryar rada mai kashe jiki ya ce, “Yayata Bahijja da abokiyata Bahijja, ita nake bawa tsoro, kuma naga ta tsorata”.
Gaba daya ta rikice, taji jikinta na ɓari, da kyar la iya daga kafa tayi ciki da sauri. Ya bita da kallon kauna yana murmushi, can ya jiyo muryarta tana cewa. “Ka fita ka kira Baba Audi ta rufe mana kofa, kuma kar ka sake zuwa mana gida da dare”. “Zan zo ko yaushe nake so, kuma in kin isa
ki fito ki fuskance ni ki hana ni”. Nan ta leko kai ta ce, “Na fuskance ka, saime?” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ki kalli cikin ido na in kin isa”. “Naki din”. Ta fada tare da rufe kofar da
karfi, ta sa (key). “Wannan yaro ya zame min damuwa gurin aiki da gida duk bai kyale ni ba, sai na hada shi da Mama”.
Tana cikin wannan mitar wani sako ya sake shigowa. Ki tabbatar kin ci abinci kafin ki kwanta,kar ki kwana da yunwa Misbah na”.
Tsaki tayi ta kashe wayar ta kwanta a wurin ko kayan jikinta bata cire ba ta kwanta a kasa zuciyarta cike da tunani kala-kala musamman na wannan sakonni dake shigo mata.
Can ta kau da tunanin ta soma tunanin yadda Deeni ya saki jiki da ita sosai, tayi zaton in ya warke a yadda ta sanshi da (Attitude) zai fita harkarta ne amma sai wani sabon shakuwa ma da kasa kusanci da ita yayi, lokaci guda sun zame mata kamar ‘yan uwa shi da mahaifansa da ‘yan uwansa. Tabbas da haka kowane mara lafiya yake mata da duk kusan mutancn kasar nan sun zama ‘yan uwanta. Shi dai Deeni daban yake, mutumin kirki ne, mutumin kwarai.
Dariya tayi da ta tuna halayyar sa da yadda yake yawan nasara akanta. “Decni kanina, ina son (sweet nature)dinsa”.
Ta yiwa kanta murmushi, sannan ta sa hannu ta dauko hoton Doctor Mislihu da danta tana kallo tana jin tsananin kewar su.
“Allah Ya jikanka, Ya maka rahama masoyina. Muhammad dana Allah Ya maka Albarka, Ya albarkaci rayuwar ka. Allah Ya kare min kai a duk inda kake”.
Hawaye ne ya dinga gangaro mata, ta tsinci
kanta cikin kewa kamar yadda ta saba kowane
dare, da hakan bacci ya dauke ta. Haka Deeni yasa Bahijja a gaba da tura sako, ya hanata sakat. Wani lokaci sai ya zo gabanta sai ya tura mata, nan da nan zai ga ta rikice tayi wurgi da wayar har ya zamana tana shakkar kunna wayar, a dole take amfani da layin saboda shi ne layin da aka santa da shi, ana iya nemanta. Haushi ya kama ta, ga matsalar me matsa mata da (text) da bata san waye bane, ga Deeni Www.bankinhausanovels.com.ng
kusan sati guda bata ganshi ba, ta masa waya bai
dauka ba, kuma bai kirata ba. Ta kira Mama ta
tabbatar mata lafiyar sa lau, aiki ne ya masa yawa. Tsaki tayi ta kasa kulla komai, can ta yanke hukunci leka shi a maaikatar sa tunda ta shige ta hango shi yana aiki bai zauna ba yana ta faman kaiwa da kawowa da ma’aikatan sa, ya leka wannan fannin ya leka wancan. Can ta ga ya hau (tractor) yana zaga cikin (farm) din nasa, ta sa masa ido tana kallonsa tana murmushi.
Nan take ta tsinci kanta cikin nishadi, tana jin dadin ganinsa haka tana matukar sha’awar halinsa, wasa da dariya da ma’aikatansa gami da mutunta su, haka tsakaninsa da dabbobi, kaji da sauran tsuntsaye tamkar abokan sa.
Harde hannu tayi tana kallonsa kamar t.v. Can ta ga wata yarinya matashiya ta zo tana kiran sa, ganinta yasa ya sauko daga kan (tractor) din ya zo yana kallonta yana dariya suna magana, haka ya bata muhimmanci sosai. Haka kawai taji ranta ya baci, ta kasa ci gaba da jure kallonsu.Harta juya zata tafi sai taji muryar sa, “Har abokiyar tawa zata tafi bamu gaisa ba?”
Ta kau da kai, “Dole ne in gaisa da kai?” “Gaisuwa ba dole bace amma ganina dolene”.
Ta harare shi, “Ta yaya ya zama dole?” “Tabbas nasan tunda har kika zo gidan gonata ba kinzo yawan shan iska bane”.
“Kwarai”. Ta bashi amsa.
“Kaji nazo gani da dabbobi”. “To ai baki gansu ba za ki tafi””Na fasa!”.
Ta fada a hasale tana kallon yarinyar alamar tana tsaye tana jiransa ne.
“Kaje ka ji da bakuwar ka”.Ya yi murmushi, “Kar ki damu
da bakuwa ta, wannan (special) ce ba rabuwa za muyi yanzu ba, gara in gama da ke yanzu in koma”.
“Yanzu ma ka gama dani, sai ka tafi”.
“Bashi yiyuwa kizo ki tafi baki shiga (office) kinsha ruwa ba”.
“Ba shi nazo sha ba”. Ta bashi”Na sani amma za kisha”.
“Dura min zaka yi?” Www.bankinhausanovels.com.ng
“A’a da hannunki”.”Wai me kake ji da shi?” Ta fada a hasale.
“Ban ji da komai sai gidan gona ta da (special) bakuwata”.
Hawaye ta ji ya ciko mata ido, jikinta ya yi sanyi, ta ce
“Deeni sati guda ba waya ba ziyara? Na kira baka dauka bako (special) bakuwar ce ta hana ka?”
Ya yi mata murmushin da ke fadar mata da
gaba, y” Tana maganar saura kiris tayi kuka har ya
lura da hakan ya yi saurin kau da kai baya ya bata
“Ki yi hakuri aiki ne ya min yawa, “Deeni ba zaka iya samun lokaci naba hakan ya bata damar zubar zubar da hawayen. Ya ce, “MEYE DANGANTAKAR MU? Bahijja kina naki duniyar ina tawa, kina farin ciki da aikin ki ina yi da nawa, idan halin haduwa ya zo sai mu hadu. Yanzu ba da bane, dukkan mu muna da abin yi, saboda me zamu dinga bata lokacin mu?”
“Haka ne”. Ta fada murya kasa-kasa. “Kayi hakuri, sai anjima”.
Ta juya jiki ba kwari da kyar take iya daga kafarta.
“Bahijja”.Ya kirata amma bata juyo ba, balle ta tsaya. Ya so ya bita amma sai ya fasa, ya nemi wuri ya zauna ya fada wata duniyar tunaninta, yana jin wani irin shauki mai karfin gaske game da ita yana ratsa shi, idon shi ya kada yayi ja yayin da guguwar kaunarta ta dinga tashi a zuciyar sa.
Bahijja ta koma (office) amma ta kasa zaune da tsaye, gaba daya ta kasa samun nutsuwar yin aiki, dole haka ta tattara ta koma gida. Nan ma tayi kokarin yin rubuce-rubucen ta amma hakan ya gagara.
Duniyar (internet) ta shiga ko zata samu abin bincikawa shima ta kasa, nan ta duako littafi amma karantun ya gagara, ranta ya yi mummunan baci, ta rasa me ke mata dadi
Wannan shi ne lokaci na farko da haka ya faru da ita a tarihin rayuwarta, damuwa da bacin rai komai yawan sa da karfinsa ba ya hanata sukuni har ta kasa yin komai, ta kasa jin dadin komai a rayuwarta. Haka ta kasance har yamma lis ita daya a gida, don Baba Andi ma bata nan ta je gai da ‘yan uwanta zata yi kwana biyu.
Kicin ta shiga amma ta rasa abin yi, ta fito falon. Tana nan tsaye ta hango kanta tsaye a gaban tafkeken madubin dake manne a bangon falon.
A hankali ta matsa tana kallon kanta da yanayin ta, gaba daya ta canja, ta birkice, ba nutsuwa ko kadan a tare da ita.
“Meye haka Bahijja?”Ta tambayi kanta.
“Me ke damun ki? Me ya hana ki sukuni?” But a Can karkashin zuciyarta tasan amsar, amma Www.bankinhausanovels.com.ng
sai ta ki amincewa wanda ita kanta tasan kin amincewa abinda kasan ba gaskiya bane yana matukar wahalar da zuciya tare da ruhi da jikin mutum gaba daya.
Idanunta suka kada suka yi ja, tausayin kanta ya kama ta. A hankali ta sa hannu ta zame gyalen da ta daure kanta dashi, ta baza gashin kanta tana shafa fuskarta da gashin ta, idanunta suka kada suka yi jajawur, ta tsinci kanta cikin tsananin kewa. Sai a wannan lokacin ta tuna cewa ita mace ce fa mai rauni, abinda ta manta da shi duka yau ta tuna, tana bukatar a kula da ita, tana bukatar soyayya, tana bukatar wani ya sota, ya
kula da ita, ya kawo karshen wannan (Emptiness)
din a rayuwarta. Bata ankara ba sai hawaye taji yana zubo mata da karfin gaske, har bakinta na bari. Ta sa
hannu duka biyu ta rufe fuska tana kuka.
Ta sake kallon kanta, “Bahijja ya kike? Ya kamannin ki yake? Ke kyakkyawa ce ko mummuna?”
“Ya kamannina yake ban taba sani ba,
kullum dai mijina ya kan kalle ni ya yabeni da
kyauna, amma ni ban taba tsayawa na kula ba”.
“Shin me yasa nake son kula da kamanni na Www.bankinhausanovels.com.ng
yau? Shin wa zai fada min ya nake? Ya kamannina
suke?” “Bahijja (you are a beautiful woman), wato Bahijja ke kyakkyawar mace ce”. Ta ji muryar Deeni tsaye a bayanta.
Ras! Gabanta ya fadi, tuni tayi wani mugun rudewa, tayi saurin jan gyalen ta lullube, ta kasa ce masa komai. “Gidanki ne amma zan miki tayin gurin
Ta rasa me yasa yake iya (controlling) dinta, bata iya musa mishi ko tayi niyya duk kuwa zafinta da jin ta isa.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG