MISBAH BOOK 2 CHAPTER 13 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

“Shin me yasa nake son kula da kamanni na Www.bankinhausanovels.com.ng
yau? Shin wa zai fada min ya nake? Ya kamannina
suke?” “Bahijja (you are a beautiful woman), wato Bahijja ke kyakkyawar mace ce”. Ta ji muryar Deeni tsaye a bayanta.
Ras! Gabanta ya fadi, tuni tayi wani mugun rudewa, tayi saurin jan gyalen ta lullube, ta kasa ce masa komai. “Gidanki ne amma zan miki tayin gurin
Ta rasa me yasa yake iya (controlling) dinta, bata iya musa mishi ko tayi niyya duk kuwa zafinta da jin ta isa.

Wuri ta nema a kujerar falon ta zauna, ta kau da kai. Ya matsa gabanta ya kafa mata ido, “Bahijja
meye damuwar ki?” “Me yasa zan fada maka damuwata?”
“Hakan na nufin cewa akwai damuwar kenan? Ina son sani”.
Sunkuyar da kai tayi ta kasa cewa komai. “Bahijja”. Ya sake kiran sunanta.
A duk lokacin daya kira sunanta tana jin wani abu me sanyi da dadi yana ratsa ta har cikin zuciya da kwakwalwar ta, yana kashe mata jiki. Lumshe ido tayi tana jin wani abu me karfi
game da shi.
Ya cigaba, “Bahijja ni da ke duk muna cikin kuncin zuciya da shauki, bambancin shi ne kawai naki ya fito nawa kuma na ɓoye shi a zuciya ta, saboda bana son bayyana shi har sai na fahimci meye a zuciyar ki. Kuncin da kika shiga yanzu ni na shige shi
na tsawon lokaci, ni kadai nasan ta yaya na rayu
da wannan shaukin”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Wayar sa ya ciro ya daddanna a gabanta, yayin da tana ji nata wayar ya yi kara. Shi ya dauka ya mika mata, gaba daya jikinta ba kwari maganganunsa kawai ke yawo a jiki da jijiyarta, da


kyar ta iya karba ta bude sakon tana karantawa, ya sa mata ido yana karanta mata abinda sakon ya ce
“I love you MISBAH”. Bugun zuciyarta taji ya tsananta, ya sake
maimaitawa yana kallon cikin idonta.
“Ina sonki MISBAH”.
Nan tayi saurin sunkuyar da kai, gaba daya taji ta rude, ta susuce, bakinta na ɓari, ta rasa abin fadu, ta kasa zaune da tsaye, gashi ya tsareta da ido.
“Na san Abokiya ta ita ce MISBAH na tun ran da na fara zuwa gidan nan, na miki abinda kika koya min ne na kirkirar sabon labarin MISBAH a lokacin, tunda kin kasa karasawa ni zan ci gaba, sauran sai mu karasa tare. Ina fatan za ki bani hadin kai mu karasa tare.
Bahijja ina matukar son ki so na hakika, zan kawo farin ciki rayuwar ki, zan kula da ke, zan shagwaɓa ki, dukkan damuwar ki zai zama nawa, zan dauki nauyin sa ki farin ciki a rayuwa.
Nasan nayi soyayya mai zafi a baya, sai dai ina so ki sani dangantaka ta da kaunata da ke ya jima sosai, tun kafin in san ke wace ce. Na jima da kaunar ki tun kafin in san ke mace ce ko namiji, ta hanyar rubutunci. Bayan haduwata da ke kin taimake ni na manta abinda ya faru baya, wanda soyayyar ki ce Www.bankinhausanovels.com.ng
ta mantar dani. Yanayin rayuwar ki abar so ce, abar koyi ne, sannan kin fahimtar dani abubuwa da yawa da baiwar ki, wanda karo na biyu na sake fadawa sonki ba don komai ba sai wannan halayyar taki wanda ita na jima ina mafarki da burin gani a wurin mata ta.
(How you cope with your loneliness) ya birgeni, ta kara min ganin girmanki, sannan lokaci guda na zo na fahimci MISBAHI na ita ce Bahijja na, sai abin ya min bibbiyu.
Halayyar Misbah da Bahijja shi ya haukata zuciyata da sonta har na manta da na taba wata soyayya a rayuwata, duk abinda MISBAH tayi yana burge ni, yana min dadi, musamman zuciyarta da ɓoye kanta da tayi wa duniya ta watsa ilimin ta da baiwarta ga al’umma suna amfana.
Bayan nan Misbah kina da kyan da ya shiga zuciyata ya zauna, murmushinki, muryar ki mai dadin sauraro, wannan bakin da ke min mita da surutu kullum, wannan idanun masu kashe min jiki  ko kirarki, iya takunki ko nutsuwarki me hana ni sukuni.
Bahijja ina sonki, kina sona?”
Gaba daya ya gama tsuma ta da kalaman sa, ya kashe mata dukkan gabban jikinta, sonshi ne mai tsananin gaske take jin yana huda dukkan ilahirin jikinta. Da kyar ta iya bude baki murya kasa-kasa ta ce.
“Kasan me kake fadi kuwa? Ni na ce maka ina sonka?”
Ya karya kai yana kokarin su hada ido amma taki, ya ce.
“Ba ke kika ce ba, ni naga haka, ni naji a jikina kuma na gani da idona lokacin da kike kishina, lokacin da hankalin ki ya tashi da na daina zuwa wurin ki na daina daukar wayar ki, lokacin da hankalin ki ya tashi da kika ganni da ma’aikaciya ta. Wannan abin shi ne so Bahijja, wannan (feelings) din da muke ji shi ne so. Ko ki so ko ki ki mun riga da mun shirya duniyar mu ni da ke tun tuni, mun tsara rayuwar mu ba tare da mun fahimci haka ba sai yanzu. Ina fada miki gaskiyar da kin fini sani”.
Ta mike da sauri, “Kar ka manta kai kanina ne, karka manta ni yayarka ce, wacce na taba aure har ma na haifi yaro. Kai saurayi ne, dan gata ne, dan asali ne. Kar ka manta ni marianiya ce da bani da asali”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Martabarki da darajar ki ya wuce haka, ke abar so ce Bahijja, ina son sani wanne ne daya kike magana akai, sona ne bakya yi ko kuma wannan bayanan zai hana ki aure na? Uwa ta gari nake nemawa ‘ya’yana na gani a tare da ke, mace saliha nake nema na gani a tare da ke, don haka ki bar wannan zancen.
Ni ne me aurenki ba mutanen duniya ba, ni zan zauna da ke na miki alkawarin soyayyar ki ba zata canja ba, haka zan cigaba da daraja ki da mutunta ki. Ke abu ce mai matukar muhimmanci da daraja a wuri na, kin wuce wasa”.
Bata furta komai ba duk da alamar maganganunsa sun ratsa ta, wucewa tayi (library) dinta hankalinta a tashe ta rasa inda zata sa kanta da soyayyar Deeni da ke azalzalar zuciya da ruhinta. Ta dauko wannan (diary) din da kullum ta tsinci kanta cikin kewa da rudani yake bata kwanciyar hankali in ta bude ta karanta, tayi ta kokarin budewa (page by page) amma ta kasa karanta komai, sai hawaye da ya cika mata idanu. Ba ta gani haka ta dinga bude shi da sauri-sauri.Ya biyota ya sa hannu ya karbi (diary) din. “Duk da abu ne mai muhimmanci a gareki Bahijja ni yana kona min zuciya, ina kishi da shi, kishin gaske da ba na wasa ba nake yi da (diary) dinki.
Kiyi hakuri ina jin wani tashin hankali, Bahijja ina tare da tsoron rasa ki, duk da ina da tabbacin kina sona, ina tsoro kar wannan (diary) din da dalilan da kika kirkiro dazu marasa tushe su sa na rasa ki.
Bahijja da can na yi hakuri amma yanzu ban san ta yaya zan fara wannan hakurin ba, saboda abinda nake ji yanzu da can ban ji rabinsa ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bahijja ni masoyinki ne, me yasa za ki hana ruhinki abinda yake bege? Me yasa za ki cutar da mu ki kuntatawa zuciyar mu?”
Muryarta na rawa tana kuka, ta ce. “Deeni saboda ina tsoro. Ina fargaba da tsoron son da nake maka, so ne mai yawan gaske, son da yafi karfina, son da ya tilasta mini mika wuya ga soyayyar ka, so mai radadi da ciwon gaske. Ina tsoro Deeni idan duniya ta raba ni da kai fa? Ba zan iya wata rayuwar jin dadi ko sukuni ba tare da kai ba ba. Ina tsoron idan na bata maka fa na ki aurenka saboda wasu dalilai da nake ganin za su iya hana mu kasancewa tare? Deeni shekara uku nake baka kai saurayi ne, ni bazawara ce, iyayenka ma ba za su amo ba, nima in nayi haka ban maka adalci ba. Budurwa ya kamata ka nema ka aura ku more rayuwar ku tare”.
“Bana son budurwar, ke nake so. Bahijja ke nake so, ko shekara nawa kike bani ke nake so ki zama abokiyar rayuwata. Iyayena ba ruwansu da aurena, wacce nake so ita zan aura, kuma zanyi alfahari da auren mace irinki”.Deeni ina tsoro”.
Ta fada cikin murya dishashshiya.
“Ina tsoro Deeni, so na kake ko kuma ina cire maka kewar Farida ne? Ina tsoro wataran kaji kana da bukatar auren budurwa (I dont want to rubbish myself) wato ban son wulakanta kaina, bana so ka aureni saboda ka rasa Farida”.
“Ba haka bane Bahijja, ke kika ja hannuna
kika sa ni mancewa da Farida da soyayyar ta”.
“Wannan gaskiya ne, amma soyayyar da nake miki na fara ta ne lokacin da soyayyar Farida ta kare a zuciyata, ki yarda dani ba Farida a zuciyata ko kadan. Farida matar wani ce, uwar wasu ce, na shafeta a babin rayuwata, SHAUKI NA YA SAUYA tun tuni, idan kika rabu dani akan haka ba ki min adalci na, kuma za ki kuntata rayuwata, kyautar da kika min na farin ciki a rayuwata za ki kwace shi. In kika yi haka za ki kuntata mana duka.
Ki tuna kece me fadakar da mutane akan wannan matsalar, yanzu kuma da yazo kanki sai ki nemi kauce masa? Bahijja ina sonki, kina so na?”
Girgiza masa kai tayi alamar eh hawaye na zuba, ta kwantar da kai tana kallonsa tana jin sonshi kamar zai hallaka ta, wani so da bata taba sanin akwai irinsa ba.
Ta ce, “Ina sonka Deeni so na sosai, ina kishin ka, ba zan jure ba nan gaba in ka auro wata, saboda wani na kasu ko gazawa a tare da ni, Deeni bakin ciki zai kashe ni wannan ranar”.
Durkusawa yayi a gabanta ya ce. “Zan miki wani alkawari yau, ina kin yarda dani?
Ta girgiza masa kai. “Na baki kyautar kaina ke kadai, ba zan taba auren wata wai don saboda ina bukatar budurwa ba don kina bazawara, idan na same ki MISBAH bana bukatar wata mace”. Ya jawo (diary) din, “Gashi a rubuce, ni
Deeni mallakin Bahijja ne kawai”. Kallon shi take tana jin wani nutsuwa a ranta, yadda dai Deeni ta amince masa tasan mutum ne da yake yin abinda ya ce, haka soyayyar sa ba karya ba yaudara, mutum ne mai gaskiya da nagarta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tayi masa murmushi, “Deeni, ba sai ka rubuta ba, na yarda da kai, nima wannan halayyar taka ita taja hankalina gareka har na saki jiki da kai muka shaku. Sai dai nima zan rubuta maka na amince maka Deeni ka auri ko wacce irin mace a duniya in kana so, amma banda mutum daya Farida wacce nasan ka daina sonta, kuma matar aure ce. Amma ita ce mace daya da nake kishi a duniya, nake jin zafin kishinta a raina, saboda nasan irin soyayyar da ka mata ba na wasa bane. Idan kuwa wani kaddara yasa ka aureta to duk hukuncin da na yanke zaka amince da shi”.
Ya yi murmushi, “Bahijja na haramtawa kaina Farida tun daga lokacin da ta zama matar wani, ba ciwon sonta na yiwa jinya ba sai ciwoncin amanar da suka min. Amma duk da haka don ki samu kwanciyar hankali na amince”.
Tayi masa murmushi me cike da kauna tana masa kallon so, ta ce.
“Deeni komai kake so matarka ta maka zan
maka shi a rayuwa duk dadinsa duk wuyar sa”.
“Ina da yakini akan haka Bahijja, kuma nima zan miki duk wani abu da miji zai yiwa matarsa, zan zama miji nagari, mijin kwarai, uba na gari ga ‘ya’yanki MISBAH na, Abokiyata, matata
Dariya suka yi duka, sun jima suna hira sannan suka sai sallama da kyar kamar ba za su rabu ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Soyayya mai tsafta da tsananin shakuwa ya kullu tsakanin Deeni da MISBAHI, dukkansu suna son juna sosai so mai ban mamaki. Dukkan su kowa na aikinsa, sai dai wannan bai hana su bawa juna lokaci daga gidan gonar Deeni zuwa asibitin MISBAH ba, nisan sa bai wuce tafiyar kafa ba.
Haka wataran Deeni zai bar abinda yake ya je wurin MISBAII yana kallonta daga nesa ko da bata sani ba baya gajiya da kallon ta, haka kullum sonta karuwa yake a ransa. Tana masa wani irin kwarjini, ya dinga jin sonta yana tsuma

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE