MISBAH BOOK 2 CHAPTER 15 BY SA’ADATU WAZIRI
MISBAH BOOK 2 CHAPTER 15 BY SA’ADATU WAZIRI
Mun tsaya
Ita dai Bahijja kanta sunkuye har Mama ta fita, shiru taji gidan yayi alamar duk an fita wurin walima. Tana nan zaune shiru zuciyarta cike da tunani kala-kala taji motsin shigowa. Kamshin turarensa ya tabbatar masa da Deeni ne ya shigo dakin, nan tayi saurin daga kai suka yi ido biyu, yana mata wannan murmushin.
Ya zuba mata idanu itama ta kasa dage idonta a kansa, ya yi mata kyau sosai. Sanye yake da (blue) shadda kalar nata kayan ya sha aiki, shigar ta matukar kyau. Hular da ya kafa a kansa ta kara fiddo da kyan fuskarsa, gashin kansa kwance irin na Fulani sak, ga sajen da ya karawa fuskarsa kwarjini da annuri. Ji tayi tamkar ta je ta fada kirjinsa ta kwanta, amma sai ta kasa saboda kunya dukda
yana mijinta. Shi ya sa hannu ya jawo hannunta yana wasa da ‘yan yatsun ta, tsigar jikinta taji tana tashi tana jin sonsa da shaukinsa yana ratsa jijiyoyinta, yana bin jikinta.
“Haba MISBAH na, ya zaki kawar min da fuska, amaryata ki tuna fa ke halal dina ce yanzu, baki san irin jin dadi da tsananin farin ciki da fuskar ki ke sauke mini bane da baki kawar da ka gare ni ba. A yau sai naji soyayyar ki ta zama sabuwa, ta zama danya sharaf a zuciyara. Taho gareni, (please) Bahijja ko zan samu nutsuwa”.
A hankali cikin nutsuwa ta matso gare shi, ya jawota jikinsa tare da bata kyakkyawar runguma, tuni ta bace a cikin jikinsa, suna manne da juna tare da jin irin sona juna da sha’awar juna.
Cikin muryar rada yake mata wasu irin kalaman soyayya masu ta da hankali da tsuma zuciya da ruhinta. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Na gode Bahijja da soyayyar ki, wannan shi ne (the most beutiful moment of my life)”. Rufe ido tayi tana jin kalaman sa na ratsa ruhinta, tana shakar kamshin sonta tare da fadin.”Deeni ina sonka, kai nawa ne ni daya, mallakina ni daya”, Haka ne Bahijja ni naki ne ke daya kamar yadda kike ke tawa ce ni daya, bana taba hada ki da kowacce mace a duniya, haka ba zan taba hada soyayyar ki da kowa ba”.
Sun jima a cikin wannan halin na tsananin shauki da son juna. A hankali ta turo kofar tayi sallama amma
shiru, hakan yasa ta kutsa kai, Farida kenan. Gabanta ya mummunan faduwa, ya dinga bugawa da karfi ganin Deeni da Bahijja a hakan ya mummunan daga hankalinta.
Wani irin masifaffen kishi taji yana turnike ta, masifaffen kyan da ta ga sunyi da Deeni da Bahijja ya razana ta tamkar dama an halicce su don juna ne. Tsohuwar soyayyar sa taji ta taso mata kasa gani da jure soyayyar da taga Deeni yana yiwa Bahijja wanda ita duk tsananin soyayyar da suka yi a baya ta dinga gani kamar wancan soyayyar wasa ce.
Ya za ayi Deeni ya so wata mace a duniya fiye da ita? Ya za ayi Deeni ya ci amanar kauna? Na zata Deeni zai yi aure ne ba don soyayya ba sai don raya sunna kamar yadda nayi, ya za ayi Deeni
ya so wata fiye da ni? Har yau ban taba son wani fiye da shi ba, duk da nayi aure na zama uwa amma soyayyar sa bai taba barin zuciyata ba ko na (second) daya. Ya zanyi in rayu da wannan bakin ciki da bacin ran da na gani yanzu?”
Nan ta sake daga kai ta kalle su, har yanzu suna wata duniyar. Ta kalli kanta ta kalli Bahijja sai taga ta mata nisa, ta mata fintinkau nesa ba kusa ba.
“Shin ni ya aka yi na kasa hada Deeni da kowane irin namiji a duniya? Tabbas saboda Allah bai taba hadani da namijin da ya kaishi bane yayin da Allah Ya hada Decni da macen da ta fini”.
Kyau daga kai tayi taji hawaye na zuba mata,
tsananin kishi da son Deeni taji yana shigarta, ta mance da abinda ya kawota, ta mance da cewa ita matar wani ce, uwar wasu ce. Karar wayarta ce ta dawo da su hayyacin su duka, nan tayi saurin share hawayen yayin da Www.bankinhausanovels.com.ng
Deeni da Bahijja suka ganta ba zata a gabansu.
Ras! Bahijja taji gabanta ya fadi, ita ma din kishin Farida taji ya shigeta, har yau in ta tuno irin soyayyar da Deeni da Farida suka yi sai taji hankalinta na tashi. Deeni ganin Farida a gabansa ba zata tana kallonsa tamkar ta hadiye shi yasa ya ji ya shiga dan rudani, musamman da ya san yaddah Bahijja take da kishin Farida a zuciyarta, duk da ya sha nuna mata cewa Farida ba ta gabansa yanzu, amma ta kasa fahimta. Sam ko kadan babu ita a ransa, mamma ya rasa dalilin da yasa yaji yayi wani irin rudewa a wannan lokacin.
Bahijja na kallon irin rudewar da yayi yasa taji ranta ya mummunan baci, hankalinta ya tashi. Dukkan su idon su ya rufe da wani irin
kishi, musamman irin kallon da Bahijja ta ga Farida na yiwa Deeni. Yayin da Farida ta dinga jin kishin irin kallon da Deeni ke yiwa Bahijja. Nan Faridan ta daure, tayi dariyar yake, tace.
“Ango da Amarya, ina taya ku murna, Allah ba da zaman lafiya”.
Bahijja bata iya ta amsa ba, sai Deeni ne ya amsa a takice, ya sa kai ya fita.
Farida ta kalli Bahijja ta ce, “Amarya, Mama ta ce in fto da ke ana jiranki wurin walima”.Girgiza kai tayi da kyar ta cije tayi dariyar yake, ta fito suka jera tare.Tun -data fito idon kowa ya koma kanta ta fito ta haska wajen gaba daya kowa sai albarkacin bakinsa yake fadi, Mama kanta ta kasa hakuri, ta taso da fara’arta ta zo ta kama hannun Bahijja ta jata zuwa gun zaman ta. Wannan ya kara bakanta ran Farida, har agun Mama ma Bahijja ta ture gwamnatin ta.
Wani hawayen bakin ciki taji yana zubo mata, wurin walimar da bata zauna ba kenan, ta juya ta koma ciki, har aka tashi daga walimar bata dawo ba.
Ranar Lahadi jama’ar biki kowa ya watse, yayin da a ranar Lukman ya tare da Amaryar sa a gidansa da mahaifin su ya bashi, yayin da Shamsuddeen ya koma saboda aikin da ya bari a kamfanin su na Kaduna. Farida kuwa da yake ana hutu da yara za su zauna su yiwa Mama hutu.
Mama ta shiryawa Bahijja da Deeni kayan su, siyayyar da ta musu na kayan sawa da sauran su ta sa a mota ta tura tare da Baba Andi taje ta shirya musu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Gidan ya yi tsit ba kowa daga Farida da yaranta, sai Deeni da Bahijja wanda suma suna shirin tafiya nasu gidan. Alhaji ne ya kira Deeni da Bahijja falo suka same shi yana zaune shi da Mama, nan suka nemi wuri suka zauna. Alhaji ya yi musu nasiha da fada sosai tare da musu fatan alkhairi, haka Mama ta kara damka
musu amanar juna tare da musu nasiha da cewa
suyi hakuri da juna, zo mu zauna zo mu saba.
Alhaji ya mika masa (key) na gida. Ya yi murmushi, “Na gode Baba, mallaka min Bahijja da kayi matsayin mata ta kadai ya ishe ni babbar kyauta. Ka mata waliyyanci, ka zama mahaifinta, yayin da Bappah ya min waliyyanci. Na gode da amanar ‘yarka da ka bani Baba, ina da gidana mallakina na gidan gona wanda ka taimaka mmin na kafa shi, haka Bahijja tana da gida, za mu zauna a duk wanda muke so. A halin yanzu rayuwar mu soyayyar mu, ayyukan mu, gidajen mu da dukiyoyin mu suna hade ne. Baba, Mama, mun gode, kuyi ta mana addu’a, muma za muyi ta muku”.
Dariya suka yi yayin da ya ce, “Allah Ya muku albarka Deeni”. “Ameen”. Suka amsa a tare, sannan suka yi sallama da su Mama ta raka su har bakin mota ita da Bahijja kamar ba za su rabu ba
Wannan soyayya da shakuwa na Bahijja da Mama ba karamin dagawa Farida hankali yake ba, sai tana ji kamar ta zama ita bata da muhimmanci. Tabbas daga Farida har Bahijja suna fama
da kishin juna da ke tsananin cin su a zuciya Kai tsaye suka wuce gidan Deeni wanda ya tsara musu shi sosai, kana shiga gidan zaka fahimci gida ne na masu ilimi daga bokon har addini.
Tun a mota Deeni ya lura Bahijja bata magana, duk kokarin da yayi don ya takale ta amma bata kula shi ba, shima sai ya nuna mata halinsa, ya dage kai ya kyale ta.
Addu’a tayi sannan ta sa kafarta a gidan, wani irin kamshi taji yana tashi mai kwantar da zuciya. Ta lumshe ido tana shaka, nan take taji hankalinta na kwanciya, fushin nan da take taji yana sauka. A hankali ta dinga bi tana zaga gidan, Deeni ya bita da ido zuciyar sa cike da sonta da sha’awar ta.
Ko ina ta gama zagawa yana biye da ita, ta dawo falo ta zauna, nan ya jawo kujera ya zauna a gabanta yana kokarin su hada ido amma ta ki. Ya Www.bankinhausanovels.com.ng
yi murmushi, ya ce. “Haka kawai Amarya taji bata son sakar min fuska a daren mu na farko a gidan mu?”
Zuba mata ido ya yi yaji kamar yanzu ma ya fara sonta.
“Ina sonki Bahijja soyayyar da ban san irinta ba, komai kika yi a rayuwa sai inga ya miki kyau. Wannan kamshin da ake sha min ma sai naga ya miki kyau, kin kara burge ni”.
Nan ya sauko yasa kanshi bisa cinyoyinta, ya jawo hannayenta kansa. MISBAH na meye ya dame ki?”Ta kwantar da kanta a kan nasa suna manne da juna, ta ce.
“(My dear nice house)”.
Ya yi murmushi, ya ce, “Na tabbatar (you will be a good home maker)”.
“Inshaa Allah”. Ta amsa.Deeni ina sonka”.
Ta fada tamkar me yin rada a kunnen sa, yana jin muryarta na ratsa shi, yana jin tsigar jikinsa na tashi, tsantsar sha’awar ta cike fal zuciyar sa.”Bahijja ki kasence dani har abadakar ki
kyale ni, ki cika min gida da irin ki da albarkar ki, ki cika min gida dAyaran ki, za ki sani farin ciki sosan gaske”.
“Komai kake so zan maka Deeni, Allah Ya bani yaran da zan cika ma su. Nima ina addu’ar Allah Ya bani irin Deeni, Allah Ya bani ikon sanya ka farin ciki da kyautata maka, Allah Ya bani juriya akan ka Deeni.
Ina maka wani so Deeni, gashi dai ka zama nawa amma zuciyata na cike da tsoro da fargaba”. “Kar kiyi fargaba Bahijja, ni naki ne”.
Bai ankara ba sai ji yayi hawaye na zuba mata ya yi saurin dago ta hankalinsa a tashe My dear mene ne?”
Idonta, jawur ta kalle shi, “Ko zaka iya. fassara min rudewar da kayi lokacin da kaga Farida? Na mene ne? Don kaji tsoro masoyiyar ka ta ganmu a manne da juna ko kuma ka rude ne saboda ka ga tsohuwar masoyiyar ka?”
Zura mata ido yayi cike da mamaki, “Haba Bahijja, ban zaci haka daga gareki ba, wannan halin na zace shi ne daga halin wata me kasa da shekarun ki, (be matured)”.ba
Ranta taji ya mummunan baci, tace. Www.bankinhausanovels.com.ng
“(I will not be) me kake nufi? Me syasa kake (avoiding) tambaya ta? Ka fada min wane irin rudewa kayi don kaga Farida?”
Ranshi yaji ya fara baci, amma sai ya daure,yace
“Ke kinga ya dace mu zauna muna bata lokacin mu a irin wannan lokaci akan wannan maganar mara tushe ko kan gado? Me ya kawo maganar Farida tsakanin mu a yanzu?”
“Akwai abinda ya kawo, ka ban amsa, me yasa mijina zai rude don yaga tsohuwar budurwar sa?”
“(For God sake) Farida matar wani ce, uwar wasu ce, saboda mene ne zaki ta da min rigima yanzu? Har sau nawa zan fada miki cewa bana son Farida, na manta da Farida. ada baya can na so Farida ne da za ki dinga daga min hankali akan Farida? Haba Bahijja, a yau zamu fara sabuwar rayuwa, ya zaki bari wani dalili mara tushe ya nemi kawo mana matsala?
To naji ya ishe ni haka, kije kiyi tunanin duk yadda ki ka ga dama, na ganta na rude sai yaya?”
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG