MISBAH BOOK 2 CHAPTER 16 KARSHE BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH BOOK 2 CHAPTER 16 KARSHE BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya 

Akwai abinda ya kawo, ka ban amsa, me yasa mijina zai rude don yaga tsohuwar budurwar sa?”
“(For God sake) Farida matar wani ce, uwar wasu ce, saboda mene ne zaki ta da min rigima yanzu? Har sau nawa zan fada miki cewa bana son Farida, na manta da Farida. ada baya can na so Farida  ne da za ki dinga daga min hankali akan Farida? Haba Bahijja, a yau zamu fara sabuwar rayuwa, ya zaki bari wani dalili mara tushe ya nemi kawo mana matsala?
To naji ya ishe ni haka, kije kiyi tunanin duk yadda ki ka ga dama, na ganta na rude sai yaya?”

Cikin zafin rai da bacin rai yake maganar wand ya kara tunzura Bahijja, ya kona mata zuciya. Ta fashe da kuka ta nufi daki ta rufe.
Bai yi yunkurin binta ba don shima yana cikin zafi, ya zurawa abubuwan da ya shigo musu da shi na ci da sha, duk ta daga musu hankali har ya ji bashi da sauran sha’awar cin wani abu.
Kukanta yaji yana matukar daga masa hankali, ga sonta dake Kara ruruwa a cikin zuciyar -sa, amma zafin zuciya ya hana ya bita daki balle ya yi lallashi. Haka ya dinga kaiwa da kawowa cikin dare, ya rasa me ke masa dadi, haka suka kwana baran-baran a daren su na fako.


An kira sallar asuba ya yi alwala ya murda kofar dakinta, ga mamakinsa bata sa key baya sameta zaune kan salla. Bai ce mata komai ba ya fice zuwa masallaci, ya dawo ya nufi nasa dakin, duk da ya kwana ba bacci kirki amma haka baccin ya gagare shi.
Karfe takwas na safe ya fito falo, anan suka yi kicibis sanye da hijabinta. “Ina kwana?” Ta fada tare da dauke kai.
Bai amsa mata ba ya sha gabanta, tayi saurin kaucewa ta kama hanyar fita.
“Ina za kije?” Ya fada cikin daga murya.
Www.bankinhausanovels.com.ng
“Cidana zan tafi”. Ta bashi amsa a takaice. “Da izinin wa? Da yardar wa? Kar ki manta baki da gidan daya wuce wannan, sannan fita a gidan nan ba da izinina ba, kar ki sake wannan kuskuren”.
Ya fada cikin tsari gida fuskar sa ba alamar
wasa, ya juya.
Wani irin bacin rai da takaici taji ya turnike ta, ta juya ta nufi kicin ranta ɓace ta dinga kaiwa da kawowa, gata ba gwana ba wurin girki, da kyar ta samu ta hada masa (patatoes) da (source) tare da yanka (fruit) da (fresh juice) da kuma ruwan (tea) a (flask) tare da sauran kayan (tea), ta jera kan (dinning table).
Yayin da Deeni yake kaiwa da kawowa, sam bai ji yadin yadda ya mata ba, to amma yana da matukar muhimmanci tasan cewa shi mijinta ne, aure suka yi, ba zata yi yadda take so ba. Haka nan zafin zuciya da jin kai ya hana shi zuwa ya lallashe ta, don shi gani yake bai mata laifi ba.
Bahijja na shiga daki ta fashe da kuka, nan ta duako (diary) din nan ciki jakarta ta rungume tana kuka.
Hankalin sa ya kasa kwanciya har sai da ya bita dakin ganinta rungume da (diary) din tana
Www.bankinhausanovels.com.ng
kuke sosai ya taba zuciyar sa. Abu biyu ne suka hadu masa, tsananin sonta da tausayinta da kuma wani zafin kishi, saboda yasan me ke cikin wannan (diary) din.
Nan ya daure ya isa gareta ya jawota jikinsa, nan ta hau kokawar kwace jikinta amma bata yi nasara ba. Ya rufeta ruf kan faffadan kirjinsa, ga turaren sa mai hade da kamshin son sa da ke ratsa ta, yana kashe mata jiki, kawai ta fashe masa da kuka.
“(I’am sorry my dear) nayi laifi, kiyi hakuri”.
Ya fada cikin murya mai taushi da lallashi. “Bahijja hawayen ki da kukan ki yana daga min hankali fiye da komai, kin san yadda nake matukar jinki a raina, kin san yadda jiki da ruhina tare da zuciyata suke tsananin sonki, (please) Bahijja kar ki daga mana hankali daga ni har ke. Ba mai samun farin ciki a kan wannan halayya taki na kishi (I’am sorry I hurt you).
Bahijja da ina da ikon share baya da na share, amma bani da wannan ikon, abinda zan iya shi ne yanzu-yanzu kuwa da nan gaba duk kece. Bahijja ina so kamar yadda kika taimaka min na manta baya na cigaba da rayuwata ina so ki
Www.bankinhausanovels.com.ng
taimaka ki bani hadin kai, mu shirya rayuwar mu mai cike da tsabtatacciyar soyayya da fahimta tare da kula da farin cikin juna.
Ina so ki sani kina da matukar muhimmanci a rayuwata, (please dont make me hurt you again)”.
Ta fashe da kuka, “Deeni na gaza ban san me yasa na kasa jurewa ba, ban san me yasa nake jin tsananin kishin Farida ba, duk da na sani matar aure ce, matar dan uwanka ne, . Deeni ka taimake ni, zan iya jure komai amma banda wannan”.
Ta dago dara-daran idanunta wanda suke rine, suka dawo ja, hawaye na zuba wanda yanayinta ba karamin tsuma shi yayi ba, ta ce, “Deeni kasan ina sonka ko? Ina sonka sosai”.
Ya girgiza mata kai yana jin tamkar ya hadiye ta don so, ya ce. “Nima ina sonki Bahijjakin san haka. Ina
sonki”. Ta kankame shi, “Na sani Deeni, (please) ka kula dani”.
Zan kula da ke Bahijja na, bari ma in fara daga yanzu”.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan yasa baki yana lasar hawayenta tare da bin fuskarta, kan idanunta ziwa wuyanta yana sumbata. Haka ya dinga bin jikinta.
Wani irin abu taji yana zaga jikinta har zuwa tsakar kanta, yayin da ta dinga jin wannan kuncin yana barin zuciyarta, sai tsananin so da shaukin sa, taji zuciyarta ta wanke tas. Nan ta biye masa itama tana ramawa kura aniyarta.
Sun jima manne da juna sannan ta zame jikinta a hankali ta nufi bayi don shirya masa ruwan wanka, yayin da Deeni ke kwance idonsa jawur, hankalinsa tashe. Kwarai ya so kasancewa tare da ita yau, saidai so kasancewar sa Bahijja na farko ya zamana a
wuri na daban lokaci na daban.
Karfe goma Mama ta turo musu da (break fast) kala-kala, sannan tayi waya suka gaisa ta kara da cewa su shirya jirgin su zuwa kasa mai tsarki, wato Saudia. Karfe sha biyu ne wanda ta biya musu suje suyi Umra su kara yiwa Allah godiya tare da yin addu’o’i, sannan daga nan in suna so su wuce duk kasar da suke so su zaga duniya har na wata guda, sannan su dawo.
Www.bankinhausanovels.com.ng
A kasa mai tsarki Deeni da Bahijja suka san sirrin juna, suka zama abu guda, suka barji gumin juna. Kwarai sun more rayuwar su yadda ya kamata.
Bayan sun gabatar da ibadar su ta Umrah tare da yin addu’o’in su, nan suka ci gaba da gudanar da ibadar su na aure, sun manta duk wani damuwa da ɓacin rai da tashin hankali da suka taba fuskanta a rayuwa, suka bude sabon rayuwa mai cike da farin ciki da kwanciyar hankali tare da yiwa juna alkawarin kula da juna da kuma kasancewa da juna har abada inshaa Allah.
Bahijja na da kyau na daukar hankali, kyau mai sa nutsuwa da kwanciyar hankali ga wanda ya mallake ta, yasan sirrin ta, ya dandani zumar ta. Don haka Deeni ya tabbatar shi din mai sa’a ne da ya mallaki mace kamar ta.
Duk inda ake son mace Bahijja ta kai ta kawo, sai dai abinda yake kara jan hankalin sa gareta da kara masa sonta shi ne halayyar ta, hikimar ta da baiwarta. Yadda take kula da shi, take sarrafa shi da rayuwar sa, irin soyayyar da take masa, take kuma nuna masa, ga wata girmamawa ta musamman. Duk da kasancewar
Www.bankinhausanovels.com.ng
ta girme masa amma bata taba nuna masa raini ba, asali ma in ba an fadi ba babu mai cewa ta girme masa, saboda bala’in dacewa da suka yi da juna.
Halayyar su ta zo daya, tunanin su ya zo daya, duk abinda daya ke ji da shi daya na ji da shi. Don haka suke yawan hakuri da juna, in daya ya hau daya na dannewa, sun zauna sun tsara yadda za su gabatar da rayauwar su cikin soyayya da saukin rayuwa.
Bayan sunyi sati biyu suka bar Saudia zuwa Dubai, sun zaga kasashe uku zuwa hudu suna yawon shakatawa da more rayuwar su. Sunyi wani irin sabo da kara shakuwa da juna sosai-sosai.
Sun kasance cikin fari ciki marar
misaltuwa, watansu guda suka tattaro suka dawo gida Nigeria.
A nan suka tarar da mummunan labari da kuma mummunan tashin hankali na rasuwar Shamsuddeen tare da mahaifin Farida.
Satin su biyu da tafiya hatsarin ya faru da su a cikin garin Kaduna, mahaifin Farida ya je duba Shamsu a ma’aikatar su don ganin ya yake
Www.bankinhausanovels.com.ng
da yadda ayyukan su ke tafiya, dama ya saba kai masa irin wannan ziyarar. Anan Shamsu ya bar motarsa a (office) ya biyo Alhaji Ahmad don dawowa gida tare, a hanyar su ta dawowa tsautsayi da karar kwana suka hadu da doguwa ta taho ba birki ta hada motoci da yawa tayi barna wasu sunji rauni wasu sun rasa rayukan su ciki har da Shamsuddcen da Alhaji Ahmad.
Cikin tashin hankali da damuwa Deeni da Bahijja suka nufi Kaduna inda ake zaman makoki.

Hmm Mu hadu a littafi na uku donjin yaddah wannan littafin zaici gaba da kayawa

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE