MISBAH BOOK 2 CHAPTER 4 BY SA’ADATU WAZIRI
MISBAH BOOK 2 CHAPTER 4 BY SA’ADATU WAZIRI
Mun tsaya
ai indai wanda ta karanta (file) dinsa ne (case) dinsa ba haka bane, abinda (report) dinsa ya ce daban abinda kuma Doctor ya fada mata yanzu da irin (treatment) din da suke masa daban.Bahijja”.Muryarsa ta katse mata tunani.Kina jina kuwa?” “Eh ina ji”.
Ta fada cikin muryar damuwa, sannan tace
“To yanzu wane shawara ka yanke? Me kake ganin zaka masa?” “Shawarar da muka yanke yanzu ni da
Doctor Yasir shi ne, zamu masa (E.C.T)”.
Tace “Whattttttt!”.
Ta fada da karfi cikin zare ido tamkar yana ganinta, hankalinta ya tashi.
Ta ce, “(Please) Doctor kar kuyi masa, kasan (dangers) na wannan (therapy) din”. “Bai kai (stage) din da za a masa haka ba?””Da hankalin ka, da tunaninka?”
“Me kike nufi? Kina so kice bani da hankali ko ban san me nake yi ba? Laifina ne ba naki ba da na fada miki, dama na lura komai ke kina son nuna kin fi kowa sani”.
Tayi kasa da murya, “Kayi hakuri (my dear) ba haka nake nufi ba, nasan ka fini, kasan komai, amma ina so ka fahimci (danger) din dake cikinsa ne, kar muyi wasa ko garaje da rayuwar wasu. Ka luna amana da yarda yasa iyaye da ‘yan uwa ke kawo mana marasa lafiya, kasan yadda (electro convulsive therapy) yake, idan ya yi (seizing) kwakwalwar sa gaba daya fa?
A tunanina baya bukatar wannan, ina ganin (right medication) da (couseling) ya ishe shi ya dawo dai dai, wato maganin da ya dace”. Maganganunta yasa shi kasala, ya ce.”Na bugo ne ki ban kwarin gwiwa ba kisa na karaya ba, ni kike yiwa maganar (right medication)? Don baki ganshi a gabanki bane da irin kokarin da nayi akansa da ba zaki fara fada min haka ba”.
“Doctor (duty) na ne in tsaida ka, (please) na rokeka kar kayi, ka sake tunani”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kashe wayar yayi ya kyaleta cikin rudani tana ta buga wayar tana ihun kar yayi amma bai dauki wayar ba ma. Hankalinta ya matukar tashi, ba shiri ta duaki hijabi ta nufi cikin asibitin da sauri.
Sai dai kafin ta zo Doctor Yasin ya yi nasara akansa na cewa. “Kasan halin mata da tsoro, da gajeriyar
kwakwalwa”, don Ya amincc amma maganar Bahijja da dalilan da ta bashi na yawo akansa, don kuwa yasan matarsa Bahijja ba ta cikin mata masu tsoro ko gajeriyar kwakwalwaa da yake ya riga da ya yanke hukuncin sai ya yi din. Don haka kafin Bahijja ma ta iso sun riga da sun yiwa Deeni abinda suka yi niyya.Yana kwance a wurin kamar gawa, dukkan gaboɓin jikinsa sun amsa, duk jikinsa ya sassake, bawan Allah shi kadai yasan wahalar da yasha. Gashi jikin Deeni jiki ne da bai saba da wahala ba, bai ma santa ba gaba daya don haka abin ya fi wahalar dashi fiye da yadda ya kamata. Tuni ya manta kansa da duniyar da yake ciki.
A lokacin da Bahijja ta shigo zama tayi ta kama kai tana kuka. Doctor me yasa kayi haka? Why?”Tuni ya harzuka, “Me kike nufi da (why)?
Ban san me nake yi bane? Me kike so kiyi (proving) da kika shigo kina min tsawa gaban abokan aikina da ma aikatana? Me kike ji da shi? Wa ya baki izinin fitowa ki zo?”
Doctor (please)”.
Ta fada cikin kwantar da kai.cl
“(This is not you) wannan ba kai bane, ba haka na sanka ba, kai mutum ne me taka tsan tsan da rayukan al’umma. Wannan ciwon nasa da ya zamo maka sabo ba firgita ka ya kamata yayi ba, ko kuma wani abin cewa sai naga ya warke ko ta halin kaka kar ace na gaza,Ka tuna asalin (purpose) dinmu shi ne mu taimaki mutane ba mu wahalar da su ba, ba muyi wasa da rayukan su ba. Yaushe tunaninka ya kauce, ya canja? Yau ina cikin bakin ciki da na kasa tsai da ka, na kasa hana ka yin abinda ba dai dai ba, sai addu’ar Allah Ya tashi kafadar wannan bawan Allah”.
Bai kulata ba sai sa kai da yayi ya fita cikin ɓacin rai, yayin da sauran suka rufa masa baya. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta mai da hankalinta kan Deeni, taje tayi dukkan iya kokarinta domin ta samu ya dawo hayyacinsa, ya farfado kafin ya yi nisa. Sai da ta dauki tsawon awa uku akansa kafin ta samu ya bude ido sannan ya sake rufewa, numfashinsa ya daidaita. Sannan ta dan samu kwanciyar hankali da nutsuwa kadan, ta koma gida hankalinta a tashe, tayi ta fama da Doctor Mislihu.
Fada yake mata ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba, ta lura yana cikin tsoro da tashin hankali, sai dai yana kaucewa hakan da fada.
Bata ce masa kala ba sai rungumar sa da tayi sosai a jikinta, ta riga da ta fahimci (fears) dinsa da tashin hankalin da ya shiga.Kwantar da hakalin ka, Inshaa Allah komai zai dai daita, baa abinda zai faru (he will be fine). Kuskure ne kowa yana yi a rayuwa, sai dai muyi kokarin kare faruwar haka a gaba. Bamu da damar yin wasa da rayuwar wasu”.
“Bahijja ban san me ke faruwa ba, na kasa gane komai. Nasan cewa duk wani (treatment) da nake masa dai dai ne, sai dai ban san me yasa ba ya (responding) ba, kuma ban yi niyyar wasa da rayuwar sa ba har zuci, ina son taimakonsa ne. Ina ganin wahalar da yake sha, ina jinsa kamar dan uwana, sannan ina son taimakon mahaifinsa shi yasa duk abinda zanyi ya kare na dauki wannan (option) din. Ban yi tunanin komai ba, sai dai nasan wannan a cikin (shock treatment) wannan (is the most safest and effective)”.”Na sani my dear, amma wannan ciwonsa (disorder) din da yake da shi ba na wannan (treatment) din ba ne. A ganina kun yiwa abin gaggawa, kuma naga kamar baku yi shi dai dai ba, dole akwai wani kuskure a wani wurin (something wrong somewhere). Wa ya baka wannan (idear) din?””Doctor Yasir”. Ya fada kai tsaye. Ta dafe kai cikin takaici, ta ce.
“Har yaushe ka fara amfani da basirar Www.bankinhausanovels.com.ng
wasu maimakon taka?””Kin san mutumin nan likita ne dan uwana, meye a ciki in munyi (studying case) na mara lafiya, munyi (sharing idear)?” “Ba laifi bare amma abin akwai daure
kai”.A wannan dare daga Dr. Mislihu har Bahijja ba wanda ya runtsa, suna tunani tare da juya al’marin a cikin ransu wanda Dr. Mislihu ya kasa jurewa gari ya waye, a daren ya fita domin zuwa ya sake ganin Deeni. Ga mamakinsa yana kofar shiga dakin, yaji muryar Doctor Yasir da wasu ma,aikatansa guda hudu wanda amintattun ma’aikatansa ne, yaji yana raba musu kudi na aikin da suka masa. Na farko sunyi ta canja duk wani magani da allurai da yace su kawo a dinga bawa Deeni. wanda wannan yasa jikin Deeni ya kara rikicewa maimakon samun sauki. Saboda yana so ya ɓatawa Dr. Mislihu suna don ya jima yana jin haushin cigaban da ya samu ya barshi.Abu na biyu shi ya so Alh. Umar ya damkawa Deeni a asibitin su saboda ya ci kudinsa sosai, amma sai Alh. Umar ya ci mutuncinsa ya ki. Tun daga lokacin ya dau alwashin sai ya dau fansa, kuma ya batawa Doctor Mislihu suna. Don haka ya bawa ma’aikatansa cin hanci.
Da farko sun ki, amma ganin yawan kudin da ya saye imanin su suka manta amana da yardar dake tsakaninsu da mai asibitin. Ya ce kuma in aiki ya yi zai kara musu.
Lokacin da Dr. Mislihu ya gama jin abinda suke fadi ya ciro wayar sa ya kira (police) sannan ya kira Bahijja yana fada mata.
“Doctor Yasir ya ci amanata, Bahijja
gaskiyar ki ne, akwai abinda ya faru wanda ban fahimta ba sai yanzu”.
Yana cikin magana da ita ya jiyo motsin su za su tafi, ya yi saurin banko kofar, bai bata lokaci ba ya cakumo wuyan rigarsa tare da shakure masa wuya yana zaginsa.
“Yau sai na kashe ka, maci amana. Ku kuma sai nasa an kulle ku, kun ci amanar yardar da nayin wasa da rayuwar wani saboda abin niya”.
Ganin yadda ya haukace musu Dr. Yasir yace “Ya zama dole muyi maganinsa kafin asirinmu ya gama tonuwa
Tuni suka hadu akansa, hayaniyar su ya ta Deeni, yayin da yake ganinsu hazo-hazo, duk baya magana da Dr. Yasir ya saba da shi da yadda yake masa. Sannan da ikon Allah da taimakon da Misbah tayi masa ya masa amfanin, dawo hayyacinsa.
Ganin yadda suka toshe bakin Dr. Mislihu suna dukansa tare da kokarin toshe masa hanci sa ya mike ya nufi inda wani bell yake wanda ake danna wa in ana danger , ya yi saurin dannawa, anan daya ya hango shi yayi kansa, suna ta kokawa, yayin da Dr. Yasir ya dauko wani almakashi ya soma cakawa Dr. Mislihu tuni jini ya wanke wurin. Yana kokarin guduwa ya ya ceci kans ko ta halin kaka, domin yasan in mislihu ya kubuta to asirinsa zai Www.bankinhausanovels.com.ng tonu.Deeni bai san yaushe ya bude baki a firgice yana ihu tare da neman taimako ba, yana fadin.Misbah
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!”.
Nan suka yi saurin toshe masa baki da hanci har ya sume a wurin, a tunaninsu ma ya an mutu ne. Za su fita kenan sai ga ‘yan sanda sun iso, kafin su gudu kuwa aka cafke su, yayin da aka yi kokarin daukan Doctor Mislihu zuwa (emergency) tare da Deeni.
Lokacin Bahijja ta iso a rude tamkar ramahaukaciya, ganin Mislihu cikin jini ya bala’in firgita ta da razanata. Tashin hankali ne wanda bata taba fuskantar irinsa ba, duk kuwa karfin hali da karfin zuciya irin nata a wannan rana sai da ta karaya, hankalinta ya nemi barin jikinta.
Tayi kan Dr. Mislihu jikinta na bari, ta rasa ma me zata mishi? Ta rude sai kiran sunansa take tana salati.
Tare aka yi wani asibiti da su da wasu ‘yan sanda don basu taimakon gaggawa, likitoci sunyi kokarin tsai da jinin dake zuba a jikinsa wanda a wuyansa suka caka masa da gefen ciki amma jinin bai tsaya ba, haka aka dinga masa kari wani na fita wani na shiga. Suna iya dukkan kokarinsu akanshi. Bahijja dai alwala tayi ta zo ta fara sallah,
daga karshe ta hau addu’a saboda ta rasa nutsuwar yin sallah. Wani likita ne ya zo ya kirata mijinta yace yana son ganinta. Jiki a sanyaye ta isa dakin tana kuka kamar ranta zai fita, ya kalleta cikin galabaita da kyar ya iya bude baki. Yace Www.bankinhausanovels.com.ng
“Kar kiyi kuka Bahijja, ko yanzu ko bayan raina, kituna yanzu nauyin asibiti da sauran al’umma da ke cikinsa na kanki, ki tuna mafarkin mu ne da burin mu wannan asibitin. Sai dai ki kula kar abinda ya faru dani ya faru da ke, mutum yana nan yana rayuwar sa bai damu da wani ba ashe makiya suna nan sun sa masa ido suna neman yadda za su cutar da shi.
Ki tuna nauyin asibiti da Muhammad na kanki, sannan in bani da rabon haduwa da Mama in ta zo kun hadu kice ta yafe min”. Bahijja dai kuka take kamar zata hallaka, ga tsoro da fargabar rasa mijinta, ga maganar sa mai kama da bankwana, ga azabar ciwon da ta ganshi a ciki,
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG